ce. “ Tsakanina da ke Allah ya isa, bazan taba yafe miki ba duniya da lahira! Allah shi kadai zai min sakayyar abunda kika min!!!” Kafin ya juya ya koma motansa ya shiga ya zauna, gagara tukin yayi sai kawai ya kira daya daga ciki security da suma jikinsu a sanyaye yace yazo ya mayar da shi hospital din.
Mom tana jin duk abunda ke faruwa amma taki fitowa, dan itama yanzu jira take Dad ya dawo ya sallame ta ta tafi, dan itama nata ya k’are.
Ga damfaran da Ashiru ya mata, ga tozarci da kunyar da ya sakata a idanun mutane, ita cutar da yake maganar ta zuba masa ma bata sani ba, kawai ta amsa ne amma bata san ma tana da wani cuta ba.
Kawai ta san tana zubar da wani warin ruwa ne daga k’asarta, amma bata san na menene ba.
Ko da taji harbin da akayi ta d’auka Saif aka kashe ma, shiyasa taji hankalinta ya sake kwanciya akan da, wayanta ma kashe shi tayi dan kiran da ake mata ya wuce na hauka.
*BAFFA POV*
Yana kwance a daki sallah asuba ma yaki fita gudun kar Gunda su tare shi, haka ya shige d’aki yaki fitowa, jikinsa ma yayi tsami sosai dan hannunsa ma da kyar yake d’agawa, yana da kudi amma yaki ya siyawa kansa magani ko abinci me kyau, gashi kwadayi da son abun duniya ya hana shi tashi ya koma sabon gidan da Saifullahi ya bashi.
Inna da Jannah suna d’aki suna jiran suji su Gunda sunzo, Inna tayi tagumi ta ce. “ Yanzu duk tilin kudin nan sai ki bawa wannan mutumin Jannah?”
“ Inna to ya zamuyi? Kina gani jiya haka aka yi wa Baffa duka a gaban jama’a, aka tozarta mu, yana da kudin ba wai bayi dashi ba amma yaki badawa, karshe ma cewa yayi sai dai a kashe shi amma bazai bada ba” Jannah ta karashe da takaicin irin halin Mahaifin nata.
“ Amma yanzu shi Saifullahi da kika amshi kudin nan a hannunsa, gaskiya dole ki aure shi”
“ Inna ba wai auren shi ne bazan iya ba, idan akayi la’akari da wani abu ma shi ya kamata na aura ba kowa ba, sai dai Safeera nake tunani”
“ Ita tayi auren ta ke ce yanzu abun tunani Jannah”
“ Inna ke nan!! Ina jin tausayin Safeera fiye da kowa a duniya, to taya zan auri Mijinta? Ta cancanci zama ita kadai a wurin Mijinta, ko ba ni ba bazan so wata ta auri Saifullahi ba duk da kuwa shi ne first love dina”
Inna tayi shuru, kafin ta ce. “ Ki dai yi tunani Jannah! Za ki iya zama da Safeera da zuciya daya, kuma nasan Saifullahi zaiyi adalci a tsakanin ku”
Har zata yi magana suka ji sallama daga waje, Inna da Jannah suka mik’e suka fito.
Baffa da yaji sallaman yaja bargo ya rufu da shi, dan ya rantse sai dai a kashe shi amma bazai bada wannan kudin ba.
Inna ta ce. “ Waye ne?”
Alhaji ya amsa da cewa. “ Kudi na nazo amsa, idan babu kuma ku fada mana sai muyi saurin kashe ku.”
Jannah ta sako hijab ta fito, hannunta rike da ATM dinta na First Bank, wanda Saif ne ya saka aka bude mata, ta iso tana cewa. “ Ina kwana?”
“ Ina ruwanki da inda na kwana, ki bani kudina kawai ko na saka a muku dan banzar duka yau”
Ta tabe baki tana bashi ATM din, ya bi da kallo yana cewa. “ Mene pin din?”
“ 5676”
Karba yayi yana mik’awa Gunda ya ce. “ Muje idan babu sai mu dawo mu kona musu ahalin su”
Da haka suka tafi, Jannah ta koma gida tana kallon Inna wacce take a tsure ta ce. “ Na basu idan sun cire zasu kawo min ATM din”
“ Allah ya miki albarka Jannah”
“ Amen “
Baffa ya bude bargon ya ce. “ Jannatuwa”
Ta kalli Inna kamar zata yi kuka ta ce. “ Kiji wani suna a wurin Baffa dan Allah” tana nufan bukkan Baffa ta shiga.
