Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da Jijjiga shi, dan yanzu ta gane ba wasa yake mata ba. Bango kofar akayi aka shigo da gudu, a razane ta juyo tana kallon kofar, mutumin da suka dauko ta ne, da sauri ya iso yana cewa. “ A garin ya? Me ya same shi? Ke kika kashe shi ko? Mutumin da ba lafiya dashi ba shine kika kashe shi ko? Idan ya mutu ke ma sai kin mutu.” A haukace ta ce. “ Sai dai mu mutu zaka ce, dalla Malam taya zan kashe mutum? Dan yazo fadi na rike shi shikenan ni na kashe shi.” Cike da takaici Sageer ya ce. “ Ni bansa me Saif ya gani ba ya nace sai ya kwanta dake, karuwa kawai.” “ Idan ni karuwa ce kai kuma kwarto ne ai, mara hankali kawai.” Ta fada a kule tana hararan shi. Wani damke hannun da Saif ya mata ne yasa ta dawo da hankalinta kan shi, haka ma Sageer din, da sauri ya ciro waya yana kiran wani number. Kansa ta daga ta daura akan cinyarta, Sageer ya ce. “ Me ya same shi?.” “ Ban sani ba fa, kawai muna tsaye dana tambaye shi iyayensa shine ya dafe kai daga nan kuma ya koma haka.” Ta fada a raunane wanda taji lokaci daya tausayinsa ya kama ta. Gyada kai yayi bai ce komai ba ya nufi kofa jin ana kwankwasawa. Hannun shi ta rike tana cewa. “ Dan Allah ka tashi.” Ta yi maganar tana goge hawayen da har yanzu suke gangaro masa. Sageer ne ya dawo da wani Doctor, gurin su suka iso Dr ya ciro kayan gwaji ya fara masa, idanunta na kan su tana karantar yanayin su, dan tsoro take ace ya mutu dan tasan direct prison za’a kai ta. Dago da kai Dr yayi yana kallon ta wanda ita ma shi take kallo zuciyarta na harbawa, muryan Sageer taji yana cewa. “ Me ya same shi?.” “ Kai ma kasan condition da yake ciki, kuma sai da nace kuna kulawa da yana yin shi, yana critical condition kai ma shaida ne, to me yasa zaku saka ciwon shi yana tashi?.” Dr ya fada ranshi a bace. “ Yanzu dai Dr ka mishi alluran da ka saba masa, next time za’a kiyaye.” Muryan Safeera har rawa ya fara, kamar wacce akace yana da ciwon HIV haka take ji, da kyar ta kwakulo yawu daya bushe ta furta. “ Wani irin cuta ne dashi?.” Kallon ta Dr din yayi kafin ya ce. “ Matarsa ce?.” Girgiza kai Sageer yayi ya ce. “ Cousin nasa ce… *Nikam ko baya muku dadi ne littafin🥹 babu wanda yayi comments fa, idan bayayi ku fadamin sai na bari ku huta 🥹* DR TEEMERH✍🏼 4- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 Gajeran labari Na Fatima Isa Manu DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU ) *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* *Page 4* Kallon ta Dr din yayi kafin ya ce. “ Matarsa ce?. Girgiza kai Sageer yayi ya ce. “ Cousin nasa ce.” “ Ok.” Kallon ta Sageer yayi ya ce. “ Zamu shigar da shi ciki dan a samu a masa allurai sannan a sa masa drip.” Gyada kai tayi, Dr Rahuz da Sageer suka kama shi zuwa dakinsa, har suka shiga bata tashi ba sai idon da take bin su dashi, ta dan dade a gurin kafin ta mike ta nufi nata dakin ta shiga. *MOM POV* Yau girkin ta ne, dokar Dad ne ya saka duk ranar mai girki a bangaren ta za’a ci abincin dare, hakan yasa aka jera abinci a daining. Fitowa Mom tayi daga daki tana tafiya tana girgiza jiki, duk suna daining table ita kadai kawai suke jira, kallo daya Ummah ta mata tana dauke kai, Mummy kuma taja tsaki wanda ya fito fili. Dad da yake zaune ya daga kai ya kalle Mummy yana girgizawa, Radiya kam abun har mamaki yake bata, sun tsufa ma amma basu daina kishi ba, kai kawai ta girgiza tana cigaba da danna waya. Isowa Mom tayi tana jan kujeran dake kusa da Dad ta zauna, sannan ta zubawa Dad kafin kowa ya zuba abun da zai