Amen.” Ya sumbaci hannun yana cigaba da murzawa.
Mayar da hankalinta tayi kan titin tana kallon yanda mutane suke bara da kuma yanda suke talla, tayi murmushi a ranta ta ce. ‘ Komai lokaci ne, tabbas akwai kaddara a rayuwa dan nikam na gani.’
Idanunta ne suka sauƙa akan wani namiji yana tsaye a gefen titin yana masifa, ta sake zuba masa ido tana kallon shi tana k’ok’arin tunawa da inda taga fuskar, nan da nan kuwa ta tuna da sauri ta damke Saif ba shiri tana nuna hanyar da hannu ta furta. “ Shi neeeee!..”
*Kuna min uzuri exams nake, zaku na samun posting jifa jifa ne*
*SAHIBA CE✍🏼*
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 26*
Idanunta ne suka sauƙa akan wani namiji yana tsaye a gefen titin yana masifa, ta sake zuba masa ido tana kallon shi tana k’ok’arin tunawa da inda taga fuskar, nan da nan kuwa ta tuna da sauri ta damke Saif ba shiri tana nuna hanyar da hannu ta furta. “ Shi neeeee!..”
“ Shi ne wa?.”
“ Wallahi shi ne, shi ne ban manta fuskar ba.”
“ Jon park.”
Da sauri yayi parking din motan yana fitowa, suma sauran motocin suka tsaya ganin wanda ogan nasu yake ciki ya tsaya.
Bude murfin motan tayi tana duba inda ta hango shi, ya zagayo inda take ya dafata ya ce. “ Ko gisau ya miki ne?.”
“ A’a na ganshi, Wallahi na ganshi.”
“ Ok kin ganshi naji, amma shi waye?.”
Shuru tayi tana zuba masa ido. “ Shi waye?.” Ta tambayi kanta kafin ta ce. “ Na manta waye ne shi.”
Tsayawa kallon ta yayi na seconds kafin ya jinjina kai ya bud’e mota ya ce. “ Shiga.”
“ Amma fa na gan shi sai dai na manta inda muka taba haduwa.” Bai kulata bayan ta shiga ya rufe kofar ya zagaya ya shiga nasa, Jon ya yiwa sauran alama da su shiga a tafi, da haka motocin suka tafi.
“ Wallahi na ganshi ka yarda da ni, na ganshi yana surutu sak yanda yake min, kuma da wasu kaya irin na masu kula da kai.” Ta nuna Jon da ke sanye da kayan sojoji tana ciga da cewa. “ Irin wannan kayan ne.”
Ya dubi Jon kafin ya mayar da kallon shi zuwa gare ta ya ce. “ Kayan army din ne yau kika manta sunan?.”
“ Army.” Ta furta kamar mai koyan magana, tana daurawa da. “ Me kuma Army?.”
Ba shi kadai ba har Jon da yake tuki sai da abun ya masa bambarakwai, ya zuba mata ido yana karantar yanayin ta, wani zufa ne yaji ya cika masa fuska duk da irin AC din da yake motan.
Ya saka hannu ya sharce zufa, ya juya harshe zuwa na china 🇨🇳 ya ma Jon magana, Jon ma ya mayar masa da amsa kafin ya dubi Safeera da ta zuba masa ido take kallon bakin nasa kamar tana jin me suke fad’a.
“ Shikenan idan muka koma gida zan barki a gurin Ummah sai ki huta.”
“ Ummah.” Ta kira sunan idanunta akansa.
“ Ita ma kin manta inda kika santa ne?.”
Gyada masa kai tayi tana mayar da hankalinta kan titin ta ce. “ Kwakwalwata ke min ciwo sosai.” Ta dafe kanta tana lumshe ido.
Saurin jawota jikinsa yayi yana rike kan nata, ya daura akan cinya yana mata tausa a hankali, har suka iso bakin 20 houses babu wanda ya sake cewa komai.
“ Jon ka shiga ka tambayi Jannah, idan tana nan ta fito.”
“ Owk Sir.” Ya fice daga motar.
Bayan kamar minti biyar ya dawo ya shiga motar ya ce. “ Sir duk na tambaya, kusan amsa daya suka bani kan cewa ta tafi kusan sati kenan.”
“ Ta tafi? To ina?.” Ya tambaya yana kallon Safeera da bacci ya dauke, kafin ya ce. “ Ka san gidan da kuka dauko Safeera time din da ta tafi?.”
