Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kunya ka rike yarinyar nan da kyau da amana" kansa a kasa ya amsa masa. "Insha Allahu xaku yi alfahari da auren nan Abba, fatana dai ku cigaba da yi min addua" "Addua Kullum a cikinta muke, fatan mu dai Allah ya tabbatar da alkhairan da ke ciki ya kade dukkan sharri, gobe idan Allah ya kaimu xan kira babanta na shaida masa, daga baya kuma sai mu je mu yi magana ido da ido" xuciyar ya sadeeq fes ya tashi ya bar dakin. da tunanin maganar da Abba ya fada masa ya kwana, ya kosa gari ya waye yaji amsar da ta fito daga gidan su Nauwar duk da cewa dai yasan baxa su hana shi aurenta ba. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:18 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣3⃣ Nauwar da saimah ne suka fito da sauri daga dakin su dakin mama suka nufa inda suka mika mata wayar da ke hannun su tare da cewa Ammi ce xa tayi magana da ke, karbar wayar tayi ta kara a kunneta tare da yin sallama cike da annashuwa suke magana, a nan Ammi ta shaida mata cewa Jibi Nauwar xata taho gida, mama bata so tafiyar Nauwar ba amma dole ta hakura sbd yanxu ita ce 'ya daya tilo da tayi ragowa a wajen iyayenta, a ranar mama ta bawa Nauwar kudi inda saimah ta rakata kasuwa suka yi siyayyar tafiya. Ya sadeeq ne xaune a Office gaba daya yau ya kasa sukuni jira kawai yake yaji sakamakon da xai fito daga bakin Abba, gashi har karfe hudu na yamma Abba bai kira shi ba, tashi yayi ya nufi gida don yau yana jin baxai iya aikata komai ba indai bai samu muradin xuciyarsa ba, A hankali cike da nutsuwa yake tuki, addu'a kawai yake yi, Allah yasa yaji alkhairi daga bakin Abba, yana isowa kofar gida ya fito daga motar, sai da ya tsaya yayi tunani na wasu yan mintuna sannan ya karasa cikin gidan, tarar da su saimah yayi suna ta fito da kayan da suka siyo a kasuwa, a hankali ya nemi gefe ya xauna kusa da mamah, jujjuya kayan ya shiga yi yana yaba kyan su, A hankali ya mayar da kallonsa ga mamah, tare da tambayarta ina Abba yake, cikin nutsuwa ta bashi amsa da yana cikin daki. wani farin ciki da dadi ne suka sauka a cikin xuciyarsa, cikin nutsuwa ya mike yana taku a hankali har ya isa bakin kofar dakin, tsayawa yayi ya gyara tsaf, sannan ya taka a hankali ya shiga dakin tare da sallama, a kashingide ya iske Abba yana laxumi, dagowa yayi tare da amsa sallamar. wajen xama yaya sadeeq ya samu, kansa a kasa yake magana. sannu da hutawa Abba ranshi a sake ya amsa masa da yawa Saddeequ ya aikin, ashe har ka dawo dagowa yayi tare da sakin takaitaccen murmushi. eh nima yanxu na shigo Abba. murmushi Abba yayi tare da duban ya Saddeeq. "nasan dai tatsuniyar gixo bata wuce ta koki, a kan maganar nan kaxo min nan, wato kaji shiru har ka kosa kaji abinda muka yi da su ko" dago kai yayi tare da sosa keya. "aa Abba dama naxo ne na gaisheka ne naga tunda na shigo ban ji motsinka ba, amma dai har da wannan maganar ma, ya ku ka yi da su Abba" duban shi Abba yayi yana murmushi. Allah ya shirya mana ku yaran xamani, yanxu yaro da kansa yake xuwa jin labarin auren sa mu kuwa a da sai dai a yi mana komai, har amaryar ma wani lokacin bai fi sau daya xaku hadu ku gaisa ba,daga nan sai aure kawai. numfashi Abba yaja sannan ya cigaba da magana. "na kira mahaifinta mun yi magana da shi ta fahimta, ya fada min cewa........." saurin dagowa ya Saddeeq yayi don jin abinda xai fito daga bakin Abba. Abba ya lura da yanayin yadda ya saddeq ya kosa yaji yadda suka yi. "ya naga har ka tsorata saddeequ tun kafin na fada maka abinda yace dani" A hankali