Share this page
da ƙwai ya fashewa a ciki, bokiti ta dauka ta nufi hanyar fita tana rawar sanyi tana zubda hawaye. Fita tayi daga gidan yayin da garin yayi tsit ba alamar motsin mutum a a nan kusa da su, kowane kofar gida ta wuce a rufe yake kasancewar lokacin sanyi ne kowa na kudundune a cikin gidansa. Tayi tafiyan tsayin mintuna goma kafin ta kai wajen bohol ɗin da zata dinga ɗibar ruwan. Haka ta dinga ɗibar ruwan tana zuwa tana kaiwa ga iskar da ke kaɗawa ga kayanta da ke jiƙe tun tana jin sanyin har ya kai ga ta daina jin sanyin. Sai da ta gama cika komai na gidan lokacin ƙarfe shida na safe, ko sallar asuba bata yi ba kuma bata isa ta ajiye ba sai ta gama, lokacin da ta ajiye bokitin ƙarshe ne yayi dai-dai da lokacin da Mallam Sani ke dawowa daga masallaci kallonta yayi tare da cewa. "Humaira dama baki cikin ɗakinki?" "Eh Baffa na je ɗebo ruwa ne." Jinjina kai yayi tare da cewa "Allah yayi maki albarka." "Ameen" Wucewa yayi ya nufi ɗakinsa ya shige ita kuma ta ɗauki buta ta nufi banɗaki, bayan ta fito ne sai ta daura alwala ta shige ɗakinta dan yin salla. Tana kai raka'an farko kafin ya tayi raka'a ta biyu Inna ta dinga ƙwala mata kira. "Humaira! Humaira!! Ke Humaira!!!" Tana salla ba damar amsa kiran da ake mata, dan haka ta cigaba da salarta. Inna dake tsakar gida ta ne ta ji shiru Humaira bata fito ba, kwafa tayi tare da jinjina kai, itace ta janyo ta haɗa a murhun dai-dai lokacin da Humaira ta fito daga ɗakinta sanye da hijabi, ta ƙaraso wajen Inna da niyyar ta durƙusa ta gaishe ta kafin ta ankare ta ji saukar mari a kumatunta. 'Yar ƙara ta saki tare da cewa "Wallahi sallah nake yi yanzu na idar." "Sallar asuba raka'a biyu ne, a cikin mintuna biyu yakamata a ce kin gama, amma saboda tsabar wulaƙanci ne yasa kikayi zamanki ko saboda mugun hali da kikayi gado wajen uwarki ko?" Tana dafe da kumatunta idanunta na zubda hawaye, Mallam Musa ne ya fito daga cikin ɗakinsa ya ce, "Habi jiki tsoron Allah akan abinda kike yiwa yarinyar nan, marainiyar Allah da bata ji ba bata gani ba batayi maki laifin komai ba ki dinga gallaza mata Allah yana ganinki." "To ya kake nayi? tun yaushe nake kiranta akan tazo ta hura wutan nan ta a dama koko ta fita da shi talla bata fito ba tana jina dan tsabar wulaƙanci tayi shiru." Juyawa tayi ta kalli Humaira ta ce, "Ba zaki haɗa wutar ba sai na haɗa ko me kike jira?" Durƙusawa tayi ta fara ƙoƙarin hura wutan, maihaifinsu ya shige ɗaki inda Inna ta cigaba da masifa. "Idan bata je ta yi tallar kokon ba ya kake so nayi? Ko kashe ka za'ayi baka da kuɗin da zaka bayar ayi cefene a gidan nan." Bayan Humaira ta hasa wutar ne ta ɗauka tukunyar da zata ɗora ruwan koko. Kwanikan wanke-wanke ta fito dasu ta haɗa a tsakar gidan inda suke yin wanke-wanke. Bayan ta kammala wanke-wanke ne sai ta share tsakar gida, Inna ta dama koko. Kallon Humaira tayi tare da cewa "Ki tafi ɗakin Salma ki tayar da ita tayi shirin zuwa makaranta." Ɗakin Salma ta nufa ta tarar da ita tana ta sharar barci, da alama ko sallar asuba bata yi ba. "Salma Salma." Bugun ƙafarta tayi a hankali, sai ta motsa tana yamutse fuska ta ce, "Ke ni sa'arki ce da zaki