“ Ya ake ciki? Naji sun tafi sun yafe ne ko me?”
“ Baffa na biya ne”
“ Kina fakiriya da wani kudin zaki biya? Ni fa harka da munafurci ne banaso”
“ Shikenan tun da baka yarda ba”
Ya dan kalle ta kafin ya ce. “ To ko dai kinsan inda na ajiye kudina ne”
Ta jijjiga kai ta ce. “ Ni fa ba kudinka na dauka ba Baffa”
“ To waya baki kudi dan ubanki”
Ta turo baki gaba ta ce. “ Saifullahi ne ya turamin jiya”
Ba shiri Baffa ya tashi ya zauna, taja baya dan tasan karshen zancen duka ne.
“ Har nawa ya baki? Kuma ina sauran kudin su ke”
“ Ni fa iya wanda zan basu ne ya turo”
“ Amma Allah ya isa Jannatu, ina laifin ki bani kudin shine kika bawa wancan sambajejan gardin” ya mike yayo kanta, da gudu ta fice a dakin tana buya bayan Inna.
Baffa kamar kudinsa ya soma fada yana cewa. “ Ka haifi yaro baka haifi halinka ba, munafukan yarinya ina laifin ta bani kudin shine taki”
“ Baban Jannah ina ga kudin nan da aka basu taimakon ka akayi”
“ A’a taimakon kan ku kukayi, ashe da macizai nake zama ban sani ba, ina laifin ku kawo a siyomin tsire naci ko zan warke”
Inna ta amshe zancen da cewa. “ Kudin naka kuma shi na gado ne”
Ya harare ta yana jan tsuki zai shiga bukkan shi ya ce. “ Ashir naki, kuma sai kin rigani mutuwa In Sha Allah”
Jannah ta ce. “ Ba amen ba” ta shige ciki da gudu.
A hankali ta soma bud’e idanunta da take jin su sun mata nauyi, ta sauke akan drip din dake mak’ale, ta sake lumshewa tana bud’ewa a hankali.
Ta zubawa d’akin ido tana kallo kamar taga sabon abu, tana mamakin yaushe aka kawo ta nan.
K’ofan taji an bud’e, sai ta mayar da idanunta kan shi tana kallon shi, ya iso wurin ta da sauri yana jawo kujera ya zauna, ya rike hannunta yana kallon ta fuskarsa dauke da murmushi.
“ Ya jikin nako?”
Ta lumshe ido ta bud’e, ya kuma cewa. “ Kan naki ya daina ciwo ko?”
Nan ma lumshe ido tayi ta bud’e, ya sumbaci hannun nata yana daura hannunsa akan cikinta, ta kalla tana furta. “ Ina Jannah?”
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 36*
*BOOK TWO*
Nan ma lumshe ido tayi ta bud’e, ya sumbaci hannun nata yana daura hannunsa akan cikinta, tabi hannun da kallo tana furta. “ Ina Jannah?”
“ Jannah!!!”
“ Eh”
“ Yau din kuma!!”
Kau da kai tayi tana sauke numfashi kafin ta ce. “ Munyi da kai zamuje wurin ta ai, kafin aka samu hatsari a hanya”
“ Hatsari kuma?” Ya tambaya da mamaki.
Ta juyo tana kallon shi. “ Ya akayi to ka kawo ni asibiti?”
“ Ohh.. ohh haka, eh… eh hatsari, ai uhm munyi hatsari ne sai muka taho nan”
“ Kamar kana tantama akan maganar naka fa?” Ta zubawa fuskarsa ido.
Murmushi ya sakar mata yana cewa. “ Yanzu dai ba wannan ba! Ya kike jin jikin naki?”
Dan tabe baki tayi tana jan hannunta mai drip din ta ce. “ Da sauki”
Doctor ne ya shigo shi da nurse, yana cewa. “ Har ta farka kenan?”
Saif yayi murmushi yana shafa hannun nata ya ce. “ Eh ta tashi!”
Dubata yayi, ya yi su gwaje-gwajen shi, kafin ya ce. “ Akwai abun da kike ji yake damun ki?”
“ Ciwon kai ne kawai!”
