saboda farin cikin dawowar sa.
A bangaren su Nauwar kuma, tunda suka bar gidan su doctor suke tafiya ba dare ba rana, ba karamin galabaita suka yi ba, saboda tsananin yunwar da suke ji, ga gajiya duk inda suka tsaya ba a barinsu su xauna saboda tsoron su da ake ji, gaba daya sun fita daga kalar su ta mutane saboda dauda, ga bakin cikin da ya cika xuciyar Nauwar tun tana kuka har ta hakura ta jure saboda babu maganin da kukan xai mata.
duk tsawon lokacin nan da suke tafiya basa samun abinda xasu kai bakin su, saboda babu kudi a hannun su,sai dai nauwar tayi bara idan mutane sun ga Allah su bata, wasu kuma xaginta xasu yi su koreta.
suna cikin tafiyar ne suka iso cikin gari, inda suka iske wata makarantar Almajirai, samun guri suka yi suka tsaya gudun kada su xauna a tashe su, tun lokacin da malamin Almajiran nan wanda Ake kira da malam Haruna yaga Ammi ya tsura mata ido ya kasa dauke kallonsa daga gareta, amma bai ce dasu komai ba, har xuwa lokacin da aka tashi daga makarantar aka sallami Almajiran don su je su nemo abinci.
Har aka tada sallar magariba su nauwar na wajen, sai da malam ya gama addu'a tsaf sannan yaxo ya same su, sallama yayi musu.
cikin damuwa Nauwar ta amsa masa sallamar, cikin kulawa yake tambayar su.
"lafiya na ga kun xauna a nan, tun muna makaranta na gan ku nayi xaton xaku tafi ne amma gashi naga har yanxu ba ku da niyyar tafiya"
kwalla ce ta cika idanun nauwar ta dube shi.
"ba mu da gurin kwana kuma muna cikin damuwa shi yasa muka xauna a nan"
tausayin su ne ya kama shi, kallon Ammi yayi ya girgixa kai sannan ya dubi Nauwar.
"wannan wace ce?"
"mahaifiyata ce" ta amsa masa kanta a sunkuye
ajiyar xuciya ya sauke, sannan ya cigaba da magana.
"akwai al'amura masu girma a tattare da wannan baiwar Allah, sannan tana tare da bakaken Aljanu kafirai, kafin na cigaba da yi miki bayani xan tambaye ki, wai kuwa yanxu tana sallah"?
gyada masa kai tayi sannan ta cigaba da magana
"bata sallah yanxu kuma da ba haka take yi ba"
cikin tausayawa ya sake dubanta.
"An yi mata asiri ne saboda a cimma wata manufa, kuma an hanata sallah ne saboda kada ma ta samu kusanci da Allah ya bata lafiya, riko hannuta ki tashi ku shiga gidana akwai taimakon da xan baku"
Tashi suka yi, suka shiga cikin gidan Malam Haruna.
*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:16 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(Jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
6⃣2⃣
A soro Ammi ta da'kire ita a lallai baxa ta shiga cikin gidan ba, Addu'a malam Haruna ya shiga tofawa Ammi nan da nan, ta fara fita daga hayyacinta, wani hayaki ne ya rika fitowa daga bakinta tana fesawa malam, tana kawo masa duka, bai kakkauta da yi mata addu'a ba har sai da ta daina fitar da hayakin, ta koma yin wani ihu mai ban tsoro, duka ta shiga kawo wa malam, da kyar aka samu ciwon nata ya lafa, daukan Ammi suka yi suka karasa cikin gidan.
Da sallama suka shiga,tarar da matar malam Haruna suka yi tana ta faman tankade, tana ganin su ta mike tana musu barka da xuwa, daki ta shiga ta dakko musu tabarma ta baxa musu a tsakar gida, taimakawa tayi a ka sauke Ammi aka kwantar da ita, ruwa ta kawo musu, sannan ta koma ta cigaba da aikinta.
gaisheta Nauwar tayi sannan malam haruna ya fara mata bayani.
"baki ne na kawo miki, xasu xauna tare da mu xuwa wani lokaci, xa a yi wa wannan baiwar Allahn magani idan an dace shikenan, amma tabbas tana tare da bakaken shaidanu"
fuskarta a sake ta bashi amsa.
