Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka shiga shi kuma ya shiga mazaunin driver, aka wangale musu get mota na gaba na security sai nasu na baya ma na security’s. Shuru motar yayi kowa da tunanin da yake yi, katsai shuru yayita hanyar tambayar Sageer. “ Kun gano wadan da suke binmu ne?.” “ Sir ba’a gano komai game da su ba, amma…” burki ya danna da karfi sakamokon motan gabansun da ya kaucewa wani mota fari. Kafin su ankara aka fara kai musu harbi ta ko’ina, da sauri Sageer ya ce. “ Ku sunkuya k’asa.” Janyo Safeera Saif yayi suka zube k’asa. Motar da su Saif suke ciki suka nufa da gudu suna harbi, wasu mutane ne kusan su biyar ko wannen su hannunsa da bindiga yana harbi, motar Saif suka nufo gadan gadon, security’s nasa ne suka fito suma suka fara kai musu harbi, bindiga Sageer ya ciro ya saka harsashi a ciki zai fita Saif ya ce. “ Sageer ka kula.” Jijjiga kai yayi ya fita da gudu daga motar yana harbi, kuka Safeera ta fashe da shi tana toshe kunne, jawota jikinsa yayi yana rungume ta tsam. Jiniyar motar yan sanda ne ya kewaye gurin da ambulance 🚑, ajiyar zuciya Saif ya sauke ya ce. “ Kukan ya isa haka. Numfashi ta fara saukewa tana rage kukan nata. A waje kuwa harbi suke kaiwa junansu ko tausayi babu, an kashe security’s guda uku yayin da aka kama daya daga cikin yan ta’addan. Sageer kuma an harbe shi a ciki ta gefe, sai jini yake zubarwa. Y’an sanda suna zuwa yan ta’addan suka gudu, mota daya ya bisu na sojoji har hanyar da suka yi. Motar Saif dan sandan ya bud’e yana sara mishi, fitowa yayi hannunsa rike da nata, ganin Sageer a kwance cikin jini ne yayi mugun d’aga masa hankali, da gudu ya saki hannun Safeera ya nufi inda Sageer yake kwance. Fito da gadon daukar mara lafiya akayi, inda Sageer yake kwance suka nufa suna daurasa akan gadon, suka shigar da shi Ambulance aka wuce da shi asibiti. Komawa gurinta yayi ya ja hannunta suka shiga mota suka bi su. Direct emergency aka wuce dashi ganin yanda jini yake zuba. Zama Saif yayi yana jawo Safeera kusa da shi, duk ta rude ta kidime kana tabata zata furgita. *DAD POV* Yana zaune a falo kusan karfe bakwai da rabi yana kallon labarai, nan aka manna hoton Saif ana fadar yan ta’adda sun tare shi a hanya har anyi asarar sara rai uku, sannan an kai mutum daya asibiti. Da sauri Dad ya mike yana furta. “ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un.!!!” Ummah da shigowarta kenan taga labarin ta fashe da kuka tana fadin. “ Sun kashe min yaro.” Da sauri Dad ya danna number Sageer amma ba’a dauka, number security wanda yake bin Saif yayi shima ba’a dauka ba. “ Hasbunallaha wani’iman wakil!!!!!!!!. “ Abun da ya ta maimaitawa kenan. Ummah kuma sai kuka ta rasa me ke mata dadi, number Saif Dad ya kira amma yana ta ringing ba’a dauka ba, sau biyar yana kira ba’a dauka ba. Number Ammar ya kira, ko ringing bai gama yi ba Ammar ya dauka, Dad ya fara fadin. “ Ammar kuna tare ne?.” Ammar da yake tuki shima a rikice zai je asibitin ya ce. “ Dad yanzu nake hanyar zuwa gurinsa.” “ Wani hospital ne?.” “ TH ne.” Ammar ya fada yana kashe wayan, a 360 ya tafi zuwa hospital din. Bai tsaya jiran komai ba Dad ya nufi hanyar fita da sauri Ummah ta shiga ta dauko hijab ta biyo shi, security’s duk sunji abunda ya faru hakan yasa da Dad da Ummah zasu fita mota hudu ne ya musu rakiya. *MUMMY POV* Ta kasa zaune ta kasa tsugunne, number wayansu take ta kira amma ba’a picking. Cilli tayi da wayar ta koma ta zauna, Radiya ce ta shigo da gudu tana kuka