tona asirin babu abunda zai faru, dan Dad bazai aureta ba tunda yaji labarin yanda take, kafin ta ce. “ Dama…dama zuwa nayi na muku Allah ya tsare gaba.”
Dad ya amsa da. “ Amen.”
Da sauri Umma Fauziyya ta fita ko bari su hada ido da Safeera batayi ba, a waje ta tarar da Saif yana zaune ya zabga tagumi, da sauri ta fice daga hospital 🏥 din.
*Some hours later*
~bayan wasu awanni~
Dad na zaune a falo shi da Ummah, suna dan taba hira.
Dad ya ce. “ Amina, a labarin da yarinyar nan ta bada baki dauki wani abu ba?.”
Shuru Ummah tayi kafin ta ce. “ Gaskiya ban fahimci komai ba, kuma….” Shuru ta danyi kafin ta daura da cewa. “ Kaman Saifullahin da ta bada labarin shine Ɗanmu ko?.”
Murmushi Dad yayi tare da jinjina kai ya ce. “ Nima haka nake gani, ance ba kyau zargi amma ni fa ina zargin Ɗanmu, kenan yaron nan ya dade yana aikata ba dai-dai ba bamu sani ba?.”
“ Hmm! Amma Saif bazai yi haka ba.”
“ Ku iyaye Mata ba’a isa a faɗi laifin Ɗanku ba, ai shikenan nikam zanyi bincike dai-dai gwargwado na har sai na gano gaskiya.”
“ Allah ya taimaka.”
“ Amen idan da gaske kike.”
Shuru Ummah tayi dan yanzu laifin zai dawo kanta, Dad ya ce. “ Nikam ina ƴan uwanki ne?.”
“ Su waye kenan?.” Ummah ta tambaya da mamaki a fuskarta.
“ Hafsat da Maimuna.”
Tabe baki Ummah tayi tana cewa. “ Ka kirasu mana ai naga matanka ne, kai zaka fini sanin inda suke.” Daga haka ta tashi ta nufi bangaren ta dan dama yau ba girkin ta bane na Mom ce.
*MOM POV*
Tana zaune har aka gama checking din result nata likitan ya dawo, da ido tabi shi har ya zauna yana mik’a mata tagardan gwajin ya ce. “ Hajjaju nayi iya bincike amma ban fahimci komai ba, na miki general check up amma Wallahi babu abunda yake damun ki.”
A hargitse ta ce. “ Taya zaka ce babu abunda yake damuna duk irin tsutsar da nake fitarwa ta gabana, duk nawan da kakeso ka fada zan biya dan asan me yake damuna.”
Murmushi likitan yayi kafin ya ce. “ Hajjaju sai dai ko zakije wani asibitin tunda ni na gagara.”
Wata tsaki ta buga tana daukar jakarta ta fice tana cewa. “ Aikin banza dama baka san komai ba.”
Wani asibitin ta nufa amma amsa daya aka bata cewa lafiyarta kalau, haka ta jera hospital kusan biyar amma duk sakamakon iri daya, daga nan ta nufo gida lokacin karfe bakwai na dare.
Tana saka kafarta a falon Dad dake zaune ya rufe hanci yana mikewa tsaye yana kallonta ya ce. “ Wai ke wani irin wari kike yi ne?.”
Shinshinar kanta tayi taji bakomai kafin ta dago kai ta ce. “ Nifah bana jin warin komai, sai dai ko hancin ka.”
Bai ce komai ba ya fice daga parlon yana komawa part nasa har lokacin ya rufe hancinsa.
Zama Mom tayi tana nazari a fili ta furta. “ Ko dai naje gurin boka ne gobe? Hmmm haka ma za’ayi goben zanje.”
*MUMMY POV*
Ko da suka gama waya da Fauziyya bacci ne ya d’auke ta mai dadi, tana farkawa Radiya ta shigo tana fadin. “ Mummy ashe Saif bai mutu ba, hatsari kawai sukayi, kuma Sageer ne yaji ciwo aka harbe shi.”
