Share this page
da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ne, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMIILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page4️⃣4️⃣&4️⃣5️⃣ Lokacin da ya fito daga gidan, kafin ya ƙarasa wajen motarsa ne ya ji sautin muryarta tana ƙwala masa kira,da sauri ya juyo dai-dai lokacin da ta ƙaraso gabanshi, rungume sa ta yi ta saki wani marayan kuka. Cikin mamaki ya kalle ta tare da cewa "Hauwa'u" Janye ta ya yi daga jikinsa tare da zuba mata idanu yadda ta ke ta kuka. Mahaifiyarta ce ta ƙaraso ta finciko hannunta tare da cewa "Taho mu tafi." Gogewa ta yi alamar ba zata tafi ba. "Ke wallahi ki kiyaye ni ki fita daga idanuna, a dalilinsa kika samu taɓin hanakali wanda har yanzu baki daɗe da samun lafiya ba, kinsan wahalar da na sha kafin ki samu lafiya kuwa? Duk a dalilin wannan mutumin?" Ta ƙarasa maganar tana nuna Adamsy da ke tsaye yana kallonsu, inda ta cigaba da cewa. "Dalla wuce mu tafi idan kuma ba so kike rayuwarki ta salwanta ba, a saka ki dogon barci." Ta ƙarasa maganar tare da jan Hauwa'u da ƙarfi, inda ta ke cigaba da cewa "Wannan da kike ganinsa ba wani alkhairi a tattare da macen da ta raɓe sa sai dai sharri." Gajeren murmushi ya yi mai cike da bakin ciki da takaici. Faɗawa ya yi duniyar tunani, yana tuna abubuwan da suka da suka faru da shi a baya. Ta ke yanayinsa ya sauya wanda kallo ɗaya zaka masa ka gane haka. Sadik ne ya dafa kafaɗarsa tare da cewa "Kada ka damu, haƙiƙa ba wata damuwa da zata ɗore har abada ni dai na san komai lokaci ne wata rana sai labari." Murmushi ya yi tare da cewa "Haka ne, Na gode sosai." Shiga matarsa ya yi direba ya ja suka bar unguwar. Da yammacin ranar ne Humaira ta fito daga cikin gidan sanye da dogon hijabi, kai tsaye wajen mahaifinta ta nufa inda ta hange shi zaune a barandar ɗakinsa. Carbi ne a hannunsa yana ja bakinsa na motsi,.da sallama ta ƙarasa wajensa, ya amsa mata cikin jin daɗi da walwala. Zama ta yi akan darduma da ke shimfiɗe a gefensa. Ina wuni Abba" "Lafiya lau ya kike?" "Alhamdulillah" "Kunyi waya da shi ya isa ladiya?" Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tare da cewa "Eh ya isa lafiya." Jinjina kansa ya yi tare da cewa "Ma sha Allah" "Humaira." Ɗaga kai ta yi ta kalle sa tare da cewa "Na'am Abba." "Ki yi biyayya ga mijinki yi na yi bari na bari a aure shi ke kara danƙon soyayya.Duk abunda ya umarce ki ki yi Matukar bai saɓawa addinin Muslunci ba." Jinjina kai ta yi tare da cewa "Ina sha Allah." "Ki kasance mai biyayya ga mijinki, mai kyautata masa a cikin gidansa. Idan ya hanaki, ki hanu, idan kuma ya umurceki, to kiyi masa biyayya daidai gwargwado, domin haƙiƙa shi ɗin tamkar uba yake a gareki" - "Matan zamanin baya, ba wani cikakken ilmi ke garesu ba, amma sun san yadda zasu tarairayi mazajensu cikin ƙauna da kyautatawa, da hakan har suka kai gaci, sai ka daɗe bakaji anyi sakin aure ba, sabida iya inganta soyayyar dake tsakanin mata da miji" - "Amma yanzu matan zamani ga ilmin, amma saidai da yawansu basu iya kula da miji ba, saidai tarin kishi mai yawa, dalilin hakan sai kaga mace-macen aure ya yawaita a wannan zamanin" Haka ya cigaba da mata nasiha sosai, kuma jikinta ya yi sanyi sosai. Daga nan suka ɗan taɓa fira ganin magrib na gabatowa ne ya umarce ta da ta tashi ta koma cikin gida. Da misalin karfe goma na dare yana zaune a falo yana kallon t.v sai Amina ta fito daga ɗakinta. Sanye ta ke da rigar barci wacce ita da babu marabarsu kaɗan ne, dan rigar iya rabin cinyarta ta ke mai shara-shara komai na jikinta a bayyane ya ke. Ta fito tana taku ɗaya bayan ɗaya sai ƙamshin turare ta ke yi, wanda ƙamshin ne ya saka Adamsy ɗagowa ya kalle ta. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke idanunsa daga kallonta ya maida kan t.v. Har ta gifta ta gabansa ta nufi fridge bai sake kallonta ba. Buɗe fridge ta yi ta ciro youghurt da kofi ta zo ta zauna a kujerar da ke fuskantarsa, ta zuba a kofi ta fara sha tana satan kallonsa. Ta ga ko kallonta bai sake yi ba, mamaki ne ya kama ta shi da idan ya ganta haka hankalinsa ke ta shi ta ke ya ke janyota jikinsa ƙarshe sai ya biya buƙatarsa da ta tado masa amma yanzu ko gezau kamar wani dutse. Sanin da ta masa sam bata iya hakuri da ita baya iya ƙyale ta indai ya ganta a haka amma wai yau shi ne ya kauda idonsa kamar ba Adamsy da ta sani ba. Kuma ko da ya bar garin nan da sha'awarta ya tafi saboda ya bukaci kwanciyar aure da ita ta bijire masa ya tafi da ɓacin ran abunda ta masa. Sannan yanzu ya dawo bata gabansa ma ya share ta, tambayar kanta ta fara yi ko dai ya fara bin matan banza ne? Ga shi girman kai ya hana ta bashi haƙuri idan ma fushi ya ke da ita. Ganin ko kallo bata ishe sa ba ya sa ta tashi ta nufi ɗakinsa dan ta san tabbas idan bata bishi sun kwana a dakinsa ba dole zai kira ta zuwa ɗakinsa. Har ƙarfe goma sha ɗaya da rabi bata ga ya kira ta ba kuma ita bata jin zata iya binsa ɗakinsa sai ya biyo ta ko ya kira ta. Shi ma share ta ya yi dan baya son abunda zai kara mata masa rai, dan ya san idan ta faranta masa na awa ɗaya daga ta bata masa rai na awanni biyar. Kuma idan ta faranta masa na sati ɗaya sai ta bata masa rai na wata ɗaya. Ta shi ya yi ya nufi ɗakinsa tare da faɗawa kan gadon yana jinsa ba walwala da kuzari tamakar ya rasa wani sashe na jikinsa. Komawa ya yi yana ta tunane-tunane, daga ƙarshe ganin Amina bata shigo bane ya sa ya fara tunanin kiranta a waya, dan gani ya ke idan ya share ta kamar bai kyuta mata ba. Wayarsa ta lalubo ya tura mata text message kamar haka :_UWAR GIDA RAN GIDA, AN SHANYA NI AI SAI A ZO A BAZA NI HAKA NAN KO_ tura mata ya yi tare da kishin giɗa yana tunanin halinta, ita ce ta masa laifi amma shi ke rarrashinta, dan kullun sai Umma ya tunasar da shi cewa Amina amana ce bata yarda ya ɓata mata ba, sau tari albarkacin Umma ta ke ci ya ke ƙyale ta idan ta masa laifi. Tana kwance ta ji shigowar messages a wayarta, san shi ne kamar ba zata duba ba sai kuma ta duba ta karanta tare da cewa "Sai yanzu da buƙatarka ta tashi ka san da ni, to ba inda zan je sai na ja aji." Gyara kwanciyarta ta yi tare da yin tsuki. Jin shiru ne ya sa shi ɗaga waya ya danna mata kira, sai ya ga an katse kiran. Sake kira ya yi ya ji wayar a kashe. Kamar ya share ta amma ba zai iya ba, duk da ba laifinsa bane amma gani ya ke kamar bai mata adalci ba. Tashi ya yi ya nufi ɗakinta yana tura ƙofar sai ya ji ta a datse. Knocking ya yi tana jinsa sai ta yi kamar bata ji ba, shima ya san da gan-gan ta yi, tunda ya kira ta sai ta katse. Juyawa ya yi tare da komawa ɗakunan, wayar Humaira ya kira suka fara fira. Sai da ya ji