daɗe ta fita daga makarantar...
A take Uncle Jalal ya ƙira wani jami'i mai tsaron get ɗin fada ya tambaya cewa Maayah ta iso kuwa?
Aka sanar da a'a.
Nan Uncle Jalal ya ɗauki superbike ɗinsa ya fita daga makarantar a ɗari...
Yana fita ya bi hanya amma bai ganta ba..yana ta tambaya amma babu wanda ya ganta..
Ya shiga tashin hankali..
Ya juma yana neman ta amma bai sameta ba, ya ƙara ƙiran fada akan ta isa, aka nasar da a'a...
Ya bi hanya yana tambaya, har ya haɗu da wani dattijo...
"Baba, ko ka ga wata ɗaliba ta wuce nan?"
Dattijon ya nuna masa can cikin kurmi. "Na ga wata yarinya tana kuka ta nufi wancan jejin."
Uncle Jalal bai tsaya wata-wata ba, ya murɗa wutar mashin ɗin, ya lulƙa cikin jejin. Yana ta gudu, yana kewayawa tsakanin bishiyoyi har sai da ya iso wani fili mai faɗi. A can gabansa, ya ga ramin da kowa ya sani, babban rami ne mai gudun ruwa a ƙasa, wanda idan mutum ya faɗa, ba za a taɓa samun gawarsa ba..
Ya hango Maayah tsaye a bakin ramin, tana ta maganganu cikin kuka...
Iskar dajin tana kaɗawa da ƙarfi, tana tura kukan Maayah zuwa cikin ramin dake gabanta... Ruwan dake karkashin ramin yana gudana da wani irin sauti mai ban tsoro, yana jiran duk abin da zai faɗo masa..
Tana tsaye a bakin rami, uniform ɗinta yana kaɗawa cikin iska da sumar gashinta duk da akwai hula akai....
"Gwara na mutu kowa ya huta!" ta faɗa cikin kuka mai cin rai. "Na gaji da wannan rayuwar ta kunya. Abul ya tsane ni, Uncle Jalal shima ya tsane ni.. Babu amfanin rayuwata!"
Ta rufe idanunta, ta sanya ƙafa ɗaya tana shirin tura kanta cikin ramin. A daidai lokacin da take jin jikinta yana neman tafiya...
"Maayah!" Wata murya ta daka mata tsawa, muryar da ko a cikin mafarki ta ji ta, ta san ta Uncle Jalal ce.
Ba ta ko juyo ba, ta ƙara zamar da ƙafarta..
"Kada ka matso! Ka bar ni na huta!"
Kafin ta samu damar sakin jiki, Uncle Jalal ya daka wani uban tsalle daga kan mashin ɗinsa. Cikin zafin nama irin na jarumai, ya damko damtsen hannunta da wani irin ƙarfi, ya juyo da ita baya da karfin tsiya..
Saboda gudun da ya kwaso, sai da suka faɗi ƙasa tare, yana kanta, numfashinsa yana fita da sauri-sauri, idanunsa sun yi jawur tsabar tashin hankali...
Ya miƙe tare da ita, ba tare da ya ba ta damar yin magana ba, ya daka mata wata uwar tsawa..
"Ke wace iriyar wawiya ce?! Mutuwa kike nema?!"
Sai kawai ya ɗauke ta da wani lafiyayyen mari..
Dukan farko ya sauƙa a kuncinta na dama. Maayah ta daskare, idanunta suka zaro waje...
Na biyun ya biyo baya. Waɗannan lafiyayyun marukan suka sa kanta juyawa, kukan ma ya tsaya mata a makoshi... Ta kalli Uncle ta ga yadda jikinsa yake rawa, ba na fushi kaɗai ba, har da na tsoron rasa ta...
"Kin san abin da kika kusan yi wa kanki kuwa? Kin san tashin hankalin da kika sanya ni?" Muryarsa ta dashe, yana sake damko kafadunta...
"Idan kin faɗi jarrabawa, wannan dalili ne na kashe kanki? Me ya rage miki a duniya idan rayuwar taki ta ƙare a nan?"
