Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more
Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.
*YAR GIDAN TAFIDA*
Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.
*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.
Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM*
Page2️⃣6️⃣&2️⃣7️⃣
Daƙyar ta iya tashi ga kanta da ke mata ciwo kamar zai fashe, tsawar da Inna Habi da dake daka mata ya sa ta nufi hanyar fita tana kuka.
Tana fita tana tafiya ba tare da tasan inda zata dosa ba.
Ta yi doguwar tafiya zuwa bakin titi zuwa lokacin ji ta yi duk ƙarfinta ya ƙare ta galabaita.
Jikin wani shago ne ta jingina kusan mintuna goma sha biyar tana wajen, mai shagon ne ya kalle ta ya ce,
"Ke lafiya?"
"Dan Allah abun hawa nake nema."
Ganin yanayin da ta ke ciki ne ya sa mai shagon ya ƙarasawa ya nemo mata abun hawa.
Tare suka ƙaraso da mai keke napep ɗin, inda ta ƙarasa ta shiga, mai shagon ya ce,
"Zaki gane inda zaki tafi ko?"
Kai ta gyaɗa masa, sannan ya kalli mai napep ya ce,
"Dan Allah ka bi da ita a hankali, dan ka ga halin da ta ke ciki."
Kai ya jinjina tare da cewa
"Insha Allah."
Daga nan ya ja suka tafi.
Mallam Musa na zaune a a ƙofar gidan sai ya ga mai napep ya tsaya a ƙofar gidan, kallon napep ɗin ya ke yi ya ga matuƙin ya fito, yana gaida Mallam Musa.
"Barka dai."
Ya buɗe baki da niyyar magana sai ya hangi Humaira na fitowa daga cikin napep ɗin.
Tashi ya yi yana kallonta cikin mamaki ya ce,
"Humaira!"
Da sauri ya ƙaraso wajenta tare da cewa
Me ya same ki haka? Hatsari kuma yi?"
Girgiza masa kai ya yi tare da cewa
"Ba hatsari bane Abba, ga mai napep nan ka sallame shi ."
Ta yi maganar tana mai jinginar da kanta da bango.
Mallam Musa ya sallami mai napep sannan ya janyo hannunta suka shiga cikin gidan.
A barandar ɗakinsa suka zauna inda ya kalle ta ya ce,
"Me ya same ki haka ne?"
Nan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da shi, ƙwallon ne ya cika idon Mallam Musa, dai-dai lokacin da Adamsy da Abdallah ke fitowa daga cikin gidan.
Kallonsa suka yi yadda idanunsa ke zubar da hawayen tausayin 'yarsa, ƙarasawa suka yi wajensu Adamsy ya kalli Mallam Musa sannan ya maida dubansa zuwa ga Humaira, cikin mamaki ya ce,
"Baba mai ke faruwa ne kuma wace ce wannan?"
"Wannan 'yata ce."
Kafin Adamsy ya sake wata magana Abdallah ya ce,
"Me ya same ta haka?"
"Dukanta aka yi"
A tare suka haɗa baki wajen cewa
"What's?"
Shiru Mallam Musa ya yi inda Abdallah ya ce,
"Ko ma waye ya mata irin Wannan dukan yakamata ki hukuma ta yi wani abu akai."
Mallam Musa ya ce,
"Mata ta ce ta mata wannan dukan."
Abdallah ya kalle shi da sauri ya ce
"Amma ba ita ta haife ta ba, dan idan ita ta haife ta ba zata taɓa mata wannan dukan ba , sai ka ce ta samu hatsarin mota."
Adamsy ya ce
"Bisa ga yadda na ga kana kula nasan da ciwo a zuciyarka, amma dan Allah ka fitar da mu haske dan ka saka mu a cikin duhu."
Ajiyar zuciya Mallam Musa ya sauke, sannan ya basu sa labarin abinda ke faruwa da Humaira, tun daga rasuwar mai mahaifiyar Humaira har zuwa wahalhalun da ta ke sha a hannun Inna Habi. Har ɗibar ruwa da asuba ta tallullukan da aka bata da ayyukan gidan da komi ba abinda ya ɓoye masu .
