Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
irin zalle-zalle a cikin ruwan ɗumi... Uma Altine ta zaro ido, ta rasa inda zata sa kanta don kunya da mamaki, ta ce. "Haba Auta! Ki rufa min asiri don Allah. Ta ya zan cire miki nonuwa kuma?" Chingching ta turo baki, cikin shagwabar da ta zama jikinta ta ce... "Yooo, ba ke kike zuba min ruwan zafi a kansu ba?" Uma Altine ta kusan yin dariya amma ta dake, ta kalli yarinyar ta ce "Ina suke to? Ni ba na ganinsu ai." "Ni dai ki samu ki yi min wankan, kuma wallahi kika jiƙa min gashina sai na gaya wa Daddy!" Chingching ta faɗa tana nuna kanta da yatsa... Uma Altine ta yi ajiyar zuciya, "Kiyi hakuri, ba zan jiƙa miki ba." Ta ɗauki soso da sabulu don ta fara goge jikin ta, amma kafin soson ya taɓa fatarta, sai ta zabura ta ja numfashi tamkar ta ga dodo.. "Haaaaaa!!! Da soso zaki yi min? Cire min fatar jikina zaki yi? Saboda kinga ni ɗin mai kyau ce!" Uma Altine ta daure ta ce.. "Ki tsaya mana, ai soson zai cire miki dattin jiki ne." Wannan kalmar 'Datti' ita ce ta zama silar rugujewar nishaɗi.... Chingching ta zaro manyan idanunta, nan take hawaye suka fara zubo mata, muryarta ta fara fita da karfi tana maimaitawa cikin tashin hankali... "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..." Uma Altine ta gigice, ta san halin Chingching idan ta fara wannan kukan, duk fadar sai ta ruɗe.. "Na shiga uku! Dan Allah kiyi hakuri, ba haka nake nufi ba Auta!" Chingching ta ki sauraronta tana nuna kanta da yatsa tana maimaita tambayar cikin kuka mai taɓa zuciya. "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..." Ta miƙe tsaye daga cikin bathtub ɗin, jikinta duk ruwa da kumfar sabulu. Tana sanye da wani gajeren short nicket da wata ƙaramar vest mai raga-raga wadda ta bayyana kyawun fatarta mai sulɓi. Gashin kanta kuwa an tukwaikwiye shi da ribbons an tura shi sama domin kar ruwa ya taɓa shi, wanda hakan ya sa kanta ya yi girma tamkar na wata baturiyar yarinya.. Ta fito daga cikin ruwan tana kuka, tana neman inda zata nufa don kai ƙarar Uma Altine wurin Sarki, yayin da Uma Altine take binta tana rarrashi cikin fargaba. Chingching ta sauƙo stairs da gudu tana kuka, ma'aikatan da ke gyaran falo duk sun bi ta da kallo cikin mamaki, amma ba ta saurari kowa ba sai maimaita tambayarta take, "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?" Ta nufi babban gate ɗin sashenta, security bakin gate suka sha gabanta don hana ta fita a wannan yanayin, sanye da gajeren wando iya cinya da riga vest ta net wadda take nuna duk jikinta, ga gashin kanta da aka tukwaikwiye shi a tsakiya. Ganin an tare mata hanya, sai ta zube a ƙasa ta fara birgima tana ihu.. "Wayyo ku bar ni na je wurin Daddy na! Za su kashe ni, wayyo Allah za su kashe niiii!" Cikin tsoron kar a ce su ne suka taɓa ta, security suka buɗe mata gate ɗin da sauri. Ta miƙe ta fice tana gudu, yayin da Uma Altine ke biye da ita a baya tana huci... A daidai wannan lokacin ne motocin Gimbiya Maayah suka shigo masarautar daga makaranta.... Suna tsaka da tafiya a kan dogon kwaltar masarautar, sai ga Chingching