Share this page
Yar gidan Tafida ta kawo muku ingantattun kayan mata 100% pure ba side effects in nace muku pure to pure Wanda akayi su da itatuwa masu kara lafiyar dan Adam 💃💃💃💯💯. *YAR GIDAN TAFIDA* Tana da alaidi Akwai pure man kadai Akwai gumba ta madara da kwakwa Akwai kuma hakki,akwai tsumi da original tabaje, sai kin gwada za ki gane sirrin 😜😍. *Duk products dinmu are 100% natural baby chemical,with zero side effects. Zaku iya tuntubata ta wannan layin 09032036606 Yar gidan Tafida 💯💯 *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka aguji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page3️⃣4️⃣&3️⃣5️⃣ Sai da ta kusa katsewa kiran wayar sannan ya ɗaya d'aga tare da cewa "Assalamu alaikum" "Wa'alaika salam." Shiru ta yi ta kasa ƙara magana har dai da ya kira sunanta sannan ta masa tare da cewa. "Na'am Mallam Barka da dare." "Barkanki, lafiya kika kirani cikin wannan tsohon dare?" "Amm uhmm uhmm dama. Zan tambaye ka ne ko kuna lafiya?" "Muna lafiya ko kuma ina lafiya? Ni da wa kika san nake a nan idan ba ni kaɗai be?" Tsoro ne ya kama Inna Habi, duk da ba wai wani tsoron na Mallam Musa ta ke amma wannan karon dole ta tsorata dan ta san irin so da ƙaunar da ya ke yi wa Humaira. "Ya Humaira da Salma fatan duk suna lafiyako?" "Alhamdulillah duk suna lafiya." Murmushin takaice ya yi lokacin da ya tuna cewa Humaira na cikin gidan a matsayin matar Adamsy. Amma duk da haka bai ji alamar sauyi ko kuma wanta nadama a tattare da Inna Habi ba, hat tana masa ƙaryar cewa suna lafiya, da dukkan alamu bata san inda Humaira ya ke ba kuma bata damu ba.kamr daga sama ta ji muryarsa yana cewa "Ki basu wayar mu gaisa da su?" Gabanta ne ta ji ya faɗi amma sai ta dake ta ce, "Yanzu fa dare ne Mallam kuma ka san Himaira na can ɗakinta, Salma kuma ta yi barci a yanzu haka." "To shikenan zanzo da kaina na duba su." Ta yi saurin cewa "Ka barshi kawai ba sai ka zo ba kai da kullun kana bakin aiki, kada ka takurawa kanka ina kula da su yadda ya dace." "Ya na ji duk yanayinki ya sauya ko baki son na zo ne?" "Ba haka bane Mallam kawai dai na ga bai dace ka bar aikinka bane tunda kuma muna lafiya." Daga nan bata jira cewarsa ba ta katse kiran wayar, zubawa Salma idanu ya yi tare da cewa "Kina jin me ya ce ko?" Kai Salma ta jinjina tare da cewa "Ina jinsa Inna." "Tsorona kada ya zo bai same ta ba kuma bansan me zan sanar da shi na." "Kada ki damu kafin ya zo ta dawo kila ma da safe ki ganta." Da haka suka kwanta ba jimawa barci ya yi awon gaba da su. A damusy ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, inda ya samu Humaira na ta barcin wahala, sai ajiyar zuciya ta ke saukewa. Ƙarasawa ya yi jikin gadon ya zuba mata ido yana kallon fuskarta yadda ta yi jajir ga idanunta a kumbure. Tausayin yarinyar ne ya kama shi tare da wani zazzafar ƙaunarta wanda ya shige shi lokaci guda ba tare da ya shiryawa hakan ba. Ji ya yi ta zama wani ɓangare na rayuwarsa duk da ƙarƙashin zuciyarsa yana ayyana yadda zamansa zai kasance da ita dangane da yanayin yadda rayuwar tasa ke tafiya. Bathroom ɗinta ya shiga inda ya