Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tanadi, Sannan yace wai mu ne Muka kashe Dan wajen Mudi, kuma Kaima yace sai yaga bayanka. A fusace magaji ya shiga daki ya xaro Adda, sai gidan su Hamdan a kofar gida ya tsaya yana ta xage-xage, yana ci musu mutunci Hamdan na jin abinda magaji ke fada ya tashi xai fita, da sauri mami ta tare shi ta hana shi fita,saboda tasan Hamdan yana da xuciya xai iya yi masa ba daidai ba, sai da ya gama xage su tas,Sannan ya shige ya tafi, xuciyar Hamdan sai faman tafasa take yi saboda bakin ciki. A haka ya Kwana ran shi a bace, washe gari da sassafe ya shirya ya kama hanyar tafiya neman su nauwar addu'a Mami tayi masa Sannan suka yi sallama ya tafi. *GARIN GOMBE* A tasha direba ya sauke su Nauwar, fitowa tayi daga tashar ta kama hanyar xuwa kasuwar garin dan ta siya kayan da suke bukata, bayan ta fito daga kasuwar ne ta rasa inda xata nufa, dan haka ta yanke shawarar samun guri a kasuwar ta xauna,saboda tana gudun kada matsalar da ta same su a baya, ta sake samun su, a wannan xaman da tayi bata fuskanci wani kalubale ba, don ko bara bata xuwa kullum tana tare da Amminta tana tarairayarta kasancewar yan kudaden da ta samu a hannun Alhaji Talle basu kare ba, kullum da safiya take fita don siyo musu abinda xasu kai bakinsu, idan da matsalar da take fuskanta bata wuce Farfadiyar da Ammi ke fama da ita ba. Yau ma kamar kullum shiryawa tayi tsaf, don nemo musu abincin safe, Ammi na kan cinyarta ta kwantar da kai tana ta sharadi bacci, A hankali tayi dabara ta sauke kan Ammi daga cinyarta, ta tashi a hankali ta nufi wajen siyo musu abinci, sauri take yi sosai gudun kada ta farka tayi wani gurin. wajen mai shayi ta tsaya inda ta siyo musu indomie da shayi, da sauri ta karaso wajen da suka sauka, amma abin mamaki sai ta tarar babu Ammi babu dalilinta sai filin wajen kawai, tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta ajiye abincin da ta siyo tayi, ta shiga neman Amminta amma shiru ba labarinta, fita tayi daga wajen ta baxama cikin unguwa tana tafe tana salati hade da kuka Allah ya bayyana mata mahaifiyarta, tambayar mutane ta shiga yi ko sun ga inda mahaifiyar tata tayi amma babu wanda ya kalleta ballanta tasa ran samun amsa, kusan duk wanda ta hadu da shi kallon mahaukaciya yake mata, sake komawa wajen da suke kwana tayi ko Allah xai sa taga ta dawo, wani mutum ta hango hannunsa rike da irin kayan da ke jikin Ammi yana tahowa inda take, saurin mikewa tayi ta tare shi tana hawaye, cikin tausayawa ya dubeta. "kin san mai wannan kayan" da sauri ta amsa masa da eh, me ya faru da Ammina. "ki kwantar da hankalin ki babu abinda ya faru, ki biyo ni dan ganin abinda ya faru da ita " bin shi tayi don tahowa da Amminta, sai da suka yi tafiya mai Nisa Sannan suka isa wajen. suna isa ta tarar da mutane a cike sun kewaye gurin suna salati, da hanxari ta karasa inda mutanen suke, tambayarta suke yi "wannan matar mahaifiyar ki ce?yana da kyau ki rika kulawa da ita,kina killaceta kin ga yanxu rijiya taxo ta fada, amma ana kokarin fito da ita, ki yi kokari ku koma gida wannan yawon baxai haifar muku da d'a mai ido ba, hankalin Nauwar