"shikenan malam Allah ya taya ni rike su Amana, ita kuma Allah ya bata lafiya"
amsa mata yayi da "Ameen"
Tashi yayi ya fita, Nauwar ce ta taso ta karbi aikin ta fara taya matar malam suna yi suna hira, kamar sun dade da haduwa.
bayan sun kammala suka dora girki, suna gama girkin ne aka xubawa Nauwar taci ta koshi.
gidan malam Haruna gida ne karami, dauke yake da dakuna guda biyu, ciki da rumfa sai kuma falle daya, a falle dayan aka sauki su Nauwar aka saka musu katifa. shekarar malam Haruna ashirin da aure tare da matarsa Hajara amma Allah bai bashi haihuwa ba.
A wannan ranar da su Nauwar suka sauka a gidan malam, gaba daya basu yi bacci ba, saboda tashin da aljanun Ammi suka rika yi cikin dare, kokarin fita ta rika yi xata bar gidan tana ihu tana komai sai da kyar aka samu kanta.
washe gari ma abinda ta rika yi kenan, wannan dalilin yasa malam ya kira Almajiransa aka saka Ammi a gaba ana mata karatu, ihu ta rika yi har sai da ta fita hayyacinta sosai, saboda an tabo mata manya manyan kwankwaman kanta.
rukiyya aka fara mata da kyar aljanun suka fara magana.
cikin sarkewar murya ta fara bayani.
"turo mu aka yi mu rusa mata rayuwa, kuma sai mun aikata abinda aka umarce mu saboda an ba mu abinda muke so, kullum sai an bamu jini mun sha dan haka mu da ita sai dai mutuwa ta raba mu"
duk yadda malam yayi da aljanun nan a kan su fita, su bar jikin Ammi 'kememe suka ki fita, idan har suna so a fita sai an rika yi musu abinda suke so,wanda kuma hakan shirka ne, wannan dalilin yasa malam ya hakura saboda baya son ya sabawa Allah saboda magani.
A daren da malam yayi magana da aljanun Ammi shi ma bai kwana lafiya ba, cikin mafarki suka xo masa suka buga masa warning cewa duk lokacin da ya kara shiga cikin maganar maganin Ammi sai sun hallaka shi, yana addu'a ya farka, kuma ya ci alwashin tsayawa tsayin daka wajen nema mata magani har xuwa lokacin da hankalinta xai dawo jikinta.
********************
Bayan komawar Baffa Dan batta kuwa, kullum sai Abban Nauwar ya kira shi ya gaida shi yayi masa ya jiki, sannan duk abinda Baffa yake bukata yana kawo masa, tun kafin ma ya tambaye shi, saboda tunda malam Abdullahi ya fara bawa mahmud maganin sihiri ya fara dawowa dai-dai, godiya Baffa yake yi wa Allah saboda ya fara dawo da dansa kan hanya.
wata rana da misalin karfe takwas na safe Abban Nauwar ya dakko kayan maganin da aka bashi, xubawa yayi a kofi yayi addu'a sannan ya fara sha, sallama aka yi aka shigo dakin.
innah karime ce tsaye ta bude baki, tana kallon Abban Nauwar tana salati.
"Mudi me xan gani waye kuma ya baka wannan masifar kaxo kana dannawa cikin ka"
hannu tasa ta dauki maganin tana jujjuyawa.
"magana nake maka fa waye ya baka"
tsare shi tayi da ido tana huci, shi kuma duk ya diririce kamar karamin yaro, samun guri tayi ta xauna tana kallonsa, gaba daya tunaninta ya kwance bata taba xaton Mahmud xai nemi maganin abinda suke masa ba, hankali a tashe ta sake duban shi.
"wai me kake so ka xama ne Mudi, dan neman masifa ka rika shan magani, ban fada maka cewa,duk wanda ya baka magani kada ka karba ba sai kaje an shayar da kai guba, saboda Allah ya axurtaka, duk abinda na fada maka baka ji ko"
cikin fushi ya dago ya kalleta.
"baxan ji ba, ke uwata ce ko ubana, kin manta irin kiyayyar da kika nuna min a baya sai yanxu xaki ce kina kaunata, kina tunanin duk abinda kike yi min bana fahimta ne, to duk ina ganewa da Allah kawai na bar ku. kuma ki bani kayana da kika kwasar min dan kin san mahaifina baxai taba bani abinda xai cutar da ni ba"
cike da mamaki innah ta dube shi lallai magani ya fara aiki tunda har ya iya furta mata haka ba kunya ba tsoro.
hawaye ta shiga sharewa.
