Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shuru kiyi.” Cike da zafin rai da kuncin zuciya ta ce. “ Kana yankewa yaran mutane hukunci akan aikata fyade har ka turasu gidan yari, ashe kai ma kana aikatawa, ko kana ganin dan kai Alkali ne yasa baza’a hukunta ka ba? To Wallahi ka sani akwai ranar sakayya, akwai ranar tsayawa, ranar da kai ba komai bane a gurin Ubangiji face bawansa wanda baya tsoron fushinsa…” Lafiyayyun mari ya sauke mata yana nuna ta da hannu ya ce. “ Ki fice min daga gida.” Murmushin da yafi kuka ciwo tayi ta sauka daga kan gadon ta fita daga gidan, tana tafiya tana kuka. Ko da ya koma gida Mom ta tusa shi a gaba tana tambayarsa me ya faru, inda ya fada mata komai da komai. Cike da murna ta soma cewa. “ Kamin dai-dai Saif, duk yarinyar da ta maka kyau kawai ka aikata abun da yazo kanka.” Nan ta cigaba da daura masa hudubar da zai kaisa ga halak’a, shi kuma ya dauka. Ammar ya sha fada masa cewa ya nemo Jannah ya bata hakuri, amma fir ya ki wai ajinsa zai zube, ba yanda ya iya da aminin nasa dan haka bai sake cewa komai ba, duk da kuwa tun wannan abun ya faru bai sake yi ba, ko da kuwa Mom ta tambaye shi sai yace eh yayi, dan abun yanzu ya fara daure masa kai, yana ganin Mahaifiyarsa amma baya so yi mata magana. Cases din da yayi akan aikata fyade babu adadi, dan yanzu ya zama Lawyer mai zaman kansa ne, duk inda ka shiga a garin borno kana cewa *_BAR SSS_* to fa ansan shi dan yayi suna sosai a taimakon mutane da kwachowa yan mata hakkin su. Yau Saturday yana gida, kuma bai shiga bangaren Ummah ba haka ma Mom, dan Mummy dama baya shiga, yana bangaren shi zaune yana dannan waya. Sallama akayi aka shigo, d’aga kai yayi ya ganta Radiya ce kanwar Mom wanda jiya tazo. Isowa gurinsa tayi ta zauna a kusa dashi tana cewa. “ Ya Saif morning.” Ba tare da ya ganta ba ya ce. “ Morning dear, how are you?.” “ Am fine.” Kowa yayi shuru, kafin ya ce. “ Akwai wani abu ne?.” Murmushi tayi tana cewa. “ Yaya dama so nake muje outing ne.” Gyada mata kai yayi ya tashi ya ce. “ Ba yau ba.” Daga haka ya shige daki, ita kuma ta tashi ta fice ranta a bace. Yana shiga daki ya kama mararsa yana cije lebe, wayansa ya dauka ya kira amintatcen driver dinsa wato Sageer, bugu daya ya dauka. Gaisawa suka yi duk da yaji muryan ogan nasa kamar ba lafiya, kafin Saif ya ce. “ Wata nakeso ka samo min amma yarinya, zata min aikin shekara daya ne.” Tsaf ya gane Ogan nasa haka yasa ya ce. “ Sir nace ka shirya muje to.” Shuru Saif yayi kafin ya ce. “ Ok ina zuwa.” Da haka ya shirya ya fito, yana tafiya yana dan daga kafa a hankali, a bakin falo Sageer yayi parking hakan yasa ya shiga ciki, mota biyu na mara musu baya. Wajen 20 houses suka yi parking, Saif ya kalli Sageer ya ce. “ Wa ka sani a nan? Bana son wacce take kazanta fa.” “ Sir nasani, nan y’an mata suna zuwa idan basu da gida ko marayu ko y’an gudun hijira.” Gyada kai Saif yayi kafin ya ce. “ Hope plate number mota a rufe?.” Sageer ya ce. “ Eh kana cewa zamu