tana fadin. “ Mummy sun kashe Saif.” Da sauri Mummy ta mike tsaye tana cewa. “ Ina gawarsa din to?.” “ Mummy yana asibiti yanzu su Dad suka tafi Ummah tana ta kuka.” “ Ayya!!! Abun tausayi.” Mummy ta fada tana dan murmushi. Da kallo Radiya ta bita ta ce. “ Mummy nasan da sa hannunki a ciki, amma bakomai akwai Allah, ki jira sakayya.” Ta karashe tana fita daga parlon. Tabe baki Mummy ta yi ta bude fridge ta dauko rufaida da ruwan sanyi ta zauna ta fara sha tana lumshe ido, wayanta da tayi cilli dashi ta dauko ta dannawa kawarta kira wato Fauziyya. Tana dauka ta ce. “ Yanzu nake ganin labarai wai Saif ya mutu?.” Dariya mai sauti Mummy tayi ta ce. “ Eh haka ne.” “ Kawata ke kika kashe shi ko?.” “ Tabbas ni ne nan na kashe dan banza, kisa me kyau ma.” “ To yanzu ribar me kika samu?.” “ Ribar raba gado mana, kinga dai-dai gadonmu zai zama da ita uwarsa din.” “ Hhhhh kawata kenan.” Fauziyya ta fada tana kashe wayan. Da ido Mummy tabi wayan tana tabe baki. *FAUZIYYA POV* Dariya ta kyalkyale dashi tana fadin. “ Yanzu zaki gane shayi ruwa ne, hhhh ki jira zuwana kawai dan sai na kaiwa Safwan voice din nan yaji, idan yaso ya sake ki ni ya aure ni.” *MOM POV* Tun bayan barowanta bangaren Saif take jin wani wari yana tashi a jikinta, ga gabanta din da take jin yana fitar da ruwa da bata gane kansa ba. Toilet ta shiga ta cire kaya dan duba meke tafiya. Ihu ta saka lokacin da idanunta ya sauka akan tsutsotsin da suke jikin pant dinta. “ Na shiga uku na mutu na lalace, wai meke faruwa da ni ne.” Ruwa ta zuba ta fara wankewa amma baya raguwa sai ma sake fitowan da yake yi. Ga dauri ta saka pad ta saka doguwar riga ta nufi hospital a haukace. Tana shiga taga motocin su Dad da Saif, bangaren female ta nufa da sauri dan kar su ganta, tana shiga ta samu likitan da take zuwa gurinsa karban maganin abotion. Yana ganinta ya fara washe baki dan yasan yana samun kudi a gurinta. “ Hajjaju makkatin.” Cewan Dr Ubaidu. “ Bata wannan nake ba Dr ka duba lafiyata tun daga sama har k’asa, ka min general checkup.” Ta fada a rikice tana zama a kujera. “ Ok.” Ya fada kafin ya dauko syringe 💉 ya dibi jininta. Abun ka da kudi tuni ya kai lap aka fara gwaje-gwaje dan tace a take take son result. *SAIF SAF POV* Ko motsin kirki bata yi, tuni zazzabi mai zafi ya rufeta, ko matsawa daga jikinsa ta gagara. Dubanta yayi ya ce. “ Zazzabi ya kama ki.” Bata ce komai ba sai sake shiga jikinsa din da take yi tana fitar da zazzafar numfashi, hannu ya daura a wuyanta jin zafi yasa ya furta. “ Subhanallah.” Daukarta yayi cak zai nufi emergency da ita, dai-dai lokacin da Ummah da Dad suka shigo. Har da dan gudu Dad ya saka ya iso gurinsa, kallon su yayi ya ce. “ Dad Ummah me ya fito daku a wannan yanayin?.” Ummah ta kalle shi ta ce. “ Saif cewa akayi fa ka mutu.” “ Ummah idan ma na mutu ai sai ku jira a kawo muku gawata, amma a wannan yanayin zaku fito da ba’a san wadan da suka aikata laifin nan ba.” Ya karashe a fusace. Cike da tausayi Dad ya ce. “ Saif Ubanka, ko baka ji ba?.” Kau da kai yayi yana k’ok’arin shiga emergency din. Wani Doctor ne ya iso yana cewa. “ Sir ba zaiyu ka shiga ba.” Wani kallo ya masa ya ce. “ Ita da bata da lafiya fa?.” “ Sorry Sir amma ga daki a gefen nan za’a iya kwantar da ita a duba lafiyarta.” Nufan dakin yayi su Dad na binsa, wasu daga cikin security’s da police suka bishi yayin da sauran suka tsaya a kofar emergency. *Idan kunyi comments na muku gobe idan ba kuyi ba na barku ku huta🙌* *DR TEEMARH✍🏼* 18- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 _Gajeran labari_ *Na* *Fatima Isa Manu* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_ Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 18* Nufan dakin yayi su Dad na binsa, wasu daga cikin security’s da police suka bishi yayin da sauran suka tsaya a kofar emergency. Kwantar da ita yayi akan gadon yana zama a gefe, nurse din ta duba ta kafin ta mata allura na hutu, nan da nan bacci ya dauke ta. Dad na fadin. “ Saif su waye suka kawo maka harin ne?.” Numfasawa yayi sannan ya ce. “ Dad ya kai 8-9 months ana bibiya na, and bansan wane ne bane, da farko da suka ga mun gane sai suka dauke k’afa, to dazu da zan fita dan siyo mata kayan sawa naga mota baki na bin mu, nan muka canja hanya, a tunanin mu sun tafi, kawai fitowar da zamuyi sai gani mukayi an kawo mana hari.” Ya nunfasa ya ce. “ Dad Wallahi nayi rantsuwa duk wanda na tabbatar da sa hannunsa a lamarin nan sai na yanke masa hunci dai-dai da abun da ya aikata.” “ Allah ya shige mana gaba kawai.” “ Amen.” “ Amma yanzu ana bincike ko?.” “ Eh an kama guda daya sauran kuma sun gudu, to ta hanyar wannan za’a kama sauran idan har suna cikin garin nan.” Ummah ta zauna kusa dashi tana rike hannunsa, kallon ta yayi kafin ta ce. “ Saif kana addu’a dan tabbas kana da makiya, kuma kasan irin aikin ka ta iya yiwa akwai masu bibiyarka baka sani ba.” “ In Sha Allah Ummah, amma ni babu wanda nake zargi gaskiya.” Doctor ne ya shigo suka juya suna kallob shi. “ Sir anyi nasaran ciro bullet din, sannan an samu numfashinsa ya dai-daita, sai dai yana buk’atar jini.” “ Babu a nan ne?.” “ Akwai amma da tsada dan jinin mai wahalan samu ne.” “ Don’t worry about the money, ko nawa ne za’a siya ku karbo ku mana aiki bani acc din da zan tura kudin.” “ Ok.” Nan ya karanto masa Acc number ya tambaye shi nawa ne kudin ya fada masa, nan ya saka har da k’ari ma. Suna zaune a dakin bayan dr ya fita wani security ya shigo, kallon shi Saif yayi ya tambaya ko lafiya. “ Sir wata ce take son ganin Oga.” Dad ya ce. “ Ni kuma?.” “ Yes Sir.” Hankalin Ummah ya dawo gare shi ta zuba masa ido. “ Kace ta shigo.” Cewan Saif yana bin hannun Safeera da kallo dan ya fara motsawa. A hankali ta soma bud’e idon tana sauke su akan matar da ta shigo da sallama. A kidime Safeera ta tashi daga kwanciyar tana furta. “ Ummah Fauziyya.” “ Safeera!!!.” Cewar Fauziyya tana ware ido tare da dafe kirji. “ Kin santa ne?.” Gyada masa kai tayi tana nuna ta da hannu ta ce. “ Kishiyar Mamata ne.” Kallon kallo aka tsaya yi kafin Ummah ta ce. “ Kawar Mummy dinka ce baka gane ta bane Saif?.” Girgiza kai yayi alaman bai gane ta ba, ya dubi Safeera ya ce. “ To ina Maman taki?.” Murmushi da yafi kuka ciwo tayi tana cewa. “ Yau zan baka labarina tun daga farko har dalilin da yasa na dawo 20 houses.” ~~~~~~WACECE SAFEERA. Haifaffiyar garin Borno State ce, Mahaifinta dan nan ne wato Malam Bukar, kanuri ne gaba da baya, matansa uku wato Hajiya, Fauziyya sai Fatima wacce suke kiranta da Mama. Malam Bukar mai kudi ne ada kafin karayar arziki ta same shi, a wajen uwargidansa yana da yara Biyar mata uku maza biyu, Fauziyya kuma biyu duka mata sai Mama wacce take da yara bakwai namiji daya. Kausar ce babba sai Falmata kafin Safeera sai Rauda Nabiya Ammi sai Umar, Allah ya bawa Safeera hakuri sai dai bata juran yunwa ko kadan. Tun bayan da Malam Bukar ya samu karayar arziki ya siyar da gidan da suke ciki ya siya guda uku ya rabawa matan nasa kowa gida, sannan ya danka