'yar cikina ce? Lokacin da ta ke aikata ba dai-dai ba na ke tsawatar mata baki san cewa 'yata ba ba ce sai yanzu? Ba ke ce kike ɗaure mata gindin rashin kunyar da ta ke mani ba, a matsayin uba na ke a wajenta amma sam bata gani na da gashi saboda tarbiyyar da kima koya mata kenan, duk halin da ta shiga kece sila."
Hawaye ne ke fita daga idanunta tana cewa,
"Duk abinda ka ce na karɓi laifina amma dan Allah ka yi tunanin wani haka ta ke ciki?"
Jinjina kai ya yi tare da cewa,
"Kafin mu je ga zancan Salma bari na maki wata tambaya."
"Ina jinka."
"Ina Humaira!?"
Gabanta ne ya fadi rass
"Na ce ina Humaira ya ke?"
"Mallam Humaira ta tafi yawon banzanta da ta saba da shi, dan mima bansan inda ta ke ba."
Jinjina kai ya ya tare da cewa
"Yanzu kika gama maganar cewa ko ɗan riko ne zaka damu da shi idan ya ɓata, ita Humaira ba riƙonta kike ba?"
Shiru ta yi tare da cewa
"Ita fa yawon isakancint..."
Kasa ƙarasa maganar ta yi ganin yadda Mallam Musa ya mata wani kallon da ya sa ta sha jinin jikinta.
Fuskarkarsa a tsuke ya fara magana yana cewa
"Ko da wasa kada na sake ji ko ganin kin alaƙanta Humaira da wannan kalmar, idan kuma ba haka ba wallahi sai na baki mamaki. Ban haifi yarinyar da zata yi yawon iskanci ba, kuma ko rantsuwa zan iya yi kan cewa Humiara ba zata taɓa iya aikata abinda kike faɗa ba."
"Aikatawa ta nawa kuma? Yarinyar da aka ce an gani a cikin mota tare da ƙaratan maza biyu? Sun zo siyen koko a bakin layi zaka ce..."
Nan ma shiru ta yi dan ta tuna gargaɗi da kallon da ta mata da ta ce tana can tana yawon iskanci.
Shiri ta yi tare da jinjina kanta cikin takaici.
Nazari Mallam Musa ya fara yi, wato waccan ranar da Humaira ta ce koko ta ke son sha har ya mata faɗa wato nan unguwar ta kawo su? Tabbas ranar Adamsy da Diraban nasa ne suka kawo ta, kenan akwai wanda ya ganta ya zo ya sanar da ita.
"Koma dai mene ne bai dame ni ba, na baki Ammar yarinya baki san inda ta ke ba kina cewa ta je yawon iskanci, kuma hankalinki kwance ba ruwanki da halin da ta ke ciki, sai da yarinyar da kika haifa ta ɓace ne zaki zaki tashi hankalina? To bari ki ji ba abunda ya dame ni ke kika san yadda kika yi dan haka ki nemo mani yarana."
Ta shi ta yi ta nufi ɗaki tana ta rusa kuka ba kakkautawa, yau ta tabbatar da cewa lallai Mallam baya ƙaunar Salma. Sai dai wani sashe na zuciyarta ta tana raya mata yadda Mallam Musa ke ƙaunar Humaira anya zai iya jin labarin ɓatarta ya iya shan ruwa hankali kwance, ko ya san inda ta ke ne?"
Haka ta cigaba da kuka babu mai rarrashinta.
*DUBAI*
Kwance suke a makeken gadon hotel din da suka kama, bayan sun ci abinci sunyi wanka ne suka kwanta.
Ƙarfe goma na dare ne, zuciyar Humaira fes da farin ciki, yau ita ce ƙasar larabawa.
Wayarsa ya janyo tare da lalubo lamabr Amina ya danna mata kira.
Da can ɓangaren tana zaune ta ke ta yi tagumi tana tunanin hanyar bi.
Tana ganin lamabar ta san cewa shi ne ke kiranta, da sauri ya ɗaga tare da cewa
"Hello"
"Uwar gida sarautar mata."
"Hmmm"
"Ya Hmmm kuma?"
"Ya ka ke ya jin daɗi? Da yawon shaƙatawa?"
"Yawon shakatawa kuma?"
"Eh"
"Me ya sa kika ce haka?"
"Haka na ke ji a jikina."
