Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
“ Kin san shi ne?.” Saurin girgiza mata kai tayi ta ce. “ A’a sunan ne kawai na tuna da mai shi, amma ina jinki sai ya akayi?.” Cigaba da cewa ta yi. “ Saifullahi yana zuwa gidan nan su dade suna hira, dan sun kusa shekara uku suna tare, sai dai ko magabatansa bai tab’a turowa ba, ko a gida ma ba’a san shi ba kawai labarinsa nakeji a gurinta; ana haka sai tazo ta sameni da batun cewa zai tafi karatu idan ya dawo zai turo manyansa, na masa fatan alkhairi, bayan tafiyansa sai Bappa ya bijiro da zancen cewa zai aurar da Jannah, nan tace tana da wanda take so shi kuma yaga kudi ya ce sam sai wanda yakeso zata aura;;;; washe gari kawai muka nemi Jannah muka rasa, ashe Bappa ya riga da ya karbi kudi a hannun mutumin da zai aura masa ita mu bamu sani ba, babu inda bamu je nemanta ba amma babu ita babu labarinta har yau da nake baki labari.” Inna ta karashe a raunane dan da alama tana jin zafin abun a ranta. Numfashi Safeera ta sauke a ranta tana cewa. ‘ Nata da sauki akan nawa.’ A zahiri kuma ta ce. “ Inna kiyi hakuri Allah zai bayyana miki ita.” “ Addu’ar da muke yi kullum kenan.” Shuru ne ya biyo baya na dan wasu mintuna kafin Safeera ta ce. “ Inna shi kuma saurayin nata baizo bane tun bayan batawarta?.” “ Har yau ban sake ganinsa ba.” Mamaki abun ya bata hakan yasa ta ce. “ Kuma an tabbatar babu sa hannunsa a cikin batawarta?.” “ Hmmm Safeera kenan, ai su masu kudi lamarin su daban ne, bamu duba ba har yau.” Inna ta fada a sanyaye. Babu wanda ya sake cewa komai a cikin su, kafin daga bisani Safeera ta tashi tana cewa. “ Inna bari na shiga daga ciki.” Gyada mata kai tayi, daga haka ta shige. *BAPPA POV* Yau ba’a gida ya wuni ba, kasancewar ba sana’a yake yi ba sai zaman banza, hakan yasa ya shirya ya fito kasuwa ko Allah zai sa ya samu na bakin salati. Tafiya yake yi a kan gwaltan har zuwa post office 🏤 yana tafiya yana magana kamar zararre, photon Safeera yaga a manne a jikin wani signboard an rubuta *MISSED* da babban baki, cak ya tsaya yana kallon hoton me kyau, shuru yayi har zai wuce sai ya dawo ya ga wani mutum kamar dan sanda tsaye da bakin kaya, a dan tsorace ya ce. “ Ina wuni Yallabai.” Yayi maganar yana dan durkusa masa. Kallon sa mutumin yayi yana cewa. “ Lafiya Baba ka tashi lafiya?.” Tashi tsaye yayi, kafin ya ce. “ Dan Allah yarona me wannan hoton yayi aka manna?.” Ya nuna hoton Safeera. Kallon hoton mutumin yayi kafin ya dubi Bappa yana cewa. “ Baba batawa tayi ana nemanta, kuma duk wanda ya same ta za’a bashi naira million daya tare da mota BMW sannan a kaisa hajji.” Sakin baki Bappa yayi, cikin k’ok’arin hado magana ya ce. “ Million daya akan wannan kuma da zuwa hajji.” “ Eh Baba In Sha Allah haka abun yake.” Wani dariyan hauka Bappa ya tafka yana cewa. “ Ashe harzikina yazo, chaiiiiiiiiii ai ko kashe mutum tayi ta gudu to Wallahi sai na nuna ta.” Kafin ya dubi mutumin yana cewa. “ Yawwa yarona waye zai bada kudin tukun?.” Murmushi kawai mutumin ya