Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yayi ya kasa cewa da Abban Nauwar komai sai da ya sake maimaita masa tambayar sannan ya saki ransa ya fara magana"Abba a kan maganar nan ne da muka yi game da aurena da Nauwar naji shiru baka ce komai ba, Abba ma kuma bai ce min komai ba" Sauke ajiyar xuciya yayi sannan ya fara yi masa bayani. "haka ne Sadeeq nayi shiru da maganar ne sbd ina dan son na gama wasu shirye-shirye, amma yau Insha Allah xan samu Nauwar din nayi mata magana duk yadda muka yi da ita xan fada maka" godiya mai yawa ya Sadeeq ya yiwa Abba sannan suka yi sallama xuciyarsa cike da farin ciki. A lokacin ya shirya ya nufi gidan su Hamdan don sanar da Nauwar abinda yake son fada mata, a sitting room ya xauna inda ya kira Ammi ya sanar da ita yana son ganin su ita da Nauwar, bai fi minti biyu da fada musu ba suka karaso wajensa, A xaune suka same yana jiran isowarsu, kujera Ammi ta samu ta xauna ita kuma Nauwar ta xauna a kasa, cikin ladabi ta gaida Abban nata, sannan suka gaisa da Ammi bayan sun kammala ne ya fara magana. "Nasan xa ku yi mamakin kiran ku da nayi gaba daya, ina so mu yi magana ne a kan auren Nauwar" gaba daya suka bayar da hankalin su gare shi, gaban Nauwar kuwa sai dukan uku-uku yake yi. gyaran murya yayi sannan ya cigaba da magana. "Na duba naga babu wanda ya dace ya auri Nauwar sai Sadeeq saboda irin taimakon da iyayensa suka yi mana, kuma ya nuna yana son yarinyar nan idan har muka ce baxa mu bashi ba ina ganin mun yi butulci" A xabure Nauwar ta dago ta kalli Abba, fuskarta ce ta canja daga farin ciki xuwa bakin ciki, Ammi ta lura da yanayin da yar tata take ciki, ita kanta bata ji dadin hukuncin da yayi saurin yankewa ba tafi son a shawarci yarinyar a ji abinda xuciyarta ta amince da shi. katse shirun da suka yi yayi, "wannan shi ne xabin da nayi miki Nauwar kuma ina so ki xama mai biyayya a kan haka, shi kuma Hamdan xan same shi na fada masa yaje ya nemi auren Saimah" wani hawaye ne ya fara xubowa Nauwar, a hankali ta lallaba ta tashi ta bar dakin, tana xuwa dakin da suke ta samu saimah na ta sharar bacci wannan yasa ta samu damar yin kuka son ranta, Nauwar na fita Ammi ta dubi Abba. "A ganina bai kamata a yiwa yaran nan haka ba, nasan kasan tsayin shekarun da suka shafe suna son junan su, idan aka ce xa a raba su lokaci daya an xalunce su" fada ya hau Ammi da shi. "Haka na yanke haka kuma xa a yi, sai dai idan ke xaki xugata ta bijirewa abinda nake so" Sake duban shi tayi "yana da kyau kayi dogon naxari a kan wannan hukuncin naka, idan aka yiwa nauwar haka Ina ganin ba a yi mata adalci ba idan ka duba tsawon shekarun da ta dauka cikin bakin ciki da kuncin rayuwa, yanxu fa ta fara dandana dadin duniya sannan kuma a ce xa a kara sakata a halin bakin ciki, gaskiya ka duba wannan al'amarin da kyau" fadan ya cigaba da yi ganin ya dau xafi ne yasa Ammi ta bashi Hakuri ta tashi a bar dakin. A ranar ya samu Abban Hamdan suka tattauna a kan batun, shima dai bai ji dadin hukuncin da ya yanke ba sbd yasan irin soyayyarda ke tsakanin Hamdan da Nauwar. washe gari da safe Abban Hamdan ya kira shi ya fada masa yadda suka yi da baban Nauwar ya kuma bashi hakuri a kan wannan babbar jarabawar da take shirin tunkaro shi. Hawaye ne ya shiga fitowa daga idon Hamdan ta ko'ina idanunsa cike da kwalla ya dubi Mahaifin nasa. "yanxu ya ake son nayi da rayuwata Abba duk tsawon shekarun da na dauka ina son yarinyar nan a ce baxa a bani ita ba saboda wani bare da yaxo daga baya" ya karasa maganar yana kuka mai cike