tarar da komai tsaf, Maryam ta gyara hatta bedsheet da suka ɓata sai da ta wanke shi a cikin washing machine ta busar da shi. Tsarkake jikinsa ya yi sannan ya ɗauro alwala,fitowa ya yi daga cikin bathroom ɗin kai tsaye ya nufi ɗakinsa. Bayan kamar mintuna bakwai ne ya dawo sanye da farar Jallabiya. Sallaya ya shimfiɗa ya fara jero sallar nafila, zuciyarsa cike da annuri da farin cikin da ya tsinci kansa a ciki. Ya yi godiya ga Allah da ya mallaka masa irin macen da ya ke so, wacce ta mallaki duk wani abinda ya ke buƙata daga wurin 'ya mace, ya ɗora da addu'ar samun zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Daga ƙarshe ya ta shi bayan ya idar ya nufi gadon ya kwanta a gefenta, ɗan nesa da ita dan ya ga tsoronsa da ta ke ji. Gaba ɗaya ya kasa barci sai tunene-tunane da ya ke yi a cikin zuciyarsa. Can a cikin barcinta ne ya mirgino tare da ɗora hannunta a saman ƙirjinsa, sai kuma ta ƙanƙame shi tamkar ta samu filo, cigaba ta yi da barcinta ya yin da shi kuma ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi dan gudun kada ta farka. Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na asuba ne, ya fara tunanin yadda zai janye jikinsa daga nata, yana tunanin yadda tashinta. Cikin dabara ya fara zame jikinsa daga nata a hankali ya maye mata gurbinsa da filo. Ɗakinsa ya nufa inda watsa ruwa tare da ɗauro alwala, sannan ya sauya jallabiyar jikinsa ya nufi masallaci. Kamar yadda ya zame masa jiki duk bayan sallar asuba, sai ya tsaya ya yi azkar ƙarfe bakwai yake dawowa gida. Amma yau kam ya kasa gaba ɗaya hankalinsa na ga Humaira. So ya ke kawai ya dawo gida ya ga halin da take ciki. Dan haka bayan ya gama addu'oi da zaiyi ne ya nufi gida. Kai tsaye ɗakinta ya nufa, dai-dai lokacin da ya tura kofar ɗakinta ita kuma tana juya kai tare da yamutse fuska, idanunta a rufe suke. Da hanzari ya ƙarasa bakin gadon nata ya riƙo hannunta, jin an riƙe hannunta ya sa ta buɗe idanunta da sauri. Ganinsa ne ya sa ta tsorata da shi sosai tare da ja da baya tana girgiza masa kai, idanunta na zaubda hawaye tana tuna irin azabar da ya ganar da ita. Har ta kai ƙarshen gadon bata daina girgiza masa kai tana hawaye ba, hango tsananin tsoronsa ya yi a cikin idanunta dan haka ya ce, "Ki kwantar da hankalinki ba abunda zan maki kin ji?" "Zan bar maka gidanka ba sai ka hora ni ta wannan hanyar ba, na san cewa baka so na Abbana ya yi saurin baka ni ba tare da ya tuntuɓe ka kana so na ko baka so na ba. Hakan da ka mani na tabbatar da cewa ba ka kauna ta." "Waye ya faɗa maki bana sonki bana ƙaunarki? " Kuka ne ya zo mata ta fara magana cikin kuka tana cewa "Saboda baka dace da Ni ba, ruwa ba sa'an kwando bane kafi ƙarfina ta ko ina, kai ɗan masu kuɗi ne ni 'yar talaka wanda idan yana da cin yau bashi da na gobe. Kai ɗan boko ne wayayye wanda ni ko karatun kirki ban yi ba, a talla na ƙare inda ƙafarka ya taka ban kai can ba, ka tashi cikin hutu da jin daɗi ni kuma na tashi cikin wahala. Na san zaka sha'awar auren mace mai ilimi ni..." Ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Ya ishe ni haka nan, waye ya faɗa maki cewa mace mai ilimi nake so? Ni ba mace mai ilimi na ke so ba mace mai tarbiyya nake so. Dan banga amfanin ilimi babu tarbiyya ba, idan aka ce mace nada tarbiya ko bata da ilimi zan ji daɗin zama da ita, dan haka ki daina alaƙanta kanki da irin macen da bata dace dani ba." Girgiza masa kai ta yi alamar a'a. "Dan ni yanzu na ga macen da ta dace dani." "Dan Allah ka barni na koma wajen Abbana bazan iya jure zaman nan ba." Ɗan jim ya yi kafin ya ɗora da cewa "Shikenan na ji, amma ki je kiyi wanka kiyi sallah." Ba abunda ya ke hangowa acikin aidanuntw face zallar tsoronsa da ta ke ji. Ahankali ta ziro ƙafarta ƙasa idanunta na kansa tana fargabar ya matso kusa da ita. Zuba mata idanu ya yi yana kallon ƙafarta yadda ta ke tafiya tana daƙyar tana ɗan buɗe ƙafa ya sa shi cewa. "Ki gasa jikinki da ruwan zafi sosai." Kamar bata ji shi ba, har ta kai bakin ƙofar banɗaki ta ji muryarsa ya ce, "Please ki bari na zo na taimaka maki" A da sauri ta shige banɗaki tare da banko ƙofar ta danna masa key. Dariya ce ta so zuwa masa amma ta ƙarƙashin zuciyarsa tausayinta ne a zuciyarsa. Fita ya yi daga ɗakin ya koma ɗakinsa, inda ya samu wayarsa na ruri. Ƙarasawa yayi ya ɗauki wayar ya duba inda ya ga Abdallah ne ke kiransa, ɗagawa yayi tare da karawa a kunnensa. Kafin ya yi magana ne ya ji muryar Abdallah na cewa *Adams kun tashi lafiya?" "Lafiya lau" "Ya jikin Humaira?" "Da sauƙi" "Kana tare da ita ne?" "Tana ɗakinta nima ina ɗakina. Amma shigowa ta kenan daga ɗakinta, dan na ga sai tsorona ta ke yi bata ma yarda na je kusa da ita." Dariya Abdallah ya yi tare da cewa "Ai dole ta ji tsoronka mutum kamar doki, har ka ɗanɗana mata ƙamshin mutuwa..." Bai jira ya kai ƙarshen zancensa ba ya kashe wayar,dan bazai iya jiran tsiyar da zai masa ba. Lambar wayar Amina ya lalubo ya danna mata kira, sau biyu yana kira bata daga ba sai a na uku sannan ta ɗaga. Tana kwance a saman gadonta lulluɓe a cikin bargo, dai tsuki ta ke yi dan ta san waye ya kira ta a daidai wannan lokaci. Tura baki ta yi tare da cewa "Hello" Murmushin takaici ya yi tare da cewa "Ki tashi ki yi sallah" "To na ji" "Ba to kin ji ba ta shi na ce ki yi." Kashe wayar ta yi tare da yin cilli da shi gefe. "Mutum sai damuwa kabar garin ma ba zaka bar mutun ya huta ba sai ka ce kai zan wa sallar." Juyawa ta yi sannan ta gyara kwanciyarta. Bayan kamar mintuna biyar ya sake kiran wayar. Ta shi ta yi tana cewa "Aifa idan ba tashi na yi ba bazai taɓa bari na huta ba." Jin bata ɗaga bane ya sa shi sanin cewa ta tashi yin sallah . Dan dama inda sabo ya saba da halinta, ƙa'ida sai ya tayar da ita wata rana idan ta farka ta ga lokacin sallar ta yi ne sai ta tashi da kanta ta yi. Dan ta san cewa ko bata ta shi ba ƙa'ida sai ya tayar da ita. Bayan ta fito daga wanka ne, sai ta ji jikinta ya mata ɗan sauƙi ba laifi sakamakon gada jikinta da ruwan zafi da ta yi. Dagowar riga na material ta saka, sannan ta saka hijabi ta hau kan sallaya ta fara gabatar da sallah. Bayan ta idar ne tana azkar din safiya kamar yadda ta saba. Bayan ta gama ne sai ta ɗan kwanta a