Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka kasance har zuwa sallar azahar, bayan tayi sallah, ta yanke shawarar sake fita don ta nemo abincin rana da na dare, yanxu ma sai satar hanya tayi ta fita ba a son ran mahaifiyarta ba. yau kai tsaye kasuwa ta nufa, don tana da yaqinin anan sai tafi samun taimako, rumfar kasuwar ta rika lekawa tana neman taimako, yau kam ta fita a sa'a don abinda ta samu ya kusa 500, don haka ta tsaya ta siya kwaki da sugar da sabulun wanka. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRAH* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *β™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *Gaisuwa ce ta musamman nake mikowa gareki, yar uwa babbar yaya gareni Hajiya Ameena Basheer (Maman siyama) Allah ya raya, Sadeeq, siyama, saudah, safiyya & suhaila, ina godiya da kulawarki gareni, ana tareπŸ€πŸ’―* *wannan shafin gaba dayanshi naki ne halak malak Dr. Aysha Abubakar ishaq, ina godiya da kulawarki gareni, Allah ya bar zumunci* 🀝 πŸ”Ÿ *T*ana dawo wa kangon da suke kwana ta nufa, da sallama ta shiga ta iske Amminta na wasa da kasa tana ganin yartata sai ta saki dariya da alamar murna da farin cikin ganin d'iyarta ta, 'karasawa wajenta tayi ta rungumeta "Ammi kin san yau me muka samu kuwa?? kwaki na samo mana..... ai kina son shi ko Ammina? kallonta kawai take ba tare da tace mata komai ba, sai murmushi da take yi, tana wasa da 'yan yatsun d'iyartata, kallo take mata mai cike da soyayya da tausayi, sai dai babu bakin magana ballantana ta gode mata. "cikin nutsuwa ta janye hannunta gareta, kallonta tayi tana mata murmushi. Ammina xan fara wanke mana kaya sai na jika mana kwakin kin ji, ita dai bin ta tayi da ido kawai. "tana mi'kewa ta ri'ke mata hannu gam ta'ki sakinta, sai ta koma ta xauna. "Ammina ba kya son na tafi na barki ko?nima bana son nisa da ke, dole ce ta sa nake tafiya na barki. murmushi mahaifiyar take yi tana shafa kan yarinyar tata, tausayin *Amminta*ne ya kara kamata, ji take a ranta ina ma dai ta rika d'aukanta suna tafiya, sai dai ba tada halin yin hakan, cigaba da lalla6ata tayi a kan ta saketa, amma taki sakinta. sai ta mika hannunta ta wanke kwakin ta xuba sugar ta fara bata, sai da tasha ta 'koshi sannan ta daina bata, cigaba da lalla6ata tayi har sai da tayi bacci sannan ta tashi ta fita. "kayan su ta dauka ta nufi wani famfo da almajirai ke d'iban ruwa don ta wanke musu , da isarta wajen tayi sa'a babu kowa, don haka ba tare da 6ata lokaci ba ta fara wanke tsummokaransu, tana yin wankin tana tunanin yanzu a haka zasu cigaba da rayuwa ba tare da kulawar dangi ba, ko kuma mahaifi. ya Allah kana sane da mu, a wajenka muke neman taimako. "tsawar da ta ji an daka mata kamar daga sama har sai da tayi kamar xata kifa qasa ita ce, ta dawo da ita hayyacinta. "ke *AL-MAJIRA* 'yar mahaukaciya matsa ki bamu guri muna da abin yi a wajenmu,kin wani xo kin tara mana tsummokarai masu wari a waje, an fad'a miki nan famfon mahaukata ne? matsa dallah can, kada ki shafa mana qarxuwar hauka. d'agowa tayi ta kallesu idanu cike da hawaye tace Allah ya baku hakuri. shigewa tayi ta barsu a wajen suna ta mita har da xaginta, har tayi nesa dasu basu daina nunata suna aibata ta ba. "mutane ta hango cike da bakin kofar kangonsu, tana ganin tarin jama'ar taji gabanta ya fadi, a tunaninta ko wani abu ne ya sami Amminta, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta shiga karantawa, 'kosawa tayi ta isa bakin