alamar tana jin barci sannan ya yi mata sallama ya katse kiran Haka suka cigaba da zama har Adamsy ya kwashe kwanaki uku a garin Katsina, ranar da aka ɗaura auren ne bayan ya dawo daga wajen dinner ne ya samu Amina a falo, tana waya amma daga ganinsa sai ta yi saurin katse kiran wayar alamar rashin gaskiya. Kallo ɗaya ya mata ya gane bata da gaskiya. Bai kula ta ba duk da cewar sallamarsa ma bata amsa ba, ɗakinsa ya nufa dan dama a gajiye ya ke. Allah ya sa dai yau an gama hidimar biki. Bathroom ya wuce dan watsa ruwa. Na jimawa ya fito sanye da white bathrobe, wani barci ya ke jin yana zuwa masa, a haka ya nufi gadon ya kwanta. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi. Ko Humaira da suke firar dare ka fin ya yi barci, ba su samu damar yi ba. Washe gari da safe sai ga Umma ta zo gidan. Yana barci ya ji ƙarar wayarsa, a hankali ya buɗe idanunsa tare da ɗaukar wayar. Ganin Umma ce ya sa ya ɗaga tare da cewa "Assalamu alaikum" "Wa'alaika salam" "Barka da safiya Umma." "Yauwa barka dai, ina falonka." Daga nan ta katse kiran wayar. Ta shi ya yi ya ɗauki jallabiyarsa ya saka. A falo ta sa me su tana zaune akan kujera Amina na zaune a saman carpet. Durƙusawa ya yi cikin girmamawa ya gaida Umma, ta amsa masa ba yabo ba fallasa. "Dama na zo ne akan maganar da matarka ta mani na cewa akwai wani mai magani a ƙasar Niger. Wai ya kware akan irin matsalar matarka, mutane da yawa sun je kuma sun dace. Shi ya sa koda ta sanar da ni na ga yakamata ta je, tunda an yi na asibiti har an gaji ba'a dace ba har ƙasar waje an fita da ita amma shiru. Jinjina kai ya yi tare da tuna wane irin hali ne da Amina, suna kwana gida guda amma ba zata iya faɗa masa buƙatar da ta ke da shi ba har sai mahaifiyarsa ta shiga ciki. "To wai ance mata masu irin matsalarta miliyan biyu ya ke aiki, kuma wai ana dacewa." Kai ya jinjina tare da cewa "Ba komai ita da wa zasu tafi Niger ɗin?" "Wai ƙawarta da ta taɓa zuwa Niger ɗin wajen mutumin." "Ba matsala zan bada." Kallon Amina ta yi tare da cewa "Shikenan ko akwai wani abu.?" "Eh akwai" "Ina jinki." "Dama za'ayi bikin ƙawata ce shi ne na ke so na canza sarƙoƙina da ɗan kunne da su warwaro da zobe duk ina son a siya mani da gudunmawa da zan bata. Idan aka haɗa jimilar kuɗin da na zuwa wajen magani Niger da hidimar bikin duka-duka jimilar kuɗin Naira miliyan biyar." Adamsy ya kalle ta da mamaki tare da cewa "Miliyan biyar da kika ce? Haba Amina wane..." "Babana ai bazai gagare ka ba, miliyan biyar ai ba komai bane a wajenka, kuma haihuwar nan ai kaina kana sonta, kuma a wajen bikin ƙawarta zata so ace tayi bajinta, idan baka da halin ni daina cika mata Naira..." "A'a Umma ki barshi kawai zan bata." Nan ta dinga masa addu'a tana washe baki, dan yanzu shima lamarin Umman ya fara basa mamaki, da duk abunda Amina ta faɗa mata ta zauna, bata ma bin ra'ayinsa Kallon Amina ya yi tare da cewa "Ki shiga dakina ki ɗauko mani wannan akwatin silver colour." Cikin rawar jiki ta tashi dan ta san akwatin kuɗi ne ya ce ta ɗauki. A can kuwa Kaduna Humaira duk ta damu da rashin waya da basu yi Adamsy ba. Kasancewar jiya da ya dawo biki a gajiye ya ke bata samu damar yin wayar ba, ballantana ta ji muryarsa. Dan haka karo na farko kenan da ta lalubo lambarsa ta danna. masa kira. Dai-dai lokacin da Kiran Humaira ya