saman darduma kewar mahaifinta kawai ta ke yi, ba abunda ta ke muradi illah ta saka shi a idanunta. Ta shi ta yi a hankali ta fara tafiya zuwa jikin window da ke ɗakin, a hankali ta buɗe glas ɗin window ta hango mahaifinta zaune a barandar ɗakinsa yana sanye da rigar sanyi mai haɗe da hula, kasancewar garin sanyin damina ne musamman da aka kwana ana ruwan sama sai wajen asuba sannan ruwan saman ya tsaya. Karatun Alqur'ani ya ke yi. Zuba masa idanu tayi tana kallonsa har Adamsy ya shigo ɗakin bata sani ba, a hankali ya ƙaraso wajen da ta ke tssye bata ma sani ba, hannunsa ya sa a saman kafaɗarta ta juyo a firgice tana kallonsa. Matsawa ta sake yi ta shige jikin bango tare da janyo labulen windon ta ɓoye kanta a ciki. "Me ki ke yi a nan?" Shiru ya yi ba tare da ta ce komai ba ƙirjinta na dukan uku-uku, dan tsoron ya zo kusa da ita ta ke yi. "Ki daina jin tsorona haka nan kinji, bazan cutar da ke." Tura baki ta yi tare da cewa "Nidai wajen Abbana zan koma." "Abbanki ya kawo ki nan ne dan ki zauna zama na har abada, mutuwa ce kaɗai zata raba ni da ke." Kuka ne ya ta fashe da shi tare da cewa "Wallahi bazan iya zama da kai ba sai dai na koma cikin ƙuncin da na fito ya fiye mani..." "Dakata kiji, nan fa gidan aure ne kuma aure ibada ne, zaman raya sunnah kike fa." "Nasan aure ibada ne amma idan da cuta barinsa halak ne." "Ta wace hanya na cutar da ke?" Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi duk da tana cikin labule baya ganin fuskarta, tura baki kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba. Murmushi kawai ya yi dan ya tuna abinda ya faru jiya daddare ne ya sa ta jin tsoron zama da shi. "Shekarunki nawa?" "Shekaruna goma sha shida, dai ranar babban sallah zan cika sha bakwai." Shiru ya yi yana nazari kalli ƙaramar yarinya ce, amma idan ka kalle ta ba zaka taɓa tunanin cewa iya shekarunta kenan ba, musamman yadda komai na jikinta ya amsa sunansa, zaka yi tunanin 'yar shekaru ashirin ce. Dan duk suffarta sun cika ga ƙirjinta a cike fam ga hips ɗinta ya fito kasancewar tana da ƙira mai kyau. Mamaki kawai ya ke yanzu ƙaramar yarinya ce ta saka shi fita hayyacinsa duk ya bi ya gigice baima san me ke faruwa ba sai da ya samu biyan buƙatarsa, jinjina kai ya yi kalli Humaira ta dabance a cikin mata. "To yanzu me kike so na maku?" "Nidai kawai zan koma wajen Abbana ne." "Kinga abunda ya faru tsakanin ni da ke jiya fa ba wani abu bane kowace mace sai da taji abinda kika ji, kuma dan na farko ne shi ya sa, amma idan muka sake ba zak..." "Sautin kukanta ta ƙara, da sauri ya yaye labulen tare da cewa "A'a ki kwantar da hankalinki ba abunda zan sake yi." Daƙyar ya rarrashe ta ta yi shiru ta daina kukan. "Muje ki yi breafast." Hannunta ya riƙe cikin nasa, ta na ƙoƙarin zame hannunta daga riƙon da ya mata, yayi saurin matse hannunta cikin nasa yadda ba zata iya zamewa ba. A haka suka fara tafiya a hankali saboda yanayin yadda ta ke tafiya,ganin haka ya sa ya ɗauke ta cak ya nufi dinning area da ita, ƙoƙarin sauka ta ke yi ne sai ya yi ki bata damar da zata sauka,a haka har suka ƙarasa ya dire