dinga kira na da Salma?" "To ai naga ba wani girma ya kikayi ba, wata ɗaya kika bani." Inna dake tsakar gida ta jiyo muryarsu ta ce, "To rasa kunya ko kwana ɗaya ne ai ta girme ki, dan haka idan na sake jin kin kira ta da Salma sai na fasa maki baki." Humaira dai fitowa tayi inda Inna ta ce, "Salma ki fito ke da zaki makaranta kada ki biyewa wannan da ba inda zata je sai zaman kashe zani." Humaira ce ta ƙaraso wajen tare da cewa "Inna dan Allah na dan ɗebi ruwan zafin nayi wanka da shi sanyi nake ji." Sanyin ya kashe ki wannan ruwan zafi na mai zuwa makaranta ne Salma ce zatayi wanka da shi, dan haka ki ɗebi ruwan randa kiyi da shi, sannan kizo ki ɗauki koko ki fitar mani da shi." *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman ƙarin bayani* 09065327995 Love you oll😍😘 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/G71cfIobTnG3W5wekkrGtv *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullah K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page7️⃣&8️⃣ "Sanyin ya kashe ki, wannan ruwan zafi na mai zuwa makaranta ne Salma ce zata yi wanka da shi, dan haka ki ɗebi ruwan randa kiyi da shi, sannan ki zo ki ɗauki koko ki fitar mani da shi." Haka ta ɗebe ruwan da ta ɗebo da asuba tayi wanka da shi, bayan ta fito ne ta shige ɗaki da sauri-sauri saboda yanayin sanyin da ake ciki ga iskar da ke kaɗawa ga wanka da ruwa mai sanyi hakan yasa take jin sanyin. Bayan ta shafa mai ne dai powder ta sanya wata riga da zani ta atamfa, duk da cewar ta koɗe amma a wanke suke tas ba alamar datti. Hijabinta ta ɗauka tare da sakawa ta fito zuwa tsakar gidan dai-dai lokacin da Salma ta fito daga ɗaki tana yamutse fuska da yin miƙa kamar wacce tayi aiki ta gaji. Kallon Humaira tayi tare da cewa. "Ke ɗebi ruwan zafin ki shirka shi ki kai mani ɓanɗaki nayi wanka." Bata isa ta ce ba zatayi ba ko ta musa, dan haka ya buɗe tukunyar ta zuba mata ruwan zafin ta kai mata banɗaki. Bayan ta fito ne ta ɗauki bokitin kunun kokon ta fita da shi zuwa ƙofar gida. Bayan ta ajiye ta dawo ne, ta ɗauki wani bokiti da ruwa a ciki wanda zata dinga wanke robobin kunu idan wani ya shanye, ta ɗauki robobin da ludayi kafin ta fita. Koda ta fita ta tarar da masu siyen kunun har sun fara zuwa suna jiranta, nan da nan ta fara saida masu kokon. Haka ya tashi da safe ba walwala a tattare da shi, ko Breakfast ma bai tsaya yayi ba ya nufi hanyar fita daga falon. Amina da ke zaune tana jiran fitowarsa dan suyi Breakfast ne taga zai fita, da sauri tasha gabansa tare da cewa "Ina kuma zaka je da sassafen nan haka?" "Fita zanyi." "Naga yau lahadi ba aiki ballantana ka ce kana sauri zaka fita zuwa wajen aiki." "Bana jin yinwa ne, kuma ina son na tafi gaida Umma." "Na ji zaka tafi gaida Umma, amma ka tsaya ko shayi ne ka ɗan sha mana." Girgiza kawai yayi tare da cewa. "Bazan iya saka komai a baki na ba, dan bana sha'awar komai." Duk yadda ta kai ga lallaɓa Adamsy akan ya tsaya yayi Breakfast amma sam ya ƙi amincewa, dan haka sai ta barshi ya fita ba don ranta naso ba. Kai tsaye gidan mahaifiyarsa ya nufa, inda ya same ta zaune a dinning room tana Breakfast, bayan yayi sallama ta amsa masa