Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Gely wanda yake ta yanyanke wa ta ce, "Warning... Battery at 15%... Chief Onyx access denied... Please... charge... me..." ​Ching-Ching tana turo baki ta ce, "Charge kanki mana! Ni ma kaina caji yake bukata... Idan na isa gida, wallahi ko ƙofa Uncle ya rufe min, sai na bi ta ramin ɓera na shiga, in je in nemi gafararsa. Ba zan iya barin Uncle na ba, koda zai mayar da ni ɓera a gidan..." ​ ​Bayan sa'o'i biyu na tafiya cikin gajiya da yunwa da ƙishi, suka isa kofar katon fadar Chief... Ching-Ching ta faɗi a ƙasa kusa da Guards... Gashinta ya hargitse, fuskarta yayi duhu tsabar wahala.. ​Masu gadin suka kalle ta cikin mamaki, amma saboda umarnin Chief, ba su buɗe ƙofa ba... ​Ching-Ching tana buga ƙofar fada da sauran karfinta tare da faɗin "Uncle! Ka buɗe min... Na daina juna-biyun! Na zama tsohuwa yanzu. Uncle wallahi ko ƙafa ta ba zan sake haɗewa da ta kowa ba, koda kuwa Yarima Leonardo ne.. Ka gafarta wa Gely, laifina ne.." ​B bodyguards kuwa sun yi ƙyammm ko kallonsu basu yi ba, domin an sanar da su akan kada su buɗe musu ƙofar.. ​A cikin falonsa kuwa, Chief Onyx yana tsaye a bakin taga, yana kallon yadda Ching-Ching take kuka a waje ta cikin kyamarorin tsaro CCTV... Fuskarsa ba ta nuna alamar tausayi ba, amma ya ƙura mata ido yana so ya ga ko da gaske take yi na son gyara halinta.... GELY yanzu ta daina tafiya ma, sai jujjuyawa take yi a wuri ɗaya. Idanunta dake hasken ja sun fara lumshewa, suna yin blinking... Muryarta ta koma ƙasa-ƙasa, kamar tsohon rediyo mai neman baturi... Muryar tana katsewa... "Ching... Ching... Sys-tem... fail-ure. Battery... at... 5 percent. Help... me... to... the... charging... port... please..." Ching-Ching ta ɗago kai tana kallon GELY cikin haushi.. "Ke dalla rufe min baki! Taimakon me zan baki? Kalli yadda na zama, gashina ya koma kalar dambun shinkafa saboda ƙura, ƙafata tana ciwo kamar an cire min ƙashi, ke kuma kina maganar caji?" Ching-Ching ta tashi zaune tana share hawaye da bayan hannunta, tana sake daka wa GELY tsawa... "Meye amfaninki ma yanzu? Da kike da caji ai kin biye min mun yi ta binciken locket, yanzu da Uncle ya yi fushi kin koma kukan caji! Da na sani ma da ban zo da ke ba. Yanzu idan na suma a nan, wa zai ɗauke ni ya kai ni ciki? Tunda ke ko hannunki baki iya ɗagawa!" GELY ta ce, "Ching... Ching... I... followed... your... logic... error. If... I... shut... down... Chief... will... recycle... me... into... a... frying... pan..." (Idan na mutu, Chief zai mayar da ni kaskon suya)... Ching-Ching ta ce, "Aii gara ma ya mayar da ke kaskon suyan, kika sani ko idan kin zama kasko ya riƙa soya naman kaza a jikinki ya ba ni in ci! Gashi nan ma kowa ya ƙi buɗe mana ƙofa. Dubi guards ɗin nan, duk sun zama kurame, sun ƙi buɗe min ƙofa gashi cikina yana ƙugi kamar an kunna injin niƙa..." GELY ta ƙara yin ƙasa, kafafunta suka fara rawa, can sai aka ji Peeeeeep Wannan alamar battery ya koma 2% kenan.. "I... see... darkness... Goodbye... Ching... Ching..." Ta daskare a tsaye, hannunta ɗaya a sama, ɗaya a kasa, tana kallon sama kamar wadda take neman taimakon hadari.. Ching-Ching ta tsorata, ta rarrafa kusa da GELY "Ke Gely! Karki mutu! Don Allah karki mutu