Tausayinta ya kama su, inada Adamsy ya ke ta maimaitawa a zuciyarsa
"Karuwanci."
Abdallah ya kalli Mallam Musa ya ce,
Yanzu kai kana kallo irin wannan abubuwan suke faruwa a gidanka, amma kake shiru ka zuba ido ba wani mataki da zaka ɗauka?"
Murmushin takaici Mallam Musa ya yi tare da cewa
Duk abunda take yi sai na fita ta ke mata shi, wani abun ma a gaban idona ta ke mata shi, dan ta san ba wani abinda zan iya mata, musamman da ta ga bani da abunyi."
Shiru ya yi yana nazari kafin ya kalli Adamsy ya ce,
"Ya za'ayi da yarinyar nan?"
"Bari na kira manaja ya zo da Dr Fatima ..."
Dama Humaira akwai tsoron allura, dan hakan dai ta ce bata so a kira kowa, dan a rayuwarta ta tsani alluran dan haka ta ce,
"Kibarshi zan warke."
Mallam Musa ya miƙa mata robar ruwa ya bata, ƙarɓa ta yi tare da yin addu'a.
Abdallah ya ce,
"Gaskiya cigaba da zamanta tare da Inna hatsari ne, dan haka ka nisanta ta da ita."
"To ai ba inda zan kaita, dan bamu da wani ɗan uwa ko 'yar uwa a nan."
"Tofa, to kawai ka aurar da ita kowa ya ta huta."
Ya ƙarasa maganar yana kallon Admsy.
"Yallaɓia na baka sadakan 'yata, ba dan komai ba sai fisabilillahi, haka kawai na ji zuciyata ta amince da hakan "
"To ban karɓa ba kuma bana buƙatar kowace mace a rayuwata."
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
0906532995
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*
*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*
Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.
Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.
Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩
1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more
Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.
*YAR GIDAN TAFIDA*
Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.
*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.
Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM*
Page2️⃣8️⃣&2️⃣9️⃣
"To ba karɓa ba kuma bana buƙatar kowace mace a rayuwa ta."
"Yallaɓai nima dole ta sa na faɗa maka haka? Saboda bani da wani zaɓi shi ya sa na ce maka na baka sadakan 'yata."
"Me ya sa dole sai ni zaka ba?"
"Saboda kai kaɗaine na ji hankalina ya kwanta da kai, kai ka ɗai ne na ji a jikina tarayyarka da ita zai zama alkhairi insha Allah."
Girgiza kai Adamsy ya yi tare da cewa
"Babu wani alkhairi da tarayya ta da wata mace, babu wani abin farin ciki ga macen da ta yi tarayya da ni babu..."
Abdallah ne ka katse shi ta hanyar cewa
"Adams ya isa haka Please."
Sannann ya juya ya kalli Mallam Musa ya ce,
"Mungode Baba da wannan kyautar da ka yi wa abokina na, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi."
Adams na da niyyar yin magana kenan sai Abdallah ya ja hannunsa tare da cewa
"Mu shiga ciki ko?"
Ba musu ya bishi suka koma ciki, Adams ya kalli Abdallah tare da fisge hannunsa ya ce,
"Haba Abdallah ya zaka mani haka? Kai kanka shaida dangane da abubuwan da suka faru a rayuwata, kuma duk marasa daɗi, na baka labarin duk wani abinda ya faru da matayen da na ke aure me kake tunanin zai faru da wannan ? Itama mutuwa zata yi ko haukacewa? Ko nakasa zata samu?"
"Babu abunda zata samu insha Allahu, na jima da wannan tunanin a cikin zuciyata, na jima ina son baka shawarar nan sai ga Allah ya kawo ta cikin sauƙi."
"Me ka ke nufi?"
A zahirin gaskiya ina zargin duk abubuwan da suke faruwa da matayen da kake aure akwai wata munaƙisa, ba haka kawai bane, na san komai daga Allah ne amma akwai sanadi."
Kallon mamaki yake masa tare da cewa
"Waye sanadi?"
"Koma waye da kanka zaka gano idan har ka ɗauki shawarar da zan baka."
"Wata irin shawara?"
