kowa ka je ka yi wani..."
Cikin ɗaya daga murya da zallar ɓacin rai ya ce,
"Shiru!"
Yadda ya ji uban gidansa ya daka masa tsawa ne ya sa ya yi shiru, dan bai taɓa jin ya ɗaga masa murya irin ta yau ba.
"Zaka saurare ni ne ko kuma zaka fara cika mani kunne da maganganun banza marasa amfani;?"
"Tuba na ke yallaɓai."
"Gani nan hanyar dawowa kada Umma ta san cewa Humaira matata ce."
Daga nan ya katse kiran tare da fara driving ya hau kan titin.
A can gida kuwa tunda Umma ta gama waya da Adamsy ne ta kalli Amina ta ce,
"Mu shiga ciki kafin ya ƙaraso."
Dai-dai lokacin da Direban Adamsy ya ƙaraso wajen tare da cewa,
"Yau su Ammi ne a gidan? Sannunki da zuwa Anty Amina."
Yamutse fuska ta yi tare da cewa
"Yauwa."
Jakkar da ya gani Direban Mummy ya fito da shi ne ya ɗauka, tare da akwatin kayan Amina.
Gaba ya yi suka rufa masa baya.
Tana zaune a kan kujera ta haɗa tagumi ta ji ƙarar ƙarar ƙofar.
Ta shi ta yi ta buɗe ƙofar, ta tare da cewa
"Sann da zuwa."
Amina d Mummy kallon juna suka yi ya yin da kowannensu zuciyarta cike da fargaba ba.
Shiru su ka yi ba wa ce zuciyarta ta amsa.
Sa ke ɗaga tambayarta ta yi tana kallon Direba da alama tana neman ƙarin bayani daga wajensa .
"Wace ce ita? Kuma me ta ke yi anan?"
Tashin hankali ta shiga dan ya tasa me zai ce mata, haka kawai sai ya tsinci kansa da cewa
"Mai aiki ce.
"Mai aiki kuma? Ba Mustapha na nan ba?"
"To ai shi Mustapha me girki ne, ita kuma tana share-share da gyaran ɗakuna da dai abinda ba'a rasa ba."
Mamaki ne ya cika Humaira, ganin Irin kallon da ya Umma ke mata ne ya sa ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Mustapha ne ya shiga da kayan ciki sannan Umma da Amina suka rufa masa baya,.
Ita Humaira tsayawa ta yi sororo ta ma rasa makama, ta tsaya wajen kamar an dasa itace.
Har Direban ya dawo bayan a juye masu kayan ya kalle ta ya yi magana a hankali yana cewa
"Dan Allah Madam ki gafarce ni ba ni da wani zaɓi ne fa ce wannan "
Jinjina kai kawai ta yi tare da cewa
"Ba komai."
Daga nan ya fice, itama ta shiga cikin falon.
Shigarta ke da wuya suka ji ƙarar horn ɗin motarsa.
Ajiyar zuciya Humaira ta sauke, dan dama kwata-kwata bata yarda da su ba, tun farkon ɗora idanuwanta akansu.
Amina ce ta kalle ta tare da cewa
"Ke baki san cewa idan anyi baƙi ki basu ruwa ba ne ko ya ya?"
Cikin sanyin muryarta ta ce,
" Ku yi haƙuri, bari na kawo maku."
Tsuki Amina ta ja tare da cewa
"Aikin banza."
Humaira ta nufi kitcheen Umma ta bita da kallo, zuciyarta na raya mata abubuwa da yawa ga me da Humaira, ganin ta zugegiyar mace wacce ta amsa sunanta mace ba namijin da zai kalle ta bai ƙyasa ba.
Gata doguwa mai diri mai kyau, tana da hips da cikakkun ƙirji, fara ce mai dara-daran idanu haɗi da dogon hanci, sai dan ƙaramin tsukakakken bakinta pink color. Ko mace ta kalle ta sai ta ƙara kallonta ballantana namiji.
Jin sallamar Adamsy ne ya katsewa Umma tunanin da ta ke yi.
"Assalamu alaikum"
Wa'alaika salam"
Murmushin ƙarfin hali ya ƙaƙaro tare da cewa
"Sannunku da zuwa Umma."
