Share this page
sanin gaibu sai Allah ba inda zan tafi da zaku je ku raba ni da imanina." "Daga taimako?" "Bana buƙatar taimakon ballantana..." Baba Ashiru ne ya katse sa ta hanyar cewa "Mai sunan Babana nima fa lamarin nan naka ya bani tsoro, da zaka bi ta shawara ta da ka bishi kun tafi." "Baba na fawwalawa wa Allah lamarina , duk abinda ya faru da ni haka Allah yaso da ni." "Shikenan ai tunda ka dage kuma na lura kai da Umman taka aƙidarku iri ɗaya ne Allah yayi mana magani ya iya mana kada ya barmu da iyawarmu." Umma ne da Baba Ashiru suka fita suka bar Adamsy tare da Sadik suma tattunawa. Bayan Baba Ashiru ya tafi gidansa ne Umma ta nemi Direbanta da ya kaita gidan Admsy. Bayan Direbanta ya yi parking ne ta fito tare da bashi umarnin ya jira ta ta fito. Amina ita da wasu ƙawayenta biyu ne a falo, suka gaida Umma. "Ina wuni Umma?" "Lafiya lau ya kuke?" Suka amsa mata da lafiya lau. Kallon Amina tayi tare da cewa "Magana zamu yi da ke mu shiga ciki sauri nake yi. Miƙewa Amina tayi ta bi bayan Umma zuwa ɗakinta. Kallonta Umma tayi tare da cewa "Ki saurare ni da kyau dan duk abinda nake yi dan ke nake yi, kowa rai yama daɗi bai kai mai shi ba." Jinjina kai Amina tayi tare da cewa "Ina saurarenki Umma." "Adamsy zai bar garin nan da zama zai koma Kaduna zai cigaba da kula da kamfanin mahaifinsa da ke can garin Kaduna. Kuma komawarsu Kaduna ba karamar barazana ba ce a gare mu." Ta ina hakan zai zama barazana a gare mu Umma? Mata nawa ne mazajensu suna can wani gari suna aiki amma matayensu basa tare da su, sai dai idan sun samu sarari su zo suga iyalinsu su koma wajen aikinsu, ni a gani na wannan ba matsala bace." Tsawa Umma ta daka mata tare da cewa. "Dalla rufe mani baki sha sha sha kawai da bata san ciwon kanta ba, to bari kiji matuƙar Adamsy ya auri wata matar to daga ni har ke zamu tashi a tutan babu, kuma bazan taɓa bari hakan ta faru ba." Kallon mamaki Amina ta dinga yi wa Umma sannan ta ɗora da cewa "Umma kada dai a ce duk abinda ke faruwa da mijina ke ce sila? Kada a ce ke ce kike raba shi da matan da yake shirin aure da waɗanda yake aure?" Jinjina kai Umma tayi tare da cewa "Ƙwarai kuwa ni ce nake shirya komai." "Ta ya ya hakan ta faru ne ye dalilinki?" Wani shu'umin murmushi Umma tayi tare da cewa. "Ta yadda akayi hakan ta faru ba yanzu zan faɗa maki ba sai dai zan faɗa maki dalilina yanzu." Kamar yadda kika sani dai suna na Hanne na taso da son abun duniya da kwaɗayin kuɗi. Sau uku ina aure yana mutuwa kasancewa ta bani da haƙuri musamman da talauci bani da haƙurin talauci dan haka idan naga bana samun inda zan huta sai na kashe auren. Wata rana ina zawarci bayan na haife ki da kwana arba'in na fita ziyara gidan ƙawata kasancewar da cikinki na fito gidan tsohon mijina to da na yi kwana arba'in sai na je ziyarar akan hanya ta dawowa gida hadari mai ƙarfi ya taso lokaci guda, sauri-sauri gudu-gudu na ke yi a kan hanya sai ga ruwa ya ɓalle mai karfi ina cikin wannan halin sai na ga wata tsadaddiyar mota ta tsaya a gaba ba, kasa motsawa na yi illa kawai na zubawa mamallakin motar idanu domin kuwa idanunsa kasa