"Na farko ina son ka amince da auren wannan yarinyar, na biyu ina son wannan auren da zaka yi ya zama auren sirri, kada ka sanar da kowa na ka wannan auren daga ni sai kai , sai kuma Allah wanda ya halicce mu. Sannan ko Mahaifiyarka kada ta san da wannan zancen ballantana matarka."
Wani irin kallo Adamsy ya watsa masa tare da cewa
"Ta ya zan yi aure ba tare da sanin mahaifiyar da ta haife ni ba?"
Kada ka damu indai sirri ne auren ba buƙatar kowa ta sani, idan auren ya yiwu zaman ya ɗora koda na shekara ɗaya ne zaka ga amfanin abinda na maka. Kuma wannan auren da ka yi tamakar ceton rai ka yi, kaga halin da yarinyar nan ta ke ciki, dan wannan matar Babanta ba imani ne da ita ba, zata iya kashe ta, kaga yadda ta tura ta wai ta je ta yi karuwanci da bata san gidan da mahaifinta ya ke ba har ta zo fa? Da sai ta je ta yi karuwanci ta kawo mata Kuɗi. Dan Allah ka amince da auren nan na kira mana Malam ga mahaifinta ya zama wakilinta kai kuma zan zama wakilinka ga shaidu sai a daura aure."
Kafin Adamsy ya yi magana ne har Abdallah ya fita.
Yana fita kuma sai ya dawo tare da cewa.
"Ka kira manajanka a waya ya zo tare da limamin masallacin kamafaninka."
Ba musu Adamsy ya kira manaja a waya ya sanar da shi ya zo da Mallam Liman.
Daga nan Abdallah ya ce bari na je na siyo dabino da goro.
"To wai duk wannan gaggawa ta me ce ce?"
Dariya Abdallah ya yi tare da cewa
"So na ke yau ɗin nan ka angonce."
Fita ya yi tare murmushi, inda ya samu Mallam Musa ya ce,
"Ina ita yarinyar ta ke?"
"Tana cikin ɗakina ta kwanta."
"To ka kira amininka ka sanar da shi zancen auren nan da yammacin nan za'a ɗaura."
Mallam Musa ya amsa masa da to inda ya masa gidiya, shi kuma ya shiga motarsa ya fita dan siyo dabino da goro.
Gaba ɗaya sun hallara a babban falon Adamsy.
Mallam Musa, amininsa Mallam Kallamu, limamin masallacin kamfanin Adamsy, Abdallah, sai manaja da Direban Adamsy.
Nan aka shaida ɗaurin auren Adamy da Humaira akan sadaki naira dubu ɗari inda Abdallah ya bada kuɗin.
Nan aka yi ta musu addu'a da fatan zaman lafiya.
Da misalin karfe takwas na dare Adamsy ya dawo daga masallaci, yana zaune tunani ya ke wai yau shine da auren wannan yarinyar, ganin abun ya ke kamar almara.
Knowing ƙofar ɗakin aka yi, ya bada izinin shigowa,da sallama ya shigo falon yana riƙe da hannun Humaira ta sunkuyar da kai.
Tana sanye da wata kuɗaɗɗiyar atamfa wadda ta sha wanki har ta fara fita daga kalarta, sai dai ba datti a jikinta, sai wani hijabi wanda shima duk ta koɗe kalar bulue duk saman kanta ta yi fari.
"Wa'alaika salam"
Adamsy ya amsa masa sallamar tare da zuba masu idanunsa.
Humaira ce ta zauna a saman carpet, Mallam Musa da ke tsaye ya ce,
"Barka da dare."
"Ina wuni Bana?"
"Lafiya lau ya ƙoƙari?"
"Alhamdulillah"
"To ga Humaira nan na kawo ta da hannuna, dan Allah ka riƙe mani ita amana kada ka duba rashin gata da bata da shi ko kuma wani abu da iyaye ke yiwa kowace 'ya idan suka aurar da ita, ko wani kayan ɗaki..."
Katse shi ya yi ta hanyar cewa
"Kada ka damu Baba duk ba buƙatar waɗannan, kuma insha Allahu zan riƙe ta da amana, sai dai duk abunda ya same ta kada ka ɗora laifin akaina, ka ɗauki ƙaddara ce haka, domin ni wannan ƙaddara ta zame mani jinin jikina."
