a kanki.”...
Ta ɗago kai da sauri tana kallonsa, sai kuma ta ga shima itan yake kallo, ta ja tsaki...
“Me kake kallo?!”
ta faɗa cikin fushi, hawaye na zuba daga idanunta...
King Diamond ya tsaya a gabanta, ya haɗa hannayensa a ƙirji. Fuskar Ayat dake kansa ta cika da nutsuwa da iko...
“Idan kina son ki dawo siffarki…”
Ya fara faɗa a hankali...
Ayat ta miƙe tsaye cikin ruɗani, zuciyarta na bugawa da ƙarfi...
“Da gaske?”
ta faɗa da muryarsa, tana matsowa kusa...
“Ka san yadda zan dawo? Ka san yanda zan koma ni?!”..
Idanunta suka cika da bege, duk da fushin dake zuciyarta...
“Faɗa min,”
ta ce da sauri,
“Me zan yi? Mene ne zan biya? Komai zan yi!”..
King Diamond ya ɗan karkatar da kai, ya kalleta kai tsaye. Sai wani murmushi mai ban tsoro ya bayyana a fuskar dake kansa, murmushin da bai kai zuciya ba...
“Abu ɗaya ne kawai,”
ya faɗa cikin sanyi...
Ayat ta runtse idanu na ɗan lokaci, zuciyarta na dukan ƙirji..
“Mene ne?”
ta tambaya cikin sauri..
Ya matsa ƙafa ɗaya gaba, ya rage tazara tsakaninsu..
“Dole ne,”
ya ce a hankali,
“mu sake sumbatar juna.”
Ayat ta tsaya cak.
Numfashinta ya tsaya...
“Me…?”
ta furta a firgice.
Ta ja da baya da sauri, idonta a zazzare.
“Ka haukace ne?!”
ta saki kuka.
“Ka manta wacece ni?!”
Ta nuna shi da yatsa tana rawar jiki...
“Ni makiyarka ce! Ni ce wadda ta zo ta kashe ka! Ta yaya zaka ce min haka?”..
King Diamond bai ja da baya ba. Murmushin nan bai ɓace daga fuskarsa ba ya ce,
“Kamar yadda muka yi a farko,”
ya ƙara faɗa cikin sanyi,
“tare da haɗuwar jini…
tare da haɗuwar rai.”
Ayat ta dinga girgiza kai tana kuka.
“A’a…
A’a…
Wannan ba zai yiwu ba…”
Ta dafe ƙirjinta.
“Wancan kuskure ne! Ba ni da iko a kaina a lokacin!”
Ta ɗaga kai ta kalle shi da tsananin fushi.
“Ba zan sake kusantar ka ba!”
ta faɗa cikin ƙarfin hali..
“Ko da zan mutu a wannan siffar!”..
King Diamond ya ɗan sunkuya kaɗan har fuskokinsu suka kusan haɗewa. Ayat ta ja numfashi, zuciyarta na bugawa...
“Ki yi tunani,”
ya faɗa a hankali, muryarta dake fita a bakinsa na girgiza shi...
“Ko ki zauna a wannan jiki…
ko ki dawo naki.”
Ayat ta lumshe idanu da ƙarfi, hawaye na sauƙa..
“Kai mugu ne…”
ta furta a raunane,
“Ka fi yadda na zata.”..
Ya ɗan miƙe tsaye, yana kallonta daga sama..
“Ba mugunta ba ce,”
ya ce cikin sanyi,
“ƙa’ida ce.”
Ayat ta buɗe idanu, ta kalle shi da wani kallo na tsana da ruɗani a haɗe...
“Idan na yi hakan…”
“ka rantse min cewa zan dawo ni.”
King Diamond ya ɗaga gira kaɗan.
“Idan hakan bai yi aiki ba,”
ya amsa,
“to babu abin da zai yi.”..
Ayat ta yi shiru.
Iskar kogin na busawa, ruwan na ƙara amo.
Zuciyarta ta rarrabu gida biyu...
