Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yiwa ya Hamdan magana ya........ A dai-dai lokacin ya shigo d'akin. "Khala Rehab yarinyar nan ta rainani da yawa, Kwana biyun nan rashin kunya take min kamar wani sa'an wasan ta. "To ba Kaine kake sa ni aiki ba, kaje kayi da kanka mana. Duka ya sake kawo mata, ta 'kara shigewa bayan Amminta ta 6oye. Ita dai Ammi dariya take musu, sannan ta yi mata fad'a a kan ta ri'ka girmama shi tunda dai yayanta ne ya girmeta nesa ba kusa ba. kuka Nauwar ta fara yi, "Ammi Sam bakya ganin abinda yake min, Allah ya tsaneni ya takura min,ta 'kara rushewa da wani kukan. Khalas share hawayen ki yi hakuri nace. Falo suka 'kara d'unguma suka koma aka cigaba da hira. Horn d'in motar Abbansu suka ji, a guje Nauwar da fu'ad suka fita, kowannen su 'ko'kari yake yi ya bud'e motar Abbanshi, yana fitowa suka rungume shi suna murna "oyoyo Abban mu suka fad'a a tare" "Yauwa dama ina ta jira ka dawo Abbana ya Hamdan ya sa ni kuka d'axu" "Ni kuma sweets ya bani Abbana" murmushi Abbansu ya yi, to duka na ji Ku sarakan surutu, mu shiga ciki sai a yi maganar a xaune xai fi ko. Dukan su da sallama suka shiga falon, d'ur'kuswa Hamdan ya yi ya gaida shi, Nauwar na ma'kale da Abbanta tana ta harar Hamdan, Idan ta harareshi sai ya gyad'a kai alamar xai kamata. Bayan sun gaisa ya yi sallama da su ya wuce gida. Abbansu ya d'an huta ya ji matsalolin yaranshi ne ya wuce part d'inshi, sannan ya sanar da Ammin su Nauwar yana son ganinta ,xasu tattauna magana mai muhimmanci da ita, umartar yaranta ta yi, da su yi alwala su yi shirin Kwanciya bacci, sannan tasa suka yi addua ta nufi sashin Mahmud. Cikin nutsuwa take takawa har ta isa gare shi, ruwan da ke a Ajiye a gabanshi ta tsiyaya mishi a cup, sannan ta xuba masa abinci ya ci, bayan ya gama ne ya fara mata magana. "Ina son ki taya ni da addu'a akwai abubuwan da suke tunkarar mu ko nace xasu tunkaromu, kuma abubuwan suna da had'ari a cikin rayuwar mu da ta 'ya'yanmu, kada na ja ki da nisa, jiya Baffa ya kirani a waya yake sanar da ni, irin makircin da su innah karime ke son yi mana mu da yayanmu, ba su da buri a yanxu banda su mallakeni da abinda na mallaka, sannan su rabani da ke, abinda nake so kada ki tada hankalin ki, kice xaki sa damuwa a ranki, duk yadda suka so cutar da mu sai Allah ya nufa abin xai same mu, kuma duk wanda ya dogara da Allah to Allah xai isar masa, nasan ke mace ce mai addu'a da dogaro ga Allah, ina son ki 'kara jajircewa sosai a kan wannan dabiar taki, kuma ki 'kara gargad'in yaran nan da kada su saki jiki da su innah, Kin ga yanxu Nauwar na da shekara sha hud'u a duniya, ta fara mallakar hankalin kanta xata iya fahimtar wad'ansu abubuwan. "Haka ne insha Allah xa mu dage da addua, Allah kuma ya karemu da karewar sa. Amsa mata yayi da Ameen sannan ta fara shirin Kwanciya bacci. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Wannan shafin gaba dayan shi sadaukarwa ne gareka ABDULLAHI MUHAMMAD LAIMAJI, ina godiya a gareka Allah ya bar xumunci* *Ina mi'ka gaisuwar ban girma gareki ZAHRA'U ADO HUSSAIN SORON 'DINKI (MAMAN ISLAM) ina godiya da kulawar ki gare ni, Allah ya bar xumunci, ya raya Islam a kan tafarkin addinin Islama da sunnar Annabi (S.A.W)* *Ina neman afuwar ku masu karatu saboda rashin ji na kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiyar da nayi, da fatan xaku min afuwa* 2⃣0⃣ *W*ayewar garin litinin, tafiya ta kama Abban Nauwar xuwa garin Abuja, domin gudanar da wata bita da gwamnatin tarayya ta shirya musu a can, da wuri Ammin Nauwar ta tashi ta had'a mishi break fast bayan ya kammala, ya bata umarnin kiran Hamdan a kan ya kai su fu'ad makaranta, saboda baya so driver ya riqa yawo da yaran shi, qarfe 7:00am ya wuce garin Abuja. A dai-dai lokacin kuma ta kira Hamdan ta yii sa'a kuwa yana gida, bai yi sammakon fita wajen aiki ba, roqonshi ta yi ya kai yaran makarantam bai musa mata ba ya d'auki mota ya nufi hanyar gidan su Nauwar. Da misalin 'karfe 8:00 ya 'karaso gidan, da sallama ya shigo falon da suke, samun yaran yayi har sun yi shiri, shi kawai suke jira,gaisawa ya yi da Ammin su Nauwar, sannan ta tambaye shi lafiyar mutan gidan su. da gudu fuad ya 'karaso ya rungume shi, "Alhamdulillah yayana nafi son dama ka kaini school" ni kuwa nafi son Abbana ya kaini inji Nauwar, kamar ma na fasa xuwa makarantar Ammi tana maganar tana kallon idon Hamdan" duk maganar da take yi Hamdan d'in na jin ta amma ko tanka mata bai yi ba, ya cigaba da wasa da fuad, jakunkunansu suka d'auka suka wuce mota. Gidan baya Nauwar ta bud'e ta shige ta kame abinta, shi kuwa fu'ad duk inda Hamdan yasa 'kafa yana biye da shi, gaban motar ya shige , har Hamdan ya xauna a motar ya fito, fuskar shi a d'aure yake magana "ni direbanki ne da xaki xauna a baya, littafinta take dubawa ko kallon shi bata yi ba, magana nake miki fa!! ya fad'i haka yana mai daka mata tsawa. a haraxane ta d'ago kai ta kalleshi yadda taga fuskarshi ta canja ba wasa, shi yasa idanunta suka cika da 'kwalla "yi hakuri yaya ban ji abinda ka fad'a min ba" "Ai yanxu kin ji ko? Gyada kai tayi alamar eh. "To oya dawo nan ki xauna. tashi tayi ta koma ta xauna, suna tafe yana mata masifa, a tsorace take a motar don haka ta 'kosa su isa makaranta ta huta da jarabar sa, ana xuwa bata bari motar ta gama tsayawa ba ta fito, ji kake kiiiiiiiiiiiiii! Motar ta goge mata kafarta, jini ne ya ri'ka xuba daga 'kafar tata, tashin hankali ne ya bayyana a fuskar Hamdan, Sunan Allah ya shiga kira, "subhanallah!! saurin me kike yi haka xaki je ki ji wa kanki ciwo, me yasa bakya son yin abu a nutse?? Shiru tayi ta kasa cewa komai sai fito da idanu take yi tana kuka. lalla6ata ya shiga yi kamar xai yi kuka, share hawayen naki ki daina kuka kin ji dear , Kin ga ciwon ba shi da yawa. nan da nan ya sungumeta sai asibiti aka yi treatment d'in ciwon, sannan ya dawo da ita gida, ranar fuad shi ma bai shiga makarantar ba saboda firgitar da ya yi. Kai tsaye daga asibiti