shawararta ta ce, “ Kin kalli mutumin da yazo ko”
“ Eh na ganshi”
Mama ta jinjina kai sannan ta ce, “ Aurena yakeso yayi”
“ Aure kuma Mama?”
“ Haka dai yace Wallahi”
“ Amma ke me kika ce masa?”
“ Shine nazo muyi shawara dai, yace gobe zai dawo, har ya bani kudin nan” ta nuna kudin da ta bawa Falmata.
Numfashi Falmata ta sauke sannan ta ce, “ To Mama idan ya kwanta miki kuma kinji zaki iya zama dashi ko yana dashi ko bayi dashi, sannan kin yarda dashi ina ga mu bamu da matsala, dan inaga Allah ne ya turo mana da sauki”
“ Falmata matsalan shi ne bansan ko zai iya rike min ku ba, kuma a halin da ake ciki yanzu duk wanda bazai iya rike min ku ba banga amfanin auren ba, dan yanzu ku zan aurar ba ni zanyi aure ba, duk da auren yanzu ya zama abun tsoro, ki dauki misali da Raudah har yau babu ita babu labarin ta”
Falmata tayi shuru jikinta yayi sanyi, ta dubi Mahaifiyar nata da matsayin Kawa wanda zasu iya zama suyi hira ta ce, “ Ki tambaye shi gobe idan yazo din, idan ya yarda zai rike mu shikenan, ni nafiso ma kiyi auren Mama ko su Ammi da Nabila zasu samu rayuwa mekyau”
Ta jinjina kai sannan ta ce, “ To Falmata Allah ya kaimu goben,” ta karashe tana kallon Nabila da ta shigo da ludayi a hannunta, Falmata ta amsa da Amen tana kallon su Ammi da Umar ta ce, “ Ku zauna mu sha”
*BAFFA*
Ko da ya dawo gida bai dubi inda suke ba yace su hada kayansu anjima zasu tafi sabon gidan.
Hakan kuwa akayi, ko chokali basu bari ba kaf suka tattari kayan su dan Baffa rufe ido yayi yace babu abunda zai siya musu gwara su tattari kayansu su tafi dashi.
Hadaddan gida ne me dauke da apartment guda uku, kuma ko wani bangare da kayaki a ciki, abunda yayi mugun birge Baffa kenan, dan har kayan kitchen akwai komai da komai, ga ruwa available.
Inna ta dauki na gefe, Baffa ya ce shi yanzu a na tsakiya zai zauna dan zaiyi aure, Inna da Jannah suka bishi da Allah ya bada zaman lafiya.
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA❤️🩹*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 42&43*
*BOOK TWO*
Inna ta d’auki na gefe, Baffa ya ce shi yanzu a na tsakiya zai zauna dan zaiyi aure, Inna da Jannah suka bishi da Allah ya bada zaman lafiya, ba kunya ba tsoron Allah ya amsa da, “ Amen idan da gaske kuke”
*SAFEERA POV*
Sai guraren mangarib kafin ta farka daga baccin da ya dauke ta, rama sallan da ake binta tayi sannan ta gyara d’akin ta shiga tayi wanka, riga da wando ta saka na sanyi, ta saka gashinta cikin hulan, sannan ta feshe jikinta da turarensa masu kamshi ta sauko falo.
Ido hudu suka yi da shi yana zaune akan two seater yana danna wayansa, ya sakar mata murmushi yana karewa jikinta kallo ya ce, “ Irin kyau haka”
Ta iso tana cewa, “ Kawai dai ka fada ne, riga ce fa da wando” ta samu guri ta zauna kusa da shi, ya ajiye wayan a gefe yana mayar da hankalinsa gareta, ya daura hannu akan cikinta da yake kwance luf ya ce, “ Kinyi kyau fa”
Murmushi tayi wanda ya saka kyau dinta sake fitowa, “ Duk daga gare ka ne kyau din”
“ Anya ma kinci abinci kuwa?”