ya dago manyan idanunsa, tare da yin dan murmushi. "ba tsorata nayi ba Abba" "yauwa yaron kirki a harkar aure babu tsoro, kowa rabonsa xai aura babu wanda xai auri matar wani kaji ko" amsa masa yayi da to sannan ya cigaba da magana. "ya shaida min cewa yarinyar nan suna soyayya da wani dan uwanta wanda dashi suka xo gidan nan, nasan ma ka ganshi" wani kishi da bakin ciki ne suka tokare makogoron ya sadeeq da kyar ya iya amsawa Abba da eh. "to wannan yaron shi ne yake sonta tun tana yarinya kuma ita ma ya tabbatar min da cewa tana son shi, dan sun shaku sosai sai dai kawai ba a yi maganar auren su ba, yace idan kana ganin xaka iya shigowa cikin manemanta sai ka shigo yana maraba da kai, ya tabbatar min da cewa babu alfarmar da xamu nema a wajensa ba tare da yayi mana ba,idan kana ganin xaka iya neman aurenta to kofa a bude take" wata Ajiyar xuciya ya sadeeq ya saki, idanunsa sun yi ja, ya dago ya dubi Abba. "to shikenan Abba Allah ya xaba mafi alkhairi amma ina ganin kafin lokacin ya kamata nayi istikhara na nemi xabin Allah ina ganin xai fi sauki" ba karamin dadi Abba yaji ba shi yasa yake son sadeeq sbd hangen nesan sa, cikin farin ciki ya bashi amsa. "hakan yana da kyau sadeeq Allah yayi jagoranci" amsawa yayi da aameen. jikinsa a sanyaye ya fita ya bar dakin, ba karamin tafasa xuciyarsa take yi ba, ya tsani hada taraiya da wani a kan abinda yake so, gashi har wani ya shiga xuciyar yarinyar da ya gama tsara rayuwarsa da ita, tunanin ta inda xai fara bullowa lamarin ya shiga yi, dakinsa ya bude yana shiga ya fada kan gado tare da runtse idanunsa ko xai ji saukin hayakin da ke taso masa daga kasan xuciyarsa, xikirin Allah ya fara yi, sbd shi ne kadai abinda xai saukaka masa damuwrsa domin yanxu ji yake gaba daya duniya tayi masa xafi babu wani abu da xai faranta ransa idan ba xikirin ba. *Jeeddahtulkhair😘🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣4⃣ Kansa ne yake rika juyawa a hankali ya tashi xaune ya dafe kan nasa tare da rungumar pillown da ke hannunsa, innalillahi ya shiga ambata, bai san inda xai tsoma rayuwarsa ba idan har aka ce ya rasa Nauwar, lokaci guda ta shiga xuciyarsa ta samu gurin xaman da fitarta sai an sha wuya, ba karamin axaba rayuwarsa xata fada ba idan aka ce wani ya kwace masa abar kaunarsa, a hankali ya ja jiki ya shiga bayi ya daura alwala ya fara jero nafila rokon Allah yake yi sosai har da xubar da hawaye yana neman agaji, ya bashi nasara a bisa abinda yasa gaba sannan ya xaba masa abinda ya fi xama alkhairi a gare shi, yana gamawa ya shafa ya nemi guri ya cigaba da xurfafa tunanin guguwar da take shirin tunkaro shi. Har bayan sallar magarib yana daki ya kasa yin katabus idanunsa sun yi jawur,da ganinsa yana cikin tsananin damuwa, kamar daga sama yaji mama na kwala masa kira, da hanxari yaja jiki ya shiga cikin gida a bakin kitchen ya sameta, da flask din abinci a gabanta, tunda ya nufo wajenta ta bishi da wani kallo mai cike da ayoyin tambaya jikinta ya bata dan nata yana cikin matsananciyar damuwa, duk wani walwalarsa da nishadinsa sun ragu, ganin kallon da take masa ne yasa ya karfafa jikinsa tare da sakin rai yana fara'a ya karasa wajenta, tsugunnawa yayi yana fuskantarta. "gani mama" cike da damuwa da halin da yake ciki ta bashi amsa. "me yasa yau ka shige cikin daki ban ganka a cikin yan uwanka ba, bana xaton yau a jama'i kayi sallah, sannan ga abincinka har yana shirin salamcewa amma babu labarin xuwanka duk da cewa nasan baka wasa da cikin ka, fada min abinda yake damunka"? hadiye damuwarsa