ki bar ni a nan ni kaɗai! Idan kika mutu wa zan riƙa sa yana min Laser ɗin abu mai ƙarfi? Gely! Tashi mu yi damben karshe!" Ta fara girgiza GELY, amma GELY ta zama dutse... Ching-Ching ta kara fashewa da kuka, ta rungume kafar GELY wadda take da sanyi da tauri... "WAYYOOO UNCLE! Kazo ka ga robot ɗinka ta mutu! Nima gani nan zan bi bayanta idan baka buɗe kofar nan ba! Wallahi zan daina cewa ina da ciki, zan daina taɓa hannun kowa, zan koma cin ganyaye kamar akuya amma don Allah ka buɗe mana!" Ba zato ba tsammani, sai aka ji ƙofar gate ɗin ta buɗe a hankali. Chief Onyx ne ya fito, sanye da ƙananun kaya na shan iska, fuskarsa tana sanye da bakin gilashi duk da yamma ta yi. Ya tsaya yana kallon wannan hoton na ban-tausayi.. Yarinya duk ƙura tana rungume da gawar robot... Chief cikin sanyin murya ta furta "Wai har yanzu ba ku daina wannan wasan kwaikwayon ba?" Ya matso kusa da su, yana kallon yadda Ching-Ching ta ƙanƙame ƙafar GELY tana kuka. Ya miƙa hannu don ya ɗaga ta ya kai ta ciki, amma sai ta goce, ta koma ta manne wa GELY dake daskarewa... Ya ce, "Ching-Ching, tashi mu shiga ciki. Kin riga kin galabaita, kina buƙatar abinci da barci." Ching-Ching tana shashshekar kuka ta ce, "A'a Uncle! Ba zan shiga ba! Ka duba GELY, ta riga ta zama dutse. Tana tsoron kar ka mayar da ita kaskon suya shiyasa ma ta daina numfashi.... Idan ba za a shigar da ita a ba ta caji ba, to nima a nan zan daskare in zama kaskon tuwo.." Chief ya yi wani dogon nishi, ya kalli GELY dake tsaye hannu ɗaya a sama kamar tana rawar Michael Jackson. Ya san cewa idan bai biye wa Ching-Ching ba, to a nan za su kwana... Ya furta "GELY ta gaza yin biyayya Ching-Ching.... Dole ne ta fuskanci hukunci." Ching-Ching ta zabura ta miƙe, ta fara dukan ƙirjin Chief da ƙananan hannayenta.. "Mugun Uncle! Azalumi! Saboda mu ne ba mu da jini a jikinmu? GELY ta biyewa logic error ɗina ne saboda tana so na. Idan baka caji ta ba, nima zan sa Laser in fasa kaina in ga me ke ciki! Wallahi yanzun nan zan daina numfashi ni ma..." Ta riƙe numfashinta, ta kumbura kumatunta har sai da fuskarta ta yi jawur tana hararar Chief... Ganin Ching-Ching tana shirin suma da gaske don taurin kai, Chief ya ɗaga hannu ya yi wa masu gadin sa guda huɗu alama.. Cikin muryar gajiya ya ce, "Ku ɗauki wannan ragowar ƙarfen ku kai ta babban ɗakin bincike, a haɗa ta da High-Voltage Charger.. Sannan a sake mata formatting na ɓacin ran da aka sa ta." Nan take Chingching ta saki numfashin, ta washe haƙora.. "Yauwa Uncle! Amma karka bar su su goge mata tunanin da muke da shi na naman kaza, kaga nima ina buƙatar ta riƙa tuna min lokacin da nake da juna-biyu kafin ka ce na zama tsohuwa." Chief Onyx bai sake cewa uffan ba, ya sunkuyo ya fizge ta ya ɗora ta a kafaɗarsa kamar buhun gishiri.. "Ayya Uncle! Karka matsa min ciki, kasan har yanzu akwai ghost ɗin jaririn a ciki..." Ya ce, "Ching-Ching, muddin kika sake yin maganar ciki, zan sa a haɗa ki caji tare da GELY!" Nan take ta yi shiru, ta laɓe a kafaɗarsa tana kallon yadda ake jan GELY zuwa ciki. A ranta tana cewa, "Gely, maza ki tashi, akwai sauran dambarwa a gaba!" ✨✨✨ ​Bayan kwanaki uku na fargaba da ɗar-ɗar, gari ya waye da wani mummunan labari wanda ya girgiza harsashin fadar