“ Bansan inda kitchen yake bane, kuma bansan ko akwai kayan abinci ba shiyasa ban girka ba”
Hararan wasa ya mata sannan ya ce, “ Sai kace kin iya”
Turo baki gaba tayi tana kawar da kai gefe ta hade rai, “ Na iya mana, lokacin da nake gida ni da Raudah muke girki”
“ Oh kawai ki ce kwararriyar mai girki nake zaune da ita ban sani ba”
Ta saki murmushi tana kallon gemun shi da yake dauke mata hankali ta ce, “ Eh fa, idan na maka girki kamar ka cinye hannunka”
Ya kama hannunta yana daura akan gemun ya ce, “ Alamu sun nuna dai birgeki yake”
Kunya taji sai ta cire hannunta tana cewa, “ Kyau kawai yake min”
“ Ban yarda ba, sha’awar shi kike ko?” Ya kashe mata ido daya.
Saurin sauke idanunta tayi daga gare shi tana girgiza kai, ya matso daf da ita har numfashin su yana haduwa, ya hura mata iska cikin kunne ta yana sauke numfashi, da sauri ta matsa ta soma wasa da yatsunta, ya kalle ta yana murmushi ya ce, “ Tashi muje kiyi abincin inga ko zan iya cin jagwalgwalen naki”
Kamar jira take a ce tashi, ta mike da sauri tana nufan hanyar da tasan shi ne kitchen din, ya girgiza kai yana damke cikinsa da yaji yana son fara masa ciwo sannan ya taso ya biyo bayanta.
Karewa kitchen din kallo tayi tana bud’e fridge na farkon, duk wasu abunda suka shafi kayan miya ne a ciki, daga kan nama, kifi, har zuwa su tomatoes komai akwai, gurin da taga roba taje ta d’auko yana kallon ta, kifin ta diba tana sakawa a cikin robar, sannan ta d’auki naman ta juya ta kalle shi ta ce, “ Kana cin nama?”
“ Eh”
Shi ma ta saka tana ajiyewa a wurin wankewa ta fara wanke shi, ya tako zuwa inda take ya tsaya ta bayanta ya ce, “ Na taya ki?”
“ Idan zaka yanka min albasa inaso, idan bashi ba banason tayin”
Yayi murmushi yana sako hannunsa ta cikinta ya mannata da jikinsa, tayi saurin sakin naman dake hannunta ta ce, “ Albasan fa yana fridge”
Shinshinar wuyanta ya fara yana manna bayanta dai-dai wajen maransa ya ce, “ Uhm nasani” jin be sake ta bane kuma bai dena yin abunda yake bane ta ce, “ Ni kaje ma na yafe tayani aikin”
“ Uhm uhm zan tayaki” ya sakar mata kiss a wuyanta yana yawo da hannunsa cikin rigarta, kamar zatayi kuka dan tasan karshen labarin ba barinta zaiyi ba, “ Ka bari na gama girkin to”
Numfashi ya sauke yana cire hannunsa daga rigarta ya ce, “ Nasan guduwa zakiyi idan kika gama”
Tayi saurin matsawa daga jikinsa tana sunkuyar da kai ta turo baki gaba, da idanunsa da suka canja zuwa ja ya matso ya ce, “ Haka mijin naki yake sai jarabar masifa da rashin hakuri, daurewa zaki yi”
Bata kalle shi ba tayi murmushi kawai tana cigaba da wanke naman, kujeran da yake kitchen din yaja ya zauna yana binta da kallo yanda take aikinta cikin nutsuwa, shi ya yanka mata albasan ya kunna gas, suna dan taba hira wanda yawancin hiran duk shi yake sakowa, da haka har ta kammala girka shinkafa da miya.
Ya taso ya kashe mata gas, sannan ya wanko plate ya tsaya kamar wani mabaraci, ta yi murmushi ta karbi plate din ta zuba masa, ya koma wajen kujeran ya zauna ya fara ci, wanke kwanukan da ta bata tayi sannan ta zauna tana kallon shi.
Sai da yayi rabi ya d’ago ya ce, “ Abincin yayi dadi sosai” ta lumshe ido tana bud’ewa, ya bata rai ya ce, “Me yasa bakya ci”
“ Bazan iya ci bane, bai min ba”
Ajiye chokalin hannunsa yayi ya rike hannunta ya ce, “ Me za ki ci?”
“ Kalaba nake kwadayin sha”
“ Me kalaba kuma?” Dan shi har ga Allah bai san wani abu wai shi kalaba ba, “ Wani zaka gan shi kamar k’asa haka a mulmule”
“ Ni ban taba ganin shi ba, sai yau ma naji sunan”
“ Shikenan kawai” ta cire hannunta daga nashi tana shirin mikewa, da sauri ya riketa yana fad’in, “ Wifey kimin bayanin yanda yake sai na nemo miki”
“ Na fada maka yanda yake a mulmule kamar tabo, akwai kuma na cimintin shi, masu ciki suna yawan shan irinsa”
“ Ohhh ki ce min farin qasa” ya fada yana dariya, ta bata rai ganin yanda yake mata dariyan ta ce, “ To me na min dariyan?”
