Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ba’a biyani hakkina ba za’a tafi, kudina zaku bani da motana.” Ammar ya ce. “ Ni zan baka bashi zai baka ba.” Tun daga sama har k’asa ya karewa Ammar kallo, wani tsuki yaja yana cewa. “ Me na sama yaci da zai bawa na k’asa? Da ni da kai din waye yafi wani arziki? Gwanda shi yana da hasken kudi da kwarjini irin na samu kudi amma kai fa sammakal babu ko daya.” Dariya kawai Ammar ya masa yana cewa. “ Bismillah ka bishi idan zaka samu.” Tsuki Bappa yaja yana fita daga falon, Ammar ya mara musu baya yana jinjina al’amarin Allah ta yanda ya jarabce Saif da son Safeera cikin k’ankanin lokaci, yayin da ita kuma take wahalal dashi ta yanda taso. Yana fitowa ya hango su sun shiga mota, da sauri ya iso gurin yana cewa. “ Saif ina zaka kai ta?.” “ Aure za’a daura mana yau, dan yanzu ma gurin Ummah zan kai ta… *TAKU HAR KULLUM DR TEEMERH✍🏼* 13- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 _Gajeran labari_ *Na* *Fatima Isa Manu* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_ *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 13* Yana fitowa ya hango su sun shiga mota, da sauri ya iso gurin yana cewa. “ Saif ina zaka kai ta?.” “ Aure za’a daura mana yau, dan yanzu ma gurin Ummah zan kai ta.” “ Ban tabbatar baka da hankali ba sai yau, ashe kai wawa ne, idan kaje sai kace ga matar da zaka aura wanda ka yiwa fyade kenan.” Runtse idonta tayi tana jin zafin kalmar, kafin ta kalli Ammar tana tana dauke kai. Saif ya ce. “ Kar ka samu, ai dadin abun ni na mata ba wani bane, kaga kuwa dole ni ne zan aure ta.” Ya karashe yana daga glass din motan, ya tada motan yana fita daga gidan da gudu. Mota Ammar ya shiga shima ya tada, da gudu Bappa ya shiga yana kallon Ammar wanda shi ma kallon shi yake, bai ce komai ba ya fita daga gudu daga gidan Bappa na masifan cewa ya rage gudu, amma ko sauraran shi bai yi ba sai ma k’ara gudun da yayi. *UMMAH POV* Ta gama girkin rana kenan ta dawo falo dan ta huta, wayanta ta dauka tana kallon videos na social media, da labaran abun da yake faruwa. Sallama aka yi ta daga ido tana kallon kofan kafin ta amsa, shigowa Mom tayi tana rangwada tana wani toshe hanci. A tsakiyar falon ta tsaya tana fadin. “ Amina kike da suna ko wace.” Ummah bata ce komai ba sai kallon ta din da take yi, cigaba da cewa tayi. “ Inaso na gargade ki, daga yau sai yau kar ki bari na sake ganin Saif yazo bangaren ki, idan kunne yaji gangar jiki ya tsira.” Da mamaki kawai take kallon ta kafin ta ce. “ Naji.” “ Good, dadina da ke kina daukar magana ai, da kinyi musu da na gwada miki ta yanda zaki fahimta ai, banza kawai.” Murmushi kawai Ummah tayi bata kuma tanka mata ba, sai ma cigaba da danna wayanta da tayi. “ Ina magana kin mantar dani.” Ta fad’a a tsawace. “ Hafsat bana son hayaniya ki fice min daga falo.” Cewar Ummah cikin rashin son damuwa. Kama k’ugu tayi tana fadin. “ Iyeee, lallai wuyanki ya kai yanka, ni zaki kalla kice na fita daga kazantar gurin nan?.” Tashi tsaye Ummah tayi tana cewa. “ Bazan tsaya ina sa’in sa dake ba, dan bansan me bokan ki ya fada miki ba, sannan inaso in fada miki cewa idan ke da boka kika dogara ni kuma da Allah ne, sannan d’a nawa ne kuma ya dawo gurina da taimakon Ubangiji, saboda haka inaso tun cikin mutunci da kamala ki dice min daga falo kafin na sauya miki kamanni, dan jiya ba yau bane, idan kinci tuwo da miya