Alhamra.. An tsinci wasu gawarwaki guda goma 10 shimfiɗe a harabar fadar, waɗanda duk jami'an tsaron fadar ne. Ba a san ta yaya aka sace su ba, kuma ba a san ta ina aka shigo da gawarwakin nasu ba.. ​An same su cikin jini, sanye da kakin su, amma rayuka sun yi halinta. A gefen gawarwakin, an tsinci wata wasiƙa mai ɗauke da tambarin fadar Sydney.... _​"Mulki ba na rarrashi ba ne. Idan kuna da ƙwarin gwiwar zuwa karɓo mutanenku da muka tsare a can Yankin Hamshara. (Wani yanki mai nisan gaske), to ku shirya zuwa da shirin yaƙi. Amma ku sani, kowace gaɓa ɗaya takun da kuka yi, tana iya zama silar mutuwar mutum ɗaya a hannunmu. Gawarwakin nan goma, somin-taɓi ne kawai."_ ​Ganin wannan barazanar, Sarki ya ba da umarnin rufe dukkan asibitoci, makarantu, da kasuwanni. Alhamra ta zama kamar garin kurwa, kowa ya laɓe a gida, tsoron dakarun Turawan ya mamaye kowa... ​Sarki Nourdeen ya fito cikin fushi da ɓacin rai, idanunsa sun yi ja. Ya tara dukkan jami'an tsaron sa, ciki har da Inuwa wanda yake tsaye cikin kakin sa, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa... ​Sarki ya sanar da cewa "Ba zan zuba ido ana kashe min mutane ba! Ruma ta wuce gona da iri. Ina neman mazajen da za su sadaukar da rayuwarsu su tafi Yankin Hamshara domin ceto mutanenmu. Wannan yaƙi ne, kuma jini zai zubar!" ​Sarki ya ba wa Master Ibrahim umarnin ware zaratan jami'ai guda hamsin da za su jagoranci wannan hari na ba-zata... ​Bayan an gama taron, Master Ibrahim ya fara kiran sunaye, amma ya ƙi ƙiran sunan Inuwa.... Inuwa ya bi Master har zuwa can gefe, muryarsa a dashe yana roƙonsa.. ​"Master, me ya sa sunana ba ya ciki? Ka sani cewa nima na san dabarun yaƙi, kuma zan iya shiga inda kowa ba zai iya shiga ba!" ​Master Ibrahim ya juyo cikin tsawa muryarsa na rawa ya ce, "Ba zan saka ka ba! Wannan ba wasan yara ba ne, yaƙi ne na haƙiƙa. Ina tsoron kada a je a raunana ka, ko kuma ka rasa ranka. Idan wani abu ya same ka, ta ya zaka cika burikan ka...?" ​Inuwa ya duƙufa yana roƙon Master "Don Allah Master, kada ka bar ni a baya. Idan ban je ba, ba zan taɓa yafe wa kaina ba. Ina da kariya, kuma zan iya taimaka muku. Idan har ka yarda da ƙwazona, to ka saka ni a cikin rundunar nan." ​Ganin yadda Inuwa ya nuna taurin kai da kuma zubar da hawayen jarumtaka, Master Ibrahim ya sauke numfashi, ya ɗauki alkalami ya rubuta sunan Inuwa a ƙarshen jerin sunayen, amma jikinsa yana rawa... Bayan an gama danbarwar ne Inuwa ya koma sashensa.. Ta shiga ɗakinta ta boyayyar hanyar sirri, tana sanye da kayan jami'an tsaron jikinta... Tana shiga ta hango wani haske mai launin shuɗi yana walwali a kan gadonta... King Diamond ne zaune, dogon sumar gashinsa na kwance a kafadarsa, idanunsa na kallon ta cikin natsuwa.. ​Cikin ajiyar zuciya ta furta.. "Daman ina son ganinka... Akwai babban aiki a gaba na." ​Ta ƙarasa kusa da shi, fuskarta ɗauke da damuwar da ta daɗe tana addabarta... ​ "Idan na tafi wannan yaƙi a matsayin Inuwa, wa zai zauna a nan a matsayin Gimbiya Ayat? Idan aka nemi gimbiya ba a ganta ba, asirina zai tonu, kuma sarki zai shiga ruɗani. Ta yaya zan kasance a wurare biyu lokaci guda?" ​King Diamond ya miƙe tsaye, tsayinsa da kwarjininsa suka cika ɗakin. Ya matso kusa da ita, muryarsa