Ta runtse idanu, hannuwanta na rawa..
“Ka juya,”
ta faɗa cikin sanyi.
“Kar ka kusanto ni yanzu.”
King Diamond ya tsaya, yana kallonta.
“Ki yanke shawara,
lokaci ba ya jiran kowa.”...
✨✨✨
Daren Alhamra ya yi nisa, amma Master Ibrahim bai ko kwanta ba. Yana tsaye a harabar fadar, idanunsa suna kallon sararin samaniya, yana jujjuya takobinsa a hannu. Akwai abin da yake damun sa, ya dace Inuwa ya dawo tun sa’o’i biyar da suka wuce, amma har yanzu babu labarinsa...
"Inuwa ba mutum ne mai taurin kai ko karya doka ba,"
Ibrahim ya raɗa wa kansa.
Ya nufi sashen ma’aikatan tsaro, inda ya tarar da wasu dakarun suna hira ƙasa-ƙasa. Cikin muryarsa mai kwarjini, ya daka musu tsawa..
"Wane ne a cikinku ya ga Inuwa tun bayan sallar azahar? Shin akwai wanda ya ga lokacin da ya fita ko ya dawo?"..
Dakarun suka kalli juna cikin fargaba. Ɗaya daga cikinsu ya matso ya rusuna,
"Master, rabonmu da shi tun safiyar hantsi. Ban sake sanya shi a ido ba."..
Ibrahim ya haɗe rai. Ya san akwai matsala. Ya juya da sauri ya nufi hanyar da take kai shi sashen dawakai. A can ya tarar da babban mai kula da dawakai yana shirin kulle wurin...
"Doki nawa ne babu a nan?" Ibrahim ya tambaya cikin hanzari..
Mai kula da dawakan ya bincika, sannan ya ce,
"Master, akwai doki ɗaya da aka fita da shi, kuma ban ga wanda ya ɗauke shi ba, amma dokin yana cikin dawakan da Inuwa yake kulawa da su."..
Wannan bayanin ya tabbatar wa Ibrahim cewa Inuwa ya fice daga fada. Amma ina ya tafi a cikin daren nan? Kuma me ya sa bai gaya masa ba?
Ibrahim bai tsaya wata-wata ba. Ya ɗauki dokinsa, ya kunna fitilar hannu mai ƙarfi ya fice daga masarautar cikin gudu. Yana da ƙwarewa wajen gane sawayen taku a ƙasa. Ya bi sawun dokin da aka fita da shi tun daga ƙofar gari, sawayen suka riƙa kai shi cikin daji, har zuwa hanyar da take kai mutum ga babban kogin nan da kowa yake tsoron zuwa...
"Me Inuwa zai je yi a wannan kogin har ya kai daren nan?" Ibrahim ya tambayi kansa, zuciyarsa tana bugawa da sauri.
Daidai lokacin da Master Ibrahim yake ƙoƙarin ƙarasowa bakin kogin, King Diamond ya ɗan karkata kansa, idanunsa waɗanda suke a siffar Ayat suka haska da wani irin haske mai nauyi. Ya fahimci cewa akwai bugun zuciyar ɗan Adam dake kusantowa cikin hanzari...
Ba tare da ya ce uffan ba, ya ɗaga hannunsa ɗaya ya kewaye su da shi. Nan take, wani irin shingen sihiri mai launin iska ya mamaye su haɗe da Ayat dake cikin siffarsa da kuma dokin dake can ɗaure. Wannan shingen ya mayar da su Fatalwa a idon ɗan Adam, babu mai iya ganinsu, jin motsinsu, ko ganin hasken sihirin dake wurin, amma su suna iya kallon duk abin da yake faruwa a waje....
Master Ibrahim ya bayyana a bakin kogin, riƙe da fitilar hannunsa dake ta haskawa. Ya zaro takobinsa, idanunsa suna yawo ta kowane sashi..
Ayat dake cikin siffar namiji ta daskare a inda take. Ta zura wa Ibrahim ido, zuciyarta tana bugawa da ƙarfi...
