ina son ganinka"
Bata tsaya jiran ko ne zai ce ta katse kiran wayar, shima yayi mamakin kiran haka ya miƙe jiki a mace ya nufi ƙofar fita dai-,dai lokacin da Amina ta fito daga ɗakinta, ta kalle shi tare da cewa
"Ango har ka fito ne?"
Ba tare da ya kalle ta na ya ce,
"Mahaifiyar Amarya ce tayi mani kiran gaggawa."
Jim tayi tare da cewa
"Allah ya sa Lafiya."
Daga nan ya amsa da Ameen ya fice.
Kai tsaye wajen motocinsa ya nufa, inda ya buɗe ɗaya daga cikinsa sannan ya shiga ya tayar, horn yayi mai gadin gidan ya buɗe masa gate ya fice.
Kai tsaye ya dauki hanyar gidansu Hauwa'u.
A falo ya same su su dinga da waɗanda ya sani da waɗanda bai sani ba, Sallama yayi wanda hakan dai-dai da ƙarasowar Mum a falo, bayan sun bashi izinin shigowa ne ya kalle su tare da durƙusawa ƙasa yayi ya gaishe su, ba wacce ta amsa a cikinsu.
Tunani ya shiga yi kodai ya ƙara gaishe su ne sai ya ji muryar Mum tama cewa
"Shikenan Adamsy dama abinda kake so kenan hankalinka ya kwanta burinka ya cika, wai me yasa kake wahalar da rayuwar bayin Allah? Me suka yi maka? Tukunna ma kai wane irin mutum ne haka da duk wacce ta aure ka sai masifa ya faɗa mata? Wane irin mutum ne kai mai baƙin ƙaddara har sau nawa zaka cigaba da saka rayuwar bayin Allah cikin hatsari meye ribarka akan hakan kayi ɗaya biyu uku kaga yadda rayuwarsu suka kare me yasa kai ba zaka haƙura ba saboda sin zuciyarka shine ka cigaba da auren wasu kana dad'a jefa rayiwasu cikin gararin rayuwa."
Wata mata daga cikin mata ta ce,
"Waya sani ko yana cikin ƙungiyar nan ta matsafa ne yasa..."
Kafin ta kai ƙarshen zancenta ne ta ji kusryarsa ya ce
"A'uzubillahi minashshaiɗanir rajim."
Nan dai suka cigaba da faɗa masa maganganu marasa daɗi, anan yake sanin cewa Hauwa'u ta haukace tuburan. Jin muryar Mum yayi tana cewa
"Abinda kayi muna sai Allah ya isar mana, sai kaga karshenka mugu mai baƙar aniyar, kuma bari ka ji koda ace yarinya ta ta warke ta dawo dai-dai to wallahi ba kai ba ita Allah ya tsare sauran 'yan matan daga sharrin ka."
Nuna masa hanyar fita tayi tare da cewa
"Tashi ka fita ka bar mana gida bana buƙatar sake gani. Ko mai kama da kaine ne a rayuwa ta, zanyi jinyar 'yata har Allah ya bata lafiya, idan kuma itama ta rasu kamar yadda na ji ance ƙawarta Fauziyya ta rasu bayan fasa aurenku da kwana ɗaya to Allah ya jiƙansu amma Alhakin mutuwarsu ya rataya a wuyanka.
Tashi yayi ya nufi hanyar fita idansa duk sun janza launi zuwa ja, wato bayan fasa aurensu da kwana ɗaya, gashi yanzu Hauwa'u dake nuna masa tsamin so ta haukace banda sauran mata huɗu da yayi yunkurin aure da wadda ya aura? Me ke faruwa da rayuwa ta ne? Tambayar da yake yiwa kansa kenan.
Motarsa ya shiga ya tayar tare da ɗaukar hanyar komawa gida.
Yana driving yana kuka yana magana shi kaɗai,
"Me ke faruwa da ni ne? Anyi na biyar mata biyar kenan Fauziyya kin rasu? Allah Sarki Hauwa'u kin nuna mani ƙauna tun bana kula ki ina share ki bakiyi zuciya kin rabu da ni ba haka kika cigaba da hakuri har ranar da na amshi tayin soyayyarki, gashi yanzu ke ce a hauka ta dalilina?."