kamar busar iska.. ​"Na san yadda zan yi, kada ki damu da wannan. Zan samar da wata Ayat da za ta zauna a maimakonki, babu wanda zai gano bambancin. Kuma yanzu ba tare da ɓata kwanaki ba zaku ta fi, kuma kina bukatar horo na musamman domin dakarun turawa ba mutane ba ne kawai..." ​Kafin Ayat ta samu damar tambayarsa wani abu, King Diamond ya sa hannu ya yi mata ɗaukan luɗa. Nan take wani irin jiri ya kwashe ta, ɗakin ya juya, komai ya ɓace cikin kiftawar ido. ​🌸 ​A lokacin da Ayat ta buɗe idanunta, ta tsinci kanta a wata duniyar daban. Wuri ne mai cike da furanni masu sheƙi da fitar da haske kalar taurari, iskar wajen tana ƙamshin da ba a taɓa ji a duniyar mutane ba... ​Wata lallausar waka, mai sanyaya rai da kwantar da hankali ta fara tashi daga ko'ina. Ba a ganin masu kiɗan, amma sautin yana ratsa ƙashi... ​King Diamond ba tare da ya sake ta ba. Ya sanya hannunsa ɗaya akan kunkuminta, ɗaya kuma ya riƙe hannunta... Ayat kuma, kamar yadda rawar turawa take, ta ɗora ɗaya hannun nata a kafadarsa itama.. ​Suka fara taku ɗaya-bayan-ɗaya, suna juyawa cikin natsuwa a tsakiyar lambun furannin... Suna bin sauti da gangar wakar... Idanunsu suka sarke cikin na juna. Ya sauya mata kayan jikinta daga na jami'i zuwa na gimbiya haɗaɗɗiya, tsabar shauƙi na lokaci guda har ta mance da batun yaƙi... A wannan lokacin, Ayat ta ji wani irin kariya dake tattare da King Diamond. Kwarjininsa ya mamaye daukacin hankalinta.. Yana mata raɗa yayin da suke rawar.. "Wannan rawar ba ta nishaɗi bace kaɗai Ayat... Tana koyar da ke yadda zaki riƙa sarrafa jikinki cikin sauri da natsuwa a lokacin yaƙi. Dole ne ki kasance kamar iska, ana jinki amma ba a ganinki." Ta lumshe idanu, tana jin ɗumin jikinsa, tana fatan wannan daren kada ya ƙare. Ta gane cewa King Diamond ba aljanin kariya bane kawai, shi ne masoyin da zuciyarta ta daɗe tana nema...duk da akwai wanda take kewa kafin shi... Waƙar da suke rawa da ita a hankali ta fara sauya sauti, daga lallausan sauti zuwa wani kiɗa mai ɗauke da sautin ƙarfe da kwarin gwiwa... King Diamond ya sakar mata kunkumi, sannan ya ɗaga hannunsa sama. Nan take, wani haske mai launin shuɗi ya ɓarke a tafin hannunsa, ya rikiɗe ya zama wani tsararren takobi mai matukar kyau da kaifi... ​Ya miƙa mata ɗaya, sannan shi ma ya zaro tasa. ​Ya tsaya takara, idanunsa sun canza launi zuwa wani irin shuɗi mai zurfi wanda yake nuna cewa yanzu lokacin horo ne, ba na wasa ba... ​"Ayat," ya ƙira sunanta cikin muryar dake amsa a cikin lambun... "Takobi ba makami ba ne kawai, ɓangare ne na jikinki. Idan zuciyarki tana rawa, takobinki zai yi nauyi. Idan zuciyarki tana da tauri, takobinki zai zama kamar fure." ​Ya nuna mata yadda zata riƙe takobin... ​Ya daidaita yatsun hannunta akan marikin takobin, yana tabbatar da cewa ta riƙe shi da duk kwarin gwiwarta... Ya gyara mata ƙafafu yadda zata samu natsuwa a ƙasa... ​Ya fara kai mata farmaki na farko, ba da nufin raunata ta ba, sai dai don ya gwada saurin motsinta.. ​ Sautin ƙarfe ya tashi a lokacin da takobinsu ya haɗu... ​"Kada ki jira in kawo hari, ki riƙa hango inda zan sa ƙafa kafin in ɗaga ta," ya faɗa yayin da yake juyawa kamar iska... Ayat ta fara bin sa, tana lura da yadda jikinsa yake motsawa. Cikin kankanin