Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ibrahim baya nan...ta yi amfani da damar rashin Master ta sulale daga masarautar. Bayan ta yi sa hannu a babban littafin fita na jami'ai, ta zura wa dokinta linzami, kai tsaye ta nufi bakin kogin da ya zama tamkar maɓoyar sirrinta... Iskar wajen mai sanyi ta daki fuskarta, amma zuciyarta cike take da tunanin Mai Farin Gashin nan, mutumin da har yanzu ba ta san asalin ko shi wanene ba, amma kewarsa ya addabeta. Ta sauƙa daga kan dokinta, ta zauna a bakin ruwan tana kallon kwarararsa. "Ina kake ne?" ta faɗa a hankali, tana mamakin yadda abokin gaba ya zama abin kewa a gare ta. Can ba zato ba tsammani, wani abu mai nauyi ya faɗo daga sama, ya sauƙa a tsakiyar faɗin filawowin da ke haskaka wajen... King Diamond ne. Jikinsa duk jini, yana aman jini ta baki da hanci sakamakon raunukan da ya samu na rushewar kogon. Cikin zafi da raɗaɗi, ya ji motsin mutum. Ko da yake ya yi nisa a cikin mawuyacin hali, hankalinsa na sarki ya gaya masa cewa ba zai iya barin kowa ya ga rauninsa a matsayin mutum ba... Cikin sauri yayi amfani da ikon tsafinsa, ya jirkita ya zama Ƙaramar Kuliya... Farin gashin kuliyar ya ɓaci da jinin da ke fita daga jikinsa, yana nishi sama-sama... Inuwa ta miƙe a zabure, ta zaro takobinta tana raba idanu, tana tunanin ko wani makiyi ne ya biyo bayanta. Amma tana isa wurin, maimakon katon jarumi, sai ta ga wata kyakkyawar kuliya mai farin gashi tana nishi cikin azaba, jini na malala daga jikinta... Zuciyar Ayat ta buga. Duk dake ita jaruma ce da ba ta tsoron jini, amma tausayin dabba ya kasance rauninta tun tana yarinya. Ta maƙale takobinta, ta nufi kuliyar da gudu... "Haba! Waye ya yi miki wannan aika-aikar?" ta faɗa cikin muryar tausayi, yayin da ta tsugunna kusa da Diamond wanda ke cikin siffar kuliya... Ta sa hannuwanta biyu ta ɗauke shi cikin kulawa, ba ta damu da yadda jinin jikinsa ya ɓata kayan jami'in da ke jikinta ba... King Diamond, yana cikin siffar kuliya, ya kalli idanun Ayat. Duk da duhun da ya fara rufewa idanunsa saboda suma, ya ji wani irin ɗumi da aminci a tattare da ita wanda bai taba ji ba.... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣0️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan Ayat ta ɗauki kyakkyawar farar kuliyar nan mai rauni, ba tare da ɓata lokaci ba ta haye dokinta da sauri. Iskar dake kaɗawa tana busota yayin da take ƙara matse kuliyar a jikinta, tana gudun kada raunukan jikin kuliyar su ƙara tsananta... Tana isa ƙofar masarautar, ta yi sa hannu a littafin jami'ai cikin hanzari, sannan ta jefa kuliyar cikin wata leda ta musamman domin ɓoye ta daga idanun masu gadi. Ta san idan aka ga kuliya a hannun jami’i irin Inuwa, zai iya tada shakku... Bayan ta ajiye dokinta a rugar dawakai, tana ƙoƙarin sulalewa zuwa cikin masarauta, sai ta hango Master Ibrahim daga nesa. Cikin sani, ta san cewa muddin idonsa ya faɗa kanta, tambayoyi ne zasu biyo baya. Ta duƙa a hankali, ta laɓe bayan dogayen ginshiƙan masarautar, tana jin wasu jami'ai suna bi ta gefenta suna wasa da dariya.. Tafiya mai nisan gaske tayi a ƙafa kafin ta bi ta wata ɓoyayyen hanya, hanyar