Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
je ya kona su, ana konawa Ammi na kuka tana magiyar kada a cigaba, saboda an yi alkawri da su asirin baxai taba warwarewa ba. tun daga wannan lokacin da malam Haruna ya warware wannan aiki Ammi ta daina magana sai dai tayi nuni da hannu idan tana bukatar wani abin, haka ta kasance har tsawon kwana shida, a ranar da xata cika sati daya bata magana ne, malam yaga abin ya yi yawa, don haka ya fita daji don neman maganin da xai hada mata ko xa a samu kanta,cin karo yayi da wani tsoho a kan hanyarsa ta xuwa daji, sanye yake da fararen kaya kafarsa sanye take da takalmin fata wanda baxa ka iya hango ko da dan yatsansa ba, kallo daya xaka yiwa tsohon ka tabbatar da cewa ba mutum bane. hannu ya mikawa malam Haruna suka gaisa, cikin taushin murya yake masa magana. "kada kayi mamakin dukkan abinda xan fada maka, kuma duk abinda xan fada maka kada kayi min musu, ka ji ni da kunne kawai" "amsa masa yayi da Insha Allahu baxan musa maka ba" tambayar malam Haruna ya shiga yi "kana da mara lafiya a gida ko" amsa masa yayi da eh. sake dubansa yayi. "wannan mara lafiyar an yi mata asiri ne kuma asirin mutuwa da lalacewa aka yi mata, an hada ta da manyan shaidanu ne wadanda ba imani a ransu, shawara daya xan baka ku dage da neman maganin karya asiri daga kai har ita da kake mata magani, saboda a yanxu shirin su na su hallaka ku ne, don haka ga wannan" wani dutse ya mika masa daure dutsen yake da wani tsumma da kuma layu. kallonsa malam Haruna yayi. "me xan yi da wannan" murmushi yayi "kana komawa gida ka jika wannan ka bata tasha, ragowar sihirin da ke jikinta xai karasa fitowa, nima na samo wannan ne a inda mugwayen shaidanun ke adana bayanan su na sirri, kada kayi wasa da shi saboda xasu iya xuwa su sace, ina dada nanata maka kada kayi wasa da wannan layar domin ita ce babban makamin da xaku yake su a halin yanxu" yana gama fadawa malam Haruna wannan maganar ya bace, godiya malam ya yiwa Allah. amma xuciyarsa bata gama amincewa tayi amfani da abinda ya bashi ba, cikin aljihu ya saka su sannan ya shige ya shige ya tafi gida. yana komawa gida ya tarar da su Nauwar da matarsa suna kokawa da Ammi xata haura katanga ta gudu, addua ya shiga yi mata, yana fara yi mata ta fadi kasa tana wani irin ihu mai cike da ban tsoro, wani hayaki bakinta yake fitarwa warin hayakin kadai xai yi haddasawa mutum wata cutar, toshe hancinsu suka yi gaba daya don kada ya shigar musu hanci. ruwan addu'a malam ya tashi ya dakko ya rika fesa mata, har ya dakko dutsen da aljanin nan ya bashi xai jika mata, kawai ya fasa saboda ba ayar Allah bane ballantana ya ji karfin gwiwar bata tasha, don haka yayi watsi dashi ya cigaba da yi mata addua. wata murya suka ji ta bushe da wata dariya mai ban tsoron, sannan aka fara magana. "da ka bata wannan dutsen da muka aiko wannan tsohon ya baka da baxa ta taba samun lafiya ba har abada, kuma kaima rayuwarka tana cikin hadari da ka bata ta sha" wurgi yayi da dutsen gefe guda, yana godewa Allah da ya tseratar da su daga sharrin tsafin aljanu, lallai duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa. karatun kur'ani suka shiga yi mata a ranar sai da suka yi mata sauka,suna rokan Allah ya bata lafiya. wani kadangare ne ya yo kan su da gudu, أعوذ بكلمات اللّٰه تامة من شر ما خلقmalam da matarsa da Nauwar suka rika karantawa, cikin ikon Allah kadangaren ya tsaya cak ya kasa tafiya, tashi malam yayi ya dauke shi ya doka shi da kasa nan take ya fadi ya mutu. duba jikin kadangaren malam ya shiga