shigo wayar, Amina na jin karar wayar. Bayan ta ɗauko akwatin ta ji wayar na sake ruri, ƙarasawa ta yi kan gadon ta ɗauko wayar tana duba mai kira. Zaro idanu ta yi cikin tsoro tare cewa "What?" Sunan da ta gani ne ya yi masifar ɗaya daga mata hankali *my Happiness* cikin ta shi hankali ta saki wayar ta ke sai ta faɗi ƙasa, har zuwa lokacin wayar bata daina ruri ba . Afusace ta nufi wayar . *_Masu cewa na dinga ƙara maku yawan pages, k yi haƙuri abubuwa sai a hankali* *Daga laƙalamin*✍️ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) 09065327995 Love you oll😍😘 Comments & share *ADAMSY* ~New blockbuster from~ Zainab Abdullahi K.N.T (Maman Ihsan) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 *GARGAƊI* Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ne, dan haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba. *BISIMIILLAHI RAHAMANI RAHEEM* Page4️⃣6️⃣&4️⃣7️⃣ Sunan da ta gani ne ya yi masifar ɗaga mata hankali, *my Happiness* cikin tashin hankali ta saki wayar da ke hannunta ta faɗi ƙasa, har zuwa lokacin wayar bata daina ruri ba. A fusace ta nufi wayar ta ɗauka tana shirin amsa kiran kenan cikin rashin sa'a kiran ya katse, duba wayar zata yi amma sai ta ga wayar da password. Cikin baƙin ciki da ta takaici ta nufi hanyar fita ta fice daga ɗakin. Tsayawa ta yi tare da yin wani tunani, idan ta je masa da zafi da rashin hankali ba zata samu abinda ta ke nema ba. Dan haka sai ta yanke shawarar amfani da salonta na baya, wanda ɓoye kishinta har ya saki jiki da ita ya sanar da ita komai. Dan haka ta yi ƙoƙarin ɓoye halin da ta shiga na baƙin ciki, sannan kuma ta aro farin ciki ta yafa. Ƙarasawa ta yi wajen da suke zaune ta ajiye masa akwatin tare da wayarsa a gabansa. Password na buɗe akwatin ya saka sannan akwatin ya buɗe. Kuɗi ya fito Naira miliyan biyar ya bata. Amsa ta yi tana washe baki tare da masa godiya. Umma ce ta kalle shi ta ce, "Babana bai dace kana ajiye kudi masu yawa haka a gida ba, rudki ne gaskiya, na sha faɗa maka haka. Jinjina kai ya ya tare da cewa "To Umma in sha Allah zan daina." "To Allah ya sa ka daina." Idanunta ne suka sauka akan Amina wacce ta faɗa cikin duniyar tunanin wace ce wannan da ta kira Adamsy a waya. "Kaga Yaya dan Allah bani aron wayarka na ɗan yin kira, tawa wayar ce ba charge." Kallon mamaki ya mata tare da cewa "Ga wutan nan 24 hours nan me zai kawo rashin charge kuma?" Yana kai ƙarshen zsncensa sai kiran Humaira ya sake shigo wayar, tunda ya ga *My happiness* ke Kira sai ya kalli Umma ya ga hankalinta na kan T.V, sai ya kalli Amina ya ga kallonsa ta ke tana kallon wayar, dan haka ya katse kiran wayar sannan ya maida wayar airplane mode yadda kira bazai sake shigowa ba. Ajiye wayar ya yi a gefe, inda ya kalli Amina ya ce, "Ki shiga ɗakina zaki ga ɗayar wayar ki ɗauka ki yi kiran wayar da ita." "Yaya ita wannan fa?" "Ba sosai na ke amfani da ita ba, dan ba kowa na ke kira da ita ba." Ba haka ta so ba amma ta shiga baƙin ciki zuciyarta sai zafi ta ke mata. Shiru ta yi ta kasa magana dan takaici. Kuɗi ya ɗeba masu yawa ya miƙawa Umma, Umma sa masa albarka ta ke yi. Sallama ta masu tare da ficewa daga gidan bayan ta saka Adamsy albarka. Ta shi ya yi ya ɗauki akwatin ya nufi ɗakinsa. Itama ɗakinta ta wuce ta ajiye kuɗin, sannan ta nufi ɗakinsa. Tura ƙofar ta yi