da ta kai ta kai tsaye zuwa cikin ɓangarenta na alfarma... Tana shiga ɗakin baccinta, wanda ke ƙamshi da turaren oud, ta ciro kuliyar da ke lumshe ido cikin galala, ta kwantar da ita a tsakiyar gadonta mai laushin gaske. A gaban babban madubi, Ayat ta fara cire kayan jami'an nan. Ta cire rawani, ta cire saje da gemun da take amfani da su wajen ɓoye siffarta. Nan take, dogon gashinta baƙi wul, ya bazu har zuwa gadon bayanta. Ta zama asalin kyakkyawar mace, mai kwarjini da izzah... King Diamond, wanda ke kwance cikin siffar kuliya, yana kallon kowane motsi nata. Duk da ciwon da yake ji, zuciyarsa ta buga ganin wannan canjin. Daga jarumin jami'i zuwa mace mafi kyau da ya taɓa gani a duniyar bil'adama. Abin da ya ƙara ruɗa Diamond shi ne lokacin da Ayat ta cire kayan jamin'an gaba ɗaya, ta ɗaura farin tawul kawai wanda ya bar fatarta mai santsi a bayyane. Ta nufi gadon, ta ɗauki kuliyar a hankali ta nufi banɗaki da shi... Yayin da take haɗa ruwan ɗumi a cikin bahon wanka, Diamond yana ta maganar zuci.. "Wannan me take shirin aikatawa ne? Shiga banɗaki tare da ni? Lallai wannan yarinyar ba ta san ko ni wane ne ba!".. Duk da haka, wani sashe na zuciyarsa yana cike da farin ciki. Masarautar nan tana kewaye da hasken garkuwa wanda ke hana aljanu da kowane irin tsafe-tsafe shiga, amma saboda canjin da ya yi zuwa dabba, kuma ta sanadin Ayat, ya samu damar shigowa har cikin zuciyar gidan... Ya ƙura mata ido yana mamakin yadda kyakkyawar mace irin wannan take rayuwa a matsayin soja. Wani irin sirri ne yake tattare da ita? Kuma wane irin ɗumi ne hannuwanta suke bayarwa yayin da take shirin fara yi masa wanka?.. Ayat ta gama gyara wa kuliyar jikinta tsaf, ta naɗe ta cikin tawul mai laushi sannan ta fito bedroom ta ajiye ta a kan gado... "Minti goma kacal zan yi," ta faɗa cikin murya mai sanyi, "amma kinsan wanka na akwai delay." Ta shige banɗakin, ta fara haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙanshi, tana shirin wanke gajiyar ta... Tana zaune a cikin bahon wankan, tana goga lallausar fatarta da sabulu, kanta na jingine da gefen bahon. Idanunta a lumshe, amma tunaninta yana can bakin kogi... "Me yasa nake kewar sa?" ta tambayi kanta. "Duk da abubuwan da ya yi min, musayar jikin nan da ya kusan haukata ni, da kuma kallon tsiraicina da ya yi a kogi, me yasa har yanzu nake jin tamkar akwai wani abu da yake haɗa mu?" Ta ji wani irin ɗumi a ranta, tana fatan da ace maimakon wannan kuliyar, 'Mai Farin Gashin' ne ta gani a yau... A cewar ta.. Tana shiga wankan, Diamond ya ji jikinsa ya fara wani irin zafi... Kasancewar Ayat tana cikin jin daɗin ruwan ɗumi, shi ma King Diamond ya fara jin wannan ɗumin ta sanadin haɗin jinin da ke tsakaninsu. Ikon tsafinsa ya dawo masa da ƙarfi saboda natsuwar da ya samu a ɗakinta.. Cikin kifawar ido, ƙaramar kuliyar nan ta zama haske, sai ga King Diamond zaune a tsakiyar gadon Gimbiya Ayat. Doguwar farar rigarsa ta masarautar aljanu ta bayyana, sumar kansa fara sol ta bazu har gadon bayansa... Ya zura wa ƙofar banɗakin ido, yana jin sautin ruwan da yake kwarara. Zuciyarsa tana bugawa. Ya tuna daren nan a bakin kogi lokacin