Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ido na wasu seconds, cike da lallashi ya ce. “ Su waye Falmata din?.” Kuka ta fashe dashi tana kallon fuskarsa ta ce. “ Y’an uwana ne.” “ Me ya same su?.” Ya tambaya yana share mata hawaye. “ Bansan inda suke ba, a gudun boko haram muka rabu dasu.” Shuru yayi yana binta da ido kafin ya ce. “ Kar ki damu zamu nemo miki su.” “ A ina? Ka sansu ne?.” Tayi tambayan tana zubawa tattoo din hannunsa ido, zanen maciji ne wanda yayi kyau sosai. Ji tayi yana cewa. “ Idan aka kira mai zane zaki iya masa bayanin yanda suke ko?.” Da sauri ta ce. “ Eh zan iya a kira shi.” “ To kiyi shuru kinji Kanwar Yayanta.” Ya fada yana goge mata kwallan da suke zubowa. Murmushi tayi tana cewa. “ To Yaya.” Duba agogo yayi yaga karfe biyu da minti goma na rana, kafin ya ce. “ Tashi muje mu nemo mai zanen.” Girgiza kai tayi tana cewa. “ Yaya nagaji kaje ka dawo.” Tabe baki yayi ya tashi ya nufi hanyar fita, sai yaji ta ce. “ Yaya bansan sunanka ba.” “ Haris.” Ya fada yana murmushi ya juyo ya ganta. Hannu ta d’aga tana masa bye bye, murmushi ya kuma yi ya fita da sauri dan yaje ya dawo. Ta kusa mintuna ashirin a zaune bai dawo ba, tashi tayi ta nufi inda taga ya shiga d’azu, tana shiga ta kalli babban frame 🖼 din hotonsa yana sanye da kayan sojoji, yana murmushi wanda ya zama masa dabi’a. Fita tayi ta dawo falon ta zauna, tana zama aka fara harbi ta ko’ina, a razane ta tashi ta nufi windows ta lek’a, sojoji taga suna ta guduwa ga harbi da ko’ina. “ Na shiga uku ni Safeera…..” Bata gama fada ba taji boma-bomai suna tashi, ihu ta saka tana fita daga falon da gudu, hanyar da mutane suke bi tabi tana kuka tana toshe kunne, tuni gurin ya bade da hayaki da kura, bom kawai yake tashi, tana gudu mutum ya fado gabanta a muce. Ihu ta kurma da karfi tana cigaba da gudu. Tuni garin ya sake rikicewa, hankalin mutane suka tashi ta ko’ina kowa so yake ya tsere da rayuwarsa, sojoji basu shirya ba aka kawo musu attack, jinin da aka zubar yafi wanda aka zubar a watannin biyun da suka wuce. Ba tare da tasan inda zata nufa ba ta shiga cikin kwalbati ta buya, tana ji motocin boko haram suna wucewa suna harbi, a cikin wajen ta kwana washe gari ta cigaba da gudu. Sai da aka dibi kwanaki ana kashe rai kafin Allah ya kawo taimako abun ya lafa. Sosai Safeera ta fita hayyacinta, dan yanzu babu marabanta da namiji, kirjin ya koma kamar kwalta haba ma bayan babu komai, ta rame ta lalace ga rashin kwanciyar hankali da nutsuwa. Watanta daya tana yawon inda zata kwana, duk inda taga dare ya sameta zata kwanta, washe gari ta cigaba da tafiya, idan taga masu abinci ta rokesu sai su bata taci, haka rayuwarta ya cigaba da tafiya. Bayan garin Borno ya samu lafiya, Wata rana tana tafiya ta shigo unguwar 20houses, wajen gida dari ta shiga, kowa yana binta da kallo, wata yarinya ta hanga wacce za suyi sa’a da ita. Yarinyar ta taso tana murmushi ta ce. “ Sannu da zuwa.” Murmushin yak’e Safeera ta mata tana cewa. “ Sannu.” “ Sunana Jannah, ga can dakina.” Ta nuna