Cikin rashin gane inda zancensa ya dosa Mallam Musa ya ce,
"Ƙaddara tana kan kowa, mutum baya gujewa ƙaddararsa."
Jinjina kai Adamsy ya yi inda Mallam Musa ya ce,
"To Humaira duk nasihar da faɗa na riga na maki su, dan haka na kawo ki dakin mijinki, hankalina ya kwanta yanzu."
Juyawa yayi ta fita ya yin da Humaira ke ta sheshshekar kuka.
Ido ya zuba mata yana kallonta ya ma rasa mai zaice mata.
Kamar daga sama ta ji muryarsa ya ce,
"Mene ne sunanki?"
Cikin sheshshekar kuka ta ce,
"Suna na Humaira."
"Kukan ya isa haka nan ki yi shiru."
Shiru ya yi sai ajiyar zuciya da ta ke saukewa lokaci-lokaci.
Tashi ya yi ya nufi kitchen ba jimawa sai ga shi ya dawo ɗauke da plate da naman kaza akai sai youghurt da robar ruwa ya ajiye mata a gabanta.
"Kici abu a cikinki ko?"
Girgiza masa kai ta yi tare da
"Na koshi ."
"Bana son gardama, kici na ce,"
Tunawa ta yi da cewa
Abbanta ya ce kada ta yi masa gardama akan duk abinda ya umarce ta da shi.
Ganin danƙwaleliyar kaza a gabanta, ga youghurt da ruwan gora ya sa ta ta ke mamaki, wai yau ita ce da abun daɗi haka a gabanta, ita da cin naman kaza har ta mance dan ko sallah idan Inna Habi ta yanka kazarta kai da ƙafa ta ke bata.
Hannu ta sa ta fara cin naman kazar, sai ta ji kunya tuna cewa yana kallonta, sai ta daga kai ta kalle shi ta ga idanunsa na kan wayarsa yana daddanawa.
Dan haka sai ta fara turawa sauri-sauri har da kashi ta ke taunawa ga yunwa dama da ya dame ta.
Jin muryarsa ta yi yana cewa
"Wa'alaiki salam Ummana ina wuni."
Daga can ɓangaren ta ce,
"Lafiya lau Babana ya aiki?"
"Alhamdulillah Umma fatan kuna lafiya."
"Alhamdulillah ya zaman kaɗaici?"
Alhamdulillah Umma.
Nam suka dinga taɓa fira kafin daga bisani suka yi sallama ya kashe wayar.
Kallonta ya yi ya ga ta yi yaga ta cinye rabin kazar har ta ture gefe ta sha ruwa.
"Kin ƙoshi ne?"
Kai ta gyaɗa masa alamar eh.
"Okay ki tashi mu shiga cikin ɗaki."
Ba musu ta bi bayansa suke shiga cikin bedroom.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*
*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*
Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.
Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.
Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩
1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more
Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.
*YAR GIDAN TAFIDA*
Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.
*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.
Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page3️⃣0️⃣&3️⃣1️⃣
Ba musu ta bi bayansa suka shiga bedroom.
Bayan sun shiga ciki ne ya kalle ta ya ce,
"Wannan shine ɗakinki, ki shiga ciki ki yi wanka ki kwanta ki huta. Sai da safe."
Yana fita ta zubawa ɗakin idanu tana kallo, lallai an kashe kuɗi a nan, yanzu ita ce a cikin wannan ɗakin ita kaɗai? Gadon ta zubawa idanu tana kallonsa
"Kaga wani gado kamar na sarauta? Har da ƙatuwar dorowar zuba kaya da ƙananan durowoyi guda biyu."
A hankali ta taka zuwa ƙofar toilet ya buɗe ta zuba idanu tana kallo,ta fara magana ita kaɗai.
"Dubi wani banɗaki kamar mutum ya kwanta ya yi barci a ciki."
Haka ta dinga surutu ita kaɗai daga karshe sai ta shiga banɗakin tana tunanin ina zata samu ruwan zafi, saboda jikinta da ke mata ciwo dole ta gasa idan ba haka ba zuwa gobe zai mata tsami ne.
Shawarar zuwa falo ta yi dan ta same shi inda zata samu ruwan zafi.