masa dan ya dauka Bappa bashi da hankali, hakan yasa ya ce. “ Ka san inda take ne? Idan ka sani yanzu zan hada motoci muje mu dauko ta sai a baka kudin ka.” Tsalle ya buga yana tafa cinyarsa ya ce. “ Alku’an muje, idan baku ganta ba ku kashe ni, bura uba ni da yarinya tana gidana tsawon wata biyu yanzu, muje na nuna maka ita.” Cikin serious mutumin ya ce. “ Wani unguwa?.” “ A bulunkutu ne.” Waya mutumin ya ciro yana danna wani number, bugu daya aka dauka, ta cikin wayan mutumin ya ce. “ Jon any news?.” Cikin harshen turanci ya ce. “ Eh wani yazo wai ya santa tana bulunkutu, wai a gidansa take tun bayan wata biyu.” “ Good job, kuna ina gamu zuwa yanzu.” “ Post office 🏤.” “ Ok gamu nan zuwa. “ Aka kashe wayan. Kallon sa Bappa yayi yana cewa. “ Kazo muje mana kuyi sauri ku bani kudin.” “ Come down.” “ Ashirrr dinka ni zaka zaga.” Cewan Bappa a fusace. Murmushi Jon ya masa yana cewa. “ Ba zagin ka nayi ba.” “ Yooo ai na dauka zagi na kayi.” “ A’a ni na isa na zagi mai Million daya.” Ya fada dana dariya. Wani baza riga Bappa yayi yana hura hanci, ya ce. “ To muje.” “ A’a muna jiran motoci ne su iso sai muje.” “ Ahh ahh tammm tammm ba matsala ai.” Sun kai kusan mintuna goma a gurin suna tsaye jiran motoci, duk bayan minti daya Bappa yana cewa muje, tun Jon yana kulasa har ya mantar da shi. Motoci ne suka tsaya a gaban su guda uku, duk bak’ake yasha tinted glasses, na tsakiyan ne aka bud’e aka fito, Sageer ne shi ma sanye da bak’aken kaya. Kallon su Bappa yayi yana cewa. “ Muje da wuri mana ni ku bani kudina, zaku rusa min shiri ne fa, inaso na k’ara aure ne dama.” Sageer ya ce. “ Sannu Baba.” “ Yawwa sannu yaro.” “ Kaga kar kasa muje a banza bamu same ta ba.” Bud’e baki yayi yana kallonsa kafin ya ce. “ Idan baku ganta ba ku kashe ni Wallahi, ko ku kaina gidan gyaran hali.” Jijjiga kai Sageer yayi yana cewa. “ Muje to.” Kafin ya kallo Jon ya jinjina masa hannu alaman yabo. Bude masa wajen me zaman banza Sageer yayi ya shiga kafin suka tada motan suka nufi hanyar unguwar Bulunkutu. Mintuna talatin da uku suka dauka kafin suka iso unguwa, dai-dai line da zai sadaka da gidan suka yi parking, Sageer da Bappa da Jon suka fito, sai mota na gaba security ne guda biyu haka ma na baya, kallon su Sageer yayi yana cewa. “ Ku ku tsaya a nan kar ku bar kowa ya shigo.” Ya nuna security guda uku, kafin ya kalli Jon da dayan security din ya ce. “ Ku muje.” Dan tuni Bappa yayi gaba. Yana shiga cikin filin gidan ya d’aga murya ya fara cewa. “ Innar Jannah ki fito da wannan yarinyar anzo daukarta.” Jin haka yasa su Sageer isowa da wuri, Inna da take daki ta fito ba shirin dan tasan halin mijin nata kila an masa tayin kudi ne shine yazo zai siyar da ita. Cak Inna ta tsaya tana kallon su, a dan tsorace ta kalli Bappa tana fadin. “ Kai kuma Malam yau da wannan masifar muka tashi.” “ Ke kimin shuru dalla, ki fito da yarinyar.” Jiki a sanyaye Inna ta shiga dakin da Safeera take dan fito da ita, kusan minti daya ta fito a burkice ta ce. “ Malam