Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
alfarma, tana wasa da wani kwarangwal ɗin zinare a hannunta... Ɗaya daga cikin bayinta ta shigo tana sanar da ita abin da Sarki ya yi wa Maayah... Zayana ta yi wata irin dariya mai sanyi, wacce take da amo kamar iska.. "Maayah yarinya ce. Tana tunanin izzah ita ce tafiya da bodyguards... Shi kuma sarki, yana tunanin fuskar Zakin nan tasa za ta tsoratar da kowa.".. Ta miƙe tsaye, tana taku cikin nutsuwa... "Maayah ta yi kuskure da ta nuna rauni ta durƙusa... Ni Zayana, babu ranar da zan durƙusa wa wannan fuskar ta Zakin. Idan ya yi kuskuren yi min tsawa, zan nuna masa cewa akwai abin da ya fi Zaki girma a daji...." Ba zato ba tsammani, sai ga Sarki Nourdeen ya ƙariso sashen Zayana... Ya shigo ne da nufin ya gargade ta kamar yadda ya yi wa Maayah, domin ya ji labarin ita ma tana wuce gona da iri... Sarki ya tsaya a ƙofar sashen nata, ya zuba mata wani irin kallo na kwarjini... Amma Zayana ba ta ko tashi daga inda take ba, ba ta kuma sunkuyar da kai ba. Ta ƙura masa idanuwa waɗanda suka fara canza launi daga baki zuwa wani kalar ja mai duhu... "Nourdeen," Zayana ta ƙira sunan mahaifinta kai tsaye ba tare da faɗin Sarki ko Abul ba.... "Kada ka kawo wannan gurnanin naka sashena. Ka riga ka sani, Ni na bambanta da sauran yaran gidann nan. Kada ka kuskura ka taɓa ikona." Wani irin iska mai sanyi ya fara kaɗawa a ɗakin, har fitulun ɗakin suka fara disashewa... Sarki Nourdeen, Zakin da kowa yake tsoro, ya ji jikinsa ya yi sanyi. Ya san cewa Zayana ba mutum ba ce kawai, tana ɗauke da wani abu da ya fi karfinsa... Sarki ya ja numfashi, ya kawar da kansa. Ba tare da tsawatarwa ba ya ce, "Zayana ki kiyaye. Iyakarki daban, tawa daban." Sannan ya juya ya fita da sauri kafin ikon Zayana ya fito fili... Zayana ta cigaba da zama, tana wasa da ƴar tsanar ƙwarangwal... "Izzah ba hauka ba ne, Maayah. Izzah ita ce ka sanya kowa ya tsoraci ko da kallonka ne, har da wanda ya haife ka.".. Ta furta tana sakin murmushin gefen baki... *SYDNEY* A can nesa, a cikin wani babban bene mai kallon teku, Ruma tana zaune a kan kujerarta ta mulki... Sanye take da tufa na alfarma, amma yatsunta suna sanye da wasu tsofaffin zobina. Babban cikinsu, wanda yake da wani baƙin dutse mai sheƙi, yana haskaka wani irin kore-kore... Ruma ta murza zoben, tana rufe idanunta. Tana iya jin bugun zuciyar Zayana daga Alhamra... Wannan zoben shi ne "remote control" na tausayin Zayana, muddin yana hannun Ruma, Zayana ba za ta taɓa sanin ma'anar jinƙai ba... "Nourdeen," Ruma ta yi murmushin mugunta... "Kana tunanin ka raba ni da ɗiyata? Ka riƙe gangar jikinta, amma ni ina riƙe da ruhinta da tausayinta. Duk sanda kake tunanin kai Zaki ne, ka sani cewa ɗiyarka tana da ikon murƙushe maka kwarangwal ɗin jikinka." ✨✨ A Masarautar Alhamra.. A daidai lokacin da Ruma ta murza zoben a Sydney, sai aka ga idanun Zayana sun ƙara yin ja wur a Alhamra. Wani irin kukan tsuntsu na daji ya tashi daga samfurin kwarangwal ɗin da ke hannunta... _______________Maayah, wadda ke cikin damuwar hukuncin da aka yi mata, ta kasa daurewa. Ta yanke shawarar zuwa