yayi ya saki rai yana mata magana "babu Abinda yake damuna mama kawai dai bana jin nishadi ne yau din nan" hade rai tayi babu alamar wasa a tattare da ita. "ka fada min gaskiya sadeeq bana son boye-boye ni mahaifiyarka ce duk wani abu naka na sani, nasan farin cikinka nasan akasin haka kaga kuwa babu abinda xai canja a tattare da kai ba tare da na gane ba, dan nasn halin dana sarai ba mutum ne mara son jama'a ba" kasa mallakar xuciyarsa yayi, kafin kace me hawaye ya cika idanunsa tuni ya fara kwarara a saman fuskarsa. hankalin mama a tashe ta dago fuskarsa tana tambayarsa. "lafiya Abubakar me ya faru da kai, ko dai korarka aka yi a wajen aiki" saboda bakin cikin da ya cika xuciyarsa ya kasa magana, rarrashinsa mama take yi kamar yaron goye, sai da yayi kukansa ya koshi ya share hawayensa sannan ya fara yi mata bayanin dalilin kukan nasa, cike da tausayawa ta dube shi. "kayi hakuri sadeeq idan Nauwar rabonka ce xaka samu, nayi mamakin yadda yarinyar nan ta shiga ranka haka lokaci guda, kai da baka sa abu a ranka,kuma damuwa bata hanaka walwala, dan Allah ka saki ranka muna nan muna yi maka addu'a Allah xai xaba maka mafi alkhairi, banda abinka ma yarinyar da ba aure aka daura mata ba kawai cewa aka yi fa da wanda yake sonta, kana da damar da xaka bayyana mata soyayya, idan rabonka ce sai kaga ka aureta har ka haifa min yan jikoki" ta karasa maganar tana murmushi. shi ma ya sadeeq murmushin yayi saboda ba karamin faranta masa mama tayi ba da ta ambaci yayan da xai samu a jikin Nauwar, lallaba shi ta rika yi har sai da ya saki ransa ya ci abincin sosai ya manta da duk damuwar da ta dame shi. yau ta kama litinin kuma ita ce ranar da Nauwar xata koma gida, tun safe ta kammala shirye-shiryen da xata yi, tana daki ta xuba tagumi tana kukan rabuwa da gidan su saimah, ita ma kukan saimah ke yi saboda ba karamar shakuwa suka yi da juna ba, kiran sunan su Abba yayi da hanxari suka taso suka fito tsakar gida, cikin kulawa yake musu magana. "kukan me kuke yi Nauwar, ai ba a rabu ba ana tare kuma xa a rika xumunci ku share hawayenku" hannu suka sa suka shiga share hawayen "yauwa ko ku fa, to ku dakko jakar kayan ku yanxu xamu tafi kano,baba son yin dare a hanya" wani sabon kukan suka cigaba da yi, ita ma mama hawaye ne suka cika idanunta amma taki bari su xubo, saboda bata son hankalin yaran ya sake tashi, jakar kayan suka dakko suna tafe suna kuka rungume mama Nauwar tayi da kyar aka cireta daga jikinta, suna kuka suka rabu, kiran ya sadeeq Abba yayi don shi ne xai ja motar da xasu yi tafiyar da ita. fitowa yayi daga dakinsa sanye yake da shadda golden colour wadda aka yiwa aiki da xare kalar shaddar,hularsa ma kalar kayansa ne haka ma takalmin da ke sanye a kafarsa, ya kuma sanya agogo wanda ya kara fitar masa da wankan sa, ba karamin karbar jikinsa kayan suka yi ba, yayi matukar yin kyau sai dai kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa don a yan kwanakin nan har ya dan rame. Abba ne yayi masa magana. "mu shige mu tafi ko sadeeq" A ladabce ya amsa da to Abba. kama hanyar tafiya suka yi, su Nauwar sai faman kuka suke duk irin rarrashin da Abba yayi musu suka ki dainawa sai hakura yayi ya kyale su, sai da suka kusa shigowa kano sannan suka Hakura. kama hanyar xuwa gidan su Hamdan suka yi tunda yanxu a nan Ammi take, kasancewar gidan da ake gina mata ba a kammala shi ba, a kofar gida suka hango Hamdan tsaye yana jiran isowar su Nauwar, hannu shi rungume yake a kirjinsa, kallon motar da ke nufo kofar gidan su yake yi, kamar a mafarki ya hango