fita na rufe duka ukun.” “ Gud, sauri ina jiranku.” Ya fada yana dauke kai. Shiga Sageer yayi yana kallon gidan, y’an mata da karuwai sai matsowa gurinsa suke, hango wata yarinya kyakkyawa yayi tana tsaye daga gefe ta kame jikinta, hannu ya d’aga mata, nuna kanta tayi ya gyada mata kai. A hankali ta fara takowa zuwa gurinsa, cikin muryanta mai dadi da amo ta ce. “ Ina wuni?.” “ Lafiya.” Sageer ya fada yana kallon ta tun daga ssma har k’asa, kafin ya kalli fuskarta a ransa ya ce. ‘ TABARAKALLAH.’ A zahiri kuma ya ce. “ Ya sunanki?.” “ Safeera.” Ta furta a hankali. Gyada kai yayi ya ce. “ Safeera aiki zakiyi wa Ogana har na shekara daya.” Da sauri ta daga kai ta kalle shi ta ce. “ Nawa zai biya ni?.” “ Zamu baki 5m.” Shuru tayi tana tunani kafin tace “ Yana ina?.” Tafiya ya yi tana biye dashi, a bakin kofar gidan suka tsaya ya nuna mata motan tsakiya ya ce. “ Yana ciki.” Kafin tace. “ Nawa zai biya?.” *Masu karatu idan baku manta ba nan ne farkon littafin ko? To yanzu zamu daura daga inda muke.* *CIGABA DA LABARI* Shower 🚿 ya sakarwa kansa ya dafe jikin bango, tunani ya fara yi tun sanda ya fara aikata zina, gani yake kamar bai aikata ba, ji yake kamar tursasa shi ake yi yake yin wasu abubbuwan. Jikinsa kwata-kwata bai basa cewa wai shi yayi zina da Jannah da Safeera ba, wai tukun nan ma ina suke? Ya tambayi kansa kafin ya furzar da iska yana dungule hannu ya kai naushi da karfi. Bai san sanda ya saki ihu ya furta. “ Safeera!!!!!.” Wanda kusan sai da ya dauki gidan. Daura towel yayi da sauri a kugunsa ya fito, inda ya jefar da wayansa ya koma ya dauka, number dazun ya kira, safa da marwa ya fara sai da ya kusa katsaiwa kafin aka dauka. Da sauri ya ce. “ Dan Allah wacece ke?.” Ta cikin wayar matar ta ce. “ Kai fa ka kirani.” “ Eh nasani, amma dan Allah kina wani unguwa ne ko gari?.” “ Malam lafiya kuwa na maka wani abu ne kakeson ka kamani?.” Dafe kai yayi ya ce. “ A’a babu abunda kika yi, kawai so nake na sani.” Shuru akayi kafin ta ce. “ Ina Maiduguri wajen 20 house’s.” Jijjiga kai ya mata kamar tana kallonsa ya ce. “ To na gode, dama tambaya nake ko Safeera tazo.” Shuru tayi ta ce. “ Safeera tun jiya da safe bamu sake ganin ta ba har yau.” Wani numfashi ya sauke kafin ya ce. “ Ke din y’ar uwarta ce?.” “ A’a haduwa kawai muka yi.” “ To shikenan nagode.” Ya karashe jiki a sanyaye wanda ya rasa na meyasa. Number Sageer ya danna, bugu biyu ya dauka yana cewa. “ Sir nazo kuma ka fita.” Bai kula zancen nasa ba ya ce. “ Sageer bayan gidan da muka je dauko yarinyar nan kasan wani gurin da take zuwa kuma?.” “ A’a Sir, dan nima ranar ce na fara ganin ta a rayuwata, amma lafiya ai naga kuna tare.” Sageer ya fada yana mamaki. Numfashi Saif ya sauke ya ce. “ Sageer wai na kore ta ne.” “ Bangane ba Sir? Kana cewa wai, me hakan ke nufi ba kai ka kore ta ba tafiya tayi?.” “ Sageer bata min rai tayi shine nace ta tafi.” “ Sir kuma ta tafi?.” Kamar zai yi kuka ya ce. “ Eh fa kuma idan na zauna sai ina kallon ta tana naiman taimako na, Sageer akwai abun da ya samu yarinyar nan, Sageer Safeera tana cikin matsala duk da nasan ni ne silan komai amma nasan ita ba karuwa bace, ai kaga da ita karuwa ce to gidan zata koma amma kaga bata koma ba, zan mutu idan banganta ba, akwai hakkinta akai na, Sageer ina Safeera take?