jiki tsoron Allah, ki sani fa ko baki da alaƙa da yarinyar nan yadda ta ke maki talla safe rana yamma ai ki bata abincin da zata ci, ko da ladan tallar da zata maki ne ai zata ci ta koshi a gidan nan."
Wani irin dariya ta sheke da shi tare da cewa
"Shikenan tunda haka ka ce, Allah ya kiyaye hanya."
Tunda ya ji ta faɗi haka yasan akwai abunda take nufi da zancenta, dan da wata manufa ta yi maganar. Sai dai bai isa ta ji maganarsa ba dan yasan idan ya tafi Humaira sai dai ta yi hakuri amma Inna Habi sai ta ninka azabar da take bata.
Hanyar fita ya nufa Humaira tabu shi a baya. Suna cikin tafiya ya kalle ta ya ce,
"Humaira ki ƙara hakuri da Habi fiye da wanda kike yi a baya, nasan cewa tana azabtar da ke amma ki cigaba da haƙuri wata rana sai labari, kinga nima yadda nake haƙuri da ita ballantana ke, lokacine zai wuce da yardar uban giji."
"To Abba ka tafi da ni can gidan da zaka koma mana, kaga bata gani na ballantana ta dinga duka na, Abba wallahi tsoro nake ji idan baka nan."
"Ki wantar da hankalinki, ba abunda zai sake ki sai alkhairi."
Jinjina masa kai ta yi idanunsa cike da ƙwalla.
"To ba zaki koma gida hakanan ba?"
"A'a ina so na je naga gidan da kaina."
"Gidan ba ba anan unguwar ya ke ba, kuma idan kinsan gidan me zaki yi? Bana so ki biyo hanya ke kaɗai."
"Abba ni da na saba tafiya unguwa zuwa unguwanni a garin nan."
"Me kike zuwa yi?"
Tallar doya da Inna ke ɗora mani."
Jikinsa ne ya yi sanyi, ya kalle ta ya ce,
"Humaira bana son ki dunga yawan tallace-tallace unguwanni, dan yanzu duniya abin tsoro ne."
"Abun hawa kike hawa ko?"
"A'a Inna Bata yarda na ɗauki kuɗi na hau abun hawa, sai dai na tafi da ƙafa."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un."
Shine kalmar da ya furta tare da kallon Humaira cikin tausayinta ga idanunsa har sun kaɗa zuwa ja.
"Kiyi haƙuri kinji dukkan tsanani yana tare da sauƙi."
.kai ta jinjina suna kawowa titi suka samu abin hawa suka shiga.
Bayan sun isa ƙofar gidan ne, kamar yadda aka sanar da shi, wayarsa irin wacce ake kira da rakanu kashi ya ciro, wayar ba murfi sai ribali da aka ɗaure ta da ita, gudan kada batirinta ta fita.
Lambar wayar Mallam Kallamu ya lalubo tare da sannan masa kira, bugu biyu ya ɗaga inda ya shida masa tana ƙofsar gidan.
Nan Mallam Kallamu ya shaida masa cewa ya knocking gidan maƙocinsu, an bawa mai gadin gidan maƙocinsu key idan ya zo a bashi.
Kallon Humaira yayi ya ce,
"Bari na ƙarasa wannan gidan nan na karɓo makullin."
Kai ta jinjina masa tare da cewa
"To"
Kai tsaye ya nufi gidan inda ya yi knocking aka buɗe, nan ya ke gabatar da kansa, inda mai gadin ya bashi key, sallama ya masa ta dawo ya buɗe gate ɗin gidan suka shiga.
Sakin baki Humaira ta yi tana kallon tsarin gidan.
Mallam Musa ya nufi ɗakinsa da ke nan kusa da gate na shigowa.
Babban ɗaki ne sai toilet a cik an zuba masa komai har da gado da kujera, ga kuma kitchen.
Sakin murmushi Humaira ke yi tare da cewa
"Abba yanzu shikenan a gidan 'yan gayu zaka dinga zama? Abba kalli da gidan kamar a ƙasar turai."