"Master! Me yake yi a nan?" ta faɗa a cikin zuciyarta. Ta so ta kwalla masa ƙira, ta so ta ce "Master, gani nan!", amma tana tunawa da muryar namijin dake fita daga bakinta da kuma siffar dake jikinta, sai ta toshe bakinta da sauri.
Ibrahim ya riƙa haska fitilar sa har daidai inda suke tsaye amma fitilar tana ratsa jikinsu ne kamar iska, bai ga kowa ba sai bishiyoyi da duwatsu. Ya tsaya daidai saitin inda dokin Ayat yake, amma ko dokin bai gani ba...
"Abin mamaki," Ibrahim ya raɗa yana goge gumin goshinsa. "Na tabbata sawayen takun dokin nan sun kawo ni har nan. Amma me ya sa komai ya ɓace? Me ya sa wurin ya yi tsit haka?"
Ya zagaya bakin kogin sau uku, yana duba ko da akwai rami ko wata alama amma sihirin King Diamond ya shafe komai. Ibrahim ya tsaya na wasu daƙiƙoƙi, yana jin kamar ana kallon sa amma ganin ba shi da wata hujja, sai ya girgiza kansa cikin shakku...
"Ƙila tunanina ne ya yaudare ni," ya furta cikin rauni... "Inuwa, kana ina?"
Ya jima a tsaye yana sauraron sautin ruwa, kafin daga bisani ya juya ya nufi inda ya bar dokinsa, ya fara tafiya a hankali yana waigowa har ya ɓace cikin duhun dajin...
Ayat ta sauƙe wani nauyayyen numfashi, jikinta har yanzu yana ɓari. Ta juyo ta kalli King Diamond wanda har yanzu yake tsaye cikin natsuwa...
"Ka ga abin da ka jawo min ko?" ta faɗa da muryarsa, cike da takaici ta ce...
"Master Ibrahim zai kamani da laifi idan bai ganni a fada ba kafin gari ya waye, masarautar nan za ta tashi a hargitse!"
King Diamond ya sauƙe hannunsa, shingen ya ɓace. Ya kalle ta da wani kallo mai zurfi.
"Ba zai gano komai ba... muddin kina kusa da ni."
Anan suka cigaba da zama har alfijr ya fito..
Ayat ta tsaya tana kallonsa. Ta sha kuka har idanuwanta sun kumbura, murya ta dusashe. A karo na farko ta sassauta muryarta...
“Dan Allah…”
ta fara cikin rauni, tana ɗan matsowa kusa,
“ka maida min siffata. Wannan ba ni ba ce. Ina jin kaina kamar baƙuwa a jikina.”...
Ta sauƙe numfashi mai nauyi...
“Ni gimbiya ce… ina da mutunci, ina da iyaka.”
King Diamond ya tsaya tsayin daka sannan ya furta..
“Sumbatar nan ita ce mafita,”
Kalmar sumbata ta buge ta kamar wuta. Ta tashi tsaye da sauri, tana zaro idanuwa..
“Me?!”
ta daka masa tsawa da muryarsa,
“Zan zabga maka mari kai da sumbatar! Kana da faɗin sumbata, sumbata, sumbata! Na bi sumbata da gudu!”...
Tana nuna shi da yatsa, hannuwanta na rawa...
“Na fahimci ka raina ni! Ka raina martabata!”...
King Diamond bai motsa ba. Ya ɗan karkatar da kai, murya ta fito cikin sanyi...
“To kuwa,
haka za mu ci gaba da kasancewa a nan… har tsawon rayuwa.”...
Kalmar rayuwa ta sauƙa a kirjin Ayat kamar theoretical hammer...
Nan ƙirjinta ya buga.
Ta kama ƙirjinta da ƙarfi, numfashinta a rikice. Wani irin sanyi ya ratsa ta. Ta ja da baya..
“Rayuwa…?”
ta maimaita a firgice.