ta tsallako da gudu tana kuka, "Ni ne mai datti?..." Direban Maayah ya daka wani mahaukacin burki wanda ya sa motar kusan tashi sama, har sai da Maayah ta bugi kanta da kujerar gaba... Security ɗin da ke bin Chingching duk sun daskare a wurin saboda tsoron ganin yadda motar ta kusan halaka ta. Amma ita Chingching ko a jikinta, ba ta tsaya ba kuma ba ta kalli motar ba, ta ci gaba da gudunta na neman Daddy, sanye da wannan gajeren kayan nata da jikinta duk a jiƙe... Maayah ta fito daga motar tana dafe kanta, ta kalli ƙanwarta cikin tsananin mamaki da fargaba, tana tunanin me ya faru da Autar tasu da har ta fito a wannan yanayin a gaban jami'an masarautar... "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?" Muryar Chingching ta karaɗe filin, tana kuka tana gudu... A cikin katafaren falon fadar King Nourdeen, iska ta yi tsit, sai ƙamshin turaren wuta na alfarma da yake tashi. Sarki yana zaune tare da babban aminin sa Tafida, da wasu fadawa guda biyu... Suna tsaka da tattaunawa sai kawai aka ji ihun Auta. Tun kafin fadawa su ankara, Chingching ta faɗo cikin fadar tana kuka da ƙarfi.. "Ni ne mai datti? Ni ne mai datti? Ni ne mai datti?..." King Nourdeen ya zabura ya miƙe tsaye, zuciyarsa ta buga ganin autarsa a wannan yanayin. Jikinta duk kumfar sabulu, sanye da wannan gajeren wando da net vest ɗin da ya bayyana surar jikinta duk da tana da shekaru kusan 17.. Chingching ba ta bi ta kan kowa ba, ta nufi wurin mahaifinta tana kuka.. "Daddy! Ka ga Uma Altine ko? Wai ni ce mai datti! Kuma har ruwan zafi ta zuba min a kan nonuwana, wai wanka za ta yi min!" Ta ci gaba da surutu cikin shagwaɓa, tana bayyana komai daki-daki ba tare da jin kunya ba, yayin da kumfar sabulun jikinta yake ɗiga a kan kafet ɗin fadar... Sarki ya shiga rarrashinta, a lokacin da Uma Altine ta bayyano tana sakin numfashi sosai domin ba ƙaramin gudu tayi ba, ta taho mata da dogon rigar sarauta har ƙasi... Ta matso tana ƙoƙarin rufe mata jiki.. Ita kuma sai faɗin, "Daddy wallahi sai an cire Uma Altine a aiki...".... ✨✨✨ Ganin ba lokacin tunani yasa ya nitse cikin ruwan ya kamo kunkuminta, ya ɗago ta sama.... Jikinta ya yi sanyi ga gashinta yanda ya bazu a saman ruwan kamar ganyen bishiya. Ya fito da ita har gaci, ya kaita karkashin bishiyar da tsuntsuwarta take, ya kwantar da ita a hankali a kan ciyayi... King Diamond ya durƙusa a gefenta yana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ruwan kogin ya ƙara wa kyau da sheƙi... Ya sanya dogayen yatsunsa masu sanyi a kan goshinta, ya fara karanta wasu maganganu na sirri tare da hura mata iska mai sanyaya zuciya a fuska.. A hankali, numfashin Ayat ya fara dawowa dai-dai.. Kirjinta ya fara sama da ƙasa yayin da take shirin buɗe idanunta waɗanda suka yi nauyi... Daidai lokacin da ta fara motsa idanunta don buɗe su, King Diamond ya fahimci cewa idan ta ganshi a yanzu za ta iya sake komawa suman. Saboda haka yana ganin ta buɗe ido ɗaya, sai ya ɓace kamar hayaƙi. Babu abin da ya rage a wurin sai ƙamshin turaren sa mai daɗi da sanyi wanda ya gauraye da iskar kogin... Ayat ta buɗe