ta a hankali saman daya daga cikin kujerin dake wajen. Zama ya yi shima yana fuskantarta. "Me zaki ci?" Tana maganar yana buɗe duk abinda ke wajen tana gani. Shayi da bread ne sai soyayyar ƙwai da dankalin turawa da plantain. Gefe guda kuma ga farfesun kaji nan da farfesun kayan ciki kallon dayan flask ɗin ta yi ta ga indomie ne da ya ji kayan haɗi. Sunkuyar da kanta ta yi tana tuna rayuwar gidansu, ga koko tana tallansa amma ba za'a bata ta sha ba, sai dai ta ci sauran tuwon jiya, Idan aka ba Salma koko tana sha sai ta ji dama ita aka bawa itama. Yau ita ce a cikin wannan daula, ga abinci nan na kalaci kala-kala sai wanda ranta ya so zata ci, ta yi nisa cikin zurfin tanani da ta ke yi ne ta ji ya taɓa mata ƙafa, ɗagowa ta yi tana kallonsa tare da cewa "Na'am" "Tunanin me kike yi ne?" Girgiza masa kai ta yi alamar ba komai. "Me zan zuba Mali?" A hankali ta ce "Ni koko da ƙuli ƙuli na ke so?" Zuba mata idanu ya yi tare da cewa "Koko kuma da ƙuli?" Jinjina masa kai ta yi alamar eh. Shiru ya yi yana nazari sannan ya kalle ta ya ce, "Me ya sa duk abinda ke nan baki so sai abinda babu shi?" "Kullun addu'a ta Allah ya kawo mani ranar da nima zan zama irin Salma na dinga shan koko da ƙuli kamar yadda ta ke ci." Bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba. Sai da yayi dariya har ya ishe sa zuba masa idanu ta yi tana kallonsa duk takaici ya ishe ta, na dariyar da ya ke mata dai da ya ga yadda fuskarta ya canza kamar zata yi kuka sannan ya dakatar da dariyar tare da cewa "Am sorry" Maida ƙwallar da ke shirin zubo mata ta yi tare da kauda kanta gefe. "Kada ki damu duk abunda kuke so shi zan maki, nidai bansan yadda zan samo maki koko ba, dan dama yau kuku da zai dinga mani girki zai iso, kuma restaurant da ake kawo mani abunci basu siyar da kokon, bansan inda zan samu ba." "Ni na sani." "Ina kenan" "A unguwarmu farkon layin shigowa anan akwai." "Shikenan bari na kira Direba ya kaimu sai ki nuna masa hanya tunda ke kika san wajen." Wayarsa ya ɗauka ya kira layin Direbansa ya sanar da shi inda zasu tafi. Kasancewar hijabi ne a jikinta sai ta miƙa hannu ta ɗauki wani jug da ke gafenta ta nufi hanyar fita, shi dai ido kawai yake binta da shi. Ga tafiyarta ya sauya dan ma hijabinta har ƙasa ya ke ja mata, sai ta ke dan tafiya a hankali yadda ba kowa zai gane yadda ta ke tafiyar ba. Ƙarasawa ta yi wajen maigaifinta inda ta ganshi zaune yana sauraren rediyo, shima an ajiye masa abincinsa. Durƙusawa tayi har ƙasa tare da gaishe da mahaifinta, ya amsa mata cikin jin daɗi da farin ciki. Dai-dai lokacin da Adamsy ya ƙaraso wajen , kasancewar dama tunda ya dawo daga masallaci sun riga sun gaisa da Mallam Musa, sai ya ke jin nauyin Mallam Musa da kuma kunyarsa, a zuciyarsa yana tunanin abunda zai masa da zai daina masa gadi, dan bazai yiwu ba a ce ya dauki 'yarsa ya basa sannan ya cigaba da masu gadi ba. Sake gaida Mallam Musa ya yi sannan ya nufi wajen motarsa, already Direbansa na cikin motar yana jiran ƙarasowarsu. Bayan ya shiga bayan motar ne yana jiran isowar Haumaira. Humaira kuwa ta kalli Mallam