fara tafiya ya samu gefen hanya yayi parking inda ya lalubo number Fauziyya ya danna mata kira, bugu biyu ta ɗaga tare da cewa
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaiki salam"
"Ina ta kiran wayarka baka ɗagawa fatan dai lafiya?"
"Lafiya lau ina gaban Madam ne shiyasa ban ɗaya kiran naki ba."
Shiru tayi tana nazari kafin ta ce
"Wace madam kenan?"
"Mata ta mana"
"Oh dama dan kana tare da ita ne baka ɗauki waya ta ba? Ko kuma wayar kowa ne baka ɗauka idan kana tare da ita?"
"Naki ne dai kawai bana ɗauka a gabanta, dan gudun ɓaci ranta."
Cikin baƙin ciki Fauziyya ta katse kiran wayar, ajiye wayar yayi tare da tada motar ya ɗauki ga hanyar gidansu Fauziyya.
Ƙofar gidansu yayi parking tare da ɗaukar wayar ya sake kiranta, sai da ta kira sau uku kafin ta ɗauka tare da cewa
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaiki salam"
"Ka iso ne?"
"Eh ina ƙofar gidanku yanzu haka."
"Okay gani nan fitowa"
Daga nan ta katse kiran wayar tare da ɗaukar hijabinta ta saka ta ɗauki hand bag ɗinta ta fito.
Mama ta samu a tsakar gida tana zaune a kan tabarma tana sauraren rediyo, durƙusawa tayi a gabanta tare da cewa
"Mama sai mun dawo"
Jinjina kai Maman tayi tare da cewa
"To adawo lafiya, dan Allah Fauziyya kada ki daɗe ku dawo da wuri kafa kiyi ta zama can "
To ta amsa mata da shi sannan ta fito zuwa waje, a motarsa ta same shi zaune yana jiranta, ta fito, buɗe murfin gaban motar tayi tare da yin sallama ta shiga. amsar mata sallamar yayi tare da cewa
"Gimbiya kin fito?'
Taɓe baki tayi tare da cewa
"Gimbiya ba ka baro ta a gida ba?"
"Eh kema Gimbiya ce"
Hmmm, Adamsy kenan, wallahi da nasan kai mijin ta ce ne da ban amince da kai ba, da nadan cewa tsoron matarka kake da ban amince da aurenka ba, ko yanzu ban makara ba, dan kan bazan iya auren mijin da matarsa tafi ƙarfinsa ba."
Dariya ya yi ya ce,
"Wai duk wannan maganar ta meye?"
"Na kira ka a waya baka ɗaya daga ba saboda kana gaban matarka, wato ba zaka ɗauki waya a gabanta ba saboda kai mijin ta ce ne? To gaskiya banzan iya ba dan kada na aure ja ace kana tsoron matarka yaushe zaka ita adalci a tsakanin mu har ka sauke haƙƙoƙina dake kamala?"
"Fauziyya kenan ni ba irin wannan tsoron nake ba, ina dai girmama mata ta dan gani nake idan na yi waya a gabanta kamar cin fuska ne, nasan kuma hakan bazai mata daɗi ba shiyasa ina girmama mata ta sosai Kuma nu ba irin mazan nan bane wadanda suke juyawa mace baya ko su lallatata a wajen Amaryar bane , ko ke na aura abinda zan maki kenan."
Murmushi tayi tare da cewa
"Na fahimce ka"
Shima murmushi yayi yana tada motar suka bar kofar gidan kai tsaye suka nufi gidan Ummansa.
Da sallama suka shiga Falon Umma na zaune akan doguwar kujera tana kallon T.V inda ta kamo tashar Africa t.v 3 inda suka saka wa'azi Sheikh Jabir Sani mai hula.
Sallamar su fa ta ji yasa ta kalli bakin ƙofar shigowa ta ce,
"Wa'alaikumus salam, barka da zuwa sannunku"
Ƙarasawa sukayi suka zauna a saman center carpet, cikin girmamawa Fauziyya ta ce,
"Ina wuni Umma?"
"Lafiya lau 'yata kuna lafiya?"
"Lafiya lau Umma"
"Ya su Maman naku duk suna lafiya?"
