Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Ina mai matukar ƙara godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara wannan sabon littafin nawa *ADAMSY* idan akwai wani sharri wanda zai amfane ku ina roƙon Allah kada ya bani ikon gama rubuta wannan labarin,ina roƙon Allah ya bani ikon rubuta abunda zai amfani al'ummar musulmi. Alkhairin da ke cikin wannan labarin Allah ya sada mu da shi, ina roƙonku kada kuyi amfani da abinda ba alkhairi ba da kuka ci karo da shi a cikin littafin nan, kuyi amfani da darasin da ke ciki, sannan ku tsoraci mai sunan ƙeya (Danasani) dake cikin littafin, ina fatan zaku karɓi wannan littafin na *ADAMSY* kamar yadda kuka karɓi littafin Inteesar koma fiye da yadda kuka karɓi Inteesar. Page0️⃣1️⃣ Aguje ta fito daga cikin ɗakinta tana ihun naman taimako,mayafinta ne ya faɗi ya harɗe ƙafarta wanda hakan yasa ta faɗi ƙasa. Fitowa yayi daga ɗakinta yana ƙwala mata kira. "Husnah! Husnah!! Husnah!!!" Tana ganinsa ta rintse idanunta tare ƙwalla ƙara, kanta ta cusa a tsakanin gwuiwarta. Amina ce ta fito daga ɗakinta sakamakon jin ihun Husnah ke yi, cewa kin mamaki ta kalle su tare da furta cewa "Lafiya kuwa amaryar da aka kawo daddaren nan waɗanda suka kawo ki ma ko awa ɗaya basu yi da tafiya ba ki fito kina ihu me ke faruwa?" Jin muryar Amina ce yasa ta Husnah ta miƙa da sauri ta nufi bayanta, ɓoyewa take a bayanta kamar wacce za'a kama. "Adams wai me ke faruwa ne? Naji ihunta ne yasa na fito cikin tashin hankali dan ganin me ke faruwa, amma abin mamaki sai naganku ku biyu akwai abinda ka mata ne?" Girgiza kansa yayi cikin damuwa ya ce, "Nima abinda ke bani mamaki kenan, lokacin da muka shigo da abokina tana tare da ƙawayenta, bayan anyi siyen baki sun tafi sai na bisu na raka su, kuma iyakar ƙofar falon nan na tsaya suna fita na rufe ƙofar, dawowa ta yanzun nan ina ina shiga naga ta kalle ni ta ƙwalla ƙara." Amina ce ta janyo Husnah daga gefenta, zuba mata ido tayi tare da cewa "Husnah me ke damunki ne?" Kuka kawai take mara sauti, idanunta kuwa kamar an buɗe fanfon ruwa. Ganin bata da niyyar yin magana ne yasa Amina ta kalli Adamsy tare da cewa "Ko dai tana da wata larurura ce?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Bana tunanin akwai wata larura a tattare da ita, dan da akwai da Ummanta ta sanar da ni" Kallon Husnah Amina tayi tare da cewa "Kinga yanzun dare yayi ƙarfe goma sha biyu saura kwata, ki je ku kwanta." Ba musu ta nufi ɗakinta yayin da shi kuma ya sunkuya ya ɗauki mayafinta yabi bayanta suka wuce. Tura ƙofar ɗakin ta yi ya shiga yana biye da ita a bayanta, bakin gadon ta zauna kanta a sunkuye, jin muryarsa tayi ya kira sunanta a hankali. "Husnah" A hankali ta ɗago kai ta kalle shi, gangar jikinsa ne kawai nasa amma kansa sam baiyi kama da na mutane ba, dan ƙaho ne ta gani a kansa ga fuskarsa buzu-buzu da gashi, idanunsa kuwa jazir, wani irin ƙara ta sake saki wanda ya fi na ɗazu a guje ta ruga sai da ta ci karo da ƙofa kafin ta fita. Amina da ke ƙoƙarin shiga ɗakinta ne ta jiyo ihun Husnah, dakatawa ta yi tare da juya