Dariya Mallam Musa ya yi tare da cewa
"Humaira kina da abun dariya."
"Eh mana Abba kalli yadda gidan ya haɗu, ina masu gidan."
"Mai gidan yana hanya bai iso ba tukuna."
"To matar gidan fa?"
"Humaira ina zan sani tunda yanzu na fara shigowa gidan."
Zama suka yi a barandar gidan fira suke.
Horn ɗin mota suka ji da sauri mallam Musa ya tashi ya je ya leƙa,hangen motar manaja yasa ya buɗe gate da sauri,motar manaja ta shigo sai kuma wata rantsatstsiyar mota ta biyo bayanta.
A wajen da aka tanada dan parking suka nufa, wanda suna tsayawa manaja da wannan direban ɗayar motar suka fito a tare har rige-rige suke wajen haɗe bayan ɗayar motar.
Suna buɗewa sai ya sako ƙafarsa ɗaya waje, Mallam Musa da Humiara ƙafarsa suka zuba wa ido, da ka kalli farar ƙafarsa kasan hutu da jin daɗi sun zauna masa.
Ɗayar ƙafar ya fito da ita a hankali cikin yanayinsa na damuwa da yake damunsa da rashin walwala.
A hankali ya fito daga cikin motar ya fara tafiya zuwa hanyar da zata sada shi da ƙofar falon,Mallam Musa da Humaira sai binsa suke da idanu har ya ɓacewa ganinsu. Yayin da manaja da Direbansa suke binsa a baya.
Humaira ce ta kalli Mallam Musa ta ce,
"Abba wannan farin mutumin shine mai gidan ko?"
"Eh shine "
Sake jefa masa wata tambayar ta yi
"Amma shi ɗan wani ƙasa ne?"
"Kamar ya ɗan wane ƙasa ne."
"Nagansa fa kamar na ɗan Nigeria ba, baka ganshi fari ba ga gashinsa ma irin na larabawa baki laɓɓansa ma sunyi ja kamar irin na mutanen indiya da muke kallo a T.V. "
Tsayawa ya yi yana kallonta da mamaki ya ce,
"Kin cika surutai da yawa , ki zo ki koma gida yanzu."
Ta ke fara'ar fuskarta ya ɗauke, dan ji ta ke kamar lahira ya ce ta tafi.
Kuka ta yi daƙyar ya lallaɓata har ta yarda zata tafi.
Kuɗi ne ya ke da ita Naira ɗari biyar 'ya ɗari guda biyar.
Ya bata ɗari biyu ya maida ɗari uku a aljihunsa.
Haka ta fita cikin sanyin jiki da rashin kuzari.
Umma ce ta shigo gidan Amina a falo ta tarar da Amina zaune tana cin abinci.
"Nan kika fi auki ai, a, sakarai sha sha sha wacce bata san ciwon kanta ba."
"Umma lafiya ko sallama babu?"
"Dalla rufe mani baki wace laflya kuma, ai zaman lafiyarki ya kare tunda har kika yi gangancin rashin bin Adamsy Kaduna."
"Umma ba yadda zanyi ya faɗa mani cewa wai ba zai tafi da ni ba."
"Ba zaki tayar masa da hankali ba?"
"Umma Wallahi kamar yadda ya ɓata mani rai haka shima da ɓacin raina ya tafi."
"Aikin banza da wofi, ai tunda baki iya binsa ba magana ya ƙare, kuma bari ki ji tafiyarsa shi kadai ita ce babbar faɗuwarmu, ki rubuta ki ajiye"
"To Umma ya aka yi kika san wannan wa ya faɗa maki?"
Ba ruwanki Idan da kin shiga motar ki ce sai ya tafi da ke ko ki tayar masa da hanakali sai dole zai tafi da ke."
"Umma to yanzu me ye abinyi"
"Abinyi sai ki ci ki kwanta kiyi barci tunda shine amfaninki tunda baki san ciwon kanki ana nuna maki annabi kina rufe idanu."
Daga nan ta fice ranta a ɓace, tana tunanin hanyar bi Adamsy dai na Kaduna.