Amina ce ta maida masa martanin murmushin da ya ke yi masu, tare da cewa
"Sannu da dawowa Yaya"
"Yauwa shine zuwa ko sanarwa babu?"
"Umma ce ta ce mu yi maka ba zata."
Jinjina kai ya ya tare da sunkuyawa ya gaida Umma.
Ta masa masa ba yabo ba fallasa.
Dai-dai lokacin da Humaira ta fito daga kitcheen hannunta ɗauke da faranti da ɗauki robar ruwa da lemukan kwali.
Suna haɗa idanu da Adamsy idanunsu ya sarƙe cikin na juna, gaba ɗaya sun kasa ɗauke idanunsu daga cikin na kowanne.
Umma tana lura da hakan sosai, duk irin kallon d sukewa juna tana kallo, dan ko Amina da ya jima bai saka ta a idanunsa ba bai mata irin wannan kallon ba, sai wannan da kullum suke tare. Jinjina kai Umma ta yaya tare da maganar zuci.
'Hmmm yaro man kaza, idan kunsan wata ai baku san wata ba.'
Humaira ce ta fara cire na ta idanun daga cikin na Adamsy.
Ƙarasowa ta yi tare da durƙusawa ta ajiye masu , ba tare da ta kalli Adamsy ba ta ce,
"Sannu da zuwa"
"Yauwa"
Ya amsa a taƙaice kuma har lokacin bai kalle ta ba.
Jikinta ne ya yi wani irin dan ganin indai ya shigo sai ya rungume ta. Amma yanzu tana gaishe sa ko kallonta bai yi ba ya amsa mata a taƙaice.
Kallon Amina yayi tare da cewa
"Ga abinci can a dinning room, bari na shiga na watsa ruwa."
Har ya mike tsaye akan ƙafarsa yana tunanin yadda zai ce masu wace ce Humaira a cikin gidan, dole ya shiga ɗauki ya yi shawara da Abdallah dan bai san yadda zai ce wa Umma alaƙarsa da Humaira ba.
Tashi ya yi da niyyar zuwa ɗakinsa dan ya yi shawara da Abdallah, kafin ya sanar da su wace ce Haumaira a wajensa.
Har ya kai bakin ƙafarsa sai ya ji muryar Umma tana cewa
"Wannan 'yar aikin da ka ajiye fa a matsayin 'yar aiki fa?"
Dakatawa baya yi tare da juyowa yana kallon Umma ya ce
"Yar aiki kuma?"
Amina ta yi caraf ta ce,
" Mustapha ya sanar da mu cewa 'yar aikinka ce ita j?"
Shiru ya yi yana nazari wato.
'Wato haka Mustapha ya sanar da su kenan? Salon su wahalar masa da mata su takura mata, amma banji daɗin jin haka ba, ina tunanin hanyar da zan bi na sanar da su ashe ya yi ɓaranɓarama.'
Jin shiru ya yi yawa ne yasa Umma cewa
"Akwai wata matsala ce?"
Kai ya girgiza tare cewa
"Ba komai"
Daga nan ya nufi ɗakinsa ya yayin da Umma ta yi wani murmushi wanda ita kaɗai ta san ma'anarsa.
Dan ko a yanzu hakan akwai abinda ta gano a tattare da junansu, dan tun shigowarsa idanunta akansu su duka biyu, dan ko kallon da ya yi wa Amina ita da suka jima basu haɗu ba bai kai kwatan kallon da ya yi wa Humaira ba.
Yana shiga ta maida idanunta ga Huamira ta ga gaba dayan ɗaya hankalinta na kan Adamsy, jinjina kai ta yi tare da cewa,
"Amina ki tashi ki bi mijinki ku gaisa yadda yakamata."
Jinjina kai Amina ta yi tare da cewa
"To Umma "
Ta shi ta yi tare da bin bayan Adamsy ta shiga ɗakinsa ta turo ƙofa.
Haka kawai sai Humaira ta ji kamar an dasa mata wani abu a zuciyarta.