Maayah ta dube shi, hawaye masu zafi suna kwarara. "Amma ai ka ce na faɗi... ka ce zaka gaya wa Abul..."
Uncle ya rungume ta da karfi lokaci guda, rungumar da ta nuna tsantsar tausayi da ƙauna, saɓanin dukan da ya yi mata yanzun nan...
"Ba zan taɓa barinki ki mutu ba a wannan yanayin Maayah. Ko da kuwa zan koya miki darasi ne amma kada kiyi tunanin na mutuwa ne. Kin nuna min yau cewa ba ki san darajar kanki ba..."
Bayan marukan da ya zabga mata, Maayah ba ta daɗe cikin hayyacinta ba. Wani irin hauka ya ƙara turnuke ta, ta fusge kanta daga rungumar tasa, ta juya da gudu ta nufi bakin ramin tana kuka...
"Ka kyale ni! Mutuwa nake so!"
Uncle ya ƙara daka wani uban tsalle ya sake cabko ta a daidai gaɓar ramin...
Saboda ƙarfin gudun da ta ɗauka da kuma nauyin jikinsa da ya faɗa kanta, sai suka rasa daidaiton sawunsu. Nan take suka fara gangarawa daga kan tudun zuwa wani gangaren mai ban tsoro...
Dake wurin sai kayi a hankali, saboda tudu da gangarensa, da kuma ramuka da yawa..
"Wayyoooooo!" Maayah ta sake wani irin ihu mai ban tsoro wanda ya karaɗe jejin...
Sunka fara gangarawa suna juyawa, wani lokacin Maayah a ƙasa, wani lokacin Uncle Jalal. Cikin zafin nama, Uncle ya sa hannuwansa duka ya kankame ta, ya danne kanta a kirjinsa don kare ta daga buguwa da duwatsu..
Maayah kuwa ta sa hannu ta damke gaban rigarsa, tana kuka da ihu yayin da suke ƙara nisa cikin gangaren...
Basu tsaya ko'ina ba sai ga su Giffffff! sun faɗa cikin wani babban kogo mai zurfi wanda ciyayi da kananan kofofin ruwa suka kewaye..
Shiru ya biyo baya. Maayah tana kwance a saman kirjinsa, idanunta a rufe ta riga ta suma saboda tsananin firgici...
Uncle Jalal ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya, jikinsa duk ya yi tsami, rigarsa ta yage a wasu wuraren. Ya yi kokarin tashi, ya juyar da ita daga kansa ya kwantar da ita a kan rantsatstsen korayen ciyayin dake cikin kogon...
"Maayah! Maayah!" ya fara jijjiga ta, muryarsa tana rawa. Ya kalli kyakkyawar fuskarta wadda ƙura ta ɓata, ya ji wani irin tausayi ya ziyarci ransa. Ya taɓa wuyanta ya ji jini yana bugawa, nan ya san tana raye...
Ya ɗaga kansa ya kalli saman kogon da suka faɗo. Ya ga nisan wurin ya fi karfin a iya takawa a hau, kuma babu wani abu da za a iya kamawa. Ya duba ko'ina, sai sautin ruwan dake gudana a cikin kogon yake ji. Sun tsinci kansu a inda ba su taɓa tsammani ba...
Ya koma ya zauna kusa da ita, ya zuba mata ido yana kallon yadda ƙirjin ta yake sama da ƙasa saboda numfashi...
Sanyin kogon ya fara ratsa ƙashinsa, ga daddaɗan sautin ƙananan koguna dake gudana a cikin kogon. Ya kalli Maayah, fuskarta ta yi fari saboda firgici da kuma sanyin dake ƙoƙarin shiga jikinta..
Ya rarrafa ya isa bakin ɗaya daga cikin ƙananan kogunan, ya tsoma hannunsa cikin ruwan mai sanyi kamar ƙanƙara. Ya dawo kusa da ita, ya fara yayyafa mata ruwan a fuska, sannan ya sa tafin hannunsa yana shafa fuskarta a hankali..