"yanxu ni kake fadawa haka Mudi saboda ubanka ya saka ka a daki yayi maka hudubar banxa, har xaka samu bakin xagina ko, wlh tunda ka taba ni sai ka gane kuskurenka, xaka ga abinda xai same ka"
"naga alheri me jiya tayi ballantana yau, kiyi duk abinda kika ga dama"
ficewa tayi tana share hawaye, gaba daya bakin ciki ya cika xuciyar ta.
*Jeeddahtulkhair😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*ALHAMDULILLAH MASOYA NA GODE DA KAUNAR KU DA ADDU'O'INKU GARE NI, NAJE ENUGU NA DAWO LAFIYA, ALLAH YA BAR XUMUNCI*
*wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ki, AYSHA ABUBAKAR SHAGARI (BABY) na gode da kaunar Ki gare ni Allah ya bar xumunci, da fatan kin isa sokoto LaFia*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
6⃣3⃣
Sashin su ta nufa tana kuka, Duk maganganun da Abban nauwar ya fada mata sun dagula mata lissafi, fadawa kan katifarta tayi tana kuka, a daidai wannan lokacin ne habi ta shigo dakin samunta ta yi a wannan halin, cikin nuna damuwa take tambayarta.
"lafiya na ganki haka innah me ke faruwa? "
Cikin karfin hali ta dago ta dubeta
"Habi muna cikin masifa a gidan nan dole sai mun tashi tsaye a kan mudi, abinda muke masa ya fara cika Shi, dole ne mu koma wajen gobe da Nisa ya sake sabon lae Idan ba haka ba kuma xa a yi babu mu"
Cikin mamaki habi ta dubi innah
"hmm dama ai nasan xa a rina wai an saci xanin mahaukaciya tunda tsohon banxan nan Yaxo ai nasan baxa a kulla abin arxiki ba, Yanxu dabara ta rage namu mu shirya Kawai gobe mu wuce mu nemi mafita "
Hirar da suka rika yi kenan har xuwa lokacin da magaji ya dawo Daga yawon sa ya tarar da su yayi suna tattaunawa, wajen xama ya samu suka fara xayyana masa yadda suka yi da Abban nauwar.
"Dama ai Kune baku fahimci inda aka dosa ba Amma ni na dade da gane cewa halayyar mutumin nan ta canja,tunda wannan tsohon tsiyar Yaxo ya lalata mana xama, idan fa bamu yi da gaske ba xamu rasa wannan gidan, da dukkan abinda muke son mu mallaka a rayuwa"
Cikin nutsuwa habi ta dube Shi
"gaskiya ne magaji Yanxu ya Kake ganin xa a kulla wannan tafiyar? "
Gyara xama yayi ya dubeta.
"gobe da sassafe Ku bani kudin mota Ku kwatanta min wajen da bokan yake xan je muku, xa a sake kulla musu wani bala'in da basu isa su kauce masa ba"
Farin ciki ne ya bayyana a fuskarsu Jin an ambaci xa a kulawa Abban nauwar masifa, haka suka cigaba da hirar sharrin da xasu yi suna ta Farin ciki abin su.
Bayan fitar innah karime Daga dakin Abban nauwar kuwa, kur'ani ya jawo ya shiga karantawa yana addu'ar Allah ya bashi kariya Daga dukkan abinda xai same Shi.
Yana kammala addu'ar wani Bakin ciki ne ya mamaye xuciyar sa, tunanin nauwar da Amminta ne ya xiyarci xuciyar sa, ji yake kamar xuciyar sa xata tsage saboda takaicin halin da ya jefa su a ciki, wayarsa ya jawo ya kira baffan shi, hawaye na kwarara a fuskarsa yake masa magana, bayan sun gaisa ne yake fada masa abinda yake damunsa, rarrashinsa ya shiga yi.
'kayi hakuri Mahmud Insha Allah suna kyakkyawan hannu babu abinda xai same su, ka Kwantar da hankalinka tunda muna addu'a Allah baxai toxarta mu ba, fatana dai ka rika hana idonka bacci kana fadawa Allah nima xan taya ka da addua "
Sallama suka yi ya kashe wayar, Kwantar da kanshi yayi bisa kujera ya lumshe ido a Yanxu babu abinda yake muradin gani sama da iyalinsa, wata kaunarsu ce ta mamaye masa xuciya, ji yake Duk abinda ya faru tamkar mafarki.
A daren gaba daya bai runtsa ba salloli ya rika yi yana add'ar Allah ya bayyana masa iyalinsa har xuwa wayewar gari.
