masa wani dan illa kadan a zuciya.”
“ Nagodeeee!.” Cewan Falmata tana sakin dariya.
Ita dai Safeera da ido ta bisu.
Wunin ranar haka suka yi shi duk yunwa, idan da sabo sun saba, Abba ma yana kwance a daki ya rasa ina zaije ya samu aiki, suna haka har aka kira sallan mangarib, koran Umar suka yi zuwa masallaci suka saka yaran a gaba suka yi salla.
Duban agogon dake manne a jikin bango Safeera tayi ta ce. “ Yau Mama har karfe Takwas bata dawo ba.”
“ Ai ba sabon abu bane Safeera, ko kin manta kowa zaman kansa yake a gidan nan?.” Cewan Rauda.
Wutan Nepa aka kawo, tashi suka yi suka yiwa Nabila, Ammi da Amma shimfidi, kwanciya Safeera tayi tana kallon yanda suka saka riga da wando kamar masu zuwa tsalle, kafin ta ce. “ Ina zaku je ne?.”
“ Ki zuba ido kawai ki gani, kafin mu dawo idan Kausar tazo kar ki bari ta kwanta kusa da su Nabila kar ta shafa musu wani cutan, sannan duk bura uban da zakiji ana yi kija bakinki kiyi shuru.” Cewan Falmata.
“ Hmm!! Zaku nemo wata masifar kenan, sai kun dawo to.” Ta karashe tana jan bargo ta rufe jikinta.
Fita Rauda da Falmata suka yi suna ja musu kofar dakin.
Har sai da suka jira Alai Bana ya kulle shago ya tafi gida, mutane sun watse a wajen ya zama shuru baka jin komai.
Nufan shagon suka yi Falmata na daukar dutsi ta buga a jikin kwadon, nan ya bud’e da sauri suka shiga cikin shagon suna dan jan kofar ta yanda baza’a gane da mutane ba.
Duk abunda suka samu kawai diba suke, sun masa ta’adi sosai da sosai, shikafa kwano biyar suka diba haka ma wake, madara da milo ba’a magana sun kwasa na kwasa.
Bayan sun gama tattare komai ne suka tsaya kallon kayan, Rauda na fadin. “ Yanzu taya zamu fara divar kayan nan?.”
“ Ai mun gama mai wahalan, ki zage ki diba kawai mu tafi kafin a kama mu.”
Kwalin fridge dake ajiye suka gani, daukowa Falmata tayi suka fara zuba kayan a ciki, har zasu tafi suka ga mayonnaise da sauri Raudah ta dauka ta saka kafin suka ja kwalin da kyar suka fita a shagon.
Da kyar suke ja har zuwa kofar gida, tura kofar Raudah tayi taji a bud’e, kafin suka daga kwalin da kyar zuwa ciki dai-dai lokacin da Abba ya fito yin mitsari.
Had’a ido suka yi ya kalle su ya kalli kwalin. “ Wannan fa a ina kuka samu?.”
Babu wanda ya kula shi suka ja zuwa d’akin su, da ido ya bisu kafin ya wuce band’aki dan a matse yake.
Bayan sun kai daki ne Falmata ta ce. “ Raudah ya zamuyi? Abba fa ya gani.”
“ Sai me idan ya gani din? Ai naga shi baya bamu abinci sannan baya kula damu a bangaren karatun mu? Mama ne kawai ke k’ok’ari ita ma yanzu ta fara gajiyawa, idan bamu taimaki k’annen mu ba waye zaizo ya taimake su?.”
Jinjina kai Falmata tayi kafin suka kai sa can lungu suka zuba kaya a kai ta yanda bazaka taba ganewa ba, jan kofar dakin suka yi suka danna kwado, get ma suka saka mata kwado kafin suka nufi dakin Mama.
Hada ido suka yi da Safeera wacce ta tashi ta zauna tana jiran dawowar su.
“ Sai yanzu kuka dawo har karfe daya ta rufa?.”
