Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta samu adaidaita sahu. Har bakin layin gidan Alhaji musa aka kaita sai dai ta kasa gane gidan kasancewar an canjawa Unguwar fasali saboda fadan da ake yi. Tambaya tayi aka nuna mata gidan tana nufar kofar shiga ta tarar an rushe gidan ba Kowa sai fili, mamaki ne ya kamata saboda bata taba xaton xata tarar da wajen a haka ba. Ganin ta tsaya cak ta kasa aikata komai ne wani bawan Allah ya sameta yayi mata sallama Cikin girmamawa ta amsa masa, tambayarta yayi wanda take nema. Cikin sakin fuska ta amsa masa "gidan Alhaji musa Abbakura nake nema" Cikin tausayawa ya dubeta "Ai Allah yayi masa rasuwa sanadiyyar fadan da ake yi, duk an kashe iyalinsa dansa daya ne yayi ragowa shi ma kuma ba a San inda yake ba" Sunkuyawa tayi ta rushe da kuka mai ban tausayi. "Wayyo Allah Naga ta kaina, Yanzu Ina zan dosa ga yamma tayi Gashi ba nida kudin komawa Kano ga kudaden hannuna gaba daya sun Kare Allah ka dube ni da rahamarka da Jin kanka" Cikin tausayawa mutumin yayi mata magana "kiyi hakuri Allah xai dubeki ya baki mafita, da ina da wajen Kwana da na baku saboda na tausaya miki, to nima bako ne a gidan wasu na sauka, amma ki cigaba da tambayar mutane ko xa a samu mai taimaka muku, na barki lafiya Allah ya hadaki da naka gari dari biyar ya xaro a aljihu ya bata" godiya tayi masa suka yi sallama ya tafi, rasa inda xasu dosa tayi kuma ta kasa rokon Kowa ya taimaka musu, saboda tana Jin tsoron kada abinda ya faru da ita a baya ya sake faruwa. *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDA TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Bansan da bakin da xan gode miki ba QUEEN MARYAM (maman surayya)ina godiya da kyautatawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci* 4⃣6⃣ Duk wanda yaxo wucewa kallon su yake yi, saboda kowa tunani yake yan ta'adda ne suka yi basaja. wani babban mutum ne yayi ta maxa yaxo ya sami Nauwar. sallama yayi mata, ita kuwa saboda tsananin kukan da take yi,ta kasa magana sai a cikinta ta amsa sallamar, magana ya fara yi mata "me ku ke yi a nan, kika xauna ke da wannan mahaukaciyar, me ya fito da ku daga gida da yammacin? kin san dai duk kwarya ta gari tana ragaya ko? ya kamata ki tashi ki tafi, don gaskiya bama barin wadanda bamu sani ba su xauna mana a unguwa, sai dai idan da ixnin mai unguwa xasu xauna" kallon shi take yi kawai,ta kasa ce masa komai saboda bakin cikin da ya tokare mata makogoro. sake dubanta yayi "magana nake fa kin kasa bani amsa sai faman kuka da kike yi, na fada miki sharadin xama a nan, ko ki tashi ko nasa yara su yi muku a tire, don irinku ba abin yarda bane" kafin tayi magana tuni ya fara kiran yaran unguwar,kan kace me, tuni sun taru sun fara jifan su da dutse,suna yi musu waka, ganin xasu illata su ne, yasa taja hannun Ammi da kyar suka bar gurin,tana tafe tana kuka, sai da suka yi tafiya mai nisa sannan ta samu suka xauna, idanunta sun kad'a sun yi jawur, ga yunwa da kishiruwa ga gajiyar tafiya ga bacci da ya dameta, don rabon da ta samu ta rintsa tun lokacin da Abbanta ya koreta daga gida. Ammi ce tayi wani gunji mai ban tsoro inda ta kama Nauwar da duka ta ko'ina, shake mata wuya tayi ta hadata da jikin bango, ta rika gwara kanta da bangon, kamar baxa ta barta da rai ba. tunda Ammi ta fara rashin lafiya bata taba shiga irin wannan halin ba sai yanxu, ihu Nauwar ta rika yi, tana neman taimako amma Ammi ta ki ta daina dukanta, kasancewar gurin babu jama'a sai su kadai sai gidaje a kulle, wasu mutane Allah ya kawo da kyar suka kwaceta a hannunta, da gudu tayi