"Amma ai kinsan cewa idan zan fita shaƙatawa ai tare da ke na ke tafiya, idan kuwa na fita ni kaɗai ki tabbatar akwai abinda na ke yi ne na wani aiki zan gudanar."
Taɓe baki ta yi tare da cewa
"Kwana nawa zaka yi?"
"Zanyi sati biyu a nan daga nan kuma zan tafi wata ƙasar na yi sati biyu"
"Okay to shikenan zan zo na sa me ka."
"Ina kenan?"
Duk ƙasar da ka ke mana ai ba inda bazan iya zuwa ba, dan na yi missing naka da yawa."
Humaira da ke kwance a gefensa ne gabanta ya faɗi, jin kalaman Amina. Ta ke sai wani abu mai ɗaci ya tokare mata maƙoshi, da ƙyar ta iya haɗiyewa.
Ta rasa dalili a duk lokacin da ta ji yana waya da Amina sai ta ji ba daɗi.
"Amina aiki fa na zo yi ba wani abu ba."
"Eh na sani, sau nawa kana zuwa aikin amma kuma kake zuwa da ni koda sati ɗaya zaka yi? Sai yanzu da har zaka yi sati biyu ne ka ke tsoron na je? Lallai akwai wani abu a ƙasa."
"Ba komai gimbiyata, saboda ba zama na ke ba idan na fita tun safe sai dare na ke dawowa."
"Na ji idan har zamu kasance da juna a tare hakan bai dame ni ba, idan ka dawo zan kasance da kai a daren har zuwa wayewar gari, hakan ma ya ishe ni."
Dafe goshinsa ya yi dan ya rasa mai zai ce mata, idan ya ɓullo ta nan dai ta ɓullo ta nan.
"Kinga Gimbiya idan kina zaune a hotel a ce sai dare na ke dawowa hankalina bazai kwanta ba, ballantana na iya taɓuka wani abu, dan haka na yi maki alƙawari idan na dawo zan saka lokaci da zamu zo mu mori lokacinmu."
"Da gaske ka ke?"
"Na yi maki alƙawari in Sha Allah, indai muna da rai da lafiya."
"Wallahi na yi kewarka bana jin daɗi idan baka tare da ni, nayi kewarka sosai."
Murmushi ya yi tare da cewa
"Nima haka bana jin daɗi kwata-kwata idan ba na tare da ke, dan rashinki a kusa da ni tamkar shayi ne babu sugar.Daurewa kawai na ke yi nima ba jin daɗin rashinki na ke yi ba, duk na shiga damuwa ji na ke rayuwar ta mani Kani."
Murmushi ta yi na jin daɗi yada ya ke nuna mata mahimmancinta a wurinsa, sosai ta ji san yi a ranta. Ya yin da zuciyar Humaira ke ƙuna da jin kalaman da ya ke faɗawa Amina.
Bayan sun gama waya ne ya yi mata sallama tare da cewa
"I love you"
Ya sumbaci wayar, itama ta maida masa martani sumbatar da ya yi tare da cewa
"Love you to"
Katse wayar ya yi sai a lokacin ne ya ji ba daɗi saboda gani ya ke yi tamkar bai wa Humaira adalci ba. Bai dace ya yi irin wadannan magana a gabanta ba, dan zai iya zama tamkar cin fuska ne a gare ta. Ƙarƙashin wani sashe na zuciyarsa kuma yana ganin ai Humaira yarinya ce ƙarama, bata isa kishi har hakan ba. Ba zata damu ba.
Ganin ta juya baya ne ya sa ya yi tunanin ko barci ta ke yi ne, baisan cewa kuka ta ke yi na baƙin cikin kalaman da ya ke faɗa wa Amina.
Janyota jikinsa ya yi tare da mata filo da faffaɗan ƙirjinsa, sai ya ji danshi kamar ɗigar ruwa a ƙirjinsa, shafa fuskarta ya yi tare da cewa,
"Baby kuka kike yi ne?"
Kai ta girgiza masa tare da cewa
"Ba kuka na ke yi ba."
Mamaki ne ya kama shi duk da cewar duhu ne a ɗakin sun kashe hasken ɗakin amma sai da ya gane kuma ta ke yi. Magana ya ke yi a zuciyarsa
'Kenan kishi ta ke yi ko me? Yanzu ita ma ta san wani kishi kenan?'
"Sarauniyata me ya saka ki kuka?"
"Ba komai"
Kasancewar ya san dalilin kuka dan haka bai dame ta da tamabaya ba.