…. *DR TEEMERH ✍🏼* 8- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 Gajeran labari Na Fatima Isa Manu DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU ) *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 8* Kamar zai yi kuka ya ce. “ Eh fa kuma idan na zauna sai ina kallon ta tana naiman taimako na, Sageer akwai abun da ya samu yarinyar nan, Sageer Safeera tana cikin matsala duk da nasan ni ne silan komai amma nasan ita ba karuwa bace, ai kaga da ita karuwa ce to gidan zata koma amma kaga bata koma ba, zan mutu idan banganta ba, akwai hakkinta akai na, Sageer ina Safeera take?.” Duk ya rikita shi yama rasa taya zai fara, yasan waye Saif kuma yasan halinsa, sai dai kwanan nan ya canza hali gaba daya. Muryansa ne ya katsai Sageer jin yana cewa. “ Baka ce komai ba ko na fita naimanta ne?.” Saurin girgiza kai Sageer yayi yana cewa. “ Sir zan nemo ta.” “ To kayi sauri.” “ Ok.” Numfashi ya sauke ya zauna yana tunani. *SAFEERA POV* Wani karamin bukka ne na kara an masa ado da kayan da, sai ka sunkuya kafin zaka iya shiga cikin bukkan. Wani tsoho ne ya shigo da kwarya a hannunsa ciki da ruwa, sai da ya sunkuya kafin ya shiga cikin bukkan. Inda mutun yake kwance akan gadon kara ya nufa, ajiye kwaryan yayi a gefe kafin ya zauna kusa da gadon kaban. Addu’a yayi yana tofawa kafin ya janye gashin da ya rufe fuskarta, kyakkyawar fuskarta ya bayyana mai cike da nutsuwa, a hankali ya fara karanto addu’a yana tofa mata da ruwa. Ya kusa mintuna goma yana yi kafin ya tsaya yana kallo hannunta din da ya fara motsi, cigaba da yi yayi yana watsa mata ruwan a fuska, wani dogon numfashi taja tana saukewa tare da bud’e idanunta. Murmushi dattijon ya mata yana cewa. “ Alhamdulillah kin farka, kina gani na ?.” Zuba masa ido kawai tayi tana kallon shi, kafin ta sake lumshewa a hankali ta bud’e. Muryanta a sanyaye ta ce. “ Waye kai?.” Tashi yayi da sauri ya nufa waje, ta bisa da ido, ko seconds bai yi ba ya dawo shi da wata mata fara kyakkyawa, nan ma bata ce komai ba sai kallon su da take yi. Zama suka yi a gefen ta, matar na cewa. “ Ya sunanki yarinya?.” “ Safeera.” Ta fada a sanyaye. “ Daga ina kike?.” Kallon dakin tayi kafin ta ce. “ Ina ne nan?.” Tsohon ne ya ce. “ Borno ne.” “ Wani unguwa?.” “ Bulunkutu.” “ A ina kuka samo ni?.” Matar ta ce.” Yanzu dai kiyi wanka tukun, sai kici abinci kafin mu fara.” Gyada kai tayi, k’ok’arin tashi ta fara Inna tasa mata hannu tana kamata, a hankali ta saukar da kafarta tana kallon yanda yaji ciwo ya gurgurje, hannunta ta gani yanda shima yaji ciwo, numfashi ta sauke a hankali kafin ta kalle su tana cewa. “ Nagode.” Murmushi Bappa ya mata yana cewa Inna ta kaita tayi wanka, shi