Chief Onyx ya zo nan domin idan ya zo, gidan sarautar zai iya zama tamkar gidan kallo, kowa zai so ya ga kwarjinin sarkin Pavilion, wanda hakan zai jawo tambayoyi marasa iyaka...
"Ba zan bari su ganshi a nan ba," Sarki ya raɗa wa kansa yana goge gumin goshinsa. "Idan ya zo nan, asirina zai ruguje a gaban ƴaƴana."...
An bar Gimbiya Zayana a tsaye, jikinta ya yi sanyi. Ta rasa gane dalilin da ya sa mahaifinta yake nuna wata irin fargaba a fili game da mutanen nan. ta juyo, tana takawa a hankali zuwa sashenta, kanta cike da tambayoyin da babu mai ba ta amsarsu.
Tana tafiya tana nazarin wasiƙar da ta ga an bayar, me ya sa sarki ya rubuta masa cewa ba sai ya zo ba? Shin me sarki yake tsoron zai faru idan kowa ya ga fuskar sarkin Pavilion?...
A can ɓangaren Gimbiya Chingching, labarin dake girgiza masarautar bai ma shigo cikin kunnenta ba. Tana zaune a kan lallausar sofa, idanunta sun ƙafe a kan TV tana kallon katun (ƴan gwaigwai), tana ta dariya tana turo baki idan aka daki ɗaya...
Wata ma'aikaciya dake gyaran falon, tana goge wani tebur kusa da ita, ta kasa jurewa sai da ta yi magana..
"Gimbiya Chingching, shin ba ki da labarin rundunar Pavilion Kingdom sun zo wannan masarautar ne?"
Chingching ba ta ko juyo ba, idonta yana kan TV, ta ce cikin shagwaɓa..
"Su waye kuma pabiliyooo...?"
Ma'aikaciyar ta ja numfashi, ganin cewa wannan yarinyar ba ta ma san me duniya take ciki ba. Ga kowa Pavilion tsoro ne da fargaba, amma ga Chingching, suna ne kawai mai wahalar faɗi. Ma'aikaciyar ta girgiza kai kawai ta ci gaba da aikinta, ta ga gara ma ta yi shiru...
Ganin ma'aikaciyar ta yi shiru, Chingching ta ɗan harare ta tana turo baki..
"Kumaaaa za ki dame ni! Yooo ni ina ruwana da wani wani wani mene sunan? Uhmmm ni ki ƙyale ni. Ni yunwa ma nake ji... Dubi ma yadda kike goge nan, kin tare min TV."
Chingching ta koma ta kwanta tana rungume da toy🧸 ɗinta.. tana jira a gama shirinta na abincin rana, yayin da duk gimbiyoyin gidan suke cikin zulumi, ita nata damuwar ba ta wuce abinci da ƴan gwaigwai ba....
Aayat tana can a nata sashen, tana ta zirga-zirga tamkar wadda aka yi wa bushara da saƙon mutuwa. Yau ta kasance rana ta musamman, domin kwata-kwata ba ta yi shigar Inuwa ba. Tana sanye da doguwar riga ta sarauta, gashinta da fuska a rufe ga farin glass akan dara-daran idanuwanta, tana jiran jin ko sarki zai ƙira duk gimbiyoyin don yi musu bayanin abin da yake faruwa...
Duk sanda ta ji motsin takun tafiya a waje, sai gabanta ya faɗi, tana tsammanin bafade ne aka turo ya ƙira su. Amma shiru, har dare ya raba sarki bai nemi kowa ba. Wannan shirun ya fi kowane hayaniya ban tsoro a wurinta, domin tana jin cewa mahaifinta yana ƙoƙarin rufe wani babban rami ne kafin kowa ya gani...
A ɗayan ɓangaren kuwa, Gimbiya Maayah tana can kwance a kan katafaren gadonta, fuskarta a murtuke ba wai don zafin ciwo kaɗai ba, har da takaicin rashin samun damar fita ta ga abin da idonta yake son gani... Faɗuwar da ta yi a kan treadmill ta bar mata raɗaɗi a ƙunkuminta da bayanta wanda ya sanya koda juyawa ta kasa yi..
Mama Liyatu tana zaune a gefenta, tana dunduma mata baya da tsumman da aka tsoma a ruwan zafi tana lallashi...