daina kallonsa yayi sai na mance da ruwan da ke duka na sai da na ji muryarsa yana cewa wai bana jin ruwa ne na shigo ya rage mani hanya. Hakan yasa na shiga tare da masa kwatancen unguwarmu, na saki jiki muka dinga fira sai da ya ji kukan jaririya da na goya ne ya ce wai ni matar aure ce na ce A'a sai yayi da dariya tare da cewa ashe Masha Allah yana fatan ni budurwa ce sai na ce bazawara ce ni, ganin ya canza fuska ne kamar baiji daɗi ba na ce masa ni budurwa ce. Daga ranar muka kulla soyayya yana gudun kada ya gane ni matar aure ce yasa na ɗauke ki kina jaririya ranar da kika cika kwanaki arba'in da biyar na cire ki daga nono na kaiki wajen yayata Karima na nuna mata cewa na samu wanda zan aura kuma na fahimci budurwa yake so don haka ta cigaba da riƙe ki a hannunta tana shayar da ke madara da aka bawa jariran da suka rasa nonon uwa. Kasancewar daga ni sai maihaifiyata ce a gida yaya Karima tana gidan mijinta tana kula da ke har aka saka ranar aure na da Alh. Muhammad Adam yana da mata ɗaya sunanta Zainab suna da ɗa guda ɗaya sunansa Adamsy, wato mijinki kenan.Har aka saka ranar aure na da da shi na dinga ƙoƙarin gyara dan kada ya gane cewa ni bazawara ce har na haihu, har ɗinki nayi da maganin budurci dan gudun zargi. An ɗaura aure na da shi an kaini gidansa inda na same shi da matarsa ɗaya da yaronsu Adamsy wanda lokacin shekarunsa biyu da watanni. Ganin irin soyayyar da Alh. Muhammad ke nunawa ɗansa Adamsy yayi yawa hatta gidaje da filaye kawai sai ya siye da sunan Adamsy ya miƙawa mahaifiyarsa, duk da cewar Zainab mahaifiyar Adamsy bata da matsala tana nuna mani ƙauna bata ɗauke ni kishiya ba sai 'yar uwa kullun da alkhairi take bina yayin da ni kuma nake da wata ƙulalliya akanta sai dai idan har ina son burina ya cika sai na da taimakon Adamsy dan haka na jashi a jikina ƙarshe ya koma ɗakina da kwana kayansa sawarsa kayan wasansa komai nasa yana wuya na, har mahaifiyarsa da mahaifinsa suke kira na da Umman Adamsy har aka saka sa makaranta ni nake masa komai da uwa ke wa ɗansa. Hatta dangin Alh. Sai kira na suke da Umman Adamsy ganin yadda na maida shi tamkar ɗan da na haifa a cikina, har lokacin ba wanda yasan na raɓa aure a danginsa da gidansa.Yaya Karima da ke riƙe da ke mijinta ya samu canjin wurin aiki zuwa Bauchi dan haka hankalina ya fi kwanciya sosai.Haka rayuwa tayi ta tafiya Adamsy ya fara wayau har yakai shekaru goma baisan cewa ba ni ce mahaifiyarsa ba kuma har lokacin ban samu ciki da Alh. ba ga shi arzikinsa sai bunƙasa ya ke yi ka tarin kadarori kuma duk rabin dukiyarsa ya mallakawa Adamsy. Wata rana Alh.yayi tafiya zuwa Abuja akan hanyarsa ta dawowa yayi hatsarin mota Allah ya masa rasuwa, bayan mun kammala takaba ne naji danginsa suna maganar rabon gadonsa, kasancewar Adamsy ne kaɗai ɗansa da ya haifa ne shi zai gaje duk dukiyarsa nikam sai dai su bani tumunin takaba shikenan tunda ban haihu da shi ba, duk da cewar kowa na kallon kamar ni ce na haifi Adamsy mahaifiyarsa da danginsa ne kawai suka san cewa ba ni na haife shi ba. Hankalinsa ya tashi ganin cewa Adamsy ne kawai zai gaje dukiyar