idanunta gaba ɗaya, ta miƙe zaune da sauri tana nishi sama-sama. Ta duba dama da hagun amma ba ta ga kowa ba. Sai dai tana tabbatar wa kanta cewa abin da ta gani ɗazu ba mafarki ba ne.. "Na ga wani mutum... sanye da fararen kaya da farin gashi," ta faɗa a hankali muryarta tana rawa. Ta kalli jikinta, ta ga har yanzu tana sanye da short nicket da bra, kuma tana kwance a busashen fili alhalin tana cikin ruwa lokacin da ta suma... "Waye ya fito da ni daga ruwa?" Ta fara waige-waige cikin tsoro, tana saurin rarrafa zuwa inda kayan maza da ta cire suke. Ta fara sanya kayan tsaro da sauri-sauri tana kuka, tana jin kamar idon wani yana kanta. Ba ta sani ba, King Diamond yana nan a tsaye a siffar aljan, yana kallon kowane motsi nata cikin murmushi... Cikin gaggawa Ayat ta fara maida kayan siffar Inuwa... Ta gyara gashin baki da sajen sannan ta naɗe uban gashinta a cikin rawanin maza.. King Diamond yana nan a tsaye a siffar aljan wadda ita ba za ta iya gani ba, yana kallon yadda take sauya kanta zuwa namiji cikin ƙwarewa. Ya ji mamaki da kuma sha'awar yadda kyakkyawar yarinyar nan take badda kama. Ya gane cewa lallai akwai babban dalili da ya sa take rayuwa cikin sirri, kuma hakan ya ƙara ba shi sha'awar bibiyar rayuwarta... Tana kammala shiri nan take ta zaro takobinta cikin zafin rai da takaicin karya mata alƙawarin da akayi na ganin fuskarta da ko mahaifinta ya kasa gani... Cikin tsawa ta fara magana tana faɗin, "Ko ma waye yake bibiyata nayi alƙawarin duk san da na sake haɗuwa da kai sai nayi gunduwa-gunduwa dakai, domin bazan taɓa yafe maka ba, a wancan lokacin ka zo har kayi faɗa dani kuma ban samu damar sararka ba, yanzu ma ka kuma na biyu to wallahi kada ka sake na sake ganinka na uku domin kashe ka zanyi..." King Diamond yana kallonta bai furta uffan ba, kasancewarsa sarkin Jinn bai taɓa jin son yayi dariya ba sai yanzu amma haka ya make daga bisani ya yi ɓacewarsa... Sai da ta gama barazanarta tana nunnuna takobinta kafin ta hau dokinta ta tafi.... Tana shigowa masarautar, ta ga komai lafiya, babu wani tashin hankali... Sai dai zuciyarta tana kan hasasho mutumin nan da dogon farin gashi... Ta kai dokinta wurin ajiyar dawakai, sannan ta nufi sashen jami'an tsaro... "Mai farin gaji ko? To ko me yellow gashi ne bazan sake jin tsoronsa ba... ​Tana tafiya tana waige-waige, sai ta ci karo da Mama Liyatu Uwar ɗakin Maayah... Mama Liyatu ta tsaya tana kallon Inuwa, domin tana sane da yadda Maayah take ruɗewa a kansa.. ​"Inuwa, daga ina kake haka jikinka duk ƙura?" Mama Liyatu ta tambaya tana binsa da kallo. Inuwa ya gyara muryarsa zuwa ta maza.. "Daga zagaye nake, ina duba tsaro ne." Ta wuce ta da sauri kafin a gano yanayin fuskarta. ​Tana ƙoƙarin wucewa ta sashen fadar sarki, sai ta jiyo muryar Chingching tana ihu... Tana nufar wurin, ta tadda Chingching tana birgima a gaban sarki, yayin da Uma Altine ke durƙushe tana ba da haƙuri.. ​"Daddy! Sai ka kore Uma Altine! Wai ni ce mai datti! Kuma har ruwan zafi ta zuba min a jikina!" ​Sarki yana zaune yana yana murmushin ciki domin bai bayyana a fuskarsa