Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
🤝🤝🤝 *GARGAƊI* Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba. *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* *Page 32* *BOOK TWO* Shuru tayi kamar tana tuna abu, ta ɗan nutsu a hankali tana tuna rayuwarta na baya, ta dafe kai da sauri ta furta. “ Wayyo kaina.” Da sauri ya sake jakar hannunsa yana riƙeta, ya ce. “ Safeera!!!.” Ta ɗago ido ta kalle shi tana rufewa. Jijjiga ta ya soma yi, duk ya fice a hankalin shi, ajiye ta yayi ya nufi fridge da gudu yana ɗauko ruwan sanyi yazo ya fara yayyafa mata. Amma shuru babu alaman zata tashi, wurgar da ruwan yayi ya ɗauke ta zuwa waje da gudu; Jon yana kallon shi yayi hanzarin buɗe mota, shiga yayi da ita a hannunsa, shima Jon ya shiga yana tada motan, mota biyu na security suka bishi dan Dad yace duk inda zaije suna raka shi har sai asirin wadan da suka kai masa hari ya tonu. Suna zuwa aka karbe ta emergency ana shirin shigar da ita, shima ya biyo bayan su da zummar zai shiga, Dr ya dakatar da shi. A harzike ya ce. “ Dalla malam matsamin na wuce.” Dr ya sunkuyar da kai ya ce. “ Sorry to say Sir amma bazaka shiga ba, idan kuma kai zaka mata aiki go ahead.” Masifa ya soma yi a gurin, Dr bai kula shi ba ya shiga emergency din, Jon ya iso yana fadin. “ Sir ba zaiyu ka shiga ba.” Wani kallo ya jefa masa wanda yasa shi ma yaja gefe yana bin shi da ido, idan yace Uban gidan nasa baya bashi mamaki karya yayi, amma wasu abun da yake kamar ba shi ba, idan yana tare da Safeera zaka rantse ransa ce, idan kuma yana tare da Jannah zaka ce rayuwarsa ce. Jon ya sauke numfashi yana cigaba da kallon shi. *MOM POV* Yau ne ranar karshe da suka yi da Ashiru cewan zata bashi kudin, amma duk abunda ta samu bai wuce 5m ba, kuma ta tura masa dazu sai dai tana ta kiran number shi baya shiga. Gashi yanzu warin da take yi ya wuce na hankali, dan har ya kai da maruru ne ke fitowa daga farjinta yayi diwa, idan ta fasa kuma sai warin tsiya, amma duk da haka bata bi ta kai ba. Ita matsalan ta daya shine kar Ashiru yayi posting din videos din. Gashi dan iskan bokan bayi da lafiya, taja tsuki tana hada zufa, ta sake danna number Ashiru a sau ba adadi, amma amsa daya ce shi ne Switch Off. Kuka ta fara dan tasan Ashiru sai ya aikata abunda yayi nisa kuwa, zata sake kira kenan wani waya ya shigo mata, ta kalli number tana mamakin waye ne, kafin ta d’auka. Ta cikin wayan aka falfale da dariya ana cewa. “ Kin duba media kuwa? Ko baki san abunda yake faruwa bane?” Kuka ta fashe da shi tana sakin wayan ta daura hannu a kai tana ihu. “ Na shiga uku, na mutu na lalace Ashiru ya cuceni a duniya, Wayyo Allah na.” Ta dauki wayan da sauri tana hawwa IG, page na farko videos din ne ragaja, *Matar Alhaji Amdaz tana aikata alfasha da wani a hotel*, haka ma Facebook da Tiktok duk maganar ake yi, kuka ta cigaba da yi tana saurin tashi ta karkame kofar ta dan kar a shigo. *DAD POV* Dawowan shi gidan kenan aka kira shi a waya Abokinsa na ce masa ya hau Facebook ya duba labarai, ko ya kunna Tv ya duba me yake faruwa. Yana sauke wayan wani kira ya shigo, ya dauka yana mamakin yanda yau abokanan shi suke kiran shi, yana dauka aka ce. “ Alhaji haka ta faru? Ya hakuri dama rayuwar duniyar sai hakuri” akakashe wayan. Dad yabi wayan da kallo, kafin yayi hanzarin shiga