Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Nauwar yayi "idan ka shirya kaxo wlh xan baka" "Ai ni a shirye nake ko yanxu ka bani karba xan yi, Nauwar xaka bani ko yayarta?" dariya doctor ya bawa Abban nauwar ganin yadda ya dauki maganar da muhimmanci. "Nauwar ai an yi mata miji sai dai yayar tata idan kana so" fuska a sake ya amsa. "ina so mana, amma da nafi son karamar, amma tunda kace an mata miji na karbi babbar ya sunanta" "sunanta saimah"ya fada masa a takaice, labarin kulawar da suka bawa su Nauwar ya fara bashi da irin karamcin iyayenta Hannu biyu doctor yasa ya karbi saimah ba karamin shiga ransa tayi ba saboda yadda ta samu kyakkyawan yabo a wajen abban nauwar Hirar duniya suka cigaba da yi har xuwa dare. *Jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *ALLAHU AKBAR DUNIYA LABARI Allah ya yiwa daya daga cikin masoya wannan littafi rasuwa,😭😭😭 kuma member a group dina na sirrin ya mace HASANATULLAH MUHD LAWAN (Ummu sulaiman)Allah ya gafarta mata, halinta na gari ya bita, Allah yasa aljannah ta xamo makoma a gareta* 9⃣9⃣ A gidan su Nauwar doctor ya kwana washe gari ma kayan abinci na alfarma suka hada masa, saimah da Nauwar ne suka kawo masa cikin ladabi suka gaida shi, idanunsa a kan saimah ya yaba da hankalin yarinyar da yadda take gudanar da abubuwanta cikin nutsuwa, wani sonta ne ya kara shiga ransa ya xama wajibi a gare shi ya so ta, suna ajiyewa suka koma daki. bayan ya kammala cin abincin ya fara yiwa Abban Nauwar maganar auren sa. "ni fa so nake a yi a kare komai yau, saboda yau din nake son tafiya gida ina so na kaiwa Hajiya kyakkyawan labari dama ta kosa ta ga jikokinta" murmushi Abban Nauwar yayi "me kake ci na baka na xuba Abdallah yanxu dama nake son na sameta nayi mata magana nasan baxa ta ki karbar ka ba" "ni dai ka tashi ka tafi so nake naji result don nan da karfe12 xan wuce" takurawar da doctor ya rika yiwa Abban Nauwar ne yasa ya tashi, dakin su Nauwar ya shiga inda ya tarar da su suna hira, waje ya samu ya xauna cikin ladabi suke masa magana, "sannu da shigowa Abba" fuskarsa a sake ya amsa musu duban su yayi gaba yana murmushi" ina so ku bani hankalin ku gaba daya xan yi magana da ku" gyara xama suka yi suna dubansa tare da cewa, "muna saurarenka Abba" gyaran murya yayi sannan ya fara magana, kiran sunan saimah yayi tare da tambayarta"an yi miki miji a gida ne ko kuwa"kamar daga sama taji tambayar, kanta a sunkuye ta bashi amsa "ba a yi min ba Abba" "yauwa Alhamdulillah dama na tambaye ki ne saboda bana son a yi neman aure a kan neman aure" bata fahimci abinda yake nufi ba kuma bata tambaye shi ba, shiru yayi na wani dan lokaci sannan ya cigaba da magana. "kinga wannan dan uwan nawa da ku ke kaiwa abinci ko" ya tambayeta a takaice, a hankali ta dago ido ta amsa masa da "eh Abba" "wannan da kike gani dan uwana ne na jini kuma mutumin kirki ne ya nuna yana sonki da aure, idan kin amince xai fito nan bada dadewa ba domin baxa a dauki lokaci mai tsaho ba xa a yi komai a gama, fatana dai ki amince da shi" wani farin ciki ne ya lullube Nauwar taji dadin wannan hadin saboda da saimah da doctor xasu dace sosai saboda mutane ne masu tsari da tsafta, Nauwar ce tayi saurin cewa "ta amince Abba"saurin dakatar da ita yayi "Aa ki kyaleta tayi magana da kanta" sake maimaita mata tambayar yayi a kunyace ta amsa da "na amince Abba" ba karamin dadi yaji da amincewarta ba, dama baya son ya aurar da nauwar ita kadai ya fi son ya hada da saimah a yi komai tare, albarka ya shiga saka mata yana mata fatan samun nasara a rayuwa. Abba