Kwantar da ita yi a jikinsa tare da kama gefen fuskarta da yana kasar hawayen da ya ɓata mata fuska.
Bayan ya gama lashewa ne ya ce,
"Am sorry."
Duk sai ta ji ita ce da laifi dan ya yi waya da matarsa yana faɗa mata kalmar soyayya ai ba aibu bane, kuma ai sun daɗe tare da matarsa ita da ta zo daga baya baikamata ta ji haushi ba ko ta yi kishi da ita ba.
Murmushi ta ƙaƙalo tare da cewa
"Ba ka yi wani abu na rashin dacewa ba ka yi haƙuri."
Sai ya ji daɗin kalamanta har cikin zuciyarsa.
Bakinsa ya haɗe da nata, ai kamar jira ta ke yi yana kai bakinsa ta fara tsotson bakinsa.
Duk abunda ya yi mata a wannan daren sai da ta yi masa fiye da yadda ya yi mata, dan Maryam matar Abdallah ta bata shawara kuma ta ɗauka.
Dan haka ta zage dantse ta faranta masa sosai, duk abunda ta san yana so sai da ta masa.
Fiye da awa ɗaya suka ɗauka suna abu guda, sun zautar da junansu, ta gigita tunaninsa, ta shayar da shi zazzaƙar zumanta mai zaƙi, ta sha sambatu da suratai haɗi da sanyawar albarkarsa.
Ya gajiyar da ita sosai kafin ya saurara mata.Haka zalika itama bata nuna masa gazawarta ba.
Haka suka cigaba da rayuwa cikin jin daɗi da ƙaunar juna. Sati biyu suka yi sannan suka tafi zuwa ƙasar Indiya. Ya yin da kuma Abdallah suka koma Nigeria.
Nan sati ɗaya suka yi daga nan suka tafi kasar London.
Nan ƙasar ma sai da suka yi yawon shakatawa, sun ziyarci wuraren daban-daban tare da ɗaukar photuna kala-kala.
Bayan sati ɗaya suka koma Nigeria.
Tun a Airport Humaira ke jin gabanta na faɗuwa, ta rasa dalili, sai furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ta ke ta furtawa. Dan jikinta ya nata wani al'mari na shirin faruwa da ita.
Direban Adamsy ne ya zo ɗaukarsu da motar Adamsy, haka aka loda kayansu a bayan motar.
Suka shiga Direba ya ja motar suka bar Airport ɗin still gabanta ne ke tsananta faɗuwa.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T.
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*GARGAƊI*Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaW2Ygg9xVJlgSoy2Q2V
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a aguji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba, ko a maida mani shi Audio ko karanta shi a YouTube ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page6️⃣2️⃣&6️⃣3️⃣
Suka shiga Direba ya ja motar suka bar Airport ɗin, haka kawai ta ke jin gabanta na tsananta faɗuwa sai dai ta cigaba da faɗin innalillahi wa'inna ilaihir raji'un acikin zuciyarta.
Bayan direban ya yi parking ne ya buɗe masu suka fito,ya yin da sauran ma'aikatan gidan suka dinga zuwa gaishe su.
Hannunta ya riƙe suka nufi cikin gidan.
Bayan sun shiga falon ne ma'ikatan gidan suka biyo su da kayan da suka dawo dasu dan ya yi masu siyayya sosai, musamman ƙananan kaya.
Baby ki shiga ki watsa ruwa sai ki ci abinci, nima zan yi wanka na je masallaci.
Ɗakinta ta nufa cikin sanyin jiki, dan ta rasa me ke damunta gaba ɗaya.
Haka nan dai ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallar azahar.
Bayan ta idar da sallar ne ta fito zuwa falo, tana sanye da doguwar riga na atamfa.
Zama ta yi akan doguwar kujera tana kallon tv, jin muryarsa ta yi yana shigowa da waya a kare a kunnensa, da alama waya ya ke da Ummansa.
"Laflya lau na dawo Umma"
Daga can ɓangaren ta ce,
"To madallah, zan yi maka wani ba zata."
"Ba zata kuma Umma?"
"Eh ba zata na ce"
"Wace irin ba zata?"
"Koma wace irin ce zaka gani, dan idan har na sanar da kai ya zama ba zata ba kenan."
Murmushi ya yi tare da cewa
"To na gode Ummana."
"Ka shiga gida ki kwanta huta gajiya."
"Umma ya aka yi kika san ban huta ba?"
"Babana kenan kai dai ka jira ba zata da na ce zan maka."