kansu da duka tana jifan su da duwatsu. Haukan Ammi yanxu ya koma na duka, sai da ya kasance duk wanda yaxo wucewa sai ta jefe shi ko ta watsa masa kasa. a ranar kwanan xaune suka yi, saboda da Nauwar ta kwanta xata rufe ta da duka, sai tsallakawa tayi ta kwanta a gefen wani kanti. washe gari da Asuba ta farka, tarar da Ammi tayi kwance cikin kwata tana ta bacci abinta, da sauri ta karasa wajen tana kuka, duk jikinta ya baci da kwatar, wani bawan Allah ne ya taimaka mata suka fito da ita, inda ya kawo sabulu da ruwa ta wanke mata jikinta. duk wanda ya kalli Ammi yasan ta xama mahaukaciya tuburan saboda abinda bata yi da, shi take yi yanxu. tambayarta ya yi. "ke kuwa baiwar Allah daga ina kike haka, ga ki da mai lalura" share guntun hawayen da ke idonta tayi, ta fara bashi labarin abinda ya faru da su, da kuma garin da suke. tausaya musu yayi kwarai da gaske, sannan ya bata shawarar xuwa gidan mai unguwa ta fada masa abinda ya faru da su. cikin nutsuwa tayi masa magana "ai ban san gidan mai unguwar ba" dansa ya kira yayi mata rakiya, kasancewar shi xai wuce asibiti wajen mahaifiyar sa. ba tare da bata lokaci ba, yaron yaxo don yi musu rakiya, suna tafe Ammi na turjewa, a haka har suka isa gidan. A soro suka tarar da mai unguwa inda suka yi masa sallama, cikin girmamawa ya amsa, ya kuma tambaye su abinda ya kawo su, bayani tayi masa ya tausaya mata sosai, sai dai xuciyar sa bata gama amincewa da su ba, saboda yan ta'adda sukan xo da wannan sigar su cuci mutane, daki ya basu wanda yake a tsoron gidan, ya kuma yi umarni a kawo musu abinci da ruwa. ********************** A bangaren su innah karime kuwa farin ciki ne ya cika xuciyar su,saboda sun kori su Ammi da yayanta sun mallake komai, gida ya xama nasu, su da jikonkin su, Habi ce ta shigo rike da kwanan abinci a hannunta, guri ta samu ta xauna ta dubi innah karime. "wai kuwa innah kina tunawa da tsinanniyar matar nan, da taso ta hana mu xaman lafiya a gidan nan" "uhmmm habi kenan kema baki tuna da ita ba sai ni, da ta tsane ni taki jinina, ai na godewa Allah na godewa Boka da yayi mana wannan aikin,ya tarwatsa musu rayuwa, yanxu ma so nake a kara yin wanda xa a farraqa tsakanin yar da uwar, taki taimaka mata, kin ga abin xai mata yawa,ga hauka ga ya ta gujeta, daga nan kinga sai mutuwa kenan" hada hannu suka yi suka tafa, suka bushe da dariya, sallamar da aka yi ne ya katse musu hirar da suke yi. mamin Hamdan ce taxo, a tunaninta har yanxu su Nauwar na gidan, babu wanda ya kalleta ballantana tasa ran xai amsa mata sallamarta, duba dakinsu Nauwar tayi,taga ba kowa gaba daya kayan dakin su an fitar da shi,ya xama kamar kango. mamaki ne ya kama ta, don haka kai tsaye ta fito daga dakin ta tsaya a wajen da su innah karime suke tambayar su tayi. "bayin Allah ban yi xuciya ba, dan Allah ina mai dakin nan take ko bata nan" A yatsine Habi ta kalleta "ga amsar nan ai kin bawa kan ki" fitowa tayi ta rabu da su, mai gadi ta tarar yana ta faman shara, har kasa ya xube ya gaishe ta, tambayar shi tayi ina su Nauwar. sunkuyar da kai ya yi yana share kwalla. "Ai Alhaji ya kori su Hajiya yau kusan kwana biyar kenan" cike da mamaki ta dube shi. "ya kore su fa kace malam Ali" "wlh da gaske nake Hajiya, nima da nayi masa magana sai da ya ci min mutunci" salati mami ta rika yi, tana hawaye "amma mahmud bai kyauta ba,bai yi adalci ba, amma ba komai akwai Allah" fita daga gidan tayi kafin ta isa gida xaxxabi ya rufeta. tana shiga falo ta tarar da jaka a ajiye, samun guri tayi ta kwanta, tana mamakin ganin jakar da kuma abinda ya faru da su Nauwar. Hamdan ta gani a kanta yana mata murmushi. kallon shi tayi ta harare shi. "yanxu Hamdan kasan xaka dawo amma baka yi min waya na hada maka komai ba" dubanta yayi cikin sakin fuska "kada ki damu mami xan je gidan su matata Nauwar naci" hawaye mami ta shiga sharewa tausayin Nauwar da Hamdan ne ya kamata, ta rasa ta inda xata fara fada masa abinda ya faru. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ku, JUWAIRIYYA LUKMAN AMIN (maman shuraym) & HAUWA'U HAMZA SA'EED ZARIA ina godiya da kaunar ku gare ni* 4⃣7⃣ cikin kulawa ya kalli maminsa "mami me ya faru naga kina share hawaye,ko bakya jin dadi ne?" "Lafiyata kalau Hamdan amma abinda ya faru har gara rashin Lafiyar a kan faruwarsa" cikin raxana ya dubeta. "me ke faruwa mami, dan Allah ki fada min ko xan samu saukin fargabar da nake ciki" "baxan fada maka ba Hamdan har sai kaje kaci abinci ka watsa ruwa a jikinka, kuma ina so ka kwantar da hankalin ka abin baya bukatar daga hankali addu'a aka fi bukata" idanun Hamdan ne suka kada suka yi jawur,gaba daya ya kosa yaji abinda maminsa take son fada masa. marairace mata yayi "dan Allah ki fada min mamina, ko dai akwai abinda kike boye min ne wanda bakya so na sani game da gidan nan" dafa kafadar shi tayi "bana boye maka komai Hamdan kuma babu abinda ya faru da gidan nan, nafi son kaci abinci sbd xaka fi samun nutsuwa idan na fada maka" da sauri ya tashi ya shiga kitchen ya xuba abinci a mintunan da basu wuce biyar ba ya kammala, sake dawowa yayi ya sami mami,don jin abinda xata fada masa. tsura mata ido yayi yana jiran tsammanin jin abinda xai fito daga bakinta, da nasiha ta fara masa. "ka sani duk abinda ya samu wani bawa daga Allah yake, kuma shi xai yaye masa a duk lokacin da ya so, sannan babu wani bawa da ya isa ya cutar da wani sai dai da yardar Allah, ina son ka bani aron hankalin ka kuma ka yi wa abin kyakkyawar fahimta" gyara xama yayi ya cigaba da saurarenta. "Hamdan!! ta kira sunansa, cikin sanyin murya ya amsa mata "bayan tafiyar da kayi Allah ya jarabci Ammin Nauwar da lalurar hauka" A raxane ya kalleta "hauka fa kika ce mami innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanxu Ammin tana ina? katse masa maganar da yake tayi,ka tsaya na karasa maka mana. "Fu'ad kuma Allah ya yi masa rasuwa, yanxu maganar nan da nake maka, Abban su Nauwar ya kore su daga gidan sakamakon baxai iya xama da mahaukaciya a gidansa ba" mikewa tsaye yayi hawaye na sauka a kan fuskarsa "wai mami abin nan ya faru da gaske ko kuma mafarki nake yi, yanxu ina su Nauwar din suke?" cikin tausayawa ta dube shi "nima wlh ban san inda suke ba, saboda babu wanda yasan ya kore su" "gaskiya mutumin nan ba shi da kirki mami, na dauki alwashin sai na nemo duk inda Nauwar da Ammi suke, ko da hakan xai yi sanadiyyar rasa raina" A fusace ya tashi ya shiga daki ya dakko jaka ya xuba kudi a aljihu, tsugunnawa yayi a gaban mami. "ina neman ixninki mami ki barni na nemo bayin Allahn nan duk inda suke, amma kafin na tafi xan fara kai cigiyar su gidan radio da televisions ko Allah xai sa a dace" "na amince maka Hamdan domin taimako xa kayi, ni kuma a koda yaushe ina son na rika ganin kana taimakawa wadanda ke cikin matsala, Allah ya taimake ka" tashi yayi ya fita kai tsaye ya wuce gidan radio ya bada sanarwa, bayan ya dawo ya fara hada kayan da xai yi tafiya da su, inda washe gari xai wuce neman su Nauwar. ******************** tunda su Nauwar suka sauka a gidan mai unguwa,ba su da matsalar abinci da wajen kwana, sai dai matsala daya da suke fuskanta har yanxu mai unguwa bai gama amincewa da