bangaren Ummah dan shine kusa yana fadin. “ Amina kunna min Tv yanzu-yanzu” Ummah ta fito daga daki ta kunna masa tana faman tambayar shi me ya faru, amma bai bata amsa ba. Videos din ne a gaban Tv na Mom da Ashiru suna kwance a kan gado yana faman kwakulanta. Ummah ta tafka salati tana kama baki, Dad yayi baya-baya zai fadi Allah yasa ya dafa kujera yana tsayawa. Da sauri Ummah ta kashe TV din tana zama, a hankali ta daga ido ta kalli Dad tana fahimtar yanayin shi. Cikin wani irin yanayi Dad ya mik’awa Ummah wayansa yana cewa. “ Ki kashe.” Ta karba tana kashe wayan ta ajiye a gefe. Tashi yayi da zummar tafiya dakinsa, ba tare da Ummah ta ankara ba taji shi timm ya fadi, da gudu ta nufa gurin shi tana kiran sunan shi tana neman agaji. Asabe ta fito da sauri jin kukan Ummah, bata tsaya wata wata ba ta nufi waje dan kiran security su kai shi asibiti. *MUMMY POV* Ita dama wayanta yana hannunta, hakan yasa ta kalla abunda ke wakana a duniya, ta saki baki tana kallo tana mamaki. “ Lallai ana bura uba a duniya!!!” Ta kyalkyale da dariya tana cewa. “ Ita nata asirin ya tonu ni yanzu nawa ne ke kan hanya, dan tabbas sai wancan dan iskan ya fallasa kan cewa ni na aike su” Radiya ta fito da wayan a hannunta da sauri tana cewa. “ Mummy kinji me yake faruwa kuwa?” “ To ni ina ruwana, ita ce bata iya wasa ba” “ Amma Mummy abun ba kyau din gani” Har Mummy zata yi magana suka ji fitan motoci, da sauri Radiya ta lek’a window, Mummy na tambayar ta. “ Waye ne?” “ Mummy ban ga kowa ba amma kamar dai Dad ne dan security’s din shi ne” Suka danyi shuru kafin wayan Mummy ya soma ringing, ta kalli Number tana dauka: ta cikin wayan aka ce. “ Hajiya idan za ki iya gudu ki gudu, dan yaron nan ya kira sunan mu, ni yanzu ma nake shirin bari k’asar, kuma nasan suna hanyar gidanki yanzu.” Ya kashe wayan. Mummy ta mik’e tsaye tana fadin. “ Na tafasa na kone, wai me nayi ne haka na shiga uku na lalace, masifa kan masifa, daga wannan sai wancan….” Ba ta kai ga karasawa ba suka ji jiniyar motar yan sanda. *SAHIBA CE✍🏼* *BAƘAR ƘAUNA* *Na* *FATIMA ISA MANU🦚* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_ 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *TWO DIAMOND STAR LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *GARGAƊI* Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba. *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* *Page 33* *BOOK TWO* Mummy ta mik’e tsaye tana faɗin. “ Na tafasa na ƙone, wai me nayi ne haka na shiga uku na lalace, masifa kan masifa, daga wannan sai wancan….” Ba ta kai ga karasawa ba suka ji jiniyar motar yan sanda. Kusan a tare suka kalli junan su, Radiya na fad’in. “ Mummy police fa” “ Radiya naji” Tayi saurin shigewa ɗakinta ta rufe k’ofa, Radiya ma ta mara mata baya. Wani daga cikin security’s din ne yazo yana tambayan police din ta turanci. “ Sir akwai matsala ne?” Police din ya mayar masa ta harcen turanci. “ Munzo kama Hajiya ce” Da mamaki security ya kuma cewa. “ Sir matan uku ne bansan wanne kake nema ba, sannan kuma mai gidan bayi da lafiya an tafi dashi hospital, and karamin alhaji ma baya nan, kaga ba damar kama daya daga cikin mutanen gidan” Jinjina kai police din yayi kafin ya ce. “ Aikin mu ne, zamu jira su har su dawo kafin mu tafi da mai laifin, amma ina da tabbacin shi SSS ya sani” ya ciro