Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da bacci yayi awon gaba da shi. Bayan yayi sallar asubah, yayi addu'o'i ne ya 'kara mayar da kanshi ya kwanta, kasancewar ba shi da lecture din safe, nan ma dai xuciyar shi yaji tana tuna masa Rehab, shi kansa abin ya fara bashi mamakin yadda ya canja lokaci guda, tunda yake a tarihin rayuwarshi bai ta6a tsintar kanshi a son wata yarinya ba, amma sai ga shi yanxu, dare d'aya ya fara son wadda ta fi 'karfinshi. shawarwari xuciyarshi ta shiga bashi, a kan ya furta mata so, wata xuciyar kuma tace ya kyaleta kawai, saboda ba lallai ta amsa tayinshi ba. yanke shawarar sanar da ita ya yi don ya jarraba damarsa ko xata amince da shi. agogon da ke manne a bangon d'akin ne ya buga, shi ne ya katse masa tunanin da yake yi, 'karfe goma dai-dai ya gani, don haka ya mi'ke ya fara shirye-shiryen tafiya makaranta. cikin mintunan da basu wuce biyar ba, ya kammala shiryawa, kulle d'akinsa yayi ya fice. 'Dakin karatu ya nufa ya samu guri ya xauna ya fara d'aukar darasi, bayan an gama ne ya fito inda ya saba xama, don yayi karatu, bai dad'e da fara karatun ba, ya gano Rehab daga nesa tana masa murmushi, da fara'arta ta 'karaso wajen da yake, gaisawa suka yi sannan suka fara hira gami da karatu kamar yadda suka saba, bayan sun gama ne, suka yi sallama xasu rabu kenan Mahmoud yake sanar da ita halin da ya tsinci kanshi a ciki, ta yi farin cikin jin wannan magana daga gareshi, saboda ita kanta ta yaba da hankalinshi da yanayin tarbiyyar da yake da ita, da kuma addininshi, don haka basu samu wata matsala da junansu ba, suka fara soyayya mai tsafta da ban sha'awa, suka xamto tamkar "yan uwa. A lokacin da suka shiga level 400 Mahmoud yake sanar da Baffansa cewa ya samu matar aure kuma abokiyar karatunsa ce, Baffa yayi farin ciki da wannan maganar, kasancewar duk 'yan uwansa sun yi aure, shi kad'ai ne ya rage a 'kasa saboda yana karatu, addua mai yawa yayi masa da fatan Alkhairi. bayan sun yi magana da baffa ne ya nemi Rehab a kan ta sanar da iyayenta maganar aurensu,tunda dai suna son juna, da farko dai ta nuna 'kin amincewarta a kan baxa ta sanar da su ba, saboda ba lallai ne su aurawa Ba'kar fata 'yar su ba, kasancewar su larabawa ne, lalla6ata yayi a kan ta fad'a musu tunda suna addua insha Allah xasu amince da abinda suka xo musu da shi. Tun da ta je wa da iyayenta maganar ta daina samun walwala da farin ciki daga garesu, saboda ita ce 'ya mace d'aya tilo a wajen mahaifanta, ta yaya xa a yi su aurawa talaka kuma ba'kar fata 'yar su, don haka suka turje, a kan baxa a bata shi ba, har sai da ta kwanta a asibiti, saboda wannan maganar daga karshe dai likita ya sanar da su cewa,idan har aka hanata abinda take so xa a iya rasata gaba d'aya, don haka suka yanke shawarar aura mata Mahmoud, amma da sharad'in dole sai dai su xauna a sudan, don basa son 'yar su tayi nisa da su. nan ma dai an sha gwagwarmaya da 'kyar suka amince aka yi biki, suka dawo Nigeria tare aka had'ota da sha tara ta arxi'ki, sannan suka samarwa Mahmoud aiki. Da farko sun kama haya ne a unguwar Na'ibawa, rayuwa suke yi mai dad'i cike da soyayya da kulawa, ga shi kullum Mahmoud dad'a samun 'karin girma yake yi a wajen aikinsu. watan su takwas da aure suka shirya tafiya xuwa garin 'Dan batta, saboda tunda suka yi aure babu wanda ya kawo musu xiyara idan ba Baffansa ba, don haka ya d'auki mota suka tafi, ya kuma yi musu siyayyar kaya masu yawa, ya siyawa Baffansa shadda su inna karime da Habi da matan su isa,ya