Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da hannu... Ya fara yi wa sarki jagora ta cikin sashe-sashe mabanbanta.. Sarki ya ga jerin motocin yaƙi da na alfarma waɗanda ba a taɓa ƙera irinsu ba a duniya.. Dawakai ne baƙaƙe, manya masu sheƙin fata, waɗanda kowane ɗaya ana masa hidima ta musamman... Kowace kusurwa akwai jami'ai, wasu a sama wasu a ƙasa, dukansu idanunsu ba ya kiftawa. Sarki Nourdeen yana tafiya ne kamar a mafarki. Wurin ya kasu Part part, kowane sashe da abin da ake gudanarwa a ciki, tun daga tsaro har zuwa na'urorin zamani da suke ta faman aiki... Daga ƙarshe, jami'in ya kai sarki zuwa wani babban falo da ya fi kowane falo da sarki ya taɓa gani a rayuwarsa. Kujerun wurin an ƙera su da wani irin fata mai taushi da launin zinare.. Suka zaunar da sarki a can, aka bar shi shi kaɗai a cikin wannan faffaɗan ɗakin.. Ba a daɗe ba, wasu ma'aikata mata waɗanda kyan fuskarsu kaɗai ya isa ya saka mutum cikin damuwa, suka shigo ɗauke da tire-tire na zinare. Suka shimfiɗa masa kayan ciye-ciye da abubuwan sha na alfarma, waɗanda ƙamshinsu kaɗai ya isa ya nuna tsadar su. Sai dai waɗannan ƴan mata ma'aikata duk ba mutane bane, su ɗin robots ne masu amfani da na'ura... Sarki ya zauna a kan kujerar, amma ya kasa ko taɓa ruwan dake gabansa. Idanunsa suna ta kai-komo, kowane motsin labule ko ƙofa sai ya tsorata shi. Yana nan zaune yana jiran jin takun tafiyar da zata sanar da isowar mutumin da ya sanya shi barin masarautarsa a lokaci guda... Falon ya yi shiru sai ƙarar sanyin na'urorin sanyaya ɗaki kawai ke tashi. Sarki ya duƙar da kansa, yana tambayar kansa.. "Me zai faru idan wannan mutumin ya fito? Shin yarjejeniyar da muka yi tsawon shekaru da suka wuce, yau ce ranar da zan biya ta?".. Sarki Nourdeen yana tsaka da fargabar jiran abin da zai faru, sai ya ji iskar falon ta canza launi. Ba tare da an ji takun tafiya ba, da motsin ƙofa ba, kawai sai ga Chief Onyx ya bayyana a tsakiyar falon tamkar iska ce ta huro shi... Tsayuwar sa kawai ta isa ta nuna cewa shi ba mutum ba ne irin na wannan zamanin, ƙirar jikinsa irin ta magabata ne, samudawan farko masu girman jiki da ƙasusuwa ƙusassu... Tsayinsa ya zarce tunanin mai kallo, faffaɗen ƙirjinsa kuma ya nuna irin ƙarfin dake ɓoye a jikinsa... Sanyi ya ratsa falon kamar wani abu mai rai ya shigo, fitilun suka ɗan fara rawa.. Kamar yadda iska ke bayyana ba tare da izini ba haka Chief Onyx ya bayyano a tsakiyar falon... Dogon baƙin rigarsa tana ja har ƙasi, amma rigar ta gaba a buɗe take tana bayyana faɗaɗen farin ƙirjinsa kamar an sassaƙa shi da ƙarfe... Farin ƙirjinsa, wanda ya yi fari ƙal tamkar madara ya fito fili, tare da wasu kwantattun gashi dake kwance a kan faffaɗen ƙirjin nasa, wanda ya ƙara fito da jarumtarsa... Manyan nonuwansa sun tsaya daram, irin ƙirar namiji tsantsa wanda kallo ɗaya zai sa zuciya ta manta bugawa... Wasu sarƙoƙi na musamman masu tsada na azurfa sun zubo daga wuyansa har zuwa kan faffaden ƙirjinsa, suna walkiya a ƙarƙashin hasken fitilun falon... Dogon baƙin gashinsa mai santsi da sheƙi yana sauƙa har kafaɗunsa, yana kaɗawa a hankali cikin sanyin AC... Gefen fuskarsa guda na rufe da wani ƙarfen azurfa mai