"To shikenan Umma sai na jiki. Zuwa yaushe ne za ki mani ba zatan?"
"Ko ma yaushe ne sai lokacin ya yi zaka sani."
Sallama suka yi sannan ya katse kiran wayar.
Kallon Humaira ya yi tare da cewa
"Baby kin ci abinci kuwa"
Yamutse fuska ta yi tare da shirin kwanciya akan kujera, cak ya ɗauke ta bai dire ta ko ina ba sai jan kujerar dinnig table.
Mamakinsa ta ke yadda kwata-kwata baya jin nauyin ɗaukarta abu kadan sai dai ya ɗaga ta.
"Me zaki ci na zuba Mali?"
Buɗe foodflask ɗin farko ya yi white rice ne da chicken soup, tana jin ƙamshin miyar ta toshe hancinta tare da masa alama ya rufe. Mamaki ne ya kama shi dan ganin yanda ta yi daga ganin abinci.
Foodflask na biyu ya buɗe, nan kuma soyayyiyar doya da ƙwai ne. Nan ma ta ce ya rufe bata so ƙarni ya ke mata.
Foodflask na uku ya bud'e jollop din taliya ce da ta ji kayan lambu, nan ma ta toshe hanci wai bata son warin abuncin.
Foodflask na hud'u ya buɗe farfesun ɗanyen kifi da ya ji kayan ƙamshi ne, tana jin ƙamshin farfesun ta fara kakarin amai a guje da wuce falo tare da zubawa akan dogon kujera.
Bin bayanta ya yi cikin hanzari tare da tamabayarta
"Me ya sa me ki? Dama baki da lafiya ne?"
"Lafiya lau na ke , ba abunda ke mani ciwo, kawai gajiyar hanya ce."
"Yanzu gajiya ce zaisa ki kasa cin abinci? Sai dai idan baki da lafiya."
"Wallahu ba abunda ke mani ciwo gajiya ne, nasan zuwa anjima zan wartsake."
"Gara ki wartsake kam kafin zuwa dare na ƙara maki wata gajiyar."
Tura baki ta yi dan dama ta san wannan ba fashi.
"Me zaki ci?"
"Fruits kwai nake so"
Wayarsa ya ɗauka tare da kiran lamabar Mustapha ya basa Umarnin cewa ya kawo mata Fruits.
Bayan wasu mintuna sai ga Mustapha ya yi sallama, hannunsa ɗauke da faranti da aka yayyanka Fruits.
Ajiye masu ya yi tare da gaishe su, Adamsy ya amsa masa. Tashi ya yi ya basu wuri.
Jiki na rawa ta ɗauki farantin tare da fara cin apple da kankana bayan ta gama da su ne ta fara shan lemo da abarba.
Haka duka ta shanye Fruits ɗin yana kallonta mamaki ma ta bashi yadda ta shanye su tas.
Jingina bayanta ya yi da jikin kujera tare da lumshe idanunta, janyo ta ya yi ya mata fillo da cinyarsa.
Cikin ƙankanin lokaci barci ya ɗauke ta, a hankali ya gyara mata kwanciya tare da nufar dinning room din dan shima yunwa ya ke ji.
Yana kammalawa ne ya ɗauki key ɗin motarsa ya fice daga falon.
Direbansa na ganin fitowarsa ya ƙaraso wajensa, key ɗin motar ya amsa daga hannunsa tare da nufar ɗaya daga cikin motocin.
Bayan ya fito da motar ne ya ƙaraso inda Adamsy ke jiransa, fitowa ya yi ya buɗe masa bayan motar ya shiga kafin ya rufe ya zagaaya mazaunin Direban ya zauna.
Suka fice daga gidan bayan mai gadin gidan ya buɗe masu gate suka fice.
Kasuwa suka nufa shagon Mallam Musa, inda ya kama hayar shago da kuɗin da Adamsy ya ba shi ne ya buɗe shagon siyar da provision.
Komai akwai shinkafa, wake, masara dauro, alkama.
Ɗayan ɓangaren kuma ga su taliya, macaroni, indomie, maggi, Madara, milo omo sabulai da dai sauran kayan provision da ake siyarwa.
Koda suka ƙarasa shagon ma hankalinsa na kan customers masu siyan kayan provision, sai wani matasahin saurayi da ya ke taya shi siyar da kaya, yana ɓangaren kayan awo.