A zabure Mummy ta mike tare da cewa. “ Bai mutu ba?.”
Cike da murna Radiya ta ce. “ Eh Wallahi Mummy bai mutu ba, zo kiga hamdalan da nakeyi.”
“ A garin ya? Kenan basu kashe shi ba? Kudina kawai suka karba amma babu abunda suka min.” Ba tare da tasan maganar ya fito sai da taji Radiya na cewa. “ Mummy da sa hannunki a ciki ko?.”
Da sauri ta ce. “ A’a naji dazu kince ya mutu ne shiyasa abun ya bani mamaki.”
Murmushi Radiya tayi ta ce. “ Ok shikenan anjima zanje duba Matar tasa dan tunda tazo banje ba.”
“ Nima banje ba kinga sai muje tare.”
“ Ok Bye mummy.” Daga haka Radiya ta koma bangaren ta.
*SAFEERA POV*
Tun bayan da suka dawo daga asibiti bata sake saka shi a ido ba, a d’aki ya barta bai dawo ba gashi yanzu har kusan karbe tara na dare, a fili ta ce. “ Ko ina ya shiga?.”
Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi d’akinsa, duk da ranta a b’ace amma hakan bai saka taji batason sa ba.
Da sallama a bakinta ta shigo dakin nasa, yana kwance akan gado ya lumshe ido, kallo daya zaka masa ka gane cewa ba bacci yake ba.
Gurin gadon ta isa ta zauna a kan bedside tana cewa. “ Saif tun dazu baka sake duba ni ba.”
Bai kulata ba kuma bai nuna yaji ba, ta cigaba da cewa. “ Ina maka magana amma kayi banza dani.”
“ Ki tashi ki fita ina neman hutu.” Ya fada a sukwane.
Jinjina kai tayi kafin ta ce. “ Amma….” Bata k’arasa ba ya daka mata tsawa a fusace wanda yasa ta mike ba shiri tana nuna kanta da hannu ta ce. “ Ni Saif?.”
*Idona bacci haka na muku typing idan bakuyi comments ba babu abunda zanyi gobe tam🧏♀️*
09027308227
*Sahiba ce✍🏼*
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Comments section
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 24*
Jinjina kai tayi kafin ta ce. “ Amma….” Bata k’arasa ba ya daka mata tsawa a fusace wanda yasa ta mik’e ba shiri tana nuna kanta da hannu ta ce. “ Ni Saif?.”
Ba tare da ya ganta ba ya ce. “ Ke din.”
Kai ta gyad’a tana murmushin da yafi kuka ciwo ta juya ta fice da sauri daga d’akin tana buga k’ofan da k’arfi, d’aga ido yayi ya kalli kofar yana jan tsuki.
Ɗakinta ta shiga tana faɗawa kan gado ta saki kuka mai cin rai, kanta ta fara tambaya, shin na masa wani laifi ne? Idan ma fushin ne ni ya kamata nayi bashi ba, amma sai gashi shi yake yi ba tare da wani ƙwaƙaran hujja ba.
Kuka take yi sosai kamar wacce aka aikota yin kukan, ta dade tana kuka har sai da kanta ya fara ciwo kafin ta haƙura, baccin wahala yana dibarta.
*SAIF POV*
Bayan ta fita ne ya tashi daga kwancen da yake yana zama, shuru yayi yana kallon agogon dake manne a ɗakin wanda ke nuni da yanzu ƙarfe goman dare da rabi.
Sauƙowa yayi ya nufi toilet, minti kaɗan ya fito jikinsa na ɗigar ruwa alamun wanka yayi.
Wajen wardrobe nasa yaje ya ɗauko gajeran wanda da jallabiya fari ya zura, sallaya ya shimfiɗa yana tada sallah.
Bayan ya idar ne ya zauna yayi addu’oi sosai kafin ya hau kan gado ya kwanta, minti kadan bacci ya dauke shi.
~*Washe gari*~
Tana tashi tayi sallah tayi wanka, a gaban mirror ta tsaya tana kallon yanda fuskarta ya kumbura, idanunta sunyi ƙanana, kallo daya zaka mata ka gane tasha kuka ba laifi.