sashen Zayana, ko da yake tana tsoronta, tana tunanin ko za ta samu hanyar fita daga halin da take ciki... Maayah ta isa ƙofar sashen Zayana, amma tun kafin ta shiga, wani sanyi ya ziyarci ƙashin bayanta.. Ta tura ƙofar a hankali, ta ga Zayana a tsaye, fuskarta babu ko ɗigo na ɗan'adamtaka... "Me ya kawo ki nan, Maayah?" Zayana ta tambaya, muryarta tana amo kamar tana magana ne daga cikin kabari. "Kin zo ne ki yi kuka domin sarki ya nuna miki cewa ke ɗaliba ce kawai?" Maayah ta haɗiye miyau, ta tsaya cikin izzarta ta ce, "Ba kuka na zo yi ba. Na zo ne mu haɗa kai. Abul yana neman ya raina mu gaba ɗaya. Idan ya fara da ni, ke ce ta gaba."... Zayana ta fashe da wata dariyar shakiyanci, ta taka har gaban Maayah... Ta matsa da fuskarta kusa da ta Maayah har suna jin numfashin juna... "Ba mu duka ba, Maayah... Ke aka raina. Ni, babu wanda ya isa ya gaya min yaushe zan fita ko yaushe zan zauna..... Ki fita daga sashena kafin na sa ki manta sunanki.".. Maayah ta ji tsoro ya fara ratsa ta, ta juya za ta fita, sai Zayana ta ƙira sunanta.. "Kuma ki gaya wa ma'aikaciyarki Liyatu, kada ta sake barin ƙafarta ta taka wannan sashen nawa. Domin bana buƙatar ko wani ƙazami, ke ma na raina tsabtar ki balle ita...." Ba ƙaramin ƙuluwa Maayah tayi ba, haka ta share ta koma sashenta cikin fushi, tana huci... Bayi da hadimai kowa ya rarrabe saboda yadda ta koro kowa da tsawa daga part ɗinta... Ta zauna a kan doguwar kujerarta ta alharir, tana kallon silin ɗakin nata... "Meye ya kaini?" Ta faɗa a fili cikin takaici... "Meye ya kaini wurin Zayana? Don tana da wani sirrin kwarjini da kowa ke tsoro? Ni Maayah ce! Ni ce wadda kowa a International Elite School ke tsoro. Idan Abul ya hukunta ni yau, ba yana nufin na zama raunanniya ba."... Ta cika da takaicin yadda ta nuna rauninta har ta tafi neman haɗin kai... A gun Maayah, neman taimako ma kaskanci ne. Ta yanke shawarar cewa daga yau, ko da za ta dawwama a sashenta, ba za ta taɓa nuna wa kowa ba, musamman Zayana, cewa tana cikin ƙunci ba... Ta ƙira Mama Liyatu... "Mama Liyatu! Ki shirya min abinci mafi tsada, kuma ki ɗauko min sabon littafin nan na Royal Dynasties... Ina son na nuna wa duniya cewa ko a kulle nake, ni ce sarauniya." Ita kuwa Zayana, tana nan zaune a daƙin da ko iska ba ta ratsawa sai da izininta. Ta san cewa Maayah ta tafi ne cike da takaici, kuma hakan daɗi yake mata... A tunaninta, Maayah ba ta kai matsayin da za su haɗa kai ba, ita Maayah tana izzah ne don tana da kyau da masoya, amma ita Zayana izzarta tana cikin jininta ne... ✨✨✨ Sarki Nourdeen yana zaune a babban falonsa, fuskarsa ta Zaki tana kallon hoton Ruma Mahaifiyar Zayana dake jikin bango. Ya daɗe yana kallon hoton, yana tunanin halayyar Zayana... "Izzar Ruma ce take yawo a jikin Zayana," ya faɗa a ransa... "Ba wani abu bane illa gado. Yadda Ruma take kallon kowa kamar kaskantacce, haka Zayana take. Ba zan taɓa mantawa da yadda Ruma ta tafi ta bar min wannan ragamar ba." Sarki bai kawo a ransa cewa akwai wani tsafin zobe a Sydney da ke juya Zayana ba... Ga shi, ganin cewa Zayana ba ta yi wa kowa tsawa ko yawo a fili kamar Maayah, sai ya fi jin kwarjininta.... A wurin Sarki, Zayana ita ce True Reflection ta mahaifiyarta, mace mai mulki da taurin kai... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣1️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* King Diamond yana zaune a tsakiyar gadon Ayat, yana shaƙar ƙamshin turaren oud dake tashi daga jikin filon baccinta.. Fuskarsa dake ɗauke da annuri da kwarjini tana haskaka cikin duhun ɗakin. Ya kalli kansa a madubin da Ayat ta gama amfani da shi, ya ga yadda sumarsa fara sol ta dace da lallausan zanen gadon.. ​"Reems..." ya furta a hankali, yana jin daɗin yadda sunan ya dawo masa da rayuwa ta sanadin Ayat. Duk da raunukan dake jikinsa, sumbar da ta yi masa a goshi ta zama tamkar maganin da ya fi kowane maganin tsafi ƙarfi.... ​A can ƙasa a babban falon cin abinci, Ayat tana zaune ita kaɗai, an jera mata kalar abinci daban-daban na alfarma... Saratu tana tsaye a gefe tana yi mata hidima, amma hankalin Ayat baya kan abincin... Tana tunanin Reems dake sama....kuliyar da ta yi amanna da ita... ​"Saratu," Ayat ta ƙira muryarta a dake.. "Na'am ranta ya daɗe," Saratu ta amsa cikin ladabi.. "Ina son ki haɗa min wani abincin a ƙaramin kwanon zinare, ki kawo min shi... Kuma ina son madara mai ɗumi." Saratu ta ɗan yi mamaki, "Gimbiya, ko har yanzu yunwar ba ta ƙare ba ne?" Ayat ta watsa mata kallo ɗaya ta cikin mayafinta, wanda ya sa Saratu ta sunkuyar da kai da sauri... "Kiyi yadda na ce." ​ Da ta kammala cin abinci, Ayat ta ɗauki farantin da Saratu ta haɗa mata ta nufi ɗakinta cikin natsuwa.. Zuciyarta cike take da tausayi, domin tunaninta gaba ɗaya ya karkata ga halittar da ta bari tana kwance a raunane... ​A sama kuwa, King Diamond ya ji takun tafiyar Ayat tana tahowa. Cikin hanzari ya lumshe idanunsa, jikinsa ya fitar da farin hayaƙi, nan take ya sake komawa siffar farar kuliyar nan mai rauni... Ya kwanta lamo a inda ta bar shi, yana numfashi sama-sama kamar mai barci.. ​Kofar ɗakin ta buɗe, ta shigo tare da rufe ƙofar a hankali kamar mai tsoron ta tayar shi daga barci, ta ƙariso ɗauke da tire na zinare... Halittar tana nan kwance a tsakiyar gadon, kamar yadda ta bar ta tun farko.. Ayat ta matsa kusa, ta sauƙe farantin a gefen gado, sannan ta ce cikin muryar lallami. “Reems… ga abinci nan. Ka ɗan ci, zai taimaka mika ka samu sauƙi.” ta faɗa cikin murya mai taushi. Ta ɗauko kuliyar ta ɗora a cinyarta, ta fara ba shi ƙananan naman kaza dake cikin kwanon... ​King Diamond a siffar kuliya ya fara cin abincin, yana jin daɗin yadda hannunta yake taba fuskarsa. A ransa yana cewa, "Ayat, idan kika san cewa Sarkin Power Pool kike ba wa abinci a hannu, da tabbas kin tsorata. Amma yau, ni ne bawanki, tunda kin zama mai ceton rayuwata." ​Bayan ya gama, ta ba shi madarar ya sha, sannan ta rungume shi a ƙirjinta. Ta ji zuciyar kuliyar tana bugawa da sauri, ita ma nata zuciyar tana amsawa... ✨✨ A babban ofishin tsaro na masarauta, Master Ibrahim ya kasa zama waje ɗaya. Ya kwashe sa'o'i yana kai da kawowa, idanunsa suna kallon agogo. Tun bayan da ya kwantar da Inuwa a gadonsa ranar da aka fasa masa goshi, ya ji shakuwar