Musa ta ce, "Abba zamu je siyan koko?" Take fara'ar da ke kan fusakarsa ya sauya, dan ya san Humaira ce da wannan aikin, da ta sa mijinta da Direbansa fita nemam koko. "Haba Humaira ke wace irin yarinya ce, kawai sai kisa mutan fita cikin sanyin nan dan kawai zai sha koko? Me ya sa ba zaki ci abunda kea gidan ba idan ma kokon kike so kisa a siyo maki gero kiyi d kanki, wannan ba girman yallaɓai bane da zai fita nemam koko." Nam dai ya yi mata faɗa sosai tare da mata gargaɗin kada ya sake jin makamancin haka. Tashi ta yi ta nufi wajen motar da suke jiranta, shi kansa Direba ya ji mamakin yadda uban gidansa wai zai je siyan koko a bakin hanya. "Yallaɓai ka bari kawai nake na nemo da kaina." "A'a ka bari muje ta nuna wanda ta ke so." Baya iya musu da shi dan haka ya yi shiru suka tsaya jiran karasowarta. Amma a zuciyarsa yana mamakin yausheuban gidan nasa ya sauya haka ne. Tana ƙarasowa suka kama hanyar fita bayan Mallam ya buɗe masu gate. Basu tsaya ko ina ba sai unguwar su Humaira, tana zaune a bayan mota ita da Adamsy. Tsayawa suka yi wajen da ake siyar da kokon, kasancewar nisa da gidansu Humiara ne,da kanta ta fito bayan direba ya buɗe mata murfin mota. Shikansa Adamsy yadda yaga yanayin unguwar da jama'ar da mutanen da suke wajen kokon bazai iya shansa sai hayaniya ake Adamsy ma ya fito yana kallonsu. Zubawa galleliyar motar idanu suka yi suna kallo, kamar wasu ƙauyawa, kallon Humaira suka yi kamar wacce suka sani mai siyar da koko, amma sai suka ce ba ita bace,waccan ina ita ina shiga wannan motar. Bayan an zuba mata kokon ɗari biyu cikin jug da ta ɗauka sai ƙuli shina ta dauki na ɗari biyu, Direban Adamsy ne ya biya kuɗin ya miƙa dubu ɗaya, mai kokon ta miƙa masa canjin dari shida, kai ya girgiza alamar ta bar canjin. Washe baki ta yi tare da godiya, bayan Sun juya zasu shiga motar ne kamar daga sama suka ji an ce "Hamaira!" A firgice ta juyo dan jin murayar mai kiranta sai da gabanta ya faɗi. *Daga alƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) *Don neman karin bayani* 09065327995 Love you oll😍😘 *ADAMSY* ~A new Blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMIILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page3️⃣6️⃣&3️⃣7️⃣ A firgice ta juyo dan jin murayar mai kiranta, sai da gabanta ya faɗi. Ba kowa bane illa Salma tana ɗauke da bokitin ruwa akanta. Kau da kanta ta yi ta shige cikin mota, Direba ya ja motar suka bar wajen. Salma ta saki baki tana kallon motar har ta ɓacewa ganinta. Gani ta yi ba zata iya gudu da ruwa ba, dan haka ta watsar da ruwan nan wajen ta ruga a guje dan zuwa kaiwa Inna Habi labarin Humaira. A cikin motar kuwa Humaira har sai da idanunta suka cika da ƙwalla,Adamsy ne ya kalle ta tare da cewa "Wace ce waccan da ta kira ki?" Girgiza masa kai ta yi tare da cewa "Ba kowa bace." "Ya aka yi ta san sunanki? Kuma me ya sa kika tsorata da ganinta?" Bata ce komai ba illah maida ƙwallarta da ta, ganin bata da niyyar a shi amsa ne ya sa ya yi shiru. Wayarsa ce ta soma ruri,sabawa ya yi tare da sakin murmushi sannan ya ɗaga wayar tare da cewa. "Barka