ban ganta ba fa.” Dai-dai lokacin da Safeera ta fito daga band’aki hannunta rike da buta, taji ana hayaniya ne shiyasa ma ta fito amma bata gama uzurinta ba. Ajiye butan tayi tana cewa. “ Inna gani na shiga bangida ne dama, naji surutu me ya far……” Maganar ne ya katsai lokacin da ta hada ido da Sageer wanda jin muryanta yasa ya juyo. *Ni da ku wai waye yake yi wa wani rashin adalci😹 ku bakwa comment yanda ya kamata ni kuma bana typing sosai😹 aje a haka ko zaku canja? Idan kun canja naga comments da ruwan likes anjima ma da dare zan sakar muku update.* *DR TEEMERH✍🏼* 11- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 Gajeran labari Na Fatima Isa Manu DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU ) *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 11* Ajiye butan tayi tana cewa. “ Inna gani na shiga bangida ne dama, naji surutu me ya far……” Maganar ne ya katsai lokacin da ta hada ido da Sageer wanda jin muryanta yasa ya juyo. Hannu take nunasa da shi cikin k’ok’arin hada kalmomi ta furta. “ Me… zaku… min?.” A hankali Sageer ya fara tako inda take cikin hikima yana fadin. “ Ki ga babu abunda zamu miki, ki taimakawa rayuwan bawan Allah kizo mu koma, Sir yana dab da rasa ransa akan ki, dan Allah kizo muje.” Baya ita ma ta fara yi tana cewa. “ Babu inda zanje, sai me idan ya mutu din, ai dama ya cancanci mutuwa, irin mutuwar da ba imani wanda tifa zai taka shi.” Bappa yayi saurin cewa. “ Kin ga Safeera kike da suna ko Sufi, kizo ki bisu dan a samu a sallame ni, dan gidan nan babu wajen zamanki kuma.” Jon ya dakatar da shi ta hanyar nunasa da hannu yana cewa. “ Baba ka kama bakinka, ita din Beb din uban gidanmu ne kabi a hankali.” Tsit Bappa yayi yana zuru zuru da ido, dan yanda Jon ya masa magana kai zaka gane gargadi ya masa, Inna hawaye ta fara dan Safeera tausayi take bata. Cigaba da magana Safeera tayi tana cewa. “ Kaje ka fada masa cewa har abada bazan zo ba, kuma zan zauna zaman jiran labarin mutuwarsa.” Hadiye yawu yayi kafin ya ce. “ Sorry dan Allah amma ko sau daya ne kizo muje ki gan shi.” “ Bazan je ba.” “ Alkur’an sai kinje, ni zaki tonawa asiri? na miki rana shine kike so kimin dare, ashe baki da mutunci?.” Bappa ya fada kamar zai haukace dan bakin ciki. Kallon shi Safeera tayi ta kalli Inna, gyada mata kai Inna tayi tana lumshe ido, jinjina kai Safeera tayi dan ta gane maganar, kafin ta kalli Sageer ta ce. “ Shikenan muje na gan shi sai na dawo.” Da sauri Sageer ya ce. “ Yawwa Thank you Maa.” Hararan shi tayi, kana ta nufi d’akin da take zama, minti kadan ta fito sanye da hijab blue wanda Inna ta bata, sosai ya mata kyau dan ya karbi fatarta. Kallon Inna tayi lokaci guda hawaye ya zubo mata, da sauri ta rungume ta tana kuka, sakin baki Bappa yayi, a hassale ya ce. “ Wannan munafurcin fa har ina? Yaushe kuka saba ban sani ba, idan ma wani siddabaru kike kulla mata to ashirr dinki, dan kudi kam kamar na samu.” Sakin juna suka yi Safeera tayi gaba su Sageer na mara mata baya, da sauri Jon