“ To ke waya hanaki bacci?.” Falmata ta tambaya yayin da take kwanciya kusa da Safeeran.
“ Na tsaya jiran dawowar ku ne.”
Tabe baki Raudah tayi ita ma ta samu guri ta kwanta.
“ Kausar bata dawo ba ko?.”
“ Hmmm!!!! Kuma kun sani ai bazata dawo ba, sai ranar da Allah ya tunatar da ita gida kuma.” Safeera ta fada tana jan bargo ta kwanta.
Can Raudah ta ce. “ Mama fa?.”
Murmushin takaici Falmata tayi ta ce. “ Ita ma tabi duniya.”
“ Ku ringa yiwa mutum kyakkyawar zato fa! Baku san inda taje ba har kun furta yawon duniya.” Safeera ta fada.
Shuru duk suka yi kafib bacci ya dauke su.
~~~~~~~~WASHE GARI
Mutane ne cike a kofar shagon kowa na masa sannu, dan ba karamin asara yayi ba, Alai Bana ya koma tamkar mahaukaci yayi zaman yan bori a k’asa yana riskar kuka yana fadin. “ An cuce ni, an tozarta ni, Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu! Allah ya isa.”
Duk hakuri suke bashi, Abba yana tsaye ya hade hannu a kirji yana kallon kowa, kafin ya juya ya koma gida.
Yana shiga ya wuce dakin Mama, dan ba kowa a filin gidan da alama har sun gama aikin su sun koma ciki duba da yanda gidan yake a kimtse babu kayan datti ko wanke-wanke, ga gurin murhu a jike da alamu an daura tukunya.
A tsakiyar dakin Abba ya tsaya yana kallon yanda kowa ya baje yana shan tea da bread 🍞 idan ka cire Safeera wacce ta zuba musu ido.
Gaishe da shi suka yi yaki amsawa yana cewa. “ Yanzu abun da kuka yi kun kyauta? Ke Falmata kece babba yanzu dan wancan ta fita zakka amma dake ake had’a baki a bata gari?.”
“ Abba yunwa kakeson ya kashe mu? Kai baka bamu to a ina zamu samu? Ko so kake mu fita yawon karuwanci.”
“ Falmata ya isa!!!!!.” Safeera ta dakatar da ita, ta cigaba da cewa. “ Uba fa uba ne, ba’a canja wani uban, kina d’aga masa murya kamar bashi ya haife ki ba, kinsan zunubin da ake rubuta miki kuwa.”
“ Ina zata sani? Ai doluwa ce, an tura ta Makarantar islamiya taje tana soyayya da malamin.” Abba ya fada ransa a bace ya juya ya fice.
Tabe baki tayi kafin kowa ya cigaba da cin abincin shi.
Washe gari Mama ta dawo gida, babu wanda ya kula ta idan ka cire Nabila wacce tayi sauri ta rungume ta.
Haka rayuwan gidan ya cigaba da tafiya, yau a kwashi bakin ciki gobe kuma akasin hakan, Alai Bana kullum yana cikin durawa wanda ya masa barna a shar, Mama da taga kayan abincin bata tambaya ba.
Sai da aka shafe watanni uku kafin wata ranar Lahadi Kausar ta dawo gida.
Falmata ta bud’e kofa tana fadin waye?
“ Yar gidan ce.” Kausar ta fada da muryanta na mazan.
Kusan duka yaran sai da suka fito dan ganewa idanun su, bankado kofar tayi ta shigo tana hararan su. “ To uban me kuke kallo? Ni ce dai ban canja ba.” Ta nufi dakinsu.
Bin ta da ido suka yi suna mamaki kafin Mama dake zaune a bakin kofar dakinta ta ce. “ Ashe zata dawo.”
Shuru Safeera tayi dan abun da ta gani ya hargitsa mata lissafi sosai, sai dai abun da bata sani ba, ba ita kadai ta gani ba har Falmata da Mama sun lura.