mata dakin dake kusa da band’aki. “ Ni kuma Safeera.” Kama hannunta Jannah tayi ta janta zuwa dakinta, daki ne babu katifa ko akwati, kawai zannuwa ne aka shimfida a k’asa, sai kayan sawanta dake kulle a tsumma, sai kula guda biyu. nuna mata gurin zama tayi tana cewa. “ Ki zauna Safeera.” Kafin itama ta zauna. Ganin yanda bakinta ke a bushe ne ya saka Jannah cewa. “ Na kawo miki abinci?.” Da sauri ta ce. “ Eh. Eh.” Murmushi tayi tana tashi ta dauko mata daya daga cikin kulan ta bata, hannu na rawa Safeera ta bud’e, shinkafa ce jollop babu mai sai magi da shima ba wani ji yayi ba. Ci ta farayi hannu baka hannu kwarya, Jannah na mata murmushi. Har sai da ta gama ci tas kafin ta dago ta kalle ta, kunya taji tana cewa. “ Kiyi hakuri na cinye miki abinci.” “ Bakomai, ai mun zama y’an uwa.” Cewan Jannah tana daukar kulan ta ajiye, kafin ta dawo ta zauna kusa da ita, muryanta ta rage tana cewa. “ Ki saurare ni.” Mai do da hankalinta Safeera tayi duka zuwa gurin Jannah ta ce. “ Ina ji.” “ Kin ga gidan nan tamkar gidan karuwai ne, sai kinyi karuwanci kafin zaki samu abinci ko ruwa, idan ba haka ba shikenan kin goma baiwa.” “ Ke ma karuwancin kike?.” Girgiza kai Jannah tayi ta cigaba da magana da muryan da bataso ajisu. “ A’a fita bara nake, da kuma aikin wanke-wanke a shaguna, sai na samu abinci da kuma kudin da zan siya ruwa jar 🫙 daya.” Jinjina kai Safeera tayi tana cewa. “ Da yaushe kike fita?.” “ Da dare nake fita bara saboda lokacin kwaratan nasu suke zuwa, kuma duk d’akin da suka tarar da mace suke shiga… da rana kuma sai na fita aikin wanke-wanke dan shima lokacin kwaratan suna zuwa, kuma idan suka ganki ko ke kikayi kanki baki isa ki gudu ba.” “ Na shiga uku.” Cewan Safeera hawaye na saukowa. “ Baki shiga ba tukun zaki shiga dai.” Jannah ta fada cikin zolaya tana dariya. “ Dariya kike min?.” “ A’a kuka nake.” Ta sake fashewa da dariya, sai kuma tayi saurin rufe bakinta ta fada a hankali. “ Kiyi shuru kar a san muna ciki a shigo, dan nikam bani da karfin guduwa.” “ To.” Safeera ta fada a tsure, sai kuma ta ce. “ Me ya sa yau baki fita ba?.” “ Allah yayi zamu hadu da ke ne.” Ta fada tana d’aga mata gira. Murmushi itama ta mata, Jannah ta ce. “ Sai kin zama gwaska fa, dan ba haka ba kin shiga uku, nima da kike gani karamar yar hau din kanta ce, babu wacce ta isa ta takani a gidan nan na barta.” “ Chabbb.” Cewan Safeera tana murmushi. “ Ke tashi mu fita kafin a shigo dan naji kamar ana son shigowa.” Ta karashe tana kama hannun Safeera suka mike tsaye, kallon kallo suka tsaya yi kafin ta ce. “ Ki dibi takalminki a hannu mu fita a sand’a, duk abunda kunnanki suka jiyo miki kar kiyi ihu dan Allah Safeera, Wallahi ban shirya mutuwa ba.” Jijjiga kai tayi tana daukan takalminta kamar yanda Jannah ta fad’a, a hankali suka bud’e kofar dakin suka fara sand’a suna tafiya. Sun zo giftawa ta kofan wani d’aki Safeera taga abunda ya goge mata hadda, mace da namiji ne haihuwar uwarsu suna iskanci sai ihu take. Cak ta tsaya ta gagara tafiya, Jannah sai janta take