abun ciki ba? To idan banso duniyar ba lahira zan so ne Innawuro.β
*SAHIBA CE*βπΌ
π*BAΖAR ΖAUNA*π
*Na*
*FATIMA ISA MANUπ¦*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )βπΌπ¦_
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
Masu neman littafin *BAΖAR ΖAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel Ιi na dan samuπhttps://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
πͺ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*πͺ βοΈ
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Ζasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauΖi_.βοΈ*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*TWO DIAMOND STAR LADIESπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈ*
*(We stand together)*
π€π€π€
*GARGAΖI*
Wannan littafin Ζagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ππ«*
*Page 29*
Inna taja tsuki ta ce. β Kai da son abun duniya kam bansan ya zaβayi ba.β
β Ina cikin duniyar kuma bazan so abun ciki ba? To idan banso duniyar ba lahira zan so ne Innawuro? Nifa makircin nan naki ne bana so.β Ya maida duban shi ga Jannah yana fadβin.
β Ko ki so ko karki so aure da Alhaji kam an gama.β
Kuka Jannah ta saka tunawa da irin wulakanci da Saif ya mata, Baffa yaja tsuki yana cewa. β Arziki ne bakya so naci, kuma sai naci sai dai ki dafa kanki ki soya.β
Inna ta janyo Jannah jiki tana rarrashin ta, Baffa ya kadβa rigarsa ya fice daga gidan yana sababi kan cewa sai anyi auren.
Inna tana rarrashin ta ce. β Jannah ina ce shine saurayinki, to meyasa yanzu bakya son shi? Ko ya miki wani abu ne?.β
Tsit kake ji tayi shuru, zuciyarta ya soma bugawa uku uku, Inna bata san komai ba game da abunda ya faru a tsakanin su.
Jin tayi shuru ne yasa Inna sake cewa. β Jannah kinyi shuru?.β
β Inna kawai bana son shi ne, Inna na tsane shi tsana mafi muni a rayuwa, Inna ni da shi bazamu iya zama inuwa daya ba.β Ta sake sakin kuka.
*MOM*~~~~~~~~~~~~
Wunin ranar a daki tayi ta gagara fita ko falo, saboda irin warin da gabanta ke yi, taje tayi gwaji amma duk amsa daya cewa wai lafiyarta kalau.
Maganar da Ashiru ya fada mata ta tuna. < Hajjaju ya kamata dai kije asibiti a duba lafiyarki>, shuru tayi a fili ta ce. β Taya yasan bani da lafiya?.β
Wani zuciyar ya ce. β Taya bazai sani ba kina karuwarsa.β Wayanta ta lalubo ta danna masa kira, bai gama ringing na farko ba ya dauka, ya soma magana a fada ce.
β Makira, ashe cuta gare ki ban sani ba kika shafa min, yar kutumar uba ni kika shafawa cutar kanjamo, to billahil lazi sai na rama kuma ki jira zuwa na gidanki.β
Tsabar firgice har gagara magana tayi, da kyar ta hado kalmomi tana cewa. β Me kake nufi Ashiru?.β
β Zaki san abunda nake nufi idan nazo gidan naki.β
Da sauri Mom ta ce. β Aβa ka rufamin asiri inason zama a gidan mijina.β
Dariyar rainin hankali ya mata yana cewa. β Ni na rufa miki naki ke ki tona min nawa? Ai baki isa ba Wallahi har shi sai na fadawa kuma ki duba WhatsApp naki na tura miki abu.β Daga haka ya kashe wayan.
Hannunta na rawa ta duba WhatsApp nata, ba shiri ta mike tana daura hannu a kai. β Na mutu na lalace.β Sassarfa ta soma yi a dakin.
Number shi ta dannawa kira yana dauka ta fashe da kuka. β Ka yiwa Allah ka yiwa Annabi kayi hakuri, na tuba karka tonamin asiriβ¦β
Ya katsai ta yana cewa. β Oh dama kinsan Allah da Annabi kenan kuma kike zuwa gurina muke aikata alfasha?.β
β Na tuba, dan Allah ka goge.β
Ya kwashe da dariya yana cewa. β Sai kin biya makudan kudade masu lasisis.β
Hawayen fuskarta da majinan ta goge ta ce. β Shikenan nawa kakeso?.β
β Hahaha!!! Da dollar π΅ zaki biya.β
β Eh naji nawa?.β
β Uhmm ki kawo ko 5,000 USD dollars ma is ok.β
A razane ta ce. β Har 5,000 USD dollars Ashiru, da ni dashi wa ya ajiye wani?.β
β Owk kar ki kawo ki jira sakamako.β Ya fada yana shirin kashe wayan.