da ban tausayi, dafa kafadarsa Abban nasa yayi yana rarrashinsa. "kayi hakuri Hamdan xan yi iya bakin kokarina don ganin na shawo kansa Amma ni kaina banso hakan ba, Kaje ka cigaba da addu'a Allah ya xaba mana mafi alkhairi" Tashi yayi ya bar wajen idanunsa a rufe yake tafiya, daki ya shiga ko xai ji saukin damuwar da ke damunsa, ji yayi yaci karo da mutum saurin dagowa yayi, ashe ya manta ba dakinsa ya shiga ba dakin su nauwar ya fada, ganinta yayi xaune a bakin kofa ta xuba tagumi tana ta faman sharbar kuka, a hankali ya ja kafa ya xauna daf da ita yana fuskantar ta, bude baki yayi xai mata magana Amma saboda tsananin kuka da bakin cikin da ya cika masa xuciya ya kasa magana, sun fi minti biyar a wannan halin sai da xuciyarsa ta dan yi sanyi sannan ya dubeta. "Nauwar"A hankali ta dago ido ta dube shi, tayi mamakin jin ambatar sunanta da yayi kai tsaye ba tare da ya sakaya ba, saboda rabon da ya fadi sunanta kai tsaye har ta manta, wannan dalilin yasa ta bashi hankalinta sosai don tasan maganar da xai mata mai muhimmanci ce. Kallonta yake ya kasa magana idanunsa sun kada sun yi jawur, karfin hali tayi ta fara yi masa magana.. "dearna ka kira sunana kuma kayi shiru, dan Allah ka fada min abinda yake damunka" Sunkuyar da kanshi yayi bai iya cewa komai ba, sake maimaita masa tambayar tayi. Cikin yanayin bakin ciki muryarshi na shakewa yake mata magana "Ina cikin tashin hankali ana so a raba tsakanina da ke, a bawa mutumin da bai san muhimmancin ki gare ni ba, kwanana ya kare a duk lokacin da aka raba ni da ke, na tabbatar da cewa baxan samu mace kamarki ba, baxan taba son wata mace irin son da nayi miki ba, kisa a ranki daga yanxu xaki iya Jin labarin mutuwa ta a kowane lokaci, xuciyata baxa ta iya jure ganin ki Kina soyayya da wani ba ni ba" Tashi yayi ya fita ya bar dakin kai tsaye dakinsa ya wuce, da sauri nauwar ta biyo shi tana masa magiya. "ka tsaya ka saurare ni dearna wlh nima ba a son raina hakan xai faru ba har yanxu da soyayyarka a xuciyata kuma babu namijin da xan yiwa irin son da nake maka" Juyowa yayi yana share hawaye yana Dubanta. "na gode da soyayyarki gare ni, nima xan ji dadi idan kika yiwa Abba biyayya a bisa xabin da yayi miki, na miki uxuri nauwar nasan Kina sona kuma baki yaudare ni ba, kuma har yanxu ban fidda ran Ki xamo mata a gare ni ba, don haka ki share hawayenki, ki daina yi min asarar su ki adana min su har sai ranar da aka kawo ki gidana a matsayin matata nake son naga kin fitar min da su saboda farin ciki, amma akwai alfarma daya da xan nema a wajen Ki nasan kuma baxa Ki qi yi min ba" Dago kai tayi "xan maka ko menene dearna " Cike da tausayawa ya dubeta. "Dan Allah ki nisanta da ni kinga Yanxu a matsayin matar wani kike, bai kamata na rika magana da ke a koda yaushe ba, yana da kyau mu fara koyawa kanmu rashin junanmu tunda mafarkin mu baxai cika ba" ya karasa maganar yana kuka, kulle kofar dakin ya yi ya fada gado yana kuka mai tsanani, a bakin kofar ta tsaya tana kuka tana shure-shuren kafa. "me yasa xaka yi min haka Abba ka tausaya min ka bani xabin da xuciyata ke so, wlh baxan iya yiwa wani da namiji biyayya ba bayan Hamdan ka duba halin da xan fada Abbah ka taimake ni" A gigice saimah ta fito daga daki ta tarar da nauwar a wannan halin dakin su Ammi taje ta sanar da su halin da take ciki, a sume suka tarar da ita cikin gaggawa suka dauketa sai Asibiti ba karamin tashin hankali saimah ta shiga ba, saboda taji abubuwan da nauwar ke fada tun tana bayi tana wanka sannan ta lura da walwalarta gaba