gida suka dawo, Ammi na ganinsu, hankalinta ya tashi a xatonta wani al'amarin ne ya faru, Hamdan ne ya fara sanar da ita yadda aka yi, ita ma dai lalla6a Nauwar d'in tayi, ta kuma yi adduar Allah ya kare faruwar hakan a gaba. Ba su fi minti goma da dawo wa daga asibiti ba, suka jiyo hayaniya a bakin gate ana xage-xage, ana dukan 'kofar gidan , jin haka yasa Ammin Nauwar ta umarci Hamdan ya le'ka ya ga abinda yake faruwa, wata mata ya hango ta yi d'amara da mayafinta, tana fad'i in fad'a da mai gadi, a tare da ita akwai wani matashin saurayi wanda ba xai wuce shekara ashirin da biyar ba, nuna inda Hamdan yake tsaye take yi tana xage-xage, duk da baya jin abinda take cewa amma sai da yaji shakkar 'karasawa gareta saboda bai san da me ta xo ba, jikinshi a sanyaye ya isa inda take, a tunanin shi xai ga yarinya matashiya ce take wannan xagin da wannan tijarar, amma sai ya ga tsohuwa 'yar kimanin shekara 70, kallon mamaki yake mata ya kasa cewa da ita komai, ita kuwa sai ashariya take d'ungumawa tana nuna shi. "Ka kaini inda shegiyar matar da ta mallake min jikana take,don nayi maganinta, ta mallake gida, ta rabamu da abinda d'ana ya haifa mana, ga shi nan har ta kawo wannan d'an mai kama da buxaye, daga jin yanayin kalamanta ya tabbatar da cewa innah karime c Wacce khalarsa ta d'ad'e tana bashi labarin mugun halinta, don haka ya juya ya koma cikin gida, tausayin khalarsa ne ya kama shi, ya ma rasa ta yaya xai fuskance ta da maganar. Da sallama ya 'karasa d'akin ya iske Ammi tayi tagumi tana jiran labarin da xai xo mata da shi. yanayin yadda fuskar Hamdan ta canja shi ya tabbatar mata da cewa yana cikin damuwa, yana shigowa ta mi'ke, ta fara tambayar shi abinda ke faruwa, sunkuyar da kanshi yayi ya fara sanar mata cewa tayi ba'kar bakuwa ne daga 'Dan batta. Jiri taji yana 'ko'karin d'ibarta don haka ta nemi guri ta xauna ta fara tunanin ko da me innah karime ta xo mata, tasan dai ita tararuwa ce mai wutsiya ganinta ba alkhairi ba ne, banko 'kofar da aka yi ne,ya dawo da ita daga tunanin da take yi, inna karime ta gani tsaye a kanta, hannunta rike da 'kugunta tana jijjiga kanta da jikinta sai watsa mata wani mugun kallo take yi, mai cike da alamomin tambaya, tsugunnawa Ammi tayi gwiwoyinta har kasa ta gaisheta, dakatar da ita tayi. bana bu'katar gaisuwar ki irin tsiya,kin xo kin mallake min jika, kuma kin hana mu more shi da komai, banxa ta fadi wato har da gayyato yan uwa a xo a ci arxiki. Hawayen da take 'boyewa ne ya fara zuba a kan kuncinta, ha'kuri ta shiga bawa inna karime. "Mahmud d'anku ne duniya da lahira ban isa na raba Ku da shi ba, wlh na tabbatar da cewa Mahmud yana 'kaunarku, kuma kuna ranshi a kowane lokaci. "Kya fad'i haka mana munafukar banxa irin mugun abu, kun bi dare kun bi rana,kun bi bokaye, kun rabamu da d'an mu, mun tattaro mun dawo mu sa ido, mu ga tsiyar da kike shukawa jinin matsiyata" Kuka Ammin Nauwar ke yi kamar ranta xai fito ta bakinta, ganin hakan bai sa innah karime tayi