"Maayah... Maayah, ki tashi..." ya furta cikin muryar raɗa..
Maayah ta fara motsa idanunta, a hankali ta buɗe su. Abu na farko da ta gani shi ne fuskarsa da take kusa da tata, idanunsa cike da damuwar da ba ta taɓa gani ba. Ta rintse idanun ta ta sake buɗewa, tana jin sanyin kogon yana sa jikinta rawa..
"Uncle..." ta furta cikin muryar da ba ta fita sosai.
Ba tare da ya ce uffan ba, ya sa hannu ya janyo ta jikinsa, ya rungume ta da ƙarfi domin ya ba ta ɗumin jikinsa.... Ba ta yi musu ba, ta ƙara shigewa jikinsa tana kuka ƙasa-ƙasa, tana jin yadda bugun zuciyarsa yake dukan ƙirjinta..
Wannan sanyin ya sa duk wani girman kai ya kau, ya bar gurbinsa ga buƙatar kariya.
Ta ɗago ta kalli saman kogon da ya yi nisa...
"Ba za mu iya fita ba, ko? Mutuwa za mu yi a nan?"
Uncle Jalal ya ƙara ƙanƙame ta, ya duba ƙwayar idonta...
"Ba za mu mutu ba Maayah. Muddin ina raye, ba zan bar komai ya same ki ba. Wannan wurin zai zama sirrinmu, babu wanda zai san me ya faru a nan."
Maayah ta kalli yadda rigarsa ta yage, ta kai hannunta ta taɓa inda ya ji rauni a kafaɗa. "Ka ji ciwo saboda ni..."
A take Uncle ya ji wani irin shauƙi ya ziyarci ransa. Ya kalli leɓunanta dake rawa saboda sanyi, sannan ya kalli idanunta... A wannan lokacin babu malami ko gimbiya, sai mutum biyu da ƙaddara ta haɗa a cikin kogon ƙasa...
✨✨✨
Bayan King Diamond ya dawo da Ayat ɗakin baccinta, ya sumbace ta a goshi a matsayin alkawarin kariya, sannan ya ɓace...
Amma yana isa duniyar aljanu, bai tarar da natsuwa ba.. Manya-manyan majalisar aljanu sun taru a kewayen Power Pool, idanunsu suna hura wuta...
Dattijon cikinsu, wanda ake ƙira da Azazil, ya tako gaba, muryarsa tana girgiza duwatsun fadar.
Azazil ya ce,
"King Diamond! Ka ƙeta dokar da aka kafa dubunnan shekaru. Ka sanya jininmu da na bil'adama ya gauraya ta hanyar shauƙi da musayar jini..... me ya sa kake ɓata lokacinka akan mace 'yar ƙasa, wadda numfashinta yake ƙarewa cikin kiftawar ido?"
Wani Aljanin ya ce,
"Mun ga yadda kake shige mata, kusancinku yayi yawa sosai....har ta kai ga a kwanaki kana kwana da ita a matsayin kuliya...Sannan ka kawo ta kana koya mata sirrin yakinmu! Ka mayar da kan ka bawan mace maimakon Sarkinmu!"
Ko wani shugaba da abinda yake faɗi...
King Diamond ya tsaya daram, gashinsa na yawo a iska, idanunsa na shuɗi sun yi jawur saboda bacin rai...
Ya furta cikin ƙwarin gwiwa
"Ina amfanin mulki idan ba zan iya kare abin da zuciyata take so ba? Ayat ba mace bace kawai, ita ce inuwar da take sanyaya min zafi na tsawon shekarun baya...."
Azazil ya ce,
"Hukuncinmu ɗaya ne! Ko dai ka yanke alaƙa da ita yanzu, ko kuma mu kwace duk Ikon Sarauta dake tattare da kai. Idan muka janye wannan ikon, ba za ka iya bace-wa ba, ba za ka iya ba ta kariya ba, kuma ba za ka iya yin aiki da ikon mu ba...."