su ta ƙara ƙarfi, amma yanzu Inuwa ya ɓace masa... "Ina Inuwa yake?" ya daka wa wasu jami'ai tsawa.. "Ranka ya daɗe, tun da ya tafi ba mu sake ganinsa ba," ɗaya daga cikin jami'an ya ba da amsa cikin tsoro.. Ibrahim ya ji wani baƙin ciki ya turnuƙe shi. Ya fara tuna maganganun jami'an da ya kora a baya, waɗanda suka ce Inuwa ya fara yawon banza da bin mata a gari... "Shin da gaske Inuwa ya fara koyon halin banza? Shin har ya isa ya fifita wata mace a kaina?" Ibrahim ya faɗa a ransa, kishi yana ƙara rura wuta a zuciyarsa. Ya riga ya mayar da Inuwa Mataimakinsa wato PA, don haka rashin ganinsa ya zame masa babban naƙasu... A can ɓangaren Gimbiya Ayat kuwa, tana zaune a gaban madubinta, tana kallon kyakkyawar fuskarta. Ta ji a ranta cewa tabbas Master Ibrahim yana cikin wani hali na damuwa. Kusan sati guda ba su haɗu ba, kuma yau ta fita amma ta laɓe masa.. Ta kalli Reems dake kwance a kan gadonta, ta saki wani ƙayataccen murmushi... "Reems, ka yi haƙuri zan je na gudanar da aikina. Ina ji a raina Master Ibrahim yana nema na," ta faɗa cikin murya mai sanyi... Nan take, Ayat ta fara cire kayan sarautar nan masu ƙayatarwa. Ta ɗauko kayan jami'an nan na maza ta zura su, sannan ta maƙala saje, gemu, da gashin baki waɗanda take amfani da su wajen yaudarar mutane... Bayan ta gama, ta nufi gadon, ta sunkuya ta sake manna wa kuliyar sumba a goshi... "Babu mai shigowa ɗakin nan domin na kulle ta ciki. Zan bi ta wannan hanyar sirrin dake ɗakin nan na fita. Kar ka ji mamaki, haka ƙaddara ta so da ni. Zan dawo ba da jimawa ba domin duhu ya fara shiga, so nake kawai Master ya ganni in kwantar masa da hankali," ta faɗa a raɗa, kamar kuliyar za ta iya amsa mata... Ayat ta matsa jikin bangon ɗakin, ta danna wani sirrin mabuɗi, nan take bangon ya buɗe wata hanyar sirri ce dake fita zuwa bayan masarauta inda babu mai gani. Ta sulale ta fice, bangon ya koma ya rufe kansa... King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya buɗe idanunsa na zinare ya bi ta da kallo. Duk da sumbar da ta bar masa dake sanyaya masa rai, zuciyarsa ta cika da mamaki da kuma sha'awar yadda wannan yarinya take rayuwa a matsayin namiji.. Bayan ficewar Ayat, King Diamond bai zauna jiran dawowarta ba. Ya sauya siffa daga kuliya zuwa asalin siffarsa ta Aljani, inda ya ɓace daga idon kowa ya bi sawun Inuwa... Yana son gani da idonsa yadda wannan kyakkyawar yarinya take gudanar da rayuwarta a cikin maza.. Yana tafiya yana kallon yadda take shiga cikin jami'ai, kwarjininta a matsayin namiji yana ba shi mamaki.. Suna isa cikin masarauta, sai ga Master Ibrahim ya fito da guguwar fushi. Da ganin Inuwa, bai tsaya wata-wata ba, ya damƙe hannunsa da ƙarfi. Don kada ya zubar masa da mutunci a gaban sauran jami'ai, ya ja shi da ƙarfi har zuwa sashensa... King Diamond yana biye da su, idanunsa suna ƙuna yayin da yake kallon yadda Ibrahim ya wurga Inuwa a tsakiyar ɗakin nasa cikin zafi. Diamond ya tsaya a gefe guda, yana sarrafa kansa da ƙyar don kada ya bayyana ya hukunta Ibrahim.... Ibrahim ya tsaya a kan Inuwa, yana huci... "Tun yaushe ka fara yawon bin mata, Inuwa?" Ya fara