da sukayi musayar jiki, sannan sumbatar da ya haɗa su ya fara dawo masa ƙwaƙwalwa...ya tuna yadda ya kalli kyakkyawar surarta tana wanka ba tare da ta sani ba... Wannan haɗin jinin da sukayi ya sa yanzu duk abinda take ji, shi ma yana ji. Yana iya jin dumin ruwan da yake taba fatarta, yana iya jin kamshin sabulun da take shafawa... "Ayat..." ya faɗa a hankali cikin ransa. "Kin zamo wata sirri a rayuwata!.. Kuma me yasa kika zama sanadin da zan ji tausayin bil'adama?"... Diamond ya miƙe a hankali daga kan gadon, ƙafafunsa tamkar baya taka ƙasi yayin da ya nufi hanyar banɗakin. Ya tsaya a jikin ƙofar, yana sauraron numfashinta.... Ya san cewa idan ta fito ta ganshi a matsayin mutum, babban tashin hankali zai faru, amma wani sashi na ransa yana son ta san cewa yana kusa da ita... A cikin banɗaki kuwa, Ayat ta fara jin wani irin yanayi na daban. Ta ji tamkar ba ita kaɗai ba ce a ɗakin... Zuciyarta ta fara bugawa da sauri, Ta miƙe da sauri daga cikin ruwan, ta ɗauki babban tawul ta ɗaura, tana sauraro da kyau... "Kamar akwai mutum a ɗakin nan..." ta raya a ranta... Ta fito daga banɗaki, sanyin ruwan ya sa fatarta yin luwai-luwai.. Tana ganin kuliyar nan a yadda ta bar ta a kan gado, sai ta saki wani irin murmushi mai ban sha'awa irin murmushin da babu wanda ya taɓa gani a masarautar nan sai ita kaɗai... Ta zauna a gaban madubi, ɗaure da gajeren tawul ɗin da ya tsaya dai-dai cinyoyinta... Ta fara shafa mayuka masu ƙamshi na alfarma, waɗanda ake yi wa gimbiyoyi oda na musamman daga ƙasashen waje. Kowane shafa mai da take yi, ƙamshinsa yana ratsa hancin King Diamond... King Diamond, wanda ya riga ya koma siffar kuliya kafin ta fito, ya kwanta lamo yana kallonta ta cikin ƙwayar idonsa. A ransa yana jin wani irin takaici da daɗi lokaci guda... "Ayat..." ya furta a zuciyarsa... "Idan kika san cewa ni ne abokin wasanki na ƙuruciya, mutumin da kika yi wa rantsuwar kiyaye fuskarki dominsa, shin zaki kashe ni ne ko kuwa zaki rungume ni?" Ya kalli yadda take shafa man a wuyanta da kafaɗunta.... Ya tuna lokacin da suke yara, lokacin da komai yake da sauƙi kafin ƙaddara ta mayar da shi sarki a duniyar aljanu.. Ganin yadda ta girma ta zama kyakkyawa haka, kuma jaruma mai faɗa a matsayin Inuwa, ya sa ya ƙara jin kwarjininta a ransa. Ayat ta juyo ta kalli kuliyar, ta miƙa hannu ta ɗaukota ta ɗora a cinyarta. Ta fara shafa kanta a hankali, tana wasa da farin gashinta.. "Kinsan me? Ke kaɗai ce kika ga fuskata a yau bayan shi," ta faɗa cikin muryar raɗa, tana nufin Mai Farin Gashin da ya ganta a kogi... "Shi ya ruguza min alƙawarina, amma ke... ke kyakkyawa ce. Zan kula da ke kamar jariri har sai kin warke."... Diamond ya lumshe ido, yana jin ɗumin jikinta da laushin hannunta. Haɗin jinin da ke tsakaninsu ya sa kowane shafa da take yi masa, yana jin sa har cikin ransa tamkar ita ma tana jin abinda yake ji... A wannan lokacin, Diamond ya manta da sarautarsa, ya manta da mulkinsa na aljanu, kawai yana son ya dawwama a haka, a jikin Ayat, yana kallon kyawun da kowa yake mafarkin gani amma shi kaɗai ya samu nasarar gani... Yayin da take cikin wannan yanayin na natsuwa, ba zato