“Ka ce rayuwa?”
Ta kalle shi, idanuwa na cikowa da hawaye, amma wannan karon hawaye na tsoro ne, ba fushi kaɗai ba...
“Ni mace ce,”
ta faɗa a raunane,
“ban san rayuwar ka ba… ban san ƙarfin jikinka ba… ban san yadda zan rayu a siffarka ba…”
Ta yi shiru na ɗan lokaci, ta haɗiye kukan...
“Idan na ji ciwo… kai ma za ka ji?”
ta tambaya cikin rawar murya...
King Diamond ya ɗan kalleta kai tsaye. Ya ɗaga tafin hannunsa, inda aka yanke, a yanzu jinin ya tsaya amma alamar ciwo na nan..
“Eh,”
ya amsa.
“Tun daga wancan haɗuwar jini… abin da kika ji, zan ji. Abin da na ji, za ki ji.”
Ayat ta runtse idanu. Zuciyarta ta buga da ƙarfi fiye da da....
“Ka ɗaure ni,”
ta faɗa cikin kuka....
“Ka ɗaure rayuwata da taka.”
King Diamond ya ɗan matsa kusa. Iskar asuba tana ɗaga sumar gashinsu..
“Ba ni na fara ba....Ke ce.”..
Ayat ta buɗe idanu, ta kalle shi da haɗaɗɗen kallo, ta jinjina kai sannan ta ce..
“zan yarda…amma ba don ina so ba, sai don in tsira..”
Ya ɗan yi murmushi ya ce,
“Na sani.”
Ayat na tsaye a gabansa, idanuwanta sun kumbura da hawaye da ta daɗe tana ɓoye wa...
“Shin kana son ɗauke min zuciyata ne?.”
Ya ce,
“Ba zan taɓa tilasta ki ba.
Ko a mulkina, babu ikon da ya fi na zuciya.”..
Ayat ta yi murmushi mai raɗaɗi, murmushi da hawaye ke yawo a cikinsa..
“Ƙarya ne...Ka riga ka shiga zuciyata… ba tare da izini ba.”..
Ta sauke kai, hawaye suna zubo wa...
“Amma yau…”
ta ɗaga kai tana kallonsa kai tsaye,
“zan buɗe iyakata da kaina.”..
A hankali ya ƙira sunanta..
“Ayat...”
“Ka saurare ni,”
ta katse shi, murya na rawa.
“Zan amince… amma ba haka kawai ba.”..
Ta share hawaye da bayan hannunta, ta ɗaga yatsa ɗaya...
“Na farko.. ba za ka taɓa amfani da iko ko sihiri a kaina ba.”
Ta ɗaga yatsa na biyu...
“Na biyu...Duk abin da zai faru tsakaninmu, sai da yardata.”
Ta ɗaga yatsa na uku, muryarta na rawa.
“Na uku… idan na ce daina,
za ka daina, ko da zaka mutu...”
Shiru ya ratsa tsakaninsu.
King Diamond ya miƙa hannunsa tare da dunƙule wa...
“Idan hakan ne farashin samunki,”
ya ce cikin murya mai nauyi,
“zan biya.”..
Ayat tana hawaye
Ta buɗe hannayenta a hankali. Jikinta na rawa...
“Zo,”
ta faɗa cikin kuka...
“Amma kada ka ɗauka nasara ce.”
King Diamond ya kusanto sannu a hankali, kamar yana kusantar abu mai tsarki. Ya tsaya gaban ta, ya buɗe hannayensa shima, a hankali ta shige faɗaɗɗen ƙirjinsa dake siffar ta...
Bugun zuciyarsu ne yake daidaituwa...
Ayat ta ɗora kanta a ƙirjinsa, tana kuka...
Hannunsa ya tsaya a bayanta, ba tare da ya matse ta ba...
“Ka sani,”
ta faɗa cikin kuka,
“idan ka karya sharaɗina,
zan tsane ka fiye da yadda nake tsoron ka.”..
