Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Hamdan ne ya kira bayan sun gaisa ya sanar musu da xuwan maminsa, farin ciki ne ya bayyana a fuskar Ammin Nauwar, tayi murna da xiyarar da xata kawo mata, saboda sun jima basu had'u ba, kasancewar Baban Hamdan mutum ne mai kulle, addu'a tayi musu Allah ya kawo su lafiya, sannan ta ajiye wayar. Kitchen ta shiga ita da Nauwar suka had'a musu delicious, sannan suka Jere musu a kan dining. Sashin Abbanta Nauwar ta shiga, samun shi tayi xaune kan kujera ya had'a kai da gwiwa, sallamar da tayi ne yasa ya d'ago kanshi yana ganin ita ce ya mai da kanshi 'kasa, d'aga mata hannu ya yi ya dakatar da ita. "Kada ki fara 'karaso min nan, fad'i duk abinda kuke bu'kata na sallame ki, warin ki ya cika wajen nan gaba d'aya, ki fad'i ko menene ki 6ace min da gani. Hawaye ne suka fara sauka a fuskar ta, ba abinda nake bu'kata a gurinka Abbana sama da dawowar farin cikin ka da Walwalarka tare da mu, ka daina kula mu ka daina son ganinmu, me muka yi maka Abbanmu??mu nemi gafara ka yafe mana, kai kad'ai ne rayuwar mu wanda muke kallo a kowane lokaci mu yi farin ciki, mu da Ammin mu, me yasa ka canja mana lokaci daya Abbana??? Kuka mai tsanani ne ya kufce mata Ya tausayawa 'yar tasa, musamman da yaji Wad'annan maganganun daga gareta, gaskiya Nauwar yarinya ce mai hankali yanxu har ta fahimci halin da nake ciki na 'kunci da rashin son ganin su. Ganin mahaifin nata ya shiga tunani ya kuma kasa bata amsa, sai ta 'kara rushewa da kuka, 'karasawa kusa da shi ta yi, ta ri'ke 'kafar shi tana cigaba da ro'kon shi ya yafe musu. Hawaye ne ya ri'ka sauka a kuncin sa, tallafo fuskarta yayi da hannunsa, yana kallonta yana'kara xubar da hawaye, ji yake gaba d'aya ya tsani kan sa, ya tsani rayuwar duniyar ma gaba d'aya. Magana ya fara yi mata bakin shi yana rawa "Wlh ina sonku 'yata, ban San me yasa na Wayi gari a cikin tsanarku ba, xuciyata tafasa take yi idan na d'ago ido na kalleku, xamana ni kad'ai ba tare da xama tare da Ku ba, shi ne Kwanciyar Hankalina, Ku gafarta min Ku cigaba da hakuri da ni a duk yadda ku ka sameni, ni dan Adam ne, Ku ri:ka yi min uxuri, kuma Ku tayani addu'a Allah yaye min abinda yake damuna. "Mun yafe maka Abban mu, kuma baka yi mana komai ba, ka kula da mu ka so mu, kuma insha Allah xamu cigaba da addu'ar Allah ya yaye maka matsalolin ka. Kuka suka ri'ka yi gaba d'ayan su babu mai iya rarrashin wani a cikinsu. Tausayin mahaifinta ne ya kamata,nan da nan ta ji xaxxabi ya rufeta don haka ta tashi ta koma wajen mahaifiyarta. Tana shiga ta sameta xaune kan sallaya tana addu'o'i,ganin yadda yanayin 'yar tata ya canja, ga fuskarta tayi jawur alamun tasha kuka ta koshi, shi yasa ta mi'ke ta tare ta hnkalinta a tashe take tambayarta abinda ya faru da ita. "Hawaye ta shiga sharewa ta xayyane mata yadda suka yi da mahaifinta, ita ma dai ha'kuri ta bata ta kuma rarrasheta a kan su cigaba da addua komai mai wucewa ne. Tsayawur mota suka ji, don haka suka fito gaba dayan su waje saboda sun San ba'kinsu ne suka samu iso wa, 'karasawa suka yi garesu rungume