Sanin cewa bata da kaya ne yasa ta dauki jallabiyar da tasa jiya ta mai-maita, dan dama jiyan kaya zasu je siyowa aka tare su a hanya.
Gyara ɗakinta tayi tana fitowa waje, kallon kofar ɗakinsa tayi tana jin kamar ta shiga tana jin kamar kar ta shiga, wucewa tayi tana nufan kitchen ko zata samu abunda zata dafa.
Buɗe kofan da tasan nan ne kitchen tayi, taga komai akwai na kayan abinci, sai ta duba kofar da yake cikin kitchen din, nan kuma taga kayan abinci ne komai, fridge ta duba taga su kayan miya har da nama da kifi.
Shuru tayi tana tunanin me zata dafa, kunna gas tayi ta wanke tukunya tana mai daurawa, kafin ta saka ruwan.
Sauri-sauri tayi ta gama girka jullof din spaghetti wanda yasha kayan lambu da kifi, kamshi sai tashi yake, dauko wani warmers tayi ta zuba kafin ta had’a ruwan shayi ta zuba a flask, a daining ta ajiye ta koma kitchen ta gyara komai, kafin ta fito ta zauna ta fara cin abincin duk ranta a jagule.
A hankali ya fara fitowa daga ɗakinsa waya manne a kunnensa, yana sanye cikin shadda brown wanda yasha dinkin zamani, agogon hannunsa da takalminsa iri daya, gashin kansa sai yalki yake dan bai saka hula ba, ga kamshin turaren da yake tashi daga jikinsa.
D’aga ido tayi ta kalle shi na second’s kafin ta sauke tana lumshe ido, zuciyarta taji tana mata zafi wanda ta kasa gane na menene, ta sake d’ago ido ta zuba masa.
Wayan ya sauke daga kunnensa yana duba inda yake jin ana kallonsa, idanunsu ne ya sarke cikin na juna, kallo daya ya mata yasan tasha kuka duba da irin yanda idanunta suka kumbura.
Da sauri ta cire nata tana cigaba da tusa abincin a baki dan ba daɗi yake mata ba.
Cike da izza ya fara takowa zuwa inda take yaja kujeran da yake facing nata ya zauna, ajiye wayoyin hannunsa yayi ya harde hannu a kirji ya zuba mata ido.
“ Me ya sameki kikayi kuka har idanunki suka kumbura?.” Yayi maganar yana kallon abincin da ta zuba.
“ Babu.” Ta fada tana tashi ta zuba masa abincin da tea din, ta koma ta zauna ta cigaba da tusa nata da kyar.
Cokali ya dauka ya fara ci yana fadin. “ Ko dan na miki tsawa jiya shine kikayi kuka?.”
“ A’a ni banyi kuka ba.” Ta fada ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba.
“ Idan akan na miki tsawa ne, sorry I don’t means to hurt you.”
Murmushi tayi ta ɗago kai ta kalle shi tana cewa. “ Karka damu na saba da jin wannan tsawan tun ina shekara sha biyar, tsawar da tafi naka ma, idan kuka ne ko kumburan fuska da ido duk ba sabon abu bane a gurina, dan kuka ya daɗe da zama abokina.”
Tun da ta fara har ta gama yana kallonta, kafin ya ajiye cokalin hannunsa ya ce. “ Sorry dan Allah, idan raina ya ɓaci bana iya control din kaina.”
Tashi tsaye tayi ta ce. “ Amma a matsayina na matarka ai ya kamata kasan me zaka ce min.” Ta karashe tana nufan ɗakinta.
Dafe kai yayi ya furzar da iska, kafin ya tattare wayoyinsa ya fice daga gidan zuwa hospital dan duba jikin Sageer.
*BAFFA*
Tun daga farkon layin gidansa ya fara horn da ƙarfi har sai da ya isa gida.
Da gudu Inna ta fito daga bukkan nasu tana cewa. “ Waye haka?….” Ta fada tana zubawa motan ido.