wajen, saboda ta ganewa idonta abinda yake faruwa da su. tunda ta kusanto wajen take jin maganganu sama-sama da alama dai taron nasu ne, gani tayi wasu mutane sun bude 'kofar kangon suna jefo musu kayansu waje, a sanyaye take tafiya jan kafa kawai take yi, babu abinda yake sauka a fuskarta sai hawayen takaici. ganin yadda ake jan Amminta ne yasa ta tafi da gudu ta rungumeta tana kuka, wasu mutanen har da dukanta saboda gaddamar da ta yi musu. masifa suke yi sosai"wallahi baku isa ba, baxa ku qara kwana a anan ba, yau-yau d'in nan sai kun bar layin nan, banda bala'i da masifa mutane ba a san asalinku ba, kawai kun xo kun tare a kangon mutane, to wallahi baxa ta sa6u ba sai kun tashi kun bar wajen nan" kuka mai tsanani take yi "dan Allah ku taimaka mana, wlh ba mu da kowa sai Allah sai ku, idan ku ka koremu bamu san inda xa mu je ba. "rufe mana baki munafukar banxa da wofi, duk matar arxiki tana gidan mijinta, kuma duk yarinyar arxiki tana gidan iyayenta, idan kuma mahaukaciya ce tana gida an killace ta, wulakantacciya ita ke bin kangwaye tana kwana, watakila ma a garin asirinku ne na mata, ku ka yi, ya koma kanta, kasa cewa komai tayi, saboda ko tayi maganar ma baxai saurareta ba. muryar wani mutum taji "ku wai dan Allah ba ku da imani ne? banda kuna da karamin tunani wad'annan mutanen sun yi muku kama da mugwaye, ku riqa aiki da lissafi mana. "kai dallah gafara can shi. mugu yana da kama ne, kana ganin yadda matar nan ta takurawa yayanmu, ba halin a aikesu sai duka da jifa da dutse, to me yayi xafin haka, yara da unguwarsu ba a isa a hanasu sakewa ba" "dan Allah ku yi hakuri ku tausaya mana, ku duba halin da muke ciki, idan kuka koremu daga nan wlh ba mu san ina zamu dosa ba. "ku tafi 'karshen duniya ma ina ruwanmu, ai duniya makaranta ce tana koyawa mutum abinda bai sani ba" "da 'kyar aka sasanta suka barsu dan su cigaba da kwana, amma da sharad'in sai an d'aurewa Ammi 'kafa, a cewarsu wai tana takurawa yaransu, haka ta yarda aka daureta ba don ranta ya so ba, saboda tasan sharri aka yi wa mahaifiyarta, Ammi ita da ko fita bata yi, a ina taga yaransu har ta dakesu. hawaye masu xafi ne suka cigaba da sauka a kan kuncinta, kayansu ta rika kwashewa tana shigar da su ciki. sannan ta rike hannun Amminta don ta shigar da ita ciki, suna tafe tana d'ingisawa kamar mai ciwon 'kafa saboda daurin da aka yi mata. "xaunar da ita tayi ta rika duba gurin da mutanen suka daketa, tana bata hakuri gami da rarrashinta, ita dai bin ta take da ido ba abinda take iya ce mata. sallama taji kamar daga sama, wannan matashiyar yarinyar ce ta sake dawowa dauke da kwanon abinci, yau dai babu alamar tsoro a tattare da ita, da karfinta take takawa, 'karasowa kusa da ALβž–MAJIRA ta yi, don a yanxu ta fuskanci ba ita ce mai lalurar haukan ba, don haka ta mi'ka mata hannu don yin musabaha, ita ma hannun ta mika mata suka gaisa. Ta mika mata kwanon abincin tayi mata godiya mai yawa sannan ta karbi kwanon da ta kawo musu abinci jiya. har bakin kangon ta rakata, har ta juya don ta kulle 'kofa, sai taga ya dace tasan sunan yarinyar da dalilin da yasa take tausaya musu haka, duk da cewa bata san asalinsu ba. "murmushi tayi sannan tace ni sunana *Saimah* gidanmu yana nan bayanku, mahaifina ne ya ganki kina bukatar taimako shi ne ya sanarwa momyna yace a rika baku abinci, sbd yaga halin da kuke ciki na talauci ga shi mahaifiyarki tana da lalura, mu a xatonmu ke din ma ba ki da lafiya sai yanxu muka gano lafiyarki kalau. a jiyar xuciya tayi sannan tace wlh lafiyata kalau, halin da ya samu mahaifiyata ne yasa ake min kallon mahaukaciya, Amma sam ba nida lalaurar hauka. "ko xaki iya fada min matsalarku ni kuma na sanar a gida, ko Allah xai sa a mu iya taimaka mu ku??hawaye ta cigaba da sharewa, na tabbatar baxa ki iya yi mana maganin matsalarmu ba, saboda abubuwa ne masu yawa suka faru da mu. 