ba, yana lallashin autarsa... "To yi haƙuri Auta, gobe zan sa a siyo miki lallausan soso daga ƙasar waje wanda ba zai cire miki fata ba." ​Ayat ta tsaya daga nesa tana kallon wannan farincikin, wani rauni ya ziyarce ta. Ta ji tana son cire wannan rawanin ta ruga ta rungume ƙanwarta da mahaifinta, amma asirin dake kanta ya fi ƙarfin hakan... Tana tsaye can nesa da babban falon Sarki, tana kallon yadda Chingching take ta rigima tamkar za ta tada fadar. Uma Altine tana durƙushe tana ba da haƙuri, yayin da Sarki yake ta faman rarrashin Autar tasa. ​Kwatsam, sai idon Chingching ya sauƙa a kan Inuwa. Ta ɗaga hannu tana nuna shi, fuskarta ta washe da murmushin shagwaɓa... Fadawan sarki ganin inda yatsan gimbiya ya nuna, suka nufi Inuwa da gudu.. Kafin Inuwa ya ankara, fadawa biyu sun cafko shi, suka yi sama da shi! ​Ayat ta zazzaro ido, zuciyarta na bugawa don tsoron kada asirinta ya tonu ko kuma laifi ta yi. Ta damƙe wuyan fadawan sosai don kada ta faɗi, har aka shiga da ita gaban Sarki aka dire ta a ƙasa... Saboda yadda aka sake ta da ƙarfi, sai da ta zauna da mazaunanta a kan kafet ɗin falon. ​Chingching ta kalli Inuwa, ta turo baki ta ce, "Ni... wannan ne zai kai ni part ɗina!" ​Sarki ya jinjina kai, ko da yake yana mamakin yadda autar tasa ta zaɓi wannan matashin sojan, sai ya ce, "Ƙaramin jarumi, tashi ka raka ta part ɗinta." ​Uma Altine ta yi maza ta miƙe don su tafi, amma Chingching ta karkaɗa kai, ta haɗe hannaye a ƙirji.. "Ni sai dai ya goye ni! Ba zan je da ƙafata ba." ​Tafida dake zaune yana kallon ikon Allah ya ce "To ai Auta da mota za a kai ki ko kuma doki."... "Ni goyo nake so!" Tana bubbuga ƙafa cikin sakalci.. Sarki ya kalli Altine ya ce, "Altine, goye ta ku tafi." ​Nan ma Chingching ta fara buga ƙafa a ƙasa "Ni! Na yi faɗa da Uma Altine, ba za ta goye ni ba! Ba wanda zai goye ni sai kyakkyawan jarumin nan!".. ​Sarki bai ji daɗin hakan ba. A matsayinsa na mai kishin ƴaƴansa, ba ya son namiji ya riƙa taɓa su ko su riƙa mu'amala da maza amma ganin yadda Chingching ta nace kuma ba ya son ɓata mata rai, sai ya gyada wa Inuwa kai alamar ya ɗauke ta. ​Ita kuwa Ayat, wani farinciki ne ya ziyarci zuciyarta. Ta daɗe ba ta riƙe ƙanwarta ba saboda shigar badda kamar da take yi. Ta duƙa a hankali, Chingching ta daka tsalle ta hau bayanta, ta ƙanƙame wuyanta.... Tana tura baki ta ce, "Dan nace maka kyakkyawa kar kayi tunanin ka fini kyau too..." Murmushi kawai Inuwa yayi.. Ya miƙe da ita da ƙyar, domin duk da ƙarancin shekarun Chingching, tana da ɗan nauyi, sannan ya fara takawa zuwa wajen fada, Uma Altine da sauran bayi suna biye da su a baya... ​Suna tafe a kan dogon kwaltar masarauta, iska mai sanyi tana kaɗawa. Chingching ta saki jiki sosai a bayan Inuwa, ta ɗora kanta a kafaɗarsa.. ​"Wai kai meye sunanka?" Ta tambaya tana wasa da kwalliyar jikin rigar sojan... ​Inuwa ya ɗan yi murmushi, ya rage sautin muryarsa don kada sauran bayin su ji yadda muryarsa take zama ta mace idan ya yi magana mai tsayi, ya ce.. "Sunana Inuwa, ya ke gimbiya." ​Chingching ta yi dariya, "Inuwa? Suna kamar inuwar bishiya. Amma