Da sauri ta ce. β Shikenan zan kawo amma dan Allah ka goge.β
β Yaushe zaki tura?.β
β Idan na samu.β
Tsuki yaja yana cewa. β Baki shirya bane, kawai ki jira.β Ya kashe wayan.
Ihu ta saka tana daura hannu a kai ta cigaba da kuka, tana cikin kukan ne message ya shigo mata, tana dubawa taga Ashiru ne ya turo mata Acc number a kβasan ya rubuta *Ki sakamin kafin nan da kwana uku dan ba haka ba social media zasu sha kallo*. Tana gama karantawa ta fashe da kuka.
Ita ciwon da yake magana ta shafa masa ma bai dameta kamar yanda videos din nan suka dame ta ba.
Yanzu ma tukun a ina zata samu 5,000 USD wanda yanzu a Nigeria 7,162,667.34 NG.
*SAIFULLAHI*
Sun je sun duba Sageer wanda yanzu ya dan fara samun sauki, kafin suka nufi hanyar gidan su Jannah.
Ammar ya ce. β Amma Saif matarkan nan kamar akwai matsala fa, ka dubi yanda tayi shuru take bin kowa da ido, anya harbin da aka tayi ranar bai taba mata kwakwalwa ba.β
Ya dubi Safeeran da tayi shuru tana kallon titi, kafin ya komar da hankalinsa kan Ammar yana cewa. β To dai ina ga idan na gama da lamarin Jannah sai na dawo nata.β
β Ya kamata dai ka gama da na matarka kafin ka koma na budurwa.β
β Aβa sai na gama dana Jannah.β
Ammar bai kuma cewa wani abu ba, amma maganar bai masa dadi ba sam, sai dai bayi da ta cewa.
Idanunta ne suka sauka akan shi yana tsaye a gefen motansa yana murmushi, ta zuba masa ido tana fadin. β Shi ne.β
Saif ya dube ta da mamaki ya ce. β Waye?.β
Ta nuna masa inda yake tsaye da hannu tana fadin. β Gashi can.β
Tsayawa Jon yayi Ammar yayi saurin fitowa shi da Saif, sai dai basu ga komai ba, ta sauko tana kallon inda motar nasa yabi tana murmushi tana masa bye bye.
Saif ya ce. β Ka gani ba, na fada maka ta zare amma baka yarda ba, dubi fa motar da take yiwa bye bye.β
Ammar yabi inda Safeeran take kallo yaga motar tana shan kwana, kafin ya dubi Safeeran cikin ido yana cewa. β Kinsan shi ne?.β
Gyada masa kai tayi tana murmushi, har yanzu idanunta na kan hanyar da yabi, Ammar ya kuma cewa. β Waye ne?.β
Shuru tayi ta fada tunani tana dan lumshe ido, kanta taji yana sara mata da sauri ta kama kan tana kama rigar Ammar dan shine kusa da ita, Saif ya bisu da kallo yana fadin. β Kanta din ko?.β Yayi saurin riketa, ta yanda Ammar bazai fahimci kishi ne yake damunsa ba ya janyeta daga jikinsa.
Ammar ya bude motan yana dauko ruwa a gora ya bawa Saif dan ya bata tasha, ya bude murfin ya kafa mata a baki, sai da tasha rabi kafin ya sauke yana cewa. β Safeera.β
Ammar ya ce. β Ku shiga mu bar nan gurin kasan ba security kar wani abu ya faru.β Da haka ya bude musu suka shiga.
Shuru babu wanda yayi magana a motan, can Ammar ya ce. β Amma Saif sai nake ganin kamar aje hospital dai.β
β Nima yanzu hankalina yafi tafiya can, dan gaskiya na fara tsorata da lamarin ta, kamar wata cyco.β Ya fada yana kallon Safeera wacce har yanzu idanunta a lumshe.
Ammar ya ce. β Ato dai.β
Jon ya tambayi Ogan nasa. β Sir hospital din zamuje ko Bulunkutu?.β
Ammar ya karbe da cewa. β Hospital.β
Saif kuma ya ce. β Bulunkutu.β
β Saif zaka yi adalci kuwa, matarka ba lafiya amma zaka wuce gurin budurwa.β
Hannu ya daga masa alaman ya isa, daga haka babu wanda ya sake cewa komai har suka isa gidan su Jannah.