juna suka yi suna farin ciki, d'unguma suka yi gaba d'aya suka shiga ciki. Kayan abinci aka halarto musu da shi suna ci suna hirar yaushe gamo. Ita kuwa Nauwar na gefe tun daga gaisuwa bata sake cewa da kowa komai ba, kallo d'aya xaka yi mata kasan tana cikin damuwa, magana Amminta tayi mata. "Kira Abbanki kice masa mamin su Hamdan taxo xa su gaisa. Kamar Wacce Kwai ya fashewa a ciki haka ta tashi ta tafi kiran shi, tarar da 'kofar dakin shi tayi a rufe don haka ta dawo ta sanar da Amminta. Tashi Ammin tayi da kanta ta je ta samu 'kofar tashi a kulle, kamar yadda ta fad'a mata, Kwan Kwas 'kofar ta ri'ka yi, amma ya yi banxa da ita, ta fi Minti 30 tana bugu bai bud'e ba, sai da ya gaji da bugun da take yi ya taso a fusace ya fara masifa. "Me kike so ne a tare da ni,da kike bibiyata haka?, kin turo 'yarki d'axu duk bai isa ba sai kin xo da kan ki. yanxu kuma me kike son nayi miki, wlh idan har ku ka takura min xan yi yaji na bar muku gidan gaba d'aya, kun dameni, ke warin ja6a 'yarki ma abinda take yi kenan. kada Ku 'kara xuwa inda nake ko da wasa, Idan kuma ku ka sake yi, xan nuna muku 6acin raina, kin ji na fad'a miki. Mayar da 'kofar d'akin ya yi ya kulle ya barta da ciwon xuciya. Hawaye ne cike da idanunta,don haka ta kasa fadawa ba'kin dalilin rashin xuwan sa su gaisa, ganin yadda ta canja lokaci d'aya daga farin ciki xuwa akasinsa ne, yasa suka tambayeta abinda yake damunta, amma sai ta'ki fad'a musu tace ba komai, don haka suka 'kyaleta suka bud'e wani babin hirar. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆 🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* Maijiddatijjania dam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *sadaukarwa gare Ku 'yan uwa na amana ina godiya da gudunmawar ku gareni* *MAIJIDDA BELLO* *UMMU EL-NAJEEB GYARA KANKI* *FEENAH YAHYA (feenah berry)* *RAHMATULLAH MAMAN UMMY* *JUMANA AHMAD* *JAWAHEER SALEEM* *ASLAMIYYA ISLAM* *MAMAN IKRAM* *INA YIN KU KUMA MUNA TARE HAR ABADA* *gaisuwa ta musamman gare ki Takwarata kuma aminiyata* *MAIJIDDA SALEH* 2⃣4⃣ Haka suka cigaba da kasancewa a cikin gidan yau da dad'i gobe ba dad'i, ba wani kyautatawa tsakanin su da shi, sai tsangwama da cin xarafi ne kullum ke biyo baya, yanxu ta kai ta kawo ko hidimar makaranta ya daina yi wa yaran sa, komai sai dai Ammin su tayi musu, gaba d'aya ya burkice ya xama wani irin mutum Mara dad'in kai. Safiyar ranar asabar ya sanarwa da Ammin Nauwar xai je 'Dan batta, addu'a tayi masa sannan ta bashi kud'i da shadda ta bayar a kai wa Baffa, ita ma Nauwar turare ta d'akko ta bashi ya bai wa kakanta, saboda ta sha'ku da Baffa suna son shi, a ko da yaushe ba su da burin da ya wuce su je su gaishe shi, amma basa samun goyan baya daga Abbansu. Mota ya d'auka ya fice sai 'Dan batta, tarar da gidan yayi ba kowa, don haka ya xauna don ya jira su, bai dad'e da xuwa ba, ya ji sallamar Baffansa, don haka ya mi'ke da sauri ya isa inda yake, fuskarsa a sake ya gaishe shi. "Ina Kwana Baffa "Lafiya lau ya iyalin naka" "Suna lafiya, gurin xama ya ba shi suka karasa gaisa wa. ga wannan kayan