Murmushi Adamsy ya yi tare da rungume hannunsa, yana kallon yadda jama'a ke ta siyayya a shagon, hakan ya masa daɗi.
Har ya kai mintuna biyar a tsaye Mallam Musa bai san ya yana nan ba. Sai da wannan saurayi da ke taya Mallam Musa sai da kaya ya kalli Adamsy ya ce,
"Allaji me za'a kawo maka?"
Sai a lokacin Mallam Musa ya lura da cewa Adamsy ne tsaye a wajen.
Murmushi Mallam Musa ya yi tare da cewa
"Yallaɓai kai ne a nan? Bisimillah shigo daka ciki."
Ya ƙarasa maganar yana janyo kujerar roba,tare da ajiye masa dan ya zauna.
Durƙusawa ya yi tare da gaida Mallam Musa cikin girmamawa, ya amsa cikin farin ciki da jin daɗi.
Zama ya yi a kujera Mallam Musa na murmushi ya ce,
"To yallaɓai sai dai zafi zai dame ka kasancewar ranka ce ba Ac ba."
Murmushi ya yi tare da cewa
"Na ga wuri Abba, ma sha Allah wuri ya yi kyau Allah ya sa albarka ya sa ka fara a sa'a."
"Amin ya Allah, yau kuka dawo ne?"
"Yau ɗin nan."
"Yau amma shi ne ka iya zuwa yau baka zauna ka huta ba."
Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce, komai ba, a ransa ya ji daɗin yadda ya ga shagon kuma kasuwa na tafiya sosai. Kuma ya ƙudiri niyyar cewa zai karawa Mallam Musa jari."
Direbansa ne ya karasa shigowa nan ma ya gaida Mallam Musa, ya kuma yi masa addu'ar sanya albarka.
Kasancewar ga mutane na ta shigowa ne ya sa Adamsy ta shi tare da yi wa Mallam Musa sallama suka tafi.
Sai da ya yi sallar isha'i sannan ya koma gida, nan ma haka ya yi ta fama da da Humaira akan ya ce abinci amma ta ƙi ci, har dai ya haƙura ya barta sai dai fruita da ta sha kawai ta ce ta ƙoshi.
Ya tamabaye ta ko bata da lafiya ta ce lafiyarta lau.
Kwanciya ta yi, sai ya ɗauke ta zuwa bedroom ɗinta ya kwantar da ita.
Ɗakinsa ya koma ya koma ya gama shirinsa na kwanciya barci sannan ya dawo ɗakinta.
Tana kwance har ta fara barci can cikin barcinta ta ji hannayensa na yawo a sassan jikinta, ga yunwa tana ji ga kasala sannan ga jarabarsa.
Tana ji ya zare mata rigar barcin da ke jikinta, ya fara shafar jikinta, sai ya ji jikin nata da ɗumi.
"Baby jikinki fa ya yi zafi me ke damunki?"
"Nima ban sani ba."
"Yakamata mu tafi asibiti kiga likita ya duba ki."
Gabanta ne ya faɗi dan ta san cewa zancen allura ko magani ne idan aka tafi asibiti, dan haka sai ta yi saurin cewa
"Ni fa ba abunda ke damuna kawai ina ga tafiya da muka yi ne ya sa na ke jin gajiya a jikina sosai, amma nasan cewa zuwa gobe zai bar jikina."
Tana maganar tana lumshe idanu, alamar barci ne a idanunta.
"To amma ai gajiya bazai saka jikinki ya yi ɗumi ba, sai dai idan baki da lafiya."
"To ni yana saka ni."
"To bari na kawo maki magani ki sha."
"Ni dai a'a ka barshi kawai ba zan sha ba "
Duk yadda ya so lallaɓa ta akan ta sha magani ƙin amincewa tayi, sai ya haƙura ya barta dan bai san ya takura mata aka abinda bata so.
Rungume ta yi dan dole baida wani zaɓi bayan ƙyale ta, dan ya ji jikinta da zafi.
A haka har barci ya ɗauke ta kafin shi ma barci ya ɗauke shi bayan ya jima barci bai dake shi ba.
Da ƙarfe huɗu da rabi na asuba ne ya farka, rigar jinkinta da ya cire mata ne ya mayar mata sannan ya guda mata kwanciya .
Bathroom ɗinta ya mufa ya yi wanka tare da ɗauro alwala, sallar nafila ya gabatar sannan ya zauna tana karatun Alkur'ani. Da aka kira sallar assalatu ne ya tayar da Humaira dan ta yi sallar asuba.