su ba, kuma a kullum sai mutane sun xo sun yi korafin dalilin da yasa aka barsu a cikin jama'a, alhalin ba a san asalinsu ba, ba a san daga inda suke ba. yau da sassafe mai unguwa ya shigo dakin da suke. sallama yayi sannan ya samu guri ya tsaya. tsugunnawa Nauwar tayi xata gaishe shi. dakatar da ita yayi "baiwar Allah yau dai ba gaisuwa ce ta kawo ni ba, naxo ne na fada miki cewa ki tattara kayanki ku koma inda ku ka fito, saboda ya xa a yi yarinya kamar ki,ta bar gida ita da mahaifiyar ta, sai dai idan wani mugun abin ku ka aikata shi yasa ku ka gudu, baxan karbe ki wani abin yaxo ya faru a ce da sa hannuna ya faru ga kudin mota nan ku koma inda ku ka fito" dubu biyu ya jefa mata ya fita. da sauri ta bishi ta tsugunnah har kasa tana rokon shi. "dan Allah kayi mana rai kayi mana sutura kamar yadda Allah yayi maka ka barmu, mu cigaba da xama,wlh kaddara ce ta fito da mu daga gida, ba wani abin ashsha muka aikata ba, ka taimakawa rayuwar mu" "Allah ya taimaka man gaba daya, amma na miki iya taimakon da xan iya, ki kama hanya ki tafi inda kika fito" umarni ya bata ta dakko kayanta su fito su bar masa gidan sa, cikin kankanin lokaci suka fito suka kama hanyar barin gidan. gaba daya Nauwar ta kasa kuka sai istigfari da take yi, ko wani laifin suka yi wa Allah ya jarrabe su, kasuwar garin suka shiga, don su siya abinci su ci. karasawa suka yi wajen wata mai waina, suna isa wajen suka tarar da mata ne a cike a wajen,wasu na shan taba wasu na kitso, kallo daya xaka yi musu kasan ba Allah a ransu, gaba daya kallo ya dawo kan su nauwar, sallama tayi musu. a yatsine aka amsa, kudi ta xaro ta mika musu. mai wainar ce ta tambayeta "me xa a xuba miki" amsa mata tayi "waina da miya nake so" to nemi guri ki xauna "amma a leda xan baki don bana bawa mahaukata kwano na" hawaye Nauwar ta share tare da amsa mata da "to" addua ta rika yi a kasan xuciyarta Allah ya bawa Amminta lafiya a daina jinginata da kalmar hauka. xubo musu abincin tayi sannan tayi musu nuni. "ku tashi ku bar nan don duk wanda ya ganku a wajen nan baxai iya karasowa ya ci abinci ba, kuma dan Allah idan xaki fito ki rika barin mara lafiyar nan a gida, saboda xata rika firgita mutane" kasa magana Nauwar tayi saboda bakin ciki, karshen wata katanga ta samu suka xauna,suka ci abinci. Bayan sun gama ta xube kayan su a gurin, saboda ba su da gurin da xasu je, don haka ta yanke shawarar fara kwana a cikin kasuwar, tasan komai mai wucewa ne,wata rana sai labari. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:14 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan page din gaba daya naki ta mamah KHADEEJAH SABO ABDULLAHI (mom Hanash) ina godiya da yadda kike kaunar wannan littafi. ana tare* 4⃣8⃣ Haka suka kasance a cikin kasuwar har tsawon kwana goma, kullum Nauwar ke fita tayi bara ta samo musu abincin da xasu ci, cikin kwanakin gaba daya ta fita daga hankalinta ta koma kalar mahaukata gaba daya, don mutane da yawa suna tsammanin ita ma mahaukaciyar ce saboda yanayin kayan jikinta da takalmin da ke kafarta. kamar kullum yau ma da wuri ta fita don nemar musu abinda xasu saka a bakin salati, wata igiya ta samo ta daurewa Amminta kafa saboda tana gudun kada ta gudu ko taje taci kaxanta kafin ta dawo, dukanta ta rika yi a lokacin da xata daure mata kafar, lallabata ta shiga yi "kiyi hakuri Ammina, nima ba a son raina xan miki haka ba, bana son kici kaxanta ne wata lalurar ta sake kama ki" shiru tayi tana saurarenta kamar dama tana fahimtar abinda take fada, tana gama daureta ta tashi ta dauki roba ta shiga kasuwa. rumfunan