"Duk lafiya Umma"
"Masha Allahu"
Adamsy ma ya gaishe ta ta ta amsa masa cikin jin daɗin da ya kasa ɓoyowa a zuciyarta, tare da tambayarsa Amina ya amsa da tana lafiya. Mai aikinta Saude ta ƙwalawa kira bayan ta zo ta umarce ta da ta kawo masu abinda sha.
Nan Saude ta cika gaban Fauziyya da kayan ciye-ciye da sha, ita dai Fauziyya daƙyar ta iya shan ruwa, nan dai Umma ta dinga janta da fira daga eh sai a'a take amsawa har suka tashi tafiya Umma ta haɗa mata kayan turarruka tabawa Adamsy ta ce,
"Babana ga wannan ka bata ko?"
"To Umma tana godiya."
Lokacin ma duk Fauziyya ta fita tana jiran fitowarsa, bayan ya fito ne suka shiga mota ya tada motar tare da yin horn mai gadin ne ya buɗe masu ƙafa suka fita.
Sai da ya biya wani super market ne yayi mata siyayyan kayayyakin tun daga kan kayan ciye ciye da maƙulashe har har ya zuwa kayan kwalliya duk ya cida mata.
A mota ya same ta tunda ya ce, ta zo su shiga ta ƙi dan haka ya shiga yayi mata siyayyan ya dawo. Manyan ledoji ne guda biyu ya zuba su a bayan motar sannan ya shiga ya tada motar dai da suka fara tafiya ne ya kalle ta ya ce,
"Me yasa baki shiga ba ko akwai abinda zaki so a ciki?"
Kai ta girgiza tare da cewa
"Kada ka wahalar da kanka na bana buƙatar komai."
Daga nan bata sake magana ba ganin tana kallon lokaci yasa ya ce,
"Wai saurin me kike yi?"
"Lokacin islamiyya nake dubawa dan daura mintuna goma, kuma bana son na makara."
Daga nan bata sake magana ba har suka ƙara da ƙofar gidansu. Ganin tana ƙoƙarin fita ne yasa ya ce,
"To ai ga saƙon Umma baki karɓa ba."
Sunkuyar da kanta tayi, ya ɗauko saƙon Umma da kuma ɗaya daga cikin ledoji guda biyu da ya siyo daga super market ya saka saka kuɗi 100k ya saka mata a cikin ledan da yayi mata super market.miƙa mata yayi tare da cewa
"Gashi."
ganin ƙarin ledan yasa ya ce,
Wannan kayan sunyi yawa ai."
"To ki rabar idan sun maki yawa."
Godiya yayi tare da karɓar ledojin ya fita, shi kuma ya ja motar yabar wajen.
Kai tsaye gidansa ya koma inda ya kaiwa Amina ɗayan ledan da ya siyo daga super market.
********** **********
Kwanci tashi asaran mai rai yau saura kwanaki bakwai auren Adamsy da Fauziyya, yayin da kowane ango da Amarya zaku ga yana zumuɗi da farin ciki amma a waurin Adamsy da Fayziy akasin haka ne, domin kuwa Fauziyya bata ƙaunar ganin Adamsy yanzu ta tsane sa sosai ko kiran sunansa ta ji anyi sai gabanta ya faɗi. Ita kanta bata san dalilin hakan ba, dan a iya saninta tana matuƙar kaunar Adamsy a cikin zuciyarta, bata son ɓaci ransa kullum bata da wani buri da ya wuce ta mallakar shi a matsayin abokin rayuwarta. Amma yanzu kam ya zamo tamkar mujiya a wurinta, ko ɗauka wayarsa m bata yi yayi ta kira bata ɗagawa ko text message yayi mata bata maida masa reply ƙarshe ma sai tayi blocking nasa.
Da abun ya ishe sa ne ana saura kwana uku ɗaurin auren ya je ya sami Baban Fauziyya bayan sallar Isha'i. Bayan sun gaisa ne Baban Fauziyya ya kalli Adamsy ya ce,
"Ya shirye-shirye?"
"Alhamdulillah, Baba"
Shiru ne ya biyo baya inda Baban Fauziyya ya ce,
"Lafiya dai ko akwai mata matsala ne?"