*Kuyi haƙuri da wannan ba yawa kuma uzuri na jina shiru kwana biyu uzuri ne*
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DuXNzdLkDfm1U0dZg9YE73
*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*
*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*
Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.
Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.
Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩
1. Gumban kwakwa da madara
2. Original tsumin Tabani ka ji ruwa
3. Original tabaje
4. Sweetener powder
5. Sweetener milk
6. Dilka soap
7. Snow whitening soap
8. Morroccan whitening soap
9. Pure sha butter
10. Special yaji and more
Ina matan da suke son su zama na musamman agun oga,in nace ta musamman ina nufin karshen_ karshen ta musamman ajin farko ..... To ku matso nan kuji Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯.
*YAR GIDAN TAFIDA*
Tana da alaidi
Akwai pure man kadai
Akwai gumba ta madara da kwakwa
Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍.
*Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects.
Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM*
Page2️⃣4️⃣&2️⃣5️⃣
Daga nan ta fice ranta a ɓace tana tunanin hanyar bi, Adamsy na Kaduna.
Bayan Haumaira daga gidan Adamsy ne sai Mallam Musa ya nufi hanyar da ya ga su Adamsy sun nufa.
Daga cikin gidan kuwa Adamsy na zaune a falo kan sofa, yayin da aka cika masa gabansa da kayan ciye-ciye, manaja da Direbansa suna tsaye a gafensa.
Mallam Musa ya yi knocking ƙofar, manaja ne ya ƙarasa wajen ya buɗe masa ƙofar.
"Mallam Musa kaine?"
"Eh ni ne ranka ya daɗe, na zo na gaida yallaɓai ne na masa sannu da zuwa."
"To bari a sanar da shi ko?"
"To ba damuwa."
Mallam Musa ya tsaya yana jiran a yi masa ido, yayin da manaja ya shiga ciki.
Ya sanarwa Adamsy zuwan Malam Musa U gaisa, inda Adamsy ya bashi izinin shiga da shiga da shi.
Bayan Mallam Musa ya shigo ne zai durƙusa ya gaida Adamsy sai Adamsy yayi saurin dakatar da shi.
"A'a Baba dan Allah kada ka durƙusa mani ɗanka ne ni. Ni ne ya kamata na durƙusa maka ba kai ne zaka durƙusa mani ba, ni ya kamata na durƙusa maka."
Mallam Musa sai ya ga girma, karamci da mutunci irin na Adamsy.
"Sannu da zuwa yallaɓai."
"Yauwa sannu Bana."
Mallam Musa ya ce,
"Ina wuni Yallaɓai."
"Lafiya lau Baba, amma dan Allah ka daina kira na da yallaɓai ko kuma ranka ya daɗe."
"Ka kira ni da Adam."
"To shikenan yadda ka ce haka za'ayi."
Jinjina kai ya yi tare da cewa
"Masha Allah."
Fatan ka iso lafiya, ya hanya?"
"Alhamdulillah"
Manaja ya kalli Adamsy ya ce,
"Sir wannan shine mai gadin da aka samo."
"Okay, yayi."
Daga nan Mallam Musa ya ta shi ya koma bakin gate.
Bayan ya Mallam Musa ya fita ne Adamsy ya kalli Direbansa ya ce,
"Zaka iya wucewa ka huta."
Diraban nasa ya yi masa sallama ya fita inda ya nufi wani ƙaramin sashe da ke bayan na Adamsy.
Kallon manaja ya yi tare da cewa
"Zaka iya tafiya, ina buƙatar hutu."
Sallama manaja ya masa sannan ya fita.
Yana fita Adamsy ya nufi bedroom nasa, inda kai tsaye ya nufi bathroom.
Wanka ya yi sannan ya fito sanye da white bathrobe a jikinsa, tsane ruwan kansa ya yi da wani ƙaramin towel.
Lotion nashi mai kmashi da tsada ya bauɗe ya na shafawa, wayarsa ce ta yi ringing. Bai kuka ba ya cigaba da abinda ya ke yi.
Bayan ya gama ne sai ya saka wata karamar riga da da wando 3 quater ya saka, inda ƙiruciyarsa da da haibarsa suka fito.