Suna isowa Baffa yana zuwa, Ammar yayi murmushi ya ce. β Baffa manya tun da aka samu mota aka hanamu sakat.β
Saif yayi murmushi yana cewa. β Sirikin nawa kake fadawa haka?.β
β Ohh haka fa, kaina kβasa.β Suka sauko daga motan, ya dagawa Safeera glass ya kunna mata AC, ta kafa fuskarta a jikin glass din tana kallon su.
Baffa ya iso da wuri yana cewa. β Alhaji Allah yaja kwana, kaga mutumin kirki.β
Saif ya dan sunkuya yana cewa. β Ina wuni Baffa.β
β Ahh lafiya kalau ya gajiyan ku?.β
β Alhamdulillah.β
β Ku shigo mana.β
Baffa yayi gaba Saif ya mara masa baya, Ammar ya juyo ya kalli Safeera yanda tayi, tausayinta ya kama shi a ranshi ya ce. β Allah zai kawo miki mafita In Sha Allah, amma bakiyi saβan miji ba.β Da haka ya wuce ciki.
Suna shigowa Jannah ta mike da sauri zata shiga ciki, Baffa ya daka mata tsawa da maganar da yasa ta tsaya. β Idan kika sake taku daya sai na tsine miki.β
Dole tasa ta juyo ta koma ta zauna, Saif ya bita da kallo yana murmushi, ya durkusa ya gaishe da Inna, ta amsa masa ba yabo ba fallasa.
Baffa ya ma Inna magana ta yare nan ta tashi ta kawo musu fura da ruwa, ya amsa yana godiya, suka dan yi hira kadan kafin ya tashi zai tafi ya ajiye musu kudi, ya fito Ammar na mara masa baya.
Ganin sun fita ne ya saka Baffa dauke kudin da wuri ya saka a aljuhu yana cewa. β Yar kwal uba tashi kije ki same shi.β
Kamar tayi kuka ta dauki hijabinta ta fito.
Yana tsaye ta iso tana hararan shi, yayi murmushi yana cewa. β Amarya ba kya laifi.β
β Allah ya kiyaye.β Ta karashe fadan tana sauke ido akan Safeera wacce ta manna fuskarta da glass dib tana kallon duk abunda yake faruwa.
Da sauri ta isa gurin motar tana kallon ta, Jannah ta ce. β Safeera.β
Murmushi ta mata hawaye na saukowa daga idanunta, Jannah ta girgiza mata kai tana fadin. β Me ya faru Safeera? Ni dama nasan ba lafiya ba, nasan akwai abunda ya same ki.β
Duk kallon su kawai suke, abun ya daurewa Ammar kai sosai, Saif kuma ya zuba musu ido yana mamakin irin kauanr da yake tsakanin su, dan ita ma Safeeran kullum zancen ta Jannah amma kwana biyun nan ta daina ko magana, daga bacci sai murmushi.
Ammar yazo ya budβe mata murfin motan ya koma gefe.
Da sauri ta rungume ta tana kuka. β Safeera ko ya cutar da ke ne? Ko ya miki wani abu ne? Dan Allah kiyi magana.β
Kai kawai ta girgiza ta ce. β Babu kowa.β
Ta tallafo fuskarta ta ce. β Ki ga ki fadamin komai kinji, Jannah dinki ne fa.β
Lumshe ido tayi tana tuna sunan, a hankali ta furta. β Jannah.β Tana kama kanta da karfi.
*SAHIBA CE*βπΌ
π*BAΖAR ΖAUNA*π
*Na*
*FATIMA ISA MANUπ¦*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )βπΌπ¦_
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
Masu neman littafin *BAΖAR ΖAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel Ιi na dan samuπhttps://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
πͺ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*πͺ βοΈ
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Ζasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauΖi_.βοΈ*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*TWO DIAMOND STAR LADIESπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈ*
*(We stand together)*
π€π€π€
*GARGAΖI*
Wannan littafin Ζagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ππ«*
*Page 30*
*END OF BOOK ONE*
Lumshe ido tayi tana tuna sunan, a hankali ta furta. β Jannah.β Tana kama kanta da Ζarfi wanda taji kamar zai tsage.
Jannah ta rike ta tana fadβin. β Safeera, ko dai kin manta ni ne?.β
Ta dago kanta ta kalleta ta ce. β Na manta inda nake jin sunan ne.β
Da mamaki Jannah ta ce. β Ko dai tayi loosing din memory ni?.β Ta tambayi Saif shi da Ammar.