ya bud’e mata back site, gudu Bappa yasa yazo ya shige motar yana fadin. “ Haka kawai na taimaka muku ku gudu kuma, ai baku isa ba chabbb sai kun biya ni kudina ni da hakkina.” Babu wanda ya kulasa har ya gama surutun shi, hawaye Safeera take yi tana kallon Inna wacce itama hawayen take. Shiga motar tayi Jon ya rufe, su ma suka shiga aka fice daga unguwan da gudu kamar zasu fure. *SAIFULLAHI POV* Tun bayan da Ammar ya masa fada akan tunani tunanin da yake yi kullum, bai kuma sake zama yayi dogon tunani ba sai dai abun da ba’a rasa ba. Haka kuma tun da Ummah ta kawo masa abinci yaci yaji kawai yana son sake cin wani girkin ta. Yau Monday yasan yana da shari’a karfe goma akan wani fyaden da akayi wa yarinya yar shekara goma, hakan yasa ya shirya cikin kayan lawyer, wanda ya masa kyau sosai kamar ka sace shi, gemunsa wanda rabon shi da yayi kyau haka tun bayan tafiyar Safeera, shafawa yayi yana murmushi wanda ya rasa gane na menene. Jakansa ya rike a hannu da hulansa da rigar daurawa akai irin nasu barrister, murmushi yayi yana rike wayoyinsa ya fita daga bangaren. Kallon apartment din yayi kafin yaji yana nufan na Ummah. A bakin kofar ya tsaya yana kallon kofar kamar zai shiga kamar bazai shiga ba, hannu yasa ya tura yana saka k’afarsa na dama tare da yin sallama ciki-ciki. Kamshin turaren wuta ne ya masa sannu da zuwa, lumshe ido yayi dan rabon da yaji wannan kamshin tun yana shekara ashirin da uku. Takowa yayi zuwa tsakiyan falon yana kallon hanyar kitchen dan jin motsi. Ummah ce ta fito da food flask a hannunta zata kai dining table, hada ido suka yi, da sauri ta ajiye flask din a dining ta dawo inda yake tsaye ta zuba masa ido. Sanyayyen murmushin nan nasa da ta dade bata gani ba yayi, bata k’ara burkicewa ba sai da taji ya ce. “ Ina kwana?.” Da sauri ta kalli fuskarsa ta ce. “ Lafiya Saif.” Kallom inda ta ajiye flask din yayi yana fadin. “ Akwai abincin ne?.” Da sauri ta ce. “ Eh kazo na zuba maka.” Dan bata fuska yayi yana cewa. “ No bazan ci a nan ba ki zoba min zan tafi dashi.” Jinjina kai tayi jiki na bari ta nufi kitchen, basket 🧺 ta dauko medium ta dauko madai-daicin food flask da tea flask ta fito lokacin ya zauna a kan kujera. Tana kallonsa tana murmushi tare da addu’a a ranta Allah yasa danta ya dawo gare ta, potato da kwai ta soya ta zuba masa, ruwan shayi ta zuba a tea flask din, milo da madara na sachet ta yanka tana saka masa guda bibbiyu, kana ta zuge zib din basket din tana daukowa. Tashi yayi ya saka hannu zai karba, girgiza masa kai tayi ta ce. “ Zan kai maka har mota, yau kadai kazo gurina cin abinci bayan shekaru da dama.” Bai ce komai ba ya nufi hanyar fita, mara masa baya tayi da basket din har zuwa compound din gidan, hango shi tayi tsaye masifa. Karasowa tayi zuwa inda take tana jin yana cewa. “ Idan shi Sageer zai fita shi daya to me yasa zai dibi sauran security’s din? Ni waye zai kai ni yanzu?.” Ya fada a fusace yana danna waya da alama kira yake yi. Hannu Ummah tasa ta karbi wayan