sarƙaƙƙiyar ƙira, wanda ya ƙara wa idanunsa kwarjini.. Idan ka kalle shi, ba wai ka ga kyau kawai bane har da tsantsar barazana... Idan ka tsinci kanka kana kallonsa tsawon daƙiƙu to jikinka zai daskare. Zuciyarka zata buga da sauri ba tare da dalili ba.. Takalmansa baƙaƙe, masu nauyi kamar na soja suna sauƙa ƙasa da ƙasa ba tare da amo ba, amma kowane taku yana da nauyin da yake sa ƙasa ta tuna da shi... Kana kallonsa zaka ce.. “Wannan ba musulmi bane.” Amma shi musulmi ne cikakke mai bautar Allah cikin sirri, mai tsananin tsoronSa, kuma mai tsananin hukunci ga wanda ya karya doka... A bayansa, tana taku cikin natsuwa da izza tamkar ɗawisu, wata zafaffiyar budurwa ce kyakkyawa dake sanye da baƙaƙen kaya matsattsu. Gashinta a kwance yake har gadon bayanta, idanunta kuwa suna fitar da wani irin haske na musamman... Wannan budurwa ba mutum ba ce, ita ce ƙololuwar fasahar Pavilion. Robot ce ta musamman, wacce aka ƙera ta don kariya da aiwatar da ayyukan da mutum ba zai iya ba. Ita ce babban makamin Chief Onyx... Halitta ce da aka ƙera domin yaƙi, tsaro, da aiwatar da umarni ba tare da tambaya ba. Ita ce hannun damar Chief Onyx. Ita ce garkuwarsa da takobinsa... Chief Onyx ya zauna a kan kujerarsa ta alfarma, ya ɗora hannuwansa a kan madafan kujerar, idanunsa suka sarƙe da na Sarki Nourdeen. Robot ɗinsa tana tsaye a gefensa tamkar mutum, idanunta suna nazarin kowane motsi na baƙon da yake gabansu... Sarki Nourdeen ya tsinci kansa da kasa magana. Duk wani iko da yake takama da shi a Alhamra, ya neme shi ya rasa a gaban Chief Onyx.. Muryar Chief Onyx ta fito da zurfi da amo tamkar ana hura busa.. "Barka da zuwa, Sarki Nourdeen. Na san ka daɗe kana jiran wannan ranar. Amma tambayar ita ce... shin kana shirye da farashin da za ka biya?"... Chief Onyx ya karkata kansa gefe guda, yana kallon Sarki Nourdeen da idanunsa dake fitar da wani irin kwarjini na daban.. Robot ɗinsa dake tsaye a gefe ta lura da yadda bugun zuciyar sarki ya tsananta.. "Nourdeen," Chief Onyx ya ƙira sunansa ba tare da lakabin sarauta ba, muryarsa tana amo a cikin falon. "Shekaru goma sha biyar sun shuɗe tun ranar da kuka kawo min yaƙi tare da taimakon dakarun turawan matar ka Ruma. Ranar da kuka so ku raba ni da gadon mahaifina. Na bar maka Alhamra ba don tsoro ba, sai don umarnin kotun duniya da kuma buƙatar kwanciyar hankali.".. Chief Onyx ya miƙe tsaye, tsayinsa ya sa sarki ya ji tamkar shi wani ƙaramin yaro ne. Ya fara takawa a hankali yana zagaye Sarki Nourdeen, yayin da takalmansa suke bada sauti a kan lallausar carpet.. "Na bar maka Alhamra a matsayin aro, amma da sharaɗi guda ɗaya. Ka amince za ka mallaka min ɗaya daga cikin 'ya'yanka don ta zama Personal Maid ɗina wato ƴar aikina. Ka yarda da hakan don kawai ka riƙe mulkin da ba naka ba. To yanzu lokaci ya yi. Na zo karɓar abin da yake nawa ne.".. Cikin Ruɗani Da Takaici Sarki Nourdeen ya duƙar da kansa, gumi na keto masa. Ya tuna lokacin da ya yi wannan yarjejeniyar, a ransa ya ɗauka lokacin ba zai taɓa zuwa ba. Amma yau, ga Chief Onyx nan a raye cikin ƙarfi da mulki fiye da kowane lokaci... "Ina buƙatar mace mai tarbiyya, jajirtacciya, kuma wacce za ta san darajar Pavilion," Chief