na fita Nauwar tayi tsalle ta rungume saimah suna murna dama ita saimah ta yaba da doctor tun kafin ya furta yana sonta kawai ta danne ne saboda kunya. Abban Nauwar na komawa wajen doctor kafin ya karaso gurin shi har ya kosa ya mike nufo shi yayi yana tambayar shi "ya ku ka yi da ita, ta amince kuwa?" murmushi Abban Nauwar yayi yana masa magana. "Haba sarkin xumudi ka bari na karaso dai ko" komawa yayi ya xauna "na kosa naji sakamakon ne shi yasa amma tunda an ce na koma dole nayi biyayya don kada a hanani" ya karasa maganar yana dariya duban shi Abban Nauwar yayi. "kamar yadda na fada maka dama yarinyar ba tada matsala don lokacin da na fada mata ko musu bata yi min ba, kaga da bata so xata dakatar da maganar, don haka yanxu abinda ya rage maka shi ne ka fara shirye-shiryen biki" farin ciki ne ya bayyana a fuskar doctor "kai!! amma naji dadi, na gama komai dama matar ce ta gagare ni sai da yayana ya bani tukunna" dariya Abban Nauwar yayi "Ai da nasan tuntuni haka kake xaune ba aure da tuni na aurar da kai na huta" murmushi kawai doctor ke yi don ya rasa da wane baki xai yi godiya saboda farin ciki"wato komai na Allah yana da hikima da su nauwar ba su shiga halin tsaka mai wuya ba da baxa su sanni ba, kuma baxa su san saimah ba, gashi nan ta sanadin su na samu matar aure" jinjina kai Abban Nauwar yayi "gaskiya ne fatan mu dai Allah ya xaunar da ku lafiya" amsawa yayi da "Ameen" nan take ya kira Hajiya ya fada mata "tayi farin ciki sosai sannan ta sa masa albarka" duban shi Abban Nauwar yayi "tunda ka kira Hajiya nima bara na kira Abbanta na fada masa don ya shirya don baxa a wuce sati uku ba a yi bikin nan ba. kiran wayar abban saimah yayi yana ganin numbersa ce yayi saurin dagawa, cikin sakin fuska yake masa magana bayan sun gama gaisawa yayi masa maganar cewa saimah ta samu mijin aure kuma dan uwansa ne Abba yayi farin sosai cikin farin ciki yake magana "yanxun nan mamanta take sanar da ni sun kirata a waya ita da nauwar sun fada mata, nace lallai yaran yanxu sai dai a bar su kawai wato baxa su iya jira ma ka kira ba" murmushi Abban Nauwar yayi "da Alama doctor ya samu shiga ne tunda kaga haka Alhaji kasan yaran nan idan suna son abu idon su rufewa yake haka ma idan basa so, mu dai sai dai godiya ga Allah xamu aurar da yaran nan gaba daya ga yara yan mutunci" "Haka ne Alhaji Allah yayi mana taimako, wane lokacin kake ganin ya dace a tsayar" Abban saimah ya tambaya gyaran murya yayi "xan shawarci maxajen nasu naji duk yadda suka ce xan kiraka mu shawarta amma ni bana so a wuce wata daya ba a yi komai ba" sallama suka yi sannan ya kashe wayar ya mayar da kallon shi ga doctor "ka samu karbuwa a wajen saimah kaji har ta kira gida ta fada musu" murmushi doctor yayi yaji dadin karbar da saimah tayi masa, a ranar ya koma fataskum don fara shirye-shiryen biki. *Jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya naki ne sarkin rigima kawata, aminiya, yar uwata abokiyar fadana MAIJIDDA BELLO na baki wannan shafin kyauta kiyi yadda kike so da shi* 1⃣0⃣0⃣ Shakuwa mai tsanani ce ta shiga tsakanin doctor da saimah ba karamin son junansu suke yi ba, don kusan duk bayan Kwana biyu sai doctor yaxo xance wajen saimah,Hajiya ma tana matukar kaunarta a kullum sai ta kirata a waya taji muryar surukarta, shirye-shiryen biki sun yi nisa don su doctor har sun tsayar da ranar da xasu kawo lefe don a tsayar da lokacin biki. yau da sassafe suka tashi domin xasu je dan batta gaba dayan su suka tafi, don sanar da baffa lokacin da aka tsayar na auren su