tun yanzu?"
"Eh mun tafi kawai da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, a bari ya huce ai shi ke kawo rabon wani."
"To shikenan ai sai mu tafi ko?"
Mallam kallamu ya tada mashin ɗinsa Mallam Musa ya hau bayan mashin ɗin suka bar kofar gidan.
Jama'ar da ke siyen doya wajen Humaira sai tausaya mata suke ganin yadda jikinta duk ya farfashe wani wurin kuma ya ɗuri ruwa.
Wani daga cikinsu ne ya ce,
"Amma duk yadda aka yi ba mahaifiyarki ce ta dake ki ba ko?"
Kai kwai ta jinjina ba tare da ta yi magana ba, inda ya cigaba da cewa
"Daga gani wannan bazai wuce sharrin kishiyar uwa ba, Allah ya saka maki wannan cin zalin da ta yi maki."
Nan dai mutane da ke wajen suka dinga alawadai da hali irin na Inna Habi.
Bayan sun kammala siya sun bibbiya ta kuɗi ne ta tashi daga wajen ta cigaba da tafiya ne sai tana ɗingisa ƙafa, wasu samari guda biyu ne suka kalle ta ɗaya ya ce,
"Ke! Doya zo nan."
Kallonsu ta yi ta ƙarasa kusa da su tare da ajiye robar doyar, ɗaya ya kalle ta ya ce,
"Ki saka mani na ɗari da hamsin shima wannan kisa masa na ɗari da hamsin."
Ya ciro ɗari uku ya bata. Ta amsa ta zuba masu doyar sannan ta zuba masu yaji da man ƙuli-kuli."
Tashi ta yi tana ɗan ɗingusawa ta miƙa masu, ɗaya ya kalli abokinsa ya ce,
"Wannan kamar gurguwa ce na ga yadda ta ke tadiya."
"Tana yawan bi hanyar nan ba gurguwa ba ce sai dai idan ƙafar ke mata ciwo ta bugu."
Ita dai bata ce masu komai ba ta zauna tana jiran su gama su bata roba ta ƙara gaba
Da suka kammala cin abincin sai suka bata roba ta ƙara gaba, tana tafiya tana ɗingisa ƙafarta ga yunwa da ke ƙwaƙukar cikinta ga doya tana gani ba hali ya ɗauka ta ci,dan ko guda ɗaya ta ci inna Habi ta ƙirga ta ga ba ko ɗaya sai ta duke ta sosai na kud'inta shiyasa duk yunwar da take ji bata taɓa mata kayan tallah.
Koda su Mallam Musa suka ƙarasa kamafanin Mallam Kallamu ne ya yi masa jagora har zuwa ciki,dai da aka shiga aka sanar wa manaja zancen ƙarasowarsa suka jira ya bada izinin shigowarsu suka shiga.
Nan dai manaja ya yiwa Mallam Musa bayanin cewa gidan da zai dinga gadin da kuma dawowar mai gidansa, kuma ya kasance kullum yana bakin aiki banda yawo indai ba aikensa aka yi ba ko wani ƙwaƙƙwaran dalili. Kuma Mallam Musa ya amince da zancen karshe suka yi masa sallama inda ya ciro kuɗi kimanin naira dubu biyar ya miƙawa Mallam Musa tare da masa bayanin daga gobe da safe aikinsa zai fara.
Sallam suka masa suka fice, Mallam Musa ya dauki dubu biyu cikin wannan kuɗin ya miƙawa Mallam Kallamu amma bai kar'ba ba.
Koda ya koma gida bai ga Humaira ba, sai dai Salam da ta dawo daga makaranta tana zaune akan tabarma tana cin doya.
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaikumus salam."
Inna Habi ce ta amsa masa, ya shiga ciki ya bai ce komai ba haka zalika suma ba wacce ta masa sannu da zuwa, a zuciyarsa yana murnar samun aikin nan da ya yi.
ya kalli Salma tare da cewa
"Baki ganni bane! Ko nine zan gaishe ki?"
Caraf Inna Habi ta karɓe da cewa
A'a Mallam akan me daga dawowarka zaka huce haushinka a kan Yarinyar nan, dama ka tsane ta ba sonka kake yi ba."