'kara tambayarta saimah tayi ko kin san lokacin da amminki ta kamu da wannan lalurar? eh "na kiyaye wasu abubuwa saboda a lokacin ban fi shekara tara ba tun daga wannan lokacin muka bar gidanmu dangin mu da garin mu muka dawo wata rayuwa tun daga sannan muke fuskantar qalubale, kala-kala idan muka je wani wajen ma cewa suke ni ba yar halak bace....... tausayi ne ya bayyana a fuskar *Saimah* tabbas kina cikin wani yanayi wanda kuke bukatar a jawo ku ajiki,don kuji sanyi da nutsuwa a rayuwarku. xan je na tambayi Abbana a kan ya baku wani d'aki asoron gidanmu ku karasa rayuwarku anan kafin Allah yasa a ga danginku,sbd xamanku anan ba dadi. "bata san lokacin da ta yi wani murmushin farin ciki ba. "dama har yanxu akwai irinku masu tausayawa bayin Allah,... Allah ya biyaku da aljannah" "kada ki damu ki daina godiya ai komai kayi kanka ka yi wa.kuma alheri danqo ne ba ya faduwa kasa banxa. "Ammi suka gani ta kwance daurin kafarta tana kokarin kama katanga xata haure ta gudu, don haka da hanxari suka 'karasa wajen tare da yin salati, "ina xaki je?suka fada tare. muxurai kawai take yi, bata ce musu komai ba,sai kawai gani suka yi har ta d'ane katangar , ga shi su kuma baxa su iya hawa ba, dan haka suka fita waje suna neman d'aukin jama'a, sai dai kafin su dawo sai filin wajen suka tarar. kuka ALβž–MAJIRA ta fara yi. Ammi ki taimakeni ki dawo ba nida kowa sai ke, idan kika tafi kika barni waye xai karbeni a duniyar nan. kukan da take yi shi ya bawa kowa tausayi a wajen, don haka wasu samari suka yanke shawarar bin ta. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRAH* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *β™»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *Alhamdulillah, Allahu mun gode maka bisa da ni'imar da kayi manaπŸ‘πŸ»A Yau Allahu madaukakin sarki ya nufemu da kammala karatun mu na degree, Allah ya bamu abinda muke nema na sakamako kyakkyawa*πŸ‘πŸ» *congratulation MARIAM TIJJANI ADAM on your POP (NYSC) I Wishes all d best, in all your indeavors may mighty Allah, guide help and give you all d best* 1⃣1⃣ *C*ikin xafin nama Ammi ta sheqa da gudu, take samarin suka bita, amma ina tuni ta yi musu nisa sosai, don haka suka yanke shawarar su samu machine su bi ta, gudu take yi ba kak'kautawa, don haka suka nemi taimakon mutane akan su riqe ta, cikin taimakon Allah suka samu nasarar kamata. dawo da ita suka yi kangon sannan suka bawa Almajira shawara ta daina fita ko'ina gudun kada ta sake guduwa, godiya ta yi wa samarin sannan suka yi sallama da saimah ta wuce gida. "zaunar da Amminta tayi tana xubar da kwallah, ita kuma Ammin sai xare idanu take yi tana naushinta da hannu". "Ammi ina xaki je alhalin baki san kowa a garin nan ba, kina son na shiga garari ne Ammina? kece farin cikin rayuwata, ke kadai nake gani naji dadi, idan kika tafi kika barni ina xan sa kaina, muxuranta ta cigaba da yi, tana 'kara kai mata duka, sai dai tana kawo hannunta Allah yake bata sa'a sai ta kauce. ******************************** saimah ce a gaban mahaifinta ta sunkuyar da kai