"Eh Baba akwai wata 'yat matsala."
"Subhanallahi ina jinka"
"Baba yanzu gaba ɗaya na kasa gane kan Fauziyya yanzu a ƙalla mun kai sati uku bamu yi maganar arziki da ita ba, gaba ɗaya ta daina ɗaukar waya ta ko message na tura mata ba amsa, ƙarshe dai blocking ɗina tayi, ko na zo nan na aiko a nan nazo bata fitowa haka zan gaji da zaman jiranta na haƙura na tafi. Har abokina da ke unguwar nan Sadik ya zo ya same ta sai ta ke sanar da shi cewa wai yanzun bata so na ta canza ra'ayinta."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu haka Fauziyya ta yi haka da kanta?"
Jinjina kai Adamsy yayi tare da cewa
"Ƙwarai kuwa, yanzu haka na janye zancen aurenta dan da muguwar rawa gara ƙin takawa."
Shiru Baban Fauziyya yayi tare da cewa
"Ka bani kwana biyu zan binciki lamarin nasan inda matsalar take."
Godiya Adamsy yayi mata tare da sallama ya tafi.
Koda Baban Fauziyya ya koma gida ya tambaye ta sai ta nuna ita bata sonsa, dan haka Baabanta da Mamanta sunyi masa faɗa sosai kamar ta haƙura amma a zuciyarta ba haka ba.
*KADUNA*
Wasu matasan 'yan mata waɗanda ba zasu wuce shekaru goma sha biyar, ɗaya tana wanke kwanika ɗaya kuma tana sanye da kayan makarantar boko tana shan koko. Wacce take sanye da kayan makarantar bokon ce ta kalli mai wanke kwanika ta ce,
"Ke Humaira ki yi sauri ki ƙarasa wanke-wanke nan kizo na aike ki?"
Maihaifinsu da ke fitowa daga ɗakinsa ne ya kalli wacce ke sanye da kayan makarnata ya ce,
"Salma me yasa kike wa yarinyar nan haka ne? Tana aiki kina mata ihu ta gama ta zo ki aike ta? Ke aikin me kike yi da ba zaki tafi aiken da kanki ba?"
Tura baki tayi tare da cewa
"Nifa makaranta zani Baba."
"To ita ba zata tafi makarantar bame? "
Kallon Humaira yayi tare da cewa
"Me yasa ke baki shirya zuwa makarantar ba?"
"Baba Inna ce ta hana ni zuwa makaranta wai ta cire ki daga makarantar."
Kallon mamaki yake mata tare da cewa
"Akan me ta cire ki?"
"Wai idan na tafi makaranta ba wacce zata dinga mata aiyukan gidan da kuma aike da ɗibar ruwa."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,"
Ya juya ya kalli ƙoafar ɗakin Inna tare da cewa
"Habi! Habi!! Habi!!!"
Inna da ke cikin ɗaki tana jin duk maganar da suke ne ta fito tare da cewa
"Lafiya Mallam kake ƙwala mani kira da sassafe haka?"
"Akan wane dalili ne yasa zaki hana Humaira zuwa makaranta? Bayan ga 'yarki nan baki hana ta ba sai ita?"
Cikin nuna isa da gadara ta ce,
"Saboda ni ba baiwarta bace kuma ba baiwar uwarta bace, idan ta tafi makaranta nine zan dinga aiyukan gidan ko yaya?"
Girgiza kai tayi tare da cewa
"Bazai yiwu ba wallahi, lokacin da uwarta ke da rai duk ranar girkin uwarta uwarta ce take aiyukan gidan sai idan 'yarta ta taya ta nima duk ranar girkina ni nake aiyukan gidan sai idan 'ya ta ce ta taya ni, don haka bazaiyiwu ace uwarta ta mutu ba sannan ni na dinga mata aiyukan gidan, bazaiyiwu ba."
"Yanzu Habi kina kishi da uwar yarinyar nan, sannan bayan ranta ma sai kinyi kishi da 'yar da ta haifa."
