yaji kafafunsa ya gagara daukar shi, zamewa ta fara yi tana yin k’asa shi ma ya biyota, kwanta da ita ya fara k’ok’arin yi, kamar a cikin mafarki ya soma jin bugawar k’ofa.
Da sauri ta jame jikinta daga nasa ta tashi tana shigewa d’aki, numfashi ya sauke yana tashi wa ya gyara wandan shi da take k’ok’arin tona masa asiri, kafin ya ce. “ Waye?” Muryansa a dan dashe.
Ammar dake tsaye ya ce. “ Maye kazo ka bude min dalla, ko ka manta cewa ana jiran mu ne?”
Dafa goshi yayi dan shi gaba daya ma ya shafa’a, kafin ya ce. “ Ka danna 252555”
Ammar yayi tsuki yana danna pin din jikin k’ofar ya shigo, ganin ko shiryawa baiyi bane yasa ya ce. “ Uban me ka tsaya yi Sai….” Maganar ya makale lokacin da ya kalli idanunsa da suke ja, ya wani kumburo fuska yana hararan shi.
“ Ban fahimta ba,,, yaushe matar taka ta warke? Ko kayi wani aure ne”
Tsuki yaja yana wucewa d’akinsa, Ammar yabi bayan shi da kallo yana sakin wata kafurar dariya ya ce. “ Yanzu sai yace ni ne na hana shi k’arasa aikin da ya fara ko” kafin ya nemi wuri ya zauna yana jiran ya fito.
Bayan ta shiga d’akin ne ta rufo k’ofa da sauri tana murmushi, hango kanta tayi a mudubi da sauri tasa hannu ta rufe fuskarta tana fadin. “ Na boni ashe dama haka yake”
*Ni kuma daga gefe nace Aa ba haka yake ba🙄 har kika samu ciki baki san ya yake ba?*
Da sauri ta wuce toilet ta gyara jikinta jin muryan Ammar yasa ta sako hijab ta fito, tana fitowa ya fito fuska a tamke kamar wanda aka masa bushara da wutar jahannama.
Ammar ya d’aga ido ya kalle su yana kwashewa da wata muguwar dariya, da mamaki ta kalle shi, kafin ta kalli inda Saif yake, wani dariya ce ya zo mata amma ta datse tana cewa. “ Yaya Ammar ina wuni?”
Sai da ya tsayar da dariyar kafin ya amsa da. “ Lafiya kalau Amarsu, ya jikin naki?”
Ta sunkuyar da kai ta ce. “ Da sauki Alhamdulillah”
Saif ya kalle ta yana cewa. “ Za muje mu dawo”
Da sauri ta ce. “ Zan bika”
“ A’a ki zauna abinki”
Ta kwabe fuska ta ce. “ Dan Allah Yaya! Dan Allah! Tun da muke bamu taba fita tare ba”
Da sauri ya juyo yana kallon ta jin karyan da tayi, tunawa da abunda likita ya ce masa yayi < kwakwalwarta yana samun tabuwa, ma’ana yana dan kaucewa, zaka iya ganin wata rana tana yin abu kamar wacce bata sanka ba, ko ta manta mutane, sai kuma daga baya tana tunawa;>
Muryanta ya katsai shi ta hanyar cewa. “ Dan Allah”
Jinjina kai yayi yana kallon shigar da tayi, ganin babu wani error ne yasa ya ce. “ Mu je” daga haka suka fita dan Ammar ya dade da ficewa tun lokacin da take tambayar shi.
Ganin yanda mutane suka cika gidan ne yasa ta dan tsorata tana rike hannunsa, ya dube ta ya ce. “ Lafiya?”
“ Bakomai”
Murfin motan ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga, Ammar ya zauna a gefen Jon, da haka suka fice bayan mai gadi ya bude musu get.
*POLICE STATION*
Da sallama suka shigo, Ammar na gaba sai Saif kafin Safeera a baya. Sergeant ya bashi hannu suka gaisa yana cewa. “ Ku ciro su” Ita dai Safeera tsoro wurin ya bata hakan yasa ta makale a jikin Saif ta sunkuyar da kai.