tana wasa da 'yan yatsunta. kanta na kasa ta kasa fad'awa mahaifinta abinda take son isarwa gareshi, ganin shirun yayi yawa, yasa ya fara magana. "yar lelen Abbanta da magana kenan tunda naga kin yi wannan gurfanan." Shiru tayi da d'an lokaci sannan tace, eh!! Abbah dama......dama cewa nayi da xamu taimakawa su AL-MAJIRA mu basu d'akin soro su xauna, saboda a can kangon da suke ba su da daki, ga shi damina ta kusa sauka" shiru yayi na d'an lokaci " haka ne Autar Abbah, kin yi tunani mai kyau, saboda Allah yana taimakon bawansa, matukar bawan yana taimakon d'an uwansa. yanxu kije xan yi waya kasuwa a taho musu, da ledar tsakar daki da labule xuwa yamma sai mu je mu taho da su". hawayen farin ciki ta fara yi "Abbah na gode Allah ya saka da alheri Allah ya 'kara arziki" Amsawa yayi da ameen yar Abbanta Allah yayi miki albarka. "kai tsaye waje ta fito, ta nufi wajen su AL-MAJIRA, tararwa tayi ana kokawar mayar da Ammi cikin kangon saboda ta sake yunqurin fita, da kyar aka samu aka shigar da ita. shiga cikin kangon tayi fuskarta cike da annashuwa, take sanar da ita yadda suka yi da Abbanta, farin ciki ne ya lallu6e AL-MAJIRA har ta rasa bakin godiya sai kuka da take yi, har kasa ta tsagunnah tana yi wa saimah godiya, tashinta tsaye tayi ta dafa kafadarta, kada ki damu kawata da sannu xa kiyi rayuwa ta jin dadi ki koma kamar kowace diya mace. "godiya ta 'kara yi mata, ban ta6a tunanin xan yi rayuwa mai dadi ba ko da a mafarki, saboda tunda muka bar gida, bamu sake had'uwa da wanda ya tausaya mana ba, koda da ruwan sha ne ballantana musa rai da wajen kwana, sai gashi Allah ya yanke mana wahala, tunda na hadu da ke na bar fargabar abinda xa mu kai bakinmu, shi yasa a kullum nake muku addu'a, yadda ku ka sakamu farin ciki, ku ma Allahu ya yaye muku bakin cikin duniya da lahira. "amsawa tayi da ameen, haka suka xauna suka rika hira har xuwa yamma sannan 'yan uwanta suka xo tafiya da su AL-MAJIRA. d'aki a ka basu a soran gidan, an gyara musu shi, an sa musu labule da ledar tsakar daki, shigar da su dakin aka yi, suna xama aka kawo musu abinci da kaya, nan da nan su AL-MAJIRA suka canja kaya suka ci abinci sannan tayi sallah. "saimah ce ta shigo tare da momynta da Abbanta, sallama suka yi, fuskarta a sake ta amsa musu, gurin xama suka samu suka xauna, cikin ladabi ta gaishe su. "Abba ne ya fara magana, muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar da kulawarku ta dawo hannunmu. muna fatan xaki kwantar da hankalinki ki d'auke mu tamkar iyayenki, duk abinda kike so ki tambaye mu, indai muna da hali xa mu yi miki, sannan nasa a sauke al-kur'ani a yi wa mahaifiyarki addua a kan Allah ya bata lafiya. risinawa tayi tana masa godiya. "ba komai ki daina godiya ai d'a na kowa ne, bawa sai mai shi. mu dai fatanmu ku samu farin ciki ta sanadiyyarmu. tashi suka yi xasu fita tayi musu sallama sai da safe, har sun kai bakin kofa suka dawo "Au!!! mun manta bamu tambayi sunanki ba. "sunana NAUWAR tayi maganar kanta a sunkuye" Masha Allah sunanki mai dadi da asali, daga yau mun daina kiranki da AL-MAJIRA tun dai mun ji sunanki, sallama suka yi da ita suka koma cikin gida, ita kuma ta koma ta xauna, mintuna kadan bacci ya dauketa. A haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki, ta xama tamkar yar gida, har makarantar islamiyya aka sanyata. ga shi yanxu Ammi na samun kulawa sosai saboda kullum suna tare da ita, a yanxu dai ba su da matsalar abinci da wajen kwana, ga shi sun samu kayan sa wa da yawa, Alhamdulillah Ala na'amihi. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRAH* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJJANI* *ADAM* *(jeeddahtul-khaeer)* *β™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *Duk inda nake, a duk inda a kasance kuna raina, bana manta karamcinku da kaunarku gareni, Bilkisu Mmn Irfan (mai gado)$ Mamah Aleeyou kd ana tare*πŸ’―πŸ€ *wannan shafin gaba d'aya naki ne ZAINAB ABUBAKAR( YAR FILLO) ina yinki 😍😘* 1⃣2⃣ *H*aka Al-ajira ta cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali, sai dai fargabar ta d'aya ciwon Amminta, ko yaushe zata dawo kamar da? Kullum ta tuna yadda rayuwarsu take a baya, sai ta zubar da hawayen takaici, duk da karancin shekarunta, amma yarinya ce mai kaifin hankali da tunani *ASALIN LABARIN* Nauwar Mahmoud shine asalin sunan Almajirah, suna zaune ne a garin Kano a unguwar Nassarawa G.R.A(Dawaki Road). Mahaifinta Mahmoud Abdullahi d'an asalin garin Danbatta ne dake garin Kano, wanda ya kasance shi d'aya tilo a wajen mahaifiyarsa, inda abokiyar zamanta Habi take da yaya hudu (4)Isa,Nasiru,Abdurrahman, sai kuma y'ar autarsu Dije. Kasancewar Mahmoud d'a d'aya tilo a wajen mahaifiyar sa wannan yasa mahaifiyar Mahmoud take fuskantar matsalar gori da habaice-habaice a wajen uwar mijinta karime, da abokiyar zamanta. kasancewar tunda aka yi aurenta da malam Abdullahi bata haihu ba, sai da ta d'auki shekaru masu yawa,wannan yasa Inna karime tasa malamAbdullahi ya auri 'yar Aminiyarta Habi. tunda Habi tazo cikin gidan, Mahaifiyar Mahmoud ta kuma shiga cikin wani mawuyacin hali, har sai da ta kai ta kawo bata da kwana,mahaifiyar malam Abdullahi ta hana shi xuwa shimfidarta, saboda ba zai yiwu yaje ya kare karfinsa a kan juya ba, ita kuwa Aisha baiwar Allah bata nuna bacin ranta ba sai dai addu,a da take yawan yi kasancewarta mace mai tawakkali, tasan dukkan tsanani yana tare da sauki. haka rayuwarsu ta cigaba da gudana, kwanaki na shudewa su zama sati daga nan su zama watanni. Aisha ta d'auki tsayin watanni bakwai ba tare da mijinta ya kalli ko da 'kofar d'akinta ba ballantana ta sami damar Le'kawa turakarsa, ana cikin wannan yanayin ne Habi ta sami juna biyu, murna kuwa a gidan ba a magana,Inna karime kuwa cewa tayi daga wannan ranar, Habi ta daina wanke-wanke,shara da girki, sai dai Aisha ta ringa yinsu, ba yadda malam Abdullahi ya iya, dole haka yasa ido Aisha taci gaba da wadannan ayyuka. Wata rana Inna karime sun tafi unguwa, ita da Habi malam da ya dai-daici sun tafi, ya dawo gida jikinsa a sanyaye hawaye yake zubarwa, yana rarrashin Aisha yana bata hakurin zalincin da ake yi mata, share masa hawayen ta fara yi, tana fad'in malam ka kwantar da hankalin ka, ni ban ri'keka da komai ba, nasan ba laifin ka bane, kuma ko Inna da Habi ban rikesu ba na yafe musu duk abinda suka min, rungumeta yayi yana shafa kanta, albarka ya saka mata daga nan suka farantawa juna rai. Haka rayuwarsu taci gaba da kasancewa, sai bayan da Habi ta haifi d'anta na biyu sannan Aisha ta haifi danta Mahmoud,haka rayuwarsu taci gaba da innarsa yau za'ki gobe mad'aci, ana cikin wannan halin ne, innar Mahmoud ta kamu da zazzafan zazzabi wanda yayi sanadiyyar mutuwar ta Mahmoud yana da shekaru takwas a duniya, tun daga wannan lokacin Mahmoud ya koma rayuwar kad'aici da maraici, shi d'aya yake kwana a d'akin innarsa, abinci ma sai Habi taga dama take bashi. wata rana yakan kai kwana biyu