iya ci aka fara ci. Cokali biyu Dad yayi ya tsaya yana kallon Ummah ya ce. “ Ina Saif ne?.” Ajiye cokalin hannunta Ummah tayi kafin ta ce. “ Rabo na dashi tun jiya da safe, wai zai je aiki, dana tambaye shi wani irin aiki ne sai yace ba sai na sani ba.” Ta karashe a raunane. Gyada kai Dad yayi kafin ya dubi Mummy ya ce. “ Ke fa kinsan inda ya je?.” Ko a jikinta ta ce. “ Alhaji kai da danka ni kuma ina zan san inda yaje? Ni a su wa.” “ Ban ce ki min zancen banza ba Jamila, tambayar ki nayi idan baki sani ba ya isa ba sai kin min rashin kunya ba.” “ Sai ayi hakuri.” Mummy ta fada tana bata fuska. Kallon Mom yayi yana fadin. “ Ke fa?.” “ Alhaji ya ce zaiyi tafiya na kusan 1 week ko yafi ma.” Mom ta fada a yanga. Gyada kai yayi bai ce komai ba, kallon Mom Radiya tayi dan tasan tabbas karya ta fada amma babu damar karyatawa. Ran Ummah fal tambaya amma tayi shuru dan bata san waye zai amsa mata tambayar ba, hakan yasa ana gama cin abincin ta mike ta nufi part din ta, Mummy ma ta nufi nata , Radiya kuma ta wuce dakinta. *MUMMY POV* Tana shiga bangaren ta ta saka key, sauri tayi ta nufi dakinta ta shige. Wayanta dake ringing tun dazu ta kalla tana danna kiran wanda ya kira ta, ringing biyu ana uku aka dauka, surutu ake ta zubawa ta cikin wayan, ranta a bace ta soma cewa. “ To uban me kuke jira da baku kashe shi ba, ai sai da nace muku ya fiku wayo kuma idan ya kufce ba lallai ku kama shi ba, ya gane kuna binshi ne shiyasa ya bace muku.” Banji mai aka ce ta cikin wayan ba sai murmushin da tayi tana cewa. “ Kun kyauta, sai naji sakamako mai kyau, zan baku tukuici mai girma da tsada.” Nan ma magana akayi sai ta kwashe da dariya ta kashe wayan. *UMMAH POV* Ko da ta shiga dakinta rufewa tayi ta fashe da kuka mai cin rai da zafi, hoton danta kwalli data tayi tana dauka ta runguma tare da fashewa da wani matsanaicin kuka. Yaro dayan da take dashi yanzu an raba ta dashi, ko gaishe ta baya yi, baya ma ganin ta a matsayin uwa, ace wai zaiyi tafiya amma bazai zo ya fada mata ba. Sake sakin kukan tayi tana jin radadi da zafi a zuciyarta, ta dade tana kukan da taga kukan bazai mata komai bane ta tashi ta dauro alwala ta fara nafilfilu da addu’a akan Allah ya kawo mata mafita da sauki, sannan ya kare mata danta da duk sharrin dake tunkaran shi. *SAFEERA POV* Tana shiga dakin toilet ta nufa dan sake gasa jikinta, sai da taji dai-dai kafin ta watsa ruwa ta fito amma har yanzu tana dan dingishi sai dai ba sosai ba. Kwantawa tayi dan ta huta bacci ya dibe ta, ba ita ta farka ba sai kusan eight, tana tashi ta watsa ruwa ta dauro alwala ta gabatar da sallah, kafin ta nufi dakinsa dan dubawa ko ya farka. Ya dade yana bacci, dan ya kwashi kusan awa uku me kyau yana bacci bai farka ba, sawun ta kusan uku amma yana bacci. Yanzu ma dawowa tayi dan ta duba ko ya farka, shigowar ta yayi dai-dai da bud’e idon da yayi, sauke su yayi a kanta yana binta da kallo wanda ita ma shi take kallo. A hankali tayi sallama tana shigowa ciki, a kan bedside ta zauna tana kallon shi tare da cewa. “ Ka farka ya jikin?.” “ A’a mutuwa nayi ban farka ba.” Ya fada a takaice yana zuro da kafarsa daga kan gadon. Tabe baki tayi tare da fadin. “ Daga tambaya.” Bai ce mata komai ba ya mike ya nufi toilet, da ido ta bishi tana kau da kai tare da furta. “ Ga kyau amma ba hali.” Wayansa ta gani a kan gado. Hannu ta kai ta dauka tana kunnawa, a bude yake ba password hakan yasa ta wuce wajen kira, missed calls sun fi goma aka masa, ba ta bi ta kansu ba ta fara danna wasu number, danna kira tayi tana mikewa da sauri ta nufi hanyar kofa da wayan, tana k’ok’arin bud’e kofan ne ya danne da hannu. A gigice ta juyo tana kallon shi dan ita bata yi tunanin zai fito yanzu ba, fuskarsa a tamke yake kallon ta cike da zargi, kafin tayi wani magana ya jefa mata tambaya. “ Wacece ke?