Turarruka mai ƙamshi ya shafa sannan ya ƙarasa haye gadon tare da ɗaukar wayarsa, kishungiɗa ya yi ya duba wayar sai ya ga number Abdallah ne ya Kira shi, murmushi ya yi tare da cewa
"Kamar yasan na iso?"
Danna masa kira ya yi inda ya daga a bugu ɗaya.
"Hello Abokina kai iso ne?"
"Eh yanzu na iso."
"Okay to gani nan zuwa."
Daga nan ya katse kiran wayar.
Lambar Umma ya lalubo, ya danna mata kira.
Bayan ta ɗaga ta ke cewa
"Assalamu alaikum. Babana yanzu nake shirin kiran lambar wayarka, ashe kiran naka na kan hanya."
"Eh Umma ne ce bari na kira na sanar da ke cewa na isa lafiya."
"Ayyah na isa Ummata."
Fira suka ɗan taɓa sannan suka yi sallama ta ya katse kiran.
Wayar Amina ya kira sau uku tana ringing bata ɗaya ba, dan haka sai ya share ta, ya san dai yanzu wayarta na tare da ita.
Ta shi ya yi ya koma falo, kai tsaye ya nufi dinning area, inda manaja ya masu odan abinci masu rai da laflya.
White rice and chicken soup ya ci bayan ya ci kamar rabin abincin ne sai ya rufe sauran dai-dai lokacin da ya ji horn, alamar cewa abokinsa Abdallah ya iso.
Bayan kamar mintuna uku ya ji knocking, shi a tunaninsa Abdallah ne ya zo sai ya ke tambayar kansa.
"Yau kuma wani sabon salo ne ka zo da shi? Da can da kake zuwa ka taɓa knocking ne? Ba shigowarka ka ke yi kai tsaye ba?"
Dan haka sai ya share sa sai da ya ji an sake sannan kararrawar ƙofar ya yi magana da ƙarfi.
"Dalla Mallam idan zaka shigo ka shigo, da can ba kai tsaye ka ke shigowa ba?"
Sai a lokacin aka buɗe ƙofar aka shigo, Mallam Musa ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaika salam, Baba kai ne?"
"Eh ni ne wani baƙo ne ya zo kasancewar ban sanshi ba ya sa ban buɗe masa gate ba, na ce sai na sanar da kai, wai sunansa Abdallah."
Murmushi ya yi tare da cewa
"Abokina ne Baba, a faɗin. Kaduna bani da wani abokin sama da shi."
Jiki na rawa Mallam Musa ya fita dan ya ji ance babban abokin mai gidan ne.
Bayan ya same shi ya buɗe masa gate ya shigo da motarsa ne ya ƙarasa jikin motar.
Bayan Abdallah ya fito daga motarsa ne Mallam Musa ya kalle shi ya ce,
"Dan Allah kayi haƙuri, ban san cewa kai amimin mai gidan bane, na yi laifi."
Murmushi Abdallah ya yi tare da cewa
"Kada ka damu na san aikinka ne ka ke yi, kuma hakan da kayi dai-da ne."
Daga nan bai sake magana ba ya wucewarsa cikin gidan.
Da sallama ya tura kofar falon ya shaga.
Adamsy har lokacin yana zaune a dinning room dan haka shima Abdallah ya nufi dinning area.
Tashi tsaye Adamsy ya yi inda suka rungume juna suna dariya fuskar kowannensu ɗauke da farin ciki.
Bayan sun zaune ne Abdallah ya ce,
"Na yi farin ciki sosai da dawowarka nan. Fatan dai komai lafliya ya Umma da madam?"
"Duk suna lafliya."
"Ai na ɗauka tare da Madam kuke."
Kai ya girgiza tare da cewa
"Ni kaɗai ne."
"Amma da ka zo da ita, ta ya ya mai mata zai koma gwauro?"
"Abdallah ina da damuwa ne, kuma ina bukatar na ga na kaɗaice ni kaɗai ba tare da kowa ba."