wayansa yana dannawa Saif kira, har yayi ringing biyu bai dauka ba. Security ya ce. “ Sai dai ku jira shi, amma gaskiya bazamu iya bari a fita da mutum a gidan nan ba da sanin daya daga cikin Alhajin ba” “ Is owk zamu jira” ya koma motansu ya zauna, sauran suma suka zauna dan jiran Saif ko Dad. Security ya koma cikin y’an uwansa suna magana. Duk yanda akaso a dawo da numfashin Dad ya zama dai-dai abun ya fuskara, har ya kai da suna shirin kai shi ICU kafin aka ci nasara ya dawo amma yana daukewa ya dawo. Ummah duk tabi ta rikice ta rasa me yake mata dadi, gashi a hospital din ma maganar akeyi ana nuna videos din, duk kunya ya dame ta taji kamar ta rufe fuskarta. Ta kira number Saif yafi a kirga amma baya d’aukawa, gashi bata da number Jon, dama na Sageer ne kuma shi ma yana kwance ba lafiya. Dago kai tayi taga Security da yake tsaye kusa da ita, kafin ta ce.” Kana da number Jon ne?” Cikin girmamawa ya ce. “ Sir Maa” yana ciro wayansa ya kira Jon, bugu daya ya d’auka; sai ya mik’awa Ummah yana komawa gefe ya tsaya. Ummah ta ce. “ Ina Saif ne ina ta kiransa baya d’aukan waya?” Jin muryan Ummah ne yasa Jon cikin girmamawa ya ce. “ Maa yana hospital ne Hajiya ce ba lafiya” Da sauri Ummah ta ce. “ Subhanallah wani hospital?” Jon ya fada mata sunan hospital din yana kallon Saif wanda ya zuba masa ido, Ummah ta ce. “ Ta wani bangare kuke muma muna ciki” Kafin yayi magana Saif ya karbi wayan, dan duk wayan da suke yi yana ji, sai ya ce. “ Ummah waye ba lafiya?” Jin muryan Saif ne yasa ta ce. “ Dad dinka ne” “ Dad!!!” Ya maimaita sunan kusan sau uku kafin ya ce. “ Me ya fari da shi?” Ummah ta ce. “ Baka san me yake faruwa bane?” “ Ummah me yake faruwa? I don’t know fa” “ Kuna ta ina?” “ Emergency” “ Tam.” Ta kashe wayan. Saif yabi Jon da kallo yana cewa. “ Me yake faruwa ne?” Jon ya sunkuyar da kai ya ce. “ Sir videos akayi posting a social media na Hajiya Mom” “ Videos!! Na me haka? Sana’a take yi ne ko me?” Jon ya sake sunkuyar da kai, dan gaskiya abun da nauyi bazai iya fada masa ba, Saif ya kuma cewa. “ Nuna min videos din” “ Sir datana ya k’are dazun” Ya bishi da kallo dan ya gane baya son ya nuna masa ne, ya jinjina kai yana kallon daya daga cikin security ya ce a d’auko masa wayansa a mota. Bayan security ya bashi ne ya kalli missed calls kusan ashirin, dana Jannah dana Ummah dana Ammar, sai kuma wasu daga cikin friends nasa. Da mamaki yake kallo dan wasun sun shekara basu yi waya ba, number Jannah ya fara kira, bugu daya ta dauka. “ Hello” Tayi shuru tana jin shi, ya sake maimaitawa, kafin ta ce. “ Ina wuni?” “ Lafiya, ya Baffa da Inna?” “ Kowa lafiya” shuru ya sake rufe zancen nasu kafin ya katsai da cewa. “ Kinyi shuru? Naga missed calls naki ne, hope lafiya?” Numfashi ta sauke tana fad’in. “ Dama…” “ Uhm, go ahead me ya faru?” “ Dama… dama.. uhmm abu nakeso” Ya saki murmushi yana samun guri ya zauna wajen waiting bench, kafin ya ce. “ Wani abu kenan?” Sai da taja numfashi kafin ta ce. “ 3m” Yayi shuru yana nazarin me zatayi da shi haka, kafin ya ce. “ Turo Acc naki” “ Nagode sosai.” Ta fada tana kashe wayan, nan da nan ta rubuta ta tura masa, yana shigowa ya gani, Opay dinsa ya shiga ya mata transfer. Number Ammar ya dannawa kira, yana dauka ya fara cewa. “ Saif ya ake ciki? Ya har yanzu baku ce a goge ba abun sai yawo yake