"Yi haƙuri gimbiyata,"
Mama Liyatu ta faɗa cikin sanyin murya..
"Gobe idan Allah ya kai mu likita zai zo ya duba ki, zai baki maganin da zai sa ki miƙe nan take."..
Maayah ta cije laɓe, tana kife da kanta akan gadon domin kibda ciki tayi...
Duk wani motsi ya tsaya a masarautar.... Ma'aikata suna tafiya ne a cikin sanɗa gudun kada su tayar da fushin sarki...
Domin a wannan ranar har zuwa gobe komai zai iya faru idan wani ya kuskura ya aiwatar da laifi wa sarki, domin a kansa za'a huce takaici...
Iskar daren tana kaɗawa da wani irin sanyi daban, mai ɗauke da ƙamshin dawakan Pavilion da wani irin ƙamshin hayaƙin motocinsu waɗanda suka riga suka bar birnin, amma kwarjinin motocin yana nan maƙale a zukatan mutane..
Kowa yana jiran gobe....
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
⚠️ SANARWA⚠️
Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya.
⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya:
kwafa
gyara
sauya
ko amfani da wani sashe na wannan labari
ba tare da izini na kai tsaye ba.
Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa..
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 1️⃣0️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Ayat ta tashi da safe tana jin wani irin nauyi a zuciyarta. Ganin ba za ta iya zama a matsayin gimbiya tana jiran abin da ba ta sani ba, ta koma asalin shigarta ta Inuwa. Ta ɗaura damararta, ta sanya kayan sojan masarauta, sannan ta fito don ganin abin da yake faruwa a tsakar gari...
Tana isa tsakiyar masarautar sai ta ci karo da Master Ibrahim. Ibrahim mutum ne mai zafi da kishin aiki, kuma shi ne yake lura da yawancin motsin ma'aikatan tsaron fada.
Ibrahim ya tsaya cak, ya zuba wa Inuwa idanu, yana nazarinsa kafin ya nisa ya ce
"Inuwa! Ina ka shiga ne kwana biyu? Ba na ganinka a wuraren aikinka, sannan ba ka bin tsarin yadda aka tsara maka hidima. Ko ka manta dokar masarautar nan ne?"
Inuwa yana sosa wuya cikin nuna alamar ba ya jin daɗi, ko da yake a ransa takaici ne ya cika shi
"Gafara nake nema Master. Kwana biyu bana jin daɗin jikina ne, shi ya sa ban fito ba."
Ibrahim ya jinjina kai, fuskarsa ba alamun wasa ya ce,
"Toh, Allah ya ƙara sauƙi. Amma yanzu tunda Allah ya haɗa mu, akwai inda nake son fita a gari. Za mu tafi tare ne don ka taya ni wasu ayyuka."
Inuwa bai yi gardama ba domin ya san idan ya ƙi, Ibrahim zai iya bincika dalilinsa wanda zai iya janyo masa matsala.
"Ba damuwa Master, mu tafi," ya faɗa a takaice...
Maimakon su ɗauki dawakai ko ababen hawa, Ibrahim ya yanke shawarar su taka da ƙafa. Suna tafiya suna ratsa lungu da saƙo na birnin Alhamra. Wannan tafiyar ta bawa Inuwa damar ganin yadda talakawan gari suke magana ƙasa-ƙasa game da motocin Pavilion da suka gani jiya...
Ibrahim ma ya yi shiru yana kallon gari, shima kansa kwanan nan bai fito ba, don haka yake son shaƙar iskar gari don jin abin da mutane ke faɗa...
Suna tafiya gefen titi, Ibrahim yana ta jansa da hira yana bashi labarai, amma hankalin Inuwa yana can nesa. Tana tunanin halin da mahaifinta yake ciki da kuma tsoron da Pavilion ya galla wa masarautarsu...
Saboda zurfin tunani, Ayat ba ta san lokacin da kafafunta suka soma raba ta da gefen titin ba, ta haura har tsakiyar titi ba tare da ta sani ba. Kwatsam! Sai wata mota kirar Jeep ta taho da gudu tana kokarin ritsa ta.