ka san me? Jikinka yana da taushi, ba ka da tauri irin na sauran sojoji. Kuma kana ƙamshi mai daɗi, ba irin na Uma Altine mai ƙamshin sabulun wanka ba.".. ​Inuwa ya ɗan zaro ido, ya ce.. "Haka ne gimbiya, ai sojoji ma suna wanka." ​Chingching ta ƙara matse shi, ta ce, "Inuwa, me ya sa kake da kyau haka? Idanunka manya ne kamar na Aunty Ayat. Ka san Aunty Ayat kuwa? Ita ma tana da kyau sosai, amma kullum tana kulle a ɗaki." ​Wani ƙwallar farinciki ya cika idon Ayat, ta amsa.. "Na san ta gimbiya. Ita ma tana sonki sosai." ​Chingching ta bushe da dariya, "To idan na sake rigima, zan sa Daddy ya ce kai ne za ka riƙa yi min wanka, tunda kai ba ka cire fatar mutum da soso." ​Inuwa ya kusa yin tuntuɓe saboda dariya, ya ce, "A'a gimbiya, wanka kam sai dai Uma Altine." ​Haka suka riƙa yin hira cikin nishaɗi har suka isa part ɗin gimbiya, kowa yana mamakin yadda wannan jarumin ya saba da Auta cikin lokaci ƙanƙani.... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 8️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan Inuwa ya sauƙe Chingching a part ɗinta, ya fara takawa cikin sanyin jiki yana shirin komawa tasa muhallin. Zuciyarsa tana cike da farincikin hirar da suka yi da kanwarsa.. ​Kwatsam yana shirin shiga wata kusurwa sai ya ji an rufe masa fuska da wani baƙin mayafi mai kauri. Kafin ya yi yunkurin kwata, wasu jami’an tsaro guda biyu masu ƙarfi suka cafko shi, suka fara jansa da karfi. Ba su ba shi damar yin magana ba, suka jefa shi cikin wata mota dake fake a gefe, suka tada motar da gudu suka nufi part ɗin Gimbiya Maayah.... ​Motar ta tsaya a harabar katafaren sashen Maayah. Jami’an suka fito da Inuwa, yana ta faman kokawa yana son ya ɓalle ya gudu, amma riƙon da suka yi masa na maza ne. Saboda yadda suka ji ba shi da nauyi sosai, ɗaya daga cikinsu sai kawai ya yi masa ɗaukan kafaɗa, ya saɓo shi tamkar buhun shinkafa, suka nufi cikin falon gimbiyar. ​Suna shiga suka dire shi a tsakiyar katafaren falon dake shimfide da kafet mai tsada... ​Maayah tana zaune a kan wata Plate Sofa kamar katifa a ƙasi tana sanye da riga ta alfarma wadda ta bayyana kyan fatarta. A gabanta akwai wani katafaren tray cike da yankakken kayan fruits masu sanyi, tana ci a nutse tamkar ba ta san abin da ke gefen ta ba.. ​Ba tare da ta kalli inda suke ba, ta daga dogayen yatsunta ta yi musu nuni da su fita. Nan take jami’an da sauran ma’aikatan mata dake falon suka fice cikin hanzari, suka bar Inuwa tsaye a tsakiyar falon cikin ruɗani. ​Daga nan ne aka cire wa Inuwa baƙin mayafi dake fuskarsa. Da farko ya rintse ido saboda hasken fitilun dake walwali a falon, yana buɗe su sai ya yi ido hudu da Maayah. Mamaki da fargaba suka mamaye shi. ​Maayah ta ajiye ƙaramin wuƙar dake hannunta, ta ƙura wa Inuwa idanu. Wani irin kallo take yi masa, kallo mai cike da nuna isa da kuma wani ɓoyayyen saƙo dake nuna sha'awa da burgewa.... Idanun Maayah sun yi wani irin sheƙi, gata kyakkyawa ajin farko.. ​Inuwa ya ji jikinsa ya fara sanyi. A matsayinsa na mace, ta san ma'anar wannan kallon. Ta san cewa inda asalin namiji ne babu abin da