yi fa” Da mamaki Saif ya ce. “ What’s wrong?” “ Kamar ya? “ “ Ban san me yake faruwa ba, tun da na koma gida na kawo Safeera hospital ba lafiya” Ammar ya ce. “ Kana nufin baka san komai ba?” “ Idan na sani zan tambaye ka ne? Ka fadamin me yake faruwa dalla Malam” “ Videos din Mom ke yawo a social media, babu inda baije ba, Instagram, Facebook, twitter, tiktok har WhatsApp duk sun je” “ Videos din na menene? Sana’a take yi yayi trending ko kuwa tasa an daure mutum ne?” “ No videos din banza ne, like Sex ana mata videos ita da wani guy” Shuru kake jin Saif yayi ya gagara magana, no wonder kenan dazu da yake tsaye ake ta ganin shi ana magana k’asa-k’asa, wani kunya yaji ya rufe shi na lokaci daya. Nurse ce ta fito daga d’akin emergency da paper a hannunta tana nufo gurin shi, ya d’aga kai ya ganta, ta mik’a masa tana cewa. “ Sir congratulations” Da sauri ya karbi file din yana dubawa hannunsa har rawa yake, bakinsa na rawa ya ce. “ Safeera!!! *SUHIBA CE✍🏼* *BAƘAR ƘAUNA* *Na* *FATIMA ISA MANU🦚* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_ 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *TWO DIAMOND STAR LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *GARGAƊI* Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba. *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* *Page 34* *BOOK TWO* Nurse ce ta fito daga d’akin emergency da paper a hannunta tana nufo gurin shi, ya d’aga kai ya ganta, ta mik’a masa tana cewa. “ Sir congratulations” Da sauri ya karbi file din yana dubawa hannunsa har rawa yake, bakinsa na rawa ya ce. “ What!!” Nurse din ta gyada masa kai tana cewa. “ Dr yana neman ka a office” “ Ok” ya nufi office din Dr, Jon na biye da shi. Bayan sun gaisa ne Dr ya ce. “ Congratulations.” “ Thanks.” Numfasawa Dr yayi kafin ya ce. “ A binciken da mukayi mun gano kwakwalwarta yana samun tabuwa, ma’ana yana dan kaucewa, zaka iya ganin wata rana tana yin abu kamar wacce bata sanka ba, ko ta manta mutane, sai kuma daga baya tana tunawa; memory’s nata na 7-4yrs yana rawa sosai” ya dan numfasa kafin ya ce. “ Tana da BP dan ya hau sosai, kuma ga ciki na wata biyu” Saif yayi shuru yana mamakin yanda Safeera ta kamu da BP, idan kuma yayi la’akari da irin rayuwar da tayi a baya sai yaji zata iya samu, muryan Dr ya katsai shi. “ Tana buk’atar kulawa sosai, sannan akwai magungunan da zata dinga sha, idan an kula komai zai dawo normal, amma idan ba’a kula da ita yanda ya kamata ba, zata iya loosing din memorys nata gabadaya.” Saif ya ce. “ Ya jikin nata yanzu?” “ Alhamdulillah, an kaita dakin hutu” “ Zan iya zuwa na ganta?” “ Why not, sai dai ba’a son hayaniya.” Ya mika masa wata takarda da ya rubuta magunguna, ya ce. “ Akwai a pharmacy zaka iya siyowa, dan akwai alluran da akeso a mata.” Saif ya karba yana tashi ya fita jikinsa a sanyaye, sai ya rasa shin murna zaiyi ko kuka? Gefe guda ga matarsa tana da ciki da kuma irin halin da take ciki, ga kuma Mahaifinsa a kwance ba lafiya, ga kunyar jama’an da yake ji na abunda Mom tayi. Muryan Ummah yaji tana fad’in. “ Ina zaka yi kuma?” Ya shafa gashin kansa yana isowa gurinta, ya mik’awa Jon takardan ya bashi ATM ya ce yaje pharmacy, kafin ya dubi Ummah ya ce. “ Ummah ya Dad din?” “ Har yanzu likitoci na kansa” ta fadi a sanyaye. Shuru suka yi kafin ya kuma cewa. “ Ya