Maganar mahaifiyar Hauwa'u ya tuna inda take cewa.
"Sau nawa zaka cigaba da saka rayuwar bayin Allah cikin hatsari?meye ribarka akan hakan?"
Kuka kawai yake yi yayi nisa cikin duniyar tunani abunda dake faruwa a rayuwarsa, yana cikin driving hankalinsa ya gushe bai ankare ba sai yaji motarsa ta bada sautin garar...
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don neman karin bayani*
09065327995
Love you oll😍😘
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM*
Page1️⃣1️⃣&1️⃣2️⃣
Kuka wai yake yi,yayi nisa cikin duniyar tunani abinda ke faruwa a rayuwarsa, yana cikin driving hankalinsa ya gushe bai ankare ba sai ya ji motarsa ta bada sautin garar...
Ashe ya daki motar da ke gabansa ne ba tare da saninsa ba, sai a lokacin ya dawo daga hayyacinsa dade goshinsa yayi tare da faɗin.
"Ya Salam!"
Mai motar da ya daka ne ya fito cikin faɗa da tijara ya nufi motar Adamsy yana cewa.
"Wannan wane irin banzar tuƙi kake yi ne ko ka san irin ɓarnar da kayi mani? To wallahi sai ka biya ni yadda ka ɗaki motata har da fasa mani Danja ka..."
Kasa ƙarasa maganar yayi sakamakon kuɗin da Adamsy ya fito da su yana miƙa masa, bandir ɗin dubu ɗari ne guda biyu wato dubu ɗari biyu kenan, amsa yayi tare da cewa.
"Yanzu na ji magana irinki ake so da ko kunyi ɓarna zaku biya har da roba bawai masu bada hakuri ba."
Horn da ake danna masu daga baya ne yasa Adamsy yayi masa nuni da hannunsa wato ya tafi ya ja motarsa sun tare na bayansu.
Tafiya yayi yana cewa
"Allah sarki ahe ma kurma ne shi baya magana."
Shi duk a tunaninsa Admsy baya magana ne, tunda koda yayi taasifarsa bai yi magana ba kuɗi ya bashi, yanzu kuma gashi yayi masa nuni da hannu.
Bayan ya shiga motarsa ya ja ne sai sai Adamsy yana nasa ya cigaba da tafiya.
Kai tsaye gidan Ummansa ya nufa, inda ya samu jama'a sun ɗan taru ba laifi, dan ya ga ɗai ɗaikun mutane a harabar gidan. Ajiyar zuciya ya sauke tare da maganar zuci yana cewa
"Allah sarki Ummana baki gajiya da tara jama'a a gidan nan, ko wane lokaci sai kinyi taro kuma auren baya yiwuwa, idan wani ya tashi kuma sai kinyi sake yi to anzo na karshe insha Allahu." Yana fitowa daga motarsa kai tsaye ya nufi wata ƴar ƙaramar ƙofa wanda ada kafin yayi aure nan ne ɗakinsa na samartaka, kuma Ummansa na sanya mai aikinta tana gyara ɗakin bata bari yayi ƙura, yana shiga ya maida kofar ya rufe kai tsaye ya nufi bedroom ɗinsa ya faɗa akan akan gadon tare da kifa cikinsa idanunsa duk sun rikiɗe zuwa ja
Kuka kawai yake kamar ƙaramin yaro yana tuna abubuwan da suka faru a rayuwarsa, ga maganar Mum ɗin Hauwa'u inda take cewa.
"Mutum ne kai mai ɓaƙin ƙaddara har sau nawa zaka cigaba da saka rayuwar bayin Allah cikin hatsari meye ribarka akan hakan kayi ɗaya biyu uku..."
Kuka ne ya ci ƙarfinsa a hankali ya ke furta kalaman Mum ɗin Hauwa'u, haka ya dinga kuka tamkar wani ƙaramin yaro.
Turo ƙafar aka yi aka shigo Ummansa ce tsaye tana kallonsa bata san kuka yake ba sai lokacin da ta ji sautin kulansa cikin hanzari ta ƙarasa jikin gadon tare da furta cewa
"Babana kana lafiya kuwa? Me ya same ka ne la kwanta kake ta kuka haka tamkar wani ƙaramin yaro?"