kuma ya tashi ya fita. Bayan sun fito daga band’akin ne Inna ta bata kaya ta ce ta saka, karba tayi ta saka tana godiya, Inna ta tashi ta fita. Shuru Safeera tayi tana kallon hannunta din da yaji ciwo sosai, hawaye ne ya zubo ba tare da ta sani ba, hannu tasa ta goge, Inna ta shigo da kwarya a hannunta. A gabanta ta ajiye, murmushi Safeera ta mata tana cewa. “ Inna sannu.” “ Yawwa dai y’ar nan, sauko na baki abinci kici dan tun da aka dauko ki daga bakin kogi har yau baki ci komai ba.” Inna ta fada tana bude biski da miyan alaiyaho da ta kawo. Da mamaki Safeera ta ce. “ Inna kwanana nawa a nan?.” “ Kinyi wata daya da kwanaki fa.” A dan tsorace ta ce. “ Kuma ban mutu ba ina raye?.” Murmushin manya Inna ta mata tana cewa. “ Kina wasa da lamarin Ubangiji ko? Ki godewa Allah kawai da yasa kina raye, amma lokacin da muka tsintoki mun dauka ma bakya raye, saboda irin ciwukan da yake jikinki.” “ Nagode.” Ta fada a sanyaye tana saukowa ta fara cin abinci. *SAIFULLAH POV* Tun bayan da ya kori Safeera hankalinsa bai sake dawowa jikinsa ba, ko zama yake ita yake kallo ko tafiya yake ita yake kallo ko bacci yake ita yake kallo, lokaci daya ya rame yayi duhu, duk cases din da yake dasu a court baya zuwa sai dai ya tura Ammar yayi wakilcinsa. Baya yi wa kowa magana a gidan, kullum yana bangarensa baya fita, abun duk ya damu Ummah da Dad, duk da kuwa ko da yana fitowan ba kulasu yake ba. Mom ma abin ya fara daure mata kai dan ko ta kirasa a waya baya picking, bata ganinsa ma bare ta tambaye shi, ya daukewa kowa na gidan kai. Idan kaga yana waya to da Ammar ne ko Sageer, Sageer din ma suna waya ne dan ko yaji labarin Safeera amma shuru. Idan yaji yunwa sai dai yaje kitchen ya hada tea ☕️ ya sha, abinci ya manta rabonsa da ci, ya baza hotunanta a gari da gidajen radio 📻, kuma ya saka kudi da mota ga duk wanda ya samo ta, amma kullum labarin daya ne babu ita. Yau ma yana zaune a falonsa, yayi duhu ya rame sai ido, gashin kansa ko gyara babu, yana sanye da three quarter baki da tea sheet fari, hannunsa rike da cup da black tea ☕️ a ciki, yana sha yana kallon hotonta da ya dauka bata sani ba lokacin da suka je dauko ta a 20 houses. Yana kallo yana tunani, hankalinsa duk baya jikinsa, yayi zurfi a tunani, fuzge wayan akayi a hannunsa. Shuru yayi bai dago kai ba dan yasan sarai waye ne da wannan aikin, rai a bace Ammar ya ce. “ Saif yaushe zaka daina tunanin banzan nan ne? Dubi yanda ka rame kayi baki ka lalace akan mace, macen ma karuwa…..” Bai karasa ba ya cukume wuyan rigarsa yana huci yake cewa. “ Ko da wasa kar ka sake cewa Safeera ta karuwa, ko da duniya zata kalle ta da wannan sunan ni bazan taba ganinta dashi ba, saboda idan ma ta baci ni na bata ta, ni zaka kira da gwarto ba ita ba, akanta babu abunda bazanyi ba dan ni na cuce ta.” Ya karashe yana sakar masa kwala. Baki a sake Ammar yake ganinsa har ya gama, kafin ya jijjiga kai yana cewa. “ Na fahimta, ashe shi soyayya babu ruwansa da kai waye, wai yau *BAR.SSS* kuma