Ibrahim ya zaro ido ganin motar zata banke Inuwa. Cikin zafin nama da kwarewa irin ta jarumai, ya sa hannu ya janyo Inuwa da karfin gaske don ceton ransa. Ibrahim ya zata zai ji nauyin jikin namiji amma abin mamaki sai ya ji kamar iska ya janyo.
Hakan ya sa Ibrahim yin baya saboda karfin janyon da ya yi, shi kuma Inuwa ya faɗa kai tsaye kan faffadan kirjinsa. Suka tafi tare suka faɗi a kasa a tsakiyar titin, yayin da sauran mutane suka daskare suna kallonsu...
A nan ne duniyar Ayat ta tsaya cak. Ta faɗa daidai kan fuskar Ibrahim, wanda hakan ya sanya lebbansu suka haɗe wuri ɗaya. Wani irin numfashi ne yake fita daga juna, bugun zuciyar Ayat ya tsananta har tana jin sautin na Ibrahim a jikinta.
Sun ɗauki wasu dakikoki a haka, kowa ya kasa motsi. Ibrahim ya zuba mata ido, yana jin wani irin sanyi da laushin da bai taba ji ba a jikin namiji. Ayat kuwa, manyan idanunta sun cika da firgici tana kallon kwayar idon Ibrahim wanda shima ya ruɗe...
Da sauri Ayat ta dawo cikin hayyacinta, ta zabura ta tashi daga kansa tana sakin numfashi a hargitse...
Abu na farko da ta yi shi ne sa hannu ta taɓa lebbanta, sannan ta riƙa taɓa fuskarta tana duba ko gemun da sajen dake fuskarta sun cire saboda gogayyar da suka yi...
Taji su nan normal, sai ta sauƙe wani nauyayyen ajiyar zuciya, duk da cewa jikinta har yanzu ɓari yake yi...
Ibrahim shima ya miƙe a hankali yana kakkabe kayansa, amma hannunsa ɗaya yana kan lebbansa. Ya kura wa Inuwa ido cikin wani irin mamaki da shakku. A ransa yana faɗin
"Ta ya namiji zai kasance da leɓe mai laushi haka? Me ya sa zuciyata ta buga da karfi lokacin da jikinmu ya hade?"
Ya so ya yi magana, amma makogwaronsa ya bushe... Shi kuma Inuwa ya ƙi yarda su haɗa ido, ya juya baya yana nishin kuncin abin da ya faru.
Sun ci gaba da tafiya ɗaf-ɗaf da juna, amma babu wanda ya iya kallon ɗan uwansa, ballantana a yi magana. Ibrahim ya lura cewa tun daga wannan faɗuwar Inuwa ya ƙara nuna wata irin natsuwa da nauyin jiki.... Don ya kawar da tunanin da yake addabarsa, sai ya riƙa kallon gefe da gefe yana son ya tabbatar wa kansa cewa Inuwa namiji ne kamar kowa...
Suna shiga tsakiyar babban kasuwar birnin, nan take yanayin wurin ya canja.. Fitowar Inuwa a fili ba tare da kowace kariya ba ya janyo hankalin kowa. Duk inda suka ɗora ƙafa, sai an dakata ana kallonsu..
Kyawun fuskar Inuwa duk da gemun da ya sanya, ya kasance wani irin kyan dake fitar da haske mai ban tsoro.
'Yan mata dake gefen shaguna da waɗanda suke ciniki duk suka saki baki suna kallo. Maganganu suka fara tashi ta kowane sashe..
"Wow! Dubi wani handsome guy! Gaskiya ya haɗu," wata yarinya ta faɗa tana dafe ƙirji..
"Ya Allah! Wani irin kyau ne haka? Anya wannan mutum ne na duniya?"
Wata kuma ta tambayi ƙawarta cikin mamaki...
Wata tsohuwa dake sayar da kayan marmari ta gyara gilasinta,
"Wannan kam aljani ne! Domin kaf birnin nan da gefenta, ban taɓa ganin wanda yake da kyan wannan yaron ba. Dubi fatarsa tamkar madara."
Duk waɗannan yabo da kirari suna shiga kunnen Inuwa, maimakon ta ji daɗi sai ta ƙara jin haushi da matsuwa... Tana jin tamkar kowa yana leƙen asirinta ne ta cikin fatarta. Ta ƙara saurin taku, tana son ta ɓace wa idanun mutane..