Buɗe murfin motan Baffa yayi ya sauko yana fadin. “ Ni ne nan Innar Jannah, ai dama mahakurci mawadaci, Allah ya dubi zuciyata ya aikomin da mutumin kwarai ya bani mota da kud’ade masu yawa.”
Inna ta ce. “ Bangane ba?.”
Dariyar rainin hankali ya mata yana fadin. “ Bazaki taba ganewa ba har sai kinga an zabga miki kishiyoyi ukuuuu. Kinga na cika sunnah na Annabinmu.”
Jinjina kai Inna tayi tana fadin. “ Aure zaka k’ara kenan?.”
“ Kwaraiiii kuwa, aure mai daraja zan k’ara, mata tulukaki zan aura masu jiki, wad’anda za suyi ki biyu ko uku ma.”
“ Allah ya bada sa’a?.”
“ Amen idan da gaske kike, kuma duk wanda yaci tuwo dani miya yasha aradu.”
Cike da takaicin halin Baffa Inna ta ce. “ Dama shi ne ka mayar da yarinyar nan dan ka samu kudi da mota?.”
“ Hadda zuwa umura ma ke.”
“ Sanadiyar son abun duniyarka y’armu ta gudu daga gida, amma baka saduda ba.”
“ Wannan ke ta dama kuma.” Ya daura da cewa. “ Da alamu dai hassada akeyi da ni.”
Inna tayi murmushi ta ce. “ Ai bazan taɓa yiwa mutum hassada ba bare kuma kai, to me na ƙasa ya samu da zai bawa na sama?.”
“ Abunda na saman ya gagara samu.” Cewan Baffa cike da son jan magana, yana mai turo hulansa gaba.
Har Inna ta buɗe baki zata yi magana ta sauke ido akan Jannah wacce ke tsaye a bayan Baffa ta sunkuyar da kai.
“ Jannah!!!!!.” Inna ta kira sunanta da ƙarfi da mamaki cike da al-ajabi.
Ba shiri Baffa ya juyo yana ganinta, bakinsa na rawa ya furta. “ Fatalwa ta dawo.”
Kuka Jannah ta fashe da shi tasa gudu ta rungume Inna gamm.
Inna ma ta fara kuka tana kankameta kamar wacce akace zata gudu.
Ja baya Baffa yayi yana fadin. “ Lakamtu summa lakamtu! Lakamtu summa lakamtu, lakamtu summa lakamtu!.” Haka yake ta faɗa yana ja baya.
Sai da suka sha kukansu kafin Inna ta zare Jannah daga jikinta tana cewa. “ Me yasa za ki min haka Jannah ta? Idan ma zaki tafi da kin sanar dani mana?.”
Sosai take kukan tana jin ba dadi, ta ce. “ Inna ta!!! Kiyi hakuri.” Ta karashe tana sake fadawa jikinta.
Da kyar Inna ta samu Jannah tayi shuru kafin ta dubi Baffa wanda ya shige motarsa ya zauna ya masa key yana kallon su, dan shi bai yarda cewa Jannah ba ce ta dawo, gani yake fatalwa ce.
*Bayan wasu mintuna*
Baffa na gefen taburman yana faman hayya hayya, Jannah tana zaune a tsakiya da fura a gabanta, Inna ta ce. “ Jannah kisha furar mana?.
“ Inna bana jin zan iya cin komai ne.” Tana mai ture furar gefe.
Baffa ya ce. “ Ke!!!.” Ya kalli Inna, ya cigaba da cewa. “ Miƙomin ni zan sha, to kar tasha din mana damuwar wa? Da ta fita yawonta wa yasan me taci.”
Shuru tayi, dan tasan halin Mahaifin nata tun ba yau ba, dan ya fadi haka ba wani abun damuwa ba ce, kafin ta dubi motar Baffan ta kalli Inna ta ce. “ A ina Baffa ya samu kudi Inna?.”
Sakin baki Baffa yayi ya ce. “ Ke da kika fita yawon karuwanci ban tambayi ribar da kika samu ba, sai ni da na nemo halalina zaki tambaya? To a gidan uwarki na samo.”