Taɓe baki tayi tare da cewa
"Dama na sani haka abin yake, lokacin da uwar ke da rai ita ce matar so yanzu bata da rai 'yar ta kuma ita ce 'yar so."
Kallon Humaira da ke zubda ƙwalla tayi tare da cewa
"Ki sani na kashe katatunki matukar kika fita a gidan nan da sunan zuwa makaranta kika dawo sai na kusan kashe ki, sannan kuma wanke-wanke da shara da wankin kayana da na Salma suna kanki, ɗibar ruwa da uku kece dakan garin kunu ko na tura duk kece ki rubuta ki ajiye karatu kam ba zaki same shi ba."
Kuka Humaira ta fashe da shi na baƙin ciki, yayin da kuma Salma ke farin ciki da hukuncin da uwarta ta yanke, dan dama Humaira tafi ta ƙoƙarin kowane lokaci ita ke zuwa na ɗaya a makaranta hakan na ƙona mata rai,dan ita ce kusan ta ƙarshe.
Cikin ɓacin rai Mallam Musa ya kalli Habi ya ce,
"Baki isa ba ni zan yanke hukunci da gida na ba ke ba, dan ni ne mai gidan."
Dariya ta sheke da shi
"Mallam Musa da ne kake mai gida lokacin da kake da abunyi ba yanzun da baka da aikin yi ko sana'ar yi ba, tunda ni nake san'a nake ɗaukar nauyin gidan nan kuwa ai nine mai gidan ba kowa ba, dan haka talla ma zata fara zuwa."
Da sauri ya kalle ta tare da cewa
"Tallah?"
Jinjina kai tayi cikin isa ta ce,
"Cif".
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗaya ta ji kunya, yaune za'ayi ɗaurin auren Adamsy da Fauziyya. Jama'a sun taru a ƙofar gidansu Fauziyya dangin Amarya da dangin Ango da 'yan uwa da abokan arziki kowa ya hallara ango da abokansa ma duk suna nan, an fara gabatar da ɗaurin aure ga waliyin ango da na amarya inda waliyin ango ya fara magana ya ke cewa waliyin amarya.
"Ni Alhaji Kabiru ina nemawa ɗana Adam auren Fau..."
"Ku dakatar da wannan ɗaurin auren!"
Muryar mace suka ji kowa ya fara kalle-kalle dan sanin wace ce take maganar, me zai kawo mace wajen ɗaurin aure? Nan fa aka fara kallon kallo.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don neman ƙarin bayani*
09065327995
Love you oll😍😘
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANRWA*
Wannan ƙirƙirerren labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba. Arashi ne mai kashe auren wawa.
Page 5 & 6
Muryar mace suka ji kowa ya fara kalle-kalle dan sanin wace ce take maganar, me zai kawo mace wajen ɗaurin aure? Nan aka fara kallon-kallo.
Fauziyya ce tsaye a wajen hajaran majaran tamkar wata zautacciya, zubewa tayi ta durƙusa akan gwuiwar ƙafarta tare da fashewa da wani matsancin kuka, kallon maihaifinsu tayi tare da cewa
"Dan Allah kada a ɗaura auren nan, wallahi bana son auren nan idan aka ɗaura shi zan iya mutuwa."
Ta ƙarasa maganar tana mai fashewa da wani sabon kuka,miƙewa tsaye tayi zata nufo inda mahaifinta yake zaune, ganin haka yasa ya mike tare da nufarta yana ƙarasawa gabanta ya wanke ta da tagwayen maruka akan fusakarta, sake ɗaga hannu yayi da niyyar kai mata mari sai Adamsy yayi saurin shiga a tsakaninsu tare da cewa
"Dan Allah Baba kayi haƙuri, a dakatar da wannan ɗaurin auren ni na janye Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare mu."
Cikin tsananin ɓacin rai mahaifinta ya ce,
"Fauziyya irin tarbiyyar da na baki kenan? Ni zaki kunyata a gaban jama'ar da na tara?"
Cikin kuka ta ce,
"Dan Allah Baba kayi haƙuri wallahi zauciya ta bata sonsa."
"Da can baki san da baki sonsa ba lokacin da kika kawo shi a matsayin mijin da zaki aura? To baki isa ba ko kukan jini zakiyi ke ko mutuwa zaki yi sai dai ki mutu amma wannan auren ba makawa sai an ɗaura shi."