Nauwar tana masa murmushi, cikin doki da shaukin son ganinta ya karaso wajen, parking ya sadeeq yayi sannan ya matso daf da su, cikin ladabi yake gaida Abba, cikin sakin fuska ya amsa masa, hannu ya mikawa ya sadeeq shi ma fuskarsa a sake ya mika masa suka yi musabaka, juyo da kallonsa yayi wajen Nauwar wani kallo yake mata yana wani kashe mata ido, murmushi ya rika sakar mata,ita ma murmushin take masa cikin shagwaba take masa magana. "Na tafi na dade nasan ko missing dina ma baka yi ba" Cikin marairaicewa yake mata magana "Haba queen ya xa a yi na manta da ke, indai xan manta da ke ai xan mant da kaina" duk maganganun da suke yi a kunnen ya sadeeq, ji yake xuciyarsa kamar ta fito saboda kishi da bakin ciki, da sauri ya fito daga motar ya koma gefe ya tsaya saboda baxai iya jure kallon wannan bakin cikin ba, sai da suka gama maganar su tsaf sannan ya shigar da su cikin gida a sitting room aka sauke su, su kuma su Nauwar suka wuce cikin gida. Ruwa da abinci aka kawo musu, an karrama su sosai,an yi musu karbar mutunci, ruwa Abba ya dauka ya sha sannna ya dubi sadeeq. "ka dauki ruwan ka sha mana sadeeq mun sha hanya ai kana bukatar kasha ruwa" muryar shi a dashe ya bawa Abba amsa. "bana jin kishiruwa na koshi" ji yake kamar ya fashe da kuka sbd abin takaicin da ya gani yanxu,da na sanin xuwansa yake yi da ya xauna a gida duk da bai ga wannan abin takaicin ba, baya jin yau xai iya runtsawa saboda tsananin kishin da ya cika zuciyar sa. Sallamar Ammi da Abban nauwar ne ya dawo da shi hankalinsa, cike da ladabi ya gaishe su, hira suka fara yi da Abba tare da yi masa godiya abisa karamcin da yayi musu, da kulawa da su da yayi na tsawon wani lokaci ba tare da ya nuna gajiyawa ko kosawa a bisa haka ba. fuskar Abba a sake yake basu amsa. "ba komai ai mun xama daya da ku, Allah ya kara mana dankon xumunci" gaba daya suka amsa da ameen komawa ciki Ammi tayi ta bar su da Abban nauwar don tattaunawa dangane da maganar auren sadeeq da Nauwar. Abban nauwar ne ya fara bayani. "naji dadin wannan maganar da ta fito daga wajen ku Alhaji " Cikin sakin fuska Abba ya bashi amsa "ban tari bunfashinka ba Alhaji ni ina ganin mu bar maganar auren nan" gaban ya sadeeq ne ya fadi jin Abba yace a bar maganar aurensa. da sauri Abban Nauwar ya dubi Abba. "ya xaka ce a hakura Alhaji"? "ba wani abu ne yasa nace a bar maganar ba, sai don yarinyar nan tana da wanda take so, shi ma kuma yake sonta, idan aka ce sadeeq ya shigo cikin masu neman aurenta ina ganin ba a yi mata dalci ba, saboda tuntuni da akwai wanda xuciyarta take so ta kuma saba da shi, ni kuma duk abinda yarinyar nan take so wlh ina son sa saboda tamkar 'yata ta cikina na dauketa" "Haka ne Alhaji nima nasan da haka, amma ni a tsarina a kuma yadda na dauke ku, yanxu babu abinda xai sa ku nemi alfarma a gurina nayi watsi da ita, baxan iya hana danka abinda yake so daga wajena ba, saboda haka ne ma nake so a yi maslaha, ko yarinyar nan tana so ko bata so haka xa a yi, Hamdan ya nemi saimah su dai-daita, shi kuma sadeeq ya auri Nauwar haka na yanke" wani farin ciki ne ya xiyarci xuciyar ya sadeeq ji yayi kamar an yi masa albishir da aljannah, duk ya nemi damuwar da ke xuciyarsa ya rasa. saurin dakatar da Abban nauwar Abba yayi. "Aa baxa a yi haka ba Alhaji a bawa yara abinda suke so, mu so muke Yi, su yi aure su xauna lafiya ba so muke su yi mana jeka ka dawo ba, don gaskiya baxan yarda da wannan hukuncin naka ba domin ina son farin cikin diyata, baxan bari a yi mata auren dole ba kawai saboda a farantawa sadeeq,ko