09027308227
*SAHIBA✍🏼*
*SAURA PAGE GOMA NA KAMMALA BOOK ONE, GA MAI BUKATAR SON KARANTA BOOK TWO ZAI IYA TURO KUDINSA NAIRA DARI ₦400 DAN AYI ADDING NASA A GROUP, ZAKU TURO KUDIN KU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 9031176727 FATIMA ISA OPAY. SAI A TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 09027308227 ALLAH YA BAWA KOWA IKON BIYA.*
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
_Gajeran labari_
*Na*
*Fatima Isa Manu*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 20*
Shuru Safeera tayi dan abun da ta gani ya hargitsa mata lissafi sosai, sai dai abun da bata sani ba, ba ita kadai ta gani ba har Falmata da Mama sun lura.
Kallon kallo suka tsaya yi kafin Raudah tayi saurin cewa. “Lallai karuwanci yayi riba, chabbb!.”
Falmata ta tashi ta nufi dakin da Kausar ta shiga tana fadin. “ Kausar!!.”
Juyowa tayi tana k’ok’arin cire bra din da yaci ubansa da datti ta ce. “ Me ya faru yar iyayi.”
Falmata ta bud’e baki zata yi magana Mama da Safeera suka shigo, Mama ta ce. “ Kausar kamar ciki ne da ke?.”
Dariyar rainin hankali ta musu tana daga muryanta irin na gardawa ta ce. “ Sai akayi uban me idan cikin ne da ni? Ai dai a jikina yake ko.”
Safeera na fadin. “ Waya miki ciki Kausar?.”
“ Bansani ba shegiya!.”
Har zata kuma magana Mama ta daga mata hannu, hakan yasa suka yi shuru, kafin kowa ya fita a dakin aka barta ita kadai.
Raudah ta dubi Falmata dake zaune tayi tagumi ta ce. “ Yanzu kuna ganin zamu samu mijin aure idan har aka san yanda gidan nan yake?.”
“ Raudah kenan!!… ke ta maganar aure ma kike, ki dubi yaran nan sune abun tausayi bamu ba.” Cewan Falmata.
“ Allah ya kyauta, amma mukam ba muyi sa’an iyaye ba sam.” Raudah ta fada tana goge hawayen da ya zubo mata.
Safeera ta tashi tana murmushin da bai kai zuci ba ta ce. “ Kar ku ga laifinta, ku duba laifin iyayenmu, sune suke da alhakin duk abunda ya faru.”
Muryan Baba suka ji daga bayan su yana cewa. “ Kowa yayi na gari dan kansa.” Ya juya ya fita.
Da ido suka bishi kafin kowa ya tashi yaje yayi abunda zai yi.
~BAYAN WATA BIYAR~
Rayuwar gidan ya sake burkicewa, dan yanzu cikin Kausar yana wata tara da sati biyu ana tunanin haihuwa yau ko gobe, yayin da Mama da Baba kullum cikin fada suke.
Safeera ce ta bude kofa ta shigo, tayi baki ta sake ramewa, tana tafiya kamar zata fadi dan yunwa.
Nabila na ganinta ta tasho da gudu tana cewa. “ Anuty Safeera kun samo min abinci.”
“ Nabila naje bara amma bansamu ba, naje neman aiki kuma ba’a daukeni ba.” Ta karashe a raunace.
“ Shikenan Anuty.” Nabila ta fada kamar tayi kuka ta koma ta zauna tana tagumi.
Gurin da su Raudah suke zaune ta isa tana cewa. “ Ina Kausar?.”
Tabe baki Falmata tayi ta ce. “ Tun safe ta fita gashi yanzu har karfe biyar bata dawo ba.”
Safera ta ce. “ Allah yasa tana lafiya.”
“ Ba Amen ba.” Cewan Raudah ko a jikinta.
Dakin Mama ta shiga ta sameta tana danne danne a waya, a gefenta ta zauna tana cewa. “ Mama yaran nan yunwa suke ji fa.”