nasa, da sauri ya d’ago kai dan ganin wani isheshen ne, lokacin da yaga ita ce sai ya kawar da kai yana cewa. “ Zan yi kira ne.” “ Zaka yi late, ka bari baka san wani uzuri ne ya fitar dashi ba, akwai sauran security’s din Dad dinka sai su kai ka.” Ummah ta fada a cikin kwantar da murya. Shuru yayi kafin ya jinjina kai, inda security’s din Dad suke ya kalla yana daga musu hannu, nan da nan suka iso gurin shi. Ummah ce fada musu cewa zasu kai Saif, nan suka kawo mota guda uku, bude masa suka yi yana shiga, Ummah ta ajiye masa basket tana fadin. “ Ga wayanka.” Karba yayi, ta kuma cewa. “ Allah ya tsare ya baka lada sannan Allah ya baka sa’a a duk shari’an da zaka gudanar, Allah ya kau da hau.” Lumshe ido yayi yana dago kai ya kalle ta ya furta. “ Ameen.” Da haka suka fice daga gidan, kafin Ummah ta nufi dakin ta. Koman da ya faru akan idanun Mom ne, har sai da ya fita daga gidan kafin ta sauke labulen tana furta. “ Akwai bala’i, kut wai matar nan da wani boka ta dogara ne, hmm 🤔 dole na koma gurin Malamin nan a sake min aiki a kan shi.” Da haka ta koma dakinta. *STATE HIGH COURT OF JUSTICES ( SHCJ )* Yana zuwa ya wuce office nasa yaci abinci, yana ci yana yabawa a kan yayi dadi. Tun bayan da ya gudanar da shari’a na karfe 10, bashi ya samu kan shi ba sai guraren karfe sha biyu da wasu mintuna. Suna zaune shi da Ammar a office suna hira, wayansa ne yaji ya fara ringing, dubawa yayi ganin Sageer ne yasa ya dauka rai a bace ya fara cewa. “ Wai Sageer ina ka shiga ne tun da safe? Bayan kuma kasan babu wanda zai kaini gurin aiki.” Ta cikin wayan Sageer ya ce. “ Sorry Sir.” Numfashi ya sauke ya ce. “ Me ya faru?.” Sageer ya ce. “ Sir kana gurin aikin ne ko zaka koma gida ko gidanka.” “ Lafiya kake tambaya na?.” Cewar Saif da mamaki. Sageer ya kuma cewa. “ Sir na samo maka Safee…” Bai karasa ba Saif ya mike a haukace yana cewa. “ Safeera ta ka samo min? A ina kuke yanzu? Tana lafiya ko babu abun da ya same ta ko? Taci abinci? Ka fadamin inda suke gani nan zuwa yanzu yanzu.. *A cigaba da sambadomin comments da like’s ni kuma zan cigaba da suburbudo muku typing 😂🤸‍♀️* *_TAKU HAR KULLUM DR TEEMERH✍🏼_* 12- 💔 *BAƘAR ƘAUNA*💔 _Gajeran labari_ *Na* *Fatima Isa Manu* _DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_ *JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION💪💪* Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T *DIAMOND 💎 STAR ⭐* *LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️* *(We stand together)* 🤝🤝🤝 *Page 12* Bai ƙarasa ba Saif ya miƙe a haukace yana cewa. “ Safeerata ka samo min? A ina kuke yanzu? Tana lafiya babu abun da ya same ta ko? Taci abinci? Ka faɗamin inda kuke gani nan zuwa yanzu yanzu.” Ta cikin wayan Sageer ya ce. “ Sir muna gidanka na GRA.” “ Ok.” Kawai ya ce yana ɗaukar key ɗin mota zai fita, tare hanya Ammar ya yi yana masa kallon mahaukaci, a fusace ya ce. “ Malam ka bani guri na wuce dalla.” “ Baka cikin hankalinka Saif, saboda haka bazan bari kayi driving ba sai dai muje