Onyx ya ci gaba da magana yayin da ya tsaya a gaban sarki.. "Ban san ko su wane ne 'ya'yanka ba, kuma hakan bai dame ni ba. Abin da nake so shi ne ɗaya daga cikinsu ta zama ƴar aikin pavilion kingdom.".. A idon Sarki Nourdeen, fuskokin 'ya'yansa suka fara giftawa... Zayana wacce take jinin Ruma ce, matar da ta janyo wannan yaƙin. Shin zai iya bayar da ita? Amma kuma Ruma ta kasance mata mai ƙarfin iko fiye da tunanin mutum, kuma jinin turawa wacce a yanzu take mulkan ƙasar Canberra babban birnin Australia... Aayat wacce take amintacciyarsa kuma take kare shi? Ya girgiza kai alamun rashin amincewa.. Maayah wacce take cikin jinya yanzu?... Chingching wacce ba ta san zafin rayuwa ba? Duk wadda ya bayar ya sani cewa ya tura ta ne zuwa bauta a gidan mutumin da yake ƙin jinin mahaifinsu.. Amma idan bai bayar ba, ya san Chief Onyx zai iya murƙushe Alhamra a cikin sa'o'i kalilan... Chief Onyx ya yi wa Robot ɗinsa nuni da hannu. Robot ɗin ta matso kusa da sarki, ta miƙa masa wata na'ura mai nuna hotuna.. "Zaka ba ni sunan wadda ka zaɓa kafin rana ta faɗi..," Chief Onyx ya faɗa cikin murya mai sanyi... "Idan kuma ka kasa zaɓa, to ni da kaina zan shigo Alhamra in ɗauki duk wacce idona ya nuna mun... Kuma ka sani, idan na shigo da kaina, ba zan fita hannu empty ba..."... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣4️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Sarki Nourdeen ya shiga cikin wani hali na ƙunci da matsanancin tunani. Ga shi a gaban babban maƙiyinsa, mutumin da yake bin sa bashin dake iya ruguje masa mulki da mutunci... Chief Onyx kuma yana nan zaune, idanunsa tamkar takobi suna sassaƙa zuciyar sarki yayin da yake jiran amsa... Sarki Nourdeen ya fara rarraba wa zuciyarsa zaɓin 'ya'yan da yake da su, amma kowace ya kalla sai ya ga cikas... Zayana! Ko kusa, sarki ba zai taɓa iya bayar da ita ba. Tsoron mahaifiyarta Ruma yake yi fiye da yadda yake tsoron kowa. Ya san idan ya bayar da Zayana, Ruma za ta iya janyo masa yaƙin da ya fi na farko muni, domin tana da ikon da zai iya girgiza dukkan masarautar... Ayat kuma wannan ma ba zaɓi ba ne a gare shi. Ayat tana da wani irin zafi da rashin haƙuri. Ba ta jure wulaƙanci kuma tana iya tunkarar kowa. Idan ya bayar da ita, ya san za ta iya tayar da babban rikici a cikin Pavilion wanda zai iya kai su ga halaka... Maayah kuma halinta da na Chief Onyx ba za su taɓa haɗuwa ba. Maayah tana da tsananin girman kai, yayin da Chief Onyx yake son mutum mai sauƙin kai da biyayya. Ba zai taɓa dacewa a kai ta can ba... Yumna kuma Shima sarki ya sani cewa Chief Onyx ba zai taɓa karɓar Yumna ba saboda dalilai na kashin kansa da suka shafi tsarin masarautar Pavilion... Ganin sarki ya yi shiru, Chief Onyx ya ɗan yi nuni da hannunsa zuwa ga babban bangon falon. Nan take bangon ya juye ya zama babban screen wanda ya fara nuna hotunan dakarun Pavilion dubu-dubai dake atisaye a ƙasa da kuma na'urorin yaƙi masu firgitarwa... "Uncle, kada ka ɓata lokaci kana tunanin yadda za ka yaudare ni," Chief Onyx ya faɗa cikin murya mai sanyi dake cike da jan kunne... "Duniya ta canja. Idan na ba da umarni yanzu, kafin rana ta fito Alhamra za ta zama toka. Ba na neman wadda kake so, ina neman wadda za ta biya bashin da nake binka ne."