"Haba na sanka fa da jarumtaka ban sanka da kuka ba kai jarumine?"
Cikin kuka ya ce,
"Umma Fauziyya ta rasu washe garin ranar da za's ɗaura aurenku aka fasa, sannan ga shi Hauwa'u ta haukace ya ɗin nan Ummanta ta kira ni take sanar da ni, Umma wai me ke faruwa ne da rayuwata, Umma wai ashe baƙar ƙaddara ce da ni?" Duk matar da na so ko bayi yunƙurin aure sai wata masifa ta same ta, kowaca a cikin su biyar ɗin kowace da irin tata ƙaddarar, mai haukacewa mai mutuwa mai makancewa, gudun wani abu ya sami Hauwa'u yasa kika ga ban amince da tayin soyayya da tayi mani ba, gashi yanzu tana cikin mawuyacin hali na hauka."
Shiru Ummansa tayi tana nazari kafin ta cigaba da cewa
"Kayi haƙuri dukkan tsanani yana tare da sauƙin, wannan ita ce ƙaddararka baka isa ka guje mata ba, mahaifinka Allah ya jiƙansa da rahama mutum ne shi mai tsananin haƙuri da tawakkali haka nake don kaima ka zama mutum jajirtacce mai haƙuri haka ma Mahaifiyarka itama..."
Kallonta yayi da sauri ya ce,
"Wata mahaifiyar tawa?"
Murmushi tayi tare da cewa
"Ba gani nan ba? Ka taɓa ganin abinda ya sa na kaga rauni na ya fito?"
Girgiza kai yayi tare da cewa
"A'a.
"To kaina haka nake son ka kasance kada jama'a su ga rauninka."
Haka ta cigaba da kwantar masa da hankali har ya ɗan saki ransa.
"Bari na kira ƙanin Mahaifinka na sanar da shi halin da ake ciki nasan zuwa anjima zasu fara shirye-shiryen zuwa ɗaurin aure."
Wayarta da ke riƙe a hannunta ta lalubo lambar wayar Baba Ashiru ƙanin mahaifin Adamsy, bugu biyu ya ɗaga inda ta ce,
"Assalamu alaikum, Ashiru kana lafiya?"
Daga can ɓangaren ya ce,
"Wa'alaiki salam lafiya lau Hajiya ya jama'a?"
"Alhamdulillah"
"Masha Allah ya aka yi ne?"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
"Kada kuje wajen ɗaurin auren nan."
Cikin mamaki ya ce,
"Wani abun ne ya faru?"
Nam ta bashi labarin komai kamar yadda Adamsy ya sanar da ita, inda ta d'aura da cewa
"Yanzu ka sanar da jama'armu halin da ake ciki."
Shiru yayi yana nazari inda ya daura da cewa
"Zan shigo zuwa gobe lokacin jama'a sun watse, akwai maganar da nake so mu tattauna da ke."
"To Allah ya kaimu lafiya sai ka zo."
Daga nan ta katse wayar ta nufi kitcheen dan kawowa Adamsy shayi.
Ba jimawa ta dawo ɗauke da kofi da shayi ta zo ta ajiye a saman side drawer ta kalle shi ta ce,
"Tashi zaune Babana."
Ba musu ya tashi zaune tare da da jingina bayansa da jikin gadon, miƙa masa kofin shayin tayi tare da cewa
"Karɓi kasha ka ji Babana."
Girgiza kai kawai yayi tare da cewa
"Umma Wallahi bana jin zan iya cin komai ko shan kimai, dan gaba ɗaya ji nake bani da lafiya."
Daga nan ne sai ya koma ya kwanta tare da jan bargo zai lulluɓe, tayi saurin riƙe bargon ta ce,
"Yakamata kasa wani abu a cikinka kafin kayi kwanciyarka."
Ba tare da ya sake mata musu ba ya karɓi kofin shayin yasha rabi sannan ya miƙa mata ya ce,
"Umma ya ishe ni haka."
Amsa tayi ta rike a hannunta, wayarsa ne ya soma ringing, kamar bazai ɗauka ba ya ga Sadik ne dan haka ya ɗaga kiran tare da cewa.
"Sadik ka sanar da abokanmu cewa an fasa ɗaurin auren yau, Amarya bata da lafiya, sai ta samu sauƙi za'a sanar da saurin auren da ranar da za'ayi."