siya musu atamfofi masu kyau da tsada, sannan ya siyawa su isa yarduka masu kyau da tsada. yana yin parking da motarsa 'yan garin suka ri'ka xuwa suna masa barka da xuwa, sun yi mamaki had'e da farin cikin ganinshi, da yadda lokaci guda ya canja, kyansa ya fito ya xama babban Alhaji mai ji da kansa. kai tsaye cikin gida suka shiga, malam ne ya hango su daga nesa, yana can yana gyarawa tumakansa turke, da hanzari ya 'karaso yana musu barka da xuwa, innah karime ya fara kwallawa kira, ita ma da sauri ta fito tana lalle maraba da ba'ki, a tuaninta wasu ne daban, amma tana ganin Mahmoud ne sai ta ja baya ta tsaya, nan da na fuskarta ta canja daga farin ciki xuwa akasin shi,kamar wacce aka aikowa da mala'ikan mutuwa, yamutsa fuska ta shiga yi gami da turo baki, har 'kasa Mahmoud ya tsugunnah ya gaidata, a wula'kance ta amsa, sannan ya gabatar da ita a wajen Rehab ita ma risunawa tayi ta gaisheta cikin harshen larabci, abinka da wadda bata jin yaren sai bude ido kawai take yi, kamar an girgiza 6era a buta,sakin baki tayi tana mamakin yadda Mahmoud ya canja ya samu cigaba a 'kan'kanin lokaci, nan fa hassadarta ta tashi, ta fara magana ranta a 6ace wannan kuma wacece mudi, ina xaton kamar karuwarka ce ko??Baffa ne ya katse mata magana,kayya!! kayya!! kayyah inna matarsa ce fa, kin riga kin sani har goran d'aurin aurensu sai da aka baki, ke da kanki da hannunki kika ri'ka rabawa. To goranta min d'an nema, ka kawo kanka duniya ban isa na fadi gaskiyar abinda na gani ba ko? shiru Baffa yayi mata saboda ya ga yadda ta fusata, idan yayi magana xata iya tsine masa, Habi ce ta fito da alama daga bacci ta tashi, tana ganinshi ta ja da baya kamar wadda taga dodonni,da alama ita ma mamakin ganin mahmoud da matarsa take yi, tambayar inna karime take, innata wannan tsohuwar guxumar kuma daga ina?yadda kika ganta nima haka na ganta inji inna karime, watakila irin takurun nan ne na saudiyya ya taho muku da tsarabarta suka bushe da wata irin dariya, ita dai Rehab kallonsu kawai take yi da ido, Mahmoud ne ya gaji da irin cin fuskar da suke masa shi da matarsa, dan haka ya ja hannunta suka koma soro inda a nan ne Baffa ya yi musu shimfida, ha'kuri Baffa yake bawa Mahmoud da matarsa a kan halin su inna karime. "kayi hakuri mudi, ko a yanxu Allah ya nuna musu iyakarsu, ka fi 'ya'yansu komai na rayuwa da kai da matarka, don haka kada ka damu da duk wani sharri ko hassadar da xasu nuna maka, hakan baxai cutar da kai da komai ba,sai ma dai d'aukaka da xai 'kara maka kai da iyalanka, kuma ka xama mai kyautatawa matarka kaga dai 'kauna ce tasa ta bar iyayenta taxo wajenka, to ka ri'ke ta da amana da gaskiya, kuma ka ri'ka hakuri da kawaici da dukkan gaxawarta, kada ka xamto mai kaushin hali a gareta, saboda ita mace an halicceta ne daga 'kashi mafi karkacewa, idan aka takura mata sai ta karye, ina yi muku fatan Alkhairi Allah ya baku xaman lafiya da yalwar arxiki, kuma ya kamata ku tashi ku tafi don bana son ku yi dare a hanya. mahmud ya ji dadin nasihohin da Baffa yayi masa, hannu yasa a aljihu ya mi'kawa masa rafar 'yan d'ari biyu, godiya mai yawa yayi masa sannan suka yi sallama suka tafi. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRAH* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *β™»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *ke uwa ce ta gari, da kowane d'a xai yi alfahari da sΓ munki a rayuwa muna godiya da yadda kike ji da mu,ki ke kulawa da mu, kike damuwa da dukkan abinda ya damemu, muna yinki, muna alfahari da ke, kuma muna sonki Auntynmu MUNEERAH ABBAH WAKEELI DANDAGO jeeddah tace ana mugun tare🀝kuma wannan page gaba d'ayanashi naki ne halaka malak* 1⃣8⃣ Hanyar kano suka d'auka, xuciyar Mahmud sai tafasa take yi saboda jin xafin maganganun su innah karime, godiya ya yi wa Allah da yasa Rehab bata fahimtar abinda suke cewa, shirun da Mahmud yayi ne,shi yasa Rehab ta fara yi masa hirar kyautatawar da wata ma'kociyarta Ke yi mata, da yadda ta jawota a jiki ta xama tamkar 'yar da ta Haifa a cikinta, Mahmud ya ji dad'in yadda ta saki jiki take mu'amala da jama'a, haka suka isa gida cikin farin ciki da Walwala. A 'yar wannan xiyarar da suka kai 'Dan batta har Rehab ta fara gane yadda inna karime da Habi ke 'kin Mahmud, tambayar shi tayi dalilin da yasa suke masa haka, har da ita ba'kuwar da bata dad'e da xuwa ba, amma Sam Mahmud ya'ki xancen ya nuna mata ba komai, suna masa haka ne saboda shi ne 'karami suna son ya tashi da tarbiyya, murmushi tayi ta kalle shi kawai, amma ita kanta tasan ba haka abin yake ba, kawai yana 6oye mata ne. A Kwana a tashi Yau Mahmud sun Kwashe shekaru biyar da aure inda Allah mad'aukakin sarki ya axurtasu da haihuwar 'Ya'ya biyu Nauwar wadda ita ce Babba sai kuma 'kaninta Muhammad wanda ake kira (fu'ad), duk wannan haihuwar da Rehab tayi babu wanda ya ta6a xuwa barka daga 'Dan batta, Baffa ne kawai yake'kokarin xuwa yaga jikikonsa, Rayuwa suke yi mai cike da farin ciki da ban sha'awa. *BAYAN SHEKARA GOMA SHA HUDU* A kullum Mahmud dad'a samun arxi'ki yake yi da 'karin girma, don har ya yi gidansa na 'kishin kansa wanda ya gina shi a unguwar Nasarawa GRA (Dawaki road) a yanxu babbar 'yar su nauwar tana da shekara goma sha biyu, 'kaninta fu'ad na da shekara Tara, ganin yadda Allah ya axurta Mahmud ne da dukiya mai yawa, shi yasa innah karime da Habi suka kudiri aniyar mallake shi, da dukkan abinda ya mallaka a rayuwa, don ya dawo 'kar'kashin ikonsu sai yadda suka yi da shi, yawon Bokaye da 'yan bori da malaman tsibbu suka fara yi, duk don su cimma burinsu na mallakar Mahmud har abada, sun shirya tattaki har 'kasar Niger don su had'u da wani Boka wanda ake kira *Gobe da nisa*, wata 'kawar Habi da ake kira gwaggo sa'ade ita ce xa ta yi musu jagora har wajen Bokan, saboda a cewarsu rehab ta mallake Mahmud sai yadda tayi da shi. Kwana biyu suka yi a hanyar xuwa Niger suna tafiya, saboda Nisan garin da xasu shiga, ko sallama basu yi da Baffa ba sai filin gidan ya tarar. A wani 'kauye suka sauka, don a nan ne xasu samu wadda xata yi musu jagora har gurin *Gobe da nisa* da sassafe suka tashi suka fara haramar tafiya, Satinsu guda a hanya suna keta 'kauyuka da dajuka, ga abubuwa masu had'ari da suka ri'ka karo da su, amma hakan bai sa sun saduda sun koma gida ba. A ranar da suka cika Kwana takwas da tafiya, suka isa 'kauyen da Gobe da nisa yake, ba su suka kai tsibirin da yake ba, sai bayan sallar la'asar ga gajiyar tafiya da suka d'akko ga yunwa da suka Kwaso Wani 'katon dutse suka gani manyan kattin maxa na kawaye da shi, tun daga nesa suka hangosu suka daka musu wata tsawa mai ban tsoro, har sai da suka fad'i don firgici da tsoron da ya kamasu, tambayarasu suka yi a kan me ya kawo su, gwaggo sa'ade ce ta bashi amsa mun xo wajen alagafarta malam ne, sake xare mata jajayen idanunsa yayi sannan ya bata amsa da ya shiga aiki baxai sake fitowa ba sai Gobe da safe, Idan har suna da bu'katar ganinsa sai dai su jirashi har ya fito. Shiru suka yi ba abinda jikinsu ke yi sai karkar wa saboda sun