King Diamond ya sunkuyar da kansa a kanta tare da sumbatar gashin dake kanta..
“Idan na karya sharaɗinki,”
ya amsa,
“to na rasa kaina.”..
A wannan lokacin, aljanu dake nesa suka durƙusa ba tare da umarni ba.
Saboda sarkin su ya karɓi yarjejeniyar zuciya...
Ayat ta buɗe iyakarta, ta ba wa King Diamond damar da ya daɗe yana nema. Duk da tsoro da fargaba dake zukatan su, sai ga shi sun tsinci kansu a cikin wani yanayi da ya zarce tunanin ɗan Adam...
Sannu a hankali, King Diamond ya rage tazara tsakaninsu. Da ya matse ta sosai, A hankali ya kai leɓensa kan nata ko ince, asalin leɓen Ayat dake jikinsa ya haɗu da nasa dake jikinta...
Wani irin zurfaffiyar sumbata ce ta shiga tsakaninsu, sumbatar da ta raba su da duniyar gaskiya...
Sumbata ce da ta ratsa kowane sassa na jikinsu, tun daga tafin ƙafa har zuwa cikin ƙwaƙwalwa...
Sun ji wani irin yanayi da ba su taɓa sanin akwai shi ba a doron ƙasa...
Ga Ayat, ta ji kamar dukkan fushi da ƙuncin dake zuciyarta suna narkewa suna zama ruwan sanyi. Shi kuwa King Diamond, ya ji kamar dukkan ikon da yake da shi ya tattara a wannan gaɓar ta leɓensa...
Wannan sumbatar ta ƙara haɗa ƙaddararsu fiye da haɗuwar jinin da suka yi ɗazu. Ta zama tamkar igiyar da ba za ta taɓa tsinkewa ba, wadda ta ɗaure rayuwarsu guri ɗaya...
Sun ɗauki tsawon lokaci a haka, kowa ya rasa sanin inda yake, kowa ya mance da siffar da yake ciki...
Rungumar da suka yi wa juna ta ƙara tsananta, hannunsa ya zagaye kunkuminta cikin kwarewa da nuna mallaka, yayin da ita kuma ta sa hannuwanta ta riƙe wuyansa, tana ƙoƙarin jawo shi kusa da ita fiye da yadda jiki zai iya haɗuwa...
A daidai lokacin da sumbatar ta kai ƙololuwa, wani irin ƙarfi ya tura su baya, domin a duniyar aljanu wannan kuskure ne kusantar bil adam har haka, sun ga Sarkinsu yana shirin karya ƙa'ida hakan yasa aka raba su da ƙarfi...
✨
Wani irin hayaki mai ƙamshi ya mamaye wurin. Bayan hayakin ya lafa, sai ga shi kowa ya tsinci kansa a asalin jikinsa...
Ayat tana tsaye, numfashinta yana fita da sauri-sauri. Ta duba hannunta ta ga ƙananun yatsunta na mace. Ta taɓa fuskarta, ta ji laushin fatarta. Ta ji nauyin dogon gashinta ya dawo kanta. Ta dawo asalin Gimbiya Ayat!
Shi ma King Diamond, ya dawo cikin siffarsa ta aljani mai farin gashi da kwarjini...
Amma wannan karon idanunsa suna kallon Ayat ne cikin wani irin natsuwa da muryar da ba za ta taɓa mancewa ba...
Dukansu biyun sun tsaya suna kallon juna cikin mamakin abin da ya faru. Har yanzu suna jin zafi da zaƙin sumbatar nan a leɓunansu. Ayat ta so ta yi fushi, amma sai ta ji muryarta ta gaza fitowa...
Zuciyarta tana gaya mata abu ɗaya..
"Yanzu kam, ba za ki taɓa rabuwa da shi ba."..
King Diamond ya tsaya yana kallonta, iskar asuba tana wasa da farin gashinsa dake sheƙi. Duk da cewa kowa ya dawo asalin siffarsa, idanunsa ba su daina kallon leɓun Ayat ba, kamar har yanzu yana jin ɗanɗanon sumbatar da ta canza musu ƙaddara...