Tafin hannunsa yasa yana rufe bakinsa, ya ciro wayansa ya lalubo number Jon ya kira, yana dauka ya ce, “ Farin k’asa zaka siyomin a bakin general hospital na dubu biyu”
“ Ok Sir”
Ya mayar da wayansa cikin aljuhu yana mai cigaba da cin abincin dan ya kai masa yanda yake so, duk loma dayan da zai kai sai ya kalle ta, haka har ya kammala cin abincin ya tashi suka fito falo.
*BAFFA POV*
A bakin kangon ya paka motansa, sannan ya fito yana sanye da wata shadda blue wanda yasha dinkin zamani, ya saka takalmi sahu ciki baki, ya mayar da wayansa wanda ke nade da lobari cikin aljuhu sannan ya doka sallama.
Nabila da ta fito fitsari ne ta leko ta ganshi tsaye, tayi saurin komawa ta samu Mama da Falmata suna zaune ta ce, “ Mama mutumin jiya ne yazo”
Suka kalli juna kamar wasu kawaye,” Je ki ce tana zuwa” Falmata ta fada tana tashi da sauri fuskarta dauke da farin ciki.
Nabila ta juya dan cika aiken da aka bata, Falmata ta d’auko hijab dinta milk colour ta mik’awa Mama dan shine me dama-dama a ciki, ta ce, “ Mama ki saka” Mama ta karba ta saka tana cewa, “ Naga farin ciki kike fa Falmata”
“ Allah ya aiko mana da sauki taya bazanyi murna ba, yanzu matsalan ma shine babu turare, da kin saka mun dan tashi kanshi da kamshi”
Tayi murmushi tana girgiza kai, ta fara tafiya Falmata tayi saurin dakatar da ita ta ce, “ Tsaya na gyara miki fuskar” bayan ta gama ne ta saki murmushi, “ Mamana kinyi kyau,”
“ Bana son shirme fa” ta mata dariya tana matsa mata ta wuce.
Ta koma ta zauna tana fatan Allah yasa ya taimake su dan suna halin matsin rayuwa.
A waje kuwa Baffa yana tsaye Nabila ta iso, ta durkusa har k’asa ta gaishe shi, ya amsa hakoran nan a waje, ta ce tana zuwa ta mike dan komawa, Baffa ya dakatar da ita yana mik’a mata dubu biyu ya ce, “ Gashi a siya ko minti ne”
Nabila ta amsa tana murna ta koma ciki, minti kadan sai ga Mama ta fito, ya sake washe baki yana cewa, “ Kaga uwar marayu har ma masu uwa”
Mama ta danyi murmushi, “ Ina wuni Alhaji”
“ Ahhh lafiya kalau, ya yaran namu,” su ka dan gaisa suka taba hira, Baffa sai washe baki yake yana dariya, sannan Baffa ya ce, “ Ya maganar namu? Ina ta kwana?”
“ Nayi shawara, amma ban san ko zaka iya rike min yarana ba tun da kaga marayu ne, kuma ba wasu suke da shi ba da zan kaisu, idan zaka iya ciyar da su da tufatarwa”
“ Idan ta wannan ne ba matsala a wurina, ai yaranki yarana ne, kuma yara ai na kowa ne… idan kin amince zaki aure ne duk me sauki ne”
Mama taji sanyi a ranta tana hamdala a zuci, sannan ta ce, “ Allah ya shige mana gaba”
“ Amen,,,, ni dai yanzu Ina da Mata da yarinya budurwa guda daya, kuma a gida daya zan ajiye ku”
Mama ta jinjina kai tana tunanin zaman da tayi a baya da kishiyoyi da irin tabon da suka mata a rayuwa, ta tuna ta sanadiyar Fauziyya Kausar tabi duniya, ta sauke wata ajiyar zuciya ta ce, “ Ba matsala”
Baffa yayi murna sosai, sannan suka yanke yaushe za’a daura auren, dan su yanzu ba yara bane da zasu jira sai manya sun saka baki, balantana ma Mama ba iyaye bane da ita, haka ma Baffa, suka yanke nan da kwana uku za’a daura auren wanda zai kama ranar jumma’a, ya tambaye ta sadakinta ta ce ya bada dubu hamsin, a take ya bata, lefe kuma yace sai tazo zai hada mata.