shiru ta daina fad'ar abinda taga dama ba. Ganin haka yasa Hamdan yace da ita *Khalaty khalliha wa sha,aniha*kai yaro kar ka Xage ni gadon rashin mutunci, da mugun hali sai in tsine maka albarka Idan ka sake cewa wani abu. A dai- dai lokacin da inna ke magana ne Magaji d'an gurin Audu ya shigo, dama tare da shi ta taho. "inna xagin ki wannan d'an marasa mutuncin ya yi. hannu biyu ya warware da niyyar marin Hamdan, ri'ke hannun Hamdan yayi, tare da murd'e shi, har sai da yayi 'kara mai 'karfi sannan yace masa *kalli balak* shiga hankalin ka, wallahi tallahi sai na rama ni xaka yiwa targad'e ko? 'ko'karin kuma cakumar Hamdan da kokawa yayi, kafin ya 'karaso inda yake tuni Hamdan yayi kukan kura ya had'a Kansa da bango, sai da ya xane shi sosai, sannan ya Kyale shi, inna karime kuwa sai ihu take yi xa a kashe mata jika, Ammi da ta ga abin yafi 'karfinta, sai ta d'auki wayarta ta kira Abban Nauwar, ta fad'a masa abinda yake faruwa ransa ne ya 6aci sosai. " kar ki barsu su kwanar min a gidana ki d'auki 20,000 ki basu xan kira driver da mai gadi su fitar min da su, cikin Mintunan da basu fi uku ba sai ga driver da mai gadi sun shigo, sun cakumi Magaji innah karime tana ina xaku kai min shi?? ko kallonta basu yi ba, kawai hannu suka d'aga mata alamar ta biyo su, binsu tayi har bakin mota. a motar suka saka shi, ita ma ta shiga motar suka tafi, ganin haka yasa Ammi sakin gwauruwar ajiyar Xuciya, kud'in ta mi'kawa inna karime, fusgewa tayi tare da bawa Ammi mummunan kallo xaki gani da ni kike maganar. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Sadaukarwa gare Ku 'yan uwa rabin jiki NADEEYA BABA IBRAHIM, AISHA BALA ILU & AISHA ISMA'IL ISAH, Allah ya bar xumunci da kaunarka juna* 2⃣1⃣ Tunda Ammi ta koma d'aki ta rasa abinda yake mata dad'i, duk tunanin duniya ya mamaye mata xuciya, tsoro da firgici ne fal xuciyarta, sai ta kasa fad'awa su Hamdan abinda innah karime ta fad'a mata. nan da nan xaxxabi ya rufeta, gumi ne yake ta yanko mata, saboda ta san sharri da makircin innah karime, tasan ko kad'an ba 'kaunarta suke yi ba ita da iyalanta. Alwala ta d'auro ta fara jera salloli tana ro'kon Allah ya bata kariya ita da abinda ta Haifa. Bayan ta idar ne Hamdan ya lura da yanayin tashin hankalin da take ciki,tambayarta yayi " Khalaty me yasa naga yanayin ki ya canja gaba daya? kada fa ki sa damuwar wannan mahaukaciyar matar a ranki, har hakan ya cutar da ke, ki sa a ranki baxa ta miki abinda Allah bai 'kaddara miki ba. ke da ki ke da Allah wace damuwa ce xata dame ki, shiru tayi har sai da Hamdan ya gama nasihohinshi gareta. "Hankalina ya tashi da maganar da ta fad'a min lokacin da xata shiga mota ne Hamdan" Me tace miki? Ya tambayeta Xan gani tace min, kuma kasan sharrinta. "Au don. Wannan maganar ma ai ba abar d'aga hankali ba ce, alheri xa ki gani insha Allah, ki manta da ita kawai". Amsawa tayi da ameen suka shiga hirar duniya. Tunda su innah karime suka hau mota suke ta tsine wa Ammin Nauwar a