“ Eh ni da Sageer muka je.”
“ Owk muje gidan.”
Tada motan Jon yayi suka nufi hanyar Bulunkutu har time din Safeera na bacci.
A dai-dai k’ofan gidan motan su yayi parking, Saif ya zubawa langa-langan ido yana tuna wasu abubbuwa da suka faru shekarun baya, ko a mafarki bazai taba manta wannan gidan ba, Jon ya katsai masa tunanin zucin nasa ta hanyar cewa. “ Sir ga gidan nan.”
“ Kai da Sageer kuka zo gidan nan?.”
Jon ya gyada masa kai alaman tabbatarwa.
Murmushin rainin hankali yayi ya ce. “ Kenan Sageer yasan gidan su Jannah ce, kuma Baffa mahaifinta ne?.”
Jon dai shuru yayi dan bai san komai game da wannan maganar ba.
“ Idan haka ne meyasa Sageer ya boyemin komai? Ina da tabbacin ya dade da sanin inda Jannah take amma yaki fadamin, kuma yasan Baffa mahaifinta ne amma ya boye min.” Ya karashe a tsawace wanda yasa Safeera farkawa ta tashi daga kan cinyarsa ta zuba masa ido.
Kallo daya ya mata ya fice daga motar, da sauri itama ta fita tana kallon gidan.
“ Shiga kace ana sallama da Jannah.” Ya fada yana harde hannu a kirji.
Safeera ta furta. “ Jannah.” Ya juyo ya ganta yana gyada mata kai, ya mika mata hannu ta iso tana makalewa a gefen shi.
A cikin gidan kuwa Jannah na zaune a taburma taji ana kwankwasa langa-langan, Inna da take cikin bukkan ta fito tana fadin. “ Waye ne?.”
Jannah ta ce. “ Inna ko naje na duba ne?.”
“ To kiyi sauri.”
Da sauri Jannah ta jawo gyalenta ta yafa ta fito.
Fitowanta yayi dai-dai da lokacin da Saif yake gyarawa Safeera mayafinta.
Cak Jannah ta tsaya ta gagara motsi, ji tayi numfashinta yana k’ok’arin daukewa, muryanta na rawa ta furta. “ Saif!!!!.”
Muryan da ko a mafarki yaji zai gane na waye ne, muryan da ya zauna a cikin kunnensa da zuciyarsa tare da gangar jikinsa, a wani slow motion ya juyo yana kallon ta.
Idanunta suka sauka akan Safeera da itama ita take kallo, ta ce. “ Safeera!!.”
“Na’am!!!.”
Da gudu Jannah ta rungume tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yayin da Saif tun bayan da suka hada ido ya sunkuyar da kai yana tunanin ya zai fara.
Sai da tayi kukanta kafin ta tallafo da fuskarta tana cewa. “ Safeera ashe zamu sake haduwa.”
Ita dai shuru tayi dan ba gane komai take ba, ganin hakan yasa Jannah ta mayar da kallon ta zuwa ga Ibilis din tana fadin. “ Me ya kawo ka kofar gidanmu?.
“ Jannah ki…!”
Hannu ta daga masa. “ Mara mutunci, wanda bai san ya kamata ba, war haka na dauka ka mutu ai ashe kana raye, azzalumi Ibilis, mai zubin fir’auna.”
Saurin runtse ido yayi yana jin zafi har cikin ransa, ta cigaba da cewa. “ Me ya hadaka da Safeera?.” Ta dubi Safeera da take kallon su kamar wata yarinya.
“ Uhm… Matata ce.”
Maganar taji kamar saukar aradu. “ Me ne??????.” Ta nuna shi, ta nuna Safeera ta ce. “ Matarka? Kai din?.”
Zata sake wata magana taji muryan Inna daga ciki tana cewa. “ Jannah lafiya kika dade?.”
“ Inna wani ne yazo.”
Fitowa Inna tayi tana sauke ido akan Safeera, ta zuba mata ido tana cewa. “ Wannan ba kamar Safeera ba ce?.”
Jannah ta ce. “ Ita ce dai.”
Safeera ta juya ta makale a bayan Saif tana magana kasa-k’asa. “ Mu tafi tsoro nake ji.”