... Sarki Nourdeen ya haɗiye yawu, ya dubi Chief Onyx cikin raunin murya... "Chief, na san na yi alkawari, kuma ban musanta ba. Amma ina neman alfarma guda ɗaya. Ka ba ni kwanaki uku kacal in koma in tsara yadda zan taho maka da ita. Ba zan iya ɗaukar ɗaya daga cikinsu a yau ba tare da wani shiri ba.".. Robot ɗin dake tsaye a gefe ta kalli Chief Onyx, tana jiran umarninsa... Chief Onyx ya yi shiru na ɗan lokaci, yana kallon yadda sarki yake gumi.. "Kwanaki uku?" Chief Onyx ya maimaita, sannan ya yi wani murmushin gefen baki wanda ya ƙara bayyana kwarjininsa. "To shikenan. Na ba ka kwanaki uku. Amma ka sani, idan kwanaki ukun nan suka cika baka kawo min wacce nake buƙata ba, to ni da kaina zan shigo Alhamra. Kuma a ranar ba zan karɓi 'yar aiki ba, zan karɓi duk masarautar ne baki ɗaya.".... Sarki Nourdeen ya ji wani sanyi, amma kuma ya san kwanaki ukun nan ba komai ba ne. Ya miƙe cikin sanyin jiki yayin da Robot ɗin ta fara yi masa jagora don fita daga falon zuwa inda helicopter ɗinsa take... ✨ Sarki ya jingina kansa da jikin kujerar jirgin, idanunsa a rufe. "Chingching," ya raɗa a fili... Itace kaɗai zaɓin da sarki yake gani zai iya fitar da shi kunya. Ba ta da uwa mai iko kamar Ruma da zata tada masa hankali, hasali ma uwarta bata raye, kuma ba ta da zafin kan Ayat ko girman kan Maayah... Amma kuma, zuciyarsa ta buga lokaci guda.... Chingching yarinya ce ƙarama, wacce ba ta san komai ba sai wasa da neman abinci... Ta yaya zai ɗauki wannan ƴar gaban goshin tasa ya kai ta matsayin yar aiki ga mutum irin Chief Onyx?... "Amma idan ban bayar da ita ba, Alhamra zata ruguje," Sarki ya faɗa cikin ransa, yana jin raɗaɗin yanke wannan danyen hukuncin... ✨ A can cikin masarautar Alhamra, kishin shaƙuwar dake tsakanin Inuwa da Master Ibrahim ya fara kai ma'aikata maƙura.. Ganin yadda Inuwa baya wani aiki na kwarai, sai dai ya fita yawonsa ya dawo ya huta, ya sa sauran dakarun fadar suka kulla masa sharri.. Sun haɗa gungunsu suka nufi wurin Master Ibrahim da nufin ɓata Inuwa.. "Master, gaskiya wannan yaron yana neman ɓata mana suna," ɗaya daga cikinsu ya fara magana.. "Wannan fitar da yake yi, ashe yawon neman mata yake yi a gari. Yana zuwa yana sharholiyarsa da mata, shi yasa idan ya dawo baya iya aiki saboda gajiya.".. Ibrahim ya ji wani irin ɗaci a ransa. Kalaman sun sosa masa zuciya, musamman idan ya tuna yau da safe da Inuwa ya sanar da shi cewa ya kwana da wata a asibiti... Amma a matsayinsa na jagora, bai nuna musu rauninsa ba. Ya share su, ya kuma ɗaure fuska tamkar bai damu ba.. "To, ina ruwanku?" Ibrahim ya faɗa cikin tsawa wacce ta sa suka ja baya. "Shi Inuwa ba namiji bane? Kamar yadda kuke son mata, haka shima yake sonsu. In dai yana yin abin da na sa shi, to ku barshi yasha soyayyarsa, lokacinsa ne!" Duk da cewa ya kare Inuwa a gaban ma'aikatan, amma bayan sun tafi, Ibrahim ya zauna shi kaɗai yana tunani. Wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyarsa wanda shi kansa bai san dalilinsa ba.. "Mata yake nema a gari?" ya tambayi kansa. Yana jin tamkar an yaudare shi. Ya fara jin cewa dole ne ya sanya ido