da kud'i, tace na baka ga kuma turare Nauwar ce ta baka. "Lallai amaryar tawa tana yi da ni, yaushe xaka kawo min su na gansu ne, na dad'e fa rabona da yaran nan. "Xa su xo insha Allah Baffa makaranta ce take tsare su, shi yasa basa samun damar kawo maka xiyara a Kai a Kai amma suna nan xasu xo insha Allah. To Allah ya kawo Ku lafiya, ai yana da kyau a mai da hankali wajen karatun yaran, Allah yayi jagora. Amsawa yayi da Ameen. Godiya mai yawa Baffa yayi masa, sannan suka fara tattaunawa a kan dad'ewar da yake yi bai kawo masa xiyara ba. "Wlh matsalar gurin aiki ne Baffa amma ai kana raina insha Allah xaka ri'ka ganina" "To Allah ya taimaka, ameen yace sannan suka cigaba da hira, yana bashi labarin girman da su Nauwar suka yi, yana ta farin cikin yadda iyalan d'an nasa suke cikin Walwala da Kwanciyar hankali. Inna karime suka hango, ta dawo daga unguwar da ta tafi, tun daga nesa ta gano Abban Nauwar, sai bud'e masa baki take yi, Baffa yayi mamakin ganin hakan daga gareta saboda yasan a da ko 'kaunar ganinshi ba ta yi, don haka ya saki baki yana ganin ikon Allah. "Yau muna da manyan ba'ki a gidan namu kenan, barka da xuwa Alhaji Mudi, ya Kwana biyu, ka ya da mu gaba d'aya, d'an le'kowar da kake yi a gaisa duk ka daina. Ita ma dai uxurin aiki ya bata, sannan ta tashi ta shiga d'aki ta kawo masa fura, kafin ta kawo masa sai da ta 'kara barbad'a garin maganin da suka je wajen wani Boka ya basu. "Ga wannan Alhaji Mudi, ka sha hanya kuma nasan baka sa komai a bakin ka ba. ai kuwa dai innah, kamar kin San ina jin yunwa ji nake yi kamar an min sata a cikina. Hannu biyu yasa ya kar6i furar, ya fara sha, Baffansa bai so ya sha furar ba, amma babu yadda xai yi ya hana shi sha, saboda ta tasa shi a gaba, yana sha tana masa dad'in baki, idan ya ce xai hana shi sha, tsaf xata iya la'antar sa, don haka yayi hakuri ya Kyale, yana ta nemar masa tsari daga tarkon sharrin da suke son d'ana masa. Sai da ya shanye furar tas sannan ya mi'ka mata Kwanon ta kar6a, tana sa masa albarka Yana gamawa ya mi'ke don yin sallama da Baffa rafar 'yan 100 ya mi'ka masa godiya ya rika yi masa yana sa masa albarka. Ganin inna karime suka yi d'auke da tarin kayanta a hannu, tambayar ta Baffa yayi. "Ina xuwa haka innah na ganki da tarin kaya a hannu? "Birni xan koma na ci arxi'kin jikana ko kana ba'kin ciki ne? tana maganar tana yarfa masa wani matsiyacin kallo. "Innah a ganina kamar lokacin komawar ki bai yi ba , ki bari Allah ya kaimu bikin Nauwar mana ba sai ki je kiyi Kwanakin da xaki yi ba, amma idan kika koma yanxu ai kamar da takura ko, kuma xa a shiga hakkin iyalansa, tunda Kinga gidan na xaman mutum d'aya ne. "To sarkin tsari xaka fara jero xancen naka ko? Gida dai ba naka bane, gidan jikana ne yadda kake da gado nima haka nake da shi, don haka dole na koma" "Shi dai Mahmud murmushi kawai yake yi, ba komai Baffa ka bari mu je da ita d'in ba wani abu". Xuciyar Baffa ba dad'i haka suka wuce suka fita daga gidan. Kayanta ya kar6a ya saka mata a cikin mota ita kuma ta shiga gidan Audu a guje ta kira Magaji, tarin tsummokaransa ya d'akko ya xuba a motar sannan suka d'auki hanyar xuwa Birni. Suna shiga gidan su Nauwar ta yi tsalle ta shige Falo ko kayanta bata tsaya d'auka ba, tarar da su tayi suna kallon film, sai ganinta suka yi ri'ke da 'kugu tana jijjiga jiki, innalillahi Wa innah ilaihi raji'un shi ne abinda Ammin Nauwar ta fad'a. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* maijiddatijjaniadam@gmail.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *yau dole na ci burki na mi'ka gaisuwa da jinjina gare ku 'yan uwa na amana, muna mugun ji da ku, gami da alfahari da ku a gidanmu na EXCLUSIVE, gidan dad'i da hadin kai, kuna raina muna mugun tare, har abada baxan manta da ku ba* *UMMY XIE* *REAL KHADY* *ACTION BABY* *ina yin ku yasin*😍 *ina mi'ka godiya gareki yar uwa ta jini SUWAIBA USMAN ADAM'S JOS, jeeddah tana godiya da yadda kike ji da ita* *wannan shafin gaba d'ayan shi naki ne uwa ga Yusuf kina yi muna jin dad'i, kina bari muna jin haushi, makiyanki fadawanki, murucin kan dutse baki fito ba sai da kika shirya, ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO, Allah ya kara miki basira da haxaka* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 2⃣5⃣ Kallonta tayi ido cikin ido, tana jefa mata wata mummunar harara, tunda Kin ga masifa da bala'i, ai dole ki nemi tsari dani. da uwar ki ce taxo nan xaki yi mata abinda kika min yanxu? Saboda kin rainani ba ni da daraja a idonki xaki dubeni ki yi min ta'awixi, don baki san daraja da mutuncin furfurar tsohuwar wasu ba ko?nasan dai duk ba'kin cikin ganina kike yi, kuma xama daram, naxo naga abinda kike shukawa ke da yaranki marasa tarbiyya, ko tanka mata Ammin Nauwar bata yi ba, haka ta cigaba da balbala masifa. A dai-dai lokacin da take fad'an ne Abban su Nauwar ya shigo hannunshi ri'ke da taummokaran da suka taho da shi, Magaji na biye da shi a baya. Me ke faruwa innah, naji hayaniyarki har waje, wane ne ya ta6a min ke? Fashe wa innah karime tayi da kuka, wlh Alhaji Mudi tunda na shigo gidan nan, yaran nan da uwar su, suka had'u suna xagina, Wai naxo daga'kauye ina warin daddawa xan 6ata musu gida, suka had'e min kai suka min xagin tsakar nama. Yana jin abinda ta fad'a na 'karya da gaskiya ya hau fad'a, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ri'ke mata hannu ya yi, ya xaunar da ita a kan kujera, kuma yayi al'kawarin duk wanda ya kara 6ata mata rai a cikin yaran sai ya kore shi daga gidan, shigewa ya yi ya shiga 6angaren shi. 'Kafa d'aya kan d'aya ta d'ora tana harar kowa d'aya bayan d'aya, kad'an ku ka fara gani In dai ina nan, xaku bada labari da kan ku nice tuwon tulu mai wuyar Kwashewa, kuma carbin Kwai mai wuyar ja. Nauwar ce ta mi'ke ta matsa kusa da mahaifiyar ta, Ammina wai wannan kaxamar masifaffiyar tsohuwar daga ina?naga taxo tana mana wasu halaye, tana son ta hargitsa mana gida ta hanamu jin dad'in mahaifin mu, to dai-dai mu ke da ita, duk abinda taxo da shi xa mu yi mata maganin shi, xa mu koya mata hankali, ta ja tsaki ta kuma dubi innah karime ta Kwad'a mata wata uwar harara. Sakin baki tayi tana kallonta, ta