Sunkuyar da kai tayi bata kuma cewa komai ba, Inna ta karbe zancen da cewa. “ Kai din ta wani halaliya ka samo? Ta fallasa da son duniya zaka ce.”
Tashi Baffa yayi yana karkade jiki ya ce. “ Oho dai, koma me mutum ya fad’a, ni kam nan gani nan bari umamen mayya, in da mayyarma kenan, idan kuma tayi dumamen; Sannan ku shirya kafin na dawo zamu bar gidan nan ba dan halinku ba.” Ya nuna Jannah da hannu ya ce. “ Ba ki tashi dawowa ba sai da kika ga nayi arziki, dan aci arzikin da ke ko? Ai duk makircinku ina sane.” Ya juya ya tafi abunsa babu wanda yayi magana.
Inna ta dafa kafadar Jannah ta ce. “ Karki saka damuwar komai a ranki.”
Gyada mata kai Jannah tayi.
Inna ta ce. “ Kin tambaya a ina Baffanki ya samu kudi ko?.”
Da sauri ta ce. “ Eh Inna.”
Numfashi Inna ta sauke ta ce. “ Wata daya baya wata yarinya Baffa ya tsinto, mun zauna da ita cikin annushuwa, dan yarinyar bata da damuwa, zakuyi sa’a ma. Jiya sai Baffanki yazo da mutane wai ana neman ta, kuma duk wanda ya samo ta za’a bashi kudi da gida da kaishi umura; shine fa Baffanki yayi yayi aka komar da ita aka bashi kudin da mota, duk da kuwa ranta bai so ba.”
Cikin sanyin jiki Jannah ta ce. “ Allah Sarki, har naji tausayinta Wallahi Allah yasa tana hannu me kyau, dan shi Baffa babu ruwansa da inda take idan za’a bashi kudi babu abunda bazai aikata ba.”
“ Hmm!! Amen Jannah, lamarin Baffanki kam sai shi, Allah Sarki Safeera baiwar Allah.”
A furgice Jannah ta ce. “ Safeera!!!.
*Idan ba’ayi comments da like dayawa ba zan huta irin yanda nayi kwanakin baya😒*
~*SAHIBA CE✍🏼*~
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Comments section
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 25*
“ Hmm!! Amen Jannah, lamarin Baffanki kam sai shi, Allah Sarki Safeera baiwar Allah.”
A furgice Jannah ta ce. “ Safeera!!!.”
Inna na faɗin. “ Ya naga kin furgita? Kin santa ne?.”
Jinjina kai Jannah ta fara. “ Eh nasan sunan dai.”
“ Ayya, dama sunan mutane yana zama daya ai, sai kiga kuma ba mutum daya bane.” Cewan Inna tana tashi ta shiga ciki.
Shuru Jannah tayi tana tafiya duniyar tunani, lokaci daya kuma hankalinta ya koma kan Safeera, tana son ta sake ganin ta ko sau daya ne, dan tabbas Safeera tasha wahala, wasu kwalla ne taji suna zubo mata, hannu tasa ta goge a fili ta ce. “ Allah yasa kina cikin farin ciki Safeera.”
*SAFEERA POV*
Tun bayan da ta shiga ɗaki, wani wahalallan bacci ya ɗauke ta, dan jiyan ba wani bacci tayi ba kuka kawai tayi.
Ba ita ta farka ba sai guraren ƙarfe goma da minti ashirin da uku na safe, a hankali ta soma buɗe manyan idanunta waɗan da suka gaji da bacci tana sauƙewa akan shi.
Da sauri ta janyo bargo ta rufe jikinta dan daga kan cibiyarta har ƙasa ba kaya, ta kafe shi da ido. “ Me ya kawo ka ɗakina?.” Ta mayar da ido kan akwatinan da suke jere guda sha biyu, ta juyo ta ce. “ Aure zaka ƙara ne?.”