a kaina jiya yau ko ruwa bazaki sha ba.” Duk ta rude ganin yanda Ummah ke zuba mata zallan magana, ga kuma tsoronta din da ya kamata na lokaci daya, amma sai ta kafse tana jan tsaki tare da juyawa ta fice a falon. Nauyayyar ajiyar zuciya Ummah ta sauke a fili tana cewa. “ Yau ni nayi magana har haka?.” Muryan mai aikinta Asabe taji tana cewa. “ Ummah tura ce takai bango shiyasa kika mayar da murtani.” Juyawa tayi taga Asabe din tana murmushi ta ce. “ Kina jin mu kenan?.” “ Hmm Ummah ina jinku duka, Matar Wallahi bata da mutunci ko kad’an, ke da yaronki wai tazo tana miki gargadi fa, Allah ya kyauta kawai.” “ Ameen. “ Ummah ta fad’a tana wucewa d’akinta. *MUMMY POV* Ita bama zama take a gidan ba balle ayi tunanin zata shiga sabgar su, amma idan tana gidan ranar sai kowa yasan Mummy bata fita ba. Bata zama kullum tana hanyar hotel, yara kanana take kulawa wanda a gida ma sai sun roke sabulun wanka a gurin iyayensu kafin suke yin wanka har su fita. Akwao wani saurayinta mai suna Shamsu, wanda Fauziyya ta hada ta dashi, a fadarta zai iya kashe Saif, kullum suna tare dashi a hotel, yaro ne karami dan duka-duka shekaransa bazai wuce ashirin da shida ba dan Saif ma zai girme shi. Amma ta makalewa yaron, shi kuma kudinta yake ci, ita tana tunanin ita kadai yake mu’amala, sai dai bata san cewa yana kula y’an mata dayawa ba, dan idan ta barshi a hotel ta koma gida sai ya kawo wata. Yau ma a chan ta wuni suka gama cin karansu ba babbaka, karshe ta mika masa kudade masu yawa tana tashi, kafin ta ce. “ Baby nifa kwana biyun nan bana jin dadin jikina, ko kaima kana jin wani abu ne?.” Girgiza kai yayi yana fadin. “ Nikam klau nake, ko zaki je asibiti ne.” “ Eh inagani kam.” Ta fada tana daukan jakarta ta nufi kofa tana cewa. “ Sai kuma gobe.” “ Yawwa Sugar mommy.” Ya fada yana dariya da shi kadai yasan ma’anarsa. *MOM POV* Ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa taya zata bullowa al’amarin kwata kwata, wayanta ta dauka ta kira bokanta a cewarta malami. Yana dauka ya ce. “ Nasan me ke tafe dake, kawai kizo muyi ta ta k’are.” Murmushi Mom tayi kafin. “ Gani nan zuwa.” Daga haka ta kashe wayan. Daki ta nufa ta shirya ta zuba kudi a handbag dinta tana fita, motarta ta shige tana tadawa, tana fita motocin Saif suna shigowa. Direct gurin parking lot ya nufa yana parking, motar Ammar yayi sai nasu Sageer, zagayowa yayi ya bud’e mata jiki na bari. Kallon shi take dan lokaci guda taji tausayinsa, tunawa da kalan abun da ya mata tayi sai ta bata rai ta fito daga motar. Kallon gidan tayi kafin ta maida idanunta kan shi, inda yake cewa. “ Muje Safeera.” Takawa suka fara yi zuwa part din Ummah wanda yake hannun dama, Ammar ya fara mara musu baya shi da Bappa, suna cikin tafiya Bappa ya rage murya yana cewa Ammar. “ Amma nan gidan bada bulo akayi ba ko?.” Kallo daya Ammar ya masa tare da fadin. “ A’a da yashi aka yi.” “ Mtsw illan kula mara kudi ke nan, da shi wannan attajirin ne mai farin anayi ai da yanzu ya bani amsa, amma da ke ance talaka yana fama dama da busheshen talauci ina yaga ta bayar da amsa me kyau.” Bappa ya fada cikin takaici. Murmushi kawai Ammar yayi ba tare da ya kula Bappa ba, dai-dai lokacin da Saif yayi sallama a falon Ummah yana saka k’afa shi da Safeera. Amsa musu Asabe tayi tana kallon Safeera wacce ita ma kallon ta take tana tunanin inda ta san fuskar. Ganin kallon yayi yawa ne yasa