"To kuwa kaɗaici ba abunda zai haifar maka face yawan tunani da damuwa."
Ajiyar zuciya kawai kawai Adamsy ya sauke inda Abdallah ya cigaba da cewa
"Wai yanzu matayenka guda nawa ne?"
Harara ya gallawa Abdallah sannan ya ce,
"Ban sani ba."
"Sorry friend ka san na je dai ɗaurin aurenka sau uku, bayan su ban sake zuwa ba, kuma ko wanda ban je ba na san zasu kai uku. Yanzu duk kana nufin ba ko ɗaya a gidanka?"
"Wai me ya haka Abdallah akwai sanin kanka ne cewa ba abinda na ɓoye maka, duka matayen nan da ka sani ba wacce mu ka yi zaman aure da ita, wasu a ranar ɗaurin auren ake fasawa guda biyu ne aka kawo su gidan suma zamana mintuna uku banyi da su a ɗaki ɗaya ba."
Tsuki ya ja tare da cewa
"Dan Allah Abdallah ka daina dawo mani da abinda ya wuce, shi ya sa na dawo garin nan dan bana son na dinga tuna baya."
Shiru ya yi tare da cewa
"Ka yi hakuri Adams, na san yadda kake ji ace ka auri mata sama da guda biyar ba wacce ta zauna da kai? Gaskiya wannan abun ba banza ba akwai wata a ƙasa. Dan duka auren soyayya kuma yi da su ballantana a ce ko dan basu sanka ne , kuma akasarinsu sune suka fara neman soyayyarka kaga kuwa karshen so kenan, tunda har mace zata iya cire kunya da bayyana maka irin son da ta ke maka, rabuwa da mai ba abu bane mai sauƙin a gare ta. Dan haka ka bincike lamarin nan amma ruwa baya tsami banza."
"Koma dai me ne ne ya zo ƙarshe bani ba sake auren jinsi wata 'ya mace."
Abdallah zai yi magana kenan sai Adams ya dakatar da shi ta hanyar cewa
"Kana fama mani tabon da ke zuciyata ne,dan Allah wannan maganar ka ɗauke shi ka yi jira da shi baya kada ka sake waiwayarta."
Jinjina kai Abdallah ya yi tare da cewa
"Shikenan tunda haka ka ce."
"Ina madam da kuma yara?"
"Duk suna lafiya suna gaishe ka."
"Masha Allah Ina amsawa."
Daga nan fira suka cigaba da taɓa wa inda har Abdallah ke cewa
"Ina ka samo wannan mai gadin ne, yana da hankali da kamala."
"Manaja ne ya sa aka kawo shi, nima dawowa ta na tarar da shi. Daura na sa a nema mani mai wankin motoci da bawa fulawa ruwa."
"Wannan kam ba matsala ba ne a yau aka nema za'a samu."
"Ga abinci nan fa ka ci ga abun sha "
Girgiza kai Abdallah ya yi
"Am okay."
Adamsy ya kalle shi ya ce,
"Bari na miƙawa mai gadin nan abinci."
Ɗaukar leda ɗaya ya yi na takeaway da robar ruwa da na lemu ya kai wa Mallam Musa.
Malama Musa ya ji dad'in hakan sosai.
Humaira na komawa gida kuwa ta tarar da Inna Habi sai zazzaga mata masifa ta ke yi.
"Wato ke da uwarki daga kan kije ki wa ubanki rakiya shine kika je kika shantake ko?"
"Kiyi hakuri Inna unguwar ce da nisa."
Dariya ta yi tare da cewa
"Albishirinki, daga yau zaki fara tallan tuwon dare."
"Tuwon dare kuma Inna?"
Ƙwarai kuwa dama na san ubanki bazai bari bane shi ya sa ban yi ba, amma yanzu tunda baya nan, yau zamu fara."
Kallon Inna Habi ta ke baki sake wato ita dai bata da lokacin hutu, da asuba ta je ɗibar ruwa da safe tallan koko, da rana tallan doya sannan ga dare kuma tallan tuwo.
Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, ganin haka ya sa Inna Habi ta ce
"Au kuka kike yi?."