Cofur Audu sai tunkude keyarsu yake yana famar Allah ya tsine musu, da haka su shida cif suka bayyana, Ammar ya ce. “ Ai ku daga ganin wadan nan kunsan yan iskan gari ne”
Saif ya ce. “ Allah ya kyauta, a mik’asu court sai muyi shari’a da su” Da haka ya mike, ita ma tana mikewa.
Daya daga cikin wadan nan din ya taba kafadan na gefen shi yana magana k’asa k’asa wanda Saif yake ji. “ Ka gane wannan yarinyar kuwa, ka manta ta ne?”
Saif ya juyo ya gan su yana fadin” Ku ka ce me?.
Idan bakuyi like ba bazan yi wani ba Aradu🫤🫤🫤
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 38*
*BOOK TWO*
Daya daga cikin wadan nan din ya taba kafadan na gefen shi yana magana k’asa k’asa wanda Saif yake ji. “ Ka gane wannan yarinyar kuwa, ka manta ta ne?”
Saif ya juyo ya gan su yana fadin” Ku ka ce me?.”
Da sauri suka sha jinin jikin su, hankulan police din ya koma kan su jin yana tambayan su, Ammar ya ce. “ Sun yi magana ne?”
“ Ina tambayar ku kuka ce me?”
Wanda yayi maganar ya girgiza kai ya ce. “ Ba da kai muke ba Wallahi magana muke yi wa junan mu”
Na kusa da shi din, wanda kallo daya zaka masa ka gane a buge yake ya ce. “ Cewa yayi yasan yarinyar kusa da kai, ko ba haka ka fada ba Jagwal?” Ya tambayi na kusa da shi.
Saif ya kalli Safeera wacce ta d’ago kai da sauri jin ansan ta ta kalle su, da sauri ta kankame shi tana ja baya ta buya a bayan shi, Ammar ya ce. “ Da walakin goro a miya”
Ogan nasu ne ya ce. “ Su suka ce sun santa amma nikam ban taba ganin ta ba”
Jagwal yayi wuf ya ce. “ Billahil lazi karya suke, duk mun santa idan karya ne mu tafi a tsaye”
Cofur Audu ya ce. “ Kai ku fadi gaskiya ko a gana muku azaba dan gusun uwarki shege yan kwaya”
Jagwal ya ce.” Baaba ka santa Wallahi, kayyy… kun manta yarinyar da Gandafi ya wurga a ruwa kwanakin baya ne… eyeeee”
Wanda yake a bugen ne ya ce. “ Kyale su yan iska duk sun sani…. ni da nace mu duba ko tana raye mu dauko ta ai ki kukayi” cewan Baaba.
Ogan nasu ya ce. “ Ku cire ni daga wannan lamarin ban sani ba” ya kalli Jagwal da Baaba da Gandafi.
Gandafi ya ce. “ Bari na fada muku gaskiya, kaga yarinyar nan mu muka tunkude ta a ruwa” Jagwal yayi saurin katsai shi ta hanyar cewa. “ Cewa zakayi kai daya ka tunkude ta”
“ Eh to koma me ne ne, ni na tunkude ta a ruwa, shi kuma Jagwal ya ce a duba ko bata mutu ba a ciro ta, sai Baaba yace mu shi bazai iya ba. Sannan Oga ya ce duk wanda zai biyo shi yazo mu tafi kar azo a kama mu,,, kaga yanda aka yi abun Oga” ya fadawa Saif.
Idan ran shi yayi dubu to ya baci, ya ce. “ Su biyun can fa”
Gandafi ya ce. “ A’a su lokacin a buge suke kamar yanda yanzu ma suke, basu san ma ya faru ba kawai muna tafiya da su ne amma da fatalwa muke tafiya”
Ammar ya jinjina kai ya ce. “ Sannun ku da k’ok’ari”
Cofur Audu ya sharba musu bulalan hannunsa, suka saki ihu yana cewa. “ Bata gari irin su sai irin mu mugaye”
Saif ya jawo da Safeera da ta buya a bayan shi ya ce. “ Kin san su?”
Ta kalle su da sauri ta dauke ido tana cewa. “ Na manta a inda na gan su”
Sergeant ya ce. “ Sir wannan kuma wani case daban za’a sake shigarwa, na kawo takarda a rubuta statement”
Ya girgiza kai ya kama hannun Safeera ya ce. “ Mu hadu a kotu kawai” ya juya suka fita Ammar na fad’in. “ Laifin ku yayi yawa, tirr da kalan halin ku” shi ma ya tafi.