… DR TEEMERH✍🏼 5- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 Gajeran labari Na Fatima Isa Manu DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU ) *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* *Page 5* A firgice ta juyo tana kallon shi dan ita bata yi tunanin zai fito yanzu ba, fuskarsa a tamke yake kallon ta cike da zargi, kafin tayi wani magana ya jefa mata tambaya. “ Wacece ke?.” Wani yawu ta hadiye mai kauri, kafin ta dan sai ta nutsuwarta tana cewa. “ Ban gane wacece ni ba?.” “ Kar ki raina min hankali mana, wa ya aikoki gurina?.” Ja baya ta fara yi ganin yana matso ta, muryanta ya fara rawa gurin fadin. “ Babu wanda ya aiko ni, kuma ai naga ku kuka dauko ni, sannan..” A tsawace ya ce. “ Munafuka dukan ku bakin ku daya, kowa kudi yake nema, burin ku kawai ku kashe ni, na dauka ke mutumiyar kirki ce na dauko ki ashe kura ce ke lullube da fatar akuya.” Da mamaki ta nuna kanta tana cewa. “ Ni!!! Me ka min da zan kashe ka, ku fa kuka dauko ni…” “ Dalla malama ki dena fakewa da ni na dauko ki, dama kin shirya cutar da ni ne Allah ya kama ki, mara mutunci kawai, ina k’ok’arin mai dake mutum ashe ke zuciyarki baki ne.” Hawayen da suke shirin zubo mata ta dauke, kafin ta mika masa wayansa tana fadin. “ Ka sallame ni zan tafi na hakura da aikin.” Gira daya ya daga mata ya ce. “ Ga hanya nan daga nan har lahira, na sallame ki, ki fice daga rayuwata ko kadan bana buk’atar ganin ki.” Jijjiga kai tayi tana kare masa kallo, kafin ta bud’e kofar ta fice daga dakin, da sauri ta sauko daga kan stairs, direct kofa ta nufa ta bud’e ta fita. Tana fitowa compound din ta nufi hanyar get, bud’e mata karamin kofa mai gadi yayi ta fice. Tsuki yaja lokacin da yaga fitan ta daga gidan, komawa daki yayi ya shirya cikin kananan kaya JC red da trouser baki, ya dauko wayansa ya fice daga gidan baki daya. *SAFEERA POV* Tafiya take yi ba tare da ta san inda zata nufa ba, wani daci take ji har zuciyarta, tun da aka haifeta har ey yanzu bata huta ba, kullum cikin wahala take tana fadi ka tashi, sanadiyar yunwa ta siyar da martabarta na y’a mace, a tunanin ta zata samu kudin da zata cigaba da karatu da kuma samun abinci, sai dai kash babu riba, bai bata kudin ba bai kuma kalle ta da daraja ba, karshe ma korar kare ya mata. Wani kwalla taji ya tsiyayo mata, hannu tasa tana taba hawayen, murmushin da yafi kuka ciwo tayi tana cewa. “ Yau ni nake zubar da hawaye? Lallai abun ya min zafi, ashe zan sake kuka?.” Ta tambaye kanta tana mamaki. Cigaba da tafiya tayi akan titin tana murmushi kamar wacce ta zauce, ciwon da take jin kasarta yake mata yanzu duk ya dena, babu abunda yake damunta kamar yunwa da kuma inda zata kwana. Shuru tayi tana zancen zuci. “ Ko zan koma gidan karuwai din ne? Amma idan na koma babu riba fa, me amfani idan na lalata kai?.” Wani zuciyar ya ce mata. “ Lalata kanki na nawa kuma, kawai kije ki cigaba da yi.” Saurin girgiza kai tayi a fili ta furta. “ Yau din ma tsautsayi ne, kuma na daina bazan taba sake kusantar zina ba ko da zan mutu da yunwa kuwa.” Ba tare da ta ankara ba har ta fita daga unguwar GRA dake garin maiduguri, tafiya kawai take ba tare da ta san inda take nufa ba, tun tana ganin mutane da motoci har ya zamana ta daina kallo baki daya, alamun dare yayi, ba