Jinjina kai ya yi
"Ki cigaba da goyon bayan yarinyar nan, ina matsayin ubanta baki nuna mata mahimmanci na ba. Ko da yake daga gobe ne ai, ba zaku ganni akai-akai ba ballantana raina ya ɓaci."
"Mallam ban gane abunda ka ke nufi ba, badai balaguro zaka yi ka barmu ba? To wallahi bazai yiwu, ka tafi ka barni da waɗannan yaran sai dai ka tafi da waccan shegiyar yarinyar mai kama da aljana."
"Karki damu ni kaina ina tausayin tafiya ina barta cikin halin da ta ke ciki, da da hali wallahi ta ƙafa ta ƙafar yarinyar nan Humaira, amma sai dai kash ba halin tafiya da ita.
"To wai m dai tukunna ina zaka tafi ka barni?"
Kafin ya yi magana ne sai suka ji sallamar Humaira . Ganin yadda take tafiya ne da raunuka jinkinta yasa Mallam Musa cewa
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Haumaira me ya same ki haka ne?"
Kuka ta saka masa tare da ƙatasawa kusa da shi ta ce,
"Sannu da dawowa Abba."
Janyo ta ya yi ya riƙe hannunta tare da cewa
"Me ya sa me ki haka ne 'yata? Naga yadda kike tafiya duk yadda akayi akwai targaɗe a ƙafarki, ga jikinki kamar ƙunar wuta."
Inna Habi ce cikin gadara da taƙama ta ce,
"Ni ce nan na dake ta."
Kallon mamaki yake mata
"Yanzu Habi wannan duk duka ne saboda rashin imani da tausayi irin naki?"
"Ƙwarai kuwa ko yanzu ta sake mani laifi irin wanda ya yi mani to wallahi sai na mata duka wanda ya fi wanannan da na mata."
"Yanzu har akwai laifin da yarinyar na zata maki wanda ta cancanci irin wannan hukunci?"
"Ƙwarai kuwa tunda ga shi nan na yi mata, akan ne ne bazanyi mata ba, in ɗora mata kokan saidawa ta fita har ta yi sakacin da za'a sace mani kuɗi sannan ka ce wai ba zan duke ta ba? Dole ne na daki kuɗina."
"Yanzu bayan an sace kuɗi kika mata duka kuma kika sake ɗora mata wani talla?"
"Ai dole tunda an sace kuɗin da wane kuɗi zamu samu na cefene tunda da kai da babu duk ɗaya ne a gidan nan."
Ajiye bokitin ta yi sannan ta mikawa Inna kud'in cinikin da ta yi.ƙirgawa ta yi sannan ta ce,
"Allah ya taimake ki."
Murmushi takaici Mallam Musa ya yi inda Inna Habi ta cigaba da cewa
"Ki je a cikin tukunyar can kan murhu ki ɗebi sauran tuwo ki ci."
Mamaki ne ya kama Mallam Musa inda ya ce,
"Yanzu duk wannan wuyar da tasha da tallar doyar duk ba zaki iya bata ba sai sauran tuwo na jiya, ita wannan da ta ke cin doyar fa?"
"Ita ai kuɗin uwarta ta ke ci."
Humaira ce ta nufi wajen tuwon ta duba tukunyar wani guntu ne ko isarta bazu ba, sannan ga shi ba miya."
Kallon Inna ta yi tare da cewa
"Inna tuwon mitsisi ne kuma ga shi ba miya."
"Kici haka nan, idan an tuƙa sabon tuwo sai ki ci."
Mallam Musa ya kalle ta tare da cewa
"Yakamata ki gasawa yarinyar nan jikinta dan akwai ciwo a ciki."
"Dai dai kada ta warke wallahi, bani da Wannan lokacin."
Kallon Humaira ya yi tare da cewa
."zuba ruwa a karamar tukunyar nan bari na leƙa shago na siyo maki indomie ki dafa kici."
Murmushi tayi dan rabon da ta ci indomie tun mahaifiyarta na da rai.
"Wallahi bata isa ba akan me zaka yi haka?"
"Ko me ta tuna sai kuma ta yi shiru ta ce,
"Shikenan ai siya mata."
Fita ya yi ita kuma Fatima ta ɗora tukunya yana kawo mata ta dafa indomie ta zuba attarigu da albasa.