Ibrahim kuwa ganin yadda Inuwa yake cin magani yana harara, sai abin ya ba shi dariya. Ya fara ƙunshe dariyar dake neman ƙwace masa, ganin yadda kowa ya rikice a kan ma'aikacinsa...
"Inuwa, ka ga yadda ka kusa janyo mana gobara a kasuwa? Ko mazan ma kallonka suke,"
Ibrahim ya faɗa ƙasa-ƙasa yana ɗan taɓa kafaɗarsa cikin sigar tsokana...
Inuwa ya juyo ya harare shi da manyan idanunsa..
"Master, don Allah mu koma masarauta. Na gaji, sannan ban son wannan kallon da ake mana."
Ibrahim ya yi murmushi, ya fahimci Inuwa baya son hayaniya. "To shikenan, mu zagaya ta wannan lungun mu koma fada, kafin wata ta zo ta sace ka ta gudu da kai."
Ibrahim ya dube shi, ganin yadda Inuwa yake faman basarwa kamar ba shi ne ya kusan cinye zuciyarsa ɗazu ba. Ibrahim ya kasa jurewa, ya ce..
"Wai Inuwa, me ya sa ba ka yi min magana ba tun bayan faɗuwar nan? Ko dai har yanzu kana jin tsoron motar ne?"
Inuwa ya ɗan tsaya, ya gyara rawaninsa da ya ɗan karkace ba tare da ta kalle shi ba ta ce...
"Ba komai Master. Kawai dai ina tunanin yanda Sarki yaƙi fitowa yau tin jiya, kuma kasuwar nan akwai hayaniya da yawa."..
Haka suka ƙaraso ƙofar masarauta, kowa na riƙe da abin da yake ji a ransa...
Suna isowa tsakiyar fada, sai wani bafade ya tarye su da sauri...
"Master Ibrahim! Sarki yana neman ka a yanzu haka a babban ɗakin taro."
Ibrahim ya kalli Inuwa, ya gyara tsayuwar takobinsa.
"Ka ga ko? Abin da kake fargaba ya zo. Mu je mu ji me Zaki yake tafe da shi."..
Inuwa cikin tsoro ya ja da baya yana zaro ido ya ce,
"A'a a'ahh iya kai kaɗai ake nema, kuma kumaa cikina ciwo yake..."
Wani jami'in da ke gefe yana dariya ya ce,
"Kodai period zaka yi ne Ɗan ƙwaƙur?..."
Ibrahim ya kalle shi tare da faɗin
"Kai, bana son iskanci faa..."
Sannan ya kalli Inuwa ya ce, "shi ke nan, ka je ka huta kawai..."
Inuwa ya gallawa wanda yayi mishi maganar nan harara haɗe da gatsine....
✨✨✨
Tun lokacin da Ayat ta taka kafarta a wajen masarauta a matsayin Inuwa, wani daddaɗen ƙamshi ya tashi ya ratsa sararin samaniya har zuwa can zurfin duniyar aljanu ta Power Pool. King Diamond dake zaune a kan karagar mulkinsa, ya ji wani irin bugawa a zuciyarsa. Bai buƙaci a faɗa masa ba, ya san Ayat ɗinsa ce take yawo a cikin gari...
Ta hanyar idonsa na tsari, ya riƙa kallon kowane takun da Ayat take yi tare da Ibrahim. Lokacin da motar ta kusan bugan Ayat, Ibrahim ya janyo ta suka faɗi har lebbansu suka haɗe, King Diamond ya daka wani uban tsalle idanunsa suka canza launi zuwa jawur tamkar wuta...
Wani azababben kishi ne ya turnuke shi...
"Aayat ɗina ce!" ya furta cikin murya mai rawar gaske dake ɗauke da fushi..
"Babu wani ɗan Adam da ya isa ya taɓa ta, balle ya ji yanayin daɗin da aka tanada domina."
Cikin kiftawar ido, King Diamond ya bayyana a kofar masarautar Alhamra ta waje. Farin dogon gashinsa dake tafe har kugu yana kaɗawa a cikin iska, idanunsa kuma suna fitar da wani irin kwarjini na ban tsoro. Ya nufo kofar masarautar cikin tafiyar izza da nuna iko, yana kallon Inuwa da Ibrahim dake kokarin bacewa cikin gida...