amma taki motsi, juyawa tayi tana ganinta, hannu Safeera ta d’aga tana nuna mata abunda ta gani bakinta na rawa ta kurma ihu… *Kuyi comments dayawa na muku typing dayawa😊* *SAHIBA✍🏼* 💔*BAƘAR ƘAUNA*💔 *Na* *FATIMA ISA MANU🦚* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_ 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Comments section https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP?mode=ac_t 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *TWO DIAMOND STAR LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 22* Cak ta tsaya ta gagara tafiya, Jannah sai janta take amma taki motsi, juyawa tayi tana ganinta, hannu Safeera ta d’aga tana nuna mata abunda ta gani bakinta na rawa zata kurma ihu. Da sauri Jannah ta rufe mata baki tana janta da karfi suka fito waje kafin ta sakar mata hannu tana cewa. “ Safeeera ashe baki da wayo? Sai da na gama miki wa’azi akan kar kiyi motsi ko magana, sai gashi ihu ma kike son yi Allah ya cece ni na rufe miki baki, da yanzu abunda ake yiwa wancan shi za’a mana.” “ Jannah tsoro naji Wallahi, kin ga yanda na kalle su ne abun kyama.” Safeera ta fada tana tufar da yawu. Dariya Jannah tayi tana jan hannunta suka fara tafiya suna hira har suka iso inda Jannah ke zuwa wanke-wanke. Cikin minti kadan suka gama wanke kwanukan, matar ta basu kudi dari biyu suka dawo, a hanyar dawowan su Safeera ta ce. “ Jannah nikam ina iyayenki ne?.” “ Hmm!!! Suna can gida.” Tayi maganar da alama abun yana damunta. Shuru Safeera tayi ganin yanda ta bata amsa din, ya tabbatar mata da abun yana damunta. Har suka iso gida babu wanda ya sake magana. Yanda suka fita a sand’a haka suka koma a sand’a babu wanda ya gansu har suka shige d’akin Jannah. Bayan sun zauna ne Safeera ta ce. “ Jannah a ina zamu samu ruwa?.” “ Dibowa zamuyi a rijiya, dana sha dana wanka, ga bokiti na.” Ta karashe tana nuna mata farin bokitin, tashi sukayi suka fito lokacin karfe hudu, gurin rijiyar gidan suka je suka bada naira hamsin suka dibo ruwa bokiti biyu, kafin suka dawo. Ganin Safeera ta kwanta ne yasa ta ce. “ Safeera bazaki watsa ruwa bane? Naga kayan jikinki duk sun yage kuma sunyi datti, ko zaki canja?.” Murmushi ta mata tana tashi ta zauna kafin ta ce. “ Jannah bani da wanda zan saka ko na canja fa.” Bata rai tayi tare da fadin. “ Sai kuma aka ce miki bazan baki nawa ki saka bane? Ni fa malama ki dauke ni tamkar yar uwarki wacce kuka fito ciki daya.” Murmushi tayi tare da cewa. “ To Jannah.” Wajen kayanta dake kulle a zani taje ta dauko ta kawo gaban Safeeran tana cewa. “ Ki zabi wanda zai miki, sai kije ki fara wankan kafin nima nayi.” Murmushi kawai ta yi tana duba kayan, wani doguwar riga ta dauka na atamfa, sai hijab blue, duk dama sun tsufa sosai amma a tsaftace suke. Bayan ta ajiye ne itama Jannah ta ciro wanda zata saka ta daure sauran ta komar, kafin suka mike Jannah na daukan bokitin ruwa guda daya suka fito waje Safeera na mara mata baya. Y’an gidan sai binsu da kallo suke har suka iso band’akin dake zagaye da langa-langa, a