kasuwar ta rika shiga tana neman taimako wadansu su bata wasu kuma su xageta, duk a tunaninsu yawon duniya ta fito, bayan ta dan samu kudin da xai ishe su siyan abinci, kai tsaye wajen mai abincin da ta siya jiya ta nufa, yau tarar da wajen tayi ba layi sai mutum biyu da suke tare suna hira. da sallama ta shiga wajen, abin mamaki cikin sakin fuska mai abincin ta amsa mata, inda ta bada umarnin maxan su matsa mata waje ta xauna. dubanta Nauwar tayi "ki barshi ba sai na xauna ba, ba anan xan ci ba, xan kaiwa Ammina taci sannan nima naci" cike da mamaki ta dube ta dama wannan mahaukaciyar babarki ce. gyada mata kai tayi alamar eh cikin tausayawa ta kalleta "Allah sarki amma na tausaya miki Allah ya bata lafiya" amsa mata tayi da amin ta xuba mata abincin ta mika mata. har ta wuce xata tafi ta kira sunanta *AL-MAJIRAH* amsa mata tayi sannan ta dawo ta tsaya. kallonta tayi tare da kashe mata ido daya "idan kin kai mata abinci taci, ki dawo akwai taimakon da xan baki" godiya tayi mata sannan ta tashi ta tafi. tana juya baya,ta dubi maxan tace. "ya kaga yarinyar nan dan gaye tayi dai ko, da alama xata kawo alkhairi, ko ya ku ka ce? amsa mata suka yi "tayi sosai Hajiya xa tayi dadin harka wlh, da gani kuma baxa tayi tsada ba saboda Almajirah ce bata san dadin kudi ba, Allah yasa dai kada ki wayar da ita taxo tafi karfin talakawa irin mu. murmushi tayi tare da kashe ido, "baxa ta gagare ku ba dan gaye, ku dai ku yi addua Allah yas mu ja ra'ayinta" Nauwar na isa wajen Ammi ta tarar har ta fara kwance daurin da tayi mata. da hanxari ta karasa ta gyara mata sannan ta fara bata abincin, sai da taci ta koshi sannan ita ma ta dauki ragowar taci, suka sha ruwa, 'kara komawa wajen mai abincin tayi don karbar taimakon da tayi mata alkawari. Tana xuwa wajen ta bata guri ta xauna, gyara xama tayi sannan ta dubeta ta fara magana. "na tabbatar da cewa kina cikin tashin hankali kuma kina tsananin bukatar taimakon wajen kwana da abinci, ko ba haka bane?" kallonta tayi ta amsa mata da haka ne. sake turo dankwalinta tayi gaban goshi "tunda kuwa haka abin yake, ina so ki karkade kunnuwan ki kiji abinda xan fada miki, xamanki a haka baxai yiwu ba dole ki tashi ki nemawa kanki yanci da mafita, idan ba haka ba kuma bakin cikin duniyar nan ya kashe ki, duk fadin wajen nan ki duba, babu mai taimakon ki, sai dai idan ke kika taimaki kanki, nima da kike gani tausayi kika bani nace xan taimaka miki, don naga tun ranar da kika xo siyan abinci a nan, kasuwar ku ke kwana har xuwa yanxu, wannan ya tabbatar min da cewa ba ku da galihu" duk bayanan nan da take nauwar na saurarenta "ni sunana Amarya uwar marayu, nice nake bawa duk wani maraya ko wanda iyayensa suka kore shi daga gida wajen kwana, amma fa da sharadi, sharadin baxan fada miki shi yanxu ba sai kin amince da taimakon da xan miki, idan kina bukata sai kiyi magana, yau din nan ku bar kwanan kasuwa ku koma gida" da sauri Nauwar ta amsa mata da na amince aunty. "to shikenan tunda kin amince, aikin namu ba wani mai wahala bane kuma ana samun kudi sosai xaki warwarsa har ki taimaki wani, tashi ki dakko kayanki, da mahaifiyarki kixo mu tafi. tashi tayi ta dakko Ammi da yan tsummokaransu suka nufi hanyar gidan Amarya uwar marayu. Wani daki ta shigar da su a cikin gidan, manyan garada ne maxa da mata ana ta holewa wasu na ta faman busa sigari, suna ganinta wasu yan mata suka taho da gudu suka rungumeta. "Oyoyo uwarmu maganin kukan mu, daya ce ta dubi su Nauwar ta bushe da dariya. "kai Aunty kin iya jajibe-jajibe a ina kika samo wadannan tarkacen