tunanin su, ita ce ta bada umarnin a fitar da su daga gidan. "Innah wlh dole mu d'auki mataki a kan shegiyar matar nan, saboda na fuskanci ta gama shanye min 'kanin mahaifi ta gama mallake shi , ni fa innah so nake yi ma gaba daya rayuwata ta dawo gidan, don naga wata yarinya mau kyau ta min a gidan, kin ga Idan na dawo sai ki bani ita na aura, komai na ubanta ya dawo hannuna,kuma ita ma fa innah baxa mu barta haka ba, dole sai mun mallaketa. "Dadina da kai kaifin hankali Magaji, ashe kaima ka fara fuskantar halin da ake ciki, wannan matar da kake gani ba karamar shu'uma bace, dole mu tashi tsaye a kan d'an nan Idan ba haka ba xa mu ga ana yi babu mu, ga shi har d'an uwanta ta kawo ya ci arxi'ki mu kuma ko oho, Wai a ce har ya samu damar yin dambe da kai, saboda yana da d'aurin gindi, to wlh baxa ta sa6u ba, dole mu tashi tsaye. "To ai duk laifin ku ne innah, inji Magaji da kun fara yun'kurin yadda xa mu yi mu koma birni da rayuwa, amma kamar Wad'anda aka yi wa d'aurin baki ku ka yi Watsi da abin, Ku ka ma daina xancen fada d'aya" "Idan d'aurin bakin aka yi abin mamaki ne? Matar nan fa matsafiya ce na dad'e da sanin haka, a haka ne dai xaka ganta kamar mumina, tana rero xance wai ita ta Allah. Ai mun gamu tunda tayi mana haka, mu xuba mu gani. Hirar da suka yi ta yi kenan har suka isa 'Dan batta. Suna huci suka fito daga motar, ko sallama basu yi wa Wad'anda suka kawo su ba suka fito. Cikin gida suka shige ran su yana ta musu xafi saboda abinda suka je nema basu samu ba, kuma bu'katar su bata biya ba. Habi suka tarar tana ta faman surfe, yadda taga yanayin su ta tabbatar da cewa, ha'kar su bata cimma ruwa ba, ga shi kuma ta ga Magaji ri'ke da hannun shi yana d'ingishi, sakin tabaryar ta yi ta 'karaso gurin da suke. "Ya na ganku haka da wuri, kuma babu alamar Walwala a tattare da Ku?" "Ta Yaya xaki ganmu da Walwala an mallake min jika ya xama na wata daban, kalli hannun Magaji ki ga aika-aikar da wani shegen yaro yayi masa" "Xare ido Habi ta fara yi, Idan na yarda da abinda aka yi Wa jikana Allah ya tsine min, yaron nan ya ta6o bala'i da hannunsa, bai san mu ba labarin mu yake ji, shii yasa ya yi karmbanin ta6o mu, ai kuwa ya ta6o masifa. "Mu shiga d'aki inji innah abin xai fi dad'in tattaunawa, kada wannan munafukin ya shigo ya ji dad'in kai musu labari. 'Daki suka shige gaba d'ayan su, tattauna abinda ya faru suka fara yi, suka cigaba da la'antar Ammin Nauwar. innah ce ta fito da dubu ashirin d'in da aka basu ta mikawa Habi. "Wad'annan kudad'en kuma na menene? Habi ta tambaya" "Su ne wanda aka bamu aka kuma koremu, aka ci mana mutunci. "Gud'a Habi ta saki, ahayye Nanaye !! Innah da Wad'annan kudad'en xamu ya'ke su, gobe mu tashi da wuri mu shirya, mu tafi gurin Bokan da Audu ya fad'a mana Kwanakin baya, mu je mu xube masa naira yayi mana aiki, ko ya Ku ka ce? "Haba Habi wannan ai rashin hankali ne, inda muke cikin matsin nan, mu je mu xube wa Boka Wad'annan kudaden gaba d'aya, gaskiya baxai yiwu ba, ki ri'ka yin abu da lissafi mana. "Tunda baxai yiwu ba a barshi, kowa ya tafi neman 'yancinsa ni xan tafi neman nawa yancin da na jikokina, ke kuma ki xauna a nan, tunda kashe kud'i a nemi magani rashin hankali ne da rashin lissafi". "A'a uwar Audu ba haka nake nufi ba, yanxu dai ki fad'a mana yadda kike ganin xa a yi." Maganar da na fad'a da farko ita xa a yi Idan kin amince. Na amince mana Allah ya kaimu goben. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *ALMAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *yau shafin gaba d'aya naku ne masoya Almajirah, nauwar tana godiya da kaunar da kuke nuna mata* *mariya Balarabe Adam* *Xahra'u Ado Husain* *xainab Abbah* *Nusaibah Abdullahi galadima* *Ummu Ammar* *Bilkisu mai Gado* *Amina saminu (maman Yousuf)* *Maman Yusra* *Fatima Ali* *ina tare da Ku masoyana* 2⃣2⃣ Da sassafe suka yi shiri sai wajen Boka, tsaunuka da daji suka ri'ka ketawa, wani rami suka gangara wanda shi ne, xai kai su har gurin da Bokan yake, wani 'katon mutum suka hango a saman bishiya jikin shi sanye yake da fatar damisa, gashin kanshi kuwa a duddun'kule yake ya sakko masa har 'kasan wuya, wata tsawa ya daka musu sai da suka firgita gaba d'ayansu, me ke tafe da Ku!!! Ya tambaye su?? Bakin su na rawa suka amsa da "wajen mai gani har hanji muka xo" Nuni yayi musu da su wuce su 'karasa wajen da Bokan yake, suna shiga suka iske shi a tsaye, hannun shi ri'ke yake da wata xabgegiyar takobi, fuskar shi kuwa kamar an shafe ta da ba'kin tukunya, kallo d'aya xaka yi masa ka tabbatar da cewa babu hasken imani a tattare da shi, a tsorace suka 'karasa inda yake, tsugunnawa suka yi da niyyar gaishe shi, dakatar da su yayi da hannu alamar baya bu'katar gaisuwar su, nuni yayi musu su samu guri su xauna. Xama suka yi sannan ya nemi su fad'a masa abinda yake tafe da su. Innah ce ta fara magana ran Boka shi dad'e yaro ne da mu, Allah ya axurta shi amma matarsa ta shiga tsakaninmu da shi ta hana shi ya Mora mana komai, yanxu abinda muke bu'kata a d'ora mu a xuciyar sa, ya xamto baya jin maganar kowa sai tamu, sannan muna son a sanya masa tsanar matarsa da ta ya'yansa, sannan a hana shi jin 'kan mahaifinsa, ya xamto baya son su baya 'kaunar ganinsu ko kad'an, bu'kata ta biyu kuma a d'ora wa matar sa warin ja6a. Gyaran murya yayi, sannan ya bushe da wata irin dariya mai ban tsoro, wannan ita ce kawai bu'katar Ku, ya tambaye su yana mai xare musu jajayen idanunsa, amsa masa suka yi da eh!!. 'kasa ya dan'ko ya xuba a wata fatar damisa ya had'a musu da wata laya, layar yayi umarni da a jefata a cikin kogi, 'kasar kuma su ri'ka jikata suna wanka da ita, xai ji duk duniya babu Wad'anda yake 'kauna Idan ba su ba. Godiya mai yawa suka yi masa, sannan suka xari dubu goma a cikin kud'in da aka basu suka mi'ka masa. Suna isa gida suka kira Magaji ya xo ya kai layar da Boka ya ba su kogi, ba tare da 6ata lokaci ba, ya d'auki keke ya tafi, yana kaiwa bakin kogin yayi sa'a babu kowa a wajen don