bakin band’akin suka tsaya Jannah na mika mata sabulu ta ce. “ Idan kika fito sai na shiga ina jiranki.” Karba tayi ta dauki ruwan ta shiga, Jannah na tsaye a bakin toilet din tana jiranta, har ta gama kafin ta fito jikinta na digar ruwa, Jannah ta shiga tayi ta fito kafin suka nufa dakinsu suna hira. Suna zaune a dakin bayan sun dawo daga bara sun samu abinci, tashi Jannah tayi ta rufe kofar ta danne da dutse, Safeera na binta da ido har ta gama ta dawo ta gyara musu wajen kwanciya. Bayan sun kwanta ne Safeera ta ce. “ Jannah bani labarin ki mana, ina nufin tarihin rayuwarki.” “ Hmm!!! Safeera a labarina babu komai sai haushi da Allah ya isa, dan labarina yana dauke da sharrin biyewa saurayi ne.” Da mamaki Safeera ta tashi ta zauna tana lalubo torch din Jannah ta kunna, da mamakin ta sai taga Jannah na zubar da hawaye, da sauri ta jawota jiki tana furta. “ Subhanallah, dan Allah kiyi hakuri banyi tunanin magana ta zai bata miki rai ba.” Cikin kuka ta ce. “ Safeera ba maganar naki bane ya bata min rai, asali ma tunawa dashi din da nayi ne ya bata min rai.” “ Kiyi hakuri to.” Safeera ta fada a sanyaye. Sakin juna sukayi Jannah ta jinginu da jikin bango, yayin da hasken torch yake tsakiya, Safeera kuma tayi zaman masu cin abinci ta zuba mata ido. “ Hmm! Safeera na zabi zaman kadaici ne.” Cewan Jannah kafin ta cigaba da cewa. “ Sunana Aisha Bukar Muddibo, amma anfi kirana da Jannah dan shine sunan da Innata ta sakamin…. Haifaffiyar garin Maiduguri ne, unguwar bulunkutu, Ni daya iyayena suka haifa daga nan Allah bai sake basu haihuwa ba, tun ina karama nake ganin halayen Mahaifina daban dana Mutane, dan Bappa Allah ya hore masa son kudi na masifa, akan kudi babu wanda bazai siyar ba, ciki kuwa har da ni. Ya sakani a makaranta na tsangaya wato almajiranci, har na girma, Inna ta dauramin tallan fura da Nono ina fita siyarwa, tun ina da shekara sha biyar nake siyar da Nono har Allah ya hadani da wani saurayina Saifullahi. Saifullahi Attajirin mai kudi ne kuma yana ji da kuruciya, mun hadu dashi ne a gurin da naje siyar da nono a bakin titi, ya tsayar dani ya siye duka, nayi murna sosai dan ganin da nayi ya min juye duka. Ai kuwa na tattara komai na koma gida, sai dai bansan yana biyo ni ba har na isa gida, na kaiwa Inna kudinta cas. Washe gari sai ga Saifullahi yazo wai gurina, da mamaki naje muka gaisa sai yace yazo siyan Nono ne, nayi murna sosai dan yau irin na jiya yamin wato juye. Har muka tsaya muka dan taba hira kafin ya tafi, tafiyarsa ke da wuya sai Baffa yazo ya kwalamin kira, da dauri na tashi naje na same shi ranshi a bace ya ce. “ Shi wannan yaron da yazo fa?.” “ Baffa fura yazo siya.” “ Kun daukeni bani da hankali dake da Innar taki ko? Yazo ya baku kudi shine zaku hanani kice wai fura yazo siya.” Inna ta fito daga daki tana cewa. “ Muddibo fura fa yazo ya siya kuma ya koma.” “ Aniyar ku ta biku, masu bakin hali, ai gobe zai dawo sai muga idan kudin yake baku ko kuma furan yake siya, masu bakin aniya kawai, bazaku hadu azo a rufawa