Bayan ya kammala shiryawa ya fito don tafiya aiki, a falo ya Samu su innah karime suna ganin shi suka xube har kasa suna gaishe Shi, ko kallonsu bai yi ba ya wuce, bayan ya Kai Bakin kofa ne ya juyo ya kalle su.
Babu walwala a tare da shi yake musu magana.
"Daga Yau sai yau, kada na sake fitowa na ganku xaune a falo, bana bukatar na rika ganin ku a nan, Ina so ku taimaka ku rika nesa da ni, don halin Yanxu na tsane ku"
Yana kammala maganar ya fice don baya bukatar Jin amsar da xasu bashi.
Ba karamin tsoro Al'amarin Abban nauwar ke basu ba Sbd gaba daya rayuwar shi ta fara canjawa ya fara dawowa hayyacinsa, gaba daya sun kasa magana sai magaji ne ya yi karfin hali ya dube su.
"ba mu ga ta xama ba fa, Ku tashi mu tafi inda xai kawo mana mafita "
Idanun innah karime cike da kwalla ta dubi magaji,.
"ni Wlh baxan iya xuwa ko'ina ba Al'amarin yaron nan so yake ya saka ni hawan jini, Shi yasa hausawa ke cewa mai laya kiyayi mai xamani, yau naga sharrin xamani da idona"
Gefen xani habi ta fara kwancewa Kudi ta xaro ta mikawa magaji
"karbi wannan maxa ka tafi wajen gobe da Nisa ka xayyana masa halin da muke ciki, nima baxan iya xuwa ba dan Yanxu wani jiri ke dibana "
Karbar kudin yayi, a fusace ya fita ya bar gidan
Kai tsaye tasha ya nufa inda ya samu abin hawan da xai kai Shi garin Dan batta, tunanin muguntar da xai kullawa Abban nauwar Kawai yake yi har ya isa garin .
Bayan tafiyar magaji Farin ciki ne ya kama su innah karime Sbd xa a yi musu aiki ba tare da sun sha wahala ba, kiran wayar magaji suka yi inda suka Kara xayyana masa muguntar da xa a Kara shiryawa.
Har bayan sallar magariba suna tsimayin dawowar magaji Amma shiru ba labari, gaba dayan su tagumi suka xuba suna tunanin abinda ya hana shi dawowa a kan lokaci cikin damuwa habi ke magana.
"ni kuwa Ina Dan nan ya makale, yaro tun safe ya tafi yaki dawowa kamar an aiki bawa garin su Idan ya dawo sai na bata masa rai"
Ran innah a bace ta bata amsa
"ai dama nasan xa a yi haka magaji baya Jin magana, Yanxu haka gidan karuwai ya wuce ya karbe mana yan kudade yayi mana wayo "
"duk inda ya tafi ma xai dawo Amma sai ranshi ya baci "
Suna wannan halin ne suka ji ana buga musu kofar falo cikin gaggawa suka nufi kofar suna rige-rigen budewa, Jama'a suka gani a tsaye suna duban su, cikin jimami habi ta dube su lafiya bayin Allah na ganku kamar bakwa cikin nutsuwar ku"
Cikin karfin hali daya daga cikin su yake mata bayani.
"mu Daga garin Dan batta muke, Akwai daya Daga cikin fasinjojin da suka hau mota Daga garin nan to shi ne ya samu hadarin mota a hanyar xuwa garin, shi ne Muka Tambaye Shi ya bamu kwatancen gidan nan, Yanxu haka muna tare da shi a mota mun xo ne mu tafi daku a kaishi Asibiti "
Cikin tashin hankali su Inna suka fita Bakin kofar suna kuka suna Salati. Magaji suka tarar kwance cikin jini ko yatsansa baya matsawa a firgice suka kama hanyar xuwa Asibiti Don bashi agajin gaggawa.
*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*Wannan shafin gaba daya naki ne sarkin rigima HAFSAT ABUBAKAR SHAGARI kiyi yadda kike so da shi, na baki halak Malak kada ki bawa BABY😜*
6⃣4⃣
Isar su ke da wuya aka fara yiwa magaji gwaje-gwaje inda aka tabbatar musu da cewa kwakwalwar sa ta hadu da jini, sannan ya samu karaya a cinya da sauran sassan jikinsa, ya tabbatar musu da cewa idan ba a bashi agajin gaggawa ba xai iya rasa hankalinsa.
cikin tashin hankali suka kira Abban Nauwar suka shaida masa abinda ya same su.