cika da mamakin yadda yarinya 'karama ta fad'a mata magana, ta kuma kasa mayar da martani. Magaji ne ya tashi a fusace ya falla mata mari ji kake tasssssss!!!! Innar tamu ki ke xagi,saboda kunya ta miki 'karanci, uwar ki ta koyar da ku rashin tarbiyya, wlh ki shiga hankalinki, a kan tsohuwar nan xan iya karya ki naga wanda ya tsaya miki. Dafe kuncinta tayi tana jin rad'ad'in marin da yayi mata, d'aga hannu tayi xata rama, Amminta ce ta dakatar da ita, don haka ta kyale shi, amma ta ci alwashin duk daren dad'ewa sai ta rama, don baxai mari fuskar ta a banxa ba. 'Daki ta shige ta fad'a kan gado,tayi kuka kamar idonta xai fad'o kasa, ta tabbatar tunda tsohuwar nan ta dawo gidan su, sun shiga uku, sun fad'a halin tsaka mai wuya ita da mahaifiyar ta. Haka ta kasance har bayan magariba bata sake fitowa falon ba, a d'aki take gabatar da sallolinta, tana addu'ar Allah ya kawo musu mafita. Fu'ad ne ya shigo sallama yayi sannan ya samu gefen gadon da take ya xauna. "Wai har yanxu kuka kike yi Yaya Nauwar? Kiyi ha'kuri da abinda Magaji yayi miki, ina nan xan rama miki, yanxu na Kyale shi ne saboda idan na kula shi xan yi sanadin 6acin ran Ammin mu, kiyi hakuri my sister. Share hawayen tayi na gode little brod, amma fa sai mun tsaya tsayin daka mun 'Kwatarwa Ammi ha'k'kinta, naga alama suna son mayar da mu ba komai ba a cikin gidan nan. "Gaskiya ne maganarki amma mu bi komai a sannu, kuma mu ri'ka addu'a saboda naga da shirin sharri ta shigo mana. Muryar Hamdan suka ji don haka gaba d'aya suka fita falon dan su tarbe shi. "Babban aboki oyoyo, inji Hamdan, hannu ya mi'ka masa suka gaisa, ya school d'in ya tambaye shi, hop komai normal? Alhamdulillah yayana muna nan muna fama. yanayin Nauwar kawai ya kalla ya gane bata cikin Walwala, ga idanunta sun 'kan'kance sun yi ja. Come on dear, taso wa ta yi ta matso gare shi, kanta ya dafa yana dubanta, Wai me ke damunki ne?ni fa a satin nan duk wani so weak nake ganinki, pls tel me what's wrong? langwa6ar da kai tayi tana sharar wasu sabbin hawayen da suke Kwarara a kan fuskarta, ya fuskanci matsaloli a tare da ita, ta kuma kasa magana gaba d'aya sai kuka, tausayinta ne ya bayyana a fuskar shi, stop crying and speakup sis! da ya ga bata son fad'a mishi sai suka koma uwar d'aki, gaba d'aya suka xauna, I don't know how say out yadda nake jin 6acin rai da ba'kin cikin abubuwan da suke faruwa da ku, idan kun lura har d'auke 'kafana nayi daga gidan nan saboda bana son ganin abinda xai tayar min fa hankali. Ki fada min abinda ke faruwa da ku, ban San ganin kina min asarar hawayen ki, take this ki share min hawayen, ki kuma yi min bayani abinda ya sa ki kuka. hand kacif ya mi'ka mata tasa hannu ta kar6a ta shiga share fuskarta. Magana ta fara yi masa tana shashshe'kar kuka, Magaji ne ya mareni, glas d'in da ke sanye a fuskarshi ya xare,What!! Me kike fad'a min haka mara dad'i, waye Magaji!!! Menene ala'kar ki da shi, da har xai samu damar marin ki, me kika yi masa? A dai-dai lokacin da yake maganar ne innah karime ta jiyo shi,don haka ta biyo sautin inda yake