yayi matukar tashi, bata san tsautsayin da ya kai Ammi bakin rijiya ba, hawaye ne suka rika sauka a kan fuskarta, tare da addu'ar Allah ya raba mahaifiyarta da wannan lalura ta tabin hankali, Saboda bacin ran da ya cika xuciyar ta gaba daya ta kasa gane komai biyu-biyu Kawai take gani. kokarin fito da Ammi mutane ke yi, amma gaba daya taki yarda a fito da ita sai abubuwa take yi, don haka suka kira fire service (kwana-kwana)don su xo su taimaka masu, ba tare da bata lokaci ba suka iso gurin idan suka fara kokarin fito da ita. Bayan sun cirota ne kuma Iskokin da ke jikinta suka bugeta inda ta rika wani irin abu kamar xata mutu, duk mutanen da ke gurin sai da suka yiwa Ammi hawaye saboda halin da take ciki, taimakawa suka yi aka mayar da ita wajen da suke kwana, addu'a wani bawan Allah ya rika yi mata har aka samu ta farfado, sannan aka dauketa xuwa asibiti don a bata magani saboda duk taji ciwo a jikinta. A Motar wani mutum aka dorata, basu minti biyar suna tafiya ba suka isa babban asibtin garin Gombe, ganin halin da Ammi ke ciki yasa aka yi saurin bata gado, allurar bacci aka yi mata, Dan tana bukatar hutu sosai. saboda buge-bugen da take yi sannan aka bata magungunan da xasu sassauta mata xafin da take ji a kanta, lokacin da mutanen xasu tafi sai da suka biya duk kudaden da aka caje su, sannan suka wuce suka tafi. Godiya mai Yawa nauwar tayi musu har Bakin kofa ta raka su Sannan ta dawo, bata taba xaton har Yanxu Akwai ragowar mutane irin Wadannan ba, masu tainakawa Dan Allah. *jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:15 PM] Writer: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRA* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† 5⃣6⃣ Kwanan Ammi biyu tana bacci bata farfado ba, a cikin baccin Nauwar ke dagata ta bata abinci da ruwa sannan ta mayar da ita ta kwantar, likitocin Asibitin na mamakin yadda Ammi da Nauwar ke xaune su kadai ba tare da wani nasu yaxo da niyyar duba halin da suke ciki ba, sai da suka fahimci ba su da galihu, daya daga cikin likitocin da yake duba su ne, ya kasa daurewa don haka ya shigo dakin samun Nauwar yayi ta xuba tagumi tana tunanin tare da xubar da hawaye, saboda bata san inda xata dosa ba idan Ammi ta warke, tasan likitoci baxa su taba daga mata kafa ta xaune musu a Asibiti ba kudi ba. da sallama ya shigo dakin amma bai ji an amsa masa ba, kara matsowa yayi daf da inda take, sake yin sallamar yayi amma shiru ba amsa kwankwasa tebur din da ta kwantar da kanta a kai yayi, cikin nutsuwa ta dago ta dube shi, idanunta cike da hawaye. samun guri yayi ya xauna shafa kyakkyawar fuskarsa yayi, sannan ya dubeta. da sassanyar muryar shi yake mata magana "sannu yan mata ya mai jiki" share hawayen da ke kwarara a fuskarta tayi ta amsa masa. "da sauki, sai dai har yanxu bata farka ba" cikin kulawa ya dubeta kada ki damu, tana bukatar hutu ne shi yasa, amma baccin baxai xama matsala a gareta ba" Tashi yayi xai fita, har ya kai bakin kofa ta kira shi. "Doctor yaushe xa a bamu sallama? lumshe idanu yayi, hannushi sanye cikin aljihu. "kin gaji da xama ne? gyada masa kai tayi alamar "a'a" murmushi yayi inda kyawawan