bayant, idanunta suka sauka a kan Husnah da ta fito a guje kafin ta ankare har Husnah ta rungume ta tana kuka, cikin mamaki ta ce, "Husnah me ya ke damunki ne haka? Kina ta ihu baki ga dare yayi ba ko so kike ki tara mana jama'a a daren nan dan Allah ki je ki kwanta." Girgiza kai tayi tare da cewa "Wallahi bazan bishi ba tsoro yake bani" "Ban gane tsoro yake baki ba, ba mijinki bane?" Shiru tayi bata sake magana ba, Amina ce ta maida dubanta ga Adamsy dake tsaye yana kallonsu ta ce, "Wai me ke faruwa ne? Ya daga kawo maka amarya yau sai matsaloli ke ta kunnowa tunda jama'a suka watse?" "Amina bani da amsar tambayar da kika mani, dan nima haka naganta tunda na shiga ta kalle ni take ta ihu." Jinjina kai tayi tare da cewa "Kodai tana da taɓin hankali ne?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Bana tunanin haka, sai dai idan wani abin ne daban, amma Husnah bata da kowane taɓin hankali." Amina ce ta janyo hannun Husnah suka ƙarasa jikin kujera, zaunar da ita tayi akan kujera tare da cewa "Husnah me ke damunki? Dama kina irin haka ne?" Kai ta girgiza tare da cewa "Bana komai shine ya ke canza siffarsa idan muka shiga ɗaki, yake firgita ni" Kallon juna sukayi Adamsy da Amina suna mamakin jin kalamanta, inda ta cigaba da cewa. "Ke Aunty bai taɓa canza maki siffarsa ba, idan kina tare da shi?" Kai Amin ta girgiza mata tare da cewa "Mijina ba wata siffa da yake da shi ko yake canza mani, ke dai sai dai kina da wata larura ne da yasa hakan take faruwa da ke, to wane irin canza siffa kamar wani aljani?" Da sauri ta kalli Amina tare da cewa "Eh wallahi Aunty ai kamar alhani haka nake ganinsa." Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka. "Ke kin isa kiga aljani da ido ko?" Amina ce tayi mata maganar tana nuna ta da yatsarta manuniya, inda ta cigaba da cewa. "Kinga ki kwantar da hankalinki ta yiwu ma mafarki kikayi kike tsorata, idan kuma ba haka ba tabbas kina da ciwon hauka." "Wallahi gaskiya nake faɗa maki ki yarda da magana ta, ni bani da ciwon hauka lafiya ta ƙalau, ni da ido na na ganshi bayan ya raka abokansa ya dawo yana shie ya fara tsoratar da ni. Amma lokacin da suke nan bai yi komai ba ya tsaya a yadda yake, bayan tafiyarsu ne sai ya fara canza siffa kamar na aljani." Adamsy kam zuba mata ido yayi yana kallonta, ya ma rasa abin faɗa, kai tsaye ya koma ɗakin zuciyarsa a cunkushe. Amina ta dinga rarrashin Husnah tare da bata haƙuri kam ta tashi da daure ta bi mijinta, sai da ta tabbatar ta ɗan saki jiki sannan ta raka ta har bakin ƙofar ta tura mata ƙofar, ta shiga sannan ta janyo masu ƙofar ta wuce zuwa ɗakinta. A hankali cikin tsoro Husnah ta ɗago idanunta ta kalli Adamsy, sai ta nufi ƙofar fita a guje, biyo bayanta yayi shima cikin hanzari yasha gabanta, wanda hakan yasa ta kalle shi tsabar tsorata yasa ta zube wajen ƙasa sumammiya. Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerar dake falon tare da yin tagumi yana faɗin "Na shiga uku" Ruwa ya ɗuko a fridge, ya ɓalle marfin robar tare da yayyafa mata a jiki, a jiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, tare sakin kuka, a hankali ya kira sunanta. "Husnah" Buɗe ido tayi tare da sauke shi akansa, take ta fashe da kuka tana ja da baya cikin tsoro. Ganin haka yasa shi miƙewa ya nufi ɗakinsa, tare da faɗin. "Ki tashi kije ɗakinki ki kwanta, sai da safe." Daga nan bai sake wata magana ba, ɗakinsa ya shige yana magana shi kaɗai "Wai wannan wane irin daren farko ne? Ace kayi aure ranar da aka kawo maka mata ta dinga gudunka tana tsoronka kamar taga wani dodo? Daren da yakamata ace nayi kwanan farin ciki sai gashi na yi kwanan baƙin ciki?" Babbar rigarsa ya cire ya nufi toilet zuciyarsa cike da saƙe-saƙe iri-iri . Ɓangaren Husnah kuwa tana ganin ya shiga ɗakinsa sai ta miƙe tsaye, a guje ta nufi ɗalibta tana shiga tayi saurin murza key tare da durƙushewa a wajen, ta jingina bayanta da ƙofar ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Kallon agogon bangon da ke ɗakin tayi, ganin ƙarfe ɗaya na dare yasa ta sakin kuka, dan ba zata iya fita a wannan lokacin da da ta fita, amma ina dare ne a tsorace ta ke , ba zata iya fita ba, Nan ta cigaba da kukanta ita kaɗai ba mai rarrashinta. Misalin ƙarfe biyu da rabi na daren ne ta ji barci ya ci ƙarfinta, duk da cewar ita batayi niyyar barci ba amma kuma barci ɓarawo ne lokacin da zai sace ka ma ba zaka sani ba, tashi tayi a hankali ta nufi bakin gadon ta kwanta, ko hasken ɗakin bata rage ba haka ta kwanta dan a tsorace ta ke. Adamsy ma a ɓangaren sa ma bai samu barcin kirki ba, dan tunda ya shiga toilet ya watsa ruwa tare da ɗauro alwala ya fito, jallabiya ya saka sannan ya shimfiɗa sallaya, sallar nafila ya gabatar raka'a huɗu, ya dinga jera addu'a akan wannan matsalar da ta tunkaro masa, ya daɗe yana addu'a kafin ya shafa, ƙarfe biyu ya kwanta. Misalin ƙarfe biyar na asuba ya farka, ganin ya kusa makara ne ma yasa ya nufi toilet ya ɗauro alwala, shiri zuwa Masallaci yayi inda ya fito dan zuwa sallar asuba. Sai da ya tsaya ƙofar ɗakin Amina yayi mata knocking dan ta farka lokacin sallah yayi, jin motsi alamar ta tashi ne yasa shi tafiya, ya tsaya ƙofar ɗakin Husnah da ba niyyar buga mata ƙofar, amma tuna cewa zata iya rikece mashi da asubar nan yasa shi fasawa, yayi ficewarsa dan zuwa masallaci. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *SANARWA* Wannan ƙirƙirerren labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suns ko hali yazo daya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page0️⃣2️⃣ A guje Adamsy ya fita da motar daga gidan, ya ɗauki hanyar fita daga layin. Kai tsaye gidansu Husnah ya nufa, a ƙofar gidan yayi parking inda ya samu mahaifinta na zaune a kofar gidan, da ya ƙara rediyo a kunnensa yana sauraron labaran BBC, fitowa yayi inda ya durƙusa har ƙasa ya gaida shi, ya amsa masa cikin sakin fuska tare da tambayarsa iyali. Shiru yayi ya kasa magana dan ya lura kamar mahaifin Husnah baisan bata gidansa ba, tunani ya fara yi idan bata gidan iyayenta to ina ta tafi? Me zai ce da iyayenta idan ba'asan inda ta tafi ba, tunanin yadda zai ɓullowa lamarin yake yi, idan ya sanar da iyayenta cewa amaryar da