mahaifinsa kuma mahaifiyarsa za'aba kasonsa dan haka na yanke shawarar kawar da ita daga doron ƙasa dan ita ce zata mani shamaki da dukiyarsa. Dan haka na karɓi magani wajen boka domin na kawar da ita ya zama daga ni sai shi, ba wacce zata gaji dukiyarsa sai ni, hakan kuwa aka yi bayan ta mutu ya zama ba wacce zata mani shamaki da dukiyarsa dan dama saboda dukiyar na shigo gidan. Nayi ta kukan mutuwarta har da sumar ƙarya na fita hayyacina kowa sai da ya tausaya mani na cigaba da riƙon Admsy da dukiyarsa yana da shekaru ashirin a duniya dangin mahaifinsa suka mallaka masa dukiyar komai da komai wanda banso hakan ba na so a ce ni ce suka damƙawa komai kafin yayi wayau, amma duk da haka baisan cewa ba ni bace na haife shi kuma ba wanda ya faɗa masa yana kyautatawa a gare ni da mani biyayya baya tsallake magana ta lokacin da ya kammala karatu ne ya fara gudanar da kamfanonin mahaifinsa a lokacin ne kuma ya tsiro da zancen aure yana da shekaru ashirin da ashirin da tara, inda hankalina ya tashi idan ya auri wata mace ta samu ciki ta haihu to duk abinda ya mallaka zai zama mallaki matarsa da ɗansa, dan haka sai na yanke shawarar tunda ina da 'ya wacce na haifa ai ita zanyi amfani da ita nasa shi ya aure ta dan mu mallake dukiyar ni da ita. Daga nan ne na kara yaya Karima ta sa aka kawo ki na nuna masa cewa ke 'yar yayata ce na bashi umarnin ya aure ki, kasancewar yana mani biyayya baya ƙetere zance na yasa ya aure ki, sai dai kash ke baki haihuwa kuma shi ya kasa kwantar da hankalinsa sai neman wacce zata haihu masa yake yi, shi ya sa duk wacce ya shirya aure sai na raba su da taimakon boka na." Gaba ɗaya Amina mutuwa tsaye ta yi da jin zancen Umma hankalinta ya tashi kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi jin munanan abubuwa da Umma ta aikata. "Umma dama ba ke ce kika haifi Adamsy ba? Ba Mummy Karima ta haife ni ba duk shirinki ne ke ce kika hana Adamsy aure kike saka shi cikin halin da yake ciki?" Ƙafafuwanta kasa ɗaukarta suka yi ta zube a wajen tana kuka tana cewa "Ke kika durƙusa kika haife ni? Abun akwai baƙin ni dai wallahi banyi sa'ar uwa ba." Umma bata saurare ta ba sai da ta kai bakin ƙofa ta juyo ta ce, "Duk yadda za'ayi ki tabbatar Admsy bai bar garin nan shi kaɗai ba, ki tabbatar ƙafarki ƙafarsa barin Adamsy shi kaɗai da zaki yi shine babban kuskure da zaki tafka a rayuwarku." *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll😍😘 *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://chat.whatsapp.com/IdLjpWceclh5VR8G5W9SFY . INA MASU BUKATAR KAYA AKAN FARA SHIN SARI KU SARA KU SIYAR KU SAMU NAKU AKAN FARASHI KALILAN MUNA DA KAYA KALA KALA KAMAR SU HIJABAI KAYAN KITCHEN ATAMFA LACE KAYAN YARA MOTHER CARE KAYAN SHAN ISKA NA ABBA MATERIAL DINKAKKE DA YADIN BEDSHEETS HULUNA DA SAURAN SU MUNA TURA KAYA DUK INDA KUKE CIKIN AMINCI UBANGIJI 💯💯💯💯💯 *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. Page1️⃣7️⃣&1️⃣8️⃣ "Duk yadda za'ayi ki tabbatar Adamsy bai bar garin nan shi kaɗai ba, ki tabbatar ƙafarki ƙafarsa barin Adamsy shi kaɗai da zaki yi shine babban kuskure da zaki tafka a