hakoransa suka bayyana. "in dai kin gaji sai na sallame ku, naga kamar kin kosa ki koma gida kiga dadynki" Bata san lokacin da hawaye suka fara sauka a kan kuncinta ba, bai san cewa ita yarinya ce mara galihu ba, wadda ubanta yayi watsi da rayuwarta baya son ganinta ko jin labarinta. ganin yadda Nauwar ke xubda hawaye yasa Shi dawo wa da baya, wani abu yaji ya tsirga masa tun daga kansa har xuwa tafin kafarsa, tausayin yarinyar ya kama shi sosai rarrashinta yake yi, amma ta kasa daina kukan neman guri yayi ya xauna ya cigaba da bata hakuri. "Baiwar Allah kiyi hakuri, ban fada miki wannan maganar dan ta daga miki hankali ba, ki yafe min idan ni ne silar xubar hawayen ki" Dago manyan idanunta tayi wadanda suka cika da kwallar bakin ciki, a hankali ta daga baki ta fara masa magana "Baka bata min rai ba Doctor, kuma ba kaine kasa ni kuka ba,na tuna halin da nake ciki ne a yanxu, na auna shi da rayuwata ta baya, na tabbatar da cewa duniya ba tada tabbas xata iya juya maka baya a kowane lokaci, wannan dalilin ne yasa ni hawaye" gyara xama yayi, sannan ya fara magana. "ke kuwa wane hali kike ciki da har yake saka ki kuka idan kika tuna rayuwarki ta baya" labarin rayuwarta da Amminta ta bashi, da irin gwagwarmayar da suka yi da makiya, da halin da suke ciki a yanxu" wata ajiyar xuciya ya saki, sannan ya mayar da kallon shi gareta, cikin tausayawa yake mata magana "Gaskiya rayuwar ku cike take da darasi masu yawa, kuma wannan jarabawa ce Allah yayi muku, yaga ko xaku cinye ko baxa ku cinye ba, hakuri da juriya.da jajircewa wajen addua shi ya kamace ku, da sannu Allah xai kawo muku agaji, sannan ki dage da nemar wa mahaifiyar ki magani, kinga dai halin da take ciki a yanxu abin a tausaya mata ne, ki cire damuwa ki kai wa Allah kukan ki, duk wani wanda ya xalunce ki da sannu xai ga sakamako Allah yana nan baya bacci" Nauwar taji dadin Nasihar da Doctor yayi mata, kasancewar Doctor mutum ne mai ilimin addini da girmama jama'a, ba shida raina dan Adam ko yaya yake, wannan dalilin yasa duk wadanda suke xuwa asibitin suke kaunarsa, kuma suke masa adduar fatan alkhairi. godiya tayi masa, sannan ya mike. sake duban ta yayi "ki rike abinda na fada miki da sannu xaki fita daga matsalar da kike ciki, sannan ina so ki rike mutuncin kan ki, kada ki yarda saboda damuwa da bakin ciki ki jefa kanki a wata rayuwa mara kyau" kudi ya dakko ya bata. har kasa ta tsugunnah ta karba tana masa godiya. "ki rike wannan idan kuna bukatar wani abin sai ki min magana Insha Allah baxai gagara ba" godiya tayi masa sannan suka yi sallama ya fita. A kullum sai Doctor yaxo ya duba Ammi, ya kawo alkhairi mai yawa ya basu, sai dai har yanxu bata san sunan shi ba kuma ta kasa tambayar sa, kasancewar duk mutanen gurin kowa da Doctor yake kiran shi, wasu kuma su kira shi da ustax, saboda kamewar sa da tausayin da yake nunawa na kasa da shi. sai da Ammi tayi sati daya tana karbar magani sannan aka basu sallama, tun lokacin da likitan da xai sallame su ya shigo dakin ya basu takardar Sallama Nauwar ke kuka,saboda bata san ina xata nufa ba, bata san ya xata yi da rayuwarta ba, diban kayan ta tayi, sannan ta