ba tsammani sai ta ji takun tafiya a babban falon ɓangarenta...ana haurowa saman bedroom... Zuciyarta ta buga. Babu wanda yake shigowa ɓangaren Gimbiya Ayat ba tare da izini ba, sai mutum ɗaya... Wato Saratu, nan ma bata shigowa sai da izini.. "Gimbiya Ayat? Kina ciki ne?" Saratu ce ta daki ƙofar ɗakin... Ayat ta zaro ido, ta kalli kuliya, sannan ta kalli kayan jami'an nan da ke warwatse a ƙasa waɗanda ba ta gama ɓoyewa ba... Idan Saratu ta shigo ta ga kayan jami'ai a ɗakin, asirinta zai tonu!... "Menene Saratu?..." Ta furta tana shafa jikin kuliya... Saratu daga bakin ƙofa ta ce, "Daman an kammala shirya dining ne..." Ta ce, "ok ki je ina zuwa, na fito a wanka ban kuma sa kaya ba..." Daga nan Saratu ta juya... Ayat ta miƙe ta ɗauko akwatin magunguna (First Aid Box) na musamman... Ta dawo kusa da kuliyar, ta fara goge mata ragowar jinin da ya bushe a wasu sassan jikin, sannan ta shafa mata magani mai sanyi da kuma turaruka masu ƙamshi don rage radadin raunin... Yayin da take gyara masa gashinsa, Ayat ta kalli cikin idanun kuliyar, wani irin tausayi da shauƙi suka mamaye zuciyarta. Ta ji tamkar kuliyar tana fahimtar kowane sauti da yake fita daga bakinta... "To ni ban sani ba, mace ko namiji?..." Tana kallon kuliyar ta kasa gane wa amma ita mace take bata... Sai kuma ta ce, "idan mace ce ke, ina son ki mun wani alama da zan gane..." Kuliyar tayi tsumu ko motsin bata yi ba.. Ayat ta kuma cewa "to idan namiji ne yi mun alama.." Nan kuliyar ta ɗago hannu tana shafa kanta.. Murmushi Ayat tayi tare da ƙara ringumarsa.. Ta ce da shi... "Ka zamo abokina ɗan amana... Daga yau, ke ba kuliya bace," ta faɗa cikin murya mai cike da shauƙi... "Zan sanya miki suna Reems... sunan mutumin da ya fi kowa daraja a zuciyata."... King Diamond, wanda ke cikin siffar kuliya, ya ji wani irin shock ya ziyarci zuciyarsa. Sunansa na asali! Sunan da ya binne shi tun ranar da ya zama sarki a duniyar aljanu. Wani daci da dariya suka taso masa a ransa, ya ce a ransa... "Ayat... ki rasa a wa zaki sanya sunana sai a dabba? Ni ne Reems dinki, asalin mutumin da kike jira, amma yau gashi kina kira na a matsayin kuliya!" Duk da haka, ya ji daɗin yadda sunan yake fita daga bakinta, ya tabbatar masa da cewa har yanzu yana raye a zuciyarta. Ayat ta miƙe ta nufi wurin tufafinta na sarauta. Ta saka riga ta alfarma mai ratsin zinare, sannan ta ɗauko ɗankwalin fuskarta ta rufe kyakkyawar fuskarta kamar yadda ta saba, ta bar idanunta kawai masu Golden Eyes a bayyane. Ta dawo bakin gadon, ta sunkuya ta manna wa kuliyar sumba a goshi... Wani irin sanyi Diamond ya ji ya ratsa shi har cikin bargonsa... "My Reems, zan sauƙa ƙasa domin yunwa nake ji. Zan taho maka da abinci kai ma ka ci, ka huta a lallausar gadona," ta faɗa a hankali sannan ta juya ta fice daga ɗakin cikin takun isa da izza. Tana fita, kofarta na rufewa, sai ga wani farin hayaƙi ya mamaye tsakiyar gadon. Nan take King Diamond ya dawo asalin siffarsa ta mutum. Ya zauna a tsakiyar lallausan gadon, sumar kansa fara sol ta bazu a kan zanen gadon Ayat... Ya ɗan gyara zama, ya taɓa goshinsa inda ta sumbace shi, sannan ya saki wani murmushin