"Kayi haƙuri Baba ka gafarce ni amma tunda har ankai ga haka, ta fito da kanta ta ce bata so na bata son auren nan to na haƙura da Fauziyya har abada."
Baba ya bar wajen cikin tsananin ɓacin rai yana huci. Adamsy kallon Fauziyya yayi tare da cewa.
"Me yasa baki so na?" Nayi maku laifi ne? Da can ne baki so na ko sai yanzu?"
"Dan Allah kayi haƙuri wallahi bana son aurenka ka taimaka kada ka bari Baba na ya haɗa wannan auren ka tausayawa rayuwa ta."
Murmushi wanda yafi kuka ciwo yayi tare da cewa
"Baza'a ɗaura ba tunda baki son auren nan, nima bazan taɓa auren macen da bata so na ba, tashi ki tafi gida."
Jikinta na rawa tayi masa godiya ta bar wajen, komawa yayi wajen nahaifin Fauziyya tare da basa hakuri yana tausansa, dan ganin cewa ya samu nutsuwa, yayin da shima kansa Adamsy ƙarfin hali kawai yake yi, zuciyarsa tafarfasa take masa da zugi."
Abokansa ne suka ja shi suka nufi mota, Sadik na mazaunin direba yayin da shi kuma Adamsy yana zaune a gefensa. Sai abokansa su uku da ke a bayan motar, Babawo Aminu sai Umar .
Lokacin da suka hau titi ne Salisu ya juya ya kalli Adamsy ya ce,
"Abokina ni fa wannan al'amari ya fara bani tsoro? Sai huɗu fa kenan, kana yinƙurin aure ko bayan auren sai zama bazai yiwu ba. Da farko dai ya auri Atika itama hala ranar ɗaurin aure aka fasa, sannan ka fara neman Basma ita kuma bayan an ɗaura auren ta ƙi yarda ta shiga gidan auren ma, duk yadda akayi ta ce ba zata yarda ta zauna da kai ba aka dinga fama ƙarshe dai haka aka hakura ka sake ta. Sannan ga Husnah bayan ankaita gidanka zama yaƙi daɗi sai gudunka take, itama ka rabu da ita yanzu ga Fauziyya ranar ɗaurin aure abun baiyuwu ba, yakamata fa ka duba magana ta mata har huɗu kuna soyayya da su da anzo kan aure sai abu ya lalace gaskiya ba banza ba."
Babawo ya ɗaura da cewa
"Nifa ina ganin kamar aljanna ce ta aure shi, shiyasa take raba shi da duk wata macen da ya so ya aura."
Girgiza kai Umar yayi tare da cewa
"Bana tunanin cewa aljannah ce ta aure shi, dan idan aljana ce ta aure shi ne yasa tabarshi tare da Amina? Ai da har da Amina ma sai ta raba su kamar yadda take raba sauran matansa."
"To ka sani ko Aminar tafi ƙarfin aljanarce shiyasa ta barta? Dan ba yadda zata yi da ita."
Haka dai suka dinga magana kowa na tofa albarkacin bakinsa, shi dai Adamsy bai ce komai ba sune suke ta zantuttukansu kowa da abinda yake cewa.
Har suka isa ƙofar gidansa baice da su komai ba, gaba ɗaya ji yake duniyar ta masa zafi. Kallon Sadik yayi tare da cewa
"Ba sai ka shiga cikin ba, ka tsayar da motar anan waje, zan shiga ka tafi da motar zuwa gobe ko anjima idan ka samu lokaci sai ka dawo mani da motar."
Bai jira cewarsu ba ya saka kai ya shiga cikin gidan.
Da sallama ya shiga cikin gidan a falo ya tarar da Amina da ƙawayenta sai kuma 'yan uwanta fa suka zo bikin, amsa masa sallamar suka yi inda ƙanwar Amina mai suna Zahriyya ta kalle shi tare da cewa
"Ango kasha ƙamshi."