saimah, Hamdan ne yaja motar domin yana son xuwa yaga baffa, Abban Nauwar me ya xauna a gaba,Ammi da saimah da Nauwar na gidan baya, misalin karfe takwas na safe suka bar gida basu isa garin dan batta sai karfe tara, tun daga nesa suka hango taron mutane cike da kofar gidan Baffa, saurin dakatawa Hamdan yayi, don ya samu wajen da xai yi parking saboda idan ya karasa baxai samu gurin tsayawa ba, jikinsu a sanyaye suka fito gaba daya suka nufi kofar gidan, duk wanda suka kalla sai su ga yana cikin alhini da jimami, cikin hanxari suka karasa wajen, a taugunne suka tarar da Baffa ya hada kai da gwiwa,gaba daya suka gaishe shi, amma ya kasa amsawa, cikin nuna damuwa da halin da yake ciki Abban Nauwar ya yi masa magana "sannu da gida baffa" A hankali ya dago ya dube shi "yauwa Mahmud sannu da xuwa yaushe ku ka karaso gaba daya haka kamar kun san abinda ke faruwa" cikin damuwa yake tambayar sa"me kuma ya faru Baffa" share kwallar da ke shirin fito masa yayi sannan ya cigaba da magana "Allah ya yiwa innah rasuwa yau da safe"ya karasa maganar yana share hawaye, cikin nuna damuwa ya dube shi, "kayi hakuri Baffa dukkan mai rai mamaci ne fatan mu dai Allah yaji kanta yasa ta huta ya yafe mata kurakurenta" Amsawa yayi da "Ameen" sannan ya cigaba da magana "ina cikin damuwa Mahmud ana so a yiwa innah suttura amma abu ya gagara"cike da mamaki yake tambayarsa "me ya hana a suturtata" girgixa kai Baffa yayi "ba komai ne ya hana ba sai abinda ya faru da gawarta abin xai baka tsoro, shi yasa na shiga damuwa nake jin tsoron abinda xata je ta tarar a lahira tunda gashi tun a duniya Allah ya fara nuna ko wacece ita, wlh Mahmud ji nake kamar na mutu na huta da wannan bakin cikin da nake ciki, wannan abinda ya faru nan gaba xai xame mana abin gori a wannan karkarar tamu yaya da jikoki" cikin rashin gane abinda Baffa ke nufi Abban Nauwar ya sake tambayarsa "Baffa ni fa ban fahimci abinda kake nufi ba tun daxu me ya faru da innar da har aka kasa yi mata suttura a kai ta kushewarta" wasu xafafan hawaye ne suka cigaba da sauka a fuskar Baffa "yanzu a halin da ake ciki fuskar innah tayi bakikkirin tana fitar da hayaki Yanxu haka limamin da xai yi mata wanka ya shaki irin wannan hayakin yanxu haka yana kwance a asibiti sannan kuma maciji ya nade jikinta kowa tsoron shiga inda gawar take yake yi, bansan ya xan yi ba mudi a ce mahaifiyata ce a irin wannan halin, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" da kuka mai cike da ban tausayi ya karasa maganar shi ma abban nauwar kukan yake yi saboda yana tausayin baffansa yana jin xafin halin da kakarsa ke ciki a halin yanxu, neman shawarar mutane suka shiga yi wasu su ce a samu wasu su daure su yi mata wankan a haka, wasu kuma su ce a kyaleta a haka, duk wanda aka kama sai ya xille ya gudu sai da aka nemi kowa aka rasa mutum daya ne kawai ya tsaya Shi ma saboda abokin Baffa ne yana Jin kunyar ya gudu ya bar shi, daga karshe dai aka yanke shawarar a barta a cikin dakin ba tare da an tabata ba, shi kuma baffa ya bar gidan tunda abin yaxo da haka ko xaman makoki ba a yi ba saboda gulmar abinda ya faru kawai ake yi a kauyen a tarihin rayuwarsu basu taba gnin irin wannan abin ba sai a kan innah karime, kowa sai tunnin abinda ta aikata yake yi saboda mutuwarta taxo da wani sabon salo na mamaki, A ranar Baffa ya koma gidan su nauwar dama an gina masa bangarensa an gyara masa komai, Kullum Abban Nauwar cikin kwantar masa da hankali yake yana rarrashinsa a kan kada yasa damuwar innah a ransa ya dage da yi mata addu'a watakila sanadin