Jannah ta furta. “ Ko wani abu ya sameta ne? Naga bata gane ni ba, ko bata da lafiya ne? A’a ko Safeera bata da lafiya idan ta ganni zata yi magana, sai dai idan wani abu ka mata makiri.” Ta kai karshe tana zagin Saif.
Jon zaiyi magana Saif ya daga masa hannu hakan yasa yayi shuru yana komawa baya, Inna ta ce. “ Shi wannan din ba kamar wanda yake zuwa gurinki kwanakin baya ba?.”
“ Shi dai.”
Jinjina kai Inna tayi hankalinta na kan Safeera da take lekan su.
Saif zaiyi magana suka ji karan horn na masifa.
*Sahibar ku*✍🏼🕊
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 27*
Saif zaiyi magana suka ji karan horn na masifa wanda ko ba’a fad’a ba kai kasan waye ne, kusan a tare suka juya har Safeeran da ta buya a bayansa.
Jon ya saki wani dariya yana saurin toshe baki ganin yanda Baffa ya fito daga motan.
Da mamaki Baffa ya iso gurinsu da dan saurin shi yana fadin. “ Alhaji namu Ikon Allah, yau kune a gidan namu kenan, to Allah dai yasa Hajiyarce ta bata na sake nemota.” Sai kuma ya sauke idanunsa akan Safeera. “ Auu ashe ba ita ta bata ba, to ince dai ba motar tawan za’a karbe ba, dan ku masu kudin nan ba damar kuyi kyauta sai kun biyo sahu da daddare, ni nayi mamaki yanda kai ka biyo rana kamar shege a kwali.”
Saif yayi murmushi dan yasan komai zai zo masa da sauki. “ A’a Baba.”
“ Baba kuma, ni ka kirani da mai gadinka ma Wallahi nagode.”
Inna cike da bakin cikin yanda Baffa yake zubar da mutuncinsa ta ce. “ Haba Baffa…”
“ Dakata Malama, ni fa banason munafurcin kin nan, ace mutum kana zaune dashi amma yana maka adawa, Allah wadaran naka ya lalace Wallahi.” Ya mayar da hankalinsa kan Saif yana cewa. “ Alhaji Allah ya kara nisan kwana, yanzu wani hidima zan maka.”
Kamar zata yi kuka ta ce. “ Haba Baffa, Saif din kake yiwa bautar nan sai kace wani sarki, ma wannan mara adalcin wanda bai san ya kamata ba, makiri….”
Saukar mari kake ji hagu da dama, yana shirin kai mata wani Inna ta janye ta tana kuka, Saif ya sunkuyar da kai, Safeera ta kankame shi kamar zata koma cikinsa, kai kace firewa sama Baffa zaiyi saboda masifa. “ Ashe baki da mutunci Jannatu, ko ince Jahannama.”
“ A’uzubillahi minal shaidanir rajim!!!.” Cewan Inna.
Baffa ya karbe da cewa. “ Ni ne shaidanin kenan.”
“ Anya zaka ga Annabi kuwa Malam?.”
“ A’a Asiya Matar fir’auna, idan nazo gani ki rufemin ido.”
“ Hmm! Allah ya kyauta.” Ta ja hannun Jannah suka koma ciki.
Baffa ya juyo yana bawa Saif hakuri. “ Alhaji, ranka ya dade, dan Allah kuyi hakuri yarinyar ce sam ba tarbiya, kasan ka haifi diya baka haifi halinka ba.”
“ Baba a cigaba da hakuri.” Ya karashe yana yiwa Jon maganar ido, nan da nan Jon ya bud’e gaban motan da Saif ya zauna yana dibo kudi dayawa.
Idanun Baffa ya sauka akai, tuni ya saki baki yawu na saukowa jiki na rawa tun kafin a mika masa ya miko hannu yana godiya, kai kace sujjada zaiyi wa Saif. “ Allah ya albarkaci rayuwarka Alhaji.”
Yayi saurin damke kudin yana sakawa a aljuhu, Jon yayi dariya ya koma gefe.
Saif ya dubi Safeera da bacci yake shirin dauka, kafin ya kalli Baffa ya ce. “ Baba dama gurin Jannah nazo…”
Ya dakatar dashi da sauri. “ Wace Jannah din?.”
“ Jannah wacce ta shiga yanzu.”
“ To to to inaji laifi ta maka naje naci ubanta yanzu.”
Murmushi yayi. “ A’a dama nazo ne mu gana ina sonta da aure.”