tare.” Cilla masa key na motan ya yi, ya karɓa suka fito haraban kotun wanda yake nan cike da mutane, ta baya suka bi dan gudun idon mutane, inda motar Ammar yake fake suka nufa, ya bud’e da sauri Saif ya shiga gurin mai zaman banza, Ammar kuma ya shiga gurin driver. Da ƙarfi ya fuzgi motar suna barin gurin, gudu Ammar yake tsalawa a tsakiyar titin kamar ba gobe, direct titin da zai sada ka da GRA suka nufa, har suka iso bakin get na gidan babu wanda yayi wa wani magana. Horn Ammar ya danna, mai gadi ya wangale get da wuri suka shiga. Ko parking dai-dai Ammar bai yi ba Saif ya fice da sauri har yana k’ok’arin fadi. Dake Sageer yasa pin din ƙofan falon hakan yasa ya bud’e musu shi da Safeera da Bappa suka shiga, sauran kuma suka tsaya a bakin ƙofar. Kallon su Saif ya yi, kafin ya saka hannu a jikin kofar, sai da yayi scanning kafin ya rubuta Welcome kana ya bud’e. A haukace ya shigo falon yana tsayawa cak lokacin da idanunsa ya sauk’a cikin nata, k’asa ɗaukewa yayi haka itama, a slow motion ya iso inda take, kafin ta ankara ya rungume ta da ƙarfi yana sauke ajiyar zuciya, wani sanyi mai ratsa jiki ya mamaye shi. Sun fi minti biyar a haka, Bappa ya sake baki yana kallon su haka ma Sageer, Ammar guri ya samu ya zauna ya daura k’afa daya kan daya shi ma ya zuba musu ido. A hankali ta fara gane me yake faruwa, tunawa da ajikin wanda take tayi hakan yasa ta fara mutsu mutsun kwace kanta, sake manne ta yayi tsam a kirjinsa yana cigaba da sauke ajiyar zuciya. “ Ka sake ni nikam ka matse ni sosai.” Girgiza kai yayi yana dan sausauta rikon dan shima yasan ya matse ta sosai. “ Ni ka kyale ni dalla.” Ta fada a fusace tana ture shi daga jikinta wanda ko motsi bai yi ba balle tayi tunanin zai turu. Jin d’igon ruwa a wuyanta yasa tayi mamaki, Ammar ne ya taso yazo ya banbare shi daga jikinta da kyar, hannu tasa ta juyanta tana lafuto d’igon ruwan, kallo take kafin da sauri ta kalli fuskarsa wanda hawaye suka wanke. Ammar da mamaki ya ce. “Saif kuka!!!.” Sageer yayi sauri ya fita daga falon dan kukan uban gidan nasa tamkar karaya ne a gare shi, Bappa kuma ya samu guri ya zauna a kan carpet yana tuna a ina yasan me wannan fuskar. Zubar da gwiwowinsa yayi a gabanta yana hade hannaye biyu yayin da idanunsa ke zubar da kwalla, Ammar da mamaki ya kamasa ya saki baki yana kallon ikon Allah. Magana ya fara yi cikin muryan kuka. “ Na roke ki, dan Allah dan girman Allah kiyi hakuri.” Shuru Safeera tayi tana kallon abun da yake yi tana mamaki, bata yarda ya zauce ba sai da taji yana cewa. “ Ki taimaki rayuwata kizo ki zauna da ni, Safeera kiyi hakuri da duk abubbuwan da na miki nasan ni butulu ne, ni kaina na sani, amma ki taimaka min ki yafe min.” Ya karashe yana kama kafarta. Ammar kamar yayi kuka ya ce. “ Saif ko dai ka zare ne? Kuka kake yiwa mace? mace fa!!!.” Bai kula shi ba, ya cigaba da fadin. “ Dan Allah ki yarda ki aure ni.” Ya fad’a yana damke kafafuwanta. “ Ni?.” Ta tambaya da mamaki tare da al-ajabi. Ammar ya ce. “ Uhm 😶.” Yana