yi, nan fa yaga abin mamaki, don kuwa sunansa ya gani da na Ammi rubuce a jikin kadangaren. *yawan comments yawan typing* *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(Jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Na tabbatar da cewa yau mutane da yawa xasu ji ba dadi idan suka karanta wannan page din musamman masoya Ammi da Nauwar, ku yi hakuri haka tsarin labarin yake, fatana dai ku cigaba da kasancewa da wannan littafin, kuma kada ku manta da cewa DUKKAN TSANANI YANA TARE DA SAUKI, KUMA DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH YA ISAR MASA* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare ki masoyiya ta amana kuma yar uwa wadda take ji da ni take kaunata, har take da burin sanyawa diyarta sunana, SUMAYYA TAMBUWAL (Aunty sumy) Allah ya bar kauna ina godiya da kulawar ki gare ni* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆 6⃣9⃣ Da sunan Allah yasa hannu ya dauke kadangaren, waje ya fita ya jefar da shi a bakin bola, sannan ya dawo gida ya cigaba da yiwa Ammi addu'a, a haka har aka samu tayi bacci. bayan sun dawo cikin nutsuwa ne suka xuba abincin dare, suka ci sannan suka ci gaba da hira, bayan sun kammala kuma suka koma daki suka kwanta don yin bacci. A daren nan gaba daya malam bai runtsa ba saboda mugwayen mafarkai da ya rika yi, ga kuma abubuwa na ban tsoro da ya rika gani a xahiri, tashi yayi ya cigaba da salloli yana addu'a Allah ya bashi nasarar abinda yasa a gaba. Asubah nayi malam ya fito don xuwa masallaci, tashin matarsa yayi sannan ya nufi dakin su Nauwar don tashinsu su yi sallah, cikin nutsuwa yake kwankwasa kofar dakin amma shiru babu motsin mutum, kiran nauwar ya shiga yi amma shiru ba amsa, bude tagar dakin yayi ya leka kansa ciki don ganewa idanunsa abinda ya hana su tashi, ja da baya yayi yana salati saboda babu su Nauwar babu dalilin su, a gigice ya shiga dakin matarsa cikin tashi hankali yake mata magana. "dan Allah kin ga inda bayin Allahn nan suka shiga, na duba dakin su ko kyallin su ban gano ba, ko kin ji motsin inda suka shiga?" a raxane ta tashi daga kwanciyar da tayi. "me nake ji haka mara dadi malam, ka duba kuwa sosai ko dai idonka ne?" Hawaye na xuba a fuskarsa ya bata amsa. "wlh na duba kuma kofar dakin su ma a kulle take da sakata, ballantana a ce wani wajen suka shiga" Da sauri suka kara rankayawa don su sake tabbatar da abinda suke tunani, cigaba da duba gidan suka yi amma sam babu dalilin su, kuka sosai malam da matarsa suke yi, suna jimamin abinda ya faru da su Nauwar, alwala malam ya daura ya tafi masallaci, wani abin da ya sake daure masa kai kofar gidan duk a kulle suke, babu alamar an bude su, bayan an idar da sallah ne malam ya bada sanarwar abinda ya faru a gidansa, jajanta masa mutane suka rika yi sannan aka yi addu'ar Allah ya bayyana su. Tunda malam ya tafi ya bar matarsa ta kasa aikata komai sai kuka da kyar ta ja jiki tayi sallah, tana idarwa ta cigaba da xubar da hawaye, gaba daya rayuwar Ammi da Nauwar tausayi take bata, saboda suna fuskantar matsaloli masu yawa, da sallama ya shigo cikin gidan, samun ta yayi tana ta kuka tsugunnawa yayi yana rarrashinta. "kiyi hakuri babu abinda ya fi karfin Allah xamu taimaki wadannan mutanen da addu'a, Insha Allah duk inda suke Allah xai basu kariya, kiyi hakuri ki daina wannan kukan, babu maganin da xai mana addu'a suka fi bukata a yanxu ba kuka ba" share hawayen tayi sannan suka dauki alkur'ani suka fara karantawa suna yiwa su Nauwar addu'ar Allah ya bayyana su. suna cikin karatun ne suka ga wata