Baffa ya washe baki yana cewa. “ Ai ba matsala duk lokacin da ka shirya kawai kazo.”
“ Nagode to, mu zamu tafi sai na sake dawowa.”
“ Nagode Alhaji a dawo lafiya, Allah ya tsare gabanka da bayanka, Allah ya kore makiyanka ya nakasa su.”
“ Amen Baba.” Kafin ya dauki Safeera a hannu wacce ta dade da yin bacci, kafin Jon yazo ya bude motan har Baffa ya bude masa, ya shigar da ita kafin ya shiga yana daura kanta a cinyarsa, da haka suka tafi Baffa sai faman daga musu hannu yake.
Lumshe ido yayi yana tuna yanda Jannah take faman zaginsa, wani murmushi ya kufce masa yana bude ido ya shafa gemunsa, ya kalli Safeera yana mamakin yanda ta sauya cikin lokaci kalilan, ya tuna yanda tasha wahala a rayuwarta, wata zuciya ta ce. ‘ Safeera ta cancanci farin ciki, bai kamata ka mata kishiya ba, kuma kishiyar ma da Jannah.’ Wata zuciyar kuma ta ce. ‘ Ai Jannah kafi cuta, kuma ita ya kamata ka aura ba Safeera ba, dan yanzu ka aure ta ba wata matsala.’
Tunanin da yake tayi kenan har suka isa gida, ya dauko ta kamar Baby ya wuce da ita part nasa har wannan lokacin tana bacci.
Baffa yana shigowa ciki ya fara da cewa. “ Aniyar kowa ta bishi.” Inna da Jannah da suke zaune akan taburma Jannah na famar kuka.
Bai bi ta kan kukan nata ba ya fara cewa. “ Ke dan ubanki dama Alhajin sonki yake kike min bakin ciki da samu na, munafukar Allah ta’ala.”
Jannah ta fashe da kuka mai cin rai ta ce. “ Baffa ni bana son shi kuma har abada bazan taba son shi baa.”
“ Ahirr dinki, kuma ai ni ne ubanki ko? To aure kam an daura miki dashi ko kinki ko kin so.”
Inna ta ce. “ Haba dai Malam, ai naga yarinyar ba kai kadai kake da iko da ita ba, saboda haka bazata aure shi ba tunda bata son shi, kuma bamu san dalilin da yasa taki shi ba.”
“ To kema a karkashina kike, kinci albarkacin igiya daya ya rage tsakanin mu, da Wallahi sai na tsinke shi.”
“ Ai yanzun ma bai baci ba zaka iya.”
Da gudu Jannah ta shige bukkan tana kuka, su Baffa da Inna suka cigaba da surutun su.
Tana tsaye a korido kunnenta makale da waya, tana fadin. “ Na bunne, kuma ina da tabbacin ta tsallake.” Ta cikin wayan akayi magana.
Ta kwashe da dariya tana cewa. “ Ai ina da tabbacin maganin yayi aiki, kuma tabbas zamu cinma nasaran mu.”
Nan ma magana akayi ta cikin wayan, ta wani tuntsire da dariya tana cewa. “ Baki da kirki Wallahi, kije kice maganin yayi aiki ayi maza a turomin da mai girma alert, kafin na cika karshen aikin na kashe ta…” Bata karasa ba taji aka kira sunanta ta baya.
Ba shiri wayan ta sulale ta fadi kasa ta fashe, kafin a furgice ta juyo tana kallon…
*SAHIBA CE✍🏼*
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 28*
Ba shiri wayan ta sulale ta fadi kasa ta fashe, kafin a furgice ta juyo tana kallon shi.
Ya kafeta da idanun tuhuma yana binta da mugun kallo, jikinta ya dauki rawa alamun dai bata da gaskiya.
“ Ki je ki kawomin ruwa.” Ya fada yana juyawa ya koma falo.
Naunauyar ajiyar zuciya ta sauke tana dafe zuciya, a fili ta ce. “ Ashe baiji ba, Allah na gode maka.” Ta durkusa ta dauki wayanta wanda ya fashe ta nufi kitchen dan kawo masa ruwan da ya buk’ata.
Bayan Asabe ta kawo masa ruwan ne ta koma ya dubi inda Ummah take yana fadin. “ Ummah ba wai ina nufin zanci mata mutunci bane, amma ku duba halin da na jefa ita dayar.”