Bayan ya dahu ne ta zo ta sauke tana shirin ɗebo ruwan zafin gasa ciwo. Dai-dai lokacin da Mallam Musa ya yi alwala zai tafi masallaci dan yin sallar la'asar.
Fitarsa ke da wuya sai Inna ta yi wa Salma alama da hannu wato ta je ta ɗauko tukunyar indomie.
Bayan Hamaira ta ɗora ruwan gashi kenan sai ga Salma ta ɗauki tukunyar indomie.
"Ina kuma zaki kai mani abinci."
"Gidan uwarki zan kai mako."
"Akan ne zaki zagi uwata?"
Bata kula ta ba ta kaiwa Inna tukunyar inda suka raba indomie biyu ta ɗauki rabi ta ba wa Salma rabi suka fara ci, inda Inna ta ce,
"Kiyi sauri ki cinye kafin ya dawo daga sallah ya tarar muna ci."
Kallon Humaira ta yi da ta durƙusa tana kallonsu hawaye kaimwai ke fita a idanunta, ga azababben yunwar da ya addabe ta.
Muryar Inna ta ji tana cewa
"Kuma wallahi kika sake kika sanarwa Mahaifinki wallahi ya fita ya barmu gidan nan sai na kusan kashe ki."
Daga nan suka cigaba da cin indomie inda Humaira ta koma ɗakinta ta kwanta ai rigar kuka ta ke kamar ranta zai fita.
Tafiya ya ke a motarsa zai nufi gidan Ummansa dan ya yi mata sallama gobe zai koma Kaduna, bankwana ya ke shirin zuwa mata, wayarsa ce ta fara ruri, gefen hanya ya tsaya ya yi parking sannan ya daga wayar
"Assalamu alaikum"
Daga can ɓangaren manajan ya amsa da
"Wa'alaika salam. Yallaɓai ina wuni."
"Lafiya ya ƙoƙari?"
"Alhamdulillah .ana gama komai yallaɓai mai gadin ma an samu gobe zai zo ya fara aikin."
"Okay an samu mai gadin?"
"Eh Mallam Kallamu ɗaya daga cikin masu mana gadin kamafani ne ya kawo abokinsa Mallam Musa sunansa, har munyi magana gobe da safe zai fara."
"To sannu da ƙoƙari."
"Bakomai yallaɓai Allah ya kawo ka lafiya."
"Ameen."
Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar ya cigaba da Driving nashi.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9
*ADAMSY*
~Anew blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*Sadaukarwa*
Wannan shafin sadaukarwa ne ga ƙungiya ta jajirtattun marubuta, fasihai kuma zaƙaƙuran marubuta masu fikira *ROYAL SATAR WRITER'S ASSOCIATION* Allah ya k'ara mana ƙwarin gwiwa.
🧏♀️💃 *INA KUKE BIG LADY'S KIKARANTA KOBAZE ANFANEKIBA ZE AMFANI WANI NAKI* 🧏♀️💃
🤩MAGANA A KEYI TA GLOIN SKIN🤩
(GYARAN JIKI SHINE MECE) DUK MACEN DABATA GYARA TO MUNA MATACE BAKAI AKIRATA MACEBA🤷♀️
HADDA MAZANMA🤨
💫 Hajiya shin kina buƙatar jikinki yayi kyau fatarki Takoma ɗanya shakaf tamkar ta jarirai ??? Kikoma tamkar zarah acikin taurari acikin mata yan uwanki✨✨✨✨✨domin fa hasken zarah dabanne💃
💫shin kina buƙatar fatarki Takoma tamkar ta jaruman Kaneewood kona novel?? Humm kinsan cewar dafata ne matan waje kekarɓe mana mazaje??🙄🙄🙄 To idan baku saniba ayau kusani, ƙyalli fata shine keruɗar mazajenmu dakuma samari kai harmada ƴammata🤷♀️
💫💫idan kinshirya gyara jikinki Hajiya kigarzayo domin samun ingatattun haɗin daze wanke Miki fatarki tass kikoma tamkar bala rabiya✨sabida ƙyalli da kyau babu kwailin balle abata miki fata, se haɗin zallar gargajiya na ƴaƴan itatuwa masu inganta lafiyar fatarki, *SABULUN WANKA, MAN SHAFAWA GA ƘAMSHI GA DAƊi, SEKUMA DILKAH WADDA ZAKIYIWA KANKI A CIKIN MINCI* dukkansu afarashi ɗaya za'a haɗa Miki duka ukkun wlh wlh wlh summa tallahi acikin mako ɗaya (one week) Zaki banbata fatarki data sauran mutane domin ingatattun kayane kuma inada granty akansu, duk wadda tayi anfani dasu mako ɗaya bataga canjiba tazo wlh Allah zan bata kuɗinta domin ko haufi banayi akansu💪gaduk me buƙatar wannan haɗin ze iya tuntuɓar wannan nomber 👉 07037092176 🙏🙏🙏 munada maganin mata kala kala namatsi na daɗi danakomai ma munada harmada na maza wanda suke fama da matsala, gadukkan me bukatar kayanmu ga nomber nan ansaka ze iya nemanmu ako ina yake afaɗin duniya zamu kaimishi insha Allah🙏 sayen nagari meda kuɗi gida me kyau bayada tsada Ako ina mungode.🙏🤗
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM*
Page2️⃣0️⃣&2️⃣1️⃣
Daga nan suka yi sallama ya kashe wayar, ya cigaba da driving nashi.