Abin al'ajabi, duk da tsayuwar sa a fili, babu wani soja ko mai gadi da yake iya ganinsa. Suna ta faman zirga-zirgarsu tamkar iska ce kawai take wucewa.
King Diamond ya yunkura zai ratsa ta tsakiyar gate din masarautar don ya biyo Ayat. Kwatsam! Sai wani irin haske mai launin gwal ya fito daga jikin bangon masarautar ya bugi kirjinsa da wani irin ƙarfi...
Sarkin aljanun ya tafi sama tamkar an harba kibiya, ya yi ta jujjuyawa a cikin iska yana neman hanyar daidaitawa. Sai da ya dage sannan ya tsaya daram a cikin iska yana kallon masarautar daga sama, fuskarsa ɗauke da mamaki...
A nan ne ya fahimci cewa masarautar Alhamra ba masarauta bace kawai ta mutane. Akwai wani tsari na musamman da aka yi mata, shinge ne na ruhaniya wanda yake toshe hanyar kowane aljani ko shaidanin abu. Wannan hasken da ya buge shi, wani irin makami ne dake iya ƙona fatar aljani ya mayar da ita toka a cikin daƙiƙa kaɗan...
Duk da azabar zafin da yake ji a jikinsa, bai cire idonsa daga kan Ayat ba...
"Wannan shingen ba zai taɓa rabani da ke ba Ayat,"
ya raɗa a cikin zuciyarsa.
"Zan nemo hanyar da zan shigo, ko da kuwa hakan zai kai ni ga rasa dukkan ikona."
Ayat ta miƙi hanyar masarautar tana shirin tafiya ciki, kwatsam sai ta ji wani irin sanyi mai ratsa jiki ya ziyarce ta, sanyin da bai dace da yanayin zafin rana na lokacin ba. Wani irin yanayi ne na daban wanda ya sanya kowace gashi na jikinta tashi tamkar akwai wanda yake kallonta daga can sama da idon ɗan Adam ba zai iya gani ba...
Ta tsaya cak, ta kasa ci gaba da takun da take yi. A hankali ta ɗaga kanta tana kallon sararin samaniya, idanunta suna yawo a cikin gajimare. Ba ta ga komai ba amma zuciyarta tana gaya mata cewa akwai wani abu...
Ibrahim wanda yake shirin barin wurin zai je ƙiran sarki, ya ji takun Inuwa ya tsaya. Ya juyo ya gan ta a tsaye tamkar gunki, kanta a ɗage tana kallon sama cikin wani irin yanayi na shauƙi da fargaba...
Ya nufe ta, ya tsaya kusa da ita, ya bi layin kallon idonta amma bai ga komai ba sai hasken rana. Ya dafa kafaɗarta, wanda hakan ya sanya ta firgita ta dawo cikin hayyacinta...
"Inuwa, me kake kallo a sama?" Ibrahim ya tambaya cikin sautin mamaki...
"Ko akwai wani tsuntsu ne da kake neman gani, ko kuwa tunanin ɗazun ne ya dawo?"
Ayat ta sauƙe idanunta cikin sauri, tana ƙoƙarin saita numfashinta da ya fara hargitsewa. Ta kawar da kai tana shafa wuyanta..
"Ba... ba komai Master. Kawai dai na ji kamar iskar sama ta canza launi ne, kila gajiya ce."
Ibrahim bai gamsu da amsar ba, domin ya ga yadda idanunta suka firfito, amma sai ya share kawai ya ce, "To mu ƙarasa ciki na rakaka, kafin rana ta ƙara dukan ka ka fara ganin abubuwan da babu su."..
Ayat ta ce, "a'a zan ƙarasa da kaina, domin wurin kwanan namun ba nisa..."
Ta ci gaba da tafiya..
Bayan ta koma sashenta, ta cire kayan maza da suka matse asalin jikinta, ta shiga wanka don wanke duk wata gajiya da ƙurar birnin Alhamra. Bayan ta fito, ta sanya kayan gimbiyanci na alfarma waɗanda suka ƙara fito da asalin kyawunta da kwarjininta na mace...