Rubutu yayi akan paper yana cewa. “ Shi ma idan kika yi bacci zai dauke!” Yana kallon Saif ya ce. “ Allah ya karo sauki”
“ Amen!” Ya daura da cewa. “ Ina buk’atar sallama”
Doctor ya dubi Safeera ya ce. “ Jikin nata bai kai a sallame ta ba, tana buk’atar kulawan likita”
Saif ya masa murmushi ya ce. “ Sai a hadamu da nurse tana zuwa tana dubata har ya warke, dan bana son zaman hospital ne”
Ya jinjina kai ya ce. “ Ba matsala, yanda kace kakeso haka za’ayi BAR.SSS, zamu had’a ka da Yusrah sai tana zuwa tana dubata!”
“ Thanks”
“ Never mind” kafin ya basu takardan sallaman yana fita.
Ta kalle shi ta ce. “ Ba buk’atar sai an hadani da wata nurse ai, ni zan kula da kaina!”
Sumbatar goshinta yayi yana cewa. “ Safeera, kina buk’atar hutu sosai da kwanciyar hankali”
Wani silent murmushi ta masa ta ce. “ Anya zan samu kuwa daga gare ka?”
“ Ban gane ba? Me kike nufi Wifey?”
“ Bakomai kawai tambaya dai nayi.” Ta karashe tana janye hannunta daga nashi, sannan ta soma k’ok’arin tashi ta zauna, ya tallafa mata ta zauna tana jinginuwa da jikin bango ta rufe ido.
Zubawa kyakkyawar fuskarta ido yayi yana fargaban taji cewa zai auri Jannah, dan yasan bazata ji dadi ba, amma to ya zaiyi no way.
Ya tashi yana cewa. “ Ina zuwa!”
Ta gyada kai tana bin shi da kallo har ya fita.
Ko da ya fita d’akin da Sageer yake ciki ya shiga dan yana kusa dana Safeeran, yana bud’e kofan ya zuba masa ido yana kallon shi, kafin ya k’arasa yana cewa. “ Sageer?”
Bud’e gajiyayyun idanunsa yayi yana saukewa akan shi ya ce. “ Sir ina wuni?”
“ Lafiya, ya karfin jikin?”
“ Alhamdulillah na samu sauki ma, sun sallame ni dama kai nake jira ma”
“ Ok sannu, na zama busy ne ban samu na shigo da safe ba”
“ Haba Oga, ai bakomai kana k’ok’ari da ni. Ina Hajiya Safeera ne?”
Ya nunfasa ya ce. “ Tana daki na uku itama”
Sageer ya ce. “ Me ya faru? Bata da lafiya ne?”
“ Eh, amma taji sauki an sallame mu ma”
“ Allah ya bata lafiya”
“ Amen” suka dan taba hira sosai, kafin Saif ya taimaka masa suka fito hannunsa rike da ledan maganin shi.
Jon yazo yana rike shi ya zaunar da shi a wurin waiting seat, Saif ya koma d’akin da Safeera take ciki.
Ta bude ido ta kalle shi ta ce. “ Ina Ummah ne ban ganta ba”
Ya rike ta suna tafiya ya ce. “ Tana wajen Dad ba lafiya”
Ta d’ago ta kalle shi ta ce. “ Dad kuma!!!”
“ Uhmm” ya fada yana kallon Nurse din da tazo tana rike Safeera ya ce. “ Lafiya?”
“ Sir Dr BG ne yace nazo mu tafi da ita”
“ Ok, saketa zan rike abata, idan munje gida ne duty dinki, but a nan nawa ne!” Ya fada murya a kausashe.
Ja baya Yusrah tayi tana hade rai, ta bata fuska tana kwafa a ranta, ta cije labba tana maganar zuci. ‘ Koma me kayi ince dai zanje gidan naka ko.’ A zahiri kuma ta saki murmushi tana kallon Sageer da ya zuba mata ido yana maka mata banzar kallo.
A wajen parking ta suka tsaya, ta kalle shi tana cewa. “ Saif amma da munje naga Dad ko!”
Ya kama hannunta yana cewa. “ Idan kika yi sauki zaki je! Amma yanzu mu koma gida tukun!”
Ba dan ranta yaso ba ta shiga motan, shima ya shiga.
Yusrah ta bude gaba zata shiga Sageer ya dakatar da ita ta hanyar cewa. “ Ga can wani mota ki shiga” ya nuna mata na bayansu, shi kuma ya shiga inda ta bude.
Kulewa tayi amma sai tayi murmushi ta matsa, Jon ya shiga wurin driver yana tadawa suka fita.
Ba don ranta yaso ba ta shiga wani motan suka tafi.