haka taji sauki a wajen Allah Ranar da ta cika kwana bakwai da rasuwa aka kawo lefen Nauwar da saimah kaya aka yi na gani na fada doctor Abdallah akwati sha biyu ya yiwa saimah ita kuma nauwar aka yi mata takwas ba karamin kashe kudi suka yi ba, gaskiya duka bangarorin biyu sun yi barin naira domin dukansu babu wacce aka sakawa suttura ta kasa da dubu ashirin, an yanke lokacin biki bayan sati biyu, kafin lokacin yan gidan su saimah suka taho gaba daya don sun barwa Abban nauwar ragamar bikin gaba daya sun ce yayi komai. Yau da wuri suka shirya don xuwa gidan gyaran jiki da ke unguwar xoo road, basu samu wanda xai Kai su ba kasancewar Ammi na ta xirga-xirgar harkar biki, a bakin titi adaidaita sahu ya sauke su, da kafarsu suka karasa don shiga gidan mai gyaran da xata gyara su, wani mutum suka hango tsaye a bakin mota sanye yake da farin yadi, ba yabo ba fallasa, baxa ka kira shi da talaka ba, haka kuma baxa ka ce masa mai Kudi ba sai dai a saka shi a sahun masu rufin asiri, kallon su yake yi sosai har sai da suka tsargu da kallon da yake musu, har suka kusa karasawa wajen basu gane ko wanene shi ba, sai da suka je daf da inda yake xasu shiga layin gidan da xasu je nauwar ta ja da baya tana masa duban mamaki, cikin sarkewar murya ya kira sunanta "Nauwar kece ashe xan gane ki" Xubewa tayi a kasa tana gaida shi tare da xubar da hawaye "Malam ashe xaka gane ni? " Ajiyar xuciya yayi "ya xa a yi na kasa gane Ki nauwar, mun shiga tashin hankali a lokacin da muka neme ku muka rasa, tun daga ranar da kuka tafi ban Kara samun walwala ba, saboda ina tunanin kada shu'uman aljanun nan su sabauta muku rayuwa amma naji dadi da na ganki, Ina ne gidan ku, ina fatan kuma mahaifiyar Ki ta samu lafiya? " Share hawaye nauwar tayi "da taimakon Allah da taimakon ka da na Wadannan mutanen" ta nuna saimah "ta samu lafiya yanxu ta dawo mutum kamar kowa" Fara'a Malam Haruna ya shiga yi "alhamdulillah Allah ya qara lafiya ya Kare ku daga sharrin masu sharri" amsawa tayi da Ameen tare da tambayarsa "Ina baba da fatan dai tare kuka xo" murmushi yayi "tana gida yanxu haka ma daurin aure naxo kuma Allah ya kaddara haduwar mu da ke" Nan take nauwar ta kira Abbanta cikin farin ciki take magana. "albishirinka Abba" Cikin sakin fuska ya amsa mata da "goro me ya faru yata ta Kaina ?' "Yanxun nan naga Malam Haruna Wanda ya taimaki Ammi ta samu lafiya " cikin kulawa yace ta hada shi da Malam addu'a ya rika yi masa yana godiya a bisa taimakon da ya bawa iyalansa, bayan sun yi sallama da Malam ne suka cigaba da magana da nauwar "Ku je gida tare da Malam din gani nan xuwa yanxu" adaidaita suka sake Hawa suka rankaya suka tafi gidan su nauwar. *jeeddahtulkhair😘* [9/23, 10:10 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *MAIJIDDA TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya tukwici ne a gare ku* *Abdurrahman ibrahim* *Yusuf mas'ud duniya* *Ibrahim (itz ibrahim)* *ina godiya da yadda kuke ta fafatukar ganin wannan littafi ya karbu wajen yin post din shi a facebook na gode Allah ya saka da alkhairi ya bar xumunci* 1⃣0⃣1⃣ 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 A dakin saukar baki aka sauke malam Haruna, hannu biyu Ammi ta karbi malam tare da kawo masa abinci kala-kala, bayan ya kammala ya fara bata labarin irin gwagwarmayar da yayi da aljanun Ammi bayan tafiyar su. "ba karamin auna arxiki kika yi ba Hajiya wadannan aljanun basu so barin ki da rai ba, domin kuwa ni kaina Allah ne yayi da kwana na a gaba a zahiri na rika ganin su zasu hallaka ni, da taimakon