Kai tsaye gidan Ummansa ya nufa, bayan yayi horn mai gadin ya buɗe masa gate ya shiga ya yi parking.
Gaisawa ya yi da mai gadin da sauran ma'aikatan gidan sannan ya nufi cikin gidan.
Tsaye ta ke sai kai da kawo da ta ke yi kamar mai safa da marwa.
Sallama ya yi ya tura ƙofar .
"Assalamu alaikum"
Dakatawa tayi tana kallonsa ta ce,
"Wa'alaika salam"
Kallonta ya ke da alamar tambaya ya ce,
"Umma lafiya kuwa, na ga sai kai da komo kike da alamar akwai damuwa."
Murmushi ta ƙaƙalo tare da cewa
"Bakomai Baba na kada ka damu."
Durƙusawa ya yi gaishe da ita cikin girmamawa, ta amsa masa cikin walwala, amma da ka kalle ta kasan hankalinta ba kwance ya ke ba.
"Umma idan akwai wata matsala ne ki sanar da ni , ba abunda zaki iya ɓoye mani, haka zalika nima bazan iya ɓoye maki halin da na ke ciki ba."
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
"Kada ka damu kanka da akwai damuwa kaima kasan bazan ɓoye maka ba."
"To shikenan tunda haka ki ka ce."
Daga nan ba wanda ya sake magana har tsawon mintuna biyu, daga bisani ya kalle ta ya ce,
"Umma gobe zan tafi Kaduna na zo na yi maki sallama ne."
Sai da ta ji gabanta ya faɗi rass cikin dakiya ta ce,
"Ni dai bana son ka yi nisa da mu Baba na, na fi son ya kasance kana tare da mu, muna ganinka kana ganinmu."
Kada ki damu Umma zan dinga yawan zuwa insha Allahu, na zaɓi na yi nesa da garin nan ne saboda abubuwan da suka faru a rayuwata, wata kila idan na nisanci garin zan samu sassaucin abinda na ke ji a zuciyata, domin zan samu canjin rayuwa."
Idan na fito na bi hanyar da ya kasance hanya ce na unguwar ɗaya daga cikin matayen da na aura ko nayi niyya sai na ji abun ya dawo mani sabo, gara na nisanci garin nan da abubuwa marasa daɗi suka faru da ni a cikinsa."
"To shikenan tunda ka matsa bazan hana ka ba, sai dai in tambaye ka shin zaka tafi da matarka ne?"
"A'a Umma ni kaɗai zan tafi sai dai zan dinga zuwa weekend."
"Amma yakamata ka tafi da ita gaskiya tunda kana da gida a can , ko dai ya ya kana tare da iyalinka ai ya fi."
"Haka ne, zan tafi da ita amma da farko ina so na je na ga yanayin wajen idan ya so daga baya zansa Direba ya ɗauko ta."
Ba haka ta so ba sai dai ba yadda zata yi tunda baice bazai tafi da ita ba, dan haka ta masa fatan alkhairi."
"To Umma ga wannan."