rayuwarki." Haka Amina ta zauna ta dinga kuka ita kaɗai tana cewa. "Dama ba Umma ta haifi Adamsy ba? Shi kansa baisan cewa ba ita ta haife shi ba,nima bansan cewa ita ce ta haife ni ba duk akan abin duniya " Kuke ta ke sosai kamar ranta zai fita, jin sautin kukanta ne yasa ƙawayenta suka shigo cikin ɗakin tare da tambayarta lafiya, hakan ya sa ta tsagaita kukan tare da ce masu ba abunda ke damunta, haka suka yi ta fama da ita akan ta faɗa masa me ke damunta amma sam ta ƙi faɗa, hakan yasa ta ce ta sallame su kowa ta tafi gidanta tana bukatar kaɗaicewa ita kaɗai a yanzu, dan haka suka bar mata gidanta kamar yadda ta buƙata. Lokacin da Direban Umma ya bar gidan Adamsy dai-dai lokacin da ya fito daga kwanar gidan Adamsy ya hau titi dai-dai nan sai ga motar Adamsy ta shigo kwanar, Sadik ne ke tuƙa motar nasa shi kuma yana zaune a gefensa idanunsa na kan motar tabbas motar Umma ce ba shakka.kallon Sadik ya yi tare da cewa "Ko mai ya kawo Umma gudana kuma?" Sadik ya kalle shi tare da cewa "Ina motar Umman ta ke?" "Yanzu suka bar nan, kuma na tabbatar daga gudana ta ke." Ba wanda ya sake magana sai da suka iso ƙoafar gidan ne Adamsy ya kalli Sadk tare da cewa "Mu shiga ciki mana." Girgiza kai Sadk ya yi tare da cewa "Na kawo ka har kofar gida ne sakamakon ganinka da na yi baka cikin nutsuwarka,dan haka ka shiga guda kuma na kama gaba na." "Okay ba danuwa tunda haka ka ce, yanzu dai tunda baka ɗauko motarka ba tana can gidan Umma to ka tafi da wannan motar tawa idan ka dauka ta ka sai ka ajiye wannan a can gudan." Daga nan ya miƙa masa hannu suka yi musabaha sannan ya fita. Sadik ya ja motar ya bar wajen kai tsaye ya nufi gidan Umma. Koda ya shiga Falon ba kowa kai tsaye ya nufi ɗakinsa dan damuwa ce fal a tare da shi, sautin kukan Amina ya ji yana tashi daga ɗakinta, cikin tashin hankali ya nufi ɗakinta. Tura ƙofar ya yi bakinsa ɗauke da sallama. "Assalamu alaikum" Kukanta kawai take yi ba tare da ta san ya shigo ɗakin ba, a hankali ta tako har ga gabanta jin motsin mutum ne ya sa ta ɗago kai ta kalle shi, miƙewa tsaye ta yi ta zuba masa idanu kamar wacce ta ga sabon halitta, faɗawa jikinsa ta yi tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya. Tausayin Adamsy ne ya kama ta, hannayensa ne ya sa ya ɗago ta daga jikinsa ya ce, "Me ya faru kike kuka?" Shiru ba amsa sai ajiyar zuciya da take saukewa. "Ne ce me ya sa me ki ne kike kuka ko rasuwa aka yi ne kike kuka?" Girgiza masa kai ta yi alamar a'a daga nan ta cigaba da kukan da ta ke yi, "To ki faɗa mani me ke saka ki kuka?" Girgiza kai tayi tare da cewa "Bakomai." "Ban yarda da cewa bakomai ba, haka kawai ba zaki zauna kiyi ta rusa kuka ba tare da wani dalilin ba." Kai ta jinjina alamar eh, girgiza kai yayi tare da cewa "Sai dai idan zaki ɓoye mani ne." "Mafarki na yi da ya firgita ni na dinga kuka." Duk yadda Adamsy ya lallaɓa Amina kan ta sanar da shi abinda ya sa me ta har ta dinga kuka ƙin faɗa masa ta yi haka ya gaji ya ƙyale ta. Da ya samu tayi shiru ta daina kumar ne sai ya nufi hanyar fita daga ɗakin, har ya kai bakin ƙofar ya juyo ya kalle ta ya ce, "Na hango