gefen baki... "Ayat... idan kika san cewa Reems ɗinki yana zaune a kan gadonki a matsayin sarki, shin zaki iya kawo min abincin kuwa?" Ya kalli ƙofar da ta fita, idanunsa suna shining da wani irin kwarjini da nuna cewa har yanzu shi ne mai iko, ko da kuwa yana cikin gidan masoyiyarsa ne a asirce.... ✨✨ Washe gari a safiyar yau, Gimbiya Maayah tana zaune a kan kujerarta ta musamman a wurin dining area na sarauta, tana cin French Toast mai kwai da zuma wanda aka kawo mata a cikin wani faranti na azurfa mai sheƙi... Gefenta tsaye masu aiki biyar sanye da fararen uniform, ɗaya na shara, ɗaya na gyaran teburi, ɗaya na kawo abinci, da sauransu... Acan bakin ƙofa Bodyguards guda biyu ne masu jikin dambe, sanye da baƙaƙen kaya.. Maayah ta ɗaga hannu, ba tare da ta kalle su ba.. “Where is my orange juice?” Muryarta a sanyaye cike da izgilanci.. Wata mai aiki, wadda kana ganinta kasan sabuwar zuwa ce, ta matso da sauri tana rawar jiki. “G-Gimbiya, a yau an kawo ruwan Passion Fruit ne, saboda an ce lemun orange ɗin ya ƙare a kitchen.” Maayah ta ajiye cokalin ta a hankali, sa'an nan ta ɗaga kai ta kalli sabuwar mai aikin. Ta yi mata kallo tun daga kanta har zuwa takalmin ta... “Kin san cewa a cikin Fadar Alhamra, Maayah ba ta shan ruwan Passion Fruit? Kuma kin san cewa lemun orange bai taɓa ƙarewa ba? Yanzu haka, ki tashi ki kawo min sabon ruwan lemun. Idan kuma ba ki same shi ba, to ki je ki samo wanda zai kawo min a cikin minti biyar, sannan ki cire kayan jikinki ki bar mun site...” Muryar Gimbiya Maayah ba ta da zafi amma ta fi ƙarfin wuta. Nan take, sabuwar mai aikin ta fashe da kuka, ta durƙusa tana roƙon afuwa... “Gimbiya, dan Allah, ki yi haƙuri. Na yi kuskure. Zan tafi in samo.” “Too late,” Maayah ta yi tsaki. Ta kalli ɗayan mai aikin, wadda ta fi ta sanin komai... “Maimaita wa wannan sabuwar dokokinmu! Ba na son ganin ta a cikin fada ta. Cire mata uniform ɗin ta. Kuma Mama Liyatu ta kawo min ruwan lemu.” Mama Liyatu ta shigo da sauri, tana sanye da doguwar riga mai kyau... “Gimbiya ta, dan Allah ki yi haƙuri, abinci yayi daɗi fa. Ki bar ta. Zan kawo miki ruwan.” Mama Liyatu ta san yadda za ta tausasa ran Gimbiya kafin ta fusata... Maayah ta yi sigh mai nauyi... “Fine. But babu wanda zai iya damuna a cikin gida na.” Mama Liyatu ta yi murmushi, amma cikin tsoro take faɗin. “An gane, Gimbiya. Duk abin da kika ce shi za a yi.” Ta juya, ta yi nuni ga masu aiki biyu da su raka sabuwar mai aikin... Bayan ɗan mintuna sai ga wani jami’in tsaro na fadar sarki ya shigo domin isar da saƙo. Ya gaishe da Maayah dake zaune a kan teburin cin abinci, sannan ya ce, "Sarki ya aiko ni, yana son ganin gimbiyarsa Maayah..." Maayah ta ɗaure fuska tare da yamutsa ta cikin isa ta ce, "Kaje kace masa Maayah makaranta zata je, sai ta dawo." Kafin Maayah ta sake furta wani abun, har jami'in tsaron ya juya ya fita domin isar da saƙon... Kamar dama jira yake ta faɗi abin da zai sosa ran sarki, domin tun ba yau ba ake sanar da sarki cewa Maayah ta ɓaci da wulakanci da girman kai tamkar Zayana, amma sarki ya ƙi yarda... Ganin jami’in tsaron ya tafi ne ya sa Maayah faɗin, "Daga cewa