a hanakali, waya ya ke yi da Humaira yana cewa "Idan ba ni na kira ki a waya ba kada ki dinga kira na." Yana jin motsi ya dan Amina ce dan haka ya cewa Humaira "Ina zuwa zan kira ka anjima." Daga nan ya katse kiran wayar tare da kallon Amina, itama shi ta ke kallo . "Wayar na zo amsa" Da hannunsa ya nuna mata wayar tare da cewa "Ga wayar can ki ɗauka." Shi a tunaninsa wayar ta zo ɗauka . Daga nan ya shiga bathroom dan yin wanka. Ɗaukar wayarsa da ya gama magana ta yi, amma password ya hana ta bincike, mamaki ta ke yaushe ya fara saka password a waya? Shi da kullum wayarsa ba password har ta ɗauka ta yi abinda zata yi da ita, amma yanzu ga password lallai akwai wani al'amari da ya ke ɓoyewa bata ɗauki wayar ba ta fice dan dama ba shi ya kawo ta ba. A ɓangaren Humaira kuwa jikinta ne ya yi sanyi, ta ga ya saba kiranta duk dare bai kira ta ba jiya, sannan yau ita ta kira yana ta ringing ba'a ɗaya ba da ga ƙarshe ta ji wayar kashe . Sannan yanzu ya kira har sun fara magana ta ji ya maida linzamin sunan zuwa namiji, wai ina zuwa zan kira ka anjima. Wato tsoron matarsa yake ko me? Sannan ya ce kada ta sake kiransa a waya idan ba shi ne ya kira ta ba, anya kuwa adalin miji na samu? Da wannan saƙe-saƙen ne har barci ya ɗauke ta bata sani ba. Amina na zuwa ɗaki kuwa sai ta ɗauki wayarta ta dannawa Umma kira, lokacin Umma shigarta falonta kenan ta zauna ta ji ƙarar kiran waya. Ganin sunan Amina ya sa ta ɗaya d'aga da sauri tare da cewa " Wannan miliyan biyar ɗin kada ki kuskura ki taɓa su, na ɓullo da wannan dabarar ce kasancewar tunda ya koma Kaduna muka rage samun kuɗi a hannunsa, da idan yana nan baya kwana biyu bai fitar da kuɗi ya bani ba idan ya zo, amma tunda ya koma can to sai dai idan wani abu ya kare ya sa a kawo amam ba wani kyautar kuɗi." "Umma har miliyan biyar ai na ga kuɗin sun yi yawa." "Ji wani zancen banza, kuɗi suna yawa ne, maza ki je idan ya fita ki zuba kuɗin a ɗaya account ɗin da muke tarawa kuɗi." Dariya Amina ta yi tare da cewa "Umma wallahi kin iya dabarar cin kuɗi, shi da yanzu ya dauka cewa da gaske ne zamu je Niger kuma ƙawata zata yi aure " Ta ƙarasa maganar tana mai cigaba da dariya. Nan dai ta saki ajiyar zuciya tare da cewa "Umma ni ina zargin kamar yana neman wata yarinya zai aura." "Me ye hujjarki?" "Lokacin da na shiga ɗakinsa wayrsa aka kira na ga sunan da ya yi saved da my happiness,na so na ɗaga amma ta katse kuma ta sake kira bai daga ba, da na bishi ɗakin dan na tabbatar na ji yana magana kuma kamar namiji ne wai zai kira shi." Shiru Umma ta yi tana nazarin maganar Amina kafin ta ce, "Ki barni da shi tunda ya na mani kallon mahaifiyarsa ba abinda ya ke ɓoye mani, zan bugi cikinsa na tabbatar da kaomai ya tafi dai-dai ." "To shikenan Umma wallahi har hikima ya yi sanyi wai an jefi kaza da gishiri." "Kada ki damu koma mene ne ina da hanyoyin da zan gano duk abunda ya ke aikatawa." Daga nan suka yi sallama ta katse kiran wayar. Bayan Admsy ya fito daga wanka ne ya tarar Amina bata cikin dakin. Zama ya yi a gefen gadon ya lalubo lambar Humaira ya danna mata kira. Tana cikin barci ta ji karar wayarta, a hankali ta buɗe ido ta lalubo wayar, ɗagawa ta yi tare da cewa "Assalamu alaikum" Murmushi ya yi tare da cewa "Sarauniyar tsoro kin tashi lafiya?" Dariya ta yi sosai ba tare da ta yi