Ta tsaya a gaban babban madubin dake ɗakinta, tana kallon kanta. Kwatsam sai tunanin wannan baƙon mutumin da suka haɗu a bakin kogi ya dawo mata a rai. Nan take annurin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka sauya launi, ta haɗe gira cikin wani irin azababben fushi...
Zuciyarta ta fara zafi tana bugawa da sauri. Wannan mutumin ya zame mata tamkar ƙayar dake maƙale a maƙoshi. Ta yi fatan ace yana gabanta a wannan lokacin, da lallai ta yi amfani da takobinta ta sare masa wuya don ta huta da wannan kallon rainin hankalin da ya yi mata...
"Waye kai da za ka keta min hurumi?"
Ta faɗa a fili tana kallon madubin, muryarta na rawa cikin fushi...
Babban abin da ya fi ƙona mata rai shi ne, ya karya mata babban alƙawarin da ta yi na tsawon shekaru. Ta haramta wa kowane ɗan Adam ganin asalin surar jikinta ko fuskarta a matsayin mace, amma shi a rana ɗaya ya ga abin da kowa ya daɗe yana nema ya rasa. Ta tuna lokacin da ta cire kayanta a bakin kogi, ashe yana can yana kallon sirrin jikinta...
Wani irin tsanarsa ne ya ziyarci zuciyarta, tsanar da ba ta taɓa ji wa kowane ɗan Adam ba. Ta kura wa madubin ido tamkar tana ganin hotonsa a ciki, tana jan numfashi mai zafi..
"Ka kalle ni... ka kalli abin da na adana wa wanda zan aura kadai," ta cigaba da magana a fili tana nuna kanta a madubi, "amma ka sani, wannan kallon da ka yi min zai zama silar halakar ka. Ko kai waye, ba zan taɓa yafe maka ba. Wallahi sai na ga bayan ka!"
Tana tsaye tana huci, idanunta cike da tsanar mutumin da ya keta mata alfarma.
"Wallahi duk inda kake, sai na sare maka wuya! Ka kalle ni ka ga asirin da na adana, amma ka sani wannan shi ne ganinka na ƙarshe!"
Tana cikin wannan zafin muryar, sai ta ga wani abu ya fara canzawa a cikin madubin..
Ba zato ba tsammani, sai hoton kanta lokacin da take matsayin Inuwa ya bayyana a cikin madubin ya fara yin dishi-dishi. Ta zaro ido, ta daskare a inda take tana kallon yadda siffarta na yanzu ya ɓace, Inuwa ne ya bayyana a cikin madubin...
Ayat ta ja baya da sauri, zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi....
"Wannan ni ne ai a matsayin Inuwa...."
Ba tare da ta ga leɓensa yana motsi ba, sai ta ji wata murya ta ratsa ɗakin, muryar tana tashi ne daga cikin madubin, tana amo tamkar ana hura busa..
"Kada ki ɓata kyawun fuskarki da fushi Ayat.... Idan har sarar wuyana shi ne zai sanyaya miki rai, to ki sani... wuyana yana nan yana jiran takobinki. Amma kafin hakan ta faru, ki sani cewa abin da na gani, ba zan taɓa mantawa da shi ba har abada."..
Ayat ta ɗauki wani butar fure dake kusa da ita ta kwala wa madubin da ƙarfinta..
"Kaaaaaaassss!"
Madubin ya fashe, ya farfaske ya zama guntu-guntu a ƙasa. tana sauke numfashi tana kallon fasassun gilasan. Jikinta yana rawa, gumi ya jige mata goshinta...
"Ta ya ya san suna na? Ta ya ya shigo cikin madubi na?" Ta raɗa tana kallon yadda kowane guntun gilashi yake nuna fuskarta guda guda..
Tsoro ya maye gurbin fushin da take ji. Ta gane cewa wannan mutumin da take nema ta kashe, tabbas ba mutum ba ne...
Cikin fushi ta furta, "Ƙarya ne ba aljan bane, mutum ne kamar kowa, kawai yana amfani da sihiri na tsafi ne kuma sai na wargaza tsafin nan..."
Ta sulale ta zauna a ƙasa, tana kallon fasassun gilasan, tana jin tamkar har yanzu idanunsa suna kallonta ta cikin tarkacen gilashin...
Can sai ga Saratu ta shigo da gudu jin ƙarar har ya sauƙa falo..