ne ta kalleshi ta tare da cewa. "Baba na kaine da sassafe haka?" Ƙara sawa yayi saman kujera ya zauna tare da jinginar da bayanshi da jikin kujera ya lumshe idanunsa kamar mai yin barci, ganin haka yasa hankalin Ummansa tashi, dan tasan cewa idan ta ganshi haka to yana cikin damuwa ne. Ƙara sawa tayi kusa da shi tare da tare da dafa kafaɗarsa, jinta a kusa da shi ne yasa shi kwantar da kansa saman cinyarta, har lokacin baiyi magana ba. "Baba na kayi haƙuri ka rungumi ƙaddararka duk abinda kaga ya samu bawa to daga Allah ne, dan haka kayi imani da ƙaddararka ta alkhairi ko ta sharri, ba wanda ya isa ya canza abinda Allah ƙaddara faruwarsa, hakazalika ba wanda ya isa ya hana abinda Allah ya ƙaddara faruwarsa sai dai idan Allah ne baisa hakan zata faru." Ta ƙaarsa maganar tana mai shafa kansa, ta ɗaura da cewa "Idan har ka yarda da abinda na faɗa maka to yakamata ka cire damuwar da ke cikin zuciyarka, ka miƙa lamuranka wurin Allah." Jinjina kai yayi tare da cewa. "To Ummana na haƙura ai." "Shine kake cikin damuwa?" "Damuwa ya zama dole Ummana na mata huɗu fa ina aure kowace da irin tata matsalar ba wacce mukayi zaman mata da miji ko na kwana ɗaya a tsakaninsu." Jinjina kai tayi tare da cewa "Na sani su dama can ba abokan rayuwarka bane, haka Allah yaso da kai, insha Allahu zaka samu abokiyar rayuwarka." Girgiza kai yayi tare da cewa "Umma ni hakura da zancen ƙarin auren nan, wata kila ba rabin zan samu ganin gudan jini na ne." "Kada ka faɗi haka kuma kada ka fitar da kanka da ragamar uban giji." "Umma na ɗaukarwa kaina alƙawarin cewa idan har Allah yayi duniya dan Manzonsa to babu wacce 'ya mace da zan gani na neme ta da sunan aure." "Kayi gaggawar canza furucinka Baba na." Wayarsa ce tayi ringing zaro wayar yayi daga cikin aljihunsa ya duba ganin baƙuwar number ce yasa ya ajiye wayar bai ɗaga ba. Har sai da aka kira sau uku sannan ya ɗaga tare da cewa. "Hello wai wake damu na ne ka kira ba'a daga ba ai sai ka hakura haka nan ko?" Muryar mace ya ki ya daki dodon kunnensa, a hankali ta ce, "N kasa hakura ne shiyasa na nace sai ka ɗauka ina fatan dai ban takura maka ba." "Gaskiya kin takura mani Wallahi." "To baka ma tambaye Ni wace ce ni ba ko?" "Dan Allah kiyi maganar da zakiyi mallama bana son takura." Murmushi tayi tare da cewa "Hauwa'u ce ƙawar Fauziyya." Cikin mamaki ya ce, "Hauwa'u dai ƙawar Fauziyya wacce aka fasa aure na da ita jiya?" "Ƙwarai kuwa nasan ka Sanni, dan munsha haɗawa da kai a ƙofar gidansu Fauziyya mu gaisa." "Eh na gane ki to me yasa kika kira Ni?" "Abinda yasa na kira ka saboda na baka haƙuri akan butulcin da Fauziyya tayi maka, dan na tausaya maka idan har zaka amince zan zame maka madadin Fauziyya." Da mamaki ya ce, "Ban gane zaki zame mani madadin Fauziyya ba." "Ina nufin zaka aure ni na zame maka mata kai kuma ka zama miji a gare ni." "Nagode da nuna mani ƙauna, amma ki sani bana da sha'awar sake wani auren kuma." Murmushi tayi tare da cewa "Zan baka lokaci dai kayi shawar nan da kwanaki biyu zan kira ka naji shawarar da ka yanke, na barka lafiya." Daga nan ta katse kiran, Ummansa dake zauna ya ɗora ƙafarsa akan cinyarta ne