magana ba. "Ya kike?" "Lafiya lau?" "Ma sha Allah." "Am um na ji kana cikin magana lokaci guda sai ka canza kamar ba da ni kake magana ba da namiji kake yi." "Eh haka ne." "To me ya sa?" "Saboda bana son ta san da mace na ke magana." "Wace ce?" "Matata ce." Wani abu mai ɗaci Humaira ta ji a maƙoshinta, shiru ta yi ta kasa magana, har ya cigaba da cewa "Kina jina?" "Uhm" Kawai ta ce a taƙaice. "Na ji kin canza ko kina kishi ne?" Shiru ta yi ita kanta tasan cewa tana kishinsa, dan duk lokacin da ta ji yana waya da matarsa ko ta ji ya ambaci ta sai ta ji ba daɗi, ta rasa dalilin haka." "Kin yi shiru." "Ni ba kishinka na ke yi ba, kawai dai..." Sai ta yi shiru ta kasa ƙarasa maganar. "Kawai dai me?" "Ba komai." "Ai ni ina son na ga kina kishi akaina, dan har daɗi ba ke ji." "Daɗin kishi kuma?" "Eh kishi alama ce ta ana son mutum, ko baki so na?" Shiru ta yi ta kasa cewa komai inda ya cigaba da cewa "To shikenan tunda baki sona bari na yi ta zama a wajen mai sona a Katsina, kinga ba zan dawo ba ballantana ki sake gani na, ba amfanin na koma inda ba'a sona ai." Tura baki ta yi tare da cewa "To waye ya ce maka ba'a sonka?" "Ana sona kenan na dawo?" Shiru ta yi ta kasa magana, inda ya cigaba da cewa "Idan ban ji an ce ana sona ba zan cigaba da zama ne a can" "To ai kaima ka sani." "Ni ban sani ba sai kin faɗa." "To eh" "Ba eh nake son ji ba." A kunyace ta fara magana ta ce, "Inaa inaa ina sonka." Daga nan ta katse kiran da sauri. Shi kuma wani farin ciki ne ya ziyarce shi har cikin zuciyarsa da gangar jikinsa. Haka kawai ya ke ta murmushi shi kaɗai zuciyarsa fes. A yammacin ranar ne Umma ta kira shi zuwa gidansa, duk yadda zata yi dan ta daki cikinsa ya faɗa mata gaskiya ko akwai wacce hankalinsa ya kwanta ya ke so amma fir ya ƙi sanar da ita zancen Humaira, har nuna masa ta yi ko ya ga wata yana son zai aura ya nuna mata cewa shi yanzu baya sha'awar sake auren wata mace a rayuwarsa. Da haka hankalinta ya kwanta har ya mata sallama ya tafi. Kasancewar ba da Direbansa ya ke ba shi kaɗai ne, da ya shiga mota kafin ya tada motar ne ya ya d'auki wayarsa ya kira Abdallah. Daga can ɓangaren Abdallah na zaune a falo ya ga kiran Amininsa, ɗagawa ya yi tare da cewa "Hellow Adams ya garin?" "Karo na biyu kenan dana yi wa mahaifiyata ƙarya, kuma duk a dalilinka, ka sa na yi auren sirri ba tare da sanin kowa nawa ba, hatta Mahaifiyar da ta haife ni bata sani ba. A zahirin gaskiya bazan iya cigaba da ɓoye mata ba, domin ba abunda ya kamata na ɓoye mata koda na ɓoyewa kowa." Ajiyar zuciya Abdallah ya sauke tare da cewa "Adams" "Na'am." "Ka yarda da ni?." "Na yarda da kai." "Kasan ba zan taba baka shawarar abinda zai cutar da kai ba ko?" "Na sani" "To da farko ka fara tunani, mata shida ko nawa ne ma ka aura, kuma dukkansu ba wacce kuka raba zama inuwa ɗaya a matsayin ma'aurata, wasu sun tare gidanka wasu basu tare ba waɗanda suka tare ba ku zauna na mintuna biyar a keɓe ba, wannan dalilin ya sa na yi tunanin akwai wata munaƙisa da ake shirya maka a bayan fage wanda ka kasa gane hakan. Shi ya sa na baka shawarar ka yi na sirri dan mu tabbatar da cewa shin daga kaine matsalar kamar yadda mafi yawan jama'a ke faɗa ko kuma wata munaƙisar ce, kaga yadda ka yi wannan a sirrance har ka zauna lafiya da ita to tabbas ba wata

Chapter 13 of 19