Saif cewa. “ Kee!!!! Me haka kin zuba mata mayun ido kina kallon ta, kin santa ne dalla dauke idanunki daga kanta.” Ya fada a tsawace. Da sauri Asabe ta furta. “ Ayi hakuri Yallabai.” Kafin ta juya ta koma kitchen da sauri. Da ido Safeera ta bita kafin ta mayar da idanunta kan kofar da aka bud’e. Ummah ce ta fito jin kamar hayaniya, kallon Saif da tayi ne a burkice ya tada mata hankali, mayar da dubanta ga Ammar tayi taga shi ma a burkice, kafin ta kalli Safeera wacce hankalinta yake kwance, inda Bappa yake ta gani shi ma hankalinsa a tashe. A dan rude ta iso gurin Saif tana dafa kafarda ta ce. “ Me ya faru? Kai da wa? Ya naga hankalinka a tashe? Wacece wannan?.” Ta nuna Safeera wacce ta sunkuyar da kai. Kallon Safeera yayi kafin ya ce. “ Ita zan aura.” Kallon shi tayi ta kalli Safeera, kafin ta kalli Ammar tana cewa. “ Anya abokinka nan yana lafiya?.” “ Lafiya kalau nake, kuma babu abunda yake damuna, ko ku aura min ita ko na kashe kaina.” A razane Ummah tayi baya tana cewa. “ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un! Inna’illahi wa’inna illahi raji’un!! Saif me ya kawo kisa ciki kuma, ance baza’a aura maka ita ba ce.” “ Bana neman izinin ku ko shawarar ku, umarni kawai nake baku.” Ya fada a burkice kamar wanda yasha kwaya. Ammar ne ya ce. “ Saif ma Ummah kake bawa umarnin?.” “ Ammar bana so mu sami matsala da kai, baka san me yake damuna ba na lura, dan haka ka barni kawai.” “ Saif dole na dawo da kai idan har kana neman hanyar kaucewa. Matsawa ta danyi daga gefen shi ganin kamar ba kalau yake ba, dan yanda yake magana a tsawace ya fara bata tsoro, ita tama ji cewa zata hakura da auren, abu kadan sai ya fara masifa yana tsawace-tsawace. Ummah ta dubi Safeera a sanyaye ta ce. “ Yarinya a ina kuka hadu dashi ne? Tun yaushe kuke tare?.” Muryanta ya fara rawa dan yanda Ummah ta cika mata ido da kwarjini, hakan yasa ta fara cewa. “ Aaa…. dama ba… ban…” Katsai ta yayi da sauri yana cewa. “ Ummah ina Dad? Ai dama shi yake daura aure bake ba, mantawa dama nayi nazo gurinki, shi idan naje a take zai daura.” Ya kama hannun Safeera yana ja dan barin gurin, muryan Dad yaji wanda tun dazu da ya shigo yake tsaye a bakin k’ofa. “ Ba sai kaje nema na ba gani nan ma Saif.” Juyowa yayi yana kallon Dad wanda yake rike da jakarsa na aiki, da sauri ya saki hannun Safeera ya nufi Dad yana kama nasa ya ce. “ Dad aure zaka min yau.” Numfashi Dad ya sauke yana kallon Ummah wacce ta fara kuka dan lamarin dan nata ya fara bata tsoro, wai akan mace duk ya haukace macen ma yarinya karama wacce bazata wuce k’anwarsa ta takwas ba da sun haihu da wuri. “ Babana ai idan za’ayi aure sai anyi bincike akan yarinyar, ansan halinta da kuma gidan da ta fito, sannan…” Saurin katsai Dad yayi ta hanyar cewa. “ A’a bana buk’atar yin bincike ni na gama bincike na tuntuni game da ita, na rigada nasan wacece ita.” Girgiza kai Dad yayi yana cewa. “ Binciken ka daban namu daban, idan har kai ka yarda to sai muma munyi bincike.” Wani yawu mai kauri ya hadiye yana duba idon Safeera wanda itama ya kad’a cike da tsoro, kafin ya dubi Ammar wanda shi ma idon ya zuba masa, duban Bappa yayi wanda yake shirin yin magana. Kafin Saif yayi wani magana tuni Bappa ya furta. “ Yoo Alhaji ai yarinyar bata da wani asali, tsinto ta muka yi a bakin kogi kuma da alama lokacin fyade aka mata….. Bappa dan kutumar uba ne🥹🥹🥹🥹🥹 *TAKU HAR KULLUM DR