Ammar ya nuna Saif da hannu alamun ta tambaye shi, Saif ya ce. β Aβa ban dai sani ba, coz kwana biyun nan ta ke nake.β
Cike da haushi ta ce. β Ita kuma ta mutu ko, ba da ni zaβayi wannan jagaliyancin ba, ka fara samo lafiyar Safeera sannan ka samo hankalina.β
Safeera dai kallon su take wai ita ce bata da lafiya, bayan kuma duk abunda suke fada tana ji.
β Jannah ki koma ciki abun ki zamu sake dawowa.β Cewan Ammar yana zagayawa ya shiga motan, Saif zaiyi magana Jannah tayi saurin shiga ciki.
Iska ya fuzzar yana bude motan ya shiga, Jon ma ya shiga suka tafi.
Sai da aka sauke Ammar kafin suka wuce gida.
*MOM POV*
Idan ana zancen dan iska na bugawa a jarida to Ashiru ya kai, ya hana Mom sakat, duk bayan awa daya sai ya turo mata da videos yana mata barazana.
Tuni Mom ta zabge ta rame ta fita hankalinta, ta rasa ya zatayi da rayuwarta, kukan ma tayi har ta gaji, ta rasa mafita ta koβina.
Tana zaune a tsakiyar dakin taji an bude kofa, a razane ta juya suna hada ido da Radiya.
Toshe hanci Radiya tayi tana fadin. β Mom lafiya baki fito ba tun jiya?.β
β Radiya kije kawai, nima yanzu ta kaina nake.β Ta kalli yanda ta rufe hanci tana fadin. β Kema kina jin warin ko?.β
Ta gyada kai ta juya ta fice dan amai ne ya taso mata.
Mom ta wani fashe da kuka tana ihu, message ne ya shigo mata, taji zuciyarta ya tsinke dan tasan waye ne, hannunta na rawa ta dauki wayan tana kallo. ββ Saura kwana daya fa Hajjaju.ββ
β Na shiga uku na lalace, na lalace na lalace, wayyo Allah na.β Ta sake fashewa da kuka, number bokanta ta kira, yana dauka ta fashe masa da kuka tana fadin. β Boka komai ya lalace.β
Ta cikin wayan aka ce. β Mai wayan yana kwance ba lafiya an saka masa drip.β
β Kutumar jarr ubaβ¦ Allah ya isa tsakanina da kai.β
Ta cikin wayan aka ce. β Ke malama ba fa me wayan bane.β Ya kashe abun shi.
Tabi wayan da kallo tana fadin. β Ta faru ta kβare, ya cuceni ya kashe ni.β Ta fashe da kuka tana tashi tsaye ta daura hannu a kai.
*MUMMY*
Radiya ce ta shigo da hanzari, tun daga falon ta soma kiran Mummy tana cewa. β Mummy! Mummy!!.β Mommy da take daki ta fito da sauri tana cewa. β Radiya uban me ya faru ne, kin san halin da nake ciki kuwa da kike kirana.β
β Mummy halin da kike ciki kadan ne akan na Mom.β Cewan Radiya tana kama kwankwaso.
Mummy ta matso tana fadin. β Me ya faru da ita?.β
β Hmm! Kinsan warin da take yi kuwa, kamar bugaggen nama.β
β Hahaha π€£, Allah shi kara, tabi bokan nata ya zuba mata cuta kenan.β
β Mummy nikam naji tausayin ta ne.β
Tsuki taja tana cewa. β Nata da sauki ai tunda wari kawai take yi.β
Cike da son jin gulma Radiya ta ce. β Mummy ke kuma me ya faru?.β
Shuru Mummy tayi kafin ta ce. β Wanda na tura ya kashe Saif ne aka kama daya daga cikin su, to yanzu yana so ya tona min asiri ne.β
Radiya tsoro fal ranta ta ce. β Mummy turawa kika yi a kashe shi? Kenan dama ke ce kika tura a kashe shi baβa same shi ba aka samu Sageer.β
β Bana son munafurci Radiya, daga fada miki zance dan ki tayani jaje shine zaki min halin naki ko.β
β Anuty Mummy kenan, ai to Wallahi kadan kuka gani duk taku biyun, yaron da bai tare muku komai ba amma kuna neman rayuwarsa, kin hana matarsa ma sukuni, ku jira sakayya.β
β Zo ki bar min gidana dan ubanki Radiya, har ni zaki na fadawa duk maganar da yazo bakinki, ba albarkaci na kuke ci ba.β
β Gida kam zan tafi tun da ba na ubana bane, kuma nikam ba ke kike ciyar da ni ba.β Ta karashe tana murguda baki ta wuce daki dan hada kayanta.