Kuɗi ya ajiye mata kimanin naira dubu ɗari biyu.
"Sannan kuma idan akwai wani abu da kike buƙata ko kuma ya ƙare sai ki kira waya na xansa aka wo har gida."
"Kada ka damu ai abincin da suke store da naman da suke fridge duk zasu kai mana wata ɗaya ma basu ƙare ba."
"To idan dai da wani abu sai a sanar da ni ko ta waya ne."
"To Allah ya yi maka albarka."
"Ameen Ummata."
Fira suka ɗan taɓa daga bisani suka yi sallama ya tafi.
Bayan tafiyarsa ne ta kira Amina a waya ta ƙara zuga ta tare da mata mummunan huɗuba, akan ta dage sai ta bi Adamsy Kaduna.
Gidansu Sadik abokinsa ya nufa, nan ma ya yi masa sallamar bankwana sannan ya nufi gidansa.
Kasancewar lokacin sallar la'asar ta yi ne yasa ya tsaya a wani masallaci ya ya sallah kafin ya nufi gidansa.
Koda ya isa gida kai tsaye ɗakin Amina ya nufa, tura kofar ya yi sa sallama.
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaikumus salam."
Kallonta ya yi ta sauke akwati tana ta koda kaya a cikin akwatunan guda uku.
"Kayan me kike haɗawa haka kamar wacce ta ke shirin barin gari.?"
"To ba garin zan bari ba?"
"Ina zaki je?"
"Kaduna mana ai ƙafa ta ƙafarka."
"Wai ba na faɗa maki cewa wannan tafiyar ni kaɗai zan fara yinta ba? Sai daga baya ne zan sa ki zo ba?"
"Nifa bazan yarda ba."
"Amina yaushe muka fara jayayya da ke ne? Bana son gardama kiyi abinda na ce maki kawai idan ba so kike mu samu matsala da ke ba."
Daga nan ya fita ya barta a ɗaki.
Ɓangaren Humaira kuwa tunda ta shiga ɗaki bayan Inna Habi da Salma sun cinye mata indomie da ta yi wahalar dafawa ga yunwa ta ya cinye ta, tana kwance tana riskar kuka tana riƙe cikinta da ke mata ƙwaƙula har barcin wahala ya yi awon gaba da ita.
Koda Mallam Musa ya dai daga masallaci ya tarar da Inna Habi da Salma zaune, lokacin har sun kammala cin indomie.
Kallonsu ya yi tare da cewa
"Ina Haumaira ta ke?"
Salma ce ta yi saurin cewa
"Yanzu ta kammala cin indomie ta shiga ɗaki wai zata huta."
Kai tsaye Mallam Musa ya nufi ɗakin da Humaira ta ke ganinta kwance ya juya baya da alama barci ta ke yi, dan haka ya juya ya koma wajen Inna Habi ya ciro kuɗi Naira dubu uku ya bata.
Washe baki ta yi tare da cewa
"Mallam ina ka samu kudi haka?"
Wani mutum ne ya ba ni su akan uban gidansa zai dawo nan garin da zama, to ni ne wanda zan dinga masa gadi, shine ya bani kyautar dubu biyar, gobe zan da sassafe zan fara aiki."
"Yanzu shi wanda uban gidansa ne zai dawo nan shine ya baka dubu biyar? Ina ga shi mai gidansa da zaka yi aiki a gidansa? Ka ce kakarmu ya yanke saƙa."
Shi dai shiru yayi yana sauraronta inda tacigba da cewa
"To ina sauran dubu biyun? Naga nan dubu uku ka bani."
"Na siyawa Humaira indomie kuma za riƙe wasu kuɗi a hannunsa."
"To can zaka dinga kwana ne kuma nawa zasu dinga biya ka?"
"Can zan dinga kwana kuma ko nawa zasu biya ni ban sani ba, sai mai gidan ya iso."
"To gaskiya sai dai ka bani sauran canjin da suka rage, saboda tsawon lokaci baka bada kuɗin cefene a gidan nan, ni ce nake ɗaukar ɗawainiyar komai a gidan nan, baki da kuɗin da zaka biyan dan haka duka dubu biyar zaka bani idan ya so na Indomie da Humaira ta ci na yafe mata."