TEEMERH✍🏼* 14- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 _Gajeran labari_ *Na* *Fatima Isa Manu* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_ Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 14* Kafin Saif ya yi wani magana tuni Bappa ya furta. “ Yoo Alhaji ai yarinyar bata da wani asali, tsinto ta muka yi a bakin kogi kuma da alama lokacin fyaɗe aka mata.” “ Ni na mata fyaden ai.” Saif ya fada yana mik’ewa tsaye. Sunkuyar da kai tayi wani hawaye mai zafi ya shiga gangaro mata, tamabayar kanta take shin tayi wa mutane wani abu ne? Mai hadin ta da Bappa da yake shirin rusa mata rayuwa? Me ya sa yake son addaba mata ne?. Dad ya kalli Safeera ya duba inda Saif yake shima, kafin ya d’aga kai ya kalli Ammar wanda shima sunkuyar da kai din yayi. Jinjina kai Dad yayi yana fadin. “ Saif maganar gaskiya ne ko kawai ka fada ne?.” Kan shi a sunkuye ya furta. “ Dad bazan taba yi maka karya ba, eh ni ne….” Saukar mari kake ji hagu da dama, kusan dukansu sai da suka kama baki dan abun mamaki ne ace Dad ya mari Saif, yanda yake son shi kadai ya isa ya sanar da su cewa ko yatsa bazai nuna masa ba. “ Hauka kake yi zaka aikata babban zunubi haka? Kasan yanda Allah yake fushi da wanda suke aikata zina kuwa? Ka san azaban da Allah ya tana da musu ranar gobe kiyama? Tirr da halinka, ban taba yin tsammanin cewa zaka yi haka ba, ko wani ne ya fadamin karyatasa zanyi, sai dai kash kai da bakinka ka amsa cewa kayi,,,,, Amina kina ganin kayan kunyar da Saifullahi ya jawo mana ba.” Ya karashe yana kallon Ummah wacce take kuka. Mai da duban shi kan Safeera yayi, yana fadin. “ Ke kuma wani wauta ne ko dadin baki zaisa ki amunta da namiji har ya tabaki? Ga ki yarinya karama amma ya lalata miki rayuwa, shi namiji ne duk inda ya shiga zai yi aure, amma ke fa!!! Kafin a aureki sai wasu sun furta cewa an taba yi mata fyade, tir da kalan rayuwar nan.” Ya karashe da takaici. Kuka Safeera ta fara tana kankame jikinta, tabbas maganar da Dad ya fada mata gaskiya ne, amma a lokacin bata buk’atar gaskiya har ta kai da ta aikata, burinta kawai ya bata kudi ta samu ta biya buk’atar ta, bata yi tunanin ita mace bace kuma wata rana zatayi aure ta haihu har ta zama uwa, hakan yasa kukan ta ya k’aru fiye da na dazu. Cike da takaici Dad ya kalli Ammar yana cewa. “ Idan shi bayi da hankali ai kai kana dashi, ko duka taku biyun hankalinku ya gushe? Madadin a samu guda daya daga cikinku ya fahimtar dashi zunubin da zai aikata sai aka samu dukan ku kan kifi gare ku.” Numfashi ya sauke yana cigaba da fadin. “ Bama sai kazo ka takura na aura maka ita ba, aurenta dole ne dama a gare ka tunda kai ka fara lalata ta ya kamata kai zaka k’arasa ai, kafin jama’an gari su san da cewa d’a daya tilo a gidan Safwan ya yiwa yarinya fyade gwara a daura muku auren.” Kudi Dad ya ciro daga aljuhunsa dubu biyar yana mik’awa Ammar ya ce. “ Kaje nan bakin titi ka siyomin minti da goro.” Karba Ammar yayi yana fita da sauri. Ummah ta ce. “ Abban Saif mai kake shirin aikatawa ne?.” Gyara bunjumansa yayi yana rike hannu ta baya ya ce. “ Ki jira ki gani.” Babu wanda yayi motsin kirki a cikinsu sai kukan da Safeera take yi wanda ya zuba mata ciwon kai, har ya kai da ta durkusa, Ummah ta bata ruwa tasha, suna cikin haka Ammar ya dawo da goro da minti. Kallon Bappa Dad yayi ya ce. “ Mu zauna a daura aure.” A furgice ta d’ago kai tana kallon shi, ta