Zama Mummy tayi a kan two seater tana yin tagumi. β Abu duk yana neman dagule min, na rasa ina ne mafita, gashi Fauziyya yau kusan sati bata amsa kirana.β
*BAFFA*
Yau ma kamar kullum suna tsakiyar gida suna faman masifar su.
Surutu suka ji daga waje alamu fada ake, Baffa yaga Inna, Inna taga Baffa.
Kafin ya ce. β Ki je ki duba waye ne?.β
β Kana namiji ina mace, kuma kace naje na duba maka.β
Tsuki Baffa yaja ya tashi yana baza babban riga yayo waje.
Fitan shi ke da wuya suka ji muryansa daga waje yana fadin. β Dan Allah kayi hakuri ku min raiβ¦
*SAHIBA CEβπΌ*
π*BAΖAR ΖAUNA*π
*Na*
*FATIMA ISA MANUπ¦*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )βπΌπ¦_
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
Masu neman littafin *BAΖAR ΖAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel Ιi na dan samuπ https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
πͺ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*πͺ βοΈ
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Ζasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauΖi_.βοΈ*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*TWO DIAMOND STAR LADIESπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈ*
*(We stand together)*
π€π€π€
*GARGAΖI*
Wannan littafin Ζagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ππ«*
*Page 31*
*BOOK TWO*
Fitan shi ke da wuya suka ji muryansa daga waje yana faΙin. β Dan Allah kuyi hakuri ku min rai.β
Inna ta dafe kirji tana faΙin. β Mun shiga uku.β
Da gudu suka yo waje ita da Jannah.
Gardawa sun zagaye Baffa a tsakiya, wani tuluki daga gefe yana sanye da blue din shadda, gajere kallo daya zaka masa ka hango munin shi, ya ce. β Ko ka biyani kudina ko na sa a kashe ka kuma na auri diyar taka tun da dai matata ce, dan na biya sadaki.β
Jannah ta ware ido, wace diyar tasa kenan?, dan ita a iya saninta Baffa ita kadai ya haifa.
Inna ta ce. β Malam me ya maka kake cewa zaka kashe shi dan Allah?.β
β Da ke ai naga aka ci kudin, dan haka ko ku biyani kudina ko na saka a miki dan banzar duka.β
Baffa da yake hada zufa ya ce. β Alhaji kamin rai, kudinka zan sa a biya maka nan da anjima.β
β A gidan uban wa zaka samu ka biyani, Gunda ku masa dan banzar duka.β
Duka suka shiga kai masa, Inna na kuka Jannah na kuka, suna bashi hakuri amma yaki hakura, Jannah ta durkusa a gaban shi tana fadin. β Dan Allah ka bar shi zan baka kudin ka.β
Ya kare mata kallo yana cewa. β Ke!!! Da gashin kanki zaki biyani?.β
Ta dubi yanda Baffa ke ihu Inna ma ke kuka, ta juyo da sauri tana cigaba da cewa. β Nawa ne kudin zan baka na rantse.β
Kallon baki da hankali ya mata kafin ya ce. β Million uku yaci a hannuna dan zai auramin diyarsa, kuma yaki.β
β Million Uku!!!.β Jannah ta fada a ranta kafin a fili ta ce. β To zan biya amma dan Allah ku barshi dukan ya isa.β
β Yaushe zan zo na karba to?.β
Shuru tayi kafin ta ce. β Gobe da safe.β
Jinjina kai yayi, ya daga hannu yana cewa. β Ku barshi ku zo mu tafi, gobe da safe zamu dawo mu karbi kudinmu, idan kuma bata bada ba ku yanka shi.β
Su ka dakata da dukan suna bin bayan Alhajin.
Inna ta isa da sauri tana rike Baffa ita da Jannah, idanun Baffa sunyi tsulu tsulu tsabar azaba, fuskarsa ya sha duka, ta kafarsa kam har da dan fashewa, Inna ta goge hawayen fuskarta ta ce. β Yanzu dan Allah me haka kayi.β
Ya kalle ta yana magana a hankali. β Ku shigar dani ku dafamin jikina.β
Inna ta ce. β Jannah rike shi mu shigar da shi.β Da kyar suka iya kai shi kan taburma, duk nishi suke.