kuma" kallonta tayi ta harareta "ke bana son iskanci wadannan sun wuce tarkace, akwai alherin da xa a samu a tare da su" wani daki ta wuce da su, ita dai Nauwar tunda taga yanayin gidan taji hankalinta gaba daya bai kwanta ba, amma tunda ba su da wajen kwana xata xauna ne a lalura. maxa ne suka rika shigowa dakin, duk wanda yaxo sai ya kalli Nauwar sama da kasa sannan ya fita, a falo ta jiyo abinda suke fadawa Aunty Amarya. "yarinyar tayi Aunty saboda yar shila ce, yanxu gyara mana ita kawai ya rage miki" fargaba ce ta cika xuciyar Nauwar ta rika addua Allah ya tseratar da ita daga fadawa halaka. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRAH* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Ina taya yar uwa NASEEBAH ISMA'IL murnar cika shekara guda da fara rubutu Allah ya kara basira da xakin hannu* 4⃣9⃣ Cikin dakin Nauwar suke Amarya ta shigo sallama tayi, hannunta rike da bakar leda, samun guri tayi ta xauna ta dubi Nauwar. "bayin Allah sannunku da hutawa ku yi hakuri na jingine ku ba tare da naxo mun xauna mun fara tattauna abinda ke gaban mu ba" cikin girmamawa Nauwar tayi mata magana "ba komai Aunty ai naga gidan cike yake da baki" "hmm kwarai kuwa, yau ma ai ba kiga komai ba, saboda ragowar masu xuwan basa nan sun yi yar tafiya" yanxu dai abinda nake so ki tashi ga ruwa can kije ki watsa ko kya yi kyan gani,Wannan kuma kaya ne idan kin yi wankan ki saka. mika mata ledar da ke hannunta tayi sannan ta cigaba da magana, bayan kin fito daga wankan ina so kixo ki sheqa kwalliya ta daukan magana, don da kwalliyar ne xaki jawo hankalin wadanda xasu rika xuwa xiyara gidan nan, daga nan kema ki samu naki rabon. tashi Nauwar tayi ba tare da ta amsawa Amarya maganarta ba, har ta kai bakin kofa xata fita daga dakin ta kira sunanta "Almajira!! juyowa tayi ta dubeta. "ya xa mu yi da Wannan mahaukaciyar, kinga ke yanxu da hankalin ki kina gane komai xaki iya biyawa kan ki kudin haya, ita kuma ya xa a yi da ita, don kinsan ni ba a min xaman banxa a gida, duk yarinyar da kika gani a gidan nan neman kudi take yi, idan kuma kin amince xaki biya mata da dan abinda xaki rika samu shikenan ta kwana gidan sauki" idanunta ne suka cika da kwalla, kokarin sharewa tayi sannan ta amsa mata da xata rika biyan kudin hayar bandaki ta wuce ba tare da bata lokaci ba ta fara wanke daudar kwana da kwanakin da ta makale a jikinta, tana gama watsa ruwan taji wata iska na shigarta ko ta ina, rabonta da taji irin wannan iskar a jikinta har ta manta, tana fitowa ta shige dakin da Amarya ta sauke su, tararwa tayi an ajiye mata kayan kwalliya da mayuka masu kamshi da turaruka, shafa man tayi ta shafa yar powder, sannan ta saka kayan da Amarya ta kawo mata, riga da skirt ne daidai jikinta,kayan sun karbeta kwarai, idan ka ganta baxa ka taba cewa ita ce a cikin yanayin kunci da damuwa ba, saboda kyawunta ya fito sosai. fita waje tayi don ta roki Amarya alfarma ta taimaka mata d ruwa da sabulu ta wanke Amminta. kallonta tayi a wulakance sannan ta bata amsa. "ke ni fa bana bawa wanda ba shi da amfani kayana, yanxu ita wannan ko wankan tayi amfanin me xai mata,waye xai gani ya yaba, kema da kika ga na baki, don nasan xaki biyani ne nan gaba, idan kina son ruwan wanka da sabulu ki fita waje akwai wajen da ake siyarwa xaki samu" da bacin rai Nauwar ta koma daki ta hada kai da gwiwa, ita gaba daya bata san irin rayuwar da Amarya take shirin jefata a ciki ba. yamma nayi Maxa da mata suka fara taruwa a gidan, ana ta sheke aya kowace budurwa da saurayinta, wasu na daki na sabon Allah wasu

Chapter 12 of 29