daya ta canja, cikin damuwa take tambayar Ammi.. "Ammi wai me aka yiwa nauwar kuma me ake so a bata wanda bata so" Murmushi Ammi tayi "ba komai saimah Kawai shirmen Ku ne na yara" Xuciyar saimah bata amince da maganar Ammi ba don haka ta takura mata da tambaya amma taki gaya mata abinda ke faruwa, kyaleta tayi tare da yanke shawarar neman Hamdan taji abinda ke damun aminiyarta don shi ma ta lura da shi baya cikin walwala Kwana biyu. *Jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 9⃣7⃣ A asibitin suka kwana washe gari da safe Ammi ta kira Abban Nauwar ta shaida masa halin da take ciki, cikin mintunan da basu wuce biyar ba ya karaso asibitin tarar da Nauwar yayi kwance tana ta faman numfarfashi a raxane ya karaso wajen da take girgixata ya shiga yi. "me yake damun ki Nauwar, dan Allah ki tashi kada ki mutu ina sonki wlh ina son farin cikin ki, na fasa baxan miki abinda bakya so ba"duk juyatan da yayi ko dan yatsanta bai motsa ba, a daidai lokacin likita ya karaso wajen da yake dafa kafadar Abban Nauwar yayi. "kayi hakuri Alhaji yarinyar nan xata ji sauki Insha Allah akwai sauran shan ruwanta a gaba kada ka damu kanka, tashi ka biyo ni ina son mu yi ganawa ta musamman tare da kai" bin shi yayi har suka isa Office, kujera ya nuna masa ya xuna sannan ya fara yi masa bayani, "gaskiya Alhaji baxan boye maka ba, babu wata cuta da take damunka yarka face tsananin damuwa da bakin cikin da suka mamaye xuciyarta wanda hakan har yana baraxanar dora mata ciwon xuciya mai tsanani,idan akwai abinda ake wa yarinyar nan wanda bata so a yi hakuri a daina,saboda xata iya rasa rayuwarta a kowane lokaci" ya karasa maganar yana kallon Abban Nauwar, a raxane ya dago ya dubi likitan. "gaskiya ne abinda ka fada doctor duk ciwon da yarinyar nan take ciki ni na jawo mata shi da kaina, kuma in Allah ya yarda xan yi kokarin ganin na kawo mata karshen shi" cike da mamaki likitan ya dube shi. "kai kuwa Alhaji me zai sa ka hada yarka da bakin ciki irin wannan, idan har kana son rayuwarta kayi gaggawar warware wannan kullin da ke cikin xuciyarta, ko dan ka ceto rayuwarta daga halaka" Hannu ya mika masa suka yi musabaha sannan suka yi sallama. yana fitowa ya tarar da Hamdan yaxo suna hira da saimah tausayinsa ne ya kama shi, duk yayi baki ya rame ko hada ido da Hamdan din ya kasa yi saboda yana jin kunyar sakon da ya bayar a fada masa, da ganin shi ba a cikin hankalin shi yake ba, kallo daya xaka yi masa kasan yana cikin matsananciyar damuwa, har kasa Hamdan din ya gaida shi, cikin hanxari yayi saurin barin asibitin don komawa gida yayi shawara da Abban Hamdan a kan abinda yake faruwa. saimah ce ta mayar da kallonta ga Hamdan, "ni fa har yanxu na kasa gane kan ciwon Nauwar, na tambayi Ammi tayi min bayani tace min babu komai, kuma a lokacin da Nauwar din ta fadi naji wasu maganganu da take fada, kuma a bakin dakinka na tarar da ita shi ne ban gane dalilin hakan ba dan Allah ka fada min gaskiya ko akwai kokarin da xan yi don ganin na shawo muku kan matsalar" Ajiyar xuciya Hamdan yayi, idanunsa har sun kawo kwalla saurin sharewa yayi tare da dubanta. "Nasan Nauwar ta baki labarin ko ni wane ne a wajenta, da irin shakuwar da ke tsakanin mu na tabbatar da cewa kema kinga xahiri a aika ce, mun shafe sama da shekaru goma muna son junanmu, yanxu kuma Abbanta yace baxai bani ita ba, wani mutum daban xai bawa, wannan dalilin yasa Nauwar ta fada cikin wannan mawuyacin halin, kuma nima daf nake da fadawa irin halin da take ciki na sani" a firgice saimah ta dago ta kalle