harde hannayensa a kirji. “ Ni karuwar ce kakeso da aure? Ko ka manta da maganganun da ka fadamin? Cewa kayi wai cutar da kai nazo yi, sannan kace ni ba mutumiyar arziki ba ce, har da cemin anyi asarar haihuwata, sannan ka ce ko iyayena basu bani tarbiya bane, a cewarka ai yaran talakawa ba’a musu halalci sai sun mayar maka da sharri.” Mikewa tsaye yayi yana fadin. “ Eh eh nasan na fadi haka amma ai…” “ Amma me Saif? Korana kayi daga gidanka kana fadin ga hanya daga nan har lahira, ko shima ka manta?.” “ A’a duk a cikin rashin hankalina nayi, kar sanadiyarki na mutu.” Ya fada a wani irin yanayi da bazai misaltu ba. Gyara tsayuwa tayi tana jinjina kai take cewa. “ Me yasa maza baku da kunya ne? Kai ba kaji kunyar idanuna ba kake cewa zaka iya mutu dan ni? Hmmm to albishirin ka ko da kai ne autan maza to na hakura gwara na mutu ba aure dana zauna da kai a matsayin miji.” Da kyar ya isa jawo numfashin nasa yana fadin. “ Safeera kar ki min haka.” A hassale Ammar ya kalle ta ya cewa. “ Ke wai ana rokon ki kina rainawa mutane hankali, har yau Saif ne zai durkusa a gaban mace yana bata hakuri kuma taki, ke wacece da bazaki iya yin yafiya ba, idan ta arziki bai sa kin aure shi ta tsiya zai saka kije kayan ki.” Kama Ammar yayi yana girgiza kai kamar yaro yana kallon ta yana fadin. “ A’a babu inda zata je, Ammar ni na cuceta koma me tayi zan dauka, amma kar tayi nisa dani.” “ Kai dalla ka barta ai ba ita ce farau ba, aikin banza da wofi ka dubi yanda ka koma akan wannan yarinyar.” Kallon Ammar take wanda yake zuba mata banzan kallo me dauke da harara, a ranta ta ce. ‘ wato shi adawa ma yake da ni, kenan so yake na tafi lallai hmm to babu inda zanje kuwa da kai da shi din duk sai na rama abun da kuka min, dan kuna ganina karama yar shekara sha takwas shi yasa kukemin wulakanci ai.’ Murkud’a masa baki tayi tana hararan Saif, kafin ta ce. “ Shikenan zan zauna da kai, yaushe zaka aure ni din?.” A bazata maganar ya diro masa, bashi kadai ba har Ammar, Bappa da yake zaune ya mik’e tsaye ba shiri, kamar zai haukace ya ce. “ Arziki har gida, ashe da rabon zanyi kudi, Masha Allah, yawwa idan bata da iyaye ni zan tsaya mata a matsayin uba.” Kallo daya ta yiwa Bappa tana dauke kai, a zuciya ta furta. ‘ Iyayena ma sun fika hankali ai, duk da jirgi daya ya dibo su amma su akwai dan hankali a tattare da su.’ Maganar Saif ne ya dawo da ita jin yana cewa. “ Yanzu muje a daura auren.” Ya kama hannunta zai tafi, jin bata motsa bane yasa ya juyo yana ganin ta. “ Sakar min hannu malam, ba makauniya bace ni da zaka min jagora.” Ta fada a kausashe. Sakin hannun yayi yana kallon ta, kamar mai koyan magana ya ce. “ Me kuma ya faru?.” Ammar da lamarin ya isheshi ne ya ce. “ Ka komar da kanka kamar yaro akan yarinyar nan Wallahi, Mtsw.” Saif bai kula shi ba sai ma cigaba da tambayan Safeeran da yayi, bata kuma cewa komai ba ta nufi hanyar fita, da sauri ya biyo bayanta yana cewa. “ Ina zaki je.” Bappa ma ya mara musu baya yana fadin. “

Chapter 4 of 17