lokaci, ta fara koyon yadda zata kaucewa hari ta hanyar juyi da kuma yadda zata kare kanta... ​Ya koya mata wani salo na musamman inda jiki zai kasance yana rawa irin ta motsa jiki, amma takobi yana saran kowane bangare... Ta riƙa yin tsalle tana kai hari daga sama.. Ya koya mata yadda zata riƙe numfashinta yadda ba zata yi saurin gajiya ba... ​Ayat ta ji wani irin ƙarfi yana gudu a cikin jininta. Duk wani tsoro na dakarun turawa ya ɓace, ya koma wani irin zafi da kishin ganin ta ceci mutanen Alhamra. Gumi ya fara keto mata, fuskarta ta yi jawur, idanunta suna kyallin jarumtaka... ​King ya tsaya, yana kallon kyakkyawar jarumar dake gabansa ya ce, "Madalla. Yanzu kin shirya. Zuciyarki ta zama ɗaya da takobinki. Yanzu babu wani soja na Turawan da zai iya tsayawa a gabanki ya yi nasara." ​Ya matso kusa da ita, ya sanya hannunsa a kanta... "Inuwar da zan bari a fada tana da ikon yin magana da aikata komai kamar ke, don haka ki saki ranki ki yi yaƙin nan don mutanenki." ✨✨✨ Iya makarantar ne kawai ya rage ba'a rufe ba saboda Examination amma an bada tsaro na musamman sosai... Shiru ne ya ratsa babban Exam Hall na makarantar Royal International Academy. Sautin agogon dake jikin bangon ɗakin kawai kake ji yana bugawa.. tik-tok, tik-tok, tamkar yana ƙirga sauran lokacin da ya rage wa ɗaliban... ​Maayah tana zaune a tsaka-tsakiya, sanye da uniform makarantar... Duk da kyawun fuskarta, yanzu fuskar ta nuna tsantsar firgici... Ta ƙura wa takardar jarrabawar ido, tambayoyin suna yi mata gizo kamar yaren jinnu... ​Iya abin da ta rubuta shi ne sunanta, SHAHZADI MAAYAH MUHAMMAD NOURDEEN... ​Ta daɗe tana kallon takardar, tana son tuno da abin da aka koyar musu, amma kwakwalwarta ta ƙi bata haɗin kai. Sauran ɗaliban dake ɗakin, waɗanda a baya ita ce take nuna musu izza, kowannensu kansa yana ƙasa yana rubutu ba kakkautawa. Malaman dake zagayawa kuwa, duk da cewa tsoronta suke ji a baya, yanzu suna wucewa ne ba tare da sun kalleta ba, domin sun san mulkin Master of Discipline wato Uncle Jalal ya riga ya kawar da tsoron fada a makaranta... ​A can gefe guda, a cikin ofishinsa, Uncle Jalal yana zaune, idanunsa kyam akan jadawalin jarrabawarsa domin ko wani malami da darasinsa... Wata zuciyar kuma tana hasasho masa Maayah a hall duk da cewa akwai wani boyayyen tausayinta da yake ji a duk lokacin da yake mata darasi a gida, musamman yadda take zubar da hawaye idan ya tsawata mata amma a makaranta, shi ne katangar ƙarfe.. ​Lokaci guda, Uncle Jalal ya miƙe, ya nufi hall ɗin jarrabawar. Takun takalmansa ya sanya kowa a ɗakin ƙara nutsuwa. Ya shigo cikin takunsa na isa, ya fara zagaya teburan ɗaliban... ​Ya iso daidai teburin Maayah. Ya tsaya cak, inuwarsa ta rufe takardar jarrabawar tata. Maayah ta ji wani irin Shock, ta kasa ɗagowa ta kalle shi... ​Uncle Jalal ya sunkuyo daidai kunnenta, muryarsa can ƙasa cike da gargadi... "Gimbiya Maayah... saura minti goma sha biyar... Shin sunanki ne kadai kika koya a duk zaman da kike a aji?" ​Maayah ta ɗago idanunta da suka rine da kwalla, ta kalli Uncle Jalal cikin yanayin roko... "Uncle... kaina ciwo yake yi, na kasa tuno komai." ​Uncle Jalal bai nuna alamun tausayi ba, ya gyara tsaiwarsa yana kallon agogonsa... "Nan ba gida ba