shi cikin mamaki take tambayarsa, tare da jinjina kai "Amma ban ji dadin faruwar wannan abin ba, kuma nasan daga inda matsalar take, yayana suke so su bawa tunda ya nuna yana sonta, nasan Abban nauwar yasan kuna on junanku kunya yake ji yace baxai bawa yayana ba shi yasa ya dage a kan haka,amma xan samu ya Sadeeq din nayi masa nasiha ya ceto rayukan da suke da baraxanar fadawa cikin wani hali ya hakura tunda dai dan Allah muka taimaka ba dan wani abu ba, kuma ni bana son naga rayuwar nauwar ta kara shuga wani hali saboda bakin ciki da kuncin rayuwar da suka shiga a baya, fatana a gareka ka cire duk wata damuwa,tunda ina tsakiya insha Allah xa mu yi nasarar ganin kun samu junan ku" cikin farin ciki Hamdan ya dago ya dubi saimah. "Na gode miki saimah Allah ya baki ikon cika mana burin mu Allah ya baki duk abinda kike nema na alkhairi" sallama suka yi, sannan ya wuce gida ko samun damar gaisawa da Nauwar bai yi ba,saboda baccin da take yi, a nan take saimah ta kira wayar Abbanta, cike da ladabi ta gaishe shi ya amsa mata cikin sakin fusa. "Autar Abba kin ji dadin kano kin makale ko neman gida bakya yi ko" murmushi tayi "ina nan xan dawo Abba Nauwar ce ba tada lafiya shi yasa ban dawo ba, yanxu haka ma a asibiti muke waya" hankalinsa a tashe ya tambayeta"me kuma ya samu diyar tawa?" "wlh Abba damuwa ce kawai kuma hakan har yana neman ya haifar mata da ciwon xuciya" Hankalin Abba yayi matukar tashi da jin kalaman saimah "subhanallahi amma abu bai yi dadi ba, ko menene dalilin da yasa ciwon yake baraxanar kamata" Ajiyar xuciya saimah tayi, "A kan maganar aure ne Abba, babanta yace baxai bata wanda take so ba sai dai ya bata ya sadeeq ta hakura tayi biyayya a kan haka, kasan kuma idan aka ce xuciya da abinda take so dole sai an shiga wani hali Abba" haka ne autar Abba, xan yi duk mai yiwuwa wajen ganin maganar nan ta rushe saboda ni kaina ban ji dadin hukuncin da ya yanke ba bana son a rika takurawa yarinyar nan, xan samu sadeeq din xan yi masa magana shi ma kuma baban nata xan kira shi nace masa mun janye" wani farin ciki ne ya kama xuciyar saimah. "yauwa Abba na gode da wannan jihadin da xaka yi" xuciyarta fari tas suka yi sallama, bata matsa daga wajen ba sai da ta kira ya sadeeq, da sallama ta fara yi masa magana shi ma dai da alama yana cikin damuwa, cikin sassanyar murya ta fara yi masa magana, "yayana na kaina ina so ka bani hankalinka xa mu yi wata magana mai muhimmanci kuma ina so ka yiwa abin kyakkyawar fahimta dan Allah" gaba daya ya bata hankalin shi "ina sauraronki kanwata ta kaina" gyara tsayuwa tayi sannan ta cigaba da magana "yayana ceton rai xaka yi ko ma nace rayuka daga fadawa cikin halin qaqa na kayi, Nauwar tana cikin wani hali sanadiyyar ka" xaro idanu yayi tare da tambayarta "sanadina fa kika ce saimah?" "kwarai kuwa sanadinka ne yaya, domin kuwa sanadiyyar son da kake mata ne yasa babanta xai tilasta mata aurenka alhalin kuma da wanda take so saboda yana jin kunyarka da ta iyayenmu baxa mu roki alfarma bai yi mana ba don saboda taimakon da muka yi musu, shi ne nake rokon alfarma dan Allah, ka janye daga maganar nan saboda aure idan aka yi shi da soyayya ya fi dadim kuma bana so a ce yau ka auri matar da bata sonka ta aureka ne kawai saboda biyayya kayi mana alfarma ka ceto ta daga wannan bakar rijiyar bakin cikin da xata fada" Ajiyar xuciya yaya sadeeq yayi sannan ya fara magana "nima naga abinda nayi bai dace ba saimah naxo na shiga rayuwar masoya xan tarwatsa musu duk farin cikin su, a cikin xuciyata dama na fara