aka kai masa jiya daddare ta gudu me zasu ɗauke da? Ba zasu taɓa yarda da shi ba sai dai su ce ya fito masu da ƴarsu. Bai gama tunanin mafita ba ya ji muryar Abban Husnah na cewa "Adam lafiya kuwa? Ko akwai wata damuwa ce?" Kafin yayi magana ne wata yarinya ƴar kimanin shekaru bakwai ta fito daga gida, ksllonsu tayi tare da cewa "Abba wai ance na duba ko ka dawo?" "Eh yanzun na dawo me ke faruwa?" "Aunty Husnah ce ta dawo daga gidan mijinta tana kuka." Abban ne ya kalli Adamsy da sauri cike da mamaki ya ce, "Adam me ke faruwa ne, me yasa ta dawo da sassafe ni bansan ma ta dawo ba, dan tunda muka dawo sallar asuba na tafi raka wasu baƙin da zasu koma yau." Shiru Adamsy yayi tare da cewa "Abba tunda aka kai Husnah gida na masu kai Amarya suka wstse, abikaina suka rako ni akayi siyen baki na tafi raka su, to wallahi tunda na dawo take ta gudu na, ko minti ɗaya ba muyi tare da ita ba, sai gudu na take tana kuka wai tsoro nake bata, a taƙaice dai ban damu nutsuwa ba har sai tsakar dare da na tafi ɗaki na na barta. Bayan na dawo daga masallaci da safe na shiga ɗakin uwar gida na muka gaisa, bayan nan sai na nufi ɗakin Husnah dan duba lafiyarta ashe sammakon barin gidan tayi." Shiru Abban Husnah yayi tare da cewa "Ka jira ni ina zuwa" Daga nan ya tashi ya nufi cikin gidan, inda duk ya same su sun sanya Husnah a gaba suna tambayarta ko lafiya, amma ba wanda yayi wa magana sai kuka take, dan bar yau gidan akwai sauran jama'a waɗanda suka zo biki daga garuruwa dake nesa basu koma ba. Dan hankalin mutane ya tashi ganin amaryar da aka kai jiya daddare ne ta gudu yau da safe ta dawo. Gyaran murya Abba yayi wanda hakan yasa duk suka ba ja baya gare da bashi waje, kallonta yayi tare da cewa "Husnah" Ɗago kai tayi tare da kallon maihaifn nata "Me ya kawo ki gidan bayan jiya aka ɗaura maki aure aka kaiki gidan mijinki? Sannan da izinin mijinki kika taho gida?" Fashewa da kuka tayi tare da cewa "Abba wallahi bazan iya zama da shi ba, tsoronsa nake ji wallahi jiya fa..." Tsawar da ya daka mata ne yasa yasa tayi shiru. "Tashi ki koma kibi mijinki ga shi can a ƙofar gida yana jiranki, kuma wallahi naji labarin cewa kin aikata wani abu wanda zai daɓawa mijinki sai nayi mummunar ɓata maki rai." Tana kuka ta tashi ta tafi, jama'ar dake gidan su a tunaninsu jin ta ce, ba zata iya zama da shi ba tsoronsa take yi yasa suka fara tunanin ko mijinta ya kasance ta ne ta tsorata da shi ne yasa ta gudu dan Azabar daren farko. Tana kuka ta miƙe ta nufi hanyar fita, dan tasan bata isa ta ja da maganar mahaifinta ba. A ƙofar gida ta zame shi zaune akan tabarmar Annabta, yayin da shi kuma Abban na biye da ita a baya, cikin girmamawa ya ce, "Abba nagode sosai Allah ya ƙara girma." Kallonsa yayi tare da cewa "Ameen ya Allah, gata nan a ƙara haƙuri da ita, kasan yarinya ce." Dubansa ya maida ga Husnah ya ce, "Ke kuma kada na sake ganin ƙafarki gidan nan ba har sai dai idan da iznin miji ba, idan kuma ba haka ba kinsan abinda zai iya biyo baya, kinfi kowa sanin waye ni, saboda haka kibi mijinki ki zauna lafiya da abokiyar