kalli Saif wanda shima ita yake kallo da zallan kauna dan shi hankalinsa kwance, sai ma sanyin da yaji a ransa a abun yazo masa da sauki, dan shi a ganinsa ai an masa adalci ne. Zama Bappa da Dad suka yi a kan carpet, Dad ya kalli Ammar da Saif ya ce. “ Ku zauna.” Da sauri Saif ya zauna yana murmushi, kallo daya Dad ya masa yana dauke kai, Ammar ma ya zauna. Ummah da al-ajabi ya gama cike ta ne ta ce. “ Alhaji ba tare da bincike ba za’a daura aure?.” “ Amina kiyi shuru a nan, ko bakiji shi yace ya gama bincike bane?.” Dad ya furta a dan fad’ace. Shuru Ummah tayi bata sake cewa komai ba. Nan Dad ya bud’e taro da addu’a, kafin suka yi niyar daura aure, Dad ya dubi Saif yana cewa. “ Kawo sadaki?.” Hannu ya saka a aljuhu yaji bakomai, tashi yazo zaiyi Dad ya dakatar dashi yana cewa. “ A nan zaka kawo kar ka tashi.” Shuru yayi yana tunanin mai zai bada kafin ya kalli Ammar, Ammar ya girgiza masa kai alaman bashi da kudi a jiki, zoben hannunsa ya kalla na Diamond 💍 wanda ya siya 5m a Saudi, cirewa yayi da sauri yana mikawa Dad ya ce. “ Shine sadakin.” Gyada kai Dad yayi kafin ya ce. “ Waye Alwalinta?.” Ammar ya ce. “ Ni.” “ Alwalin shi din fa?.” Bappa yayi saurin cewa. “ Ni zan zama.” Nan aka daura auren Saifullahi da Safeera akan sadaki zoben diamond, sannan aka shafa fatiha aka raba goro da minti. Saif kamar ya zuba ruwa a k’asa yasha yake ji, yayin da Safeera ta zama mutum mutumi, dan har yanzu bata yarda da cewa ta zama matar aure ba, matar auren ma na Saif wanda sai da ya kwanta da ita yaji yanda take kafin ya aure ta, hakan yasa ko motsi ta gagara daga zaunen da take akan tiles. Ummah ta kalli Saif wanda idanunsa na kan Safeera yana murmushi, kafin taga Safeeran, ajiyar zuciya ta sauke ta nufi d’akinta. Tashi Dad yayi ya nufi shi ma part nasa, Bappa ya dubi Saif ya ce. “ Dan Allah Ango ku bani kudina da motana.” Nuna Ammar yayi idanunsa nakan Safeera yana mikewa ya ce. “ Shi zai baka.” Ya tashi yaje gurin ta, shima ya zauna yanda ta zauna yana zuba mata ido. Bappa ya kalli Ammar, Ammar yana sakar mishi murmushi. Saurin dauke kai yayi a ransa yana fadin. ‘ Na shiga uku, ashe shi zai bada kudin, na boni yanzu duk rashin kunyar dana masa ashe shine mai arzikin ba wancan dak’ik’in ba.’ Ya fada yana dafe goshi, kafin ya kalli Ammar yana cewa. “ Yarona ka tausayawa bawan Allah ka taimaka ka agaza kaji kaina ka bani kudin.” Yana hade hannayensa ya fad’a. Dariya Ammar ya masa yana cewa. “ Mai na sama yaci da zai bawa na k’asa?.” Kamar Bappa zaiyi kuka ya ce. “ Wallahi arashi ne irin na harce, kayi hakuri.” D’aga kafad’a yayi yana tashi ya nufi kofa, ya juyo ya kalli Saif wanda ya koma kamar gunki shi da Safeera, girgiza kai kawai yayi yana cewa. “ Nikam na tafi zanje nayi aiki kafin na dawo.” Hannu kawai Saif ya d’aga masa, da sauri Bappa ya bi bayan Ammar har yana shirin fad’i, har gurin mota suka je Bappa yana bashi hakuri akan ya bashi kudin yana da abunda zai yi. Sai da ya wahalal da Bappa kafin ya bude gurin mai zaman banza yana ciro envelope ✉️ wanda ciki yake cike da kudi guda biyu ya mika masa, sai zai karba sai ya janye, haka ya masa har sau uku kafin ya bashi, kamar Bappa zai haukace haka yayi lokacin da ya karba, yana bud’e yaga key din mota. Ihu Bappa yasa wanda yasa hankulan security’s ya dawo kansa, kare da suke kulle suma suka haushi kamar zasu fito. “ Nagode Allah ya k’ara kawo irin wannan