guguwa tayo kansu, dagewa suka yi sosai da karatun da suke yi, tana xuwa daf da su ta dakata, sai kuma wani hayaki da ya cigaba da tashi, wata dariya aka saki mai ban tsoro har sai da malam ya raxana. tambayarsa matarsa tayi dalilin raxanar sa saboda ita bata ganin komai shi malam shi yake ganin abinda yake gani, basar da xancen yayi ya cigaba da karatunsa. sake bushewa aka yi da dariyar sannan aka fara magana. "mun ja daga kun ja, babu yadda kuka iya dole ku hakura wannan al'amari ne da babu warkewa a cikinsa" cigaba da dariyar aka yi, cikin xafin rai malam ya mayar da martani "mun dogara ga Allah kuma mun san xai isar mana,tsafi aiki banxa ne kuma da sannu xaku ga karshen ku, don babu abinda ya fi karfin mahalicci" hayakin ne ya cigaba da tashi sannan aka cigaba da jawabi. "hahhha baxa ka kara ganinta ba ballantana har ka bata magani, mun yi nisa da ita baxa ka kara haduwa da ita ba har abada, mun dauketa ta xama mallakin mu" ana gama wannan maganar hayakin ya gushe, hawaye ne ya rika sauka a fuskar malam, idanunsa sun yi ja saboda tausayin abinda ya faru da su Nauwar. cikin kulawa matarsa ta dube shi, "malam ni fa tun daxu nake ji kana wasu maganganu wanda ban gane kansu ba, da wa kake ne" share hawaye yayi ya dubeta. "Shaidanun nan su suka sace bayin Allahn nan" "innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta ambata" ita ma hawayen ta shiga xubarwa "lallai duk wanda ya yiwa matar nan asirin da ta shiga wannan halin baxai gama da duniya lafiya ba, ya Allah ka saka mata xaluncin da suka yi mata, Allah ka bata lafiya, Allah ka cigaba da tsare bayin nan naka a duk inda suke" kuka suka rika yi, a ranar basu rintsa ba saboda tausayi, yadda suka ga dare haka suka ga rana. rokon Allah suke yi Allah ya warware musu wannan mugun kulli da makiya suka yi musu, a ranar sun sauke alkur'ani ya kai sau uku suna nemawa su Nauwar rangwami a wajen Allah. *yawan comments yawan typing* *Jeeddahtulkhair😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Dan Allah a yi hakuri da jinkirin typing da nayi hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiya da nake fama da shi* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ki yar pot FAREEDA SULAIMAN (fary nice fareeda) na baki shi kyauta ba dan halinki ba* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣0⃣ Bude idanu nauwar tayi ta gansu a cikin wani kango mai cike da ciyayi babu komai a cikin sa sai taron bola da kaxanta gami da busassun kashi, jikin bangon da ke kangon rataye yake da tsummokarai abin dai babu kyan gani, a hankali ta bude idanu tare da ambaton Allah, mamaki ne ya cika xuciyarta ji take tamkar a mafarki, laluben gedenta ta shiga yi tana sake murje idanunta don ta tabbatar da gaskiyar abinda idanunta suke gane mata, sake bude idanu tayi sosai tabbas ba mafarki take yi ba su ne dai a wannan halin, Salati ta fara yi tana kuka tana ambaton Allah wani abinda ya Kara daure mata Kai shi ne, kofar kangon a kulle take Sannan basu ji wata alama na cewa an dauke su ba.mayar da kallonta tayi ga Ammi ganinta tayi tana ta faman bacci bata ma san abinda ake yi ba, tausayin Amminta ne ya kamata ta cigaba da share hawaye, tabbas lalurar hauka ba karamar tawaya bace ga dan Adam. A hankali tasa hannu ta janye ta daga bakin bolar da take, dankwalinta ta shimfida ta Kwantar da ita, a hankali ta janye jikinta daga nata, kofar kangon ta nufa, budeta tayi Sannan ta leka kanta waje mutane ta gani suna ta xirga-xirga babu wanda ya lura da su a wajen, komawa tayi ta xauna ta fara Shawara