Haka take bin madubin da ya farfashe a ƙasi ga kuma Gimbiya a durƙushe cikin ɓacin rai..
Saratu ta ƙaraso tana faɗin
"Gimbiya meya faru ne? Ke da wa? Meyasa kika fasa madubin ki? Wa ya ɓata miki rai?..."
In short answer Ayat ta ba da
"Ba komai..."
Haka Saratu ta lallashe ta..
Sannan ta share mirror ta gyara ɗakin gaba ɗaya...
Bayan Saratu ta share fasassun gilasan ta fita, Ayat ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na kunci da fargaba. Shirun da ɗakin ya yi ya dawo mata da sauti da kuma kwarjinin muryar da ta ji daga cikin madubin....
Tana zaune a gefen gado, tana kallon inda madubin yake a dā, yanzu kuma babu komai sai bango. A ranta tana tambayar kanta..
“Waye wannan mutumin? Ta yaya har ya san sunana?”....
✨✨✨
A can bangaren Gimbiya Maayah, ɗakin ya cika da sautin nishi mai ban tausayi...
Maayah tana kwance rubda-ciki, fuskarta jiƙe da hawaye da gumi. Faɗuwar da ta yi a kan treadmill ba ƙaramin rauni ta ji ba..
ƙunƙuminta ya taɓu, ƙashin bayanta kuma yana mata wani irin raɗaɗi tamkar ana huda ta da mashi...
Mama Liyatu tana gefe guda tana lallashi, amma Maayah ihu take ta saki..
"Abul! Spinal cord ɗina ya samu matsala! Shikenan ba zan sake tashi ba! Wayyo Allah na... ku taimake ni! Ba zan iya motsa ƙafata ba!"
Sarki Nourdeen, wanda yanzu ne labarin hatsarin ya isa gare shi, ya shigo ɗakin da fadawansa suna biye da shi cikin matuƙar damuwa..
Ganin ƴarsa a wannan yanayin sai da zuciyarsa ta girgiza...
Sarki ya zauna a bakin gadon, ya dafa kanta cikin muryar rarrashi,
"Kiyi haƙuri Maayah... komai zai wuce."
A daidai wannan lokacin Doctor ya shigo da sauri, ɗauke da kayan aikinsa. Ya gaishe da Sarki cikin sauri sannan ya fara duba Maayah. Kowane taɓi da zai yi mata a baya sai Maayah ta tsandara uban ihu dake firgita kowa...
Doctor ya duba idanunta, ya duba yadda ƙafafunta suke motsawa sannan ya yi shiru yana nazari...
Sarki ya kalle shi cikin fargaba, "Doctor, ya ake ciki? Shin raunin yana da girma?"
Doctor ya gyara gilashinsa, ya kalli Sarki sannan ya kalli Maayah dake kuka...
"Mai martaba, ƙashin ƙunƙuminta ya ɗan goce ne, kuma tsokokin bayanta sun kumbura sosai. Za ta yi jinya ta tsawon lokaci, kuma dole ne ta daina yawan motsi ko fushi, domin kowane tashin hankali zai iya sa jikinta ya yi paralysis."
Jin haka Maayah ta ƙara fashewa da kuka. Girman kanta da izzarta duk sun bi ruwa, a yanzu kawai neman sauƙi take...
A daidai lokacin da Doctor yake ƙoƙarin yi wa Maayah allura, ihun kukanta ya ƙaru sosai
"Wayyo bayanaa! Wayyo Allah na!",
Ta can gefe guda kuma aka fara jin waƙe-waƙe da raye-raye...
Ba zato ba tsammani, sai ga Chingching ta shigo, tana sanye da doguwar riga mai sheƙi, tana riƙe da toy ɗinta a hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma tana riƙe da gorar ruwa. A bayanta wasu bayinta ne guda biyar suke mata rakiya, kowaccen su tana ɗauke da tiren fure da lemo, suna tafiya a jere yayin da Chingching take ta rera waƙarta da ƙarfi..
_🎶🎶 Gimbiyar mata, Firdausi autar mataa, Firdouss babu kamar kiii, Firdouss, Firdausi ƴan mata, Firdouss tauraruwar mataaa..🎶🎶_
Chingching ta ƙaraso tsakiyar ɗakin, ta tsaya tana kallon
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 39