Haka ta dinga zuba masa rashin mutunci har ya mika mata sauran kud'in dan masifarta.
Da misalin karfe goma na dare, ya fito daga bathroom sanye da white bathrobe a jikinsa, yana goge kansa da farin towel.
Lotion ɗinsa mai ƙamshi ya shafa da body spray sannan ya haura saman gadon yana jiran shigowar Amina.
Har ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare yana jiran Amina amma bata zo turaka ba gashi kuma yan buƙtarta.
Wayarsa ya ɗauka tare da lalubo wayarsa ya tura mata daƙo kamar haka.
"Ina jiranki"
Bayan ya tura mata saƙon ne sai ya ajiye wayar.
Ita kuma tana kwance a ɗakinta sai juyi ta ke yi ta rasa hanyar da zata bi akan tafiyarsa ɗin nan, ƙarar shigowar messages ne ya shigo a wayarta, dubawa ta yi ta karanta, ajiye wayar ta yi bayan ta karanta sauƙon ta yi tsuki tare da cewa
"Ba inda zan zo, tunda har kasa zanyi kwanan baƙin ciki to kaima sai dai ka yi kwanan baƙin ciki dan ba zaka ɓata mani rai a banza ba sannan na biya maka bukatarka ba."
Jin shiru har ƙarfe goma sha biyu bata zo ba ne yasa ya kira wayarta, ringing ya yi bata ɗaga ba har ya tsinke.
Jin kiran ya tsinke ne ya sa shi yin tunanin ko barci ta ke yi, dan haka ya miƙe tsaye tare da nufar ɗakinta, dan shi a buƙace ya ke da matarsa a wannan lokacin.
Tura kofar ya yi ya shiga tare da sallama duk da a tunaninsa ta yi barci ne, wutar ɗakin a kashe ya ke sai ya kunna, a can ƙarshen gado ya hange ta kwance a tunaninsa barci ta ke yi, kashe hasken ya yi kai tsaye ya nufi kan gadon ya haura, shiga cikin bargon ya yi tare da janyota jikinsa, a firgice ta tashi tare da cewa
"A'uzubillahi minashshaiɗanir rajim."
Hasken wayarsa ya kunna tare da cewa
"Amina ni ne fa."
"Ai nasan kaine."
"Shine kike mani ta'awizi kamar kinga shaiɗani ne ya kusanto ki?"
"To me ka zo yi ɗakina?"
"Baki ga kiran wayata bane?"
"Na gani mana."
"Shine baki zo ba?"
"Kai da ka matso ka ke da buƙata ai na ga kazo, kuma duk da haka ba zaka samu abinda ka ke buƙata ba, dan bazai yiwu a ce ka ɓata mani rai kai ka zo na faranta maka rai ba."
Mamaki ta bashi duk da cewar wannan ba sabon abu ne a wajensu ba, ko ya buƙace ta sai ta ga dama ta ke yarda da shi idan bata ga dama ba kuwa haka ta ke hana shi kuma ya haƙura ya ƙyale ta.
"Wai me ya matsalarki ne wannan abun da kike ƙoƙarin aikatawa jefa ki zaiyi cikin fushin Allah, mijinki ne ni, baki san duk matar da ta bijirewa shimfidar mijinta Mala'iku suka tsine mata har sai gari ya waye ba, ko kina son ne ki kwana cikin tsinuwar Mala'ikun Allah?"
Jin ta yi shiru ne ya sa shi tunanin ko ta haƙura ne, dan haka ya sake janyo ta jikinsa nan ta ture shi tare da cewa
"Adamsy wallahi ba zaka taɓa samun abinda ka ke so ba wallahi yanda ka ɓata mani rai nima sai na bata ranka kowa ya kwana cikin baƙin ciki."
Duk da tsananin buƙatar da ya ke da ita haka ya hakura ya koma ɗaukinsa dan inda sabo ya saba, mararsa da ke ɗan masa ciwo ne yasa shi buɗe drawa ya ciro maganin da ya ke sha a duk lokacin da sha'awar ta taso masa bai samu biyan buƙata ba."
Washe gari da safe bayan ya kammala shirinsa na tafiya, ya shirya cikin ƙananan kaya baƙin wando da jar riga, Direbansa na jiransa a harabar gida.