da xuciyar ta yadda xata nemawa kansu mafita, kokari tayi ta fita sai dai rashin samun suturar da xata rufe jikinta ya hanata fita, kasancewar basu taho da komai ba sai kayan jikinsu, bata son ta dauki dankwalin da Ammi ta kwanta a kai gudun kada ta tashe ta. Dudduba kangon ta shiga yi inda ta hango wani kwali a can nesa duk ya baci da kaxanta, tashi tayi ta dakko shi ta karkade Shi tsaf, shimfidar da ammi tayi a kansa sannan ta dauki dankwalinta ta daura. Hawaye ta shiga sharewa tana neman taimakon Allah, tunanin Malam Haruna ne ya fado mata a ranta, tasan duk inda suke hankalinsu ba a kwance yake ba, suna can suna tunanin halin da suke ciki, sosai ta rika ambaton Allah tana neman taimako a gare shi tasan bai manta da su ba, sake bude kofar tayi ta fita. Rasa inda xata dosa tayi don haka ta tsaya tana karewa wajen da suke kallo, unguwa ce ta masu rufin asiri kuma da dukkan alamu mutanen unguwar basu damu da jin halin da wani yake ciki ba, don duk wanda yaxo kallonta Kawai yake ya wuce ba tare da yace mata komai ba. Ganin tsayuwar da take yi baxai amfaneta da komai ba yasa ta fara bara tana neman sadakar kaya da abinci, haka tayi barar ta gaji don ko yar kallo bata ishi mutanen unguwar ba haka ta gaji da kewaye ta koma kangon, tana bude kofar taci karo da Ammi xaune a tsakiyar bola tana cin busashshen kashi, da gudu ta karasa ta kwace ta karkade mata hannu, fuskarta tayi ta mayar da ita inda ba bola. Kuka nauwar ta shiga yi mai cike da tausayi,duk wani mai imani idan yaga halin da take ciki sai ya tausaya mata. Rungume Amminta tayi tana hawaye, tana waigawa gefenta taci Karo da wani abin mamaki kwarya ta gani cike da nono an ajiye a gefenta, addua ta shiga yi gami da karanta ayatul kursiyyu nan da nan ta nemi kwaryar ta rasa. Tsoro ne ya mamaye xuciyarta tabbas idan suka cigaba da xama a wannan kangon wata rana xasu wayi gari aljanu sun sace su gaba daya. A yi hakuri ba Yawa *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *Dan Allah a yi hakuri da jinkirin typing da nayi hakan ya faru ne sakamakon rashin lafiya da nake fama da shi* *wannan shafin gaba daya sadaukarwa ne gare Ki yar pot FAREEDA SULAIMAN (fary nice fareeda) na baki shi kyauta ba dan halinki ba* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣0⃣ Bude idanu nauwar tayi ta gansu a cikin wani kango mai cike da ciyayi babu komai a cikin sa sai taron bola da kaxanta gami da busassun kashi, jikin bangon da ke kangon rataye yake da tsummokarai abin dai babu kyan gani, a hankali ta bude idanu tare da ambaton Allah, mamaki ne ya cika xuciyarta ji take tamkar a mafarki, laluben gedenta ta shiga yi tana sake murje idanunta don ta tabbatar da gaskiyar abinda idanunta suke gane mata, sake bude idanu tayi sosai tabbas ba mafarki take yi ba su ne dai a wannan halin, Salati ta fara yi tana kuka tana ambaton Allah wani abinda ya Kara daure mata Kai shi ne, kofar kangon a kulle take Sannan basu ji wata alama na cewa an dauke su ba.mayar da kallonta tayi ga Ammi ganinta tayi tana ta faman bacci bata ma san abinda ake yi ba, tausayin Amminta ne ya kamata ta cigaba da share hawaye, tabbas lalurar hauka ba karamar tawaya bace ga dan Adam. A hankali tasa hannu ta janye ta daga bakin bolar da take, dankwalinta ta shimfida ta Kwantar da ita, a hankali ta janye jikinta daga nata, kofar kangon ta nufa, budeta tayi Sannan ta leka kanta waje mutane ta gani suna ta xirga-xirga babu wanda ya lura da su a wajen, komawa tayi ta xauna ta fara Shawara da xuciyar ta yadda xata nemawa kansu