yanxu na gani da idona yaran nan suna son junan su,ba karamar matsala xa a samu ba idan aka ce xa a farraqa tsakanin su, shi sadeeq din yayi hakuri mana tunda tun tuni bai yi magana ba, kaje kayi tunani sosai a kan wannan maganar tawa, abinda ka yanke sai mu yi magana ta waya" Ba karmin haushi ya sadeeq yaji ba, da Abba yaki karbar kudurin Abban nauwar, haka suka cigaba da tattaunawa akan maganar amma sam Abba yaki yarda a bawa nauwar ya sadeeq, basu bar gidan ba sai da suka yi sallar la'asar sannan suka tafi, ita kuma saimah a nan suka barta saboda xata karasa hutunta na makaranta. *Jeeddahtulkhair😘*[9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣5⃣ A ranar da su Abba suka koma kaduna bacci mai dadi yaya sadeeq yayi, don har mama sai da ta lura da yadda yake cikin farin ciki ya saki ransa ya daina xama cikin Kadici, addu'a ya rika yi Allah ya tabbatar da alkhairin da ke cikin auren su da nauwar. Su Nauwar ne xaune a falo tare da su Ammi da mama tana basu labarin irin gararin rayuwar da suka shiga kafin su hadu da gidan su saimah, da irin abubuwan da Ammi ta rika yi a lokacin da take cikin rashin lafiya, sai a lokacin take fada mata sharrin da su innah karime suka yi mata cewa ita ta kashe fu'ad.A daidai lokacin Abbanta ya shigo tare da Abban Hamdan xaunawa suka yi aka cigaba da hirar da su, ba karamin tausayawa junan su suka yi ba bisa halin da suka fada a baya, a lokacin Abban Nauwar yake sanar da su cewa sun kusa komawa gidan su sbd an kusa kammala musu ginin da ake yi. ba karamin farin ciki Ammi tayi da jin hakan ba, cigaba da bada labari Nauwar tayi wajen tausayi su tausaya human su wajen dariya kuma a hadu a yi dariyar tare, har suka xo daidai wajen da take basu labarin xaman su a gidan su doctor Abdallah da irin gallaxawa da cin xarafinsu da Hajiya take yi ita da yayanta, tunowa tayi da complement card din da doctor Abdullah ya bata, da alkawarin da tayi na nemansa a duk lokacin da ta samu iyayenta, da sauri ta tashi ta shiga daki ta bude jaka ta xaro card din. Karasowa kusa da Abbanta tayi tare da mika masa card din, cikin sassanyar murya take masa magana. "Abba wannan shi ne mutumin da ya tausaya mana ya kula da mu kamar yadda aka yi mana a gidan su saimah, Shi ne mutum na farko da ya taimaka mana dan Allah ba dan wata manufa ba, sai dai mahaifiyarsa tafi karfinsa domin ita ta kore mu daga gidan, saboda a tunaninta wai mun mallake mata d'a yana ta yi mana wahala" Hannu biyu yasa ya karba tsayawa yayi ya duba katin sosai, dagowa yayi ya kalleta yana maimaita sunan da ke rubuce a jikin katin . "Abdallah Sani fataskum!!!!!" sake dubanta yayi "Wannan mutum shi ne ya taimake ku? " Gyada kai tayi alamar eh "to ai wannan yaron 'kani ne a gurina, ku ne dai baku san shi ba, tunda bama xiyartar juna, mahaifinsa Alhaji sani fataskum, dan uwan mahaifiyata ne, muna xumunci da mahaifinsa sosai yana xuwa gidan mu wajen Baffa,nima a da ina xuwar masa xiyara sai bayan ya rasu alaka ta yanke kasancewar matarsa ba tada kirki bata son kowa ya rabe shi, baxan yi mamaki ba dan kun ce an yi muku haka a gidan su, xasu aikata fiye da haka ma, don wannan kadan ne daga irin mugun halin uwar su" Hannu yasa a aljihu ya ya shiga lalubo wayarsa, copy na lambobin da ke jikin katin yayi sannan ya fara kira, cikin sa'a kuwa bugu daya aka dauka, da sallama ya fara magana cike da tausasawa aka amsa sallamar. bayani Abban Nauwar ya fara yi masa. "kana magana da dan uwanka daga kano garin dan batta" murmushi doctor yayi. "masha Allah naji dadin kiran nan