aminina yana k’ok’arin dukana akan mace yar kwalta.” A tsawace ya furta. “ Ammar ya isa!!!!, ka daina kiran Safeera da banzayen suna.” “ Naji Saif kuma na daina, sai dai ka sani wannan tunanin bashi zai saka ta dawo ba dan bata ma san kanayi ba, sannan ka sani al’umma suna buk’atar ka, kuma mutane dayawa suna jiranka a court dan shari’arsu yana hannunka.” Ya kai karshe yana juyawa zai fita. “ Bani wayana sai ka tafi.” Mika masa yayi yana tausayin shi, dan yasan yanzu ya fara dan akwai hakkin Jannah ma ga kuma na Safeera, idan har bai nemo su ba ba lallai ya samu sukuni ba. *UMMAH POV* Tana zaune akan sallaya tana addu’o’i, hannu ta d’aga sama tana addu’a hawaye na gangaro mata. “ Allah ka fini sanin komai, Allah kai kasan me ke faruwa da dana, ya Allah na roke ka ka dawo min dashi gare ni, Allah ka kare shi a duk abubbuwan da yake yi, Allah ka shiga lamarinsa…. Amen.” Hawayen ta goge tana tashi ta nade sallayan ta fito falo, yau girkinta ne amma Dad tun da safe ya fita a gidan kuma kafin ya dawo sai dare kusan goma. Abincin dare ta dafa tuwo miyan egusi, dan favorite din Saif ne, tana gamawa ta had’a a kula ta saka a basket 🧺 ta nufi bangaren shi da addu’ar Allah yasa kar ya mata wulakanci. Ko da ta isa bangaren a bud’e tun bayan fitan Ammar ba’a rufe ba, sallama tayi ta shiga falon zuciyarta na harbawa cike da tsoron dan nata. A inda Ammar ya bar shi a nan yake bai tashi ba, yaji sallaman sarai amma bai amsa ba kuma bai daga kai ya kalle ta ba. Inda yake ta iso tana kallon yanda ya koma, kwalla taji yana k’ok’arin zubo mata tayi saurin saka hannu ta goge tana cewa. “ Saif.” Bai kulata ba ya cigaba da kallon wayansa, sake kiran sunansa tayi a karo na biyu, nan ma bai amsa ba. Zama tayi a kusa dashi, da sauri ya tashi tsaye zai tafi, hannunsa ta kama hawaye na zarya akan fuskarta tana fadin. “ Ka saurere ni mana ko sau daya ne yarona, ni fa Mahaifiyarka ce.” Lumshe ido yayi yana jin wani iri a zuciyarsa game da kukan nata, kuma ya gagara kwace hannunsa daga nata sannan ya gagara tafiya, haka kawai ya tsinci kansa da zama a gefenta din. Numfashi ta sauke tana cewa. “ Saif kaci abinci dan Allah ba dan ni ba.” Gyada mata kai yayi duk da kuwa bai juyo ya ganta ba, sake cewa tayi. “ Dubi yanda ka rame kamar ba kai ba me ya same ka ne?.” Muryansa chan kasa ya furta. “ Babu komai.” Sanyi taji a ranta jin cewa ya mata magana, hakan yasa ta ce. “ Bari na zuba maka abinci ko.” “ Ba yanzu zanci ba, idan ina buk’ata anjima zan diba ki tashi ki tafi kaina yana ciwo.” Ya fad’a yana lumshe ido. Gyada kai tayi tana tashi da sauri ta nufi kofa, tana tafiya tana juyowa tana ganinsa har ta fita. Tashi yayi ya rufe kofar ya koma ya kwanta. *DR.TEEMERH✍🏼* 9- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 Gajeran labari Na Fatima Isa Manu DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU ) *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 9* Tashi yayi ya rufe kofar ya koma ya kwanta. Kwanciya ya yi amma sai dai ba bacci yake yi ba, idanunsa ne kawai a rufe amma zuciyarsa a bud’e take, tunaninta yake ko a zaune ko a kwance, ya rasa ta ina zai samota. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tashi yana bud’e abincin da Ummah ta kawo masa, duk da yasan favorite dinsa ne amma ba a lokacin nan yake buk’ata ba. Tsakura ya yi yana rufewa, kana ya tashi ya nufi dakinsa. *MUMMY POV* Yau hankalinta kwata-kwata baya jikinta, tun da aka kirata a waya aka ce Saif baya fita kullum yana gida, ta rasa ta wani hanya zata bi dan a kashe mata shi, ga shi bama zuwa gurinta yake ba balle ta saka masa ko poison a abinci. Tana cikin tunanin zucin ne aka yi sallama, dago da kai tayi tana kallon matar da ta shigo, tuluk’a ce kuma bak’a, ba wani kyau ne da ita ba, sannan bata da tsayi, kawar Mummy ce wacce suke kullawa tare wato Fauziyya. Murmushi Mummy ta mata tana tashi tsaye, rungumar junansu suka yi Fauziyya na cewa. “ Me ya faru naganki duk cikin damuwa? Akwai wani abu ne?.” “ Ai gwara da kika zo Fauziyya, zauna tukun na kawo miki ruwa da abinci sai mu fara.” Mummy ta fad’a tana wucewa kitchen dan samo mata abun da zata ci. Kallon falon Fauziyya ta fara yi tana tabe baki, tare da bacin rai wanda lokaci daya ya bayyana akan fuskarta, a ranta ta ce. ‘ Idan ban fitar dake daga gidan nan ba hankalina bazai kwanta ba sam, kina cikin daula ni kuma ina chan ina neman abun da zan ci, hmmm.’ Isowa Mummy tayi da tray a hannunta ciki dauke da drinks da abinci, ajiye mata tayi tana cewa. “ Ki ci kafin mu daura.” “ To.” Cewar Fauziyya ta fara cin abincin tana sauri, dan yunwa dama take ji. Sai da ta gama cinyewa tas kafin ta dago kai ta kalli Mummy tana fadin. “ Ina sauraranki kawata me yake gudana?..” Gyara zama Mummy tayi tana cewa. “ Fauziyya sanin kanki ne cewa tun da Alhaji ya auro ni ban taba haihuwa ba ko?.” “ Gwaraii ni ce shaida.” “ Yawwa, kuma kinsan bada mahaifana nayi kafin har aka min aiki akan Alhaji dan duk na samu na mallake shi.” “ Uhm me ya faru to ai naga kin mallake shi din, dan aikin malamin nan baya fadi k’asa banza.” “ Eh tabbas na mallaki Alhaji sai dai ba kalan yanda nakeso ba Fauziyya, na mallake shi ne na wucen gadi kafin wancan kafurar matar tasa tayi aika-aikanta ta kwace shi.” “ Gaskiya Lubuna kinyi sake, wai har a kwace miki mijinki mtswww.” “ To Fauziyya ya zanyi ne? Ni yanzu wannan dan iskan yaron nashi nakeson kashewa ma, na saka a kashe shi wai ya bace musu.” “ Kina nufin Saif wai?.” “ Eh shi nake nufi.” “ To muje wajen bokanmun mana ai kinsan karamin aiki ne inde kashe mutum ne.” Cewar Fauziyya tana washe mata baki. Jijjiga kai tayi tana cewa. “ To bari na dauko mayafi sai muje ko.” “ Eh maza tashi kiyi sauri dan zaune bata kamaki ba.” Tayi maganar tana nuna abun ya dame ta, Mummy na shiga ciki Fauziyya ta kwashe da dariya tana bude gorar 5alive ta kifa a baki. *SAFEERA POV* Fitowa tayi daga cikin bukkan tana kallon gurin, gida ne a zagaye da wajen sai bukka guda ukun da suke wajen, ga