kajin komai sai kukan tsuntsaye kawai. A bakin gada ta zauna tayi shuru, tunawa da tayi bata yi sallan mangarib da isha ba, da sauri ta mike ta nufi inda ta ga ruwa a kogi. Tana isa ta tsugunna a bakin kogin, muryan gardawa ta fara ji suna tunkaro inda take, da sauri ta waiga dan ganin su, su shida ne kuma kallo daya zaka musu ka gane a buge suke. Inda take suka nufo, alamun tsoro ne ya bayyana a fuskarta, da sauri ta mike dan guduwa, dayan ne ya sha gabanta yana dariya da fadin. “ Ga nama har gida yau.” Dariya suka kwashe da shi, ta gefe tayi zata gudu suka zagaye ta, a dan tsorace ta furta. “ Ku matsamin zan wuce.” Dariya suke daya na kama hijabinta, kan kame jikinta tayi tana cewa. “ Ku barni dalla ni ba irinku bace.” Dariya daya ya mata ya ce. “ Hahhhh… haba… ashe keeeee… ba iriiiiin mu bace… ya kamata ki zama irinnn mu kam.” Ya fada yana fuzgota da karfi zuwa jikinta. Ihu ta saka tana cizonshi a hannu, wanka mata mari yayi yana yage mata hijabi da karfi, bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba. Wurgar da ita yayi a kasa yana shirin hawa kanta, da sauri tayi burgima ta nufi bakin ruwan, jawo kafarta suka yi, ta naushe shi a kafa, da sauri ta mike tana kallon su, duk da dare ne sosai amma hasken wata ya haska fuskar su. Kafin kowa ya ankara daya daga cikinsu ya saka hannu ya tunkude ta cikin kogin, ihu ta saka tana fadawa ciki, kusan a tare suka ce. “ Kashe yar mutane kayi fa, kasan zurfi da kogin nan yake dashi.” Tuni suka wartsake daga mayen da suke, wanda ya yaga mata hijabi ne ya ce. “ Azumi ya hau kanka san tabbas ta mutu.” Shuru gaba dayan su suka yi, kafin wanda ya tunkude ta ya furta. “ Kuzo mu tafi kawai, anyi an wuce wajan.” “ Baaba wannan fa ba eya bane, mu gwada shiga ko zamu same ta mana.” Cewan wani daga cikin su wanda tun da suke maganar bai ce komai. “ Ba dani za’ayi aikin nan ba, kunga tafiyata, wanda zai biyo ni muje to.” Tafiya suka yi, dayan na juyawa yana kallon kogin.. *Hmmm nace kunga na muku typing kadan ko, yoo ai bakwa yin comments da like’s ne, kuma maganar gaskiya na zauna kusan awa uku, biyu ina typing, common comments bazaku iya ba😉 sai da ku. Muje a haka more comments da like more typing.* *DR TEEMERH✍🏼* 6- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 Gajeran labari Na Fatima Isa Manu DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU ) *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* *Page 6* Tafiya suka yi, dayan na juyawa yana kallon kogin, ji yake kamar ya koma ya duba ko ta na nan, tsayawa da tafiya yayi yana kallon baya. Juyawa suka yi ganin baya bin su, daya daga cikin su ya ce. “ Kazo mu tafi kafin police su iso.” “ To.” Ya fada yana bin su suka bar wajen, duk da kuwa hankalinsa bai kwanta ba. *SAIFULLAHI POV* Tun bayan fitansa daga gidan bai tsaya ko’ina ba sai gidan su, yana zuwa security suka bud’e masa get ya shiga yayi parking, ko kallon bangaren Mahaifiyarsa bai yi ba ya wuce apartment nasa ya shige. A falonsa da ya sha haduwa ya zauna ya rasa me yake masa dadi, idanunsa sunyi ja gashin kansa ya hargitse, dafe kai yayi yana tunanin abun da ya mata. Wayansa ne ta soma ringing, mantarwa yayi sai da yayi ringing sau biyu ana uku ya dauka ya manna a kunne ba tare da ya duba number ba. Muryan mace yaji tana sallama, sauke wayan yayi ya duba yaga number kafin ya manna ya amsa sallaman. Ta cikin wayan aka ce. “ Dazu an kirani bana kusa shine na kira.” Shuru yayi yana tunanin ma wa ya bawa wayansa, muryan matar ce ta katsai shi, da sauri ya tuna cewa Safeera ta dauka, hakan yasa ya ce. “ Sorry mistake din number nayi.” Matar na cewa. “ Ba komai nagode.” Da haka ya kashe wayan yana cilli da ita, tashi yayi ya shiga daki. *WAYE SAIFULLAHI?