juna asiri ba, ina zaune daku ashe da macizai nake zaune.” Ya juya zai tafi yana guna-guni. “ A sannu a hankali kowa halin shi zai fito.” Jikinmu ni da Inna yayi sanyi na juya na shiga daki. Washe gari kuwa sai ga motan Saifullahi yazo, na tashi na kai masa fura sai dai bashi bane wani ya aiko wai Sageer, muka gaisa har zai tafi sai Baffa yazo. Ganin ba kudi ya bani ba yasa Baffa bai ce komai ba juya ya tafi. Ana haka soyayya mai bala’in karfi ya shiga tsakanina da Saifullahi, sai dai wani abun mamaki duk zuwan da Saifullahi zaiyi bai taba haduwa da Baffa ba sai dai Inna, Innar ma wani lokaci ne, ranar da Baffa yazo sai ya zama Sageer ne, har Baffa ya fara cewa da Sageer muke tare. Mutanen rugarmu suka fara kananan maganganu, amma dake soyayya ya rufemin ido, idan ya shiga ta nan sai ya fita ta can. Mun kai kusan watanni muna soyayya da Saifullahi, wata rana yazo da dare. Muna tsaye a jikin motarsa ya ce. “ Jannah!!.” Na amsa da. “ Na’am.” Numfashi ya sauke yana cewa. “ Zan tafi karatu Cairo, bazan dade ba idan na dawo zan turo magabatana sai ayi maganar aure.” Duk da naji ba dadi amma sai nayi murmushi nace. “ Bakomai Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya.” Ya amsa da. “ Amen, Amma ki rikemin amana, bazan dade ba duka duka bai wuce wata biyu zuwa daya zanyi ba, In Sha Allah idan na dawo za’ayi magana.” Muka dan taba hira kafin ya tafi, na dawo na sanar da Inna. Bayan tafiyarsa da wata biyu Baffa ya bijiromin da zancen aure wai ya min miji, nan nace nifah akwai wanda nakeso kuma idan ya dawo zai turo ayi magana. “ Alkur’an baki isa ba, ni zaki tozarta a idon duniya dan malafar gidanku, ai kuwa gobe Alhaji zaizo a daura muku aure dan ya biya sadaki ma dubu dari, kuma wallahi sai kin aure shi.” Nan na fara kuka Inna na tayani, cikin dare na sulale na gudu daga gidan ban sanar da kowa ba, kuma babu wanda yasan inda naje har yau. Ina cikin gudu naji an daukeni, bansan inda nake ba sai washe gari na ganni a kan gado. Da mamaki nake bin dakin da kallo kafin na sauke idanuna akan shi, yana sakar min murmushin nasa mai daukemin hankali da tunani. Ya budi baki ya ce. “ Jannah ta!!!.” Ban amsa ba sai ma cewa da nayi. “ Yaushe ka dawo?.” Tasowa yayi ya zauna a kusa dani ya kama hannuna ya rike yana cewa. “ Jiya da daddare na shigo garin, kawai sai naji inaso na ganki, ban isa gidanku ba na ganki a hanya kina gudu cikin dare, ina zakije haka?.” Kuka na fashe masa dashi ina cewa. “ Baffa ne zaimin auren dole, shine na gudu.” Banga bacin rai a tare dashi ba sai ma cewa da yayi. “ To meyasa baki yarda ba?.” “ Saboda akwai alkawari a tsakaninmu.” Murmushi yayi da bangane me yake nufi ba ya ce. “ Haka ne, tashi ki watsa ruwa sai kici abinci.” Daga haka ya fita daga dakin. Numfashi ta sauke idanunta na zubar kwalla ta kalli Safeera ta ce. “ Safeera kinsan me ya faru?.” Girgiza kai Safeera tayi alamun tanason cigaba da labarin, Jannah ta ce. “ Zama muke yi a gidan tamkar Miji da Mata.” Da sauri Safeera ta ce. “ Ban gane ba Jannah? Aure