zamanki kada na ji wata matsala daga gare ki." Kallon Adamsy yayi tare da cewa "Tashi ku tafi Allah ya baku zaman lafiya." Amsawa yayi da Amin tare da yiwa Abban godiya, daga nan ya miƙa ya nufi motarsa ya shiga. Har ya shiga ya zauna ne amma Husnah bata tashi ba, tsawa Abba ya daka mata wanda hakan yasa ta tashi da sauri ta nufi motar Adamsy. Buɗe mata yayi ta shiga ta zauna tare da ɗaura kanta akan cinyarta tana mai cigaba da rera kuka. A hanya haka ya dinga rarrashinta dan ta yi shiru ta daina kuka amma bata daina ba, dan haka dole ya haƙura ya ƙyale ta. Ƙofar gidansa ya tsaida motar tare da danna horn, mai gadin ya wangale masa ya shiga yayi parking. Ɗago kanta tayi jin ya tsaida motar kuma yayi shiru baice da ita komai ba ne yasa ta ɗaga kanta dan taga ina suke. Kallon gidan tayi hakan ya tabbatar mata da cewa sun iso, juyawa tayi ta kalle shi, abun mamaki sai ta sake ganin wannan fuskar mai bata tsoro da firgitata ya bayyana akan fuskar Adamsy, ƙara ta saki tare da ficewa daga motar a guje. Cikin gidan ta shiga inda ta faɗa ɗakin Amina, yayin da ita kuma Amunar tayi wanka ta gama saka kaya kenan sai Husnah ta shigo ɗakin cikin dakin a guje , Amina ana tsoro ne ya kama ta cikin tashin hankali ya ce, "Lafiya me ke faruwa ne?" Kafin tayi magana sai Adamsy ya turo ƙofar ya shigo, kallon Husnah yayi tare da cewa "Me ke damunki?" Ido ta zuba masa tana kallonsa ba tare da tayi magana ba, kuma bata tsorata ba . "Na ce me ke damunki?" "Bakomai" "To me yasa kike gudu na? Kar fa ki mance auren soyayya mukayi ba na haɗib ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya kinji?" Kai ta jinjina masa alamar to daga nan ya ja hannunta suka wuce zuwa ɗakinta.Suna shiga sai ga shi ta kalle shi tayi wannan ihun, a guje ta fice daga ɗaki. Haka zaman nasu ya cigaba da kasncewa, abun na Husnah mamaki yake ba Adamsy, idan shi da ita suka kaɗaice to abin sai Addu'a dan ta dinga ihu tana guduwa. Wannan dalilin yasa Adamsy ya kai Husnah a duba ƙwaƙwalwa, inda aka tabbatar masa da cewa ƙwaƙwalwarta rta lafiya lau suke, ba wani abu dake damunta. Daga nan sai ya fara tunanin bata sonsa ne, dan idan baya gidan zata zauna ita da Amina suyi ta fira, amma idan har da shine ma bata yarda su karɓe, idan ya shiga ɗakinta tun kafin ma ya shiga zaiji ta datse ƙofar, bata ma yarda su haɗu ita da shi, da abun ya ishe shi ne ya tafi yakai ƙara gidansu inda Ummanta ta zo har gida tayi mata duk kamar yadda Abba ya umarce ta, da yi. Duk da fa wannan abinda akayi mata ba abunda ya ragu ko ta canza Haka suka cigaba da zama har wata rana da Adamu ya gaji gaji ko minti ɗaya bata taɓa zama da shi ba, dan haka ya sauwaƙe mata inda yayi mata saki ɗaya, murna a wajen Husnah ba'a magana . Zama yayi yana nazari shi wace mace zai aura ne? Dan gaskiya bazai iya haƙura da zancen ƙarin auren nan ba, dan yana buƙatar haihuwa a rayuwarsa baya da burin da ya wuce yaga yaransa, gashi mata biyu yana aure basu taɓa yarda ko kusa da shi suzo , ga uwar gidansa Amina tana da matsala likitoci sun tabbatar masa da cewa ba zata taɓa haihuwa