Kamar jira take tayi magana ta fara masifa. “ Safeera ubana zan yanka musu su ci? Ku kyale ni fa, kar ku dameni ga can uban naku ya gagara tabuka komai, ni zaku zo ku addaba.”
Hawaye ne suka gangaro ta dubi Mahaifiyar tasu ta ce. “ Mama amma…..”
Shuru tayi sakamakon wayan da Mama ta d’aga, ba’a jin me ake fada a wayan, amma yanayin Mama yasa ta gane ba lafiya.
“ Mama me ya faru?.”
“ Kausar ce take asibiti ta haihu.”
Maganar ya sauka a kullen su, da sauri suka mike tsaye Raudah na fadin. “ Yarinyar nan dai ta rantse sai ta haiho mana iftila’i, Allah yasa yaron ko yarinyar ta mutu.”
Falmata ta amsa da. “ Amen Ya rabbi.”
Babu wanda yabi ta kansu Mama ta dauki hijab nata ita da Safeera suka tafi.
~3 hours later~
Kausar ce ke zaune ta rike yarinyar a hannu, gefe guda kuma su Falmata ne da Raudah da Safeera sun zubawa sarautar Allah ido, gefe kuma Mama ne tana cewa Ammi da Amma. “ Ku hada ruwan zafin a yiwa yarinyar wanka mana.”
Ammi da Amma suka tashi suke je hura wuta, Nabila ta matso kusa da Kausar tana kallon yarinyar hannun nata ta ce. “ Yarinyar nan bata kama da ke Yaya Kausar.”
Karaf Falmata ta ce. “ Wallahi da wannan arnen take kama wanda suka yi fada muka raba su dinnan, baku lura da hancin nasu iri daya ba.”
Raudah ta daura da cewa. “ Ai kowa yayi nagari dan kansa.”
Tashi Safeera tayi ta nufi dakin Mama ta kwanta, tunanin rayuwarta duk ya isheta, da haka har bacci ya dauke ta.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau dadi gobe akasin hakan, ranar suna yarinya taci sunan Mamar Mama, wato Hajara suna kiranta da Anaya.
Kausar zata goyi Anaya a baya ta saci hanya ta tafi barikinta, tun su Falmata na tausayin yarinyar kar ta kamu da cuta har suka hakura, idan Mama ta fita bata dawowa sai dare, Nabila tayi kukan yunwa har ta hakura dan yanzu ya zama jikinsu.
Wata ranar lahadi Baba ya tashi da matsanaciyar ciwon ciki mai zafi, Mama ta kaisa asibiti, inda likitoci duka tabbatar da poison yaci kuma ya taba masa hanji, hakan yasa aka sallamo su zuwa gida.
Safeera ta shimfida masa taburma, Mama da Falmata suka kama shi ya zauna ya jinginu da bishiya, ya kalle su da murmushi akan fuskarsu ya ce. “ Zan warke karku damu.”
Safeera ta kama hannunsa tana shafa masa man zafi, Mama ta dubi Falmata ta ce. “ Kizo ki rike shi bari na dama masa kunu.” Falmata ta tashi tazo ta rike Baba, Mama taje ta hada masa kunu, ta dawo ta fara bashi.
Sai ta zuba masa a baki sai ya zubar, kwallan tausayin shi ya zubo mata ta ce. “ Ka daure kasha.” Yayi murmushi ya saka hannu a aljuhu ya ciro kudin da suke ciki ya mika mata, idanunsa suna kafewa, hakoran shi suka matse guri daya, jikinsa ya sake yayi sanyi lokaci daya.
Hannunsa da Safeera take shafa masa man zafi ya koma sanyi, lokaci daya gashin kansa yayi baki fuskarsa ta koma na saurayi, Raudah dake facing nasu ta fara kuka ta ce. “ Kuna zaune Baba fa ya…..”
Bata karasa ba Safeera ta rufe mata baki tana kuka, Mama ta zabura ta fashe da matsanacin kuka tana fadin. “ Na shiga uku na lalace, Bukar meya sa zakamin haka, kafa min alkawari bazaka barni ba, dan Allah ka tashi.”