ta le'ko da kanta, ubanka tayi masa, munafuki mai shiga tsaknin 'yan uwa, kai kuma waye da xaka xo ka shiga fad'an yan uwa? Shishshigin menene ya kawo ka har uwar d'aki, algungumi da kanka kamar na mutane. Shiru ya yi mata, da ya gaji da sababin da take ta yi, ya fice ya bar mata d'akin, Ammin Nauwar ya tarar a falo tana ta jimamin fad'an da take masa, amma ba ta da halin yin magana, ha'kuri ta ri'ka bashi, haba khalaty kada ki damu ai idan da sabo mun saba da halin su, sallama yayi mata ya wuce gida. Nauwar ce ta biyo bayansa da sauri har da ta tarar da shi, kiran sunan shi tayi, ya Hamdan!!! Juyo da fuskar sa ya yi ya kalleta, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, tarin takaici ne a cikin ranshi, kayi hakuri ya Hamdan dan Allah kasan halin mutanen nan sai su, kada kasa wannan abin a ranka. 'Dan murmushi yayi, ba komai Kanwata, ki koma gida kada kiyi laifi, juyawa tayi ta tafi,tana tafiya tana waiwayen sa har ya fita daga gidan. *jeeddahtulkhair*😘 [9/9, 9:11 PM] It B Y Ebrerheem: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *AL-MAJIRA* 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 *NA* *JEEDDAH TIJJANI* *ADAM* *(jeeddahtulkhair)* Maijiddatijjaniadam@gmai.com *♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *Wannan shafin gaba d'ayan shi naki ne MAMAH ALEEYOU KD, JEEDDAH tana ji da ke, kuma tana alfahari da ke a cikin 'kannenta, yasin ina yin ki MAMATY kuma muna mugun tare*🤝 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆 2⃣6⃣ Hamdan na isa gida ya shiga 6angaren mahaifiyar sa samun ta ya yi tare da wata ma'kociyar su hajiya maryam, wadda kuma aminiyar maminsa ce don tare suka taso tun suna yara. har 'kasa ya tsugunnah ya gaida su, cikin sakin fuska suka amsa masa, sannan ya tashi ya shiga cikin d'akinsa . bin Hamdan Hajiya maryam tayi da kallo har ya wuce d'akin sa, sannan ta dawo da kallonta ga mamin Hamdan. " Hajiya zeenah anya baxa mu yi had'in xumunci tsakanin N Ajmal da Hamdan ba kuwa, ina ganin yaran xa su dace da junan su, yadda muke aminan juna, ya kamata a ce mun had'a yaran mu don xumuncin mu ya d'ore ko ba haka ba? " Nima na dad'e ina wannan tunanin Hajiya Ajmal yarinya ce mai nutsuwa shi ma Hamdan d'in haka, kuma dukannin su suna da biyayya da sau'kin kai, ina ganin baxa mu samu matsala da su ba. "gaskiya ne Aminiya Allah ya wuce mana gaba" "Amin suka amsa gaba d'ayan su, suna ta farin ciki. Har bakin gate mamin Hamdan ta rakata, sannan ta dawo ta shiga gida. Shi kuwa Hamdan d'akin sa ya shige, ya fad'a kan gado,idanuwansa na kallon sama ya fara tunanin hanyar da xai 6ullo wajen taimakawa su Nauwar, saboda halin da suke ciki ya fara ta6a masa xuciyarsa sosai, wayar shi ya janyo ya kira Ammin Nauwar, sallama tayi masa bayan sun gaisa ya shiga yi mata nasihohi masu ratsa xuciya, tare da bata misalai masu kyau wad'anda xasu kwantar mata da hankali, ya kuma umarceta da dagewa da karatun kur'ani, godiya tayi masa sannan suka yi sallama ya kashe wayar. ******************* Bayan Nauwar tayi sallama da Hamdan kuwa kai tsaye falo ta shige, tana