motar Umma da zamu shigo layin nan lafiya dai ko?" Jinjina kai ta yi tare da cewa "Lafiya lau ta shigo ta gaishe ni ne?" "Kuma wannan kukan da kike bida nasaba da zuwanta?" "Ko da ta shigo ta fita lafiya lau bayan fitarta ne kaina ke ciwon?" "Kinsha magani?" "Eh na sha." "To ki kwanta " Nufar gado ta yi ta kwanta kamar yadda ya umarce ta. Shima fita ya yi tare da barin ɗakin kai tsaye ya nufi ɗakinsa. Zama ya yi akan sofa tare da jinginar da bayansa ya shiga aikin tunanin da ya saba yi, dan labarin haukacewar Hauwa'u da mutuwar Fauziyya sun girgiza shi sosao, hawaye ne suka fara gangarowa daga idanunsa ya furta a hankali. "Allah kai kasan sirrin ɓoye da na fili, Allah ka iya mani abinda bazan iya ba, Allah ka magance mani matsalata." Wayarsa ce ta fara ruri dubawa ya yi ya ga manajansa ne na Kaduna, ɗagawa ya yi tare da cewa "Assalamu alaikum" Daga can ɓangaren manajan ya ce, "Wa'alaika salam. Barka da warhaka yallaɓai." "Yauwa Barka dai." "Akan maganar da muka yi ɗazu ne na tanadi komai tunda ka ce a fitar da komai na gidan a zuba sababi gidan ma a sabunta sa duk an fitar da komai na gidan kamar yadda ka buƙata za'a sabunta shi, amma kayan da aka fitar daga cikin gidan ya za'ayi da su ne?" "Ka bawa masu buƙatarsu." "To yallaɓai Allah ya saka da alkhairi. Uban giji ya ƙara buɗi, yanzu idan an gama sabunta gidan sai a yi order sabbin furniture's da kayan kitcheen." "Ba matasla." Daga nan suka yi sallama ya katse kiran. Farin ciki ne kawai ya lulluɓe manaja dan ya san cewa wasu daga cikin kayan wasu kuma zai ba wasu dan komai sai da aka fitar daga cikin gidan kuma ba wai dan sun tsufa ba sai dai ƙura da suka yi. Gaba ɗaya kayan falon biyu sautin kujera biyu da gado da ke cikin kowane bedrooms guda huɗu sai da aka fitar, da fridge da freezer gas kayan kitcheen labulaye carpet komai sai da yasa aka fitar ya ce a zuba sababbin a cikin gidan . Sake kiran wayar manaja ya yi inda cikin rawar jiki ya ɗaga kiran wayar tare da karawa a kunnensa. "Hellow yallaɓai ." "Kana jina?' "Eh ina ji yallaɓai." "Ka samo mani mai gadi da zai zauna a gidan ya dinga kwana, kasan wancan mai gadin tunda ya yi jinya ya koma ƙauyensu bai dawo ba nima ban nemi wani ba, so yanzu ina bukatar mai gadi." "Okay ba danuwa yallaɓai zansa a samu ko mai gadin kamafaninka idan na masa magana zaiyi saurin samo mani, dan kwanakin baya ba'ayi sati biyu ba ya zo ya same ni wai abokinsa na son aiki ko na gadi ne, zan masa magana sai ya kawo wancan ɗin idan bai samu aikin ba." "Okay to ka bai cika sai na jika." Daga nan suka yi sallama ya katse kiran wayar. Tana tafiya tana ɗauke da bokitin tallar doyar da ta ke yi, amma kallo ɗaya zaka mata ka gane cewa ƙarfin hali ce kawai, amma tana jin jiki sosai. Tafiya ta ke yi tana ɗangisa ƙafarsa da inna Habi ta buga mata ita ce, ga duk inda ta taɓa a jikinta ciwo ne sai kuma wasu wuraren da sun ɗuri ruwa sunyi bororo musamman ta cikin rigarta daga gefen ƙugunta, gashi bata jin zata iya yawon rallar da ta saba saboda yanayin tafiyarta ƙafarta na ciwo sosai ƙara sawa ta yi wani ƙofar gida da maza ke taruwa ta yi sallama