King Diamond ya yi murmushin rainin wayo sannan ya ce,
"Kuna tunanin ikon da nake da shi ne yake sa ni faɗa? A'a. Zuciyata ita ce babban ikona. Ko da za ku janye komai, zan tafi wurinta a matsayin kowane irin hali. Idan har kariya ta tana nufin zan zama mazauni a duniyar mutane, to na shirya!"
Majalisar ta yi kukan ruri, hasken ɗakin ya fara dishi-dishi da wani irin walƙiya...
Azazil cikin ɓacin rai ya furta
"Ka zaɓi kaddararka. Daga daren yau, mun janye kashi saba'in na ikonka. Ba za ka iya keta hazo cikin sauƙi ba, kuma duk raunukan da za ka ji a duniyar mutane, za su zama raunuka na haƙiƙa a jikinka. Ka zama tamkar mutum mai ɗan karamin ikon aljani."
King Diamond ya ji yadda karfin dake jikinsa yake raguwa, ya ji nauyin jikinsa ya ƙaru, amma bai nuna tsoro ba...
Sai ma cewa da yayi..
"Ku kwace duka idan kuna so. Amma ku sani, ko da hannu ɗaya zan yi faɗa, ba zan taɓa barin Ayat ta zama ganima ga kowa ba..."
Sauran Aljanun suka furta
"Akwai sauran hukunci zuwa gaba..."
Daga nan duk suka ɓace..domin sun san shi da masifar taurin kai da kafiya akan abu...
Bayan wasu sa'o'i yana zaune yana faman saƙe-saƙen zuci...
Kodayake an rage masa kashi saba'in na ikonsa, amma ragowar kashi talatin ɗin sun isa su girgiza duniya...Abokinsa Prince Zarith yana gefensa, yana ta faman zazzaga surutu..
"King, ka saurare ni! Wannan yarinyar bil'adam za ta zama silar rugujewar ka. Ka barta tayi rayuwarta ita kadai, domin babu aure a tsakaninku...kar ka zo kayi biyu babu, ka ceci kanka daga fushin dattijan aljanu!"
King Diamond ya yi banza da shi, idanunsa suna kallon sararin samaniya. Tunaninsa ɗaya ne...
"Ta yaya zan samar da Ayat ta biyu wadda za ta zauna a fada ba tare da an gane ba?..."
Lokaci guda, fuskar ɗan uwansa, Chief Onyx wato Ra'ees ta faɗo masa a rai...
Onyx kaɗai ne yake da fasahar da za ta iya ƙera Robot wanda zai yi kamanin Ayat ɗari-bisa-ɗari...
Ba tare da cewa uffan ba, King Diamond ya miƙe, hasken shuɗi ya gauraye jikinsa. Zarith ya saki baki yana kallo, sai kawai ya ga Diamond ya ɓace kamar walkiya...
Bai sauƙa a kowane lungu ba sai a gaban katon babban gate ɗin masarautar Pavilion City...
Wani birni ne da aka gina shi da gilashin da ba ya fashewa, cike da fasahar da ta wuce tunanin ɗan Adam...
Wannan ne karon farko da zasu yi face to face tin yarinta kuma akan wani aiki..
Duk da a cikin zuciyar King Diamond bai so ya je wurinsa ba domin yana tunanin ai bai damu da shi ba...
Shima Chief onyx Yana ganin tunda King Diamond aljan ne ai zaifi neman yadda yake ya neme shi amma bai damu da shi ba..
Sai kowa ya sharar da kowa saboda kowa a cikinsu yana fama da girman kai da jiji da kai...
Ga kuma King Diamond yana jin haushinsa yadda ya wulaƙanta Ayat a walimar sauƙar al'kur'ani su...
King bai zo da sauƙin kai ba... Yana takowa, wata irin ƙaƙƙarfar guguwa mai ɗauke da sanyi da ƙura tana biye da shi, tana kakkarya duk abin da ya yi yunkurin tare shi...
Bodyguards ɗin Chief Onyx, dakarun zamani masu ɗauke da makaman lantarki, suka fara yo kansa...