Ajiyar zuciya Sadik ya sauke tare da cewa
"An sake samun akasi kenan kamar yadda aka saba, la fito kawai ka ce an fasa ba wai kayi mani nuƙu-nuƙu ba."
"Shikenan koma meye an dai fasa shikenan."
"Kana ina ne yanzu?"
Sanin cewa Sadik zai iya zuwa da abokansa yasa ya ɓoye masa dan baya son hayaniya ya ce,
"Ina wani waje ne anjima zan kira ka idan na dawo."
Daga nan ya katse kiran tare da kashe wayar gaba daya.
Girgiza kai Umma tayi ta fita daga ɗakin ta ja masa ƙofa.
*KADUNA*
Tana zaune a kofar gidansu saman benci tana siyar da koko. Duk wanda yazo zai siya ta zuba masa idan da sigar ne ma akwai rober sugar a wajen sai ta zuba masa.wani matashin saurayin yazo ya zauna kusa da ita a saman bencin da take zaune, kasancewar bencin dogo ne sai ya matsa can gefe bayan taga kusancin nasu yayi yawa tana mace yana namiji.
"'Yan mata meye haka dan na zauna kike wani matsawa kamar ba mutum irinki ba?"
Tsuke fuska tayi tare da cewa
"Idan koko zaka siya na zuba maka idan kuma ba shi zaka siya ba ka tashi ka tafi anan."
Dariya yayi tare da cewa
"Zuba mani kokon hamsin sugar na hamsin."
"Da ake bada na hamsin amma yanzu ba na hamsin gero yayi tsada."
"To zuba mani na dari da sugar na hamsin."
Zuba masa kokon tayi ta zuba sugar ta saka masa ludayi ta bashu. Wani dattijo yazo wajen Tsoho da shi ya kalle ta ya ce,
"Akwai koko?"
"Eh Baba akwai."
"To yarinya a zuba mani ma hamsin."
"To Baba bari na zuba maka."
Wannan saurayin ya kalle ta ya ce,
"Yanzu fa kika ce ba na naira hamsin."
"Eh babu, ai shi tsoho ne ko baka gani ba ne."
Kasancewar akwai mutane a wajen ne wannan tsohon ya hangi bishiyar mangwaro ya ce,
"Bari na zauna jikin bishiyar can."
"To Baba bari na zuba sai na kawo maka a wajen."
Tsohon ya nufi gindin bishiyar gidan Mallam Tanko maƙocin gidansu Humaira ga zauna."
Bayan ta kammala zuba masa ne ta nufi inda yake dan ta kai masa ne sai wannan saurayin da ke zaune kusa da ita ya fara waige-waige yaga ba mai kallonsa ya buɗe murfin robar da Humaira ke ajiye kuɗi ya kwashe kuɗin duka ya yi saurin barin wajen.
Koda ta dawo dama kokon ya kare sai ta ga ba saurayin a wajen sai robar kokon da bai gama shansa ba ma ya ajiye.
Sai a lokacin ta duba robar da take ajiye kuɗi taganshi a buɗe ba ko sisi a ciki, cikin tashin hankali ta fara waige-waige tana nemansa, gabas da yamma kudu da arewa babu shi babu alamarsa tashin hankali ya shiga domin tasan mai ƙwatar kanta sai dai Allah ƙadiru manyasha'u.
Hannu ta ɗaura akai ta fashe da kuka tana cewa
"Shikenan baya kwashe kuɗin ya janyo mani masifa wallahi sai ji mani ciwo."
Kukanta ne ya janyo hankalin ilahirin jama'ar da ke wajen suka gane me take ciki, nan wasu suka dinga cewa ai ko waye ya ɗauki kud'in yanzu tafi ba zata gansa ba, haka aka dinga bata haƙuri har Salma ta foto sanye da kayan zuwa makaranta taga halin da ake ciki, nan ta riga gida aguje ta ta sanarwa mahaifiyarta halin da ake ciki, nan Inna Habi ta miƙe ta tare da cewa
"Jar uba! yanzu kuɗin kokon nawa aka sace, to wallahi yarinyar nan sai na kusa kashe ta a gidan nan."