gama tsorata da mutanen Sam babu annurin imani a tattare da su, umarni ya basu da su tashi daga inda suke kowaccensu ta tsugunnah ta kuma sunkuyar da kanta, har xuwa wayewar gari, saboda a cewarsu aljanun gurin basa son kallo ido cikin ido, kuma dokarsu ce ba a xama haka sai an sunkuyar da kai, haka suka sunkuya xuciyar su cike da fargaba, sun dad'e basu ga mutane irin Wadannan ba, saboda siffarsu tamkar ta arnan daji take. A haka suka kasance kawunansu a sunkuye har Allah ya Wayi garinsa, da sassafe aka yi masu ixni da su shigo su gana da shi. 'Kofa aka bud'e musu wata 'katuwar Bukkah suka tarar, duk an Kewaye jikinta da layu da fatun namomin daji daban-daban, da sallama suka shiga ciki tsawa ya daka musu," kun 6ata mana aiki kun cuci kanku,ba a yi mana sallama a nan, ma son sallama, Ku juya Ku fita da baya da baya, baxan kalleku yau ba, inna ce ta fara bashi hakuri ya xare mata jajayen idanunsa, jikinta na rawa ta ja bakinta tayi shiru, haka suka juya a tsorace da baya da bayan har suka fice daga gurin. Sai da suka fi awa hud'u da fita sannan ya sake yi musu umarni da su shigo. Da baya da baya suka ri'ka shigowa d'aya bayan d'aya,nuni yayi musu da su xauna a kan buxun, "me ke tafe da Ku?ya tambayesu cikin wata murya mai ban tsoro" kallon kallo suka fara yi, kowacce na xungurar yar uwarta a kan ta fara bayani,saboda kwarjini da ban tsoron da mutumin yake da shi, inna karime ce tayi ta maxa ta fara bayani " mun xo ne a kan maganar wani jikana, so muke yi dama........."kafin ta 'karasa maganar ya dakatar da ita "innah ta fada mana komai, tun kafin ku xo an xayyana mana duk abinda kuke tafe da shi, kun kawo kukanku inda xa a share muku hawaye, xaku juya shi yadda kuke so, wani mudubi ya d'akko yana jujjuya shi sai ga hoton fuskar Mahmud ya fito a ciki, nan da nan ya fara kiran sunayen wasu manyan aljanu, wata tukunya ce ta fad'o tsakiyar bukkar wani haya'ki ne yake fitowa daga cikinta, ya mi'ka musu yayi, hannu biyu Habi tasa ta kar6a, bayanin yadda xa su yi da tukunyar yake musu " Ku je Ku binne wannan tukunyar a sabon kabari, amma kafin Ku binneta sai kun nad'eta da likkafani, duk yadda kuke so xa ku yi da shi, xaku juya shi kamar Waina, xaku sarrafa shi kamar ra'kumi da akala. Ku tashi Ku tafi bana bukatarku a nan". Ku juya da baya kamar yadda kuka shigo, godiya inna karime ta fara yi, daka mata tsawa yayi" wa yace ki gode mana? kina 'kara yi innah xata shanye miki 6argo sai dai wata ba ke ba, don haka ki kiyaye gaba, idon innah karime ne ya firfito ba abinda take iya cewa sai gyad'a kai da take yi, su Habi kuwa tuni suka fice suka barta a wajen. Tarar da su tayi an sake basu umarnin sunkuyar da kai, sannan aka umarce su da su canja hanya, kada su bi hanyar da suka biyo suka xo gurin, tafiya suke cikin daji babu abinda suke ji sai sautin kukan tsuntsaye, a tsorace suka cigaba da tafiya har Allah yasa suka iso wani d'an 'karamin 'kauye inda suka roki mutan garin da su basu gurin Kwana, da farko sun 'ki amincewa da kar6arsu, sai daga baya suka amince aka kai su gidan mai gari. Washe gari da duku-duku suka fara haramar tafiya ko karyawa basu tsaya yi ba, suka wuce gidan da suka sauka, bayan sallar axahar suka kama hanyar dawowa Nigeria. Sai bayan sallar la'asar suka isa 'Dan batta, malam Abdullahi suka tarar a bakin 'kofar gida yayi jugum yana tunanin halin da su innarsa ke ciki, duk ya rame yayi ba'ki abin tausayi, Kwana da Kwanaki yana nemansu shiru ba labarinsu, Yau ma wuni yayi yana kewaye gari duk jikinsa