tayi murmushi tare da cewa "Babana da ka bata dama, tunda har ta nuna tana ƙaunarka, a matsayinta na 'ya mace mai kima ta iya furta maka tana sonka to tabbas tana matuƙar ƙaunarka, kayi nazari akai, amma da zaka bi shawara ta Kawai ka amince mata ka aure ta." Gajeren murmushi yayi tare da cewa "Umma kenan, amma tunda kin nuna kina so bazan ƙi ta taki ba." Murmushi tayi tare da cewa "Allah yayi maka albarka ." Ta amsa da Ameen Kullun sai Hauwa'u ta kira Adamsy akan maganar soyayyarsu amma sai yayi biris da ita, har ta kai yau dai ya yanke shawarar zuwa gidansu. Tana zaune a falonsa ita da Mum ɗinta da kannenta maza biyu, suna fira wayarta tayi ƙara a hankali ta juya ta kalli wayar sai taga Adamsy ne ke kiran wayar ta, ƙara zare idanu tayi cikin mamaki tana kallon mai kiran wayar, dan Adamsy bai taɓa kiranta a waya ba sai yau, sai dai ita ta kira shi idan tava dama ya ɗaga idan kuwa baiga dama ba bazai ɗaga ba ko sau nawa zata kira shi, idanunta suka gaskata mata cewa lallai Adamsy ke kiranta wani tsallen murna tayi tare da yin ihu wanda ya janyo hankalin gaba ɗaya jama'ar da ke falon, kallon mamaki suke mata tare da furta lafiya? Ɗakinta ta nufa da sauri ta turo ƙafar. Amsa wayar tayi tare da faɗawa kan gado ta ce, "Hellow, kaine ke kira na ko mafarki nake yi ?" Murmushi yayi tare da cewa "Wane irin mafarki kuma?" "Na daɗe ina addu'ar Allah ya nuna mani ranar da zaka kira ni, hakan ya nuna cewa ka fara amsa tayin soyayya da nayi maka ne." "Kada fa ki zaƙe dayawa" Bai taɓa sakewa da ita sukayi fira ba sai yau, kuma taji daɗin hakan sosai, daga ƙarshe sai ya nemi ta turo masa address na gidansu, take ta tura masa zuciyarta fal da farin ciki. Bayan ta gama ne ta fito falon inda tabar Mum ɗinta da kannenta, kalli ɗaya Mum ɗinta tayi mata taga yadda take cikin farin ciki, dan haka ta ce, "Me kika samu ne haka na farin ciki?" "Mum dole ki ganni cikin farin ciki, mutumin da kullun nake kiransa sai yaga dama yake ɗauka duk na shiga damuwa akansa, kwatsam yau rana ta farko ya kira ni, sannan ya nemi da na bashi address na gidanmu gobe zaizo." Cike da takaicinta Mun ɗinta tayi tsuki "A matsayinki na 'ya mace ke ce zaki dinga bibiyar ɗa namiji ba shi zai dinga bibiyarki ba? Ina abinki naki yake mace da aka sani da alkunya gaskiya kin bani takaici wane irin namiji ne shi haka?" Mum wallahi tausayinsa nake shine fa wanda ranar da za'a ɗaura aurensa da Fauziyya ta ce, bata sonsa." "Yanzu tsohon mijin ƙaawarki kike so kenan, dama can kina sonsa ko?" "To dama tun farkon gani na da shi ya burge ni, amma ban taɓa tunanin wani abu game da shi ba da naga ƙawata ta wulaƙnata shi a ranar da zasuyi aure, kuma kanta tayiwa dan wallahi ya haɗu Mun baki ganshi bane fari ne dogo kuna kyakkyawan ƙarshe, ga lafiyayyen sake da yayiwa fusakarsa ƙawanya da kin ganshi kin..." Mum ɗin ta ce ta katse ta hanyar cewa "Dalla rufe mani baki, kamar ni ina Mahaifiyarka sai ki zauna kina zayyane mani siffar irin na namijin da kike so? Saboda baki da kunya ko?" Sunkuyar da kamata tayi tana dariya ta ce, "Mum ke fa kika tambaye ni..." "Ni ban tambaye ki fiffofinsa ba, sannan kibi a hankali, ba