A mota Ammar ya ce. “ Safeera ki ka ce kin manta inda kika san su?”
Saif ya katsai shi ta hanyar cewa. “ Haka dai ta ce, kasan sai a hankali sai anayi ana hakuri da wasu abun, dan akwai matsala dama”
Ta kalle shi ta ce. “ Ni din ce da matsala?”
Yayi saurin girgiza kai yana fad’in. “ Ke kuma? A ina ke nan? A’a wani hiran mu daban muke yi, ai ke yanzu Lu’u lu’u ce sai da kulawa”
Murmushi kawai Ammar yayi yana danna wayansa, Jon kuma hankalin shi na kan tukin shi, da haka aka isa gida.
Ammar ya koma cikin masu zaman makoki, Saif ya kama hannun Safeera suka nufi bangaren Ummah, ta kalli bangaren Mom tana cewa. “ Matar chan tana nan?”
Ya dubi inda ta nuna ya ce. “ Wa ya sani ne” da haka suka shiga falon Ummah da sallama a bakinsu, mutane sun cika falon tim, da makwabta da abokanan arziki, da yan gulma.
Ta zame hannunta daga nashi, suka gaishe da mutanen falon kafin ya nufi d’akin Ummah tana biye da shi.
Makwabciyarsu wanda suke kira da Maman Ihsan ta yiwa na gefen ta magana da murya k’asa-k’asa. “ Ita ce wanda ya yiwa fyade ubansa ya aura masa ita”
Wanda suke gulmar ne ta ce. “ Amma fa yarinyar tana da kyau”
Maman Ihsan ta tabe baki ta ce. “ Ina fa taga kyau, mutum kamar aljana, ni da naso uwarsa tace ya auri Ihsan dina amma yaki” haka suka ta dibarwa kansu zunubi.
Ba kowa a dakin sai Ummah, wacce ita ma waya tazo yi ta bar falon, da sallama suka shigo Ummah ta amsa musu cikin sakin fuska tana fadin. “ Mara lafiyan har ta warke ne?”
Ta sunnar da kai tana durkusawa har kasa. “ Ummah ina wuni?”
“ Lafiya kalau ya karfin jikin?”
“ Alhamdulillah “
Asabe ce ta shigo da sallama a bakinta hannunta rike da tray, kallo daya Saif ya mata yana dauke kai, ta gaishe da Ummah tana gaishe da Saif, ya amsa ciki ciki, ganin bata gaishe da Safeera ba ne yasa ya ce. “ Ke!”
“ Na’am”
“ Ba’a koya miki gaishe da manya bane”
“ Yallabai na gaishe ka fa” Ta fada cike da bakij ciki.
“ Ita matar tawa rainata kika yi?”
Bata ba shi amsa ba, ta kalli Safeera da su take kallo ta ce. “ Ina wuni”
“ Lafiya”
Ummah ta ce. “ Tashi ki je abinki Asabe”
Tashi tayi ta nufi kofa zata bud’e, ta juyo suka hada ido da Safeera tayi kwafa a ranta kafin ta fice daga dakin.
Ummah ta dubi Saif tana cewa. “ Ka duba Mom dinka kuwa?”
Samun guri yayi ya zauna kusa da Safeera ya ce. “ Ban je ba, ni tunda abun nan ya faru ma ban sake waiwayarta ba”
“ Ka je ka dubata dai”
“ Tam” suka dan taba hira da Ummah akan mutuwar Radiya, nan Safeera ta san me ya faru, kafin daga bisani ya mike zasu fita Ummah ta ce. “ Ta samu ta huta dai”
Ya kalli Safeeran yana cewa. “ In Sha Allah zata huta sosai” ya karashe maganar yana kashe mata ido daya.
Da haka suka fita daga bangaren.
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 39*
*BOOK TWO*
Ya kalli Safeeran yana cewa. “ In sha Allah zata huta sosai” ya karashe maganar yana kashe mata ido daya suka fice daga bangaren.
A bakin part nasa ya barta dan yasan idan ya shiga sai ya aikata wani abu, hakan yasa ya juya ya koma cikin jama’a bayan ya barta ta shiga.