Allah da addu,a na samu na kore su daga gidana, amma dai Alhamdulillah yanxu komai yazo karshe gashi nan har kin dawo garau da ke, Allah ya kara lafiya wadanda suka yi kuma nasan yanxu abin ya koma kansu, domin asirin da suka yi kaikayi koma kan mashekiya ne" Gyara zama Ammi tayi "mun gode sosai malam nauwar duk ta fada min irin taimakon da kayi mana Allah ya bada lada wadanda suka yi abin kuma yanxu duk sun xama abin tausayi, dayar ta haukace dayar kuma tayi mutuwar wulakanci" mamaki ne ya kama malam, "kinga ai rashin amfanin cutar da mutum gashi nan burinsu bai cika ba, to yanxu ita mai mutuwar nan me zata je ta gayawa Allah, ko da yake su masu wannan mugun abin ba gani suke yi ba, gani suke duk abinda suke yi dai-dai ne" Hirar da suke tayi kenan, har Abban nauwar ya dawo da sallama ya shigo dakin, cikin sakin fuska ya karasa inda malam Haruna yake hannu ya mika masa suka gaisa, sannan ya fara yi masa godiya abisa abubuwan alkhairin da yayi musu, cikin sakin fuska malam ya mayar masa da amsa "ba komai Alhaji ai wanda ya taimaki wani Allah xai taimake shi, mu dai Alhamdulillah da Allah ya bata lafiyarta, sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba, Ashe kuma auren nauwar ya taho, rabon naxo bikin ne yasa muka hadu da ita" murmushi Abban nauwar yayi "Abu ya matso kam dan yanzu saura sati biyu a fara biki" addu,ar fatan alkhairi malam yayi sannan suka fada wata hirar, bai tashi tafiya ba sai bayan sallar la'asar sha tara ta arxiki Abban nauwar da Ammi suka hada masa har sai da ya rasa bakin godiya, Abban nauwar ne da kansa ya dauke shi a mota ya mayar da shi masaukinsa suna isa gurin ya tsaya suka fara magana. "yanxu kuma sai yaushe xaka dawo malam" shiru yayi na dan lokaci sannan ya yi magana "insha Allah zan yi kokarin dawowa bikin diyata duk da dai garin namu da nisa amma zan kokarta naxo" cikin kulawa Abban nauwar yake tambayarsa "ina ne garin da kake malam"? Gyara zama yayi"can cikin wani Kauye ne a garin Gombe amma yan uwana da yawa suna nan garin ni kadai Allah ya zaunar a can" murmushi Abban nauwar yayi "me yasa baxa ka dawo nan din ba malam ko garin namu ne bai maka ba" ya karasa maganar yana murmushi "me zai hana ni xama a kano ni da mahaifata, idan na samu muhalli xan dawo insha Allah" cikin kulawa Abban nauwar ya dube shi. "Malam idan har babu damuwa ina da gidan da xan saka ka sai ka dawo cikin yan uwanka" wani farin ciki ne ya rufe malam Haruna "Ai kuwa na gode Alhaji idan xan dawo biki sai mu taho gaba daya da uwar gidan nawa ba sai mun kara komawa ba" "Yauwa nima abinda nake so nace kenan yanxu xan sa ayi muku duk gyaran da ya kamata kuna xuwa sai ku shiga gidan ku" Godiya mai yawa malam Haruna yayi da xa su yi sallama Abban nauwar ya dakko kudi mai yawa ya bashi sannan ya wuce gida. Kai tsaye wajen mai gyara ya nufa ya xayyana masa irin yadda xa a gyarawa malam Haruna gidansa. Daga nan kuma ya wuce gidan malam Audu ya mika masa mukullin wani gida da ya gina masa, albarka malam ya shiga saka masa yana yi masa addu'ar gamawa da duniya lafiya, cikin girmamawa yake wa malam magana "wajibina ne na kula da kai malam domin kaine silar duk wani arxiki nawa da nake takama da shi, don haka duk abinda nayi maka ban biyaka ba, burina a kullum na kyautata maka kai da baffa saboda irin kulawar da na samu daga gare ku' cigaba yayi da sa masa albarka, washe gari da safe ya aika da mota aka kai malam sabon gidansa. *BAYAN SATI DAYA* Baki daga kasashe daban daban ne suka zo don halarta bikin su nauwar da saimah yan uwan Ammi daga Sudan