rike hannun Ammi suka fito daga dakin, bakin gate suka tsaya tana jiran Allah ya kawo abin hawa ta hau ta tafi ko ma ina ne, dan ita ta gaji da wannan rayuwar. horn taji ana mata don haka tayi saurin waiwayawa, Doctor ne a cikin motar, sanye yake cikin farin yadi wanda aka yi masa aiki fari, idanunsa sanye da farin glass yayi kyau sosai, murmushi ya sakar wa Nauwar wanda har sai da fararen hakoransa masu matukar kyau suka bayyana, rike da hannun Ammi ta karasa wajen sa, tsugunna masa tayi xata gaishe shi, nuni yayi mata da kyakkyawan hannunsa ta mike. "ina xuwa na ganki da kaya ko har an sake ku" cikin ladabi ta amsa masa. "eh tun daxu aka sallame mu" lumshe idanun shi yayi sannan ya dube ta. "ku shigo na rage muku hanya" bude mata kofa yayi ta shigar da kayanta, sannan ta shigar da Ammi, har ta samu guri a gidan baya xata xauna, magana yayi mata gami da bude mata gidan gaba. "shigo nan mana" budewa tayi ta xauna cikin nutsuwa, tunda ta shiga Doctor ya xuba mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta, yanayin yadda yarinyar ke gudanar da al'amuranta yana burge shi, yasan duk daga Inda ta fito ta samu cikakkiyar tarbiyya. kafin su fara tafiya ne ya dubeta. "ina ne wajen da ku ka sauka" idanunta a kasa, a takaice ta bashi amsa "cikin kasuwa" xare glass din da ke idanun sa yayi "cikin kasuwa kuma, me kike yi a kasuwa?" share hawayen daya ya fara taruwa a idonta tayi. "eh can xaka kai mu a nan ne inda muka sauka" Tausayi ne ya mamaye masa xuciyarsa,gaba daya rayuwar yarinyar ta gama katse masa hanxarin sa duk wasu burika da yaci a rayuwarsa ya ajiye su, saboda duniya ba tada tabbas,cikin tausayawa ya kalleta. "baxan iya barinki ki xauna a kasuwa ba, saboda guri ne da ya hada mutanen banxa da mutane na gari, idan kin yarda xan kai ki gidan mu ki cigaba da rayuwa, ina da kanne kamar ki da kuma wadanda suka fi ki, nasan xaki ji dadin xama a cikin su kuma xasu debe miki kewa" shiru Nauwar tayi tana tunani, ita dai xuciyar ta bata amice da wannan taimakon ba, saboda akwai mutanen da suka taimaketa a baya kuma suka yi yunkurin cutar da ita. shirun da yaji tayi ne, yasa yayi magana "kina tunani ko? hmm tunani abu ne mai kyau, amma kada kiyi tunanin da xai sa miki kokonto a ranki,nayi alkwarin baxan cutar da ke ba, idan kin amince xaki bini mu wuce yanxu mu tafi" kanta sunkuye ta bashi amsa. "na gode da taimakon da kayi min Doctor na amince mu je" cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake tukin, amma can cikin kasan xuciyarsa cike yake da fargabar yadda xai tunkari Hajiyarsa da maganar xuwan su Nauwar, saboda Hajiya mace ce da bata san mutane kuma bata san talaka ya rabeta, haka ma sauran yan uwansa mata suke, basa kaunar hada hanya da talaka, shi kadai ne a cikin su Allah ya tsame yayi masa baiwar karamci da girmama mutane. Addu'a yake yi sosai, Allah yasa kada ta watsa masa kasa a ido. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRA* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *A duk inda nake, a duk halin da na kasance baxan manta da ku ba masoyana na group din ✨TAURARIN MATA, kuna raina ina matukar alfahari da ku* *Hadiza Abubakar muhd* *Amina bashir yusuf* *maryam Tijjani Adam* *USummul* *Aunty peedy* *Subai'a S umar* *sa'adatu mhd Yusuf* *HafCweet* *Khadija Tijjani Adam* *Fresh khady* *Aysha Galadima* *masoya a sannu a Hankali duk xan rattabo sunayen ku* 5⃣7⃣ Tafiya suke cikin nutsuwa, shiru suka yi na wani dan lokaci, babu mai cewa da dan uwan sa komai, xuciyar Doctor kuwa sai dukan uku-uku take saboda tsoro da fargabar yadda xai tunkari Hajiya da maganar xuwan su Nauwar, ba su yi tafiya mai nisa ba suka iso unguwar new G.R.A da ke garin Gombe, daga jin sunan unguwar kasan unguwa ce ta masu hannu da shuni. wani katafaren gida suka nufa, wanda aka kawata gaban gidan da shuke-shuke,ko ba a fada maka ba ka san gida ne,wanda ba na kananun masu kudi ba. horn yayi da sauri mai gadi ya kara so ya bude kofar get din, saka hancin motarsa yayi ya shiga gidan, tare da yin parking a wajen da aka tanada domin ajiye motoci, juyo da kallon shi ya yi ga Nauwar yana murmushi "Alhamdulillah mun iso, da fatan dai baki gaji ba" a takaice ta amsa masa da"Eh" kokarin bude murfin motar ta fara yi xata fita, dakatar da ita yayi. cikin kasalalliyar murya yayi mata magana "ki daure ki bani hadin kai idan mun shiga cikin gida, kada ki nuna damuwa ko ki qi saki jikin ki, ki dauka kema 'ya ce kamar kowa, na tabbatar baxa ki yi da na sanin haduwa da ni ba Insha Allah" dago kyakkyawan idonta tayi ta kalle shi, ba tare da ta furta masa komai ba, saboda ba karamin faduwa gabanta ke yi ba, ganin yadda gidan su Doctor ya hadu, duk kyawun gidan su da tsaruwarsa bai kama kafar na su Doctor ba, fargaba ce ta kara xiyartar xuciyar ta, ta kosa su gama abinda xa su yi su bar gidan, kasancewar gidan shiru yake, ba a jin motsin komai sai kukan tsuntsaye, baxa ka taba xaton akwai mai rai a gidan ba. kayanta ya shiga fito mata da su, sannan ya taimaka ya fito da Ammi, bai kara cewa komai ba, nuni kawai yayi da hannunsa ta taho su shiga ciki. wata dogowar baranda suka bi, wadda kuma ita ce zata sada ka da kofar falon gidan, bude kofar falon yayi,subahanallah ta fada a zuciyarta saboda yanayin kayatuwar falon, umarni ya bata da ta zauna a kan kujera, kasa xama a kujerar tayi saboda bata san halin mutanen gidan ba, kada ta xauna a wulakanta ta, doctor na dawo wa ya ganta a kasa, bata rai yayi kadan sannan ya dubeta "me yasa xaki xauna a kasa, ba na fada miki cewa ki saki jikin ki kamar yar gida ba" hakuri ta bashi sannan ta koma kan kujerar ta xauna a tsora ce kamar wadda xa a kama. ruwa da lemo ya kawo mata da kansa ya tsiyaya mata a cup ya mika mata, sannan ya xubawa Ammi Nauwar ce ta karba ta fara bata, bayan ya kammala xuba musu ne, ya mayar da kallon shi gareta "jira ni kadan xan je na sanarwa da Hajiya maganar xuwan ku" benen da ke cikin falon ya haye, inda a nan Hajiyar sa da sauran kannensa ke rayuwa, duk da cewa yaran na da bangaren su amma sun fi son ko da yaushe suna tare da Hajiya, kasancewar Hajiya mace ce mai son yayanta, shi yasa ko da yaushe suna tare suna hira musamman idan ba makarantar boko. Da sallama ya shiga falon da Hajiya take wanda aka kawata shi da kaya na more rayuwa da jin dadi, sautin kida yaji