Salma ta fita a guje tana jin daɗin yau Humaira ta shiga hannu, duk da cewar kullun cikin dukanta ake amma yau kam na daban ne.
Haka Humaira na kuka ta tattara bokitin koko da robobi da ludaya ta zuba a cikin bokitin ta shiga cikin gida.
Ɗari-ɗari ta shiga cikin gidan tana kuka ta ƙarasa gaban Inna Habi dake fere doyar da zata ɗorawa Humiara talla da rana.
Durƙusawa tayi akan guiwarta ta fashe da kuka ta ce,
"Inna Dan Allah kiyi haku..."
Kafin ta kai ƙarshen zancen ne Inna ta ciro itace da ke cikin murhu yana ci da wuta ta fara dukan Humiara da shi, ihu take tana neman taimako azaba biyu ga dukan itace ga zafin ƙunar wuta.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://chat.whatsapp.com/IdLjpWceclh5VR8G5W9SFY . INA MASU BUKATAR KAYA AKAN FARA SHIN SARI KU SARA KU SIYAR KU SAMU NAKU AKAN FARASHI KALILAN MUNA DA KAYA KALA KALA KAMAR SU HIJABAI KAYAN KITCHEN ATAMFA LACE KAYAN YARA MOTHER CARE KAYAN SHAN ISKA NA ABBA MATERIAL DINKAKKE DA YADIN BEDSHEETS HULUNA DA SAURAN SU MUNA TURA KAYA DUK INDA KUKE CIKIN AMINCI UBANGIJI 💯💯💯💯💯
*GARGAƊI*
wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM*
page1️⃣3️⃣&1️⃣4️⃣
Kafin Humaira ta kai ƙarshen zancenta ne Inna ta ciro itace da ke cikin murhu yana ci da wuta ta fara dukan Humiara da shi, ihu take tana neman taimako azaba biyu ga dukan itace ga zafin ƙunar wuta.
Ihu take kamar ranta zai fita wasu masu siyen kokon da basu riga sun watse ba sai Allah wadai da halin Inna Habi suke yi, maƙota ma na son shigowa dan cetonta amma sun kasa shigowa saboda sun saba shigowa sai dai ta kara azabtar da Humaira fiye da yadda tayi niyya, ta ce wai ta ja ana zaginta ko kuma ta tsige wacce ta shigo mata gidan.
Wata tsohuwa ce ta haifi Inna Habi, ganin me ke faruwa yasa ta yi wurin ƙarasowa a tafiyarta a duƙe tayi saurin jan itace ta ce,
"Haba Habi kina son ki shuga aljannah kuwa?"
Habi ta kalle ta ta ce,
"Idan makullin shiga aljannah a hannunki yake idan na zo shiga ki rufe."
Duk yadda tsohuwar nan ta so ƙwatar Humaira kasawa tayi dan ta tsufa sosai ba karfi, ga Inna bara saurare ta ba ƙarshe sai ta nemi tura ta ta faɗi ƙasa, ganin haka yasa ta nufi hanyar fita tana Allah wadai da halin Inna Habi.
Sai da ta mata duk lilis sanan ta barta ta koma gefe tana huci.
"Yar banzan yarinya da bata san Abun arziki ba, kuɗin nawa zakiyi sake da shi ayi mani sakiyar da ba ruwa? To wallahi bazan ɗauki asara haka nan kawai ba dole ne kema kiji a jikinki ehe."
Daga nan ta tashi ta cigaba da free doyar da take yi, ta gama ta koma cikin ɗaki tana huci, Humaira kuwa gaba ɗaya ta kasa koda ɗaga hannunta.
Bayan ta fito ne ta watsa mata wani matsiyacin kallo ta ce,
"Ki tashi kije ki shirya ki tafi tallar doya"
Daƙyar ta iya motsawa ta tashi a hankali ga jikinta da ke mata ciwo ga kuma inda wutar suka kona ta suka ɗari ruwa duk sun tashi. Tana kuka tana tafiya har ta iya shigewa ɗakinta.
Kayan jikinta ta cire kasancewar duk sun lalace ta fito ta nufi randar ruwa ta buɗe ta debi ruwa cikin bokiti ta nufi hanyar banɗaki dan yin wanka.