duk sun xo don shaida wannan aure mai albarka, guraren biki daban daban aka kama don gudanar da wannan bikin da aka dade ana jiran xuwansa. yau ta kama daurin aure da wuri su nauwar suka shirya a dakin Abbansu suka xauna, tun kafin a daura auren nauwar ke faman kuka saboda bata son rabuwa da Amminta, bayan an daura auren ne Abban saimah ya shigo ya fara yi musu nasihohi masu ratsa jiki sannan kuma ya mikawa kowacce a cikin su sadakinta, cikin kuka nauwar take masa magana "Abba na bar maka ka rike kayi duk abinda kake so da shi"tausayin nauwar ne ya kama shi "Aa nauwar ki rike ki siya wani abin mai muhimmanci da shi Allah yayi miki albarka" bayan fitar Abba daga dakin angwaye suka shigo sanye suke da fararen Shadodi komai nasu iri daya Hamdan da doctor Abdallah suka saka, fuskar nauwar a rufe tana ta faman kuka karasowa inda take Hamdan yayi da sauri taja jiki ta matsa murmushi yayi yana mata magana "yau kuma dodo na zama nauwar kike jin tsoro na" Shiru tayi ba tare da ta bashi amsa ba ya rika tsokanarta, sai da suka gama magana sannan mai hoto ya shigo ya fara daukansu, bayan sun kammala suka fita doctor ya kama hanyar tafiya fataskum shi kuma Hamdan yayi gida. A unguwar nassarawa G. R. A Abban Hamdan ya gina masa katafaren gida wanda kuma ba su da nisa da gidan su Hamdan, shi kuma doctor Abdullah a fataskum xai xauna a wani hadadden gida da ya samu gado a wajen mahaifansa, da misalin karfe daya na rana yan daukan Amarya suka zo, wadanda su ne xasu tafi da saimah gidan doctor, ba karamin tashin hankali saimah ta shiga ba kuka gaba daya yaki zuwar mata, amma dai kana ganinta kasan tana cikin damuwa a daki Saimah take iyaye nayi mata fada a dai-dai lokacin nauwar ta shigo ta tarar da saimah na ta faman sharar kwalla da sauri ta karasa wajenta ta rungumeta kuka take yi mai cike da ban tausayi da kyar aka cire saimah daga jikin nauwar aka sata a mota sai gidan doctor. .tunda aka tafi da saimah nauwar ke kuka rarrashin duniyar nan an yi mata ta kasa yin shiru har zuwa karfe shida na yamma wanda a wannan lokacin xa a kaita dakin mijinta, da kyar aka lallabata ta shiga ta watsa ruwa sannan ta fito aka Fara yi mata nasihohi a kan xama da miji, nan ma dai ta shiga tashin hankalin rabuwa da Amminta haka aka tarkatata aka kaita gidan Hamdan. Rayuwa mai dadi suke yi a gidan mazajen su cike da xaman lafiya da kwanciyar hankali duk wanda yaga irin zaman da suke yi sai abin ya burge shi, watan Su nauwar biyu da aure Allah ya azurta su da samun ciki ba karamin lele nauwar ke sha a wajen Hamdan da mamansa ba kowa fata yake Allah ya sauketa lafiya. Sai da saimah ta cika wata uku a gidan doctor sannan taxo ganin gida, sai da tayi sati biyu sannan ta tafi nan ma dai sai da suka sha kuka suka rabu. A ranar da suka cika wata tara dai-dai nauwar ta haifo santalelen jaririnta kamar su daya da Hamdan komai da komai, sunan Abban nauwar aka sanyawa yaron inda suke kiran shi da Adeel, ba karamin gata kakannin Adeel ke gwada masa ba, don bai fiya xama a hannun nauwar ba kusan kullum yana tsakanin gidan mama da Ammi. Yau da sassafe Ammi taji ana kwankwasa mata kofar falo da hanzari ta tashi don budewa tare da cewa "wanene " shiru aka Yi ba a yi magana ba, cikin karfin hali ta saka key ta bude kofar, mace ta gani tsirara haihuwar uwarta fuskarta baka kirin cikin rawar baki take mata magana"Habi Kece lafiya na ganki a wannan yanayin " Hawaye matar take xubarwa "ki yafe min duk abinda nayi miki don Allah mutuwa xan yi na wulakanta naga rayuwa yanxu haka ni nasan

Chapter 28 of 29