da safiya Ummana." "Yauwa Barka dai Babana fatan ka tashi kafiya." "Lafiya lau Ummana, fatan kema haka." "Nima haka shalelena yau har ka ta shi barci da wuri? Kai da na san idan na kira ka irin wannan lokacin sai dai na ji kana barci. Fatan dai lafiya ko?" Tunawa ya yi da zancen Sadik na cewa wanann auren ya kasance auren sirri ne, kada ya sanar da kowa ciki kuwa har da mahaifiyarsa, duk da tunda ya ke da ita baya mata ƙarya, gaskiya ya ke faɗa akan koma Menene. Amma yau karo na farko a rayuwarsa da Ummansa ya tambaye shi abu da zai mata ƙarya . "Lafiya lau Ummana wata fita ce ta gaggawa ta kamani." "Akan me kenan?" Ɗan jim ya yi tare da cewa " Dama na fito ne na nemi abin breakfas" "Kai da ake kawo maka abinci kuma sai ka fita ka nema?" "Am dama na ji sha'awar shan koko ne da ƙuli shine..." Dariyar da ya ji Umma ta yi ne ya sa shi dakatar da maganar da ya ke yi. "Babana yaushe ka fara mani ƙarya ne?" "Umma ƙarya kuma?" "Ba ɗabi'arka bace ƙarya, kuma a duk lokacin da ka faɗe ta sai an gane, dan baka iya ta ba." Shiru ya yi ya kasa sake magana, inda ta cigaba da cewa "Ina ji a jikina cewa akwai wani abu da ke faruwa a gidanka da kake ɓoye mani." "Ba abunda na ke ɓoye maki Ummana, kema kinsan d'anki bazai ɓoye maki komai ba." "Shikenan tunda haka ka faɗa, to ya aikin?" "Alhamdulillah" Fira suka ɗan taɓa daga bisani suka yi sallama ya kashe wayar. A guje ta shiga cikin gida ko sallama ba ta yi ba, dama ba ta saba sallamar ba. "Inna! Inna!! Inna!!!" Da sauri ta fito daga cikin ɗaki tare da cewa "Ke lafiya irin wannan kira haka?" "Inna wallahi na ga Humaira tare da wasu maza su biyu, kuma inna masu kuɗi ne fa, saboda a cikin wata danƙareriyar mota su..." Ta yi saurin katse ta ta hanyar cewa "Ina suke!" "Sun shiga mota su tafi?" "Sun tafi ina?" "Nima ban sani ba, amma na gansu a farkon layi sunzo siyen koko sun tafi." Inna ta ɗora hannu akai tana salati "Amma tunda na ke ban taɓa ganin mutum wanda ya ke saurin manta alkhairi kamar waccen yarinyar ba, wato ta samu namiji ta mance da ni ko?" Taɓe baki Salma ta yi tare da kau da kai. "To ba ke kika tura ta ba." "Ko da na tura ta dan ta nemo kuɗi ta kawo mani, ba wai ta je ta tare gidansa ba." Nan dai ta cigaba da masifarta ba mai cewa ta yi shiru, Salma dai itama ta fara typing tunanin hanyar da zata bi dan ta shiga irin rayuwar da Humaira ke ciki, domin tana ganin cewa karuwancin da Inna Habi ta ce ta je ta yi shine ta ke yi. Zaune ta ke a dinning chair tana shan koko tana tauna ƙuli, yana zaune a gefenta yana kallonta, yadda ya ke sha, dan ko da ace yana shan koko da ƙosai ma bazai iya shan na wannan ƙaramin yankin ba. Yadda dai ya ga ana ɗebe shi ga yara masu siya sun dabaibaye ta kamar zasu shiga ciki, ga wajen ba tsafta ne da shi ba. Shima kansa ba wani breakfast na kirki ya yi ba, ruwan Lipton kawai ya sha. Dai da ta sha rabin jug ɗin sannan ta ajiye, sauran mulkin m ya ɗaure shi a leda ta ajiye gefe. Gyatsa ya yi alamar ta koshi, hakan ya sa ya juyo tare da kallonta. A hankali ta ce, "Alhamdulillah" Murmushi ya yi tare da

Chapter 10 of 19