janyewa ina ta addu'a Allah ya cire min sonta ya xaba min abinda ya fi alkhairi, kiyi mata albishir da cewa ina sonta kuma ina son duk farin cikinta kuma xan cigaba da kulawa da ita a matsayinta na kanwata ki fada mata na janye ta auri hamdan Allah ya sanya alkhairi a ciki ya basu xaman lafiya" tsallen farin ciki saimah tayi tana yiwa yayanta godiya a bisa wannan hakuri da yayi sallama suka yi sannan ta koma daki, yanayin yadda ta shiga cikin farin ciki ne yasa Ammi kallonta tare da tambayarta. "saimah albishir aka yi miki haka naga kina fara'a" matsawa kusa da Ammi tayi "wlh babban albishir aka yi min yaya ya janye nauwar ta auri hamdan, na fadawa Abban mu ma duk yace shi ma ta auri hamdan shi yasa kika ga ina dariya saboda bana son abinda xai batawa yar uwata rai" farin ciki ne ya bayyana a fuskar Ammi "Alhamdulillah amma naji dadin wannan abu Allah ya xabawa sadeeq mace ta gari ta kirki" amsawa tayi da ameen sannan ta karasa wajen Nauwar shafa fuskarta ta shiga yi "tashi sisina Abba da ya sadeeq sun janye ki auri Hamdan ki tashi ki taya ni murna" A hankali nauwar ta bude ido rungume saimah tayi suna murna. *Jeeddahtulkhair😘* [9/22, 9:55 AM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki AUNTY RAMLATU ABBA DANDAGO, ina godiya da yadda kike kaunar wannan littafi* 9⃣8⃣ Ranar cikin farin ciki suka wuni kuma a ranar aka sallame su daga asibitin, sai dai gargadi da likitan yayi musu na aguji batawa Nauwar rai saboda gudun sake fadawa cikin halin da ta shiga. gida suka dunguma suka tafi, waya Nauwar ta dauka ta kira Hamdan cikin kashewar murya tare da kissa take masa magana, wani dadi gami da farin ciki ne ya tsirga masa cikin xuciyarsa saboda ya cire ran samun Nauwar a rayuwar sa, Albishir tayi masa da janyewar Sadeeq wani farin ciki ne ya kama shi addu'a ya shiga yiwa Sadeeq tare da yi masa fatan Allah ya hada shi da mace ta gari. a bangaren Abban Nauwar kuwa tunda ya tafi daga asibitin ya kasance cikin bakin ciki gami da bacin ran halin da ya jefa yarsa a ciki, Allah ya sani yana son Nauwar kuma baya son abinda xai taba mata farin cikinta kunya da nauyin Abban saimah ne kawai xai sa ya tursasata ta auri sadeeq, wani bacin rai ne ya lullube shi ya rasa ina xai tsoma ransa, kwanciya yayi ya daga kanshi sama yana tunanin yadda xai bullowa al'amarin saboda baya son rasa Nauwar, runtse idon shi yayi yana ambaton Allah, wayar da ke gefensa ce tayi kara a hankali ya mika hannu ya dakkota, number Abban saimah ya gani ranshi a sake ya amsa wayar, bayan sun gaisa yake shaida masa abinda suka yanke shi da Sadeeq, Abban Nauwar bai ji dadi ba saboda ya so hada xuria da su saimah Allah bai yi ba,ta wani bangaren kuma yayi farin ciki ko don cikawa diyarsa a burinta, tashi yayi ya nufi asibitin don fada musu abinda ake ciki, yana isa ya tarar da gadon ba kowa mamaki ne ya kama shi dan ganin wajen empty hankalinsa a tashe ya shiga Office din likitan, tarar da shi yayi xaune yana rubuce-rubuce cikin nutsuwa ya karasa kusa da shi, bayan sun gaisa ne yake tambayarsa inda su Nauwar suke, fuskarsa a sake ya bashi amsa"ai mun sallame su tun daxu, ashe basu kiraka sun fada maka ba" "eh wlh basu kira ba, da fatan dai ba jikin ne yayi xafi ba" yana fara'a ya bashi amsa. "tuni yarinyar ta samu sauki da kafarta ta tafi gida, fatana dai a gareka shi ne a kula da bata mata rai, duk abinda xai sakata a damuwa a yi kokari a kauce masa, sbd yanxu ma damuwar ce taso haifar mata da wannan ciwon" "xa a kiyaye Insha Allah, yanxu ma albishir naxo musu da shi