ta ajiye robar doyar, dama kullun suna siya idan ta kai masu doyar, dan haka suna ganinta suka fara tambayrta. Ɗaya daga cikinsu ya ce, "Humaira lafiya kuwa?" "Lafiya lau. ina wuninku?" Wani dattijo da je gefe ya ce, "Ruwan zafi ne ya zube maki a jiki?" Kai ta girgiza alamar a'a. sai tya sake tambayarta da cewa "Ga jikinki duk kunar wuta " "Idanunta ne suka ciko da ƙwallon ta ce dukana aka yi." Gaba ɗaya jama'ar da ke wajen suka haɗa baki cikin mamaki suka ce "Duka?" Kai ta jinjina alamar eh Wani daga cikinsu ya ce, "Wane irin duka jikinki ya yi haka?" "Da itacen bakin wuta ne shiyasa " Salati suka saka tare da tambayarta waye ya mata haka, nan ta sanar da su matar babanta inda suka shiga tsinewa Inna Habi . Mallam kallamu ne ya yi sallama kofar gidan abokinsa Mallama Musa, baya nan sai inna Habi ta amsa ta sanar da shi baya nan. Yana shiri barin ƙofar gidan sai ga Mallam Musa ya ƙaraso zai shiga gidansa. "To Mallam Kallamu kai ne da rana tsaka?" "Eh ni ne." Hannu ya miƙa masa suka gaida inda ya ce, "Sauri na ke zan koma bakin aikina, samu ne ya sa na zo na sa me ka." Murmushi yayi tare cewa "Alhamdulillah" "Yauwa abinda ya sa na zo na same ka saboda maganar da ka zo har wajen aikina ka sa me ni kan cewa kana neman aiki ko gadi irin wanda na ke yi ne hakan yasa na samu manajan kamfanin da nake gadi ya ce babu yanzu kuma na sanar da kai." Kai Mallam Musa ya jinjina tare da cewa "Eh haka ne ba shakka." "To yanzu aikin gadin ya samu dai dai ba irin nawa bane ban sa ni ba ko zaka iya." "Gadi ai gadi ne." "Mallam Musa kenan, ai nawa gadin daga ƙarfe bakwai na safe ne zuwa bakwai ma magrib na tashi akwai security da ke kwana yana gadi,to kai kuma na ka yanzu na zama ne din din din, wato nan zaka dinga wuni kana kwana, akwai ɗakinka da banɗaki a cikin gidan kowane lokaci kana nan zaka iya, dan irin wannan aikin 'yan cirani sunfi haka, amma kai na ga da iyalinka." Bakomai zan yi na gaji da zaman nan na rashin abinyi ga wulaƙancin Habi akan abinda ta ke wa Haumaira, saboda bana kawo abinci bata kallona a matsayin mai gida, yanzu haka sammakon barin gidan na yi amma ban samu abinyi ba. Na amince zanyi gidan waye?" "Shugaban kamfaninmu shi zai dawo nan da zama yanzu haka ana kan gyaran gidan ne an ce gobe na zo da kai." "Masha Allah. Allah ya kaimu nagode sai mu tafi na fara aikin. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll😍😘 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9 *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🧏‍♀️💃 *INA KUKE BIG LADY'S KIKARANTA KOBAZE ANFANEKIBA ZE AMFANI WANI NAKI* 🧏‍♀️💃 🤩MAGANA A KEYI TA GLOIN SKIN🤩 (GYARAN JIKI SHINE MECE) DUK MACEN DABATA GYARA TO MUNA MATACE BAKAI AKIRATA MACEBA🤷‍♀️ HADDA MAZANMA🤨 💫 Hajiya shin kina buƙatar jikinki yayi kyau fatarki Takoma ɗanya shakaf tamkar ta jarirai ??? Kikoma tamkar zarah acikin taurari acikin mata yan uwanki✨✨✨✨✨domin fa hasken zarah dabanne💃 💫shin kina buƙatar fatarki Takoma tamkar ta jaruman Kaneewood kona novel?? Humm kinsan cewar dafata ne matan waje kekarɓe mana mazaje??