*FAUZIYYA POV*
Tun da taji abunda ya faru da kawarta kuma aminiyarta Mummy sai ta tsorata, ta tattare kayanta kaf ta hau mota a tsakar daren ta bar garin.
A hanyarta na Maiduguri zuwa Yobe motansu yayi hatsari da wata tifa, kaf motan babu wanda ya tsira da rai, dan motan da wuta ya kama kuma cikin dare ne, hakan yasa babu wanda ya taimake su.
Sai da safe tayi kafin aka samu k’asussuwansu, aka dauki number da suka rubuta a takarda wanda ake bari a tasha aka kira mutanensu, aka sanar da abunda ya faru, Ummah Fauziyya aka kira number Mummy amma a kashe.
Haka aka tattari kasussuwan nasu aka binne.
*DAD*
Ba laifi jikin nasa ya samu sauki sai dai bai farfado ba, amma koman shi normal.
Ummah ce ke kula dashi 24/7 tana tare da shi, duk wani motsinsa akan idanunta yake, yau ne ma taga yana motsi sosai ba kamar kullum ba.
Tana zaune akan sallaya bayan ta idar da sallan Azahar tana jan charbi, taga yana motsi da hannunsa yana son bude idanunsa, da sauri ta tashi daga wajen ta koma kusa dashi tana kallon shi.
A hankali ya soma bude idanunsa bakinsa na rawa kamar yana fadar wani abu, Ummah ta matso da kunnenta kusa da bakin nasa dan taji me yake cewa, sunan Mom yake kira hawaye na gangarowa ta gefen kuncinsa, yana faman kiran “ Hafsa!! Hafsa!!!
Idan kunyi likes nayi wani gobe idan bakuyi ba adoii idan nayi😂😂😂
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA❤️🩹*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 44&45*
*BOOK TWO*
A hankali ya soma bud’e idanunsa bakinsa na rawa kamar yana fad’ar wani abu, Ummah ta matso da kunnenta kusa da bakin nasa dan taji me yake cewa, sunan Mom yake kira hawaye na gangarowa ta gefen kuncinsa, yana faman kiran “ Hafsa!! Hafsa!!!”
Hannu tasa ta goge masa hawayen, ta soma karanto masa duk addu’oin da ya shigo bakinta tana tofawa, kusan minti biyar a haka kafin ya bud’e idanunsa yana sauke su akanta.
“ Alhaji ka tashi!!! Ya jikin naka? Bari na kira likita da sauri” ta mike da sauri, ya saka hannu ya rike nata yana magana a raunane wanda kallo daya zaka masa kasan akwai abunda yake damunsa.
“ Kun taba neman abu kun rasa daga gareni Amina?”
Ta zauna tana girgiza kai hawaye na zarya akan kuncinta, “ Alhaji ta lafiyanka muke yanzu, dan Allah ka bar maganar nan”
“ Amina tambayanki nake?”
“ Bamu taba neman abu mun rasa ba, komai kana mana ko da bamu tambaya ba”
“ To meyasa Hafsa zata min haka? Mesa ta bukaci ta tozartani a idanun duniya, meyasa ta zubarmin da mutuncina? Me na mata da zafi? Ko na kuntata mata ne?” Ya ja wani numfashi yana saukewa a hankali, ya lumshe ido yana jin yanda zuciyansa ke masa radadi.
*Bayan kwana biyar*
*SAFEERA POV*
Yusrah zata zo da sunan wai bata magani, sai dai bashi take yi ba hankalinta yana kan Saif, duk motsin shi akan idanunta, har ya kai da Safeera ta fara ankara da kallon da take masa.
Yau ma suna zaune bayan Yusrah ta bata magani, sai ta zauna wai zata huta kafin ta tafi, Safeera bata ce mata komai ba ta tashi ta nufi kitchen dan daura abincin da za’a kaiwa Dad da Ummah a asibiti.
Tana cikin girkin ne taji sallaman shi daga falo, kafin ta amsa ta fito taji Yusrah na cewa, “ Ina wuni yallabai, ya gajiya,”
Ya amsa bata ba yabo ba fallasa yana kiranta, “ Wifey?”