Ya matso mataki ɗaya kusa da ita, muryarsa ta fito cikin wani irin amo mai sanyi wanda yake ratsa bargon jikinta..
"Kinyi nasara Ayat. Kin dawo cikin gidan sarautarki, kin dawo cikin siffar da kike alfahari da ita."..
Ya ɗan dakata sannan ya ɗaga hannunsa ya nuna saitin zuciyarta...
"Amma ki sani, sumbatar da muka yi ba wai kawai ta maido mana da siffarmu ba ne, ta zama tamkar Sa hannu a takardar rayuwarki. Daga yau, ba za ki iya ɓoye min komai ba. Idan kina cikin farin ciki, zan ji a jikina. Idan kina zubar da hawaye, zuciyata za ta buga..."
Ayat ta tsaya tana kallonsa, jikinta har yanzu yana ɗan goosebumps saboda kwarjininsa...
Ya cigaba da cewa..
"Ki koma fada, ki ci gaba da wasan ɓoyon da kike yi da mutanenki. Amma karki manta sharaɗinmu, Ni naki ne, ke tawa ce. Duk ranar da kika ji kishirwar gani na, kawai ki kira sunana a cikin zuciyarki, zan bayyana a gare ki ko da kuwa dakarun duniya dubu ne suka kewaye ki."..
Kafin Ayat ta samu damar cewa uffan, King Diamond ya yi wani ɗan gajeren murmushi sannan jikinsa ya fara rikiɗewa ya zama tamkar hasken taurari..
Cikin kiftawar ido, ya ɓace a gaban idonta sai ƙamshinsa kawai ya rage yana tashi a sararin samaniyar kogin...
Ayat ta sauƙe wani nauyayyen ajiyar zuciya, ta dafe ƙirjinta tana jin yadda zuciyarta take bugawa da ƙarfi. Ta duba tafin hannunta, ta ga tabon ciwon nan ya ɓace radau, amma ta sani a ranta cewa alamar dake zuciyarta ba za ta taɓa goge wa ba...
"Ya Allah..." ta raɗa a hankali...
Tana tsaye sai kuma ta ga siffar gimbiyancin ta ya sauya ya koma siffar Inuwa, yanda take kafin wannan lokacin..
Ta shafa fuskarta ta ji akwai gemun da sajen, bata san lokacin da ta sau murmushi ba..
Ta juya da sauri ta nufi inda dokinta yake ɗaure, ta hau shi tare da zaburar da shi da gudu domin ta isa Masarauta kafin idon mutane ya fara lura da bacewarta.....
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 1️⃣3️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Gari ya waye garau, hasken rana ya fito. Master Ibrahim yana tsaye a bakin kofar daƙin dawakai, fuskarsa a murtuƙe, idanunsa sun yi jawur saboda rashin baccin daren da ya yi yana neman Inuwa. Zuciyarsa tana tafasa yadda yake jin Inuwa a ransa ya wuce kima har ma yana mamakin yadda damuwar namiji ɗan uwansa take neman mayar da shi tamkar wanda ya rasa budurwa...
Yana nan tsaye, sai ya hango dokin Inuwa yana tunkaro fadar. Inuwa ya ƙaraso yana sauka daga kan dokin, ya sauke numfashi yayin da ta ci karo da firgittaccen kallon Master Ibrahim..
Ibrahim ya tako cikin sauri, ya tsaya a gabanta, muryarsa tana rawa tsakanin fushi da sauƙaƙawa..
"Inuwa! Daga ina kake? Tun jiya nake nemanka a kowane lungu na fadar nan! Na je har bakin kogi amma ban gan ka ba. Me ya faru da kai?"..
Ayat ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin saita muryarta ta Inuwa domin ta kare kanta. Ta san dole ne ta bayar da ƙwaƙƙwarar ƙarya..