Gadan-gadan ta nufi inda Humaira ke tsaye ta daga hannu ta sauke mata tagwayen maruka biyu, sannan ta cigaba da jibgarta tana ihu tana neman taimako, ba mai taimaka mata.
Sai da ta mata lilis da duka sannan ta barta.
"Ki ta shi ga wanke-wanke can ki wanke su tun ɗazu suke jiranki."
Daƙayar ta iya tashi ta nufi wajen da aka jibga kwanikan wanke-wanke sannan ta buɗe randa da niyyar ɗibar ruwa da za ta yi wanke-wanke da su ta ji an daka mata tsawa.
"Ke!"
Da sauri ta juya tana kallon Inna Habi wacce ta saka mata tsawar.
"Kada ki kuskura ki ɗebi ruwan gidan nan, sai dai ki je can rijiyar ƙofar gidan Barumi ki ɗabo ruwa."
A hankali ta ke tafiya dan jikinta ciwo ya ke mata, ga wurin da ta ƙone da wuta ranar da Inna Habi ke dukanta da itacen wuta, ta kone ta a gafen ciki kuma har yau tana jin zafin wurin.
A haka ta fita ta yi tafiya mai ɗan tsayi sannan ta ƙarasa rijiyar.
Guga ta ɗauka ta zura cikin rijiyar, zata jawo kenan sai taga an janyo mata, ɗaga kai ta yi dan ganin waye.
Salman ta gani tsaye yana kallonta yana murmushi.
"Je ki zauna ko huta zan ɗebe maki ruwan."
Jan gugan ta yi tare da cewa
"A'a ka barshi zan ɗiba da kaina."
Ta ƙsrasa maganar tana tsuke fuska, dan ta lura da takensa yana yawan shiga lamarinta.
Haka suka dinga jayayya da shi, da ta ga alamar ba zai barta ba, kuma zai ɓata mata lokaci ta sake shan wani duka, hakan ya sa ta sake masa gugar ya dinga janyo ruwan yana zuba mata har bokitin ya cika.
Ta ɗauka tana shirin ɗorawa a kanta ya yi saurin ɗauka ya riƙe a hannunsa.
Sanin cewa ba bata zai yi ba yasa ta bin bayansa, yana riƙe da bokitin a hannunsa.
Haka ta cigaba da rayuwa cikin ƙunci da baƙin ciki.
Kullun ƙarfe huɗu na asuba zata tashi, idan bata Inna Habi ta kwara mata ruwa, dole ta farka. Ta tafi ɗaban ruwa bayan ta dawo ta yi sallah zata fara sharan gida da wanke-wanke idan kayan Salma da Habi sun taru ita zata wanke ta masu. Sannan ta dama koko ta tafi talla, idan ta siyar ta dawo ta wanke kayan da ta dasu robobin da ludaya. Sannan zata fere doyar da zata tallah da rana, bayan ta dafa ne ta yi wanka zata tafi talla. Kuma ko ta dafa doyar Inna Habi shi zata ci da rana, Salma ma shi zata ci amma ita ko yanka ɗaya na doyar ba za'a bata ba, hala za'a lissafa mata idan kuwa kuɗin ɗaya ya ɓace sai ta sha duka kamar za'a kashe ta.
Idan ta dawo tallar doyar ba abinci wata rana Inna zata ce mata wai ta bari sai an gama abincin dare sannan ta ci, wata rana a ce ta a ce ta siyo gari ba sugar ta sha. Sannan ta fara shirin zuwa tallar tuwo bayan sallar magrib. Tunda Mallam Musa ya bar gidan shikenan komai ya sake tsanani ga Haumaira, Salma kam ta sai iko da mulki ta ke nuna wa Haumaira, dan sai abinda ta ce da ita. Kuma duk aikin da ta saka ta bata dole sai ta yi mata shi.
Mallam Musa ma yana samun alkhairi a wajen Adamsy dan sosai ya ke bashi kyaututtukan kuɗaɗe, ba wai sai albashi ba.