zancen Mom din?” “ Sai ya tashi tukun” Wayansa ne ta soma ringing ya duba yaga daya daga cikin security na gida ne, dauka yayi yana mannawa a kunne, ta cikin wayan security ya ce. “ Sorry Sir for disturbing you” Saif ya ce. “ Is owk, what’s wrong?” “ Sir police ne suka zo wai zasu tafi da Hajiya, sannan wai sun kiraka sun sanar da kai” Saif yayi shuru dan shi ya maida ma Mom ce, kafin ya ce. “ Wace Hajiyar?” Hankalin Ummah ya dawo kan shi jin ya ambaci sunan Hajiya, security ya ce. “ Ban san wacece ba, dan nace sai sun jira daya daga cikin ku ya dawo” Saif ya jinjina kai ya ce. “ Ba shi wayan” Security ya mik’awa Police din waya ya koma baya, ya manna a kunne yana fadin. “ Sir Afternoon!” Bai kula ta gaisuwar da yake masa ba ya ce. “ Wa ya baka permission na kazo ka tafi da daya daga cikin gidan Safwan?” Police din ya ce. “ Sir ina ga baka gane ni bane, akan case naka ne kai da wadan da suka kawo maka hari” “ Then me ya kawo case nawa cikin gidanmu har zaka tafi da daya daga ciki?” “ Sir wacce muke zarga tana cikin gidan!” Sai da yayi shuru kafin ya ce. “ Ok ina zuwa!!!” Ya kashe wayan. Ummah ta zuba masa ido tana jiran taji me zai ce, tashi yayi zai tafi ta ce. “ Ina kuma?” Ya shafa gemunsa yana jin zufa na karyo masa, kansa yaji ya fara sara masa alamun ciwon kai na shirin sauko masa, ya numfasa ya ce. “ Ummah ina zuwa!” Security suka fara rufa masa baya ya daga musu hannu alamun su tsaya, ya ce. “ Bani zaku kare ba, ahalina zaku kare, by the way Dad na kwance, Safeera na kwance and Sageer, ni idan kun biyoni me zakuyi?” Ya ja tsuki yana fita daga gurin. Horn yake dannawa kamar zai tashi sama, da gudu mai gadi ya wangale get, ya cinno da motan ciki, ko parking me kyau baiyi ba ya fita ya iso wurin police din. Hannu suka mika masa suka gaisa, yana daurawa da cewa. “ Waye suspect nakun?” Wayansa ya ciro yana nuna masa hoton Hajiya Mummy, ya amsa yana kallo, har da zooming yayi dan shi bai yarda ba. Ya mik’a musu wayansu yana cewa. “ Evidence?” Police din ya mika masa wasu hotuna, wanda Mummy take magana da mutanen da suka kai masa harin, ya daura da bashi recording na wayan da Mummy take, tun bayan da suka fara zargin ta, suka fara bibiyar wayan da take yi. Ya jinjina kai yana basu hanya ya nuna musu part din Mummy, ya koma jikin motansa ya nad’e hannu a kirji yana kallon su. Police mazan suka tsaya daga waje, macen ta shiga cikin falon, sallama take yi amma babu wanda ya amsa, ta fito ta sanar da ogan nasu. Ganin haka yasa Saif tambayar mai gadi. “ Mummy ta fita ne?” “ A’a Alhaji tana ciki da ita da Hajiya Mom.” Ya jinjina kai ya isa wurin police din yana cewa. “ Tana ciki, sai dai ko maybe ta buya!!!” Cewan Saif yana musu jagora zuwa d’akin Mummy. Knocking macen police din ta soma yi,,,, Mummy tana ji taki budewa, sai zufa take hadawa har rigarka ya jike tsabar zufa. Saif yayi murmushi ya ce. “ Ku balla kofar” Jin haka yasa Mummy shigewa toilet da gudu ta rufe k’ofar. Daya daga cikin police din ne yayi baya ya buga k’ofar da karfi, timm kake ji sai gashi a k’asa. Radiya da ta tsorata ce ta fito da sauri, Saif ya zuba mata ido yana ganin yanda gumi ya jik’ata, yana dauke kai suka shiga d’akin Mummy. Duba ko’ina suka yi amma babu Mummy, Saif ya kalli k’ofan toilet din ya ce. “ Sa ke balla wanna.” Police ya ce. “ Sir kar balla