ne, kuma ni ba Uncle ɗinki ba ne a nan. Ni malamin jarrabawa ne. Idan baki rubuta komai ba, za'a raba miki takardar 'F' ɗinki a gaban kowa, sarki ya gani." ​Ya matsa daga gefenta, ya cigaba da zagawa yana cewa, "Sauran dalibai...saura minti goma! Duk wanda bai gama ba ya hanzarta." ​Maayah ta ji zuciyarta tana dukan uku-uku. Ta kalli bayan Uncle Jalal, tana jin wani irin shauƙi na ƙiyayya da kuma sha'awar yadda yake nuna mata rashin tsoro. Ta ɗauki alkalaminta, hannunta yana rawa, ta fara kokarin zana duk abin da ya zo mata a rai, ko da kuwa ba shi ne amsar ba, don gudun kada Uncle Jalal ya kunyata ta a gaban mutane... ​A ƙarshen hall ɗin, Uncle Jalal ya juyo ya kalle ta. Kwayar idonsu ta sarƙe. Shi ma ya ji wani irin tausayi ya ziyarci ransa, ganin yadda take ta faman kokawa da alkalami, amma dole ya danne domin ya mayar da ita mutuniyar kwarai... Bayan ya fita zuwa ɗakin jarrabawa na gaba, Ɗakin ya ɗan yi sanyi. Maayah ta ƙura wa takardarta ido, tana jin tamkar kanta zai rabe biyu... Sadiq wato saurayinta na wasa wanda take aikansa ya siyo mata abu, yana zaune a kujera ta kusa da ita, ya kammala nasa rubutun tsaf. Ya lura da yadda Maayah take zufa, duk da sanyin dake ɗakin.. ​Sadiq ya yi mata ɗan tari na ƙarya. Maayah ta ɗago idanunta da suka rine.. Ya yi mata nuni da idanu akan ta miƙo masa nata booklet ɗin, shi kuma ya miƙa mata nasa wanda ya riga ya kammala amsoshin. Cikin sanɗa da sauri, suka yi musayar takardun a karkashin tebur.. ​Wani malami dake zagayawa ya gansu, amma ganin Maayah ce, gimbiyar da kowa ke shakka, sai ya ɗauke kansa kamar bai gani ba, ya cigaba da takunsa.. ​Ta fara acting...Ta duƙufa tana kwaikwayon rubutu, amma hannunta yana rawa. Tana rubuta haruffa marasa ma'ana a gefen takardar Sadiq, tana yawan ɗagowa tana kallon ƙofa.. ​Kwatsam! Sai ga Uncle Jalal ya dawo ajin. Ya shigo da wani irin kwarjini, ya tsaya a gaban class ɗin yana bin kowa da kallo ɗaya bayan ɗaya. Idanunsa masu kaifi suka sauƙa akan wani ɗalibi dake can baya yana satar amsa a karkashin tebur... ​Uncle Jalal ya nufe shi gaba-gaɗi... "Give me that!" Ya daka masa tsawa da turanci. Ya fizge takardar, sannan ya karɓe booklet ɗin dalibin ya yaga shi gida biyu... "Get out of my class. Now!" ​Bayan ya gama zagayawa, ya nufi hanyar fita, amma wani abu ya tsaya masa a rai. Ya juyo ya kalli Maayah. Ya lura da yanayinta, bata danna biro kamar yadda mai rubutu yake yi, kuma yawan ɗagowan da take yi tana kallonsa ya ba shi shakku... ​Ya tako a hankali har ya iso gefenta. Ya tsaya kyam, ya zuba mata ido... "Anya kina da gaskiya kuwa, Gimbiya?" ya faɗa cikin muryar raɗan nan tasa mai tsoratarwa... ​Maayah ta daskare. Ta kasa magana, sai dai kawai ta zuba wa booklet ido... ​Uncle ya sa hannu ya janye littafin. Ya buɗe shafin ƙarshe, ya ga har tambaya ta karshe an amsa ta.. "Yanzu a fitar tawa har kika kai ga tambaya ta karshe?" ​Cikin zargi ya buɗe shafin ƙarshe na takardar. Nan take ya ga rubutun daban ne, rubutu ne mai ɗaukar hankali, ba irin na Maayah dake tangal-tangal ba. Ya sake juyo da shafin gaba don ganin sunan dake kai... ​ABUBAKAR YUNUS... ​Zuciyar Uncle ta buga. Ya kalli Sadiq, sannan ya kalli Maayah wadda ta riga ta fara hawaye. Sadiq kuwa ya gama