'Kenan dama wannan ita ce matar Adamsy Amina?' To ga shi tana gidan, su kuma an sanar masu cewa ita mai aiki ce, ga shi Adamsy ma bai ƙaryata cewa ita ba mai aiki ce ba matarsa, an faɗa masa ya yi shiru bai ce komai ba, yanzu haka zata cigaba da zama a cikinsu a matsayin 'Yar aiki?'
Haka ta dinga saƙe-saƙe a zuciyarta dan ganar da wannan lamarin.
Jinjina kai kawai ta yi dan tana tausayin kanta da kanta, musamman ma yanzu yadda zamansu zai kasance tare da su. Dan da alamar basu da mutunci.
Tana shiga ta sa me shi tsaye yana ƙoƙarin kiran wayar Abdallah dan ya yi shawara da shi.
Jin ƙarar buɗe ƙofa ya sa ya juya, ganin Amina ce ya sa ya fasa kiran Abdallah.
Rungume shi ta yi ta bayansa tare da cewa
"Nayi missing ɗinka"
"Nima hakan ta ke a wajena."
Murmushi ya yi tare da cewa
"Shi ne kuka zo ko ki sanar da ni cewa kuna hanya ko?"
"Umma ce ta ce mu yi maka bazata."
"Dama wannan ne bazatan da zata Mani."
"Eh."
Murmushi kawai ya yi wanda ita fatar bakinsa ta tsaya.
"Ka watsa ruwan sai mu ci abinci, kasan mu daɗe ba mu ci abinci tare da kai ba "
"Okay"
Ya ce sannan ya nufi bathroom.
"Ko na zo na tayaka ne?"
Girgiza kai ya yi tare da cewa
"Na hutar da ke dan na san cewa ke ma a gajiye kike. Yakamta kema ki je ki ki yi wanka ku ci abinci ki huta."
"Ko na zo muyi wakar tare."
Murmushi ya yi tare da cewa
"Ki je can ɗakin ki yi dan kinga Umma na falo fa ko baki jin kunyar surukarki?"
Dariya ta yi ta fice ba tare da ta sake cewa komai ba.
Kallon Humaira Amina tayi tare da cewa
"Ke!"
Huamira ta juya ta kalle ta ba tare da ta sake cewa komai ba.
"Me ye sunanki?"
"Sunana Humaira."
Maida dubanta ta yi ga
Umma ta ce,
"Umma yanzun me zaisa Yaya ta ɗauki 'yar aiki mace daga ita da sai shi a nan."
Murmushi kawai Umma ta yi tare da cewa
"Ke dai ku zuba idanu ki kalli yadda wasan zai ƙare"
Ta ƙarasa maganar tana wa Humaira wani shu'umin murmushi.
Amina ce ta nufi ɗakin da suka sauka dan watsa ruwa
Bayan kamar mintuna ashirin sai ga Amina ta fito daga ɗakin, ta sauya kayan jikinta daga atamfa zuwa doguwar rigar shadda.
Ƙarawarta ya yi dai-dai da fitowar Adamsy daga ɗaƙinsa, sanye ya ke da ƙananan kaya, wando broun da riga milk colour.
Tunda ya ƙaraso wajen ƙmashin turarensa ya daki hancin Humaira ta ji wani wari ya ke mata, gaba ɗaya bata son ƙamshin turaren.
Toshe hanci ta fara yi wanda ba wanda ya lura da hakan sai Umma.
"Ke Humaira kike ko wa? Tashi ku zuba mana abunci."
Da sauri ta nufi dinning room suka rufa mata baya.
Plates ta fara janyowa da cokula, Umma ta zauna akan kujeran da ke kusa da Adamsy, Amina na facing Adamsy.
Humaira na bud'e foodflask ɗin stew and chicken soup ɗin sai ta ji wari stew ɗin ke mata, ga wani amai da ya tunkaro ta lokaci guda.
A guje ta nufi toilet da ke cikin falon tana kwara amai, ya yi da Adamsy ya bi bayanta cikin tashin hankali.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘
Comments & share
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaW2Ygg9xVJlgSoy2Q2V
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ne ga Jajirtattu Writer's association (j.w.a)
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page6️⃣6️⃣&6️⃣7️⃣
A guje ya nufi toilet da ke cikin falon tana kwara amai, yayin da Adamsy ya bi bayanta cikin tashin hankali.