musu takardun gidan a cewarsa ko bayan mutuwarsa kar kowa tayi fada akan gidan. Duk inda aka ce mata bin malami to Fauziyya ce gwana kuma ita ce a farko, ta rusa duk wani farin cikin gidan. Babu asirin da bata yi ba dan Mama ta mutu amma yaki cinta, karshe ma sai ya fada akan Hajiya wacce rana guda aka samu gawarta a daki ta mutu, yaranta sunyi kuka sosai inda Mama ta dauki karamar cikinsu wato Amma zata zauna da ita. Tun Kausar na karama Fauziyya ta mata asiri wanda ya kamata har yau da bata warke ba, ta haukatar da yarinyar sosai, babu inda Mama bata je ba dan neman magani amma abu yaki ci. “ Bukar ni fa na gaji da lamarin gidan nan ka sake ni na wuce garin mu.” A cewar Mama a tsakiyar gida. Kuka kawai su Safeera ke yi dan Kausar ma bata gidan ta tafi yawo tazubar dinta, su Nabiya da Ammi kuma suna kanana haka. “ Komai na duniyar nan yar hakuri ce, ki cigaba da hakurin da kike yi wata rana sai labari.” Cewan Malam Bukar wanda suke kira da Abba. “ Ina bazan iya ba kuma ta ishe ni yanzu kam.” Safeera tazo da gudu tana kama Mama ta ce. “ Mama dan Allah kiyi hakuri.” Fuzge jikinta tayi a fadace ta ce. “ Idan baki sakeni ba sai naci uwarki a gidan nan, shegiya kawai ai kuna gani Baban ku baya kawo abinci a gidan nan kullum ni nake fita aiki nake samu, gashi aikin ya kare dan ubanku a ina zamu samu.” Cikin sanyin murya Abba ke fadin. “ Ku bawa Mamarku hakuri, da ai ina kawowa yanzu ne karfina ya kare.” “ To Bukar tunda karfinka ya kare ai sai ka sauwake min nayi gaba ko? Haba kubi ku haukata mutum.” “ Kema kinsan inasonki Fati.” “ Bukar Wallahi sai ka sakeni ko a rasa kwanciyar hankali.” Falmata ta kama hannun Ammi da Nabiya ta kai su daki ta ce. “ Kar naga kafarku a wajen nan?.” “ To.” Cewan Nabiya. Shigowa da gudu Umar yayi yana fadin. “ Falmata, Safeera! Rauda kuzo an kama Kausar a bakin line ana dukarta.” Ba shiri Safeera ta mike tsaye, da gudu Falmata ta nufi kitchen ta dauko tabarya, janyo mayafinta Safeera tayi ta fita a dari, Rauda na mara mata baya hannunta rike da sanda, da gudu Falmata ta fito ita ma hannunta rike da tabarya. Mama zata biyo su Abba ya ce. “ Ki zauna ai gidan mata ne, su zasu je su dawo, ki bar su.” “ Kaga ba? Sana’ar kenan, burinka a kashe min yara sai hankalinka ya kwanta, munafukar matarka tasa babbar y’ata tabi duniya gashi ana can ana dukanta, yanzu suma idan suka je bansan me zai faru ba.” Abba bai ce komai ba ya shiga dakinsa dake kusa da kitchen wanda mara bansa da kurkukun kadan ne. A waje kuwa Safeera na isa taga yanda aka rufe Kausar da duka a k’asa har sun fasa mata jiki, tana kuka ta shiga tsakanin su tana basu hakuri, amma sam basu ji ba sai ma cigaba da suka yi da dukan su su biyun. “ Ku dauko taya ku hada musu, gobe bazata sake yin sata ba ai.” Cewan wani mutum yana tsaye da sanda a hannunsa. Hango su Falmata da Rauda suka yi suna zuwa da gudu ko wacce rike da abun duka, kai ko mahaukaci ne idan kaga yanda suke zuwa da gudu kawai ka bar gurin. Kafin suce me tuni Falmata ta kai tabarya kan mutumin dake dukan Kausar. “ Dan kutumar ubaka kai ka yita ne da kake dukanta kamar yarka.” “ Ni kika kwalawa tabarya.” Bai gama rufe baki ba Rauda ta kai masa sanda a k’afa. Da sauri Safeera taja Kausar gefe, fada aka shiga yi tsakanin su da mazan, ta ko’ina duka ake kaiwa mutum, kafin su ankara an bugawa Rauda sanda a koshi nan da nan ya fashe sai jini. “ Wayyo!!! sun kashe ni.” “ Char uba kanwata zaku fasawa goshi.” Cewan Falmata tana kaiwa wanda ya bugawa Rauda