sosai kan Inuwa, ba don sharrin ma'aikatan ba, sai don yana son tabbatar wa kansa cewa lallai Inuwa namiji ne cikakke mai sha'awar mata, domin har yanzu akwai wani abu game da Inuwa da ya kasa ganewa.. ✨✨ Bayan kwana biyu... Yau ma, Inuwa ya sulale ya fice daga fadar ba tare da Master Ibrahim ya sani ba, ya nufi tsakiyar kasuwar birnin Alhamra domin ɗan zagayawa ya rage wa kansa damuwa.. Kasuwar tana nan cike da hayaniya da rance-rancen ma'amaloli. Muryoyin masu talla suna tashi ta kowane gefe, musamman muryar mai sayar da abubuwan zaƙi, wanda ƙamshinsa ya cika ko'ina. Inuwa ya tsaya a gaban mai tallan, ya ji yana sha'awar saye amma duba aljihunsa ke da wuya, sai ya ga kuɗin jikinsa ba zai isa yayi siyayyar da yake so ba. Cikin sanyin jiki ya kawar da kansa ya yi gaba... Ba tare da ya sani ba, King Diamond yana biye da shi a baya, idanunsa na yawo akan kowane motsi na Ayat, amma sai dai a wannan lokacin bai fito a mai siffar farin gashi ba, ya koma gashinsa irin na ko wani mutum amma yana sanye da fararen kaya domin yana son farin abu a rayuwarsa.... Ganin yadda ta bar wurin mai zaƙin nan cikin rashin nasara, King Diamond ya isa wurin, ya nuna abin sannan ya ciro guda ɗaya daga cikin tsayayyun lu'u-lu'unsa ya miƙa wa mai sayarwa. Mai tallan ya daskare, ya kasa yarda cewa an biya shi da lu'u-lu'u akan kayan zaƙi!.. Inuwa ya cigaba da tafiya har ya tsaya a wurin mai snacks, ya sayi wasu ƴan abubuwa ya cigaba da tafiya. King Diamond ya sake tsayawa a wurin, yana kallon bayanta cikin nazari... "Tana son cakes ne?..." ya tambayi kansa a hankali. Shi ma ya sayi wasu nau'ukan snacks ɗin, ya sake biyan mai sayarwar da lu'u-lu'u. Mai snacks ɗin ya fara murna da rawa domin abin da aka biya shi ya fi ƙarfin abubuwan da yake sayarwa ninkin-ba-ninki... Daga ƙarshe Inuwa ya tsaya a wani babban tebur dake cike da littafai. Mai tallan yana ta shela.. "Books for sale! Littafai na tarihin duniya!" Inuwa ya fara dubawa, can sai idonsa ya sauƙa akan wani littafi mai taken "The Legend of the White Cat." Wani murmushi na natsuwa ya bayyana a fuskarsa, ya sayi littafin cikin farin ciki ya rungume shi, ya cigaba da tafiya... King Diamond ya ƙaraso wurin mai littafin, idanunsa suna kallon yadda Inuwa yake tafiya yana rungume da littafin nan... "Kana son littafai ne, Sir?" Mai littafin ya tambaya cikin girmamawa.. King Diamond bai amsa ba, ya zura wa bayanta ido yana maganar zuciya.. "Me ya sa take farin ciki da sayan littafi kuma? Me yake cikin wannan takardar da ya sa ta murmushi haka?" Ya ji wani irin shauƙi na son sanin komai game da ita, abin da take so, abin da yake sa ta dariya, da kuma abin da take karantawa a cikin sirri.. King Diamond ya matso kusa da mai littafin, idanunsa har yanzu suna kan Ayat dake ƙoƙarin ɓacewa cikin taron mutane.. Cikin murya mai natsuwa da iko ya yi tambaya.. "Shin kuna da littattafai waɗanda suka fi waɗannan inganci da kuma ƙarancin samu?" Jin wannan tambayar, mai littafin ya matso kusa da shi cikin girmamawa yana mamakin kwarjinin wannan baƙon mutumin. Ya tambaya, "Wane irin littattafai ne kake nema waɗanda ba a cika samu ba? Ko irin su Spring palace"... King Diamond ya ɗan yi shiru