A kusa da Ammar ya zauna yana fad’in. “ Sannu ka samu kayi wanka mana”
“ A dakin naka zanyi bayan kayi aure dan uwarka” ya fada da murya na iya su biyun za su ji.
Saif yayi murmushi ya ce. “ A huce haka, amma ai bance kar kayi aure ba”
“ Bana son gori”
“ Shikenan” kafin ya kuma cewa, “ Dad yana kwance a hospital kuma inason zancen aurena da Jannah ya taso”
Ammar ya masa kallon mara hankali yana cewa. “ Ai ko Dad lafiyansa kalau bai kamata kayi aure yanzu ba, matarka fa ba lafiya tana buk’atar kulawa, gashi ka ce tana da karamin ciki kaga bai kamata ka taso da zancen aure ba, auren ma da kawarta Jannah”
Yayi murmushin da shi kadai yasan ma’anarsa ya ce, “ Ammar kafin nasan Safeera sai da nasan Jannah, asali ma nafi wahalal da Jannah akan Safeera, kaga ko nace zan aureta ba laifi nayi ba,,, batun kawancen su kuma su suka hada kansu dan ni bansan yaushe hakan ta faru ba”
“ Saif a ganina ka kyale Jannah tayi rayuwarta kawai tunda kayi aure, itama ka barta taje ta auri wani”
“ A gaskiya bazan iya ba, dan inason Jannah tamkar raina, ita kuwa Safeera jinta nake tamkar bugawar numfashi na a zuciya, kaga dukansu biyu bazan iya rayuwa babu su ba”
“ Allah baku zaman lafiya” Ammar ya fada a takaice, Saif ya amsa da Amen yana kau da kai gefe.
Ko da ta shiga bangaren nasa, dakinta direct ta nufa ta cire hijab ta hau gado bacci na daukar ta.
A cikin wani irin yanayi suke tafiya wanda kallo daya zaka musu ka gane yunwa ya gama lahani da rayuwarsu, yarinyar da take rike da robar ne ta goge gumin da ya karyo mata tana cewa, “ Mama ki zauna ni zan nemo mana a inda zamu samu abincin”
Matar ta girgiza kai ta ce. “ Nabila tun safe haka muke, munyi baran amma shuru babu, ga can Ammi tana kwance kamar gawa, ni na kwammace da mutuwa akan wannan rayuwar”
“ Mama Allah bai manta da mu ba, kuma In sha Allah zai taimaka mana”
Tsayawa da tafiyan suka yi suka samu guri kusa da kwalbati suka zauna, suna kallon motocin dake tafiya, Mama tayi murmushi ta ce. “ Ko ina Safeera ta shiga kuma sai Allah”
Nabila ta dafa hannun matar tana cewa. “ Mama ni nasan da Safeera ko Raudah daya yana nan Wallahi ba zamuyi wahalan nan ba”
“ Ita kaddara rubutacciya ce, tun kafin mu fito duniya shi ya iso”
“ Mama….” Maganar ce ta makale lokacin da wani mota bak’i ya tsaya a gabansu, suka yi saurin tashi tsaye suna bin motan da kallo.
Bude murfin motan akayi mamallakin motan ya fito, yana sanye da Army trouser da black tea sheet, fuskarsa kamar kullum a sake, ya dube su da kyau ya ce, “ Sannun ku”
Mama taga Nabila suna had’a ido, kafin ta amshe da cewa, “ Yauwa dai sannu yaro”
Ya gyara tsayuwar shi yana kallon su mekyau, wanda ko ba’a fada kasan uwa da y’a ce, kafin ya ce, “ Nasan an hana bara a garin nan, amma ku naga kuna yi”
Mama tayi saurin cewa, “ Bawan Allah kuyi hakuri, Wallahi mun san an hana amma yunwa ce zata kashe min yara, dole tasa na fito ko zan samu”
Ya jinjina kai yana zancen zuci, ‘ kenan har yanzu ana wahalan yunwa, to me amfanin shuwagabannin mu da bazasu iya biyawa mutane buk’atan su ba, kenan basu da amfani’ kafin ya bude gaban motansa.
Nabila taga Mama tana mata alama da su gudu kar ya zama dan yankan kai ne, Mama ta mayar mata amsa ta ido akan cewa su tsaya.