haka ya faki ido ya jefa layar cikin ruwa. Da farin ciki ya dawo gida ya sanar wa su innah nasarar da ya samu na jefa laya, murna suka ri'ka yi kamar Wad'anda aka yi wa albishir da gidan aljannah, ruwa Habi ta shiga dafawa tana kiran jikokinta da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai suna wanka da ruwan. Yau jama'a Abban Nauwar ya dawo daga bitar da ya je garin Abuja, ledodi ne ri'ke a hannunshi ya shigo gidan, da gudu yaranshi suka xo suka rungume shi. "Oyoyo Abbanmu mun yi missing d'inka" murmushi yake ta musu. "Nima ai nayi kewarku 'yan yarana" Karbar kayan shi suka yi suka raka shi har d'akinsa, Ammin Nauwar ya tarar tana sallar la'asar, don haka ya tsaya jiranta har ta idar da sallar. Jin kan shi yayi yana juya masa, jiri ya ji ya debe shi, har yana 'ko'karin fad'uwa don haka ya nemi kujera ya Kwanta a kanta. Nan da nan idanun shi suka kad'a suka yi jawur, jin shi yake kamar ba a duniya yake rayuwa ba. Sai ya tsinci Kansa baya son jin muryar ko wane bil Adama a kusa da shi, don haka ya rarrafa ya shiga band'aki ya kulle Kansa. Tana idar da sallar ta tambayi Nauwar inda Abbanta yake, sanar mata tayi da ya je toilet xai watsa ruwa, don haka tafi kitchen ita da Nauwar suka had'o masa kayan ciye-ciye da lemuka kala-kala, a tunanin su suna dawowa xasu tarar da shi ya fito amma sai suka ga sa6anin haka, xauna wa suka yi suka cigaba da jiransa amma bai fito ba har sama da awanni biyu. Gajiya Ammin Nauwar tayi ta fara 'Kwan'kwasa 'kofar band'akin, tsawa ta ji ya daka mata. "Bana son sake ganin wani a d'akin nan, kafin na fito kusan inda dare yayi muku, Idan ba haka ba gaba d'ayanku sai ranku ya 6aci. Mamaki ne ya kama su gaba d'aya, Nauwar ce tayi karfin halin yin magana. "Me ya faru Abbanmu waye ya 6ata maka rai?? "Ban sani ba, Ku fita nace Ku bar min d'aki wlh Idan na fito na sameku sai na sa6a muku. Hawaye ne suke sauka a fuskar Nauwar ita kuwa Amminta gaba d'aya ma ta kasa aikata komai saboda abin ya gama d'aure mata kai, tunda take da Mahmud bata ta6a ganin fushinsa ba, amma yau gaba d'aya ya burkice musu ko 'yar tasa ma da ya fi so baya son ganinta. Rarrashin Nauwar take yi sannan ta lalla6ata suka fita daga d'akin. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* Maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *DUK A INDA NAKE KO NA KASANCE KUNA RAINA MASOYANA INA SONKU INA GODIYA DA 'KAUNARKU GARENI, ALLAH YA BAR XUMUNCI* Ameenah Nasir Zainab Muhammad Hafsee Maman Humaira Asma'u Abubakar Lolo Meena luv Haleemah MK Hindatu A'kilu Sabo Aysha Muhammad Hauwa Tijjani *Muna mugun tare*🤝 *WANNAN SHAFIN GABA 'DAYA NAKI NE 'YAR UWA RABIN JIKINA* *SALEEMAH SAMMANI BABA, INA YINKI INA 'KAUNARKI'YAR UWATA, ANA TARE*💯🤝 2⃣3⃣ Falo suka dawo gaba d'ayan su suka xauna, sun yi jugum-jugum dasu, saboda jimamin canjin da suka samu daga Abbansu, wayar da ke gefen su ce tayi 'kara, gaba d'aya suka mayar da kallon su gareta, wadda ita ce ta katse musu shirun da suka yi,

Chapter 5 of 29