sannan ya ce, "Ko Spring Palace ko Winter Palace, ko ma mene ne... muddin dai ba a cika samun su ba. Kuma dole ne su kasance suna magana ne akan Jin King’s Requite..." Mai littafin ya jinjina kai, fuskarsa cike da fara'a ya ce. "Eeee... muna da littattafai akan Requite.".. Daga nan, mai littafin ya buɗe wani akwati na musamman ya ciro wani littafi mai taken.. "Prince Regent’s Requite" Ya miƙa wa King Diamond littafin yana ƙarin bayani.. "Babban jarumin wannan littafin ba Jin King ba ne, sarki ne shi ma.".. King Diamond ya karɓi littafin, ya bi rubutun dake jikin bangon littafin da kallo. Ta ke ya karanta sunan littafin a ransa.. "An Evilly Charming Emperor’s Requite" Ma'ana (Sakamakon Wani Mugun Sarki Mai Kwarjini da jan hankali..).. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya karanta ɗan taƙaitaccen bayanin farko da na ƙarshe dake cikin saƙon siyan littafin, yana ƙoƙarin fahimtar dalilin da ya sa Ayat take sha'awar irin waɗannan labaran. Ya ji wani irin murmushin gefen baki ya subuce masa, yanzu ya fara gano hanyar da zai bi ya shiga zuciyarta ta hanyar abubuwan da take so... King Diamond ya buɗe shafin farko na littafin, idanunsa suna yawo akan kalmomin da aka rubuta da fasaha. Ya furta a hankali, "Alƙawarin rayuwa?... haka sarakuna suke biyan sakamakon soyayya." Mai littafin ya gyaɗa kai cikin gamsuwa, ya ce, "Haka ne, ka gane ma'anar kenan.".. Wani sanyayyen "Ohhh!" ya fito daga bakin King Diamond, yayin da wani haske ya ratsa ƙwaƙwalwarsa.. "Ashe shi ya sa ba ta taɓa gaya min ba duk da lokacin da muka ɗau a wancan lokacin..." Ya fara fahimtar cewa Ayat tana ɓoye abin da yake ranta ne saboda kunya ko kuma girman abin da take ji... Mai littafin ya yi murmushi, ya ƙara da cewa, "Ai tana da kunya ne.... Ya kamata ka kasance mai nuna himma da ƙwazo wajen neman soyayyarta." Ya ƙarasa maganar yana ɗan dariya, yana ƙarfafa wa King Diamond gwiwa... King Diamond bai sake cewa uffan ba, ya tsaya kawai yana kallon mai littafin da wani kallo mai zurfi. Sannan ya sanya hannu cikin aljihunsa, ya ciro ƙarin wasu lu'u-lu'u masu tsada, ya miƙa wa mutumin a matsayin lada... Mutumin ya karɓi diamonds ɗin hannunsa na rawa, ya shiga murna da farin ciki maras iyaka, domin wannan abin ya fi ƙarfin duk wani littafi da ya taɓa sayarwa a rayuwarsa.. King Diamond ya juya ya bar wurin yana rungume da littafin An Evilly Charming Emperor’s Requite a ƙirjinsa. Yanzu ya sami makamin da zai yi amfani da shi wajen narkar da zuciyar Ayat.. zai koyi yadda ake zama sarki mai jan hankali wanda zai iya sadaukar da komai don masoyiyarsa.... Daga kasuwa kai tsaye masarautar ta nufa, a bakin gate ta tarar da master Ibrahim.. Ta ƙarasa tana dariya, ta gaishe shi.. Master ya ce, "ina ka je?..." Inuwa ya ce, "na shiga kasuwa ne.." Ibrahim ya sauƙe idonsa akan littafin da ke hannunsa ya karɓa yana faɗin "wannan fa? Kaima kana son karanta littafan almara ne...?" Inuwa ya jinjina kai tare da faɗin "Eeee! Master..." Ya jinjina kai sannan ya ba shi umarni da ya shiga... Yana hanyarsa ta koma wa sashensa sai kwatsam ya haɗu da wasu jami'an da ya gane su, sune masu tsokanarsa... Nan suka dakatar da shi suna faɗin "Ya Ɗan ƙwaƙur