Jannah ta ce. β Haba Baffa, tunda kana da kudin ka kawo a bashi kawai.β
Murya irin na wadβanda suka daku ya ce. β Ko kashe ni zaiyi sai dai su kashe ni.. amma kudina.. ba.. zan.. bada ba.. Allah ma ya rufa asiri bai san motan nawa bane, da fasawa za suyi, masu hassada sun cika gari ta koβina.β
Inna tayi murmushin takaici ta ce. β Kudinsu fa kaci, kuma ni bansan yaushe kaci har million uku ba Wallahi.β
β Ina zaki sani tunda ban kashe miki ba.β Ya fada yana cije baki ya daga hannu da kyar, Jannah ta ce. β Sannu Baffa.β
β Babu wani sannun da zaki min, ke ne kika jawo, da kin auri Alhaji Saifullah ai da yanzu ba zancen ake ba.β
Jannah ta sunkuyar da kai tana fadin. β Baffa ni fa ba son shi nake ba, kuma bazan iya auren shi ba.β
Pillow da ya daura hannunsa a kai ya buga mata yana fadin. β Sai goben idan sun dawo su kashe ni, amma kudina kam bazasu yi ciwon kai ba, ke kuma.β Ya nuna Inna, yana cigaba da cewa. β Ko na mutu a binne ni da kudina.β
Ya kalli Jannah ya ce. β Idan Alhajin yazo sai karki yarda ki aure shi, kin ga idan na mutu alhakina a kan ki, yar kusun uwa.β Ya karashe yana taba goshinsa da ya kumbura tim.
*SAFEERA POV*
Tana zaune a falo ta dukunkule a kan kujera tayi shuru, Saif ya fito daga dakinsa sanye da kayan barrister zai tafi aiki, ta daga kai ta kalle shi tana saukewa.
Ya iso gurinta yana cewa. β Sweet pie zo muje ko.β
Girgiza kai tayi tana cewa. β Aβa zanyi bacci ni.β
Ya zuba mata ido yana karantar yanayin ta, kafin ya tashi ya sumbace ta a goshi ya ce. β A mana adduβa zamu shiga.β
Bata kulasa ba ta kwanta akan kujeran tana lumshe ido, ya dade yana tsaye kafin ya sauke numfashi ya fita, ta baya ya rufe kofar ya tafi da key din.
Bacci tayi sosai har na awa uku, kafin ta farka duk jikinta zufa, tana kallon cikin falon a razane, a hankali ta ce. β Mama.β
Sai ga hawaye zurr sun zubo kamar an bude famfo, kuka ta fara tana tunawa da yan uwanta. β Ko ina suke? Ko sun ci abinci ko basu ci ba babu wanda ya sani? Allah sarki Raudah ina ga ni na cuce ki.β
Nan taji kanta ya sara kamar zai fashe, da sauri ta damke kan tana lumshe ido, kusan mintuna biyar tana haka, kafin ta budβe idon tana tashi ta nufi hanyar fita a falon.
Tana kβokβarin budβe kβofan ta ga an turo kofar, suka tsaya suna kallon juna, sun dade kafin ya ce. β Ina zaki je?.β
β Wajen Raudah.β
Yayi shuru yana kallon ta dan shi ya manta ma wacece Raudah din, sai da ya tuna labarin ta kafin ya tuna wacece, amma ai bata san inda take ba.
β Kin san inda take ne?.β
Ta masa kallon Up and down tana bi ta gefe zata wuce, ya toshe hanyar yana cewa. β Ina zuwa?.β
Cikin daga murya ta ce. β Dalla Malam ka matsamin zan wuce, ka wani toshe min hanya.β
β Yau din kuma?.β Ya fada da mamaki, dan shi yanzu ya rasa yanayin Safeera din, kafin ya ce. β Ina zakije idan kika fitan?.β
Shuru tayi kamar tana tuna abu, ta dan nutsu a hankali tana tuna rayuwarta na baya, ta dafe kai da sauri ta furta. β Wayyo kaina.β
Da sauri ya sake jakar hannunsa yana riketa, ya ce. β Safeera!!!
*SAHIBA CEβπΌ*
*BAΖAR ΖAUNA*
*Na*
*FATIMA ISA MANUπ¦*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )βπΌπ¦_
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
Masu neman littafin *BAΖAR ΖAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel Ιi na dan samuπ https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
πͺ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*πͺ βοΈ
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan Ζasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauΖi_.βοΈ*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*TWO DIAMOND STAR LADIESπ§ββοΈπ§ββοΈπ§ββοΈ*
*(We stand together)*
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 17