zai hana sha'awarsa ta tashi a wannan lokacin saboda yadda Maayah ta baje kyan surarta a gabansa cikin kissa da kisisina... ​"Inuwa..." Maayah ta kira sunansa cikin wata irin murya mai sanyi da take ratsa jijiya. "Ka ga yadda ka yi nasarar sa ni tunani tun daga ranar da idona ya fara ganinka? Meye sirrinka? Me kake boyewa a karkashin wannan rawanin naka?" ​Inuwa ya sunkuyar da kai kasa, yana tunanin yadda zai fita daga wannan tarkon na Gimbiya Maayah ba tare da asirinsa ya tonu ba. Maayah ta tashi daga kan katifar ta a hankali, tana taku ɗaya-ɗaya tamkar kyanwar da ta ga ɓera... Rigar jikinta tana jan ƙasa, ƙamshin turarenta na Oud mai tsada ya mamaye hancin Inuwa. Ta zo daidai gabansa, ta tsaya tana kallon kwayar idonsa, kafin ta fara zagaye shi kamar yadda zaki yake zagaye abincinsa... Ta sanya hannunta ɗaya ta fara shafa kafaɗarsa tana gangarawa zuwa hannunsa. Muryarta na fita ƙasa-ƙasa, tana raɗa masa a kunne.. "Inuwa... na yi bincike a kan duk sojojin masarautar nan, amma ban ga kamaninka ba. Ba ka da ƙasusuwa irin na maza sojoji. Ka yi fita daga daban, kuma hakan ne ya sa zuciyata ta kasa nutsuwa." Ita kuwa duk wannan shashshafa da kalaman Maayah ba su motsa mata komai ba face takaici da haushin yadda ƴar uwarta take nuna rashin kamun kai. Ta ɗaure fuskarta cikin yanayi na gatsine, tana jujjuyar da manyan idanunta tana kallon silin ɗin ɗakin. A ranta tana cewa, "Wannan mahaukaciyar me take nufi ne? Shin ba ta da sauran abin yi ne sai bibiyar sojoji?" Maayah ta kai hannunta tana son ta shafi gefen fuskarsa, Inuwa ya kauce da sauri yana harararta.. Maayah ba ta fasa ba, ta sake zagayawa ta bayansa, ta tura kanta a tsakanin kafaɗunsa, ta rungumo shi ta baya tana ƙoƙarin jin bugun zuciyarsa... "Me kake gudu Inuwa? Izza kake nuna min ko kuwa tsoron matsayina kake ji? Idan ka karɓi soyayyata, zan mayar da kai babban kwamandan da kowa zai rurrusuna masa a ƙasar nan," tana goga fuskarta a bayan rigarsa. Inuwa ya ja wani uban tsaki a cikin ransa, wanda ya kusa fitowa fili. Ya fara jin ƙyamar yadda Maayah take ƙanƙame shi. Ya yi amfani da dabarar maza sojoji, ya juyo da ƙarfi ya raba jikinsa da nata, ya matsa baya taku biyu yana huci.. Cikin muryarsa ta maza wadda ya riga ya koyi kwaikwayonta, ya ce.. "Gimbiya Maayah! Na zo nan ne don hidimar tsaro, ba don wasan kwaikwayo na soyayya ba. Ni talaka ne, ke kuma gimbiya ce. Bai kamata ki ɓata mutuncinki a kaina ba. Kuma idan har kika sake sanya a kamo ni ta wannan hanyar, zan kai ƙararki gaban mai Martaba Sarki, duk abin da zai faru ya faru!" Maayah ta daskare a wurin, ta zaro ido tana kallon Inuwa. Ba ta taɓa tunanin akwai wani namiji a duniya da zai ƙi wannan tayin nata ba. Maimakon ta ji tsoron barazanar sarki, sai kawai ta ji Inuwa ya ƙara mata kyau da kwarjini a idonta. Ta ciza laɓe, tana murmushin mugunta... "To ka je ka faɗa wa Sarkin! Amma ka sani, duk inda ka shiga a masarautar nan, idona yana kanka. Ba za ka taɓa tsira daga tarkona ba har sai na mallaki abin da nake so a tare da kai." Inuwa bai sake tankawa ba, ya juya cikin fushi ya nufi ƙofa, ya