zazzaga masa maganganu masu zafi na zargi da lalata, yana ganin cewa hakan ne ya sa ya ɓace tsawon sati ɗaya.. Inuwa tana ƙasa, kanta a sunkuye, ta ƙi ɗagowa ta kalle shi. Ta san idan ta yi magana, za ta iya kuka, kuma idan ta kalle shi, fushinsa zai iya sa ya fahimci wani abu a fuskarta... Ba zato ba tsammani, fushin Ibrahim ya tafi, sai ya maye gurbinsa da wani irin lallami mai sauti. Ya durƙusa a gaban Inuwa, ya sa hannu ya ɗago haɓar sa. A wannan lokacin, Master Ibrahim ya fara magana cikin muryar raɗa kamar yana yi wa mace magana, yana lallashinsa a kan kada ya sake nisa da shi... "Zan yafe maka kuskurenka," Ibrahim ya faɗa cikin murya mai sanyi, "amma hukuncinka shi ne, yau kai za ka yi min tausa daga wuyana har zuwa kunkumi..." Nan take Inuwa ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, wani irin gumi ya karye mata. Tausar namiji daga wuya har kunkumi? Wannan babban haɗari ne ga sirrinta duk da ba yau ne farko ba.. A daidai wannan lokacin, King Diamond ya dafe ƙirjinsa saitin zuciya. Saboda musayar jiki da suka yi a baya, yanzu duk firgicin da Ayat take ji, shi ma yana jinsa a jikinsa. Ya ji yadda jinin Inuwa ya fara gudu da sauri, hakan ya harzuka shi matuƙa. Yana kallon Master Ibrahim da wani irin kallo na kisa, yana jira ya ga inda wannan lamari zai ƙare... Inuwa ta haɗiye miyau, ba ta da yadda za ta yi. Domin ta wanke kanta daga zargin da yake mata, dole ta yarda da wannan hukunci na Master Ibrahim, ko da kuwa hakan yana nufin ta taɓa jikin namijin da ba nata ba.. Master Ibrahim ya cire rigarsa, ya nuna faffaɗan bayansa mai cike da kwarjini, sannan ya kwanta rub da ciki a kan katafaren gadonsa na alfarma. Inuwa ta matso jiki na ɓari, ta zauna a bakin gadon, sawayenta suna taɓa ƙasa. Ta fara kai hannunta kan wuyansa tana masa tausa cikin tsananin kulawa da fargaba. Hannunta mai laushi ya sa Ibrahim lumshe ido, yana jin wani irin sanyi dake ratsa shi... Daga gefe guda, King Diamond yana tsaye, idanunsa sun canza launi zuwa wani ja mai ban tsoro. Kishin aljani ya ninka na mutum sau dubu, ganin Ayat, mace ɗaya tilo da take da ikon shiga zuciyarsa, tana taɓa jikin wani namijin, ya sa ya ji kamar zai fashe tsabar zafi. Ya kasa sarrafa kansa, zuciyarsa ta buga, nan take ya rufe idanunsa ya dunƙule hannuwansa biyu cikin tsananin fushi. Ba zato ba tsammani, sai aka ji wani sauti... Wani irin ƙarfin tsafe-tsafe dake fita daga jikin Diamond ya daki gadon. Nan take duk ƙafafun gadon suka kakkarye... Master Ibrahim ya ji gado ya tafi da shi ƙasa. Da ba don katifa mai kauri ba, da tabbas ya faɗi a kan ƙarfuna da katako... Inuwa ta miƙe da sauri, zuciyarta na duka da sauri-sauri, tana mamakin abin da ya faru... "Lafiya, Master?" ta faɗa cikin murya dake rawa. Master Ibrahim ya sauƙo daga kan rugujajjen gadon yana zaro ido. Ya kalli ƙafafun gadon da suka zama guntu-guntu kamar an sare su da gatari.. "Wanne irin abu ne wannan?" ya faɗa yana waige-waige. Ya kasa gaskata cewa gadonsa mai ƙarfi zai ruguje lokaci guda ba tare da wani dalili na zahiri ba. Ya fara zargin ko akwai wani sihiri dake kewaye da sashen nasa.. King Diamond