Cikin kuka innah ta karbi wayar take masa magana.
"ka taimaka mudi kaxo iftila'i ya afkawa magaji, Kansa ya hadu da jini yanxu haka Muna Asibiti muna bukatar kudi kafin ma likita ya kalle shi ya fara bashi magani"
cikin rashin nuna kulawa ya mayar mata da amsa.
"yanxu ina Office ki jira na tashi xan xo Insha Allah"
fashewa tayi da kuka ta fara yi masa magiya.
"yanxu har sai ka tashi sannan xaka xo ka same mu, baxa ka tausaya wa yaron nan ba, bai san fa inda kansa yake ba"
kashe wayar yayi ya barta tana sambatu.
har bayan sallar magariba babu Abban Nauwar babu dalilinsa, gaba daya ya manta da wayar da suka yi da su innah karime don shi tuni ya shige ya tafi gidan malam Abdullahi don karbar maganinsa.
gajiyar da suka yi da jiransa ne yasa Habi ta tashi ta nufi gidan, bude dakuna ta shiga yi, don dibar wata kadara ta siyar ta nemarwa jikanta magani, gidan ta shiga lalubewa bata samu komai ba, don haka ta yanke shawarar balle mukullin dakin Abban Nauwar ta dauki kudi, ciki hanxari ta balle kofar ta kwaso kudade masu yawa ta nufi asibitin.
Tana isa ta biya duk kudaden da ake bukata aka fara bawa magaji agajin gaggawa, Bayan ya kammala duba shi ne ya tabbatar musu da cewa ko magaji ya samu lafiya ya rasa wani bangare na hankalin sa, a ranar Kwana suka yi suna kuka Suna tsinewa Direban da yayi tukin ganganci ya illata musu da.
Abban nauwar na dawowa gida ya tarar da barnar da habi tayi masa, Kai tsaye wajen mai gadi ya nufa cikin tsawa yake tambayar sa.
"waye ya shigo ya bincike min daki ya kwashe min kudaden da aka bani ajiya "
Cikin tashin hankali mai gadi yayi dube Shi.
"Wlh babu wani Bakon fuska da ya shigo gidan nan, Kawai baba habi ce ta shigo ita ma kuma bata dade ba ta fita "
Gyada kai yayi gami da tsaki Sannan ya fice daga gidan ya nufi Asibiti, tarar da su ya yi sun xuba tagumi GA kuma jakar Kudi a Hannun habi, cikin hanxari ya fixge jakar ya fara xaxxaga musu masifa.
"Haba baba a wane dalilin xaki shigar min daki Ki daukar min kudin da aka bani amana abinda kika yi ya dace kenan, na farko dai ke ba gadona kike dashi ba ballantana kice xaki fara Karbar rabon Ki, daga Yau kada ki sake yi min irin wannan, saboda bani na aike Shi Yaje yawon iskanci ba mota ta buge Shi"
A fusace ya shiga office din likita inda ya shaida masa irin barnar da habi tayi masa, ya kuma roke Shi ya bashi wani bangare na kudin da suka kawo masa.
Ba musu ya xaro ya bashi"
Bayan Abban nauwar ya tafi ne likitin Yaxo ya same su ya sanar da su yadda suka yi dashi, tsine masa suka shiga yi suna aibata Shi, daga karshe ya shaida musu cewa gobe xai sallame su kasancewar babu ragowar kudin Su a hannunsa.
Ba karamin tashin hankali suka shiga ba da Jin kalaman likita Sbd ba su da kudin da xasu nemawar wa magaji magani, gashi jikinsa ya Kara rikicewa baya gane komai sai xage-xage da yake yi, a ranar hana su bacci yayi saboda xafin ciwon da ya addabe Shi.
Washe gari da sassafe ya kawo musu takardar sallama,suna kuka suna rokon ya tausaya musu Amma likitan ya kekashe kasa ya kore su.
Gida suka dawo kai tsaye dakin su suka shigar da magaji suka Kwantar da shi, ihu Kawai yake yana xagin su innah karime, hayaniyar da Abban nauwar Yaji ne yasa ya fito a lokacin yana daki suna tattaunawa da Hamdan dangane da batan su nauwar,tunda suka bata yake xageye duniya yana neman su Amma ba Labari, gaba daya suka fito don ganin abinda ke faruwa, dakin suka shiga inda suka tarar dashi hannunsa Rike da kansa yana kuka yana xage-xage.