Ta fito daga kitchen tana watsawa Yusrah kallon banza ta ce, “ Sannu da dawowa,” ta isa da sauri tana rungume shi kam ta sumbace shi a kumatu.
Yusrah ta kawar da kai tana hadiye wani yawu me kauri, shi ma ya sumbace ta a goshi, “ Naji kamshi na tashi hala dai girki kika yi?”
“ Eh ma su Dad nayi wa”
“ Anjima zasu dawo fa, ba kin huta abun ki, kina so kina bawa babyn mu wahala ne,” ya shafa cikin nata yana murmushi.
“ Nama gama fa,”
“ Muje na gani ko yayi dadi,” suka nufi kitchen.
Yusrah ta bisu da kallon tsana tana jin kamar ta kashe Safeera, ranta a bace ta dauki jakarta ta fice har tana k’ok’arin fadi dan kishi, ta isa wurin parking ta tsaya tana zubawa Sageer ido.
Ya kwashe da dariya har da tafawa,“ Ya dai malama? Kina min kallo sai kace ni na hana Oga ya ganki ko ya kulaki”
Ta kule amma sai ta danne ta gyara handbag dinta, ta masa kallon up and down, “ Kai ka sani kuma, hospital zaka kaini na gama aikina nima na huta da haduwa da karuza irinka,”
Bai ce mata komai ba ya dubi Jon ya mik’a masa key na mota ya masa magana wanda iya su biyu suka ji abun su, Jon ya gyada kai ya tada motan ta shiga, mai gadi ya wangale get duka fita.
Suna barin unguwan yayi parking a gefen titi, kafin tayi magana ya daka mata tsawa, “ Get out,” ba maganarsa ba iya kallon shi ya isa aji tsoron shi, dan zubin samudawa Jon yake da shi.
Jikinta har rawa yake ta dauki handbag nata ta fice, yaja motansa ya koma gida.
Yusrah kamar tayi kuka haka ta ta tsayawa a rana har machine yazo ta shiga.
*MOM POV*
Yanda babu wanda yasan da zamanta a gidan, haka itama ta zauna a bangaren ta ita kadai, ko fitowa bata yi, tun ranar da tayi casting ta rufe kofanta har yau bata bud’e ba, bata san me yake wakana a gidan ba, kuma taji shuru Dad bai zo ya sallame ta ba.
A rana tana canja pad sau biyar dan yanda farin ruwa me wari yake fita ya ishe ta ishara, ta rana me yake mata dadi, ta rame tayi baki ga manyan kuraje a jikinta kamar chickenpox, sai taji yunwa yana neman rayuwarta sannan zata tashi ta hada shayi tasha, haka take ta rayuwa.
*MUMMY POV*
An rubuta statement an mika su kotu, idan laifin Mummy na kisan kai ne, da k’ok’arin sake kashe mutum har an kai masa hari.
Sauran kuma yan ta’adda ne, hakan yasa Saif baiji kunyar yanke mata hukunci dai-dai da abunda tayi ba, kuma baiji kunyar gani ita matar ubansa bane, yayi saurin yanke hukunci kafin mahaifin nasa ya dawo gida.
Ya yankewa Mummy hukuncin zaman gidan yari na shekara uku, sannan a mata daurin rai da rai, sauran kuma ya tura su gidan gyaran hali har na shekara goma nan gaba, Mummy tayi kuka sosai ganin babu tausayi Saif ya yanke mata hukunci, haka aka saka ta a mota aka wuce dasu gidan gyaran hali.
*BAFFA POV*
Sai ka ce budurwa zai auro duk yabi ya rude, sai jeka ka dawo yake kamar sabon kwarto, ya saka an gyara bangaren da zai ajiye Mama me kyau, an goge komai an kintsa komai, ya zuba kayan abinci enough.