kyawun siffa ko kyawun ƙira ake so ba a'a kyawun hali ake buƙata " "Eh har kyawun hali yana da shi." "Kin zauna da shi ne?" Girgiza kai kawai tayi ba tare da tayi magana ba. Washe gari kuwa kamar yadda Adamsy yayiwa Hauwa'u alƙawarin zuwa gidansu kuwa sai gashi ya zo, murna a wajen Hauwa'u ba'a magana kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha take ji sun taɓa hira inda yake bata labarin duk abubuwan da suke faruwa a rayuwar sa na dangane da aure-auren da yayi ne, har zuwa yau ba abunda ya ɓoye mata ya nuna cewa idan zata soshi a haka ba matsaka shikenan. A cikin wata ɗaya aka gama komai na dangane da auren Adamsy da Hauwa'u, inda biki ya rage saura kwana bakwai ana ta shiyrye- shirye daga kowane ɓangare. Ana gobe ɗaurin aurensu ne da misalin ƙarfe biyu na dare sai ga ƙawayen amarya sun fito a guje daga ɗakin amarya, saurin rufe ƙofar sukayi ta wace yayin da sai kwaramniya da sautin fashewa abubuwa da ake tarwatsewa. Kai tsaye bedroom ɗin Mum suka nufa, cikin tashin hankali suke bubbuga ƙofar suna kuka. Cikin barci Mum ɗin Hauwa'u da ƙannen mahaifinta da ke kwance a ɗakim Mum suma sunzo daga Abuja, jin ƙarar ƙofar na tashin hankali yasa suka farka a firgice da sauri Mum ɗin ta ta tashi suma suka biyo bayanta, buɗe ƙofar tayi tare da cewa "Ku lafiya daddaran nan me ke faruwa ina ƙasar taki." Ɗaya daga cikin ƙawayen amaryar ne ta fara kuka sosai tana cewa "Mun Hauwa'u ta haukace." "Ke wai ni sa'arki ce da zaki ce mani 'yata tilo ta haukace? Ina take ne?" Ɗaya daga cikinsu ta ɗaura da cewa "Wallahi ta haukace tuburan tana ta fashe-fashe har da dukanmu wallahi daƙyar muka sha a hannunta, shiyasa muka zo faɗa maki gata can mun rufe ta a ɗaki." *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll😍😘 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9 *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟* {R.S.W.A} https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_* _(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_ *Alk’alaminmu ‘yancinmu* *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM* Page9️⃣&1️⃣0️⃣ Wallahi ta haukace tuburan tana ta fashe-fashe har da dukanmu wallahi daƙyar muka sha a hannunta, shiyasa muka zo faɗa maki gata can mun rufe ta a ɗaki. Cikin tashin hankali Mum ɗinta ta nufi ɗakin Hauwa'u, ta tura kofar wayam bata ga kowa ba,sai ta ji motsi a bayan ƙofar ta waiga da sauri taga Hauwa'u kanta a warwatse ga kayan jikinta duk ta yayyage su hatta pant ɗinta ana gani. Mum ɗinta ta fashe da kuka tare da rungume ta a jikinta. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Hauwa kece haka na shiga uku na..." Kasa ƙarasa maganar da tayi niyyar yi tayi sakamakon wani raɗaɗin azaba da ta ji, lokacin da Hauwa'u ta gantsara mata wani masifaffen cizo a damtsen hannunta iya ƙarfinta, ƙara Mun ɗinta ta saki wanda ya janyo hankalin gaba ɗaya ilahirin jama'ar da ke cikin gidan. Cikin hanzari kowa ya nufi cikin ɗakin, daƙyar aka ɓanɓare bakin Hauwa'u daga damtsen hannun Mum ɗinta, sai jini ke tsiyaya daga hannunta, ga shaidar cizon nan sunyi zurfi sosai lokacin da aka ɓanɓare bakin daga hannun Mum ɗinta sai da