ya akayi ne..." Ɗaya daga ciki ya make mazauninsa tare da faɗin "Ɗan ƙwaƙur mai manyan ɗuwawu...burgeni suke saboda mata ne masu irin shape ɗin ɗuwawun nan..." Ɗaya ya ce, "ai tin da yana da ɗuwawu to bazai rasa nonuwa ba, mu ji su..." Ya kai hannu yana shirin taɓa su, Ayat tayi saurin ja da baya.. Tana shirin bin ta gefensu ta wuce suka riƙo ta, suna faɗin... "Muna son yau mu ji ya girman zarman lulunka yake, mun ji labarin kana neman mata..." Ɗaya ne ya kai hannunsa da sauri wurin gabanta, ya yi nasarar canke wa, da sauri Ayat ta ja da baya... Mutumin ya zaro ido cikin izgilanci yana faɗin "kaiii ya ban ji komai ba, Ɗan ƙwaƙur ko dai har yanzu kaciyar takan bata girma bane, kuma da haka kake biyan buƙatarka a wurin mata?...." Sauran ma hannu suka kai zasu taɓa su ji, kawai suka ji an riƙe hannunsu tare da murɗawa... Waiwayowan da zasu yi sai suka ga Master Ibrahim ne, haka gaba ɗaya ya riƙe hannunsu su ukun ya fara muɗewa, ihu suka shiga yi suna bashi haƙuri.. Shi kuwa sai da ya ji hannunsu yayi ƙaƙasss kafin ya sakar musu, ya juya zai kalli yanda Inuwa ya ke akan su bashi haƙuri sai ya ga bata nan, tin zuwan Ibrahim ta sulale ta gudu... Babu wanda yasan hanyar da ta bi, ta shiga private garden yanda hanyar sirrinta yake wurin koma wa part ɗinta... King Diamond yana tsaye a bayan masarauta, inda hasken dake jujjuya aljani ya zamar da shi toka yake ta walƙiya. Ya san idan ya yi ƙoƙarin shiga da jikinsa to rayuwarsa za ta shiga haɗari... Ya kalli ledar da yake ɗauke da Sugar-coated Haws da kuma sauran snacks ɗin da ya saya mata a kasuwa.. "Aayat..." ya raɗa sunanta a cikin zuciyarsa, yana amfani da igiyar jinin dake tsakaninsu.. Maimakon ya shiga, sai ya yi amfani da wata tsohuwar dabara.. Ya ajiye ledar kyaututtukan a ƙasa, sannan ya yi wasu kalaman tsafi waɗanda suka sanya kyautar ta zama tamkar shadow... Ledar ta zama Inuwa wanda ba'a iya ganin ainahin ledar, don haka hasken tsaron masarautar ba zai iya gano ta ba... Ya tura wa Ayat saƙon hoto a cikin zuciyarta na inda ya ajiye kyautar daidai jikin taga na ɗakinta... Ayat tana zaune a ɗakinta, tana ƙoƙarin buɗe littafinta na White Cat wanda ta saya a kasuwa, ga kuma hawaye a fuskarta na baƙin cikin abinda jami'an nan sukayi mata. Nan take ta ji wani irin bugun zuciya, sannan ƙamshin Sugar-coated Haws ya bugi hancinta, ƙamshin da ta ji a kasuwa lokacin da take son saye.. Ta ɗaga kai sai ta ga wani abu yana walƙiya a jikin tagarta. Ta matso kusa sai ta ga wani leda mai kyau dake lulluɓe da wani sanyayyen haske mai launin diamond...alamun an masa garkuwa ne.. Tana taɓa ledar, sai hasken ya ɓace, ledar ya zama na gaske a hannunta.... Tana buɗewa, sai ta ga duka abubuwan da take sha'awa a kasuwa.. Sugar-coated Haws masu zaƙi.. Cakes da Snacks masu daɗi.. Kuma a ƙasan ledar akwai wata ƴar takarda da aka rubuta.. "Sakamakon sarki ba ya karewa a baki kawai. Ki ji daɗin zaƙin da kika rasa a kasuwa.". Ayat ta daskare, gabanta ya faɗi. Ta san babu kowa a masarautar nan da ya ga lokacin da ta so sayan waɗannan abubuwan sai shi. Tsoro da wani irin shauƙi suka gauraye ta.. Ta zauna a gefen gadonta, tana kallon tarkacen zaƙi da snacks

Chapter 11 of 39