mishiyoyi nashan iska har da bishiyar mango wanda ya zubo k’asa kuma ya nuna, gefe kuma ga na lemon. Murmushi tayi tana gyara rigar da yake jikinta wanda Inna ta bata, doguwar riga ce matso mai ratsin ja da blue, tsayin ya mata rawa sosai amma rigar cib-cib dinta, dan har saman kirjinta daya matsa yana nunawa, ta danyi haske sai dai ba sosai ba kuma fuskarta ya dan cika, hancin nan ya fito ga ido gwanin ban sha’awa, sai karamin lips 👄 nata da yake nan pink kullum. Gyale baki ne irin ma abaya a kanta, gashin kanta ya dan fito kad’an, ana kallon bakin gashin. Takowa ta fara yi zuwa gurin bishiyar mango 🥭 tana murmushi, zama tayi a kujeran da yake gurin tana tsinko guda daya, butan da yake gabanta ta dauka sai taji da ruwa, wanke mangon tayi kafin tayi bismillah ta fara sha har da wani lumshe ido dan mangon ya nuna sosai kuma zaiyi zak’i. Inna da fitowarta daga band’aki kenan hannunta rike da buta ta tsaya kallon ta, murmushi ita ma tayi tana isowa gurin da take ta zauna. Bud’e ido Safeera tayi tana kallon Inna, kunya taji hakan yasa ta sunkuyar da kai tana fadin. “ Inna yaushe kika iso?.” Murmushi Inna ta mata tana cewa. “ Ina zaki sani kuwa tunda kin lumshe ido kina jin dadin mangoro.” Dariya ta mata wanda ya bayyanar da asalin kyau dinta, hakoranta da suke farare tas suka bayyana wushiryanta ya nuna, karamin dimple dinta ya lotsa. Inna a zuciya ta furta . ‘ Tabbas Allah yayi halilta, Masha Allah.’ Muryanta taji tana cewa. “ Inna ba mangaro ake cewa ba fa, Mango ake fadi.” Ta karashe da dariya. “ Yoo ni ina nasani, dama Jannah ce mai wannan takuran dole sai ta gyaramin, ke ma gashi kinzo.” “ Inna wacece kuma Jannah?.” Numfashi ta sauke kafin ta ce. “Jannah diyata ce, sai dai kwanaki biyu baya an nemeta an rasa sakamakon abun da Bappa ya mata.” Mai do da hankalinta tayi tana fadin. “ Inna me Bappan ya mata?.” “ Safeera kenan Bappa akan kudi zai iya aikata komai, ciki kuwa har da siyar da yarsa…. More comments more typing 👌🏻🫤 *DR TEEMERH✍🏼* 10- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 Gajeran labari Na Fatima Isa Manu DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU ) *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 10* Mai do da hankalinta ta yi tana fad’in. “ Inna me Bappan ya mata?.” “ Safeera kenan Bappa akan kudi zai iya aikata komai, ciki kuwa har da siyar da y’arsa.” A razane Safeeera ta ajiye mangon da yake hannunta tana fad’in. “ Inna bangane ba sam, kina nufin na gudu ban tsira ba? Ita Jannah tana ina?.” Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tana cewa. “ Ina ga yau zai yi kusan wata bakwai ko takwas rabona da saka ta a ido.” “ Me ya faru da ita to?.” “ Dogon labari ne.” Cewar Inna. “ Koman tsayinsa zan saurara, burina kawai naji me ya faru.” Gyara zama Inna tayi tare da cewa. “ Jannah tun tana da shekara sha shida suke tare da wani saurayinta Mai suna Saifullahi….” “ Saifullahi!!!.” Safeera ta maimaita sunan. Dago kai Inna tayi ta ce.

Chapter 3 of 17