Sai jeka ka dawo yake shi a dole yana so ya kulal da Inna, ya buga shadda fari wanda ya saka Musa tela dinka masa, ya fito daga bangaren shi ya shiga na Inna yana faman daga murya, “ Kadde har yanzu adawa ake min ban sani ba, ina murnan zanyi aure ana min hassada”
Jannah dake zaune akan kujera ce ta juyo tana kallon Baffan nata, tana sanye cikin shadda maroon dinkin bubu, tayi kyau haskenta ya sake fitowa, har wani jiki ta danyi, ta saki murmushi ta ce, “ Haba dai Baffana, waye zai mata hassada ana zaune kalau, daga ni har Innata murna muke maka”
Inna da ta fito daga hanyar kitchen ce tana fadin, “ Atoh fada masa dai Jannah, mu ai gaba ta kaimu”
Baffa ya tabe baki ya ciro bandir na dari biyar ya mikawa Inna, ta amsa tana kallon kudin, ya ce, “ Kudin danna kirji ake cewa ko” sannan ya juya zai fita ya ce, “ Sai a mana addu’a da zuciya daya zamu je daurin auren”
Kusan a tare Jannah da Inna suka furta, “ Allah ya bada zaman lafiya”
Ya amsa da Amen yana fita.
Inna ta zauna ta zuba tagumi, tasowa Jannah tayi daga wurin da take tazo ta zauna kusa da Mahaifiyar ta ta tace, “ Inna ki roki Allah ya hada kanku, ki dena tagumin nan bashi da amfani, ina ji a jikina wacce za’a kawo bazata sakaki kuka ba”
“ Allah yasa Jannah”
Jannah ta amsa da Amen, ta ringa bata dadin baki har Inna ta wartsake, sannan ta mike ta koma dakinta.
Tana shiga ta fada kan gado tana lumshe ido, wai dama zata cigaba da farin ciki a rayuwarta, ashe dama rayuwarta zai canzu ta silan Saif, kenan shi ne farin cikin rayuwarta?
Ji tayi zuciyarta tana kewarsa, hakan yasa ta dauki wayanta nokia ta lalubo number shi tana kira.
********************
A masallacin unguwa da suke zaune aka daura auren Baffa da Mama, inda Limamin unguwan ya zama alwalin Mama, Baffa kuma ya dauko limamin unguwan da suka zauna a baya, shi ya zama alwalin shi, aka daura aure aka shafa fatiha.
Umar ya shigo da gudu yana tsalle yana fadin, “ Wallahi an daura auren Mama da mutumin”
Ihu Nabila da Ammi suka saka suna tsalle suma, Falmata ta fito sanye da hijab tana fadin, “ Ashe baku da hankali ban sani ba, haka zaku dinga masa a gidan inda munje? Ashe kuwa zaku zauna a nan”
Suka yi shuru Nabila na fadin, “ Anuty Falmata kiyi hakuri bazamu sake ba”
Taja tsuki ta koma wajen Mama tana fadin, “ Kuma sake”
Mama tana zaune tayi shuru tunanin duniya ya ishe ta, taji muryan Falmata na cewa, “ Mama tunani idan ya miki yawa ciwo zai saka miki fa”
Ta sauke numfashi, “ Falmata ina tunanin wani rayuwa zamu sake shiga ne”
Falmata ta cigaba da hada kayansu, dan Baffa yace ana daura auren zasu tafi, ta girgiza kai ta dubi Mama, “ Ki roki Allah ya baku zaman lafiya, mu kuma In Sha Allah ba zamu taba jawo miki magana ba”
Kafin su sake cewa wani abu ne suka ji muryan Baffa daga waje yana tambayan Umar,” Ina Maman taku kaje kace su fito mu tafi”
Umar yayi gudu ya shigo yana fad’in,” Mama inji mutumin wai ku fito mu tafi sabon gidan namu”
Falmata ta dankwale shi da hannu ta ce, “ Ubanku ne fa ba mutumin nan ba! Shege shine sabon mahaifin namu”
Unar ya tukudo baki gaba yana guna-guni, Mama ta ce, “ Ma Falmatan kake yi wa haka?”
“ Bar shi Mama ni da shi Wallahi, naga kwana biyun nan yana ji da sabon balaga ne”
Jin abunda ta fada ne yasa Umar kyelkyalewa da dariya yana maimaita sunan, ya fice da gudu yana dariya, Mama da Falmata suka kimtsa kayan da zasu dauka suka fito, Mama sai wani jin kunya take kamar sabuwar bazawara.
Baffa ya saki murmushi yana washe hakora, ya bude mata gaban mota ta zagaya ta shiga, sauran kuma suka shiga baya.
Baffa ne da Umar kawai suke hira, sauran kuwa duk sunyi shuru har aka iso kofar gidan, suka zubawa get din gidan ido, Baffa na sauqa yaje ya bude get, sannan ya koma ya shigo da motan.
A tsakiyan gidan ya danna parking yana buga wata uwar horn
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 17