yana tsaye a gefe, yana kallon Ibrahim da wani irin kallon raini... Duk da cewa fushinsa ya sa ya kusan bayyana kansa, ya san dole ne ya yi haƙuri. Idan har ya fita daga masarautar nan a yanzu, to tabbas ba zai sake samun damar dawowa ba saboda tsananin garkuwar dake kewaye da gidan. Dole ne ya zauna a kusa da Ayat a matsayin Reems har sai ya gama shiga jikinta... Ibrahim ya juya ya kalli Inuwa, duk sha'awar tausar ta tafi, ya maye gurbinta da fargaba.. "Inuwa, tafi kawai. Zan sa a gyara gadon nan gobe. Amma ka sani, sa ido na yana kanka!" Inuwa ta ruga da gudu ta koma sashenta, zuciyarta na bugawa da sauri bayan hatsarin da ya faru a ɗakin Master Ibrahim... Tana shiga, ta kulle kofarta, ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya. Ba ta ɓata lokaci ba, ta shige bandaki ta watsa ruwa don wanke gajiyar ranar da kuma kawar da tunanin Ibrahim... Ta fito daga wanka, ta nufi wurin tufafinta. Ta zaro wata lallausar rigar bacci mai siririn hannu (spaghetti strap), wadda ta tsaya dai-dai gwiwarta. Rigar ta zauna daram a jikinta, tana nuna kyakkyawar surarta ta mace. Ta saki gashinta ya bazu a bayanta, sannan ta haye gadon ta zauna. Ta miƙa hannu ta ɗauko Reems. Ta rungume shi sosai a kirjinta, tana jin ɗumin jikinsa. Ta fara lulluma dogwayen yatsunta cikin farin gashin jikinsa, tana shafa shi cikin nutsuwa da kwarewa... Shi kuwa King Diamond, a siffarsa ta kuliya, ya lumshe idanu. Wani irin daɗi da kuncin rai suka ziyarci zuciyarsa. Yana jin kamshin turaren jikinta da kuma taushin hannunta dake yawo a jikinsa. Duk da cewa yana kishin yadda ta taɓa Ibrahim, wannan tattalin da take yi masa ya sa ya manta da komai.. Kamar yadda kuliya take nuna nishadi idan ana shafa ta, King Diamond ya saki jiki, numfashinsa yana sarkewa tsabar jin dadi. Yayin da take wasa da kuliyar, hankalinta ya tafi wata duniyar daban. Ta fara tunanin mutumin nan da ta hadu da shi a bakin kogi, mutumin da har yau ba ta san sunansa ba, amma kwayar idonsa ta gaza bacewa a ranta.. "Ina zan sake ganin sa?" ta fada a hankali, muryarta na nuna begen sa. Ta kara matse kuliyar a kirjinta, ba tare da sanin cewa mutumin da take mafarkin shine dai dake hannunta a matsayin dabba ba... Can kuma sai tunanin Master Ibrahim ya faɗo mata. Ta sauke ajiyar zuciya, "Allah ne kawai yayi hukuncinsa ya karya gadon nan," ta raya a ranta. Ta tabbata cewa Allah ne ya kare ta daga taɓa jikin namijin da ba nata ba, tunda ita mace ce kuma tana da darajar da take karewa.. King Diamond ya ji daɗi a ransa da ta danganta rugujewar gadon da hukuncin Allah, bai so ta fara zargin cewa akwai wani sihiri a kusa da ita ba... Ya ƙara shige jikinta, yana fatan dare ba zai waye a wannan yanayin ba... To pah zamu tsallake mu je pavilion meke faruwa a can ne😅😅😅 A cikin Pavilion City... Bayan wata guda da fara zaman Ching Ching a katafaren gidan Pavilion, rayuwa ta canja salo. A yau, tana sanye da kayan aiki tana mopping a babban falon Chief Onyx... Shi kuwa Chief yana zaune a kan kujera, hankalinsa gaba ɗaya yana kan kwamfutarsa yana danna ayyukansa, yayin da kofin coffee yake gefensa yana huce