Koda ta je taga ba kowa a falo, plate da ta rage kaza da robar ruwa suka basa nan, da alamu ya kwashe kayan.
Tana ta ƙarewa falon kallo ganin yadda ya tsaru, babban photonsa da ke manne a bango ta zubawa ido, ita kaɗai ta ke magana.
"Shi wannan mai gidan wani irin mutum ne? Shi dai ga shi kamar wani ba'indiye ko balarabe, amma ya ji Hausa sosai, amma siffarsa sak irin na larabawa, ga hasken fatarsa kamar na su ga gashin kansa da wajensa a kwance luf-luf kamar balarabe, sannan ga laɓɓansa suka sunyi ja kamar ya shafa jan baki, duk yadda ka yi wannan mutumin ba ɗan ƙasarmu bane."
Ƙarar tafiya ta ji sai ta waiga ta ganshi sanye da farin jallabiya.
"Lafiya me kike nema?"
"Ruwan zafi"
Kanta a sunkuye ta yi maganar, dan ya mata kwarjini da yawa ba zata iya kallon cikin idanunsa ba.
"Wane irin ruwan zafi? Me zaki yi da shi?"
"Wanka zanyi."
"To ai kwai ruwan zafi a toilet."
"Ban gani bane."
"Muje na gani."
Tana gaba yana binta a baya har suka shiga cikin bathroom.
Da kansa ya mata bayanin idan ruwan zafi ta ke so ga yadda zata yi, sannan ya nuna mata yadda zata yi amfani da ruwan sanyi.
Daga nan ya fice dan dama wayarsa zai syauka shi ya sa ya zo falon ya ganta.
Koda ya koma ɗakunan komawa ya yi ta haye saman bed ɗinsa ya lalubo lambar Abdallah ya danna masa kira.
Bugu biyu ya ɗauka tare da cewa
"Ango Ango Ango."
Cikin sigar tsokana ya ke magana tare da cewa
"Ina Amaryar ta ke?"
"Tana ɗakinta"
"Kai kana ina ne?"
"Ina ɗakina"
"To me ya sa ba zata zo nan ku kwana tare ba, ko kuma kai ka bita can? Meye amfanin auren ni gani ga Madam ɗina a gefe na."
Ajiyar zuciya Adamsy ya sauke tare da cewa
"Ina jin tsoron abinda zai je ya dawo, dangane da abubuwan da suka faru a baya. Yanzu mata guda shida kenan na aura babu wacce na zauna na mintuna biyar da ita ƙeɓance, daga wacce ta haukace sai wacce ta makance, sai wacce ta tubure ta ƙi ayi auren ga kuma wacce ta rasa rayuwarta gaba ɗaya. Hakan ya sa na yanke ƙauna daga auren ko wace irin mace a rayuwata, yanzu ga shi an bani auren wannan yarinyar bansan ita kuma wace masifar ce zata afka mata ba.
Shiru ya yi yana tuna kalaman maihaifiyar Hauwa'u wacce ta haukace ranar ɗaurin aurensu.
A hankali ya fara tuna zancenta inda take cewa
'Shikenan Adamsy dama abinda ka ke so kenan, hankalinka ya kwanta burinka ya cika,wai me ya sa kake wahalar a rayuwar bayin Allah? Me suka yi maka? Tukunna ma kai wani irin mutum ne haka da duk wacce ta aure ka sai wani masifa ya faɗa mata, kai wani irin mutum ne mai bakin ƙaddara,har sau nawa zaka cigaba da saka rayuwar bayin Allah cikin hatsari me ye ribarka akan hakan? Kayi ɗaya biyu uku kaga yadda rayuwarsu suka kare me zaisa kai ba zaka haƙura ba saboda son zuciyarka,shine ka cigaba da kafa rayuwar wasu...'
Abdallah ne ya katse masa tuni ni da cewa
"Na ji la yi shiru."
"Wani abu na tuna."
"Okay"
"Ina madam ta ke ne?"
"Tana tare da ni."
"Gobe insha Allahu zanzo na bata kudi ta haɗawa Humaira kaya da akwati."
"Okya to Allah ya kaimu sai ka zo."