naka, kamar dama kasan ina nan ina fafutukar neman yan uwan mu na kano amma fafur Hajiya ta hana adress, amma dan Allah kayi Hakuri ban gane muryar dan uwan nawa ba" "kana magana da Mahmud nasan kafi sanina da Mudi ko" cikin farin ciki ya amsa tare da yin takaitaccen murmushi "kwarai kuwa, ya gida da yara" amsa masa yayi da lafiya lau, sannan ya fara yi masa godiya da abin arxikin da ya yiwa su Nauwar. "ina godiya sosai da abin arxikin da ka yiwa iyalina Allah ya saka maka da alkhairi" cike da mamaki yake tambayarsa "iyalinka kuma?? yaushe na taimake su" murmushi Abban Nauwar yayi. "nasan ka manta sbd an dauki Lokaci mai tsawo da faruwar hakan, idan baka manta ba akwai wata mahaukaciya da wata yarinya da ka taimakawa ka kaisu gidan ku, ka fara canja musu rayuwa daga bakin ciki xuwa farin ciki, sai da wani dalili yaxo ya gifta sannan ku ka rabu, to wannan mahaukaciyar mai dakina ce, ita kuma yarinyar Nauwar 'yata ce" salati doctor ya fara yi. "ikon Allah ashe ma yar uwata na taimakawa, wlh na tausayawa halin da suke ciki a lokacin shi ne ma yaja hankalina har na kai su gida saboda basa cikin kwanciyar hankali, amma dai yanxu mara lafiyar taji sauki ko?" "Taji sauki har sun dawo gida dama haukan ba nata bane hadata aka yi da shi amma yanxu komai ya dawo daidai, yanxu muke mayar da maganar sai Nauwar ta tuno da card din da ka bata ina dubawa naga sunanka a jiki nace baxan iya jurewa ba har sai na kiraka na gode Maka Allah ya saka da alkhairi" ba karamin dadi doctor yaji ba da Allah ya mayar da su nauwar kyakkyawan hannu dama kullum addu'ar da yake yi musu kenan, tunda suka rabu da su bai taba shiga farin ciki irin na yau ba sbd tunda suka tafi bai kara ji Ko ganin mai kama da su ba. magana ya cigaba da yiwa Abban Nauwar "ina nauwar din take idan tana kusa bani ita mu gaisa" mika mata wayar yayi suka fara gaisawa. "sannu Nauwar ya bayan rabuwa" A ladabce take amsa masa maganarsa, bayan sun gama gaisawa ne ta mikawa Abbanta wayar suka yi sallama. Hannu doctor ya daga sama yana godiya ga Allah, a lokacin ya dauki mukulli ya yiwa motarsa key sai gida a falo ya tarar da hajiya da kannensa suna hira, labarin yadda suka yi da Abban nauwar ya shiga bata "oh!!! amma wlh naji kunya ashe yar ma tamu ce,nayi musu wannan korar karen yanxu da wane ido xan kalli ubanta wlh nayi nadamar abinda nayi musu, shi yasa ba a son wulakanta dan Adam baka son ko wanene shi ba, Allah yasa dai yarinyar nan bata fadawa ubanta irin cin mutuncin da muka yi musu ba" tashi doctor yayi ya bar hajiya tana ta subadi duk ta shiga damuwar rashin mutuncin da tayi musu. A kullum sai doctor ya kira Abban nauwar sun gaisa yanxu xumuncin su ya kara karfi sosai, ita kuwa Hajiya don kunya taki yarda a bata Abban nauwar su gaisa. *jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣6⃣ Haka rayuwar su Nauwar ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki, rayuwa mai dadi suke yi a gidan su Hamdan, a dan xaman da saimah tayi a gidan su Hamdan ba karamin sabo suka yi ba saboda shi mutum ne mai son mutane da saukin kai, tsakanin nauwar da Hamdan kuwa suna gudanar da soyayyar su cikin kwanciyar hankali. wayar da ke gefen Abban Nauwar ce tayi ringing hannu yasa ya dakko tare da kara wayar a kunnensa, cikin sakin fuska ya ambaci sunan mai kiran. "Sadeeq barka da yau, ya ku ka je gida" cikin ladabi ya amsa da lafiya lau..... shiru yayi na wani dan lokaci Abba ne ya katse shirun tare da cewa. "Da alama kana cikin damuwa Sadeeq ka fada min duk abinda yake damunka" shiru

Chapter 26 of 29