Ba wasu kaya ya ɗauka ba 'yan kadan ne a haka sai system ɗinsa da wayoyinsa, kiran Direban ya yi a waya yazo nan falo ya ɗauki kayansa ya kai mota.
Shi kuma ɗakin Amina ya nufa, da sallama ya shiga ɗakin tana zaune ta haɗa tagumi ko sallamar bata amsa ba,shima bai damu ba kasancewar yasan akwai wadatattun kayan abinci da ya siya komai ya ajiye mata hakan yasa ya ciro kuɗi kimanin naira dubu ɗari biyu ya ajiye mata.
"Ni zan tafi."
"Allah ya raka taki gona."murmushin btaikaici ya yi sannan ya fice abinsa.
Ma'aikatan gidan ma duk ya masu kyautar kuɗi sannan ya shiga mota direba ya motar suka kama hanyar Kaduna.
Ɓangaren Humaira kuwa tunda ta kwanta tana barci bayan fitar Mallam Musa Inna Habi ta tayar da ita ta hanyar watsa mata ruwa, ta shi ta yi a firgice.
Inna Habi ta saka ta aikin tankaɗen garin tuwo har ta gama dai a galabaice ga tsamin jiki.
Bayan an gama tuwon ne an zuba mata ta ci tayi sallar isha'i sai ta ɗebi ruwan zafi ta gasa jikinta a ɓanɗaki, bayan ta fito ne sai ya ɗebu wani ruwan zafi ta zauna tana gasa ƙafarsa tana 'yar sakin ƙara, inna Habi da Salma suna kallonta ba wacce ta kula ta, Mallam Musa ne da shigowarsa kenan ya ƙarasa wajen yarinyar yana duba ƙafar, nan ya ga bugawa ce ba targaɗe ba.
Fita ya ya ya siyi man zafi ya shafa mata sannan ya ce ta je ta kwanta.
Washe garin yau kuwa sai ta tashi da sauƙi Alhamdulillah.
Duk da haka sai da inna Habi ta ɗora mata tallan koko, bayan ta dawo ne Mallam Musa na shirin zuwa gidan aikinsa ta matsa kan cewa zata bishi ta ga gidan da yake, ba musu kuwa ya amince kan cewa su tafi tare, dan ya na tausayinta idan ya tafi ya barta da inna Habi Allah kaɗai yasan halin da zata shiga a hannun inna Habi.
*Daga alƙalamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
09065327995
Love you oll😍😘
Love you oll😍😘
Comment & share
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsSG6oTSnSa3L81qAg5hs9
*ADAMSY*
~A new Blockbuster from~
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
❤️YAR GIDAN TAFEEDAH Beauty world ❤️
1,. Snow Whitening Soap
2,. Snow Whitening Oil
3,. Glowing Oil
4,. WhiteningFace cream
5,. Pure whitening scrubs
6,. Lightening Dilka Soap
7,. Anti-dandruff Hair Oil
8,. Shampoo Deep Comfortable Deep Cleaning
9,. Maganan infection da na Sanyi
10,. Ruwan matsi
11,. Gunmban Dabino da
Madara, Gunmban Kwakwa da Madara
12,. Tabajen Zo Mubaje
13,. Tsumin Tabani ka Ji Ruwa
14,. Sweetener powder
15,. Kamshi Khumar
16,. Kamshi Oils
17,. Pure Shea Butter and pure Alydi Oil And More
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka q guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMIILLAH RAHAMANI RAHEEM*
Page2️⃣2️⃣&2️⃣3️⃣
Dan yana tausayin hain da zata shiga idan ya tafi ya barta da Inna Habi.
Ya figo da jakar kayansa Humaira ya amsa ta riƙe masa, ya shiga ɗakin Inna Habi ya mata sallama,ta fito tana cewa
"Mallam ba zaka kara mani wani kaɗan ba kasan halin da ake ciki."
"Na faɗa maki dubu biyar nan bani ita aka yi, sai dai ku yi haƙuri tunda ga sana'a kina yi idan na samu albashi ai komai zai yi dai-dai."
Albashi da nan da wata ɗaya kenan, sai mu ci uwar me idan ka tafi, to tukunna ma dai ita wannan yarinyar waye zai ciyar da ita tunda ubamata bai aje ba."
"Habi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 19