yayi la'asar, inna ce ta kira sunansa "Kai kan tace, da yake da wannan sunan take kiransa a mafi yawan lokuta, tunanin me kake yi haka? dagowa yayi a firgice ya tsugunnah, "na dad'e ina nemanku ina kuka shiga haka? Ba damuwarka bace sanin inda muka tafi, mi'ko min mu'kullina don bana son ka cika ni da shegen surutunka na banxa. Gida suka shige ita da Habi, kai tsaye d'akin inna aka shiga aka fara labarin gurin gobe da nisa "gaskiya Bokan nan gaske ne innah, Allah yasa dai aikinmu ya ci, mu mallake wannan shegen yaron mai mugun abu, kiga d'a tunda yayi arxi'ki ya guji kowa baya tsinana mana komai, tunda muke da shi bamu ta6a morar komai daga gareshi ba sai Wahala" "Shi yasa nace mu mai da hankali kanshi don so nake su nasiru su koma gidan da ya gina gonakin shi na nan kuma a bawa Isah ya cigaba da gudanar da harkokinsa, ni da ke kuwa duk can xamu koma, mu Kyale wannan banxan a nan" inji inna karime Dariya suka rika yi, oh!! Innah Allah dai ya sa mu yi galaba a kan yaron nan. Wa kike ganin xamu samu yaje yayi mana ha'kar nan a kabari innah? Bari Isah yaxo ko Audu nasan xasu iya yi, amma wannan shashan nasiru baxai iya ba tausayi ya masa yawa. Bayan sallar magariba Isah ya shigo a tsakar gida ya tarar da su, bayan sun gaisa suke fada masa abinda suke je yi Niger da aikin da suke son ya yi musu. Da farin ciki ya amsa yaji dad'in abinda suka xo masa da shi, don haka ko gidansa bai shiga ba ya saka 'yar shara ya ri'ka kewaye unguwa yana neman likkafani, a wajen wani mutum ya samu, ya wuce gida ya fara aikin nad'e tukunyar a ciki. Yana kammalawa ya mi'kawa innah karime da fara'arta ta kar6a tana sa masa albarka, shi kuma ya wuce gidansa da niyyar xuwa ya dawo, 'ya'yan gidan Audu ne suka shigo dauke da Kwanon abinci, mi'kawa inna abincin suka yi sannan suka cigaba da tsalle-tsallensu na yara, suna cikin wasan ne d'aya daga cikin yaran da ake kira musa yayi tsalle a kan tukunyar nan ta rugurguje. Innah karime na gani ta hau salati, nan fa ta hau yaron da duka da xagi tana tsine masa albarka, jin haka yasa Habi ta fito a guje tana tambayar abinda ya faru,"Wai a ce duk Wahalar da muka sha ta xuwa gurin Bokan nan da Kwanakin da muka shafe muna tafiya a ce wannan shegen yaron ya xo ya fasa mana tukunyar nan" kuka ta fashe dashi. A dai-dai lokacin da suke maganar ashe malam yana soro yana jinsu, sai da ya ji dukan da suke yi wa yaron yayi yawa sannan ya shigo ya basu hakuri, komawa kanshi suka yi suna xagi, a kan cewa shi ne ma yayi adduar da hakan ta faru, mallake Mahmud dai ba fashi, wucewa yayi d'akinsa ya kyalesu suna ta yi masa bala'i. Yana shiga ya lalubi waya ya fara kiran Mahmud ya shaida masa sharrin da su innarsa suke shirin 'kulla masa, ya kuma gargade shi da ya dage da addua da neman tsari shi ma yana nan xai taya shi, godiya yayi masa sannan suka yi sallama. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRA* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *β™»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† I Owe this all to you Hubby! my life would have never been this happy if you had not been there to save me. You saved me from myself and all my mistakes. You gave me another chance to be worthy of someone again. I love you with all my heart and I can never imagine my life without you. I dedicate this page to youπŸ’ž *MUSTAPHA MUKHTAR*😘 *Gaisuwa ta musamman gareki yar uwa NUSAIBA ABDULLAHI GALADIMA, jeeddah ta gode da 'kaunarki gareta* 1⃣9⃣ *A* fusace Isah ya shigo, saboda takanas ta kano