kukayi?.” Girgiza mata kai tayi ta cigaba da bata labarin. “ Tun lokacin da ya kawoni gidan a daki daya muke kwana muci abinci tare, tun ina nuna masa kar shaidan ya shiga tsakaninmu har na daina damuwa dan naga shi bai dauka a wani abu ba. Ana haka wata rana Sageer ya shigo dashi ba lafiya, a rude na nufo su ina cewa. “ Me ya faru dashi?.” Sageer ya ce. “ Ciwon ciki ne yake damunsa ki hada masa tea da lemon tsami idan yasha zai warke bari naje na dawo.” Gyada kai nayi na nufa kitchen da sauri na hada masa Tea dan dama ya koyamin yanda ake amfani da gas, na hada masa na dauko lemon tsami a fridge na matsa masa na fito. Sai dai baya falon ya nufi dakinsa, hakan yasa na bisa dakin dan na kai masa. Yana tsaye daga shi sai gajeran wando, da sauri na ajiye tea din dan tun da nake dashi ban taba ganinsa haka ba, na juya da sauri zan fita ya kirani. “ Jannah ta.” Cak na tsaya na gagara motsi zuciyata na dukan uku uku, inaji ya tako inda nake ya tsaya dab da ni. Hannu yasa ya zageye cikina yana daura kansa a kafadata ya fara shinshinar wuyata, da sauri na zame jikina na ce. “ Saif ka manta ba kyau, kuma kamin alkawari bazaka tabani ba har sai munyi aure.” Bai ce min komai ba ya jawoni jikinsa yana saka hannu ya kashe wutan dakin, a Wannan daren labarin rayuwata ya canja ya tashi daga budurwa zuwa budur bazar, na tashi daga macen da take killace kanta zuwa ballagaza, na tashi daga saliha zuwa karuwa. A wannan daren nayi kukan da ban tabayi ba, nayi dana sanin guduwa daga gidanmu, nayi Allah wadai dani yafi sau billion. Bai barni ba har sai da ya zubar da ishinsa sau biyu, kafin ya barni nasha iska. Ya taimakamin na tsaftace jikina sannan ya bani magani nasha na kwanta baccin azaba. Tun daga wannan ranar kuma ya mayar dani Matarsa, duk lokacin da ya jiyo ishinsa sai yazo kaina ya sauke, wani lokacin sau uku a rana wani lokacin sai biyu, tun ban saba ba har na saba dashi, dan kullum cewa ya ce. “ Zan aureki, ni ne mijinki ko na kusance ki ba matsala ba ce.” Sai dai ba nan gizo ke sak’ar ba, wata rana yazo da daddare zai nemi ni nan na bijire nace sam ban yarda ba, ai kuwa mukayi kaca-kaca dashi daga karshe ya koreni daga gidansa, ni kuma na fita ba tare da na sake waiwayarsa ba, ban tsaya ko ina ba sai nan gidan. Zuwana nan gidan na fara sabon rayuwa na manta da wani Saifullahi, sannan na manta da ina da wasu iyaye, na zabi na killace kaina daga aikata zina, na zabi wahala sannan na gane illan rashin bin umarnin iyaye da biyewa saurayi. Ta karashe bada labarin tana kuka mai cin rai, Safeera ma tana tayata kukan. Cikin kuka Safeera ta ce. “ Jannah kin biyewa saurayin da bashi da tabbas.” “ Safeera nima nasan nayi dana sani, kuma na gane kuskure na duk da a kurarran lokaci na gane.” Goge hawayen fuskarta Safeera tayi tana matsowa kusa da ita ta rike hannunta ta ce. “ Ba’a kurarran lokaci bane Jannah, za ki iya gyara goben ki idan kin amince.” “ Safeera ta ya?.” “ Ki koma ga iyayenki, ki nemi yafiyarsu, ina mai tabbatar miki cewa Saifullahi zai dawo yana rokonkj