“ Saif a nan dai bakayi amfani da hankali ba sam, auren naku kwanan shi nawa ne? Ai sai ka jawo mata zagi a dangi.”
“ Ummah babu abunda zai faru d a izinin Allah.”
Ba dan taso ba ta ce. “ Allah ya kyauta.”
“ Amen.”
“ Ina Safeeran ta ke?.”
“ Tana bacci a daki, ni na fara daura tunani ma akanta Wallahi, tana yin abu kamar wacce bata da kwakwalwa.”
“ Dan zaka yi aure ne kake ce mata bata da kwakwalwa?.”
“ A’a Ummah ba haka nake nufi ba, wai army clothe ne bata sani ba, kuma da suka hadu da Jannah yanayin yanda tayi kamar bata taba saninta ba, Ummah can you believe dana kira sunanki bata ganeki ba.”
Mamaki fal fuskarta ta ce. “ Ban gane ba.”
“ Ummah I think kamar tana da tabin kwakwalwa ko kuma ta danyi loosing memory.”
“ Tayi loosing memory kuma ta gane ka? Sai dai ko wani abun, ka kawo min ita.”
Da to ya amsa yana mai tashi ya fita, a hanya kiran Ammar ya shigo masa, ya daga yana fadin. “ Allah ya shirye ka Ammar.”
Ta cikin wayan yayi dariya yana cewa. “ Amen Saif, ya masu jikin?.”
“ Da sauki Alhamdulillah, kai kuma tun shekaran jiya baka sake leko ni ba.”
“ Busy nake Wallahi Aminina, amma anjima zan shigo ayi hakuri da ni.”
“ Ya na iya.”
Suka danyi hira kafin ya kashe wayan dai-dai lokacin da Mom ta fito daga part dinsa ta wuce nata kuma bata gan shi ba.
Da sauri ya shiga dan yasan ba lafiya bane, yana shigo ya hangi Safeera ta dunkule a k’asa tana kuka, da gudu ya iso yana dafa ta ya fara cewa. “ Ke da wa? Waya saka ki kuka kuma? Me aka miki?.” Ya jero tambayar a hargitse.
Dago da kanta tayi ta kalle shi tana cigaba da yin kuka.
“ Safeera!!! Me kuma aka miki?.”
Cikin kuka ta nuna kofa tana fadin. “ Wata ce ta zo yanzu ta dakeni.”
“ Ta dake ki?.”
Ta cigaba da kukan tana fadin. “ Ban santa ba kawai ta shigo tana zagina ta mareni ta tunkude ni.”
Tausayi ta basa, sai kawai ya jawo ta jikinsa ya soma rarrashi dan yasan sarai in dai Mom ce zata aikata; har sai da tayi shuru kafin ya ce. “ Kiyi hakuri.”
Ta gyada masa kai kawai tana sake shigewa cikin kirjinsa har da lumshe ido, ya kuma cewa. “ Bacci kike ji?.”
Nan ma gyada masa kai tayi, sannan ya ce. “ Ok tashi idan munje gurin Ummah sai ki kwanta a can, dan zaman ki a nan akwai matsala, gashi ban gane yanayin ki ba.” Da haka suka mike suka nufi bangaren Ummah.
Suna shiga ya zaunar da ita akan two seater yana nufan dakin Ummah dan kiran ta.
Juye-juye ta fara tana kallon falon kamar ta shigo sabon duniya, Asabe ce ta fito rike da cup a hannunta ciki da kunu ta iso gurinta ta mika mata.
Da ido tabi cup din tana dauke kai.
A dan tsawace ta ce. “ Za ki karba ne ko sai na dura miki da zafin shi!!!.”
Jikinta ya soma rawa ta fara girgiza kai tana cewa. “ A’a na koshi.”
“ Wallahi baki isa ba, dura miki zanyi bari ki gani.” Ta kama bakinta tana k’ok’arin bud’ewa, Safeera ta dantse hakoranta tana dauke kai, cup din ta dauka da niyar zuba mata a baki, ba shiri ta kai hannu ta zubar mata a jiki.
Ihu Asabe ta saka jin zubewar kunun kamar wuta, da sauri Safeera ta tashi tana jijjiga kai tana baya, kusan a tare Ummah da Saif suka iso.
Yayi wajen Matarsa da sauri yana rungumeta, Ummah ta kama hannun Asabe wanda kunun ya zube a shi tana fadin. “ A garin ya?.”