ba tare da yasa komai a bakinsa ba, Sai dai Idan malam ya faki idonsu Inna karime da dare ya bashi abinda Allah ya hore masa. A wannan lokacin baffansa yace masa Mahmoud ina son na kai ka birni kayi karatun allo a can, saboda takura ka da a keyi a cikin gidan nan yayi yawa, gara Kaje can kayi karatunka, abinda Allah ya hore min zan ringa kawo maka. sannan ina yi maka wasiyya da kaji tsoron Allah a duk inda Kake, ka zama mutum mai amana, ka sani duk tsanani yana tare da sauki, kasa a ranka komai mai shigewa ne kaji d'ana shashshekar kuka baffansa ya fara yi,wanda yasa jikin Mahmoud ya 'kara sanyi Wanda dama tunda mahaifinsa ya fara jawabi yake zubar da hawaye,d'agowa yayi yana sharewa mahaifin nasa hawayen, Baffana kayi hakuri insha Allah zaka yi alfahari dani,na kasancewa ta danka, ka sani a duk inda nake ba zanyi watsi da tarbiyyar da kayi mini ba, rungume shi baffansa ya kara yi, yana yi masa addu,oi na fatan alkhairi,sannan suka nufi gida. *WASHE GARI* *M*isalin karfe 10:00 na safe suka iso cikin garin Kano ta Dabo, inda Mahmoud ya ji kansa na juya masa,kasancewar bai saba ganin cinkoso da yawan ababan hawa ba irin wannan take Mahmoud ya ................. A yi Hakuri da wannan yau ina busy a yi min afuwaπŸ‘πŸ» *jeeddahtulkhir😘* [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRA* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITES FORUM* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *wannan shafin gaba d'ayanshi sadaukarwa ne ga duk wani masoyin littafin Almajirah, ina kaunarku kamar yadda kuke 'kaunata, Allah ya barmu tare, ana tare*πŸ’―πŸ€ *ina mika gaisuwar ban girma gareki big admin ummiey xee Abakson, ina godiya da kaunarki garen, da dukkan 'yan uwa na exclusive writer's Allah ya 'kara hada kanmu*πŸ‘πŸ» 1⃣3⃣ Fashewa mahmoud yayi da kuka, "Baffana mu koma gida, bana son xama a irin wannan garin, an ce mutum d'an iska yake komawa, yana yin maganar yana share hawaye da majina. dariya Baffa yayi, lallai mahmoud da abin dariya kake, wanene ya fad'a maka wannan ruwayar? haka mutanen 'kauyenmu suke fada Baffa. to ba haka bane mahmoudu na duk wanda kaga ya lalace shi yasa kansa, ni dai fatana ka kiyaye Allah, kaji tsoransa a duk inda ka kasance, kuma kada ka tara bautar Allah da waninsa, kuma banda abinka ma ai wannan birni ne na albarka, burina a yanxu bai wuce kayi karatu ba ka share min hawayena, kasancewarku d'a na gari shi xai sa nayi alfahari da kai. 'karasowa bakin hanya suka yi, ya siya masa robar Abinci da kwaki da sugar, basu yi wata tafiya mai nisa ba suka isa makarantar malam Audu da ke unguwar 'kofar wambai, inda a nan ne mahmoud xai yi karatu. da sallama suka shiga xauren da malam Audu yake karatu tare da almajiransa, yana ganin Baffan mahmoud ya mi'ke ya tarbeshi da farin ciki, hannu ya mi'ka masa dan yin musafaha, shi ma mi'ka masa yayi suka gaisa, cikin ladabi mahmoud ya tsugunnah har 'kasa ya gaishe shi, amsawa yayi fuskarsa a sake, da kuma farin cikin ganin d'an nasa, kasancewar malam Audu aminin Baffan mahmoud ne tare suka tashi tun suna kanana. bayan doguwar gaisuwar da suka yi, malam Audu yasa aka kawo musu Abinci da ruwa, bayan sun nutsu ne mahaifin mahmoud ya fara magana. "malam dama wata bu'kata naxo maka da ita, ina son mahmoud ya xauna a wajenka, ya xama d'aya daga cikin almajiranka, dan gaskiya ina son ya samu haddar al-'kur'ani, ya kuma xama masani a bangaren littafan addinin musulunci, ina fatan xaka

Chapter 2 of 29