kowa dake wajen yayi mamakin irin wannan cizon. Hajiya Talatu ƙawar Mum ce ta kalli wata mata dake gefenta ta ce, "Maman Fahad dan Allah kuje ki duba ta kiyi mata duk abinda ya dace." Maman Fahad wata ƙawar Mum ce da take aiki a asibiti , ta ja hannun Mum suka fita tare ta nufi ɗakin Mum da ita. Abun ɗa da uwa, ita kuma Mum ba ta cizon da Hauwa'u tayi mata bane ke damunta a'a halin hauka da 'yarta ke ciki ne ya fi daga mata hankali matuƙa. Bayan fitar su Mum ne sai kawai Hauwa'u ta janyo hannun wata ƙawarta tayi tare da kai mata duka ta ko ina, daƙyar aka ƙwace ta dan yanzu wani ƙarfi ne na ban mamaki Hauwa'u ke da shi, kamar na ƙarfinta ba, mutane kusan su biyar amma ta rinjaye su daƙyar suka iya dakatar da ita daga dukan ƙawarta da take . Fita suka yi suka barta ita kaɗai a ɗakin suka rufe ta ta waje. Kasancewar dare ne a lokacin kusan ƙarfe uku saura kwata ne a gidan ba wanda ya iya yin barci daga masu kuka sai masu alhini. Mum kuwa kwana tayi tana kuka duk yadda aka dinga rarrashinta abu ya ci tura gaba ɗaya ta kasa daina kukan haka suka ƙyale ta. "Ya kuke so na yi idan banyi kuka ba, yarinyar nan bata da mahaifi ni nake kula da su da ranta da lafiyarta lokaci ɗaya ranar jajibirin aurenta ace ta haukace lokaci guda ni fa da kaina na shiga ɗakin da na ji hayaniyarsu tayi yawa na ce ƙarfe goma sha biyu tayi su kwanta suyi barci, har tana ce mani sai da safe sun daina fitar a cikin awa biyu da rabuwa ta da ita ta haukace tuburan har da dukan mutane." Ta ƙarasa maganar cikin kuka mai cike da cin rai, nan aka dinga rarrashinta inda Hajiya Talatu ta cigaba da cewa "Kinga addu'a zaki yi mata Allah ya yaye mata, sannan wannan auren da za'a ɗaura gobe a dakatar da shi har sai ta samu lafiya, a kaita asibitin da ake kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa ayi mata magani, idan Allah yasa komai ya dai daita sai a daura auren." Jinjina kai Mum tayi tare da cewa "Shikenan hakan za'ayi yadda kika ce." Washe gari da safe ne ƙawayen Amarya suka watse kowa tayi hanyar gidansu, wacce Hauwa'u tayi wa duka kuwa jikinata yayi kumburi musamman fuskarta, gefen idanunta ma ɗaya a kumbure bata gani da idanun sosai. An haɗa Breakfast masu aikin gidan ba wanda ya nufi dinning area ballantana yayi breakfast. Umma ce ta dauki kofin shayi dan zuwa ta kaiwa Hauwa'u ko zata sha, tunda tasan ko tana jin yunwa ba zata iya magana ba, dan haka ta nufi ɗakin Hauwa'u da kofin shayi a hannunta. Tura kofar tayi zata shiga sai taji muryar Hajjo ƙanwar Baban Hauwa'u ta ce, "Nifa ina tsoron ki shiga ɗakin nan bansan kuma abinda zata aikata maki ba." Murmushin takaici tayi tare da cewa "Wata uwa ce zata guji 'yarta a duk halin da 'yar ta tsinci kanta?" Daga nan bata sake magana ba ta kutsa kai cikin ɗakin, ta same ta tana ta safa da marwa a dakin, a hankali Mum ɗinta ta tari gabanta tare da sakar mata murmushi ta ce, "Hauwa'u?" Dakatawa tayi tana kallon Mum kamar taga sabon halittar da nata taɓa ganin mai kama da ita ba, miƙa mata kofin tayi da niyyar kaiwa a bakinta sai ta buge kofin ya faɗi ya tarwatse ƙasa, sai ta duƙa zata ɗauki fasassaun kofin Mum tayi saurin riƙe mata