Dariyar da bai shirya ba yayi ya zauna kusa da ita yana rike hannunta ya fara murzawa. “ Ai ko auren zanyi ke zan sake aura.”
Kallon tuhuma take bin shi dashi. “ Naga akwati har sha biyu, sannan kace wani wai ba aure zaka yi ba?.”
Nan ma murmushi yayi. “ Kayan lefenki ne, na saka an haɗa maki duk abunda ake buk’ata tun jiya, shine yau naje na ɗauko, amma ba aure zan ƙara ba.”
Sauƙowa tayi daga kan gadon ta cire hannunta daga nashi ta isa gurin akwatin, ƙare musu kallo tayi kafin taja na duk ta buɗe, mamaki ne ya kamata lokacin da taga tilin Abaya, ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce. “ Kuma nawa ni kaɗai?.”
Jinjina mata kai yayi yana murmushi, ya harɗe hannu a kirji yana kallon yanda zallan murna ya cika ta.
Wani ash ta ɗaga ta ce. “ Yaya Saif wannan zai yiwa Jannah kyau Wallahi.”
Dan murmusawa yayi ya ce. “ Nikam ko zamu je gurin Jannah din kin nan ne?.”
Da sauri ta juyo ta ce. “ Eh Wallahi.”
Murmushi yayi ya ce. “ Amma da alkawari?.”
Tasowa tayi ta koma wurin sa ta zauna dab dashi ta ce. “ Inaji Yaya.”
Murmushi yayi yana kallon lips nata kafin ya ce. “ 2 rounds.”
Turo baki tayi gaba tana ta fara kunkuni, tabe baki yayi yana k’ok’arin tashi tsaye, da sauri ta rike hannunsa ta shagwabe fuska ta ce. “ To naji amma sai mun je.”
Dan sosa kai yayi ya ce. “ To yanzu tashi kiyi wanka ki shirya, muje gurin Ummah ki gaishe ta sai muje.”
Bai ƙara faɗa ba ta wuce toilet tana dariya. “ Yanzu zaka ga na gama.”
“ Bari nazo na tayaki mana.”
Da sauri ta rufe toilet din tana dariya ta ciki, shima murmushi yayi ya dawo ya zauna yana tunanin kadde Jannan da yake tunani ne.
Yana zaune a wurin har ta fito, yana kallonta yanda ta cika tayi haske, amma wuyanta ya dan faɗa alamun akwai damuwa, gaban dressing mirror taje ta shafa mai ta shafa turarukan da ta gani, kafin ta je ta ciro wata shadda ash dinkin doguwar riga bubu, wanda yasha ruwan stones, ta ciro bra da pant da underwear.
Ta juya ta saci kallon shi taga ba ita yake kallo ba, da sauri ta saka kayan.
Murmushin gefen baki yayi dan duk abunda take yana kallon ta kawai yayi shuru ne yana tunani.
Gabansa ta iso ta miƙa masa dankwalin ta turo baki, bin ɗankwalin yayi da kallo yana karba ya ce. “ Me zanyi Wife?.”
“ Ɗaura min zaka yi.”
Sake baki yayi yana bin dankwalin da kallo, kafin ya ce. “ Wife ina na iya ɗaurawa?.”
Haɗe fuska tayi tana shirin fara kukan shagwaba ta fara bubbuga ƙafa. “ Ni kai zaka daura min ko na fasa.”
Ji yayi jinin jikinsa ya fara charkewa, yaji wani zirr tun daga saman kansa zuwa babban yatsarsa, saurin saita nutsuwarsa yayi. “ Shikenan zan ɗaura miki.”
Zama tayi akan cinyarsa tana sakalo hannunta ta wuyansa, ya zuba mata ido yana mamakin yanda yau ta koma wata karamar yarinya.
Cinno baki gaba tayi ganin ya zuba mata ido bai ɗaura ba, kafin tayi magana yayi saurin fara daura mata, sai ya jawo ta nan sai ya komar ta nan haka yata fama har ya gaji, ita kuma taki tayi magana sai dariya take masa.
Numfashi ya sauke ya ce. “ Madam na kasa fa.”