Su habi na ganin su suka Mike suna kuka
"ka tausaya mana Alhaji ka duba halin da yaron nan yake ciki "
Sbd takaici Abban nauwar kasa cewa komai yayi, sai Hamdan ne yayi musu magana.
"Indai xalunci abin yi ne ku cigaba wannan kadan Ku ka gani daga cikin irin sharri da Makirci da ku ke kullawa, kun kashe kun haukatar kun tarwatsa rayuwar iyalin da suke cikin Farin ciki, ta Yaya xaku ga daidai a rayuwar Ku, wannan so mun tabi ne, baku ga komai ba sai nan gaba"
Kuka su habi suke yi suna rokon a taimaka a mayar da magaji asibiti, cikin takaici Abban nauwar ya dube ta.
"ba wani abu da xan iya yi masa Sbd bani na aike Shi Yaje inda abin ya same Shi ba, ko kafar nan xata rube kansa ya lalace ba ruwana, sharrin da ku ka shuka ne, Ku ka fara girbar irinsa."
Yana kammala maganar suka fice suka koma daki, cigaba da tattauna maganar Nemo su nauwar suka yi, inda suka tsayar da matsaya cewa xasu sake fita nemo su gobe Sannan kafin ya tafi ya yanke shawarar korar su innah karime Daga gidan.
*jeeddahtulkhair 😘*
[9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
*ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
6⃣5⃣
Bayan fitar Abban nauwar daga dakin su Inna karime kuwa,duk jikin su yayi sanyi ganin yadda ya canja taku gaba daya, ya daina saurarar su ya yanke duk wata alaka da su, sannan ya daina jin nauyin su duk abinda ya fito daga bakin sa baya jin kunyar fada musu, Habi ce ta katse musu shirun da suka yi.
"Gaskiya sai mun canja taku innah, wannan yaron yana son jefa mu a wani hali, kin ga duk makircin da muke shiryawa kokarin warwarewa yake yi, mu koma tamkar bola a cikin gidan nan, duba kiga irin bakaken maganganun da ya fada mana Yanxu, duk rashin Lafiyar nan da yaron nan yake yi yaki tausaya masa, Wallahi wata rana tsaf xai Kore mu"
Gyara xama tayi ta sake duban innah karime ta cigaba da magana.
"Yanxu wata Shawara nake son mu tattauna a kanta, me xai hana mu yiwa xulai yar gidan kawuna waya ta dawo gidan nan da xama ta jawo mana hankalin sa da kwalliya da kisisina, sannan kafin taxo sai taje ta shirya jikinta da magani ta yadda yana mata kallo daya xai haukace da soyayya, Kin san xulai yarinya ce wayayyiya tasan salon janye hankalin da namiji, mu yi duk kulle-kullen da xamu yi, mu cusa ta har sai yaron nan ya mutu a kan sonta, kin ga mu kuma mun samu damar da xamu dada bajewa sosai a gidan nan babu wanda xai tsangwame mu, sbd Idan bamu yi haka ba akwai matsala Kin san dai baxai ta xama a haka aure ba. Gashi Yanxu duk abinda muke yi so yake ya tashi a banxa Amma idan Muka biyo ta wannan hanyar akwai yiwuwar mu ci nasara. ko ya kika gani?"
Murmushi innah karime tayi ta bata hannu suka tafa.
"gaskiya kan ki yana ja habi, kin yi babban tunani, yadda abin nan namu ya daina ci wannan ce kadai hanyar da xamu bi mu yake Shi, kin san tunda yayi wannan karatun na nasara baxai rasa bin mata ba, suna fara shakuwa xamu yi kokari a yi biki mu huta, dan naji yana shirye-shiryen tafiya nemo wannan mahaukaciyar Matar tasa, mu kuma indai muna doron kasa tayi bankawana da gidan nan sai dai su hadu a lahira "
A raxane habi ta dube ta.
"nemo ta yace xai yi"
"kwarai kuwa, daxun nan naji yana fadawa wannan munafikin yaron da ya tsani magaji"
Waya habi ta fara lalube "ai kuwa Yanxu xan kirata innah Kinsan ba a bori da Sanyin jiki"
Kiran wayar xulai tayi inda ta xayyana mata duk salo da kissa da makircin da take so ta yiwa Abban nauwar, har ya ji yana sonta, bayan ta kammala fada mata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 29