ballan suyi yawa” Bai kula shi ba, wanda ya balla na farkon ne ya sake balla wannan, da sauri macen ta shiga cikin toilet din. Mummy ta fashe da ihu tana fadin. “ Saif bani da laifi kar a kamani, ni fa uwarka ce!” “ A’a ke ba uwata bace” ya fada yana kau da kai, dan shi mamakin ta ma yake, me ya tare mata da take neman rayuwarsa haka, ko ya mata wani abu ne. Handcuff aka sa mata a hannu, macen ta fara jan ta da karfi, amma taki tafiya sai rokon Saif take, shi kuma ya kawar da kai gefe ya mantar da ita. Idanunta ne ya sauk’a akan bindigar dake kwankwason police din, ta saci kallon shi taga hankalin shi baya kan bindigar, kafin ka ce me ta fuzge rikon da matar ta mata ta dauke bindigar dake kwankwason police din. A furgice duka suka yi baya, Saif da yafi kowa tsorata ya buya a bayan police din yana fadin. “ Ke baki da hankali ashe! Ku kwace bindigar” Mummy ta saita kan Saif tana kuka tana fadin. “ Gwara na kashe ka na huta, ko zanji sauki a raina, Saifullahi na tsane ka, tsana mafi muni a rayuwa.” Ta nuna police din da bindigar tana cewa. “ Idan daya daga cikin ku ya matso sai na harbe shi.” Saif ya wani hadiye yawu mai kauri yana cewa. “ Naji amma ki ajiye bindigar nan, kar ki kashe mutum?” Ta gyara saitin bindigar tana saitawa dai-dai shi ta ce. “ Idan na kashe ka, ko an kasheni bani da matsala” Radiya ta shigo da gudu tana cewa. “ Mummy karki min haka!!!!” Ta kalle ta tana fadin. “ Ki bar nan gurin” Saif ya fito daga bayan police din yana cewa. “ Mummy ki bari karki yi harbin nan.” Ta saki wani murmushi tana harba bindigar, ji kake tauuu ya bula cikin….. *SAHIBA CE✍🏼* *BAƘAR ƘAUNA* *Na* *FATIMA ISA MANU🦚* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_ 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* 🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *TWO DIAMOND STAR LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *GARGAƊI* Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba. *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* *Page 35* *BOOK TWO* Saif ya fito daga bayan police d’in yana cewa. “ Mummy ki bari kar ki yi harbin nan.” Ta saki wani murmushi tana harba bindigar, ji kake tauuu ya bula cikin ta. Waro ido waje duka suka yi suna kallon ta, ta kama cikinta tana sakin murmushi ta kalli Saif, ta zame a hankali tana fadiwa k’asa. Da gudu Saif yayi kanta yana kiran sunanta. “ Radiya!!! Radiya!!! Radiya!!!!” Mummy ta saki wani ihu tana cillar da bindigar tayo kanta da gudu, da sauri Police din ya d’auke bindigar yana rike Mummy da ta nufi kan Radiya. Ta lumshe ido ta bude tana kallon shi, cikin kokawa da numfashinta da ya fara daukewa ta ce. “ Saif… ina… sonka!!!” Tana gama fadar haka jikinta yayi nauyi, idanunta suka kafe wuri daya, jikinta yayi sanyi hannunta ya sake. Mummy ta fashe da kuka mai karfi tana cewa. “ Radiya ki tashi Radiya!!!!” Ya zuba ma fuskarta ido yana kallon ta, jikinsa yayi sanyi sosai, da fa yanzu shi aka kashe da bata shiga ba, kuma wani kayan kukan a tafin hannunsa ta rasu. Police din ya ja Mummy da karfi suka fitar da ita, aka bar Saif da police uku. Ya rufe mata idanunta a hankali, ya cireta daga kan cinyarsa ya ajiyeta a wurin, ya mik’e jiki ba kwari ya fito, ya kalle su an bude musu get, ya daga hannu, kafin ya k’araso wurin yana kallon Mummy ya

Chapter 13 of 17