Sakin baki Umma da Amina suka yi suna kallonsu.
Ba komai cikin cikin nata hakan ta dinga kakari kamar zata amayar da hanjin cikinta. Sai sannu ya ke jera mata akai-akai yana riƙe da kafaɗarta.
Umma ce ta keƙo toilet d'in yadda ta sa me su ya manne mata a jiki kuma ga riƙe da kafaɗarta yana cewa,
"Ko dai mun dawo da tsarabar indiya ne?"
Bayan ta gama ne tana mai da numfashi ta ce,
"Ina tsarabar ta ke?"
"A cikin cikinki mana, na sani ko na kusa zama Baba."
Ya ƙarasa maganar cikin tsanin jin daɗi da farin ciki.
Jin hakan ne ya sa Umma ta toshe baki cike da mamaki, ta juya da sauri ta fice, su kansu basu san cewa ta shigo cikin toilet ɗin ba, dama toilet ɗin yana kusa da ƙofar shigowa falo. dan haka suna ƙoƙarin fitowa daga toilet ɗin shi Abdallah yana shigowa.
Kasancewar toilet ɗin corridor yake ya sa Adamsy na ganin Abdallah ya shigo ya saka shi yin ji hamdala a cikin zuciyarsa, janyo sa ya yi cikin corridor ɗin.
Abdallah ya buɗe baki da niyyar yin magana Adamsy ya yi masa alama da ya yi shiru, cikin mamaki ya kalle shi inda ya ya yi masa raɗa a kunne ya ce,
"Gwanda da Allah ya kawo ka, dama kai ka haɗa wannan cakwakiyar dan haka kai kasan yadda zaka yi ka warware shi."
Ban gane me ka ke nufi ba, ni ina can hankalina ne a tashe wani maƙoci na ke sanar dani cewa wai ya ganka a titi har ka yi accident."
"Manta da wannan Allah ya kare ba abunda ya d sa me ni, yanzu ga Ummata da Amina sunyi mani dirar mikiya."
Da mamaki ya kalle shi tare da zare idanu ya ce,
"Kuma shine kwatsam daga sama cewa ba sanarwa?"
"Wallahi ai dalilin haka ne ina cikin dariving abun ya faru."
"Me ta ce da ta ga Humaira?"
"Dama na gargaɗi Direba akan cewa kada ya sanar da su, maimakon ya yi shiru har sai na dawo shi ne ya je ya ce masu wai 'yar aiki ce, hakan bai mani daɗi ba dan zasu iya wahalar da ita ga shi bata jin daɗi."
Jinjina kai Abdallah yayi tare da cewa,
"Ni banga laifina direbanka ba, dan hakan da ya faɗa ne kaɗai zai sa su yarda hankalinsu ya kwanta. Da me ka ke so a ce masu? Dadironka ce ko me? Ko kuma ace karuwarka? Hakan da ya ce shi ne dai-dai. Da ace sun sanar da kai ne to da ba zaka bari su zo su tarar da ita ba dole ne ka nemar mata wani gida ka ajiye ta dan hakan shine mafita, amma tunda sun tarar da ita ba wace hanya da ta wuce wannan."
Ganin yadda ta ke langwaɓewa ne tare da jingina da bango ya sa Abdallah ya ce,
"Me ke damunta?"
"Amai ta ke yi?"
"Zazzaɓi ne ko me ye?"
"Allah masani, ga shi yanzu ma ba halin na kaita asibiti, bansan yadda zan ce da su ba."
"Wannan abu mai sauki ne shawara da zan baka ita ce, tunda har an riga an sanar da su cewa 'yar aiki na a tafi a haka, sai dai la nuna masu cewa bata da lafiya dan su ɗaga mata ƙafa,sannan kai kuma ka zama mai haƙuri da juriya da kau da idanu akan Humaira.matukar ka kasa cire ifanunka ambata to lallai ne sai asirinka ya tonu . Za'a sake maimaita 'yar gidan jiya dole ka cire idanunka da nuna ko ina kula a gabansu. Idan kuwa ka cigaba da nuna damuwarka akanta har suka gani a idanunka asirinka zai tonu shawara zan baka kenan."