xuwa, tarar da magaji tayi da innah karime suna tattaunawa, don haka ta shiga kitchen don ta samu abinda xa ta ci, jiyo magaji tayi yana cewa da innah karime "Ni fa innah tun da naxo gidan nan kwanakin baya naji ina son yarinyar nan, wlh kwata-kwata na kasa sukuni, na gama yin xurfi a 'kaunarta, marin nan ma da nayi mata yanxu haka nadama nake yi, innah ya xa a yi yanxu,ki shige min gaba don wlh ina sonta, kuma idan har ban sameta ba, komai xai iya faruwa da ni,ki taimaka min innata. "Duk naji bayanan ka amma kai yanxu kana ganin wannan shegiyar 'yar mai tsiwar tsiya ce xata so ka, ga d'an banxan girman kai, da rashin tarbiyyar da aka gina su a kai, ka tuna fa kai ba kowa ba ne, face mutumin da yaxo daga karkara ita kuma talaka, ita kuma 'yar birni, 'yar boko 'yar masu kud'i, ina wannan had'in xai had'u, ka duba fa saboda Allah" "Duk wannan maganar ki shareta innah, idan muka koma gurin gobe da nisa, sai na fad'a masa abinda yake faruwa, nasan akwai taimakon da xai min dole ta so ni,ko tana so ko bata so. "Gaskiya ne d'an nan, dad'ina da kai saurin fuskanta, ni na manta ma da gobe da nisan gaba d'aya, shi yasa na musanta maganarka tun a farko, amma yanxu abinda xa a yi shi ne, ka ri'ka sakar mata fuska kana d'an janta a jiki, kana yi mata wasa da dariya, yadda muna doka asiri aikin xai kamata da sauri tunda dama kun saba, kasan fa ya'ki d'an yaudara ne. "Dariya ya ri'ka yi ya ji dad'in maganar da ta fad'a masa. tattaunawar da suka ri'ka yi kenan, sai da Nauwar ta gama jin duk abinda suke fad'a sannan ta fito daga kitchen d'in, gaba d'ayan su kallo suka bi ta da shi, ita kuwa ko inda suke ma bata duba ba ta wuce d'aki. Fu'ad ta tarar yana ta faman yin game a system d'in shi, don haka ta 'karasa kusa da inda yake ta ajiye abincin, labarin abinda ta jiyo daga wajen su innah ta bashi. fu'ad ya ji xafin labarin da ta ba shi amma sai ya danne xuciyarsa, saboda idan ya nuna ya damu xai saka 'yar uwar shi a damuwa, shawarwari ya shiga bata. "ya Nauwar ina ganin kada ki nuna ba kya son magaji, kuma kada ki nuna musu kin ji abinda suka fad'a, saboda matar nan bata tsoron Allah komai xata iya yi don ta cuce mu. yanxu ki taso mu je wajen Abbanmu mu fad'a masa abinda yake faruwa. xaro idanu Nauwar tayi "yanxu kana ganin idan muka fad'awa Abba baxai kore mu ya ci mana mutunci ba?kasan fa Abba ya canja ba irin yadda ka san shi da bane. "kada ki damu insha Allah babu abinda xai faru, ke dai ki taso mu sanar da shi, saboda matsala tun tana 'karama ake maganinta ba sai ta girma ba. tashi suka yi suka shiga sashin mahaifinsu, tarar da shi xaune suka yi yana danna waya, yana ganin su ya mi'ke tsaye, xare musu ido yayi gami daka musu tsawa "me kuke bukata ku ka shigo min d'aki a irin wannan lokacin ko munafukar uwar taku ce ta turo ku, ku ga me nake yi. ko me nake aikatawa? a fusace fu'ad ya fice ya bar d'akin saboda xuciyar sa baxa ta iya jure jin maganganun da yake gayawa mahaifiyar su ba. "Wlh Abbah duk ba wannan ne ya kawo mu ba, dan Allah ka taimake mu ka saurari abinda muka xo maka

Chapter 6 of 29