sanda tabarya a ciki. Gurin ne ya hargitse da mutane ganin ana k’ok’arin yin kisa, wani daga gefe ya kira motar y’an sanda kafin kace me har sun iso. Kama Kausar Safeera tayi da zummar guduwa, amma aka tare su, saka su aka yi a motar y’an sanda zuwa police station 🚉. Da gudu Umar ya koma gida yana kuka. “ Amma.” Sunan da yake kiran Mama dashi kenan. “ Amma!!! An tafi da Safeera da su Kausar police station.” Hijabi ta saka ta fito da gudu suka nufi police station din, duk ta rude lokaci daya ta rame. “ Ni fa babu wanda zai saka ni a cell tun da ba kisa nayi ba, ai self defense ne naga.” Cewan Falmata tana kama k’ugu tana hararan wanda suka yi fadan dashi. A tsawace police din ya ce. “ Shut off!!! Kar ki mana raini a nan.” Murkuda masa baki tayi tana dauke kai, a fusace yayi kanta da sauri Safeera ta shiga tsakiyar su tana cewa. “ Dan Allah kayi hakuri.” Ta hade hannayenta ta durkusa. “ Haba dan Allah Safeera, kina zubar mana da aji Wallahi to wani laifi muka yi da zaki bashi hakuri.” Cewan Rauda tana hararan police din dan sun gan shi gajere duk sun fishi tsayi. “ Ke!!! Ubaki shegiya da masifar gida zamuji ko da naku.” Cewan Safeera kamar zata yi kuka. “ Safeera ki zauna fa, mu gama wannan tukun muje gidan dan Wallahi sai maci uban Kausar tun da ita rayuwarta nema mana magana ko? Shegiyar yarinya dama barinki akayi ba’a haife ki ba, sai yau kin gane kuranki.” Falmata ta fada a fusace. Komawa police din yayi gurin sauran yan uwansa yana magana k’asa k’asa. “ Wadan nan fa sun fimu hauka kuma daga gani babu kudin da zamu samu a gurin su, the early the better mu bar su tunda Oga bai dawo ba.” Jijjiga kai suka yi kafin suka dubi inda suke sun zuba musu ido, a tsawace officer ya ce. “ Ku kira ayi billing naku sai ku tafi.” Nuna musu jikin bango Falmata tayi ta ce. “ Billing is free, ko ka dauka bama jin turancin ne? Mu fa idan da sabo mun saba zuwa gurin nan, infact gida ne ma a gurin mu.” “ Ke baki da kunya ku tashi ku tafi.” Tabe baki tayi tana mike ta harari Kausar tayi kwafa, mayafinta ta gyara tayi gaba, Rauda ta rike goshinta wanda ke zubar da jini ta fita tana Allah-Allah a isa gida, kama Kausar Safeera tayi suka fito daga police station din. Suna fito suka hadu da Mama ta sauko a machine ita da Umar fuskarta duk kwalla, tausayinta Safeera taji. Da sauri ta iso gurin su taga Kausar ba shiri ta fara kai mata duka, ko motsi su Falmata basuyi ba, da kyar Safeera ta kwace ta a hannun Mama. “ Ku kashe ni ku huta kawai.” Babu wanda yayi magana machine din da ta taho dashi suka shiga suka koma a hanya aka tsaya a chemist aka yiwa Rauda dressing na goshinta aka manna mata bandeji suak cigaba da tafiya zuwa gida. Mama ta biya kudin machine suka shigo ciki, kafin kace me tuni Falmata da Rauda sun fara dukan Kausar, Mama bata kula su ba ta nufi dakinta. “ To ku kasheni ku huta mana haba.” Cewar Kausar tana daga hannu sama, dan dama muryanta ya fita daman a gidan saboda yayi kama da namiji. “ Dan uwarki zamu kashe ki kuwa, kullum kina cikin jawo mana fada, kije kiyi yawon karuwancin ki ki dawo ki jawo mana fada.” Cewan Falmata. Safeera ta zauna ta fara kuka ta ce. “ Ku ko tausayin Mama bakwa ji sam, duk kun zama yan iska, ita wannan sai yawo tazubar kamar busuru.” Ta wurgawa Kausar kofin dake kusa da ita. “ Ke kam kika tabani sai na sauya miki kamannin fuskarki.” Cewan Kausar tana kallon Safeera. “ Au haba ni din?.” Ta nuna kanta kafin ta tashi ta tsinka igiyar sanya tayo kanta a haukace, tana zabga