makaranta zan je shikenan sai ya tafi? Faɗa kawai nayi, amma ba wai naƙi zuwa bane..." Ta ƙarisa maganar kamar mai fargabar abun da zai je ya dawo... Mama Liyatu ta ce, "To tinda hakane, kawai ki tashi kije ƙiran sarki. Idan ya ganki da uniform ɗinki, zai fi sallamarki da wuri, ya fi dai baki je gaba ɗaya ba." Maayah ta kalli Mama Liyatu cikin isa ta ce, "Mama Liyatu, ni fa ba a bani shawara ballantana umarni. Abin da naga ya dace shi zan yi." Mama Liyatu ta yi shiru, ba ta sake cewa uffan ba.. Maayah ta ƙara da cewa, "Ya je ya sanar ɗin tinda shi munafuki ne, bai jira na gama magana ba ya tafi. To makarantar zan je, na ga ko kashe ni za a yi!" Ta ci gaba da cin abincinta cikin kwanciyar hankali, babu ruwanta da kukan yarinyar da aka kora ba tare da wani dalili na kirki ba.... Cikin minti biyar, direbanta wanda shima yake sanye da uniform ya iso ya tsaya a gabanta... "Gimbiya, motar tana nan a shirye. Makarantar za a tafi yanzu?" "Yes. Amma ba zamu bi hanyar da talakawa ke bi ba a yau. Zamu bi ta hanyar Presidential Gate, ina so naga yadda take a yau."... Direban ya sunkuyar da kai, "Kamar yadda kika ce, Gimbiya." Maayah ta tashi, ta zuba ido ga Mama Liyatu ta ce, "A cikin mako mai zuwa Mama Liyatu, ina so ki shirya min gagarumin party.... Zan gayyaci 'ya'yan ministoci da 'yan kasuwa masu kuɗi... Ba na son ganin talaka a cikin fadar Maayah.. Ki tabbatar an kammala komai kafin na dawo daga makaranta." Ta fita tana takun alfarma da kasaita, dakarun tsaron ta guda biyu suna biye da ita.... Motar Lexus mai sheƙi ta ɗauke ta ta bar bangaren nata... Kafin Maayah ta bar bangarenta, har jami'in tsaron ya isa gaban sarki ya sanar da shi yadda suka yi... Tafida dake zaune a gefe ya cika da mamaki ya ce, "Maayah ce ta ce haka?" Jami'in tsaron ya tabbatar masa. Sarki Nourdeen yana zaune a kan karagar sa cikin siffarsa ta Zaki, bai ce komai ba... Suna zaune Kwatsam, sai wasu jami'an tsaro suka sanar cewa, "Ga motocin Gimbiya Maayah nan zasu wuce makaranta." A lokacin ne Sarki ya miƙe tsaye cikin kwarjini. Shi da kansa ya nufi wajen fada zai fita. Wasu fadawa cikin girmamawa suka ce, "Mai Martaba, ka bamu izini mu dakatar da su, ba sai ka fita ba." Sarki ya ɗaga musu hannu alamar su kyale shi... Yana fita, daidai lokacin da motocin Maayah suka raba titin gate ɗin fita, sarki ya saki wata irin uban tsawa mai firgitarwa cikin muryar Zaki mai cike da daji... "MAAAYAAAHH!!!" Wata irin girgiza motar su ta yi har sai da ta ɗan ɗagu daga ƙasa... Direban ya danna burki da kansa, motocin suka tsaya cak! Saura kaɗan motar da Maayah take ciki ta kife. A cikin motar, Maayah ta yi sumar zaune saboda tsananin firgici... Kaf jami'an tsaro, fadawa, bodyguards, da dakarun sojoji babu wanda bai tsorata ba, wasu ma har neman guduwa suke yi.. Fadawan dake kusa da sarki ma kowa ya ruɗe, har sai da wani ya saki fitsari a jikinsa saboda tsananin firgici.... Kukan birkin motocin ya haifar da wata baƙin hayaƙi mai yawa a harabar Gate... A cikin motar Lexus ɗin, Maayah ta daskare, idanunta sun fito waje, numfashinta ya tsaya na mintuna biyar.. Ba ta taɓa jin muryar mahaifinta cikin wannan