Ma Ammar ya bugawa kira, yana d’auka ya ce. “ Ka saka an cire posting din?”
Ta cikin wayan Ammar ya ce. “ Eh an goge a kaf media! Shi yaron ma nasa a nemo shi”
“ Ok nagode fa Ammar”
“ Kar ka damu ana tare, ya jikin Madam din ban samu nazo na duba ku ba Wallahi duk a burkice muke!”
“ Da sauki muna hanyar gida ma.”
“ Ka bata hakuri dan Allah ko gobe zanzo na duba ta”
“ Allah ya kaimu”
“ Amen… nikam ya maganar wad’an da suka kawo maka hari din ne?”
Sai da yayi shuru ya ga motan iya su ya sune kafin ya ce. “ Ammar abun ba cewa komai Wallahi! Gidanmu a cike da police!”
“ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un! Me ya faru?”
Safeera ta juyo ta kalle shi tana zuba masa ido, ya mata murmushi kafin ya cigaba da cewa. “ Mummy ce tasa aka kawo min harin! Kuma ta harbe Radiya, karshen zance ma Radiya Allah ya mata cikawa dazu a hannuna.”
Ba Ammar ba har Jon da Sageer sai da suka jijjiga da maganar, Safeera kam cewa tayi. “ Mutuwa akayi a gidan?” Ta zaro ido waje.
Ya jawo ta jikinsa yana cigaba da cewa. “ Anjima za’ayi Jana’izar ta, dan nasan war haka jama’a da yan uwanta sun iso”
“ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un!!!” Shine kalman da Ammar yake maimaitawa, da haka Saif ya katsai wayan dai-dai lokacin da suka iso layin gidan nasu suka ga mutane cike a kofar gidan, har da y’an jaridu.
Sageer ya ti saurin cewa. “ Wadan nan fa?”
Jon ya ce. “ Wa ya turo su?”
Saif ya amshe da cewa. “ Labarin duniya bata buya ai, sunji ne suka zo, tun da police sun ji ai kowa ma zai ji.” Ya jawo matarsa jikinsa gam yana kankame ta kamar ance masa za’a warce ta.
Horn aka danna mai gadi yazo ya bud’e suna shiga.
Duk ta tsure ta tsorata, ya mata murmushi yana rike hannunta suka nufi part nasa Yusrah na mara musu baya tana juye-juye tana son taji meke faruwa.
A falon suka tsaya ya kalli Yusrah yana cewa. “ Idan kinzo nan za ki na shigowa”
Ta gyada kai tana cewa. “ Tam Sir”
Kafin ya ce. “ Yanzu zaki iya komawa, ki ma Jon magana ya komar da ke sai gobe ki dawo.”
Ba dan ranta yaso ba ta juya ta fita, Safeera na binta da kallo kafin ta ce. “ Ni fa kwata yarinyar nan bata kwanta min a rai ba”
Rungume ta yayi a faffadar kirjinsa yana shafa bayanta ya ce. “ Hakuri zakiyi har ki warke, kinji Wifey”
Ta gyada kai tana lafewa a jikinsa, a kunne ya rada mata. “ Soon za’a fara kiran mu da Daddy and mummy!”
Tayi saurin dagowa ta ce. “ Me ne????”
“ Yes” ya daga mata gira daya yana cewa. “ Kina da ciki na wata biyu”
A bazata taji maganar, da sauri ta janye jikinta daga nashi tana ja baya, ta soma girgiza kai, sai ga hawaye kamat famfo .
Da mamaki ya ce. “ Safeera abun murna ce fa!”
“ Ni bazan haihu ba, zubar da cikin zanyi banaso…
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 37*
*BOOK TWO*
A bazata taji maganar, da sauri ta janye jikinta daga nashi tana ja baya, ta soma girgiza kai, sai ga hawaye kamat famfo .
Da mamaki ya ce. “ Safeera abun murna ce fa!”
“ Ni bazan haihu ba, zubar da cikin zanyi banaso”
Ya saki baki yana kallon ta, dan shi abun ma mamaki ya bashi, dariya zaiyi ko kuka zaiyi ya rasa gane kan ta, abunda za’ayi murna amma ita har da hawayen ta.