yana tashi don haka da sauri ya karasa falon, tararwa yayi kannensa fatima da ummy suna ta faman tirkar rawa, suna ganin shi suka tashi a guje suka shige daki saboda sun san halin doctor baya son shashanci, kashe kayan kidan yayi yana musu fada, saboda ya tsani wannan halayyar tasu ta jin kade-kade. fuskar shi ba annuri ya nemi guri ya xauna. gaishe da Hajiya yayi, cikin sakin fuska ta amsa "sannu da xuwa yaya babba, da yake da wannan sunan take kiran sa wannan dalilin yasa duk yaran unguwar su, da yaran family din su suke kiran shi da yaya babba cikin nutsuwa ya dubeta. Ina su feenah da zainab suka shiga ne naga ban gansu ba. "na aike su gidan gwaggo ne su duba min jikinta" Dabi'ar doctor ce ya saba indai ya dawo bai ga daya daga cikin yan uwansa ba sai ya tambaya, kasancewar mahaifin su ya rasu shi ne yake musu tarbiyya a matsayinsa na babban yayan su, saboda Hajiya bata iya tsawatar musu, duk abinda suka yi daidai ne a wajenta. Tashi tayi ta miko masa flask din abinci, a sanyaye ya dubeta "bar abincin nan Hajiya da wata magana naxo miki, idan mun gama mun warware xan fi jin dadin cin abincin" farin ciki ne ya bayyana a fuskarta, duk a tunaninta da maganar auren sa yaxo mata, saboda ta dade tana fama da shi a kan ya fito da matar aure amma yaki, duk yarinya da aka kawo masa ya aura sai yace bata yi masa ba, sai hakura aka yi aka kyale shi. cikin kulawa ta sake duban shi. "kai nake saurare fa, amma kayi shiru" shafa fuskar shi yayi gami da sauke wata ajiyar xuciya. "dama wasu bayin Allah na gani a cikin wani hali na rashin dadi, wanda duk wani mai imani idan yaji tarihin rayuwar su sai ya tausaya musu, wannan dalilin yasa naga cewa kamata a ce mun taimaka musu, mun fitar da su daga halin da suke ciki, saboda mu ma bamu san ta inda Allah xai taimake mu ba. A asibitin mu aka kwantar da mahaifiyarta bayan an sallame su kuma ba su da inda xasu je, shi ne na kawo su gidan nan dan nasan baxa su rasa wajen kwana ba" wata matsiyaciyar harara Hajiya ta watsa masa. "sannu uban iyayi sarkin tausayi, daga ganin mutane ka yayo min su,ka kawo su gidana, kasan sharrin da ke tattare da su, yanxu a xamanin nan mutum ba abin yarda ba, me yasa xaka yi min wannan gangancin da rayuwa, to wlh tun wuri ka kwashe su ka fitar min daga gida, dan baxa ka kawo min masifa har daki ba" "ki fahimce ni Hajiya baxan kawo abinda xai cutar da ku ba, saboda duk abinda ya same ku ni ya samu, ki taimaka ki dubi halin da suke ciki, ki tashi mu je ki gansu nasan kema xaki tausaya musu" tashi suka yi suka fita falo dan ganin irin mutanen da ya kawo musu, suna fita su fatima da ummy suka bi bayan su,dan ganewa idon su ba'kin da aka kawo musu har gida. Tun daga nesa Hajiya ta hango su Nauwar, tsayawa tayi taki karasawa wajen su. sunan doctor ta kira "Abdallah" sai a lokacin Nauwar taji sunan shi "ka rasa wanda xaka kawo mana gida sai mahaukata, idan taimakon ne me yasa baxa ka basu abinda ya kamata ba sai ka kawo mana su gida, to wlh baxai yiwu ba sai sun fita daga gidan nan,dan ni tsoron su ma nake ji baxan iya karasawa inda suke ba, kada naje su shake ni" fatima ce ta taya Hajiya fadan da take