Bayan ta tashi ne ya fita zuwa masallaci. Ita kuma ga gabatar da sallarta a gida.
Tana idar da sallar asuba ta yi addu'a ko azkar bata tsaya yi ba kamar yadda ta saba yi. Daga nan samar sallayar ta yi barci.
Koda ya ya dai daga sallar asuba lokacin ƙarfe bakwai na safiya ne, kai tsaye ɗakinsa ya nufa, inda ya shiga bathroom ya yi wanka, nan da nan ya shirya cikin shigar suits blue riga da wando sai ta ciki fara.
Ɗakin Humaira ta nufa inda ya sa me ta kwance a saman sallaya tana barci.
Shafa gefen fuskarta ya yi inda ya ji jikin nomal yanzu ba ɗumi.
Tashi zaune ta yi tare da cewa
"Ina kwana ?"
"Lafiya lau ya jikinki."
"Ni dama lafiyata ƙalu."
"Zan fita da wuri yau zuwa office, saboda ina da meeting da safen nan, kuma aiki ya mani yawa."
"To Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya."
"Amin, na san ba zaki ci komai ba idan na tafi aiki, dan haka tashi muje dinning area."
Marairaice fuska ta yi tare da cewa
"Ni Fruits kawai na ke so."
Bai ce komai ba dan ya san ba ci zata yi ba.
Fita ya yi daga ɗakin ba tare da ya sake wata magana ba.
Bayan kamar mintuna goma sai ga shi ya dawo hannunsa ɗauke da madaidaicin bowl Wanda ke ɗauke da fruits da aka yanka su gutsi-gutsi, sai peck milk da ya juye mata gawangwani ɗaya a ciki.
Ƙarasawa ya yi a gabanta ya ce,
"Ki tashi ki sha."
Haka ta tashi ta ɗauki bowl ɗin da cokali ta fara sha, sai da ta ƙoshi sannan ya fita zuwa office.
Da misalin karfe biyu na rana tana kwance a falo, ta ji ƙarar mota maigadi ya buɗe gate.
Haka kawai ta ji gabanta ya tsananta faɗuwa, dafe ƙirjinta ta yi tare da miƙewa tsaye ta nufi window ta buɗe glass ɗin window dan ganin motar da ta shigo, dan jikinta ya bata cewa ba Adamsy bane .
Ganin waɗanda suka zo ne ta zuba masu ido tana kallonsu, dan bata san daga ina suke ba. A zuciyarta ta ce,
'Waɗannan matan kuma daga ina?'
Yana tsaka da driving a tsakiyar titi, ga ababen hawa suna ta kai da kawo, wayarsa ce ta soma ruri bai yi niyyar ɗaukan kuran ba amma ganin Ummansa ce ta sa ya d'aga yana rike da haya da ɗayar hannunsa ɗayan hannun kuma yana driving da shi.
"Assalamu alaikum, Umma ina kan hanya ne bari na ƙarasa gida zan kira ki."
"Ina jiran ka dan nima gani nan a cikin gidanka na Kaduna."
Bai ankare ba sai ya ji sautin
Gafff!
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaW2Ygg9xVJlgSoy2Q2V
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAHI RAHMANI RAHEEM*
🦋PAGE -----64----&-----65🦋
"Ina kiranka dan nima gani nan a cikin gidanka na Kaduna."
Bai ankare ba ya ji sautin
Gafff!
Sai a lokacin ne ya tuna cewa driving ya ke yi a tsakiyar titi, ta jikin mirror ya hangi go slow da ya haɗa a kan tati.
Fitowa ya ya yi cikin sanyin jiki yana duba motar da ta daki na sa, ba abunda ya samu motar sai dai shi ta sa motar ce aka fasa ma sa danjar baya.
Hakuri ya su sannan ya shige motarsa ya ja tare da barin wajen.
Gefen hanya ya sa mu ya yi parking tare da lalubo lambar wayar Direbansa.
Bugu ɗaya ya ɗauka tare da cewa
"Hello Yallaɓai."
"Kana ina nr?"
"Ina guda Yallaɓai"
"Umma da Amina fa?"
Cikin rashin gane inda zancensa ya dosa ya ce,
"Yallaɓai ban fahimta ba."
"Umma ta ce suna gidana na Kaduna, kuma duk rintse kada ka faɗa mata cewa Humiara matata ce."
Da mamaki ya ce,
"Yallaɓai dama bada sanin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 19