innah ta taka, taje har gidansa ta sanar da shi, aika-aikar da Musa d'ansa ya yi musu, shi ma dukan yaron ya ri'ka yi kamar baxai barshi da rai ba, sai da 'kyar Habi ta kar6eshi. "Cuta ce dai yaron nan ya cuce mu ya gama da mu, shekarar arxi'kin mu ta kama, amma yaro ya yi mana ba'kin ciki, amma fa duk da haka baxa mu saurara ba, sai d'an nan ya xama mallakin mu, yanxu Isah babu dabarar da xa a yi a gyara tukunyar nan don Allah? wlh mun sha Wahala sosai a kan abin nan. "Babu yadda xa a yi innah, ta gama lalacewa sai dai mu yi ha'kuri. ko kuma ga Shawara, me xai hana gobe mu shirya mu je gurin wani Boka a bayan gari? "Ai kuwa abinda xa a yi kenan inji innah, Allah ya nuna mana goben sai mu fita da wuri don mu samu, mu gabatar da abinda muke so a kan lokaci. Amsa mata ya yi da amin, sannan ya tattara kan 'ya'yansa suka wuce gida. Yana shiga gidansa ko sallama bai yi ba, ya fara sababi yana fad'awa matarsa murja abinda ya faru, da yadda suke son yi wa Mahmud da iyalan sa, ita ma ta ji haushi sosai a kan abinda yaron ya yi musu, sannan ta 'kara 'karfafa masa gwiwar su sake komawa wajen wani Bokan, saboda ita kanta tana son ta samu canji ita da 'ya'yanta. ************************** Nauwar ce xaune a falo ita da Amminta suna karatun al-kur'ani mai tsarki, bayan sun idar suka yi addua suka shafa, sannan suka fara hirar duniya. "Ammina ina son ki fad'awa Abbana ya canja min school, saboda sam bana jin dad'in yadda Abbanmu yake kashe kud'i masu yawa a kan karatun mu, murmushi Ammi tayi. "Banda abin ki don an kashewa ilimi kud'i da yawa ai ba wani abu bane daughterna, ke dai ki taya Abbanki da addu'a, Allah ya 'kara masa yalwar arxi'ki, Amin tace, sannan suka cigaba da hirar duniya tana bata labarin 'kawayenta na makaranta suna ta nishad'i abin su. Sallamar wani matashin saurayi ne ya katse musu hirar da suke yi, matashin baxai wuce 25years ba, Irin samarin nan ne da ake kira FIRST CLASS. He is handsome, well dressed nd classic. Kana ganin shi xaka tabbatar da cewa jinin Rehab ne, don kamarsu d'aya da su Nauwar, kamar an tsaga kara, abu d'aya ne ya banbanta su da shi, He's chocolate in complexion, while su kuma farare ne 'kal. Ammi na ganin shi ta mi'ke tana mishi barka da xuwa, da gudu fu'ad ya 'karasa gare shi ya rungume shi yana oyoyo ya Hamdan, Where is the sweets you promised me? To cika ni mana sarkin rigima, ai na taho maka da shi, hannu ya saka a aljihu ya ciro masa sweets d'in ya bashi. Thank you ya Hamdan!! ya koma ya xauna kan cinyar shi yana ta farin ciki da ganin shi, ita kuwa Nauwar ko d'an kallo bai isheta ba, ta cigaba da kallon TV abinta. Tashi ya yi daga gurin da yake, ya dawo kusa da ita ya ja kunnenta, 'kara ta 'kwalla, Wayyo Ammina!! Fuskar shi a d'aure yake magana. " baki ga mutane bane?? kina ganina ki d'auke kan ki don ba ki da kunya ko? "Ka sakar min kunnena Ya Hamdan Allah ban ganka ba am sorry, oya get up ki bani juice a fridge, turo baki tayi, Allah ya Hamdan ban son tashi Idan ina kallon film d'in nan, dukan bakinta yayi, Wayyo bakina fa ka daka Yaya. xan fasa bakin da yake min rashin kunya ne. tashi tayi ba a son ranta ba ta d'akko mishi juice d'in ta kawo ta Ajiye. "Sai na ro'ke ki xaki xuba min ko?? I will deal with the hell in you,Idan kina min 'kiwa fa. "Harar shi ta fara yi da dara-daran idanunta, ta Mi'kewa tsaye tayi tana murgud'a masa baki, mai dukana sai dai ruwa yaro, a guje suka xuba ta fada jikin Amminta tana numfarfashi. "Me ke faruwa ta tambayeta? Ammi ki

Chapter 4 of 29