“ Wallahi zubarwa za’ayi banaso”
Zama yayi akan kujeran yana kallon ta yana dariya, hade rai tayi tana goge hawayen da suka zubo, with serious talk ta ce. “ Ina maka magana shi ne kake min dariya! Dan nace a zubar da cikin banaso”
Ya girgiza kai har yanzu yana dariya, sake kulewa tayi sai kawai ta damke hannu ta fara kaiwa cikin naushi, a haukace ya mike yana rike hannun nata, cike da zallan bacin rai ya fara mata masifa. “ Ashe ba ki da hankali ban sani ba? Kwakwalwanki da gaske ya samu matsala kenan!”
Tsit tayi tana zaro ido waje dan ta tsorata da tsawan da ya mata, ta girgiza kai tana ja baya.
Furzar da iska yayi yana shafa kansa, cikin sanyin murya ya ce. “ Sorry Wifey, uhm abun ne ya bata min rai amma sorry kinji!”
“ Amma ka ce da gaske kwakwalwata ya samu matsala, kenan bani da hankali fa ka ce”
“ A’a subutar baki ne!” Ya jawo hannunta suka zauna akan kujera ya soma magana cikin rarrashin. “ Wifey kina bugun cikin kin manta shi ma rai ne da shi? Idan wani abu ya same shi baza kiji dadi ba, kuma ke zaki yi jinya”
“ To too ai nace maka dama bana son shi, kuma ni har cikin raina na fada maka gaskiya”
Ya lankwabar da kai ya ce. “ Ni ma kenan bakya so na ko?”
Turo baki gaba tayi tana bata rai, ya saki murmushi yana cewa. “ Ki tashi kije kiyi wanka, bari ni naje wurin jana’izar nan”
“ Nima zan je idan kun dawo daga makabartan”
Girgiza mata kai yayi ya ce. “ A’a, kiyi bacci baki da lafiya! Ummah zata zo ta karbi ta’aziya”
“ To Dad din fa da waye zai zauna?” Ta tambaya.
“ Yana dakin hutu, babu wanda zai shiga ya gan shi, kuma akwai security a wurin!!! Kuma kin ga ita Mummy tana police station, Mom kuma kunya bazai bari ta fito ba”
“ Me ya faru da Mom din?” Ta tambaya cike da son jin amsa.
Agogon witsiyar hannunsa ya kalla ya ce. “ Ki je kiyi abunda na saka ki, ke ba yar jarida ba sai tambayoyi.” Ya karashe yana nufan hanyar fita.
Murmushi tayi tana daga murya ta yanda zaiji ta ce. “ Amma ai Mijina Barrister ne kuma Lawyer”
Ya juyo ya ganta yana murmushi ya fita.
*BAFFA POV*
Bayan su Gandu sun kawo mata ATM ne, Baffa dake zaune a gefe akan taburma ya ce. “ Jannatuwa, ki siyo min tsire mana a bayan layin nan”
“ To Baffa ina kudin?”
“ Ohhh ni zan baki kudin ma kenan? Bayan kuma wanda Alhaji ya baki”
“ Wannan fa bashin da kaci na biya, kuma ba ko biyar a acc din nan”
“ Auuuu to shikenan ai, ni ma ba kudin ne da ni ba”
Inna ta jijjiga kai tana cewa. “ Zaka mutu ka bar kudin nan fa”
Da kyar ya tashi yana cewa. “ Ke kika sani kuma” yayi wucewarsa zuwa wurin motarsa da tun shekaran jiya yake ajiye ba’a hawwa ba, sai k’uran bala’in da yayi, yana cewa. “ Jannatu yanzu ina laifin ki wanke min motana”
“ Ai Baffa babu kilin ne, da na wanke maka”
Aljuhun rigar jikinsa ya saka hannu yana ciro naira dari, ya mik’a mata yana cewa. “ Zo kije ki siyo omo na hamsin, sai ki kawo min canji na”
Inna ta ce. “ A’a haba dai Malam! Mace da wanke mota”
“ Yooo ki ce yarinyarki ta gwal ce”
“ Ni bance ba”
Baffa ya jijjiga kai yana yin kwafa ya ce. “ Wallahi aure zanyi, sai na samo bazawara mai yara gand’a gand’a sai na aura, ni ne maganin ku ai, bari ma naje na duba gidan da zamu koma, dan nasan gidan har mata biyar za’a iya ajiyewa” ya bud’e motansa zai shiga, Jannah ta ce. “ Baffa zaka iya tukin nan kuwa jikinka fa baiyi sauki ba”
“ Ni na fada miki cewa ban warke ba?” Ya karashe fada yana tada motansa, Inna ta kama hannun Jannah tana cewa. “ Muyi baya kafin ya buge mu”
Wani reverse 🔄 Baffa yayi yana fuzgar motar da karfi ya fita, suka bishi da Allah ya kiyaye.