* Alhaji Amdaz Saifullahi shine asalin sunan Dad, haifaffan garin Maiduguri ne, Iyayensa ma ƴan garin ne, shi daya suka haifa daga shi kuma Allah bai sake basu haihuwa ba, ba masu karfi bane amma hakan bai hana su sa yaronsu a makarantar boko da kuma addini ba. Tun daga nursery school har degrees Dad yayi, haka ma saukan Al-Qur’ani, yana gama degree bangaren business ya fita da aikinsa, nan da nan kasuwanci ya budu Allah kuma yasa masa albarka a ciki. Sosai yake taimakawa iyayensa, haka ma yan unguwa, duk inda ka shiga idan kana aibanta shi sai an maka cha akai, sosai Al’umma ke son shi, gidajen mai yana da su kusan guda biyar, company ma haka ga albarkan iyaye na ta bin shi. Babban gida ya gina a unguwar Gomari, apartment guda biyar ya gina a ciki, nan ya kawo iyayensa apartment daya, shi ma ya zauna a daya, nan kuma Nanah ta fara damunsa kan cewa ya isa ya ajiye iyali yanzu, nan ya bata zabi kan cewa ta nemo masa wacce zai aura. Nanah taji dadin hakan inda ta tuntubi Baffa kan cewa yana da wacce yakeso Amdaz ya aura ne? Baffa ya bata wuka da nama ta nemo masa na aure, ita kuma ta nemo masa yarinyar kawarta wato Ummah, auren ko sati biyu bai kai ba aka daura, Ummah ta tare a gidan a apartment daya. Sosai zaman lafiya ke wakana a cikin gidan, Ummah tana bin umarnin Amdaz sawu da kafa, haka ma tana yiwa iyayensa biyayya dai-dai gwargwazo. Ana haka ne kuma Zazzabi ya kama Nanah, wanda ko kwana biyu bata yi ba ta ce ga garinku nan, Amdaz yayi kuka sosai wanda har ya zuba masa ciwon kai, haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau da dadi gobe babu. Ummah tayi shekara biyu a gidan amma ko batan wata bata taba yi ba, tun Amdaz baya damuwa har ya fara yi, sun je asibiti da dama amma abu daya suke fada musu cewa lafiyansu kalau yake. Ranar Amdaz ya samu Ummah ya ce. “ Amina zan kara aure.” Bata ce masa komai ba sai fatan zaman lafiyan da ta musu, duk da kuwa zuciyarta na mata zafi amma haka ta daure ta danne zuciyarta. A wata ranar Asabar aka daura auren Amdaz da Hafsat wato Mom, inda zaman lafiya ya burkice a gidan, dan kullum Ummah da Amdaz suna cikin masifa akan cewa baya adalci amma haka yayi burus da maganar. Mom sai da tayi shekara daya a gidan amma bata haihuwa, inda Amdaz ya sake shiga damuwa sosai har ya fara tunanin shine bashi da lafiya, amma sai ya samu Mom ya ce. “ Hafsat zan sake aure.” Ba tare da ko kunya ba ta fara kwashe masa albarka. “ Amdaz baka isa kayi aure ba, kai baka haihuwa amma kaman bunshuru kullum cikin aure.” Bai bi ta kanta ba ya fice daga dakin, washe gari kawai sai ji sukayi yayi aure, kusan karamin hauka akayi a gidan, amma Ummah ko fitowa bata yi ba. Baffa ya musu wa’azi da nasiha amma a banza dan yana gamawa Mom da Mummy suka cigaba da masifa. Tun ranar kuma Dad bai sake samun kwanciyar hankali ba, ana haka ne kuma ciwon ajali ya kama Baffa, satinsa daya a hospital ya rasu. Mom da Mummy kullum suna cikin masifa, Ummah idan ta musu magana sai su dawo da fadan kanta, hakan yasa suna farawa zata koma apartment nata ta rufe, ansha fasa TV a gidan ba adadi. Mummy tayi shekara daya a gidan Allah ya bawa Ummah ciki, wanda sai da Amdaz yayi murna sosai kamar zai kashe kansa dan dadi. Mom babu shege da ficen da bata yi ba dan cikin ya zube amma yaki fita, Mummy ma haka kullum tana cikin fita amma sunyi sunyi abun yaci tira, hakan