biyar. Ta haddace hadisan Manzo (S.A.W) da sauran litattafan fikihu."
Sheikh ya ci gaba, "Ta aiko ni ne ta roki alfarma, tana son gudanar da gagarumar walima a masarautar nan. Amma tana son a bincika idan akwai sauran Gimbiyoyin da suka haddace Alkur'ani domin su gudanar da walimar tare."
Sarki ya sake murmushi mai ƙayatarwa, sai dai abin mamaki a yanzu babu fuskar zakin nan, asalin kamanninsa ne,
Ya ji daɗin wannan albishir domin sai hamdala yake tayi...
"Masha Allah! Wannan ita ce kyauta mafi girma da ɗiya zata ba mahaifinta."
Nan take ya bada umarnin a ƙira masa dukka Gimbiyoyin masarautar ba tare da bata lokaci ba.
A lokacin ne motar jami'an tsaron Maayah ta shigo masarautar daga makaranta. Aka tsaida su aka gaya musu sakon Sarki. Maayah ta firgita, ta yi saurin goge hawayen dake fuskarta na takaicin Uncle Jalal...
"Wayyo kar dai maganar auren ne?..." ta faɗa tana turo baki, zuciyarta na bugawa. Ita ce ta farkon shiga fadar, tana taku ɗaya-ɗaya har ta samu waje ta zauna, tana kokarin boye idanunta dake jawur.
Ba a daɗe ba, sauran Gimbiyoyin suka fara isowa. Zayana ta shigo cikin takun gadara. Sai kuma Ayat ta bayyana, a yau ta yi sa'a tana matsayinta na Gimbiya ba Inuwa ba. Ta zauna cikin sanyi da nutsuwa, fuskarta a rufe da siririn mayafi...
An buƙaci ganin malaman dake koyar da yaran gaba ɗaya dake ko wace gimbiya da malaminta...
Malaman gida suma sun iso...
Malamin Ayat shiru-shiru mai yawan nazari da nuna Dattaku...
Sai malamin Zayana wanda kullum take bashi wahala...
Sai kuma Sheikh Shureim dake zaune gefe ɗaya, idanunsa a kasa.
Daga ƙarshe, Gimbiya Yumna ta shigo. Ta sha bamban da sauran, fuskarta tana fitar da wani irin haske na tarbiyya da karatun Alkur'ani. Tana shigowa, idanunta suka sauka akan Sheikh Shureim. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, tana jin wani daɗi dake gauraye da kunya na cewa "Ga masoyina, ga kuma abin alfaharina."
Ta gaishe da mahaifinta, sannan ta zauna kusa da Aunty Zayana...
Sarki ya kalli Gimbiyoyin nasa guda huɗu da suka hallara...
"Na ƙira ku ne domin na ji labari mai daɗi daga bakin Sheikh Shureim game da Yumna. Tana son yin walimar saukar Alkur'ani, kuma tana son wacce ta haddace a cikinku ta fito su yi tare."
Sarki ya kalli kowacce ɗaya bayan ɗaya.. "Zayana? Maayah? Aayat? Shin akwai wacce ke da haddar Alkur'ani a cikinku?"
Zayana ta kau da kai, Maayah kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta tana tunanin notes din Uncle Jalal... Sai Ayat ce kadai ta ɗanyi motsi, amma ba ta ce uffan ba...
Bayan tambayar Sarki, Malam Mubarak ya yi murmushi mai cike da alfahari, ya gyara zama...
"Ranka ya daɗe, tabbas Gimbiya Aayat ma ta haddace Alkur'ani mai girma da wasu daga cikin litattafan Manzo Allah (S.A.W). Dalilin da ya sa kuke ganinta tana ba ni hutu ne saboda ta kammala komai, tana tilawa ne kawai a kowane lokaci."
(A ranta, Ayat ta sauke ajiyar zuciya, domin ta san dalilin dakatar da shi shine don ta samu sararin fita a matsayin Inuwa, amma hakan bai hana ta kasancewa mai kwazon karatu a ɓoye ba).
Sarki ya jinjina kai, fuskarsa cike da mamaki. "Masha Allah! Amma batun boko fa?"