Umar ya rike Mamansa yana cewa. “ Umma ki daina kuka suma yayi bai mutu ba.” Mama ta ture shi tana rike Baba tana cewa. “ Ka tashi Bukar, kar ka min haka.” Kafin kace me tuni gidan ya rikice da kuka, Falmata kam ta daskare a guri daya ta zuba masa ido.
Makwabta suka fara shigowa, Umar ya nemo Limamin unguwarsu yazo yayi addu’a kafin ya rufe masa ido, gidan ya rikice da kuka da babu mai rarrashi, Nabila sai dai ta bisu da ido dan bata san me mutuwa ba, Ammi da Amma suka share gidan tas aka saka taburma.
A daren aka masa wanka aka masa sutura, aka kira yaransa da Umma Fauziyya aka sanar da su, Babu wanda yazo a cikinsu sai Fauziyya da itama gulma ce ta kawo ta, kuma tana zuwa ta koma, dama babu takaba a kanta tun da ya saketa.
Haka gidan ya kwana da kuka, washe gari da safe mutane suka cika gidan, motocin da suke waje ya isa ya sanar daku cewa Bukar mai jama’a ne duk da a baya yayi arziki kafin karayar arziki ta same shi.
Karfe goma cif akayi jana’izar sa a kofar gidansa, wanda ya cika da mutane, inda aka kaisa makwancinsa ana masa fatan haduwa da mala’ikun rahama.
Alai-Bana ne ya kawo shinkafa da hatsi aka dafa aka bawa mutane.
Har akayi sadakan uku Kausar bata nan, kuma bata san da zancen ba, Safeera da Falmata sun rame, duk da cewan baya musu komai amma idan suna ganinsa yana rage masa zafi.
Da daddare Kausar ta dawo ita kadai babu Anaya, Safeera ta ce. “ Kausar ina Anaya?.” Ko a jikinta ta ce. “ Na siyar da ita ma wasu turawa.”
“ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un!! Inna’illahi wa’inna illahi raji’un!!!.” Cewan Safeera tana daura hannu a kai.
Raudah da idanunta suke a kumbure ta ce. “ Kausar Anaya kika siyar?.”
“ Eh ita na siyar a dollar 💵 dubu ashirin, kuma na bawa saurayina kudin ya juya mana.” Ta karashe tana murmushi.
Falmata ta ce. “ Kinyi k’ok’ari sannu, Baba kuma ya mutu.”
Tabe baki tayi ta ce. “ Allah ya hada shi da mala’ikun rahama ai yaci zamanin shi.”
Mama tayi murmushi ta cigaba da jan charbi.
Kausar ta dibi kayanta tas ta kalle su ta ce. “ Saduwan alkhairi nikam na tafi.”
Babu wanda yace mata ci kanta haka ta fita daga gidan.
Rayuwar gidan ta canza gaba daya, yunwa ta karu, har ya kai da sun saka gidansu a kasuwa, wani attajiri yazo zai siya gidan yaga Safeera yace yanaso, nan tace masa matar aure ce amma ga Raudah dan kamarsu daya, nan yace to.
Aka samu Mama da zancen tace Allah ya zaba mafi alkhairi, zuwansa na biyu yazo da magabatansa, Limamin unguwar ne ya zama a matsayin mahaifin su.
Nan ya ce a daura aure a wajen, abun ya yiwa Alhaji Hashim dadi kuwa, nan aka daura auren Raudah da Hashim akan sadaki dubu dari biyar.
Murna gurin Safeera ba’a magana, kuma yace kar a mata komai haka yakeson matarsa, inda Mama ta masa godiya sosai.
Falmata da Safeera suka karbi kudin suka siyo kayan abinci da kayan da Raudah zata saka, abaya kala uku suka siyo mata sai takalmi flat guda biyu, da bra da pant da underwear.