yasa suka zubawa sarautar Allah ido. Cikinta ya cika watq tara ta haiho kyakkyawan yaronta, inda yaci suna Saifullahi wato takwaran Baffa suna kiransa da Saif. Yaron ya tashi cikin gata da jin dadi, gashi da shiga rai da wuri, kowa ya gani sai yaje wajensa, Mom kullum cikin bakin ciki take idan taga yaron, Mummy kuma ta kawo wani sabon munafurci kan cewa yaron a gurin ta zai na kwana. Ummah taki amma Dad ya yarda dan kwata baya jin maganar Ummah sai dai na Mummy da Mom, tana ji tana gani suka kwace mata yaro. Ranar girkin Mom musamman Dad baya fita ko’ina, Mummy ma haka komun aikin da yake dashi bazai fita ba, amma idan na Ummah ne sai dare yake dawowa, tun abun yana damunta har ta barwa Allah komai. Saifullahi yana da shekara biyar ya gudu daga gurin Mummy ya dawo gurin Mahaifiyarsa, abun ba karamin batawa Mummy rai yayi ba, da ta yiwa Dad magana sai yace ai yaro na kowa ne saboda haka ta barshi yaje ko’ina, inda ita kuma taci alwashi masu yawa akan shi. Saif an saka shi a Makarantar masu kudi na boko da islamiya, kuma yana da ilimi sosai dan duk abunda aka koya masa tsaf zai haddace, yana da shekara sha biyar ya kammala secondary school nasa, washe gari kuma yayi sauk’a. Dad da Ummah suka hada masa party da walima, wanda ya tara manyan mutane da yan kasuwa, kuma ya samu kyaututtuka masu tarin yawa da bangarori da dama. Dad ya turasa Egypt 🇪🇬 dan yayi degree dinsa a bangaren Law, inda ko shekaru biyar ba’a tara ba ya dawo da certificate, nan aka yi murna kamar ba gobe. Nan da nan gomnati ta dauke shi aiki a matsayin Lawyer, kaf borno sun san Barrister Saifullahi Safwan Saifullahi wanda yake yiwa kansa inkiya da Bar. SSS, ko plate number motan da yake hawwa da BAR. SSS ne a jiki. Sosai yake son iyayensa, haka ma kishiyoyin Mamansa, kyakkyawa saurayi mai jini a jika, ga kasaita da aji, sardauna kuma hamshakin mai kudi, ga saurin shiga ran yan mata. Yasha yankewa maza hukunci akan fyade, ciki kuwa har da abokinsa Yazeed, wanda suka yi Secondary tare. Duk inda kaga Saif zaka ga Ammar, tun da suka hadu a Egypet suka zama abokanai, dan tasu tazo daya kuma abu daya suka karanta. *DR TEEMERH✍🏼* 7- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 Gajeran labari Na Fatima Isa Manu DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU ) *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 7* Duk inda kaga Saif zaka ga Ammar, tun da suka hadu a Egypet suka zama abokanai, dan tasu tazo daya kuma abu daya suka karanta, sai dai Saif yana da ciwon zuciya mai zafi, sannan yana da BP amma idan ya tashi suna k’ok’arin control din shi. Tun Saif nada shekara ashirin da takwas ya daina ganin Ummah a matsayin mahaifiyarsa, dan yama daina kulata gaba daya ko gaisuwa baya had’a su, abun ba karamin burge Mom yake ba dan yanzu a gurin ta yake. Yana da budurwa mai suna Jannah, sun dade suna soyayya dan tun kafin ya tafi Makaranta, ko da ya dawo bai sauya zani ba, sai dai ya canza hali, dan idan suna hira sai ya taba jikinta, ta nuna bata so amma sai ya ce. “ Baki waye ba, idan kuma ba sona kike ba sai ki fadamin na sani, akwai mata dayawa zan iya son duk wacce naga dama.” Dake tana son shi sosai, sai ta bashi hakuri ta nuna yayi duk yanda yake so da ita, shi kuma ya samu dama har ya kai da sun kwanta tare, ranar Jannah tayi kuka sosai saboda tasan yanzu kam ba auren ta zai yi ba, kuma ba iyaye ne da ita ba. Ko da Saif yaga tana kuka sai ya tabe baki ya sha kunu yazo inda take ya ce. “ Kin ga ba kanki farau ba, kuma ba kanki karau ba, idan zakiyi

Chapter 2 of 17