🙄🙄🙄 To idan baku saniba ayau kusani, ƙyalli fata shine keruɗar mazajenmu dakuma samari kai harmada ƴammata🤷‍♀️ 💫💫idan kinshirya gyara jikinki Hajiya kigarzayo domin samun ingatattun haɗin daze wanke Miki fatarki tass kikoma tamkar bala rabiya✨sabida ƙyalli da kyau babu kwailin balle abata miki fata, se haɗin zallar gargajiya na ƴaƴan itatuwa masu inganta lafiyar fatarki, *SABULUN WANKA, MAN SHAFAWA GA ƘAMSHI GA DAƊi, SEKUMA DILKAH WADDA ZAKIYIWA KANKI A CIKIN MINCI* dukkansu afarashi ɗaya za'a haɗa Miki duka ukkun wlh wlh wlh summa tallahi acikin mako ɗaya (one week) Zaki banbata fatarki data sauran mutane domin ingatattun kayane kuma inada granty akansu, duk wadda tayi anfani dasu mako ɗaya bataga canjiba tazo wlh Allah zan bata kuɗinta domin ko haufi banayi akansu💪gaduk me buƙatar wannan haɗin ze iya tuntuɓar wannan nomber 👉 07037092176 🙏🙏🙏 munada maganin mata kala kala namatsi na daɗi danakomai ma munada harmada na maza wanda suke fama da matsala, gadukkan me bukatar kayanmu ga nomber nan ansaka ze iya nemanmu ako ina yake afaɗin duniya zamu kaimishi insha Allah🙏 sayen nagari meda kuɗi gida me kyau bayada tsada Ako ina mungode.🙏🤗 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9 *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* 🧏‍♀️💃 *INA KUKE BIG LADY'S KIKARANTA KOBAZE ANFANEKIBA ZE AMFANI WANI NAKI* 🧏‍♀️💃 🤩MAGANA A KEYI TA GLOIN SKIN🤩 (GYARAN JIKI SHINE MECE) DUK MACEN DABATA GYARA TO MUNA MATACE BAKAI AKIRATA MACEBA🤷‍♀️ HADDA MAZANMA🤨 💫 Hajiya shin kina buƙatar jikinki yayi kyau fatarki Takoma ɗanya shakaf tamkar ta jarirai ??? Kikoma tamkar zarah acikin taurari acikin mata yan uwanki✨✨✨✨✨domin fa hasken zarah dabanne💃 💫shin kina buƙatar fatarki Takoma tamkar ta jaruman Kaneewood kona novel?? Humm kinsan cewar dafata ne matan waje kekarɓe mana mazaje??🙄🙄🙄 To idan baku saniba ayau kusani, ƙyalli fata shine keruɗar mazajenmu dakuma samari kai harmada ƴammata🤷‍♀️ 💫💫idan kinshirya gyara jikinki Hajiya kigarzayo domin samun ingatattun haɗin daze wanke Miki fatarki tass kikoma tamkar bala rabiya✨sabida ƙyalli da kyau babu kwailin balle abata miki fata, se haɗin zallar gargajiya na ƴaƴan itatuwa masu inganta lafiyar fatarki, *SABULUN WANKA, MAN SHAFAWA GA ƘAMSHI GA DAƊi, SEKUMA DILKAH WADDA ZAKIYIWA KANKI A CIKIN MINCI* dukkansu afarashi ɗaya za'a haɗa Miki duka ukkun wlh wlh wlh summa tallahi acikin mako ɗaya (one week) Zaki banbata fatarki data sauran mutane domin ingatattun kayane kuma inada granty akansu, duk wadda tayi anfani dasu mako ɗaya bataga canjiba tazo wlh Allah zan bata kuɗinta domin ko haufi banayi akansu💪gaduk me buƙatar wannan haɗin ze iya tuntuɓar wannan nomber 👉 07037092176 🙏🙏🙏 munada maganin mata kala kala namatsi na daɗi danakomai ma munada harmada na maza wanda suke fama da matsala, gadukkan me bukatar kayanmu ga nomber nan ansaka ze iya nemanmu ako ina yake afaɗin duniya zamu kaimishi insha Allah🙏 sayen nagari meda kuɗi gida me kyau bayada tsada Ako ina mungode.🙏🤗 *BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM* Page1️⃣9️⃣&2️⃣0️⃣ "Masha Allah.Allah ya kaimu nagode sai mu tafi na fara aikin." "Kai Mallam Musa

Chapter 5 of 19