wa... Muryar Ching Ching ce take tashi a falon yayin da take rera waƙarta cikin nishaɗi, tana goge ƙasa da bucket a hannunta. Tana tafe tana goge-goge har ta zo dab da inda yake zaune... Cikin rashin sani ko kuma ince da gangan, ƙafarta ta zame a kan wurin da ta riga ta jika da ruwa. Nan take ta yi kamar za ta faɗi, sai kawai ta kai wa bucket ɗin watsa, ta kwarara masa ruwan tun daga kansa har zuwa jikinsa... Chief Onyx ya daka wata uwar tsawa yayin da ya miƙe tsaye, ruwa yana digowa daga jikinsa. Ya watsa mata wani irin kallo cike da takaici da fushi, yana tunanin wani irin hukunci ya dace da ita... Ita kuwa Ching Ching, maimakon ta ji tsoro, sai kawai ta tuntsire da dariya, ta rasa yadda za ta tsayar da kanta... "Wane irin rashin hankali ne wannan?" Onyx ya daka mata tsawa cikin zafin rai... "Ke ba ki da hankali ne ko kuwa ba ki san darajar mutane ba?!" Ching Ching ta turo baki gaba, ta fara gunaguni cikin shagwaba "Nifa ba a min tsawa!" Yayin da Onyx yake huci kamar zaki yana zazzaga mata faɗa, ita kuma sai ta ƙara haɗe rai tana murguɗa baki... Onyx ya sake daka mata tsawa, "Wane irin iskanci ne wannan? Kin san ko ni wane ne kuwa?!" Cikin rashin tsoro, ta sake murguɗa baki ta ce, "Gaskiya nifa ba a min tsawa. Idan za a yi magana, a yi ta cikin lallashi." Onyx, wanda kowa yake shakka a gari, sai ya tsaya turus yana kallon yadda take shagwaba kamar ba ita ce ta jika shi sharkaf ba. Fushin da yake yi sai ya nemi ya tafi, ya rasa yadda zai yi da ita saboda kwarjininta da rashin tsoronta. Daga ƙarshe, ya girgiza kai yana murmushin takaici.. "Lallai ke ba ki da dama. Kin jikani, sannan kuma kina min gatsali? To ki ma za ki samo min tawul kafin na sake canja ra'ayi!"... "Gaskiya ba zan je ba," ta ƙara turo baki tana murguɗa shi gefe. "Sai ka sake lallashina sannan zan je na samo maka. Ai da zafi-zafi ka yi min magana ɗazu." Onyx ya zuba mata ido, ya kasa yarda da abin da yake ji. Yarinya ƙarama take gaya masa ya lallashe ta bayan ta jikashi? Ya sauke ajiyar zuciya, ya rage muryarsa ƙasa-ƙasa cikin yanayi na rarrashi duk da cewa ransa a ɓace yake.. "To... kiyi haƙuri ranki ya daɗi. Don Allah sarauniyar shagwaba, ko za ki iya taimaka min ki kawo min tawul ɗin kafin sanyi ya kashe ni?" Ching Ching ta girgiza kai, "Gaskiya wannan lallashin bai yi daɗi ba, sam bai ratsa ni ba. Sai ka sake wani mai daɗi wanda zai gamsar da ni, sannan zan tashi." Onyx ya dafe kansa, ruwa yana digowa daga gashinsa zuwa fuskarsa... Ya cika ya yi fam, amma ganin yadda take kallonsa da idanunta masu cike da shagwaba ya sa ya kasa kure ta. Ya matso kusa da ita, ya sassauta muryarsa sosai kamar mai rarrashin jariri... "To Shugaba Ching Ching, kiyi hakuri don Allah. Ke ce mai gida, ni ne yaronki. Don darajar waccan dariyar da kika yi, ki taimaka wa bawanki da tawul, idan ba haka ba rashin lafiya zan yi, wa zai rika kula da ke?" Ching Ching ta sake tintsirewa da dariya, tana kallon cikin ƙwayar idonsa ta ce.. "Haba Uncle Onyx! Har yanzu dai lallashin nan akwai saura, bai kai can ba..." Tana cikin maganar ne, Onyx ya ga ba zai iya jure wannan shagwabar

Chapter 18 of 39