Rufewa yayi hannunsa rike da dimin kudi wanda a kalla zai kai dubu dari ya mikawa Mama, Mama tabi kudin da kallo tana cewa, “ Na me kenan bawan Allah”
Yayi murmushi wanda yasa dimple nasa lotsawa ya ce, “ Kyauta na baku”
Nabila tayi saurin amsa tana cewa, “ Allah ya biyaka da gidan Aljanna, mun gode sosai”
Yayi murmushi ya juya zai shiga motansa Mama tayi saurin katsai shi ta hanyar cewa, “ Bawan Allah, Allah ya baka abinda kake so”
“ Amen,,,, amma ki min addu’a dan kema uwa ce a gurina, kuma addu’ar uwa karbabbiya ce!”
Mama ta danyi shuru sannan ta ce, “ Wani addu’a kake buk’ata?”
“ Allah ya hadani da yarinyar da nake nema”
“ In sha Allahu zaku hadu, Allah ya hadaku! Allah ya maka albarka”
Ya amsa da Amen sannan ya shiga mota, har zai rufe Mama ta ce, “ Bawan Allah sunanka fa?”
“ Haris!!!”
Mama ta jinjina kai, daga haka ya tafi ya bar wajen.
Nabila taga Mama suka hada ido sannan ta ce, “ Kin ga Allah bai manta da mu ba Mama”
“ Haka ne Nabila” sannan suka mike, Mama ta ajiye robar dake hannunta ta amshi kudin hannun Nabilan sannan suka tsallake kwalta.
Wani kango suka shiga wanda babu windo da kofa, cilin ma ba’a saka ba.
Da gudu Ammi ta nufo Mama tana fadin, “ Mama yunwa”
Mama ta kira Umar, ya taso da kyar dan yunwa ya gama shiga jikinsa, dan ya koma bak’i ya rame sai tsayi, ya iso yana zama ya ce, “ Mama ga ni”
Mama ta ciro dubu uku daga cikin kudin ta mik’a masa ya amsa sannan ta ce, “ Ka siyo mana gari da suga da gyada da madara sai ruwa” jikinsa har rawa yake ya amsa ya tafi aiken da sauri.
Falmata da take tsaye jikin bango ne ta dubi Nabila ta ce, “ A ina kuka samu kudi?”
Nabila ta ce, “ Wani mutum ne ya bamu kudi”
“ Allah sarki Allah ya biya masa bukatun shi, mun gode” sannan ta k’araso ta ce, “ Mama ki zauna ki huta”
“ Falmata ina naga hutu baku ci abinci ba, ki dubi Ammi da Amma kamar mutum mutumi”
Nabila ta ce, “ Anuty Falmata idan mun sha garin sai mu kwanta sai gobe”
Ammi ta ce, “ Mama za ki siyamin mota da jirgi ko”
Duk sukayi dariya, Mama na cewa, “ Har yanzu Ammi baki girma ba, eh zan siya miki har da keke Napep”
Falmata ta bude baki zata yi magana suka ji ana sallama daga waje, Mama ta juya dan ganin waye ne, ido hudu suka yi da shi yana kallon su hannunsa yana cikin aljuhun wandonsa yana washe mata baki…
*SAHIBA CE✍🏼*
*BAƘAR ƘAUNA❤️🩹*
*Na*
*FATIMA ISA MANU🦚*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )✍🏼🦋_
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbAnyqU05MUeZnXKtP1z
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*GARGAƊI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*Page 40&41*
*BOOK TWO*
Falmata ta bude baki zata yi magana suka ji ana sallama daga waje, Mama ta juya dan ganin waye ne, ido hudu suka yi da shi yana kallon su hannunsa yana cikin aljuhun wandonsa yana washe mata baki.
Mama ta ce, “ Bawan Allah lafiya haka?”
Baffa yayi dariya sannan ya ce, “ Na baki tsoro ko? Kuyi hakuri”
“ Ba komai” Mama ta fada tana jiran taji da me yazo, dan ta tsorata kar sawunsu aka biyo a kwace kudin,, Baffa ya katsai mata zancen ta cewa, “ Ina mai gidan?”