mafita, kokari tayi ta fita sai dai rashin samun suturar da xata rufe jikinta ya hanata fita, kasancewar basu taho da komai ba sai kayan jikinsu, bata son ta dauki dankwalin da Ammi ta kwanta a kai gudun kada ta tashe ta. Dudduba kangon ta shiga yi inda ta hango wani kwali a can nesa duk ya baci da kaxanta, tashi tayi ta dakko shi ta karkade Shi tsaf, shimfidar da ammi tayi a kansa sannan ta dauki dankwalinta ta daura. Hawaye ta shiga sharewa tana neman taimakon Allah, tunanin Malam Haruna ne ya fado mata a ranta, tasan duk inda suke hankalinsu ba a kwance yake ba, suna can suna tunanin halin da suke ciki, sosai ta rika ambaton Allah tana neman taimako a gare shi tasan bai manta da su ba, sake bude kofar tayi ta fita. Rasa inda xata dosa tayi don haka ta tsaya tana karewa wajen da suke kallo, unguwa ce ta masu rufin asiri kuma da dukkan alamu mutanen unguwar basu damu da jin halin da wani yake ciki ba, don duk wanda yaxo kallonta Kawai yake ya wuce ba tare da yace mata komai ba. Ganin tsayuwar da take yi baxai amfaneta da komai ba yasa ta fara bara tana neman sadakar kaya da abinci, haka tayi barar ta gaji don ko yar kallo bata ishi mutanen unguwar ba haka ta gaji da kewaye ta koma kangon, tana bude kofar taci karo da Ammi xaune a tsakiyar bola tana cin busashshen kashi, da gudu ta karasa ta kwace ta karkade mata hannu, fuskarta tayi ta mayar da ita inda ba bola. Kuka nauwar ta shiga yi mai cike da tausayi,duk wani mai imani idan yaga halin da take ciki sai ya tausaya mata. Rungume Amminta tayi tana hawaye, tana waigawa gefenta taci Karo da wani abin mamaki kwarya ta gani cike da nono an ajiye a gefenta, addua ta shiga yi gami da karanta ayatul kursiyyu nan da nan ta nemi kwaryar ta rasa. Tsoro ne ya mamaye xuciyarta tabbas idan suka cigaba da xama a wannan kangon wata rana xasu wayi gari aljanu sun sace su gaba daya. A yi hakuri ba Yawa *jeeddahtulkhair 😘* [9/9, 9:17 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 7⃣1⃣ Haka suka kasance a wannan hali a kullum akwai kalar abubuwan ban tsoro da xata ci karo da shi, ga ciwon Ammi ya dada dawowa sabo saboda rashin kulawar da take samu, sannan ga kwana a kusa da bola, a lokuta da dama har ji take ana kiran sunan ammi ana cewa ta taso su tafi sai ta tsananta addu,a sannan take daina jin muryar da take kiranta, ba karamar wuya take sha ba a halin yanxu ita kanta aljanun na mata baraxana da rayuwarta, dagewa tayi da fadawa Allah matsalarta Sannan taji saukin abubuwan. Yau ma kamar kullum dankwali ta yafa ta fita yin bara, kallo daya xaka yi mata ka gane tana cikin matsala kuma tana matukar bukatar taimako, duk kayan jikinta sun yage, takalmin kafarta ya tsinke sai kullewa tayi da Leda, ga dauda ko ta ina saboda ta dade bata ga ruwan wanka ba, duk tayi baki ta fita daga hayyacinta, kafin ta fita sai da ta daurewa ammi kafa da tsumma don gudun kada ta haura katanga ta gudu, kulle kofar kangon tayi sannan ta fita, yau dai a sa'a ta fita domin kuwa ta samo alkhairi masu yawa, mutane da dama sun tausayawa halin da suka ganta a ciki, wannan dalilin yasa suka rika bata sadaka, sai dai ta samu abincin da xai riketa kwana uku ba tare da ta fita bara ba. Haka rayuwar su ta cigaba da kasancewa har tsawon sati bakwai yau da dadi gobe ba dadi, wata rana su samu abincin kaiwa bakin salati, wata rana kuwa sai su yi kwana biyu basu samu abinda zasu ci ba, haka suka xauna cikin wannan hali har xuwa lokacin da Allah yasa saimah ta kai su gidan su inda ta roki mahaifanta alfarma ya ba su daki. Lallai baxa