buɗe ta da ƙarfi ya fice, ya bar Maayah a tsaye tana kallon inuwarsa tana shafa wurin da ya taɓa, tana jin wani irin shauƙi daban. Ya fara takawa cikin sauri yana ficewa daga sashenta, yana muzurai shi kaɗai ƙasa-ƙasa... "Banza! Mahaukaciya! Jaka kawai!" ya furta tare da jan wani dogon tsaki. "Wato ita a tunaninta kowa ma namiji ne ko? Ta rasa wanda za ta bi sai ni? Yarinya ba ta da sauran aiki sai lalata da ma'aikata? Allah ya kyauta!" Haka ya riƙa surutai yana gunguni har ya ɓace a cikin duhun dake tsakanin gine-ginen masarautar, ya nufi tasa part don ya cire wannan kayan sojan da yake ji sun yi masa nauyi saboda haushi. A can cikin falo kuwa, Mama Liyatu tana laɓe a bayan labule tun ɗazu tana kallon duk abin da yake faruwa. Bayan Inuwa ya fice ta fito a hankali tana takawa zuwa inda Maayah take a tsaye, tana kallon ƙofa tamkar gunki... Mama Liyatu ta ga yadda Maayah ta zama wata iri, fuskarta na sheƙi, kuma tana shafa hannunta da Inuwa ya taɓa.. "Gimbiyata," Mama Liyatu ta kira sunanta cikin muryar tsoro. "Wannan yaron da kike bi... shin kin tabbata namiji ne na ƙwarai? Na ga kyan fuskarsa ya wuce na namiji, sannan yadda kika rungume shi ɗazu bai nuna wani yanayi na namiji ba. Meye sirrin dake tattare da shi?" Maayah ta juyo ta kalli Mama Liyatu, wani murmushin mugunta na nan a kwance a fuskarta. Ta koma ta zauna a kan kujera, ta ɗauki koren apple ta gutsura.. "Mama Liyatu, shi ya sa nake son sa. Domin ya banbanta da kowa. Sannan ya nuna mjn ba ya buƙatar soyayyata. Wannan shi ne babban kalubalen da nake so. Amma ki sani, koda mace ne shi a siffar namiji, sai na mallaki zuciyarsa, balle kuma ina da yakinin cewa jarumi ne mai jinin sarauta a jikinsa.".. Mama Liyatu ta girgiza kai, "Amma Gimbiya, idan Sarki ya ji labarin nan fa? Kin san yadda yake kishinku." Maayah ta yi wata 'yar dariya mai sauti. "Sarki yana can yana fafutukar yadda zai kare masarautarsa daga barazanar Pavilion, ba shi da lokacin binciken wanda nake so. Ke dai kawai ki sa ido a kansa, duk inda ya sanya ƙafa ki sanar da ni." ✨✨✨ A ɗayan ɓangaren kuwa, Ayat ta isa sashenta. Ta banka ƙofa ta shiga, ta cire rawanin kanta ta wurgar a kan gado. Ta kalli kanta a madubi, gashin kanta ya bazu a kafaɗarta, idanunta sun cika da ƙwallar takaici... "Wace irin rayuwa nake ciki?" ta tambayi kanta... "Ina tsaka-tsakiyar yaƙi da kaina.." Ta shige banɗaki don yin wanka.. Bayan ta kammala wanka ta cire duk wata siffa ta Inuwa, ta saka lallausan leshi mai kyan gaske wanda ya dace da jikinta. Ta sauko ƙasa zuwa babban falonta tana takawa a hankali, fuskarta a rufe.. Tana isa falon, sai ta tadda ma’aikatanta, karkashin jagorancin Saratu, suna tsaye jere tamkar wadanda suke jiran sako daga sama. Fuskar kowacce dauke da tambaya da kuma damuwa. Saratu tana kallonta, sannan ta yi gyaran murya ta ce. "Gimbiya, me ya sa yanzu kika koyi wannan halin ne? Tun safe ba kya fitowa sai dare, anya lafiya kuwa? Abun ya yi yawa ai..." Ayat ta ji wani irin haushi ya taso mata, domin ranta ya riga ya ɓaci da rigimar Maayah. Ta tsaya cak, ta kalli

Chapter 6 of 39