mata igiyara tana fadin. “ Dama na gaji dake a gidan nan, ni ce dama ke tausayinki amma tun da zaki sauya min kamanni bari na gwada sumar dake kadan.” Ta fada tana buga kanta da jikin bango. Sai da su Falmata suka raba su kafin taje ta zauan tana huci. “ Bar muku gidan zanyi kowa ma ya huta.” Ta mike zata fita. Safeera ta mike a fusace ta wurgar da dankwali ta soma cewa. “ Wallahi Kausar idan kika fita sai na miki tsindir a gaban yaran nan naci ubanki, sai suga nonon da kike zuwa karuwanci dashi…. *SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼* 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 _Gajeran labari_ *Na* *Fatima Isa Manu* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_ Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP?mode=ems_copy_t *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 19* Sai da su Falmata suka raba su kafin taje ta zauan tana huci. “ Bar muku gidan zanyi kowa ma ya huta.” Ta mike zata fita. Safeera ta mike a fusace ta wurgar da dankwalin kanta ta soma cewa. “ Wallahi Kausar idan kika fita sai na miki tsindir a gaban yaran nan naci ubanki, sai suga nonon da kike zuwa karuwanci dashi.” Komawa tayi ta zauna dan duk haukarta tana tsoron Safeera idan ta burkice. ~~~Washe gari~~~ Da sassafe kafin kowa ya farka Kausar ta fita daga gidan, ko da suka farka basu ganta ba idan da sabo sun saba hakan yasa masu aiki suka fara yi. Cikin mintina kadan aka gyara gidan abun ka da gidan mata, rub da ciki duk suka yi yunwa na damun su. Mama ta fito cikin shirinta na tafiya aiki ta gan su tare da cewa. “ Ku karbo ko garin kwaki da sugar a shagon Alai bana idan na samo wani abun daga aikin sai na biya shi.” Tashi Safeera tayi ta dauko hijab din ta. “ To Mama bari naje Allah ma yasa ya bamu dan yana bin mu bashin dubu biyu.” “ To Amen, ina Kausar ne?.” Falmata ta ce. “ Hmm!!! Ta fita yawon nata tun asuba.” “ Allah ya kyauta, ya jikin naki Rauda?.” “ Alhamdulillah kan ya dena ciwo ma.” Daga haka ta fita bayan ta musu fada kan cewa ko Kausar ta nemo tsokana kar su tare mata. “ Dan Allah Alai bana ka bamu bashin Wallahi idan muka samu kudi zamu baka ka taimaka.” Cewan Safeera kamar zata yi kuka. Matso da bakinsa yayi kusa da kunnenta ya ce. “ Idan kin yarda kullum zan na baku abinci amma da sharadi.” “ Ina ji koma menene zanyi.” “ Kullum za ki na zuwa shagona kina kwana da safe sai ki koma.” Baya tayi tana girgiza kai. “ Ni ba yar iska bace kuma bazan koma yar iska ba.” Kamar zai hauta da masifa ya ce. “ Iskanci na nawa kuma? Ke da uwarki take fita yawon karuwanci Yayarki kuma ta zama karuwa.” Kuka ta fashe da shi ta koma gida da gudu tana shiga. Da sauri Falmata ta nufeta. “ Me ya faru waya tabaki?.” Cikin kuka ta soma cewa. “ Falmata kowa kallon karuwai yake mana a unguwar nan! Kausar ta bata mana suna.” Ta karashe cikin kuka. “ Yanzu wa ya zage ki?.” Cewan Rauda tana zama. “ Alai bana ne nace ya bani bashin gari shine ya soma cewa wai Mamata yawo karuwanci take haka ma Yayata saboda haka kawai nazo shagon shi zai na bamu abinci idan har zan dinga kwana.” “ Kutumar jar uba.” Cewan Falmata tana tashi tsaye. “ Dawo ki zauna! Dawo ai ba yanzu zamu rama ba sam!!.” Rauda ta fada tana koran yaran a falo kafin ta kalle su ta ce. “ Kun san Allah babu abun da zai hana yau bamu masa tabargaza a shago ba.” Safeera ta ce. “ Rauda ban gane ba? Nifa banason hayaniya ko masifa.” “ Dakata Malama, ke dama an saba zaginki ki hakura amma nikam sai na tabbata na

Chapter 7 of 17