Falmata ta gansu sannan ta ce, “ Bamu san shi ba, mu kawai zama muke a ciki”
Baffa ya sake washe baki yana cewa, “ Kin ga yarinya ba mai gidan nan nake nufi ba, ina nufin Ubanku”
Mama ta amshe zancen da cewa, “ Ya rasu ai, amma Malam ba Ubanku ake cewa ba Babanku zaka ce”
“ Hausar nawan ce sai a hankali dai, amma kuyi hakuri”
Mama ta ce, “ Ba matsala”
Gyara tsayuwarsa yayi a jikin motan, dan har yanzu inda aka dakeshi yana masa zafi sannan ya dubi Mama da kyau ya ce, “ Idan ba damuwa inason magana da ke”
“ Amma lafiya? Ko laifi muka maka ne?”
Ya girgiza kai, “ Ko kadan asali ma alkhairi nake tafe da shi,”
Mama ta kalli yaran nata sannan ta ce, “ Falmata ja kannenki ku shiga ciki,” ta gyada kai tana kama hannun Ammi da Amma ta saka Nabila a gaba suka shige d’akin da suke kwana wanda ko leda babu sai yashi, zanin su suke shimfidawa suke kwanciya, ga sanyi.
Umar ya shigo da saurin shi dan ya kawo musu su jik’a su sha, Mama ta ce, “ Kai ma ka wuce ciki, ku fara sha ina zuwa,” Ya gyada kai ya nufi ciki yana waigowa yana kallon Baffa.
Cikin ran Baffa kuwa tarin tambayoyi ne, ‘ Kadde wadan nan duka zuri’arta ce, kutumar jar uba kenan, haka nakeso daga gani wannan zata ci uban Innar Jannah’
Mama ta ce, “ Ina jinka”
Baffa ya saki murmushi yana cewa, “ Yawwa ba komai bane ke tafe da ni sai alkhairi kamar yanda na fada miki tun farko,” Mama ta jinjina kai alamun tana saurara, ya cigada jawabi, “ Wadan nan yaran naki ne?”
“ Eh”
“ To bayan su akwai wasu ne?”
“ Lafiya dai ko?”
“ Lafiya kalau, tambaye ce kawai”
“ Eh akwai guda uku, biyu sun bata daya tayi aure bata sake dawowa ba”
‘ Ahh wannan oga ce, yara har takwas, duk da haka dai ba ja baya’ ya saki murmushi a zahiri yana cewa, “ To Allah ya raya su” Mama ta amsa da Amen, ya daura da cewa, “ Ni da ke dai duk ba yara bane, kuma a wannan shekarun idan kinga mutum yazo wajen ki kinsan me yake nufi”
“ To akwai wacce ta maka ne a cikin yaran nawa da kazo?”
“ Ko kadan, ai yaranki yara na ne,,, ni Mamarsu ma nake nema”
Mama ta saki baki tana kallon shi, ya bud’e mota ya ciro kudi yana mik’a mata ya ce, “ Ansa ko zaki siya kayan kwalliya”
Mama tabi kudin da kallo ta d’aga kai ta kalli sararin samaniya tana fad’in, ‘ Allah iya yau kadai ka nuna mana kana tare da mu kuma baka manta da mu ba,’ sannan ta saka hannu ta amshi kudin,
Baffa ya ce, “ Kiyi shawara da yaranki danni ko yau a shirye nake da a daura auren” sannan ya shiga mota ya ce, “ Gobe zan waiwayo naji inda aka tsaya”
Ta gyada masa kai dan ta gagara magana, ya tada motansa yana barin wurin, Mama ta juya ta koma ciki.
Ko da ta shiga ta same su sunyi jigum-jigum suna jiranta, Mama ta ce, “ Lafiya har yanzu baku fara sha ba”
Nabila ta ce, “ Mama muna jiranki ne” suka bi kudin hannunta da kallo.
Ta mik’awa Falmata kudin sannan ta zauna a tsakanin su tana cewa, “ Nabila je ki nemo ludayi, Ammi da Amma ku je waje ku gyara kyadan, Umar je ka jik’a garin” duk suka mik’e dan cika aikin.
Mama ta dubi Falmata da ta zuba mata ido tana jiran k’arin bayani, sannan ta zauna me kyau tana kallon yarinyar nata da yanzu ita ce abokiyar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 17