Jinjina kai Adamsy ya yi tare da cewa
"To idan ya kasance da gaske cikin ne da ita kuma Umma ta tambaya da?"
"Sai ka sanar da ita cewa matar aure ce, matar ɗaya daga cikin ma'ikatan gidan nan ne, ya tafi gida ƙauyensu aikin noma ne ita ya barta zai je ya dawo."
Shiru Adamsy ya yi yana kallon fusakar Abdallah tare da cewa
"Na gode Aminin ƙwarai."
Shiga gaba ya yi yana rike da hannun Abdallah, ya bar Humiara a baya saboda Umma da Amina.
Da sallama Abdallah ya ƙaraso falon Umma da Amina suna zaune a dinnig room sun kammala cin abinci.
Amsa masa sallamar suka yi cikin fara'a Umma ta fara magana
"Marhaba waye na ke gani kamar Abdallah?"
Murmushi ya yi tare da cewa
"Ni ne Umma"
"To Bisimiillah ƙaraso ga abinci ko?"
"Alhamdulillah Umma daga gida na ke."
Durƙusawa ya yi ya gaida Umma cikin girmamawa, ta amsa masa cikin sakin fuska da walwala.
Tasowa suka yi daga dinning area suka ƙaraso falon, Amina ma ta gaishe shu.
Zama suka yi akan kujera Umma na sake tambayarsa iyalinsa ya tabbatar mata da cewa suna lafiya, ya kuma yi mata alƙawarin zai kawo ta ta gaishe da su.
Idanun Umma ne suka sauka akan Humaira da ta zauna akan carpet, ta jinjina bayanta da kujera tana lumshe idanu. Tunawa ta yi da lokacin da ta leƙa toilet Humaira na amai ta gansu manne da Adamsy na cewa;
"Ko dai mun dawo da tsarabar indiya ne."
Wani murmushi Umma ta yi wanda ita kaɗai ta san ma'anarsa, kallon Humaira ta yi tare da cewa
"Ƴata zo nan."
Humaira ta kalle ta kasancewar ta san ita ce mahaifiyar mijinta dan haka ta tashi ta nufi inda Umma ta ke ta zauna a gabanta can center carpet.
"A'a ta so zo nan ki zauna 'yata"
Ta ƙarasa maganar tana nuna mata gefenta ta zauna, Kasancewar doguwar kujera ne ta ke zaune a kai. Kai Humaira ta girgiza mata tare da cewa Umma nan ma ya yi.
Bata sa ke mata magana ba sai dai ta janyo ta tare da zaunar da ita gefenta ta yi mata filo da cinyarta.
"Sannu ko? Me ke damunki?"
Humaira dai shiru ya ba tare da ta ce komai ba, inda Umma ta cigaba da
"Me zaki ci ne na ga kinyi amai ko?"
Zuciyar Adamsy fal da farin ciki, inda ya yi saurin cewa
"Ai Umma bata iya cin komo yanzu sai dai Fruits salad kuma..."
Abdallah ne ya ɗan daki ƙafarsa da dabara hakan ya sa bai ƙarasa maganar da ya ke yi ba, ya kalli Abdallah, da ke masa kallon wata tambaye ka.
Shiru ya yi inda sai a lokacin ya fahimci ɓaran ɓaramar da ya ke ƙoƙarin yi.
"Ina zuwa ko?"
Umma ta faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin kwantar da Humaira a kan kujera, a kan kujera.
Kitcheen ta nufa kai tsaye Amina dai sai kallonta ta ke tana mamakin canzawarta.
Bayan mintuna sai ga ta ta dawo hannunta ɗauke da wani madaidaicin bowl wanda ta haɗo mata haɗin youghurt Fruits wanda ya ji madara. Ɗaya hannunta kuma farantai ne da aka yayyanka Fruits fa fork ta kawo mata.
Murmushi ta sakar mata tare da cewa
"Tashi ki samu abunda kika saka a ciki ko?"
A hankali ta tashi zaune ,inda Umma ta fara miƙa mata bowl ɗin ta fara sha.
Ta sha ya kai rabi kafin ta ajiye alamar ya ishe ta. Miƙa mata farantin Umma ta yi tare da cewa
"Ki ci wannan ko?"