Bayan ta fito ne ta saka kayan da zata saka doguwar riga ce ta atamafar roba sai hijabinta da ta saka.
"Wai dan uwarki ba zaki fito ki ɗauki tallar doyar bane? Ko so kike tayi kwantai 'yar baƙin ciki kawai."
Tafiya take inda ta kalli ƙafarta inda ya ƙone da wuta ya girma ya ɗari ruwa, sai kuma gefen cikinta da take ji yana mata zafi sosai sai guiwar ƙafarta da ke mata ciwo inda Inna ta buga mata itace. Fitowa tayi tana fitowa ta watsa mata harara tare da cewa
"Ki kama jiki bakwai ki dinga tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki."
Lokacin da ta fito har Inna Habi ta kammala zuba mata doya a farin bokiti irin wanda ake ganin duk abinda ke cikin robar , sannan ta ajiye mata garin yaaji da soyayyen man gyaɗa.
Bayan ta fito daga cikin ɗakin take tafiya a hankali sai ta ji muryar Inna tana cewa.
"Dalla kama jiki kina tafiya kamar wacce bata da kaka a jikinta."
Bayan ta ƙaraso ne ta ɗauki bokitin doyar tare da ɗaukar soyayyen mai da ya ji ta nufi hanyar fita.sai ta ji muryar Inna Habi ta ce,
"Doyar nan ta dubu biyu ce ko naira biyar tayi ciwon kai wallahi sai jikinki ya faɗa maku."
Haka ta fita tana tafiya tana ƙyangyashi ƙafsrta na ciwo dai-dai guiwar ƙafar damanta wajen duka, kuma gashi tallar doyar yawo zata dingayi ba zama ba ballantana a ce zata huta.
Haka ya wuni kwance wayoyinsa ma a kashe, gaba ɗaya ya rasa sukunin da walwala, ya ɗaurawa kansa alhakin abinda ya samu 'yan matan nan a kansa. Gani haka shine sanadiyyar komai da ya faru dan haka garin da abubuwan nan suka faru ma ya masa zafi, ji yake gaba ɗaya ya tsani garin da zamansa, gara ya canza gari ko zai rage damuwa, ya yanke shawara koda ya koma wane gari bazai taɓa bari wata 'ya mace ta shiga rayuwarsa ba ballantana wata masifa ta same ta sanadiyarsa
Sau yamma sannan Baba Ashiru ƙanin mahaifinsa ya zo Lokacin jama'a suka sun watse, Umma ce tayi masa Jagora har zuwa ɗakinsa, Bayan sun gaisa ne ya kalli Umma ya kalli Adamsy ya ce,
"Nifa wannan al'amari ya fara isa na, a ce mata ɗai-ɗai har guda biyar kuma kowace na ta kalar masifar daban, lamarin nan fa abin dubawa ne, wannan ta rasu wannan ta haukace waccan ta makance kowa da irin tata masifar."
Ajiyar zuciya Adamsy yayi tare da cewa
"Na yanke wata shawara Allah yasa zaku amince...
*Kuyi haƙuri da Wannan*🙏
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don neman ƙarin bayani*
09065327995
Love you oll😍😘
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
https://chat.whatsapp.com/IdLjpWceclh5VR8G5W9SFY . INA MASU BUKATAR KAYA AKAN FARA SHIN SARI KU SARA KU SIYAR KU SAMU NAKU AKAN FARASHI KALILAN MUNA DA KAYA KALA KALA KAMAR SU HIJABAI KAYAN KITCHEN ATAMFA LACE KAYAN YARA MOTHER CARE KAYAN SHAN ISKA NA ABBA MATERIAL DINKAKKE DA YADIN BEDSHEETS HULUNA DA SAURAN SU MUNA TURA KAYA DUK INDA KUKE CIKIN AMINCI UBANGIJI 💯💯💯💯💯
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
Page1️⃣5️⃣&1️⃣6️⃣
Nan ya yanke wata shawara Allah yasa zaku amince..."
Umma ce ta kalle shi tare da cewa.
"Wata shawara ka yanke?"
"Ina son zan koma garin Kaduna dan na cigaba da tafiyar da kamfaninmu da ke gari, dan wallahi zaman garin nan ya ishe ni na gwammaci nayi nisa da garin nan ko zan iya mancewa da muanan abubuwan da suka faru a rayuwa ta."