Wata rana Humaira ta dauki tallar doya ta fita, tana tsaka da tafiya kafin ta kai bakin titi tsautsayi wasu samari su biyu a saman mashin sun gudu suke zaubawa, jin sautin mashin ɗin yasa Humaira ta waiga, tana waigawa kafin ta ankare sun kaɗe ta da mashin ɗin ta faɗi a wajen robar doyar ta farfashe.
Wanda aka goya a bayan ne ya cewa na gaba
"Kayi sauri mu gudu"
Dan haka suka gudu suka barta kwance a wajen.
Wata mata ce da zuwa ta hange sanda suke wucewa da gudu ta ƙaraso ashe ma ta san Humaira.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Humaira zaki iya tashi kuwa?"
Hakan ya sa ta yunƙura da taimakon matar ta tashi. Ganin yadda robar doyar ya ragargaje ne matar ta ce tabar shi tunda ga doyan duk sun watse a ƙasa.
Daƙyar ta ke tafiya har suka ƙarasa gidan, da sallama suka shiga, Inna Habi har ta buɗe baki zata amsa ganin yadda aka shigo da Humaira ba doya sai ta sura wata irin ashariya.
Jin haka ya sa Humaira ta ƙanƙame matar tana kuka, ganin haka ya sa matar ta dinga ba wa Inna Habi haƙuri.
Murmushin yaƙe Inna Habi ta yi ta nunawa matar ba komai, har matar ta yi godiya ta tafi.
Bayan fitar matar ne Humiara ta korawa Inna Habi bayanin abinda ya faru ta kuma bata haƙuri tana kuka.
Kukan kura Inna Habi ta yi tare da yowa cikin Humiara a yarda ita ƙasa ta haye saman cikinta ta fara dukanta.
Humaira na ihu sosai tana bata haƙiri amma ina, bata saurare ta ba, maƙota suna ji amma ba halin su shigo, dan ko sun shigo ma Inna Habi cin mutuncinsu ta ke da zagi, dan haka kowa ya fita harkarta.
Ƙarshe sai da Humaira ta suma a hannun Inna Habi, da ta ga bata motsi ne ta ɗaya d'aga ta.
Ruwa ta ɗebo ta yayyafa mata a jiki sannan ta farfaɗo.kuka ta ke sai har idanunta sun kumbura saboda naushi da ta sha a idanunta bakinta ma ya fashe.
"Tashi ki je ki nemo kuɗi ki biyani kuɗin doya na."
"Inna Ina zan samu Kudi wallahi ban dan inda zan samo ba."
"Na faɗa maki yadda za ki samu?"
Kai ta gyaɗa mata alamar eh.
Dan haka sai ta ce mata
"Ki je ki yi karuwanci ki kawo mani kuɗina."
Da sauri ta kalli Inna Habi ta ce,
"Karuwanci?"
"Eh haka na faɗa ko ke ba mace ba ce."
Nuna mata ƙofar fita ta yi
"Fice ga ƙofa nan ina jiran kuɗina."
Daƙyar ta iya tashi ga kanta da ke mata ciwo kamar zai fashe, tsawar da Inna Habi da dake daka mata ya sa ta nufi hanyar fita tana kuka.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll
*ADAMSY*
~A new blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DuXNzdLkDfm1U0dZg9YE73
*YAR GIDAN TAFIDA KAYAN MATA PURE AND NATURAL WITH ZERO SIDE EFFECT*
*Matan gidan nan mace seda gyara , Ina masu fama da rashin sha'awa to matsalar ku ta kau in sha Allah,muna da abinda za ki sha ya canza miki yanayin jikinki ki fara jin kema macece.*
Kina fama da matsalar rashin gamsuwa ko gamsar da me gida ? To ga solution🥰🥰.
Ina macen da takeson ko yaushe ta jita ajiqe muna da abinda zamu ba ki ,kisha ya saukar miki da ni'ima💃💃💃.
Mata masu son su gyara fatar su ,su dinga sheki da ƙyalli da haske me kyau bana bleaching ba ki zama kalar hutu🧖
Kuma akwai naku .🤩🤩
1. Gumban kwakwa da madara
2.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 19