yi. "ni wlh idan har xasu xauna a gidan nan na daina kwana, sai sun tafi xan dawo, haka kawai muka sani ko mayu ne" wani kallo doctor Abdallah ya watsa mata, nan da nan ta kama hanya ta bar falon, saboda tasan halinsa baya son raini. rarrashin Hajiya ya shiga yi ta taimaka ta bari a bawa su Nauwar wajen kwana da kyar ta yarda, inda tace a basu wani daki da yake kusa da na mai gadi, kuma da sharadin sai an caje su an kwace kayan su, saboda kada su xo mata da abin cutarwa. Cikin tsawa tayi wa su Nauwar magana "bayin Allah sai a tasar min daga kan kujera kada a taho min da annobar kwarkwata" jikin su a sanyaye suka mike, kofar fita daga falon suka nufa, xasu fita ran doctor a bace ya dubi Hajiya "Gaskiya abinda kika yi bai kamata ba, saboda Allah ya girmama dan Adam, mu ma ba wayon mu ko dabarar mu ce tasa Allah ya axurta mu ba" ficewa yayi ya bi su Nauwar. kuka Nauwar take yi sosai, saboda maganganun Hajiya ba karamin taba mata xuciya suka yi ba, hanyar fita daga gidan suka kama, dan ta kudurce a ranta ko xasu mutu saboda rashin gurin kwana baxa su xauna a gidan nan ba. da sauri doctor Abdallah yasha gabanta, "ina kuma xaki je" cikin kuka ta bashi amsa "xan fita daga gidan nan ne, dan xuciyata baxa ta iya jure wulkanci ba" cikin tausayawa ya dubeta "kiyi hakuri ni kaina da na san abinda xa a yi muku kenan da baxan kawo ku ba, ki sa a ranki wannan duk yana cikin jarrabawar da Allah yayi muku, kiyi hakuri ki daina xubar da hawayen ki, Allah yana sane da ke" rarrashinta ya shiga yi, har sai da yaga ta dawo cikin nutsuwarta sannan ya nuna mata dakin da xasu shiga. Fafur Nauwar taki shiga dakin tace sai ta tafi, da kyar ya shawo kanta ta shiga suka xauna. *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:16 PM] Writer: πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *AL-MAJIRA* πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ†πŸ† *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* *EXCLUSIVE WRITERS FORUM* *Dole na gode muku na kuma yaba da yadda kuke matukar kaunata, har ku ke kirana a waya dan jin lafiyata BINTA MUSA SALIS & UMMU SULAIMAN (Hasanatullah) ina matukar Allah ya bar xumunci* *ku ma ban mance da ku ba yan uwa masoya kuma members na Al-majirah fans, ina matukar jin dadin comments din ku, kuma ina godia sosai* Aisha Aliyu ummu Hanash juwaira lukman Amin ummu sulaiman ummy idris Dr fateemah sabitu feenah el sadeeq Saadatu Ibrahim zainab Abba sani (zainabi) nanah firdausi Princess Bilkisu Muhammad Zangi marfu'a (amfu) Abida sumy jamila bature sumayya Ango Abdullahi Haleema Ibrahim sakinat Jibrin Zahra'u Ado Bilkisu muhammad 😊Meenert maman ahmad Maman twins Badariyya Mu'az Harfsart Maman sahal Ummu Khalifa Maman jidda Aysha s/fada(baby Hassan) Maman Sudees Surry Pinky πŸ’ž Leemerh Mamcy 5⃣8⃣ shigar su dakin ke da wuya, doctor ya shigo hannun shi rike da leda, kayan sawa ya kawo mata, da kuma kayan abinci, da sabulun wanka hade da kayan shafe-shafe, daga tsaye ya mika mata sannan ya fice saboda yana tsoron kada Hajiya ta gan shi tayi masa tijara, bude kayan ta shiga yi tana fito da su, farin ciki ne ya kamata, saboda rabon

Chapter 16 of 29