Raudah dai sai dai ta bisu da ido tana kallon su, washe gari Alhaji Hashim yazo yace zai tafi da matarsa dan zai bar nigeria ne, zai je Egypet wani aiki.
Nan gida ya burkice sai kukan rabuwa, da kyar aka iya babbare Safeera da Rauda, tana kuka suna kuka ta shiga mota suka tafi.
Gidan ya koma kamar na mutuwa, duk da yanzu akwai kudi a hannunsu kuma akwai abinci, sai dai babu farin ciki.
Haka har aka shafe watanni uku babu labarin Rauda, ga Kausar ta tafi, nan hankalin su ya fara tashi ganin babu labarin Raudah.
Ana cikin wannan yanayin ne kuma yan boko haram suka shigo garin, inda aka fara gudun hijira, a hakan ne kuma Safeera tabi wani hanya daban, Falmata da Mama da Nabila, Ammi, Amma, da Umar suka bi hanya daya.
✍🏼
💔*BAƘAR ƘAUNA*💔
_Gajeran labari_
*Na*
*Fatima Isa Manu*
_DR. TEEMAH ( SAHIBAR JAJIRTATTU )_
Masu neman littafin *BAƘAR ƘAUNA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*TWO DIAMOND STAR LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
*Page 21*
Ana cikin wannan yanayin ne kuma y’an boko haram suka shigo garin, inda aka fara gudun hijira, a hakan ne kuma Safeera tabi wani hanya daban, Falmata da Mama da Nabila, Ammi, Amma, da Umar suka bi hanya daya.
Ba tare da tasan inda ta nufa ba, haka ta din ga gudu tana kuka, har tsakar dare kafin ta samu wani k’ango ta fake a gurin.
Washe gari da safe ta farka ta cigaba da tafiya dan neman inda zata samu y’an uwanta, haka wunin ranar tayi shi tana kuka tana neman su, amma shuru babu alaman su.
Sai da aka d’auki kusan sati daya me kyau ana kashe kashe kafin aka samu sauki abun ya lafa, garin ta ko’ina idan zaka wuce gawa zaka tarar kwance ba kai, ko kuma ba hannu 😢.
Haka Safeera ta cigaba da neman y’an uwanta amma babu su babu labarin su, ta koma gidansu sai dai gidan ya kone kurumus babu komai har langa-langan ya tafi a iska.
Haka tasha kukanta kafin ta nufi hanyar Baga road, shi ma shuru kamar ba kasuwa ba babu komai kuma babu alamun mutane.
Karamin shago ta shiga ta zauna tana jan k’ofan ta rufe, a gurin take kwana, idan safiya yayi ta fita neman abinci, dan yawancin shagunan a bud’e aka barsu, sai ta shiga ta dauki abunda zata ci ta fito, har mutane suka fara hallara.
Watan ta daya a wannan gurin tana fafuta da rayuwarta, wata ranar talata da dare wani ya shigo shagon da take kwana, a buge yake sosai ya nufo gurinta inda take bacci.
Cikin bacci taji ana ja mata riga, da sauri ta farka tana kallon shi fuskarta cike da mamaki zuciyarta tana harbawa, kamar mai koyan magana ta furta. “ Me ya faru.”
Ko kulata bai yi ba, sai ma ture ta din da yayi yana kwanciya gefe bacci ya dauke shi.
Tashi tayi ta lek’a wajen taga dare ne sosai, komawa ciki tayi ta tura kofan ta kwanta a nesa dashi, nan da nan bacci ya dauke ta.
Washe gari da sassafe ta farka tana kallon shi, yana zaune ya sunkuyar da kansa baka ganin fuskarsa, jikinsa sanye da Army’s trouser da tea sheet green, kafarsa sanye cikin takalmin sojoji, yatsunsa suna sanye da wani ring 💍 mai yalki sosai, fari ne sosai, ga gefen wuyansa da yasha shatin wuk’a.
Wani yawu mai kauri Safeera ta hadiye tana cewa. “ Waye kai.”