Umma ce ta kalle shi ta ce,
"Mancewa da abubuwan da suka faru a rayuwarka ba abu bane mai sauƙi, a tunani na mancewa da su wani abu ne mai kamar wahalal."
Gajeren murmushi yayi Wanda ya tsaya iya fatar bakinsa bai kai zuci ba, sannan ya ɗora da cewa
"Ummana koda ban mance komai ba amma zan rage wasu damuwar tunda bana ganin unguwanni kowa cikinsu."
Baba Ashiru ne ka kalli Adamsy ya ce,
Ta wani ɓangaren maso komawa da zaka yi, dan kamfanin mahaifin naka da ke can an banzatar da shi ba kulawa ba komai, kuma ga gidajenku da ke can maihaifinka da ke can.
Maida dubansa yayi zuwa ga Umma sannan ya ce,
"Maganar matsalarsa da yaron nan yake fuskanta ne abun dubawa, ba haka kawai abubuwan nan suke faruwa ba dole akwai ummul'aba'isin faruwar komai. Walau mutum ko aljan."
Shiru Umma tayi kamar mai nazari sannan ta ɗora da cewa
"To yanzu me kake so ayi ne?"
"Mu tafi wajen Shatima ya bincika mana wannan lamarin dan ya gano komai, indai Shatima ne wannan abun shan ruwa ya fi shi wahala a wajensa, tun daga farko har ƙarshe zai sanar da mu komai ko sanya hannun ɗan Adam ko kuma sharrin jini wata aljana ce ta aure da duk zai gani."
Umma ce ta kalle shi tare da cewa
"Shatima ai boka ne."
"Kinga ba wani boka kawai..."
Adamsy ne ya katse masa hanzsrinsa ta hanyar cewa
"Baba Ashiru ni dai duk wannan zancen a barshi kawai, na fawwalawa lamarina, komai ya faru da ni hala Allah yaso da ni."
"Kai da matarka zaka koma Kadunar ne ko yaya?"
Umma ce tayi masa wannan tambayar.
"Zan fara komawa ni kaɗai amma idan naga yanayin wajen yayi mani sai na dawo na ɗauke ta mu koma can."
Baba Ashiru ne ya kalle shi tare da cewa
"Ni kuma bazan so ka tafi da matarka can ba, dan idan ka tafi da ita sai mun daɗe kafin mu ganka, amma idan yakasance tana nan tare da mu to ganinka bazai mana wahala b. Nasan zai dinga dawowa week koda bayan sati biyi ne ko idan ya ɗauki hutu ya zo wajen mu gansa.
Gajeren murmushi yayi tare da cewa
"Kada ka damu duk inda nake kuna cikin raina, ai ba zan taɓa ɗaukan tsawon lokaci ba tare da na zo naga Ummata ba kuma tunda mahaifina ya rasu kai nake gani a matsayinsa kasancewarsa ƙaninsa, kallonsa nake maka."
Turo ƙofar akayi aka shigo tare da sallama, Sadik ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.
"Assalamu alaikum"
Gaba ɗaya suka amsa masa da
"Wa'alaika salam"
Gaida Umma yayi da Baba Ashiru sannan ya maida dubansa ga Adamsy dake masa kallon mamaki.
"Ya aka yi kasan ina nan?"
"Ya bazan sani ba, bayan na kira ka baka sanar da ni inda kake ba illa kawai ka ce an fasa ɗaurin aure, na je gidanka matarka ta faɗa mani baka nan shiyasa nasan cewa baka da inda zaka je da ya wuce nan."
Kama hannunsa yayi tare da cewa
"Tashi mu tafi."
"Mu tafi ina kuma?"
"Wajen wani malami dan wannan lamarin naka zuwa yanzu ya fara bani tsoro sosai, abun naka dole sai an danganta shi da malamai na kira shi na sanar da shi halin da kake ciki sh ne yake sanar da ni cewa rayuwarka tana cikin hatsari mu zo tare da kai yana don ganinka."
Fisge hannunsa yayi daga riƙon da Sadik yayi masa tare da cewa
"Kai dalla rabu da ni, waye ya faɗa maka rayuwa ta tana cikin hatsari shi yasan gaibu ne? Ai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 19