ba, gashi burinsa a duniya bai wuce yaga yaransa ba. *Jiya banaga comments naku ba yadda kuka saba ba, ko labarin bai maku bane , yawan comments naku yawan readmore naku* *Daga alƙalamin*✍️ Zauna Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Dan neman ƙarin bayani* 09065327995 Love you oll😍 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba. *SANARWA* Wannan ƙirƙirerren labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar a yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page 3&4 Likitoci sun tabbatar masa da cewa ba zata taɓa haihuwa ba gashi burinsa a duniya bai wuce yaga yaransa ba. Kasancewar sa mutum ne mai matuƙar son 'ya'ya hakan yasa ya fara tunanin ƙara wani auren. Wata rana ya tafi wurin abokinsa Sadik a wata unguwa, inda yaga wata 'yar unguwar sanye take da hujab zata koma gida bayan an tayar da su daga islamiyya. Nan Adamsy ya ganta ya nunawa Sadik yana sonta, Sadik yayi masa jagora zuwa gidansu Fauziyya, dan su fahimci juna. Cikin ikon Allah kuwa ta amince da Adamsy dan taga tabbas ya haɗu ta ko ina ba maccen da zai ce yana sonta ta ce a'a. Nan da nan soyayya ya ƙullu tsakanin Adamsy da Fauziyya, har wata rana ya nemi da ta shirya ya kaita ta gaida Ummansa, dan sunyi magna da Umman akan Fauziyya zai kai mata ita su gaisa. Bayan ya gama shiri cikin manyan kayansa ya saka hula ya fesa turare, takalminsa ya saka tare da ɗaukar wayarsa ya fito zuwa falo, Amina na zaune a falo idanunta na kan wayarta, ƙamshun turarunsa ta ji yasa ta ɗago da kai tana kallonsa, murmushi yayi tare da zama a gefenta. Hannunsa ya riƙo cikin nata tare da cewa "Zan ɗan fita ne? "Fita kuma naga yau weekend ne baka zuwa ko ina?" "To idan kuma fitar ta kama da ya za'ayi? " "Wannan irin kwalliya haka kamar wani ango?" Dariya yayi tare da cewa "Ai ango ne" Da sauri ta sake kallonsa "Ango wace ce?" "Angonki mana " Dariya tayi tare da cewa "Faɗa mani gaskiya ko dai ƙanwa kake shiri sake kawo mani ne, tunda Husnah ta guje mu." Shiru yayi yana nazari wayarsa ta soma ruri dubawa yayi yaga Fauziyya ce take kiransa, sai ya juya ya kalli Amina dan yaga ko ta lura da mai kiran wayarsa, ita kuma ta lura taga sunan wacce ta kira, amma sai tayi saurin ɗauke kanta, dan taga zai kalle ta, ganin ba wayar take kallo ba idanunta na kan wayarta yasa shi tunanin bata ,gani mai kiran wayar ba, bai ɗaya daga ba har wayar ta tsinke aka sake kiransa a karo na biyu duk Fauziyya ce, nan ma bai ɗaya ba sai dai ya saka wayar a silent. "Ba kiran wayarka ake ba ne?" "Kiran ba mai mahimmanci bane shiyasa." Murmushi tayi tare da maida hankalinta kan wayarta, text message ne ya shigo wayar dubawa yayi yaga Fauziyya ce take cewa "Na gama shiryawa kai nake jira.' Amsa ya mayar mata inda ya ce "Okay gani nan zuwa' Daga nan sai ya kalli Amina da duk abinda yake akan idonta ne ya ce "Ni zan fita ne" "To mijina muje na raka ka ko?" Tashi sukayi hannunsu sarƙe cikin na juna, inda ta rika shi har bakin motarsa, sannan ta koma ciki. Horn yayi mai gadin gidan ya wangale masa gate ya fita da motarsa. Har ya

Chapter 1 of 19