kiɗimewa, numfashinsa yana fita da sauri-sauri... Uncle Jalal ya tsaya kyam a gefen Maayah, inuwarsa ta mamaye teburinta, wanda hakan ya sa numfashinta ya kusa tsayawa...Ya sanya dogayen yatsunsa ya janye booklet ɗin a hankali.. Maayah ta kalli Sadiq da gefen ido, shi ma Sadiq ya riga ya daskare, zufa tana keto masa ta ko'ina duk da sanyin AC dake ɗakin.. ​"Ina kika samu wannan dabarar, Maayah?" Uncle Jalal ya faɗa cikin murya mai sanyi mai cike da ɓacin rai... ​Maayah ta yi tsuru-tsuru, muryarta tana rawa.. "Uncle... rubutu na ne, kawai na yi sauri ne shi ya sa ya canza." ​Wani murmushin takaici ya subuce wa Uncle... "Sauri? Sauri har ya mayar da sunanki Abubakar Yunus?" Ya ɗaga littafin sama yadda kowa zai gani, sannan ya kalli Sadiq wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa yana rawar jiki... ​"Abubakar Yunus! Tashi tsaye!" Muryar Uncle Jalal ta daki bangon ɗakin kamar ƙarar tsawa... ​Sadiq ya miƙe tsaye jikinsa na kyarma... "Sir... dama... dama taimaka mata zan yi..." ​Uncle Jalal ya taka zuwa gaban Sadiq, ya raba shi da booklet ɗin dake gabansa, wanda kusan babu komai a ciki sai sunan Maayah... "Taimaka mata? Shin kai ne Sarki da zaka bayar da tallafin maki a ɗakin jarrabawa? Ko kuma ka ɗauka dokokina na wasan yara ne?" ​Ya juyo kan Maayah, wadda hawaye suka fara wanke mata fuska.. "Gimbiya Maayah, kin nuna min cewa duk kokarin da nake yi a gida asara ne. Kin gwammace ki yi sata da sunan wani namijin, maimakon ki faɗi da mutuncinki." ​Ɗakin ya yi shiru, sauran daliban suna kallon ikon Allah. Malami na farko da ya share su kuwa ya ɓuya a can gefe yana zaro ido... ​Uncle Jalal ya yage booklets guda biyun a gaban kowa, fatsa-fatsa!... ​"Kuje ku fita daga ɗakin nan! Maayah, Abubakar, kun faɗi wannan darasin... Kuma ina tabbatar muku, sai na sanar da Minister da kuma Mai Martaba Sarki abin da kuka aikata yanzun nan." ​Maayah ta fashe da kuka mai karfi. "Don Allah Uncle Jalal! Kada ka gaya wa Abul, zai iya min kowane hukunci!" ​Uncle ya nuna musu ƙofa da yatsa, idanunsa sun yi ja tsantsar ɓacin rai. "Fita! Tun kafin in rasa natsuwata a kanku!" Bayan sun fita.. Maayah bata wani tsaya ba domin daman Uncle Jalal ne mai zuwa ɗaukanta a gida idan an tashi kuma ya mayar da ita.. Ya dakatar da kawota a tsararrun motoci sama da biyar da bodyguards saboda a tunaninsa hakan zai sa tana yawan ji da kai.. A wannan lokacin haka take takawa tana tafiya a hankali, ba'a san ta fita ba ma... Kawai tafiya take tana hawaye, a tunaninta ta gama amfani yanzu.. Ba wai gida ta nufa ba, kai tsaye cikin daji tayi.. Tana tafiya hankalinta ya gama fita daga jikinta.. Bayan sa'o'i guda.. Kowa ya fito a exam, Sadiq ya samu Uncle a office Yana ta roƙonsa amma Uncle yace, "ai ya riga ya faɗi a wannan exam sai dai ya kiyaye zuwa next.." Sadiq yayi magiyar har ya haƙura.. Ya fita.. Can motoci ne suke zuwa ɗaukan ɗalibai dake duk makarantar na ƴaƴan masu kuɗi ne....kuma an ƙara kafa tsaro saboda yanayin garin bashi da kyau sai satar mutane ake.. Uncle ya fito daga office ya tambaya ina Maayah akan zai kaita gida shi kuma sai ya wuce... Amma an dudduba ko ina ba'a ganta ba.. Sai Sadiq ne da zai tafi motarsu tazo ɗaukansa yake sanar wa cewa Maayah fa ta

Chapter 38 of 39