"Tsaya a nan! Waye kai?...!"
King Diamond bai ko kalle su ba. Wannan guguwar dake biye da shi ta riƙa ɗaukar bodyguards ɗin tana sama da su, tana buga su da ƙasa. Yana tafiya yana ratsa cikin dogayen gine-ginen gilashin fadar. Duk da cewa gilasan Pavilion an kera su ne da gilashi masu bala'in ƙarfi, amma kwarjinin King Diamond ya sanya su fara faffashewa ɗaya-bayan-ɗaya...
"PHAS! PHAS! PHAS!" Sautin fashewar gilashin yana tashi kamar ƙarar bindiga...
A can cikin babban falon masarautar, Chief Onyx yana zaune a kan kujerarsa ta alfarma. Gaban faffaɗan allon Plasma dake nuna podcast na duk abin da yake faruwa a bakin gate...
Yana kallon yadda wannan guguwar take tunkaro shi. Ya ga wani matashi mai farin sumar gashi da idanun shuɗi, wanda kamaninsa da nasa kusan iri ɗaya ne, yana take duk dakarunsa...
Ko kiftawa Onyx baya yi, kuma bai nuna alamar tsoro ba, duk da yadda gine-ginen falon nasa suke girgiza..
Onyx ya gyara zama, idanunsa suka yi walwali da wani boyayyen sirri. Ya san wannan ba kowa bane face ɗan uwansa, tagwayensa, wanda duniya ta raba su shekaru 23 da suka wuce...
Wasu robots ne kala-kala suka shigo falon da Chief yake suna sanar dashi irin ta'adin da wani Jinn yake musu..
Abinda Chief ya furta cikin rashin damuwa shine
"Ku bar shi ya ƙaraso..."
Ya ƙarasa maganar tare da ɗaukan lemon juice ya kurɓa...
Yana sanye da silver mask ta gefen fuska wanda yake rufe sirrin kamanninsa..
King Diamond ya isa ƙofar falon ƙarshe, ya sanya kafarsa ta dama ya buga ƙofar, guguwar dake bayansa ta haɗiye ɗaukacin hasken falon...
Sun faɗo cikin duhu, kuma babu wani haske da zai iya bayyana yadda za su fita...
ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAH!!
ALHAMDULILLAH!!!
📢 EXTRACT: DOMIN CIGABA DA BOOK TWO!
Anan muka kawo ƙarshen Book One. Shin yaya za ta kasance tsakanin manyan tagwayen nan biyu a masarautar Pavilion?
Shin Inuwa (Ayat) za ta iya jure wa yaƙin dake jiran ta?
Ko kuwa ya zata kasance da Uncle Jalal da Maayah a cikin kogon can mai zurfi?
*SHIN WANI SCENE NE YAFI BURGE KU KO YA KWANTA MUKU A RAI?*
_CHING-CHING— CHIEF ONYX—GELY.._
_AYAT—KING DIAMOND._
_MAAYAH—UNCLE JALAL_
To fa ga kuma Zayana har yanzu a Cell, sarki kuma yana son kawar da tsoron Ruma a zuciyarsa ta hanyar cigaba da tsare Zayana...
Domin samun cigaban wannan labari a Book Two, ga yadda tsarin yake:
Paid Group (Page by Page): N500 kacal.
Full Document (Bayan an kammala): N700 kacal.
Kada ku bari a ba ku labari, domin Book Two ya fi komai zafi!
*MASU KARATU, KU SHIRYA DOMIN BOOK TWO YA FI WANNAN ZAFI DA TASHIN HANKALI!....*
_BAYAN SALLAH ZA'A ƊORA DAGA YADDA AKA TSAYA GA WAƊANDA SUKA YI PAYMENT..._
Za'a fara saka sunaye a list tun yanzu.
Da zarar lokaci ya yi, za a ɗora kai tsaye.
ACCOUNT DETAILS:
Opay / Palmpay
9065443871
Asma’u Muhammad Auwal
📩 Tura shaidar biya + sunanki domin a saka ki/ka a list....
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 39