D’ago da kansa yayi ya zuba mata idanunsa masu rikitarwa, lokaci daya ta tsure tana ja baya, dogon fuska ce dashi wanda sajensa ya kwanta luf, da tsiririn hanci wanda yayi dai-dai da karamin bakinsa, giransa sun hade saboda tsabar gashi, abun cikin idanunsa brown ne.
Murmushin gefen baki yayi wanda idan ba ka lura ba bazaka san yayi ba, ya furta. “ Ke waye ke?.”
Gagara magana tayi sai ma tashi tsayen da tayi zata gudu, taku daya yayi ya cafko ta yana mayar da ita inda ta tashi, ya juya baya yana ciro wayansa ya amsa kira.
Ba tare da yace komai ba ya kashe wayan ya juyo yana kallon ta. “ Me ya kawoki nan?.”
“ A nan nake kwana.” Ta fada tana zuba masa ido.
Kallon sama da k’asa ya mata kafin ya tabe baki ya ce. “ Tashi mu tafi.”
Girgiza kai tayi da sauri ta ce. “ A’a bazan bika ba.”
“ Dalili?.”
Shuru tayi tana kallon kafafunsa dake cikin takalmi, sake tambayarta yayi. “ Dalilin Meyasa ba zaki bini ba?.”
“ Bansan ka ba .” Ta fada tana komawa gefe.
“ Ni ma ai bansan ki ba, kawai taimakon ki zanyi duba da ke macece, ba kyau a barki a nan gurin dan bata gari kar suzo su miki wani abu.” Ya fada yana mika mata hannu alamun ta taso.
Bin hannun tayi da kallo kafin ta mik’a nata ta taso, waje suka fito yana rike da hannun nata, motocin sojoji guda uku ne a jere, yana isowa suka sara masa.
D’aga kai tayi ta dube shi, murmushi ya sakar mata yana bude mata mota ta shiga kafin ya zagaya aka bude masa ya shiga.
Tafiya motocin suka fara, can taji ya ce. “ Me sunanki Kanwata?.”
“ Safeera.”
“ Feera zanna kiran ki dashi kawai.”
Dariya ta masa wanda rabon da tayi ta manta, kafin ta ce. “ Me kuma Feera? Haba ina laifin Saf.”
Murmushi yayi ya ce. “ Kawai ace Afeera ko?.”
“ To me laifin S din?.”
Bai ce komai ba yayi murmushi yana danna wayansa, a Barack suka tsaya aka bude masa kofa ya fito, kafin ya zagaya ya bud’e mata ta fito.
Rike hannunta yayi suka nufa cikin barack din, duk inda suka wuce sai an sara masa, har suka iso wani gida.
Key ya saka ya bud’e kofan kafin suka shiga sauran sojojin suka tsaya, murmushi ya mata yana fadin. “ Ki zauna bari a kawo miki abinci idan kika ci sai mu tafi.”
“ To Yaya.”
Jan kumatunta yayi yana fadin. “ Yawwa Kanwar Yayanta.” Kafin ya nufi wani daki ya shiga, da ido tabi shi kafin ta sauke numfashi tana tunawa da Falmata da Nabila, a fili ta furta. “ Ko suna wani hali yanzu?.”
Kwanciya tayi akan kujeran bacci yana daukarta, cikin barcin tayi mafarkin suna ihu suna neman taimakon ta, Raudah tana mik’a mata hannu tana kiran sunanta, sai dai duk gudun da take yi bata iya zuwa gurin su, Falmata tana kiran sunanta tana kuka.
A furgice ta farka tana saka ihu, da gudu ya fito daga dakin yazo inda take yana rike ta.
“ Suna kuka ka barni naje gurinsu, Raudah tana kuka zanje na taimake ta, Nabila Falmata!!!!!! Wayyo Allah.” Ta fada tana kuka tana k’ok’arin kwace kanta zata mike.
Jijjigata yayi yana cewa. “ Tsaya!!!.”
Cak ta tsaya tana zuba masa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 17