gafara.” “ In Sha Allah.” Kafin Jannah ta ce. “ Safeera saura naki.” Dariyar da yafi kuka ciwo Safeera tayi tana bata labarinta tas tun daga farko har karshe. Jannah tayi kuka na fitan hankali jin labarin Safeera sai taga nata bakomai bane, ashe nata nafila ce. Kafin ta dubi Safeera da ta zuba mata ido babu hawaye a fuskarta ta ce. “ Safeera ina Haris?.” “ Hmm!! Jannah da zanga Haris da nafi kowa murna a duniya.” “ Lallai Allah yana jarabtar bawa dan ya gwada imanin shi, duk da irin halin da kika shiga amma kinki ki aikata abunda ba dai-dai ba.” Jannah ta fada tana jinjina kai. Sai kusan karfe shida na safe suka kwanta bayan sunyi sallah. Haka rayuwar Jannah da Safeera ya cigaba da tafiya har kusan na watanni uku, sun koma tamkar yan biyu, duk inda kaga daya zaka ga daya, rayuwarsu abun sha’awa, maza sun musu tallan kudi dayawa dan su bada kansu amma sunki. Ana haka ne wata rana Jannah ta fita da sassafe zuwa wanke wanke, Safeera kuma tace ta gaji yau. Tana sanye da hijab ja wanda kanshi ya kode yayi datti sosai, ta fito wajen gidan tana tsaye, wani motoci uku suka tsaya a gabanta. Wani mutum ya fito ya tsaya a gabanta ya kare mata kallo kafin ya ce. “ Aiki zaki mana.” “ Nawa zaka biya ni?.” Murmushi ya mata kafin ya ce. “ Kuɗi ba matsala bane muddin za ki yi aiki me kyau.” “ Sai naji nawa za’a bani kafin zan yarda, idan naji ingancin kafin zan yi.” “ Zan baki 5m.” “ Yayi kaɗan.” Da mamaki ya kalli yarinyar, yarinya karama da son kudi, amma sai ya ce. “ Iya shi zamu baki idan kin yarda muje idan baki yarda ba kuma shikenan.” “ Ka ƙara wuta ban yarda ba.” Safeera ta fada tana ta dube duben Jannah dan yau ta dade, kuma ga bonanza yazo na kudi ta tabbata idan ma sukayi aikin aka biya su shikenan su da talauci ya kare, idan aka biyasu 10m zata bawa Jannah 5m itama ta dauki 5m, tana tsaye har mutumin ya dawi yace zasu bata 10m ganin Jannah bata dawo bane yasa ta ce bari taje idan ta gama aikin sai ta dawo. *Idan baku manta ba nan ne farkon labarin ko?* *_~MUN DAWO DAGA LABARIN SAFEERA~_* Safeera ta karashe bawa su Labarinta tana kuka, ba ita kadai ba har Dad sai da ya goge kwalla, Ummah kam kuka take sosai, Umma Fauziyya sai da ta tausayawa Safeera. Saifullahi kam shuru yayi ya zuba mata ido, ga tunanin Jannah da yake yi, dan tabbas ita ce ba wata ba. A hankali ya tashi ya fice daga dakin jikinsa a sanyaye. *Ku suburbuda min comment🥹* 💔*BAƘAR ƘAUNA*💔 *Na* *FATIMA ISA MANU🦚* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_ 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Comments section 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *TWO DIAMOND STAR LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 23* Saifullahi kam shuru yayi ya zuba mata ido, ga tunanin Jannah da yake yi, dan tabbas ita ce ba wata ba. A hankali ya tashi ya fice daga d’akin jikinsa a sanyaye, tana mai bin shi da kallon tuhuma. Dad ya mayar da duban shi zuwa ga Fauziyya yana cewa. “ Kin ce kina nema na.” Saurin girgiza kai tayi, dan yanzu ko ta

Chapter 9 of 17