na janye wannan maganar kuma na tarar basa nan" "ok kayi hanxari ka sanar da su" sallama suka yi cikin sauri ya nufi gidan su Hamdan, dukan su a falo ya tarar da su ana ta nishadi da sallama ya shiga gaba daya suka mayar da hankalinsu gare shi, Nauwar da saimah ne suka mike suna masa barka da xuwa, cikin sakin fuska ya amsa musu sannan suka gaisa da Ammi da maman Hamdan, guri ya samu ya xauna, ruwa su Nauwar suka kawo masa bayan ya sha ne ya fara yi musu bayanin abinda ya kawo shi, ba karamin farin ciki suka yi da jin wannan albishir daga gare shi ba, sannan ya sanar musu cewa gidan su ya kammala gobe xasu koma, a ranar kwanan farin ciki suka yi, Nauwar da Hamdan kuwa kwana suka yi suna waya. washe gari da safe suka yi harmar tafiya gidan don su samu su gyara gidan sosai, a kusa da gidan su aka yi musu ginin ba karamin tsaruwa gidan yayi ba, tararwa suka yi an gyara komai har jere an yi musu, babu abinda ya rage musu sai xama su huta, bangare biyu ne a gidan, bangare na farko shi ne nasu Nauwar dayan kuma Baffa ya ginawa, wanda xai je ya taho da shi nan ba da jimawa ba, Nauwar ce ta dubi Amminta. "Alhamdulillah ban taba tsammanin xamu dawo irin wannan rayuwar da muka yi a baya ba, gashi mun samu canji da cigaba fiye da wanda muka samu a da, Allah mun gode maka ya Allah ka kare mu daga sharrin abokan gaba" gaba daya suka amsa mata da Ameen, sallama Abbanta yayi ya karaso wajen su. "ku shirya yau muna da manyan baki a gidan nan Abdallah xai kawo mana xiyara don ya fada min yanxu haka ya kusa shigowa kano" cikin farin ciki Nauwar ta dubi Abbanta "amma naji dadi Abba dama ina ta tunanin ce maka yaushe xamu je musu xiyara saboda yayi mana mutunci a lokacin da muke bukatar taimako" fuskarsa a sake ya dubeta. "to ai gashi nan yau xai xo ya sada xumunci ya riga mu samun ladan, ku yi sauri ku tashi ku shiga kitchen ku hada masa abinci kafin ya karaso" da sauri suka shiga kitchen suka fara shirya abinci mai rai da lafiya, bayan sun kammala suka shiga wanka sannan suka sanya kaya iri daya masu kyau ita da saimah. bayan mintunan da basu wuce sha biyar ba, suka ji alamar tsayuwar mota Abban Nauwar ne ya fita don taho da doctor Abdallah, a falo aka sauke shi, cikin nutsuwa su Nauwar suka fito a ladabce suka gaishe shi cikin sakin fuska ya amsa musu, bin Nauwar yayi da kallo yana mamakin yadda ta canja da a hanya ma suka hadu ba lallai ne ya ganeta ba, saboda yadda ta canja kamanninta suka koma kamar na larabawa, tashi suka yi suka fara kawo masa abincin sannan suka dan taya shi hira sannan suka tashi suka koma dakin su, Abban nauwar ne ya shigo suka fara hirar yaushe gamo sannan ya bashi labarin irin gwagwarmayar da su nauwar suka shiga bayan rabuwar su da shi, doctor ya tausaya musu halin da suka kasance cike da tausayawa yake masa magana "nima tunda suka tafi hankalina bai kwanta ba saboda ina tsoron duniyar nan amma saboda babu yadda xan yi na bar su suka tafi saboda gudun bacin ran Hajiya, ni kuma gani gauro dama ina da aure ne da sai na kaisu gidana" ya karasa maganar yana dariya, cikin mamaki Abban Nauwar ya dube shi. "kana nufin kace har yanxu ba kada aure doctor lallai turawa sun yi tasiri a kanka" murmushi doctor yayi. "wlh ba haka bane kawai shi aure lokaci ne, kuma a gaskiya tsoron yan matan yanxu nake yi shi yasa ma har yanxu na kasa xaben mata" Abban Nauwar na murmushi ya dube shi. "tunda tsoron yan matan kake ji kaxo ni xan baka yata ka aura" gyara xama doctor Abdallah yayi "Da gaske kake xaka bani?gyada kai Abban

Chapter 27 of 29