Dariya tayi tana karban dankwalin ta mike tsaye, jawo kujeran gaban mirror tayi ta zauna, fara daurawa tayi yana kallon ta har ta gama.
Ya zuba mata ido ya ce. “ Amma kinyi kyau.”
Dariya ta masa tana cewa. “ Next time kai zaka ɗaura min.”
Farin gyale ta ɗauko ta yafa ta saka flat shoe ta tsaya a gabansa ta masa sigina.
Shafa gemunsa yayi ya mike suka fito hannunsa sarke cikin nata har part din Ummah.
Da sallama suka shigo, Asabe dake goge tv stand ta amsa tana kallon Safeera, itama ita take kallo tana mamakin yanda kullum idan ta shigo take kallon ta, Saif ya lura da kallon ya daka mata tsawa. “ Uban me kike kallon ta haka? Cinye ta zakiyi ne?.”
Girgiza kai tayi. “ Ayi hakuri Yallabai.”
Wani tsawan ya daka mata wanda yasa ta tashi ba shiri ta fita, ya dubi Safeera wacce jikinta yayi sanyi ya ce. “ Wifely kin santa ne?.”
“ A’a.” Ta fada a takaice tana kallon hanyar da Asabe tabi.
Muryan Ummah suka ji tana faɗin. “ Lafiya Saifullahi kake wannan tsawan?.” Ta zauna a gujera mai zaman mutum biyu.
Har ƙasa Safeera ta ɗurkusa ta ce. “ Ummah ina kwana? An tashi lafiya?.”
“ Lafiya Alhamdulillah Amarya gajiya?.” Cewan Ummah cikin sakin fuska.
Murmushi kawai tayi tana mikewa, isa sukayi suka zauna a gujera mai zaman mutum uku Saifullahi na cewa. “ Ummah wannan yar aikin naki nake tunanin ta kusa tafiya.”
“ Me ta maka kuma?.”
“ Idan ta fara kallo kamar mayya, ko gifta ido fa bata yi sai kace mayya anya ma Ummah ba mayya ba ce.” Yayi maganar iya gaskiyarsa dan shi bai yarda da ita ba.
Ummah ta danyi shuru kafin ta ce. “ Ba kyau zargi fa Saif.”
“ A’a Ummah Nifah da gaske nake.”
“ Ai shikenan kuma amma bazaka kora min yar aiki ba, ita ce mai dibe min kewa kusan shekaru goma da baka kulani.”
Shuru yayi bai kuma yin magana ba, Safeera ta saci kallon shi taga yanayinsa ya sauya, cikin ranta ta furta. ‘ Shi kuma ko wani dalili yasa har shekaru goma baya kula mahaifiyarsa?.’ Sanin babu mai bata amsa ne yasa tayi shuru ta zuba musu ido.
Katsai shurun Saif yayi ta hanyar cewa. “ Ummah mu zamu wuce sai anjima.”
Ummah ta dubi Safeera ta ce. “ Daughter sai anjima ko, za kizo tayani hira ai ko?.”
Murmushi tayi tana gyada kai, kafin suka fita daga falon.
A compound din ya tsaya yana kallon wanda zai tuk’asa, kafin ya nuna Jon da hannu, da sauri Jon ya dauko mota, isa gurin suka yi ya bude mata baya ta shiga ya zagaya ya shiga, kafin suka fice daga gidan.
Suna tafiya ya ce. “ Wifely!.”
Ta juyo ta ganshi tana furta. “ Na’am.”
“ Tunanin me kike yi haka?.” Ya zuba mata ido.
Dan murmusawa tayi tana cewa. “ Tunanin komai.”
“ Kamar me kenan?.”
“ Ina tunanin ranar da zakazo kace ka rabu dani ne.” Yaji maganar kamar saukar aradu, ba shiri ya ce. “ Wani irin banzan tunani ne haka? Bazan taba barinki ba har abada.” Ya rike hannunta.
Bin hannun tayi da ido kafin ta kalle shi. “ Hmm, Allah ya sa.”
“
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 17