"Gafara nake nema Master," ta faɗa cikin murya mai nuna gajiya. "A daren jiya lokacin da nake kan hanyata ta dawowa, na ci karo da wata mata wadda ta samu hatsari mai tsanani a kan titi. Jini yake zuba daga jikinta babu kowa a kusa. Dole ta sa na ɗauke ta zuwa asibitin gari dake wajen fada, na zauna a can ina jiran likitoci har na tabbatar ta farfaɗo. Shi ya sa na kwana a asibitin har gari ya waye."..
Jin kalmar Na kwana a wurinta, sai Master Ibrahim ya ji wani abu ya soke shi a ƙirji. Wani irin azababben kishi ne ya turnuƙe shi, kodayake a zahiri yana kallon Inuwa ne a matsayin namiji, amma jin cewa ya sadaukar da daren sa ga wata mace ya sanya shi jin zafi..
Ibrahim ya haɗe rai, ya kawar da kansa gefe yana huci kafin ya sake duban Inuwa..
"Hatsari? Kuma sai ka kwana a wurinta? Inuwa, ashe kai jarumi ne har a fagen soyayya da taimakon mata?". Ibrahim ya faɗa cikin sautin izgilanci dake nuna ɓacin ransa..
Inuwa ta ɗan firgita da yadda muryarsa ta sauya..
"A'a Master, taimako ne kawai na yi..."
Ibrahim ya katse ta, ya matso kusa da ita sosai har tana jin ɗumin numfashinsa...
"Kayi ƙoƙari, hakan yana da kyau. Amma daga yau, ko da tsuntsu ne ya samu hatsari, dole ka sanar da ni inda za ka je! Masarautar nan cike take da maƙiya, kuma ba zan iya jure rashin ganinka na tsawon sa'o'i biyar ba, balle har gari ya waye."
Ya sake jaddada maganar cikin nuna iko
"Karka sake kwana a wajen masarauta ba tare da izinina ba. Yanzu maza ka je ka huta, ka wanke jikinka. Amma ka sani, wannan matar da ka taimaka, kada hakan ya zama silar shagala daga ayyukanka."..
Ibrahim ya juya ya fice daga wurin cikin takun fushi, ya bar Ayat a tsaye tana mamakin irin wannan damuwar da Master Ibrahim yake nuna mata. Ba ta sani ba cewa, a cikin zuciyar Master, rami ne aka haƙa wanda ba na abota ba ne kaɗai...
Tana isa ɗakinta, ta tarar da shi tsit, sai ƙamshin turare dake tashi...
Ta garzaya zuwa gaban madubin da aka mayar mata da sabo, ta cire sajen da gemun fuskarta, sannan ta cire rawanin dake kanta...
Gashinta ya zubo ya rufe mata baya.
Ta tsaya tana kallon kanta. Duk da cewa Master Ibrahim ya nuna mata damuwa da kishi, amma ba ta ko tuna maganarsa ba. Abin da yake dawo mata a kunne shi ne muryar King Diamond dake cewa.
"Ni naki ne, ke tawa ce."
Ta ɗaga hannunta ta kalli tafin hannunta inda sumbatar nan ta warkar da shi. Babu ko alamar ciwo, amma tana jin wani irin ɗumi dake yawo a jikinta, ɗumin da ya samo asali daga wannan sumbatar da ta canza mata rayuwa...
"Mugu..." ta raɗa a hankali, tana shafar leɓunanta..
"Ta yaya ya shiga rayuwata haka? Ta yaya kaddararmu ta sarƙe a cikin dare ɗaya?"
Wani irin tsoro mai haɗe da shauƙi ya ziyarce ta. Ta tuna yadda ya amshi sharaɗan ta. Ko da yake ta tsane shi a farko, amma yanzu tana jin wani irin haɗi dake tsakaninsu wanda ko da tana so, ba za ta iya tsinkewa ba...
Ta matsa kusa da madubin tana kallon kwayar idonta. Tana neman ko za ta ga inuwar King Diamond a ciki, kamar yadda ya ce yana tare da ita..