Daga nan suka ɗan taɓa fira daga bisani suka yi sallama ya katse kiran.
Ta daɗe barci bai ɗauke ta ba tana tunanin halin rayuwa.
Shima a bangaren nasa yana tuna abubuwan da suka faru da matayen da ya aura a baya, sannan kuma yanzu ga wata ta bakwai na su ko me zai faru da ita bai sani ba.
Sai da dare ya raba sannan dukkaninsu suka yi barci kowa da abinda ke ransa.
Kasancewar ta saba da kullum tana cikin barci ne sai Inna Habi ta shigo ta watsa mata ruwan sanyi a jikinta, wata rana kuma har ta haɗa mata da duka.
Sai ta yi mafarkin wai tana barci a gida sai Inna Habi ta watsa mata ruwa kamar yadda ta saba kuma sai ta haɗa mata da suka .
Hakan ya sa ta farka daga mafarki a firgice tana ihu, dai-dai lokacin da Adamsy ya fito daga ɗakinsa zai je masallaci.
Jin ihunta yasa ya shiga ɗakin cikin tashin hankali, kwance ya same ta sai kuka ta ke tana cewa
"Inna Habi dan Allah ki yi haƙuri wayyo Allah."
Bubbuga kafaɗarta yayi tare da cewa
"Ke Humaira laflya ?"
Sai a lokacin ta buɗe ido ta tuna cewa mafarki ta ke.
"Me ke damunki?"
Girgiza masa kai ta yi tare da cewa
"Mafarki na yi"
"To kiyi addu'a ki tashi kiyi sallah."
To ta amsa masa sannan ya fita zuwa masallaci.
Shiga bathroom ta yi tare da sake gasa jikinta da ruwan zafi, kuma haka ta ji dadin jikinta, sosai da sosai bata jin tsamin jikin yanzu.
Kayan da ta cire wanda ta zo gidan da shi da hijabi shi ta maimaita sawa.
Bayan ta idar da sallar ne ta yi azkar sai ta kwanta a saman sallaya. Nan da nan barci ya ɗauke ta.
Da misalin karfe goma na safe ne ya shigo ɗakin ya same ta kwance a saman sallaya tana barci, kiran sunanta ya yi tare da cewa
"Humiara har yanzu barci kike yi ne?"
Kai ta jinjina masa tare da cewa
"Ina kwana"
"Laflya lau kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah"
"Ki tashi ki je kiyi Breakfast rana ta yi."
Tashi ta yi tare da bin bayansa, kai tsaye dinning room ya nufa, ta bi bayansa.
"Kiyi breafast ni zan fita zuwa gidan abokina."
"To ni dawa zan zauna a gidan?"
"Ke kaiɗai mana."
Tura baki tayi tare da cewa
"Wallahi tsoro na ke ji gidan nan ya mani girma ni kaɗai."
"Ba abinda zai same ki a Gidan nan, ki kwantar da hankali bazan daɗe ba, ga T.V nan kiyi kallo idan kina buƙatar cin wani abu akwai snacks da cake a fridge har youghurt da ice cream ma koda kin ji yunwa zaki iya sha kafin a kawo abinci."
Daga nan ya fita sai da ya gaida Mallam Musa sannan ya shiga motarsa Direbansa ya ja suka wuce.
Horn Direbansa ya yi a kofar gidan abokinsa Abdallah.
Mai gadin gidan ne ya buɗe masa gate ɗin gidan ya shiga.
Direbansa ya jira shi a mota shi kuma ya nufi cikin gidan, knocking ya yi Maryam ta buɗe masa .
"Ango kasha ƙamshi"
"Sannu da zuw"
Ta faɗa cikin fara'a tana riƙe da yarinyar da ta yaye kwanan nan.
Ƙarɓar yarinyar ya yi dama shi mai son yara ne.
Bayan ya zauna a falo ne Maryam ta shiga ta sanar da shi zuwan Adamsy, da fara'arsa ya na cewa
"Lallai shi ya sa ya na ga garin ya mana hadari ashe ruwa za'ayi da ƙanƙara."
Mika masa hannu yayi suka yi musabaha inda Adamsy ke cewa
"Ina fatan ka sanar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 19