Bata iya mata musu dan haka sai ta karɓa ta fara sha.
Ƙaɗan ta ci, apple yanka ɗaya sai kankana da abarba suma yanka ɗaya ta ci kowane sannan ta ce,
"Umma na ƙoshi"
Murmushi ta yi tare da cewa
"Shikenan."
Ajiye sauran ta yi akan Centre table da ke gabanta.
Janyo Humaira ta yi tare da sake kwantar da ita a cinyarsa.
Amina ce ta kalle ta ta ce,
"Wai me ke damunta ne?"
Umma ce ta kalli Adamsy tare da cewa
"Ina ka samu yarinyar nan ne? Gata yarinya ce ƙarama bata jin daɗin jikinta."
"Umma ai matar aure ce."
Da mamaki Amina ta kalle ta kalle shi tare da cewa
"Wannan matar aure ce? To ne ta ke yi a nan? Ina mijinta ya ke."
Mijinta ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan nan ne, ya tafi aikin gona ne a ƙauyensu, shine ta barta dama ita ta ke aiyukan cikin gidan."
Taɓe baki Amina ta yi tare da cewa
"To ina ta ke zaune?"
Nuna mata ɗakinta ya yi da mamaki ta buɗe baki tana kallon ɗakin, kishinta ne ya motsa inda ta ke cewa
"Ta ya ya za'a ce wai tana matar aure amma ba za'a ware mara wani ɓangare a cikin gidan nan ba sai ɓangaren mai gidan? Kuma ba kowa a ɓangaren daga shi sai ita? Wai wan..."
Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon hannu da Mummy ta ɗaga mata, alamar dakatarwa.
Sai cika ta ke tana batsewa tana kallon Humaira yadda ta ke kwance idanunta a lumshe, gani ta yi kyau dai iya kyau idan aka zo kan Humaira zance ya ƙare, dan ko ita ta halicci kamata iyakacin abinda zata yi kenan.
Humaira kam idanunta ta lumshe zauciyarta cike da takaicin zancen Adamsy, wato ita ce ya ke cewa wai matar wani ko? Maganar zuci ta fara.
'To me ye zai sa ya ɓoyewa mahaifiyarsa cewa ita matarsa ce? Saboda bata cancanci zama matarsa ba ko saboda me ne ne?'
Haka aka cigaba da fira sama-sama har barci ya ɗauke Humaira.
Abdallah ne ya yi musu sallama zai tafi, inda Adamsy ya raka shi har mota sannan ta dawo
Daddare ma bayan Mustapha ya gama girki ya jera a dinning table ya tafi ne Amina ta fito daga ɗakin Adamsy ta nufi ɗakin Umma.
Da sallama a bakinta ta shiga ɗakin, inda ta samu Umma na ta kai da kawo, sai Safa da marwa ta ke yi, Amina ta kalle ta tare da cewa
"Umma lafiya kuwa?"
"Ba komai me kika gani?"
"Na ga ne gaba ɗaya kin kasa nutsuwa."
"Kada ki damu ba komai"
"Na ga baki fito cin abinci ne?"
"Gani nan zuwa."
Dai-dai lokacin shina Adamsy ya shigo ɗakin bayan ya yi sallama sun amsa masa.
Gaida Umman ya yi tare da ta tambayarta ko akwai wani abu ne, ta nuna masa cewa ba komai.
Gaba dayansu suka fita zuwa wurin cin abinci, gaba ɗaya hankalinsa na ga Humaira, amma ba halin ya je wajenta.
Umma ce ta kira Mustapha tare da ba shi umarnin ya haɗo Fruits salad, da kanta ta nufi ɗakin Humaira.
Da sallama ta tura kofar inda ta samu Humaira na barci a saman sallaya. Da alama tunda ta idar da sallar isha'i ne bata ɗaga daga wurin ba.
Ƙsrasawa ta yi tare da taɓa goshinta sai ta ji muryar Humaira na cewa
"Dan Allah ka rabu da ni barci ne ke ji."
"Tashi mana 'yata."
Ta shi ta yi jin ba muryar Adamsy ba ne.