hannu nan suka dinga kokawa da ita har Mun ta faɗi ƙasa dai-dai lokacin da Hajiya Talatu suka shigo tare da wasu mata guda biyu, tayar da Mum sukayi inda Allah ya taimaka na bata yi muguwar faɗuwa ba. Ganin yadda take daga ita sai bra da pant ne yasa Hajiya Talatu nufar drawar kayan Hauwa'u, ta ɗauki nata wani riga doguwar ta abaya tare da dogon wando da zasu sanya mata a ciki. Ganin yadda ta tuɓe kayan jikinta ya saura daga ita sai bra da pant bayan ɗaya daga cikinsu ta kwashe kofin da Hauwa'u bata fasa ta gyara wajen. Sai da suka nemi taimakon wajen mata biyu suka zama su biyar tukun sannan suka fara saka mata kaya, da ƙyar ta bari suka saka mata kayan jikinta amma sai kawai suka ga tana ƙoƙarin yaga kayan ne suka riƙe mata hannu ta kasa cire kayan jikinta Nam aka dinga kokawa da ita dukkansu mutum biyar ɗin nan sai da ita kaɗai ta kwaci kanta daga hannunsu hakan yasa suka fita tare da janyo mata dakin suka rufe suka zare key suka tafi da shi. Mum ɗintac ta ɗauki wayar tare tare da kiran wayar Adamsy yana ta ringing amma bai ɗaga dan haka ta ce kila bai kusa ne anjima kaɗan zata gwada kiransa, dan kada ya zo baisan da zancen cewa an fasa ɗaurin auren ba yazo da jama'a alhalin ba'a faɗa masa ba, dan haka ta ajiye abin duniya duk ya ishe ta. Sautin Sallama ta ji a cikin kunnenta. "Assalamu alaikum" "Wa'alaiki salam" Hajiya Saratu ce ta shigo wato ƙawar Mum ce ita ganin yadda idanun Mun suka kumbura suka yi jazir yasa ta cikin tashin hankali ta dafa kafaɗarta tare da cewa "Lafiya kuwa me yake damunki haka? Yau ranar bikin 'yarmu ranat farin ciki ne a gare mu ." Girgiza kai tayi tare da cewa "Nikan wannan ba farar rana bace a gare ni, baƙin rana ce ranar da bazan taɓa mancewa da ita ba a tarihin rayuwa ta." Idanun Hajiya Saratu ya sauka akan wani jaka na kwali mai ɗauke da hoton Amarya da ango wato Adamsy da Hauwa'u. Zaro ido Hajiya Saratu tayi cike da mamaki ta ce, "Kada dai a ce Adamsy ne mijin da Hauwa'u zata aura?" Cikin mamaki ta ce, "Eh Admsy sunansa kin san shi ne?" Kai kawai Hajiya Saratu ke girgizar tare da cewa "Babu alkhairi a tattare da Adamsy mata guda biyar yake aure sannan kiga wata masifa ta samu kowace a cikinsu ." Cikin tashin hankali Mum ta ce, "Dan Allah kiyi mani bayani nasan inda zancenki ya dosa ba." "Bari kiji duk matar da ta aure Adamsy sai wata nakasar ta same ta, a takaice dai wallahi mata biyar kenan idan aka haɗa da 'yarki shida kenan, ciki. Matan nan biyar wata ta mutu wata ta haukace wata wata ta makance ta zama makauniya ta cikin su biyar ba wacce ta tayi rayuwa salin alin." Ɗora hannu aka Mum tayi tare cewa "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Adamsy ka cuce ni baka sanar da ni cewa kana da matsala ba gashi yanzu ka haukata mani yarinya." Da mamaki Hajiya Saratu ta ce, "Kina nufin yanzu har 'yar ta mu ta haukace ?" Kai ta jinjina mata tare da cewa "ƙwarai kuwa" Adamsy ne ya kira lambar Mum dan kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta canza shawara ta dauka, jin muryarsa tayi yana cewa "Assalamu alaikum " "Wa'alaika salam,kana ina ne Adamsy?" "Ina gida Mum." "Kazo yanzu

Chapter 3 of 19