yanayin ba. Jikinta ya fara rawa, izzar da take ji yanzu ta narke ta koma tsoro tsagwaronsa... Sarki Nourdeen ya taka zuwa tsakiyar hanyar, takunsa na girgiza ƙasa... Fuskarsa ta Zaki mai cike da gashi tana wani irin haske na ban tsoro, idanunsa ja wur kamar garwashin wuta... Ya tsaya gaban motar Maayah, kowa na wajen ya ɗuka, wasu sun kifa fuskarsu a ƙasa don kar su kalli fuskar Zakin... "FITO!!!" Ya sake daka wata tsawar, wadda ta sa gilashin motar Maayah fara tsagewa... Ƙofa ta buɗe a hankali. Maayah ta fito, cikin takun tsoro da firgita, ƙafafunta sun kasa ɗaukar nauyinta... Ta zube a ƙasa gaban mahaifinta, uniform ɗinta ya ɓaci da ƙura... "Barka da safiya... Abul," ta faɗa cikin murya mai rawa, kanta a ƙasa... Sarki ya matso kusa da ita, inuwar fuskarsa ta Zaki ta mamaye duk jikinta. Ya sunkuyo da kansa daidai kunnenta, tana iya jin zafin numfashinsa da kaurin kishirwar jini da ke tashi daga gare shi... "Izzah tana da iyaka, Maayah," in ji Sarki, muryarsa tana fitowa daga can ƙasan makogwaro kamar gurnani... "Kina tunanin don na ba ki damar fita school, hakan yana nufin kin fi ƙarfin umarnina? Jami'in tsaro na ya zo gare ki, amma kika ce sai kin ga dama? Shin kin manta cewa ni ne na gina wannan masarautar da jinina da kuma wannan fuskar tawa?" Maayah ta fashe da kuka, "Don Allah Abul... kayi haƙuri. Ba nufina ke nan ba." Sarki ya ɗago kansa, ya kalli dakarun tsaron da ke kewayen motar. "Daga yau, an soke fitar Maayah makaranta na tsawon wata guda. Za ta zauna a ɓangarenta, kuma kowane malami zai zo har gida ya koyar da ita kamar sauran..." Ya kalli direban da bodyguards ɗin, "Ku mayar da ita ɓangarenta. Idan na sake jin ta nuna isa ga wanda na aiko, to zan tabbatar ta san cewa ni Zaki ne, ita kuma 'yar dabba ce a gabana!" Sarki ya juya ya bar wajen, takunsa yana barin gurbin ƙafa a kan kwalta. Fadawa suka fara rarrafe suna mara masa baya, yayin da Maayah ta rage a durƙushe a tsakiyar titi, tana kuka mai ban tausayi, duk izzarta ta koma kaskanci a gaban kowa... Bayan kora da aka yi wa Maayah, an mayar da ita bangarenta karkashin tsauraran matakan tsaro... Tana zaune a ɗakinta, ta kalli kayan makarantar da aka hana ta saka, ta watsar da su gefe guda cikin fushi da takaici... Washegari da safe... Malami ya zo har gida domin koya mata, amma Maayah ta ƙi fitowa daga ɗaki. Tana jin kanta ya ragu, musamman yadda yanzu sauran ƴan uwanta za su riƙa yi mata kallon wadda aka hukunta... "Mama Liyatu!" Ta ƙira da karfi... Mama Liyatu ta shigo jiki na rawa. "Gimbiya, gani." "Ki sanar da malamin nan ya tafi. Ba zan fito ba. Kuma ki tabbata babu wanda ya sake ambata sunana a gidan nan yau, idan ba haka ba zan sa a yanke harshen duk wanda ya yi hakan."... Duk da Sarki ya hukunta ta, Maayah tana kokarin dawo da ragowar izzarta akan talakawa da masu aiki... Amma a zuciyarta, tana tsoron ranar da za ta sake haɗa ido da mahaifinta mai fuskar Zaki... Labarin abin da ya faru da Maayah ya isa kunnen Gimbiya Zayana... Zayana tana zaune a nata sashen, wanda yake can nesa da kowa, cike da kamshin turaren na musamman... Zayana tana kwance a kan wata gadon

Chapter 17 of 39