abun, Allah yasa ta sake b’ata na nemo ta, ai wannan batar nata ni yayi wa rana Aradu, huuuu huuuu huuuu, yau sai nayi wata amarya billahil’lazi, na more nima chass.” Kafin ya kalli Ammar yana cewa. “ Tsaya tukun, ina motar mukulli kawai ka bani ashe.” Shiga motarsa Ammar yayi yana nuna Sageer ya ce. “ Kaje ka bashi key din zai dauko maka motar.” Da haka ya zuge glass yana fita daga gidan. Zuwa gurin Sageer yayi yana cewa. “ Saura kai.” Kafin ya bashi key din yana cewa. “ Motar zaka bani.” Karban key din Sageer yayi yana kallo kafin ya ce. “ BMW.” Wani get Sageer ya nufa Bappa na biye dashi. Jerin motoci ne har guda goma a gurin, inda BMW yake Sageer ya nufa yayin da Bappa ya tsaya a dai-dai gurin GLK yaki matsawa. Juyawa Sageer yayi ya kalle shi yana cewa. “ Baba ga naka nan ka k’araso.” Girgiza kai Bappa yayi yana nuna na gabansa ya ce. “ Wannan nakeso ba wancan ba… *Kun fara rage comments ko🥸* *DR TEEMERH✍🏼* 15- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 _Gajeran labari_ *Na* *Fatima Isa Manu* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_ Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 15* Juyawa Sageer ya yi ya kalle shi yana cewa. “ Baba ga naka nan ka k’araso.” Girgiza kai Bappa ya yi yana nuna na gabansa ya ce. “ Wannan nakeso ba wancan ba.” Murmushi Sageer ya yi dan shi a tunaninsa tsufa ke damun Bappa, hakan yasa ya ce. “ Baba wannan yafi kyau akan wancan din ai.” “ Kai yaro gar nake ganin ka, ina ganin zabgegen mota kace wai wancan dan karamin yafi kyau.” Cewan Bappa yana shafa GLK din. Dan mamaki Sageer ya ke kallon shi, dan shi tun da yake bai taba ganin mai son duniya irin Bappa ba, ko a labari ko film, sai gashi yau a zahiri kuma a gabansa. Rufe bakinsa yayi fuska ba annuri ya tsare ya dakawa Bappa tsawa yana fadin. “ Kai!!!! Ka bar nan idan na fito maka da naka sai ka karba, tsabar son duniya a baka mota na over a million amma kana son na gaba da shi.” Shuru Bappa yayi yana kallon shi har ya gama kafin ya ce. “ Kaje gurin ubangidan naka ka tambaye shi waye ni a gurinsa? Ni din nan da kake gani Sirikinsa ne atoh diyata ya aura.” Sageer ya dube shi me kyau yana fadin. “ Yaushe ka zama sirikinsa? Malam zaka fita daga nan ko sai na fitar da kai da karfiin tsiya?.” Kama kugu Bappa ya yi tare da cewa. “ Yooo fitar da ni ta tsiyar.” Bai gama rufe baki ba Sageer ya bude karnukan da suke cikin cell a kulle su biyar. Haushi suka fara suna yiwo kan Bappa, a haukace Bappa yasa ya gudu yana fita daga gurin, ihu yake yana gudu tsakaninsa da Allah yana magiyar a taimake shi. Ya tusa ta a gaba ko gifta ido bayayi, sanyayyen murmushi yake sakar mata. Yana dar-dar haka ya daura hannunsa akan nata, wanda hakan yasa ta juyo da fuskarta zuwa gare shi ta zuba masa sexy eyes dinta. Kame-kame ya fara dan ya rasa me zai ce mata, janye hannunta tayi daga nasa tana tashi tsaye, da sauri shima ya tashi yana mata murmushi ya ce. “ Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida.” Harara ta banka masa tana jan tsiririyar tsuki, annurin fuskarsa ce ta sauya ya ce. “ Akwai wani abu ne?.” A zafafe kamar zata hayo kansa ta soma cewa. “ Sakina zaka yi malam, dan bazan zauna da mazinaci ba dan bansan bayan ni mata nawa kayi mu’amala da su ba.” Kallon ta yake cike da mamaki ya dafa kafadarta yana cewa. “ Kar ki kawo zargi cikin auren mu, dan zai iya rusa duk wani farin

Chapter 5 of 17