Sauran jama'ar da ke falin ne suka jiyo suna kallonsa,cikin mamaki suka ce
"Angon ne ya dawo gida da wuri haka? Ba zaka bari har dare yayi mu watse ba kafin mu watse ba."
Murmushn ƙarfin hali kawai yayi tare da wucewa zuwa ɗakinsa, buɗewa yayi ya shige.
Babbar rigarsa ya cire bayan ya cire hularsa, sannan ya kwance agogonsa, rigarsa ya cire duk ji yake yi wani zafi na damunsa duk da sanyin AC dake ɗauka a ɗakin. Ƙara gudun AC yayi sannan ya haye saman gadon ya kwanta tare da jan bargo, wani zazzaɓi ne yaji yana son kama shi ya rasa me ke masa daɗi.
A hankali ya dinga tuna abubuwan da suka faru da shi ya ce,
"Mata huɗu da farko zasu nuna mani so da ƙauna amma daga baya sai sai su zame kuma sai anzo dai-dai gaɓar aure lokacin dukansu zasu zame su guje sa, cikin guda haɗun biyu ma anɗaura aure biyu gabanin ɗaurin auren ne suke fasawa.
"Shin me mene ne matsala ta?" Meye aibu na da can basu lura da cewa ina da wani abu ne ko kuma rashin dacewa da su sai anzo gaɓar aure? Amina ke kaɗai ce kika zauna da ni da badon lalurarki ba da ba abinda zaisa na nemi wata 'ya mace, son 'ya'ya ne ya kaini ga wannan halin, kwaɗayin yara ne fa yasa ni haka.
Anyi ta ɗaya anyi ta biyu, anyi ta uku, anyi ta huɗu to anyi ta ƙarshe babu wata 'ya mace da zan ƙara gani na tare ta da sunan ina sonta insha Allahu."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ɗuara da cewa
."Na haƙura da kowace 'ya mace Allah ya bani ikon cinye wannan jarabawar."
Kamar daga sama yaji ance
"Ameen."
Kasancewar yasan ita ce kaɗai zata shigo masa ɗaki kuma ya ji muryarta duk da baisan lokacin da ta shigo ba. Ɗaya kai yayi ya ɗan kalle ta sannan ya ɗauke idanunsa daga gare ta a hankali ya ce,
"Dan Allahu ki fita Ina son kasancewa ni kaɗai "
Ta yaya zan fita kuma naje ina? Bayan naga ka fita cikin farin ciki da walwala yanzu kuma ka dawo cikin damuwa, yau ranar farin ciki ne a gare ka ranar murna to me yasa kake cikin ƙunci? Sannan ka ce wai na fita na barka ta ina zan fara wallahi zuciya ta ba zata taɓa samun nutsuwa ba sai naji abinda ke samun mijina."
Ta ƙarasa maganar tana kallon fuskarsa tare da zama bakin gadon dai-dai saitin filon da ya ɗaura kansa akai.
Gashin kansa take shafawa a hankali cikin sigar rarrashi.
"Bana sonka cikin damuwa nafi son kullun naganka cikin farin ciki da walwala, anya ma ka iya zuwa wajen ɗaurin auten? Ko kuma jikinka ne ya hana ka zuwa wajen yasa ka dawo gida?"
Murmushin takaici yayi tare da cewa
"Wani ɗaurin aure kuma Amina? Ai ba wannan zancen kuma."
"Ban gane me kake nufi ba."
"Amina aure na da Fauziyya ya ruguje."
Kallon rashin fahimta tayi masa tare da cewa
"Ban gane me kake nufi ba, ko kana nufin ka ce mani wai an fasa auren ne ko kuma ya?"
Kai kawai ya jinjina ba tare da yayi magana ba, gane amsar da ya bata yasa ta ce,
'innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, me ke faruwa ne?"
Ita da kanta ta nufi wajen ɗaurin auren a bainar nasi, ta ce bata son aurren idan kuma aka ɗauka to zata kashe kanta."
"Subhanallahi wace irin masifa ne wannan, amma ta yiwu ko ja ɓata mata rai ne yasa ta yi haka da ba'a dakatar da ɗaurin auren ba an barta kawai an ɗuara idan yaso daga baya zata saki jinkinta ta haƙura ta fauwalawa Allah komai."