"Karka ɗauka kayi nasara...."
Ta maimaita maganar da ta gaya masa, amma a ranta tana jin cewa ita kanta ba ta san waye ya yi nasara a tsakaninsu ba...
Tana cikin wannan tunanin sai ta ji an buga ƙofar ɗakin..
"Gimbiya! Gimbiya Ayat kina ciki?!" Muryar Saratu ce ta katse mata tunani.
Ayat ta firgita, ta goge fuskarta da sauri. Dole ne ta saita kanta, ta dawo Gimbiya Ayat mai natsuwa, ko da kuwa zuciyarta tana can bakin kogi tare da sarkin aljanu...
✨✨✨
A yau ba tare da kowa ya sani ba..
Da misalin ƙarfe huɗun asuba, lokacin da kowa yake nannaɗe cikin bargo, Sarki Nourdeen ya fito sanye da manyan kayan sarauta fuskarsa cike da damuwa..
Baya son gimbiyoyinsa su sani, don haka ya ba da umarnin a shirya babbar Helicopter ɗinsa ta alfarma a filin jirgi na sirri dake bayan fada...
Koda Master Ibrahim bai san da wannan tafiyar ba har sai da aka buga musu ƙofa. Sarki ya zaɓi dakarun tsaro guda biyar kacal, waɗanda ya amince da su, ciki har da jami’an tsaro na musamman da za su raka shi...
"Ba ma neman yaƙi," sarki ya faɗa wa shugaban masu tsaron nasa. "Zamu je ne don mu cika alƙawarin da aka daɗe da yi. Amma ku kasance a shirye da kowane irin yanayi."..
Ƙarar injin Helicopter ta mamaye sararin samaniyar fadar.
Sarki Nourdeen ya shiga ciki, ya zauna a mazauninsa na alfarma ya zuba wa masarautar Alhamra ido ta taga yayin da jirgin yake shawagi sama...
A ransa yana addu'ar wannan tafiyar ta zama silar zaman lafiya, ba silar rugujewar mulkinsa ba..
Tafiyar ba ta da tsawo sosai ta sama, amma ga sarki, kowane minti ɗaya tamkar shekara yake...
Suna isa ƙasar da suka nufa, daga sama ya fara hango wani babban birni dake kewaye da baƙaƙen ganuwa da hasken fitilu masu launin purple...
Wannan ita ce daular Pavilion...
Ganin tsarin gine-ginen wurin kaɗai ya isa ya nuna maka cewa wannan ƙasa ce dake da ƙarfin da ya zarce na kowace masarauta...
Yayin da Helicopter ɗin take neman gurbin sauƙa a katafaren filin jirgin Pavilion, sarki ya hango dakarun Pavilion sanye da baƙaƙen kaya sun jera layi tamkar bango. Babu wani rurrusunawa, babu wata gaisuwa ta girma sai kallo mai cike da kwarjini...
Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya gyara kambunsa...
"Lokaci ya yi," ya raɗa wa kansa yayin da matattalar jirgin ta sauƙa..
Sarki Nourdeen ya fito daga helicopter ɗin, kansa a ɗage amma zuciyarsa tana bugawa. Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un! Abin da ya gani ya wuce misali...
Girman gine-ginen Pavilion kawai ya isa ya sanyaya wa mutum jiki. Ko’ina ka kalla dakarun Pavilion ne sanye da baƙaƙen kaya, tsaye daram ba sa motsi tamkar gumaka, idanunsu ƙafe a kan kowane taku na baƙin..
Sauran jami’an tsaron sarki da suka biyo shi, suka tsaya a tsakiyar katafaren harabar fadar, fuskokinsu cike da tsoro da mamaki. Sun ji kansu ƙanana a cikin wannan makeken fili wanda aka ƙawata da dutsen marmara mai sheƙi.
Wani babban jami'in Pavilion wanda kwarjininsa ya kusan zarce na sarki kansa, ya tako a hankali ya yi wa sarki nuni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 39