ta manta da karamcin da iyayen saimah suka yi mata ba, su suka fitar da su daga halin kunci da takaicin da suka kasance a ciki na shekara da shekaru. Tana kammala tunanin da take yi ne, taji anyi sallama cikin dakin da suke, saimah ce da Abbanta da mamansu tare da yayyenta guda biyu suka shigo dakin, sallama suka yi, cikin nutsuwa nauwar ta amsa musu sallamar samun guri suka yi suka zauna. Cikin nutsuwa ta tsugunnah har kasa ta gaida su, tare da sakin fuska suka amsa mata da lafiya lau. Duban Ammi suka yi suka yi mata sannu, kwance take tana ta faman sharar bacci cikin kulawa Abban saima ke mata magana. "Tunda kun samu watanni a gidan nan kun huta kun dawo cikin nutsuwar ku, ya kamata musan tarihin rayuwarki da abubuwan da suka faru da ku domin mu san irin taimakon da ya kamata mu baku." Share hawaye nauwar tayi ta fara basu labarin abubuwan da ya faru da su da irin gwagwarmayar da suka yi da makiya, kuka sosai suka rika yi saboda labarin su cike yake da abubuwan takaici da bakin ciki. Cikin karfin hali Abban saima yake magana. "lallai yarinya kina cikin yanayin da ya kamata duk mai imani ya tausaya muku, kuma insha Allah muna da taimako na musamman da xamu baki, abinda xamu fara yi yanxu shi ne mu nemo nahaifinki mu sanar da shi halin da ake ciki yanxu" Mayar da kallon shi yayi gareta. "kina da number wayarsa ne mu kira mu sanar da shi inda zai same mu? Share hawayen da ya cika idonta tayi. "ba nida ita Abba, ammi ce kawai ta haddace " Cike da tausaya ya dubeta. "bana so naga kina kuka, kiyi hakuri mu bi komai a sannu insha Allah xamu same shi ba tare da mun sha wahala ba" Godiya ta yiwa Abba. "ba komai nauwar insha Allah kinxo inda xa a tausaya miki daga nan kuma Xaki hadu da abbanki" Murmushin farin ciki ta rika yi sbd dadi har da rufe fuska tana dariya, tunda suka bar gida bata taba jin dadi irin na yau ba, saboda an mata albishir din haduwa da mahaifanta. Abba yaji dadin yadda yaga nauwar na farin ciki, magana ya cigaba da yi mata "yanxu nasa a kira mai magani ya fara bata taimakon gaggawa saboda tana bukatar a kula da ita sosai idan ya kama ma sai an mayar da ita gidan maganin duk xamu amince sabd Lafiyar ta tafi mana komai a halin yanxu." Mikewa suka yi gaba daya suka bar dakin, har bakin kofa nauwar ta raka su, tana dawowa ta fadi tayi sujjadar godiya ga Allah, tabbas duk wanda ya dogara ga Allah xai shiga cikin lamarinsa ya taimake shi. Tun daga wannan lokacin rayuwar nauwar ta fara canjawa daga bakin ciki zuwa farin ciki, kullum addu'arta bata wuce Allah ya bawa amminta lafiya ba, ya kuma juyo da hankalin Abbanta kansu. Saima ce ta shigo da gudu dakin nauwar, tana murna, kwala mata kira ta shiga yi "sisina tashi naxo mana da albishir din arxiki" kwance ta tarar da ita, a raxane nauwar ta mike tana harar saima. "ni har kin bani tsoro kawata, wane abu kika kawo min haka" "Sai kin tashi daga kwanciyar da kika yi xan nuna miki idan ba haka ba kuma na koma da kayana" Da sauri ta tashi tana dubanta tana murmushi Uniform ta mika mata. "karbi gobe ki shirya akwai makaranta saura kuma kiki tashi don nasan mutuniyar tawa akwai nauyin bacci" Tsalle nauwar tayi ta rungume saima tana godiya "Alhamdulillah na gode sisina Allah ya biya Abba da aljanna babu abinda xamu iya biyansa dashi Sai dai addu,ar fatan alkhairi domin yayi mana komai " Wani hawaye taji ya taho mata da sauri saima tasa hannu ta share mata hawayen. "to uwar saurin kuka har idanun ki xai kawo ruwa ko, kinga bana so kike wannan kukan mun zama daya fa" Share

Chapter 20 of 29