Girgiza kai yayi tare da cewa
"Ba zata haƙura ba ai ba tun yau bane ta fara nuna bata so, har na janye mahaifinta ne ya dage yasa na haƙura da zancen, dai ga shi kankat kenan har wajen ɗaurin aure taje."
Jinjina kai Amina tayi tare da cewa
"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare ku, Allah ya baka wacce tafi ta ."
Saurin girgiza kai yayi tare da cewa
"Gara kawai na haƙura mata huɗu kenan, anyi ɗaya biyu uku anyi huɗu to yakamata na fauwalawa Allah lamuran na."
Shiru tayi sannan ta ɗora da cewa
"Zaka iya haƙura da son yara da kake yi? Nima kaina ina masifar ganin kayi aure ta haifa mani yara dan 'ya'yanka ai nima 'ya'ya na ne."
Haka ta cigaba da yi masa malamai masu daɗi da kwnatar masa da hankalin sannan ta ja masa kofa ta fita ganin zaiyi barci.
Bayan sallar isha'i 'yan biki sun watse kowa ta tafi gidanta, sau dai wasu dangin da suka zo bikin daga wasu garuruwa. Baban Fauziyya ne zaune a tabarma a tsakar gidan sai Mamanta dake zaune a gefensa.
Abun duniya duk yabi ya ishe su Fauziyya ta gama kunyata su a idon mutane ya rasa wane irin hukunci ma zai ɗauka aknata ne.
Isah yayan Fauziyya ne yayi sallama ya shigo gidan, amsa masa suka yi ya ƙarso yazo gabansu ya durƙusa cikin girmamawa ya gida iyayen nasa.
"Baba dan Allah ka daina wannan tunanin haka nan, bana son ganinku cikin damuwa wallahi ko kaɗan."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Isah ba dole kaga na shiga cikin damuwa ba, ka duba abinda yarinyar nan tayi fa ɗazu."
Jinjina kai kawai Idan yayi tare da miƙewa tsaye ya nufi ɗakin Fauziyya.
Tana zaune a bakin katifarta sai taga yaynta Isah ya shigo ɗakin, ganin yanayin fuskarsa yasa ta ji gabata ya faɗi, kafin ta ankare ai tuni ya zare belt ɗin wandonsa ya fara jibgarta kamar Allah ne ya aiko shi.ihu take tana ihun neman taimako, kasancewar duk kama'ar kowa ne ɗaki Mamansu da Babansa ne kawai a waje, koda suka ji ihun da take basu damu ba.
Jama'ar da ke ɗaki 'yan biki da suka zo daga wasu garuruwa duka ji ihunta suka fito a guje daƙyar suka iya ƙwatarta daga hannun Isah, suka dinga masa faɗa bai kula su ba ya fita yana huci.
*KADUNA*
Kwance take tana barci da misalin ƙarfe huɗu na asuba, Habi ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ganin tana barci yasa ta komawa ta nufi randar tukunyar ƙasa, ta ɗebe ruwa rabin bokita tana zuwa ta kwarawa Humaira a jiki,a firgice ta farka tare da sakin nannauyen ajiyar zuciya.
"Tashi ƙarfe huɗu na asuba tayi kina kwance kina barci bayan kinsan aiyukan da ke kanki."
Daga nan ta fita Haumaira ta kalli yadda jikinta da kanta suka juƙe sharkaf ga shi lokacin sanyi ne ruwan kamar na fridge, kuka ta fashe da shi ta haɗa kanta da guiwar ƙafarta.
Dawowa Babu tayi tare da cewa
"Uwar ne kika tsaya yi da baki fito ba?"
Tashi tayi ta nufi jakar kayanta da niyyar canza wasu kayan, tsawar da Habi ta daka mata ne yasa ta dakata tare da cewa
"Inna sanyi nake ji zan canza wasu kayan ne."
"Ba zaki canza ba haka zaki barshi a jikinki har sai sun bushe, fita dalla kije kiyi mani aikin da kikasan yana kanki."
Daga nan ta fito ta barta nan tsaye kayan jikinta na tsiyayar da ruwa.
Haka ta fito kamar kazar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 19