Ta shi ta yi zaune Umma ta cire mata hijabin tare da janyo hannunta, a hankali suka nufi ƙofar fita.
Zaunar da ita ta yi akan ɗaya daga cikin kujerar da ke wajen.
Haɗa idanu suka yi da Adamsy, idanunta ne da nasa suka sarƙe cikin na juna. Kafin ta ɗauke idanunta daga gare shi.
Fruits salad da Umma ta sa aka haɗa mata shi ta bata.
Kowa na cin abinci sai ita kawai da bata iya ci.
Umma ne ta kalle ta tare da sakar murmushi.
"Yata ko na zuba maki abincin kaɗan ne?"
Girgiza kai ta yi tare da cewa
"A'a Umma na gode."
Ta shi ta yi ta koma falo dan abincin ma bata son jin ƙamshinsa.
Umma na lura da ita bata ce komai ba. Bayan ta kammala sha ne ta kai bowl ɗin kitchen inda ta dawo falo ta tarar da Umma tana falon.
"Umma zan je na kwanta"
Murmushi ta yi tare da cewa
"Tun yanzun?"
"Eh Umma barcin na ke ji."
"To ki kula da kanki ko?"
Jinjina kai ta yi ta ce,
"To Umma."
Sai da safe ta mata sannan ta kalli ɓangaren da Amina ta ke ta ce,
"Anty sai da safe."
Ba yabo fa fallasa ta amsa mata da
"Allah ya tashe mu lafiya."
Tana zuwa ta yi alwalar kwanciya barci sannan ta fito ta haye gadon bayan ta yi addu'ar kwanciya barci.
Umma ma ɗakinta ta shige inda Amina ta ja hannun Adamsy suka nufi ɗakinsa.
Haka suka cigaba da kasancewa a gidan Umma na bawa Amina kula sosai, yayin da Adamsy ke jin daɗin hakan.
Tsawon sati ɗaya kenan Adamsy na son keɓewa da Humaira ba dama, saboda Umma ta kasa ta tsare kuma kullun Amina a ɗakinsa ta ke kwana, kuma duk lokacin da ya yi sex da ita baya jin gamsuwar da ya ke samu daga Humaira.
Dan haka yau ya ƙudira a zuciyarsa sai ya shiga ɗakin Humaira a daren yau, dan ya ji kewarta sosai, yana son yau sai ya ɗanɗani zumarta da ya kwana biyu lashe ta ba.
Dan haka da misalin karfe ɗaya na dare Amina na barci ya zame jikinsa ya nufi ƙofar fita.
A falo kuwa Umma ke safa da marwa ta kasa sukuni, kai komo ta ke ta yi.
Adamsy ne ya fito daga ɗakinsa kai tsaye ya nufi ɗakin Humaira, Umma na ganinsa ta yi saurin matsewa da jikin bango. Tana kallonsa ya shiga ɗakin ya turo ƙofar ya rufe.
*Daga alƙalamin*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘Pls haFollow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaW2Ygg9xVJlgSoy2Q2V
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ne gare ku masoyana, masu ƙaunar rubutuna, na yaba kuma na gode da irin addu'oi da kuke mani Allah ya bar ƙauna. I love you lodi-lodi😘😘
*End of book 1*
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page6️⃣8️⃣&6️⃣9️⃣
Adamsy ne ya fito daga ɗakinsa, kai tsaye ya nufi ɗakin Humaira. Umma na ganinsa ta yi saurin matsewa da jikin bango. Tana kallonsa ya shiga ɗakin ya turo ƙofar ya rufe.
Mutuwar tsaye ta yi tana kallonsa, mamaki da al'ajabi ne duk suka bi suka ishe ta.
Koda ya shiga ɗakin Humaira na barci a tsakiyar gado, kasancewar bata kashe hasken ɗakin duka ba ta dai rage ne. Kashe hasken ya yi gaba ɗaya sannan ya haye gadon tare da shigewa cikin bargon ya janyota jikinsa.
Farkawa ta yi cikin tsoro da niyyar buɗe baki ta yi ihu ne ta ji ya saka bakinsa cikin nata, ya fara tsotson bakinta cikin salonsa wanda hakan ya sa ta gane cewa shi ne.
Cire
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 19