“ Hajiya kunu na kawowa Hajiya shi ne ta zubar min a hannu.”
“ Inna’illahi!!.” Ummah ta fada tana kallon Safeera wacce Saif ya kankame ta, ta ce. “ Safeera me ya sa kika yi haka?.”
Saif ya karbe da cewa. “ Allah ya kara, Allah ma yasa hannun ya kone.”
Kuka Asabe ta saka tana komawa kitchen, Ummah ta ce. “ Haba Saif! Matarka ta konawa yar mutane hannu shine kuma kake bin bayanta.”
“ To Ummah ban da shishigi da gutsiri tsoma, uban wa yace ta kawo mata kunun? Ce mata akayi sha zata yi ne, ni fa bana son gulma ne da munahinci.”
“ Amma Saif baka da kirki, kaje ka siyo maganin da za’a shafa a hannun.”
“ Ashe kuwa hannun zai rube, ni nama fasa bar Matata a nan duk inda zanje zanna tafiya da ita kawai, ban isa da wannan makircin na mai aikin naki ba.” Ya juya ya rike hannun Safeera suka fita.
Ummah ta bishi da kallo tana girgiza kai kawai.
Part din Mommy suka je, ya bude suka shigo da sallama, Mommy ta amsa tana zuba musu ido.
Radiya dake zaune ta zubawa Safeera ido tana cewa. “ Ita ce aka auro kenan.”
Wani banzar kallo ya watsa mata nan da nan taja bakinta ta komar da hankalinta kan TV, Mommy na cewa. “ Sai yau kayi niyar kawota kenan.”
Kamar bazai yi magana ba ya ce. “ Mummy busy muke shiyasa.”
“ Ai ka kyauta kuwa.” Ta tabe baki tana kallon Safeera wacce ke makale a jikin Saif ta ce. “ Ita gold din bata iya gaisuwa bane?.”
Yaga Safeera yana mata alama da ta gaishe da Mummy amma ta nuna kamar bata gani ba, sai kawai ya ce. “ Bata jin Hausa sai Larabci.”
Sakin baki Mummy tayi suka hada ido da Radiya. “ Larabci?.”
“ Eh fa.”
“ To taya kuke magana ko kurmaye haka hada?.”
Radiya ta ce. “ Mummy ko kin manta shi ma yana jin Larabcin.”
“ Oh haka fa, to Allah ya kyauta, su Larabci manya.”
Ganin kamar suna son raina masa hankali ne yasa ya juya yaja hannun matarsa suka fice.
Mummy ta tabe baki ta ce. “ Amina dai ta koyawa yaron nan bakin hali, ko wani boka ne ta rike har ya mata aiki akaina ta kwato shi oho.”
Radiya ta ce. “ Mummy boka kuma.”
Filo Mummy ta wurga mata, ta tashi da sauri ta gudu tana fadin. ” Mummy Wallahi Anuty Fauziyya zata kaiki ta baro ki ne.”
“ Uwarki Radiya.”
*BAFFA*
Tsabar iskanci a mota yake kwana, har da bargon shi na rufuwa.
Ya iso cikin gidan yana sababi. “ Jannah idan mutuwa hutu ce a gareki to Allah ya miki rahama, amma auren ki da Alhaji kam an gama, mutumin kwarai wanda yasan darajar mutane, mai kamala.”
Jannah ta ce. “ Shi Saif din?.”
Baffa ya ragumo buta ya jefeta dashi yana fadin. “ Alhaji zaki kira shi dashi dan kutumar kullisuwar gidanku.”
Cikin kuka ta tashi tana fadin. “ Nikam Wallahi bazan aure shi ba, bayan kuma yana auren Safeera kawata.”
“ To ita Safna take da suna ko Safa ni ne na zama alwalin mijin nata, a gidan nan tazo ta zauna, yanda tasha fura da nono ai dole a mata kishiya, dan haka auren ki dashi an daura Wallahi, shi nake jira ma yazo muyi magana dan kar mu tafi gidan can ya zama kuma bai san gidan ba. Kin ga kuwa ana daura miki aure nima zan daura aure da kishiyar mamarki.”
Inna taja tsuki ta ce. “ Kai da son abun duniya kam bansan ya za’ayi ba.”
“ Ina cikin duniyar kuma bazan so
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 17