An kai Radiya gidanta na gaskiya bayan da aka gama yin bincike game da yanda Mummy ta kashe ta, Ummah tayi kuka sosai, dan mutuwar ya Jijjigata, dan Radiya akwai kirki.
Duk wannan hayaniyar da akeyi Mom taki fitowa, duk da kuwa taji gidan ya dauko mutane sosai, sai dai hakan bai sa ta fito ba.
Jikinta ya fitar da kuraje kanana kamar maruru, ga warin da k’asarta ke yi kamar mutaccen abu, tana tashi ruwa zai na bin jikinta, hakan yasa ta hakura ta mikawa Allah lamarin ta.
Jira take Dad ya dawo taji hukuncin da zai yanke mata, ta kira number Ashiru amma baya d’auka har ta hakura ta ajiye wayan.
An kafa rumfa a filin gidan ana zaman makoki, ta ko’ina jama’a sun taru, wasu gulma ce ta kawo su dan suji taya ta mutu, wasu kuma dan su kalli Mom suka zo.
Shi da Ammar suke karban gaisuwa, sun zauna a cikin jama’an kamar munafukai, Ammar sai sunkuyar da kai yake.
Police ya iso yana mikawa mutanen wurin hannu, kafin ya isa wurin su Ammar ya mik’a musu hannu suka gaisa yana musu ya hakuri, kallon Saif yayi yana masa alama da yazo, kana ya juya ya koma wurin motarsa.
Saif ya kalli Ammar, suna tashi suka isa wurin shi.
Police din ya ce. “ Sir an kama ogan nasu dan yanzu ma yana office, shi da yaransa guda biyar, so muna bukatar kazo”
“ No need sai naje ku tura su court kawai.”
Ammar ya ce. “ ba za’ayi haka ba, ya kamata kaje ka gan su kafin a tura su.”
“ Na musu me to? Mutanen da suke neman rayuwata idan naje me zan musu?”
Ammar ya cewa police din. “ Kaje gamu nan biyo ka”
Ya jijjina kai ya nufi wurin motarsa ya shiga ya tafi, Ammar ya kalli Saif yana cewa. “ Je ka dauko wayanka sai muje”
Ba tare da yayi musu ba ya nufi part nasa, da sallama a bakinsa ya shiga falon, yana mayar da kofan ya rufe, sanyayyen kamshin turaren da tasa ne yake tashi, wanda ya haifar masa da wata muguwar sha’awa.
Ya lumshe ido yana budewa ya sauke akanta, tun daga k’asa ya fara kallon kayan da yake jikinta, wata abaya bak’i ce wanda ya siyo mata a cikin kayan akwati, mai ratsin stone pinch colour, ta daura dankwalin a kanta, fuskarta tayi fayau irin wadan da suka tashi daga rashin lafiyan nan, gashin kanta yana sheki alamun ta wanke shi, ta gyara giranta, ta saka kwalli, bakinta sanye da lips glow, tana sakar masa murmushi.
Kamar wanda ake ja haka ya fara nufowa wurinta ya ware mata hannu alamun ta iso ta rungume shi, da gudu ta karasa kafin ya iso tana fadawa faffadan kirjinsa, ya kankame ta kam yana kumshe ido.
Ya rada mata a kunne. “ Kinyi kyau sosai”
Dariyan da ta dade bata yi ba ta masa tana cewa. “ Duk kaine ka saka kyau din”
“ Kyau dinki tun fil azal halilta ce, a cikin matan ke din ta musamman ce, ko an ware dubu da kyar a samu biyar masu irin kyau naki, Safeera ina alfahari da zamowa mijinki, Allah ya miki albarka”
Sake kankame shi tayi tana jin wani dadi na ratsa cikin jikinta, ya saka hannu yana tallafo da fuskarta, ya zuba mata ido itama tana kallon cikin idanunsa, ya bi bakinta da kallo yana jin kamar wani magnet na jansa, da sauri ya daura bakinsa akan lallausar labbanta ya soma tsotsa.
Saurin runtse ido tayi tana kai hannunta kan gemunsa duk da irin bugawar da zuciyarta ke yi, sake jawota yayi yana bata wani hot kiss wanda ya kusan zautar da su, ya riketa da hannu daya yana daura dayan kan bobs nata wanda suka cika saboda cikin jikinta.
Jikinsa ya soma rawa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 17