Malam Mubarak ya ci gaba, "Alhamdulillah! Ta ƙware a Turanci da rubutu. Ta bitar darussan kimiyya irin su Physics, Chemistry, Maths, har ma da fannin tattalin arziki (Economics). Ta hadiye duk wani fanni da ake koyarwa."
Sarki ya kalli Ayat da matsanancin farin ciki..
"Daman burinta ta zama likita tun tana ƙarama, ashe har kin shirya."
Ba zato ba tsammani, Ayat ta ɗaga kai ta cikin mayafinta, muryarta a sanyaye cikin natsuwa...
"Abul... yanzu na fasa zama likita."
Fadar ta ɗauki shiru. Sarki ya zaro ido, "Me ya sa? Bayan kin gama tattara duk darussan fannin kin karance su?"
Ayat ta yi murmushin nan nata na shagwaɓa wanda Sarki ba ya iya musa mata duk mayafi ya rufe...
"Abul, ni yanzu Criminology nake so. Burina shi ne in zama Sojan Sama wato Air Force Officer..."
Sarki ya kalli 'yarsa kamar bai taɓa ganinta ba. "Kina Gimbiya? Kuma matar wani nan gaba? Kuma da wannan rufin fuskar koda yaushe za ki yi aikin soja? Wannan wane irin buri ne Ayat?"
Ayat ta ɗan matso kusa da mahaifinta cikin sigar lallashi da shagwaɓa..
"Abul, please mana. Duk wanda zan aura ai zai bar ni in yi abin da nake so. Kuma duk sanda na zama sojan sama, to zan yaye wannan mayafin in sanya kakin soja. Batun gimbiyanci kuma... uhmm uhmmm," ta turo baki tana dariya.
Duk waɗanda ke fadar suka daskare.
Sheikh Shureim ya ji jiki ya yi sanyi ganin yadda 'yar Sarki ke da babban buri na jarumta..
Maayah ta daina kukan zucin da take na Uncle Jalal, ta tsaya tana kallon Ayat da mamaki, tana tunanin yadda za a yi mace ta zama soja..
Sarki kuwa ya rasa abin da zai ce, domin ya san tauri da kaifin zuciyar Ayat idan ta sa abu a gaba.
Sai kawai ya juya kansa a hankali zuwa ga Gimbiya Zayana, muryarsa a nutsuwa yake furta wa Ayat...
“Bari na koma ga ƴan'uwanki kafin na dawo gare ki...”
Sarki ya kalli Zayana, ya tambaye ta game da nata karatun. Zayana ta yi shiru, tana wasa da zoban hannunta cikin ko-oho..
Da Sarki ya kalli Malam Mahmud,
“me zaka iya cewa ga me da Zayana?”
Malam Mahmud ba tare da ya kalli idon Zayana ba, balle ya damu da kwarjininta ko matsayinta..
Ya fara ƙiƙƙina, murya tana rawa..
"Ranka ya daɗe... a gafarce ni. Gimbiya Zayana ko izu biyu ba ta kai ba. Idan na je koyar da ita, wulaƙanta ni take yi ta kore ni, har tana cewa ba ta son sake ganina."
Sarki ya ji wani zafi ya ziyarci zuciyarsa. Ya fara mata faɗa mai ratsa jiki, yana tuna irin taurin kan mahaifiyarta da ya shafi rayuwar Zayana...
“Zayana! Har yanzu baki gane darajar abin da kike yi ba? Al-Kur’ani ake magana, kalmar Ubangiji! Ke kuma kina raina malaminki, kina kore shi kamar bawa? Wannan wace irin tarbiyya ce?”
Zayana ta ɗaga kai cikin izzah, idonta babu ko ɗigon nadama..
Sarki ya cigaba,
“Na ba ki malamai, na ba ki lokaci, na ba ki duk abin da ’ya mace za ta nema amma ke kina zaɓar girman kai akan ilimi! Kina son ki zama me? Sarauniya marar addini?”
Nan take Zayana ta yi dariyar raini, ta matso gaba kaɗan..
“Abba, ka daina min wannan wa’azin. Ba kai ne ke zaune a zuciyata ba, don haka ba ka san abin da nake ji ba.”
Sarki ya harara ta, muryarsa ta ƙara tsananta.
Ya ce,
“Ke fa ’yata ce! Zan gyara ki ko kin so ko ba ki so! Addini ba zaɓi ba ne a wannan fadar!”
Zayana ta ɗaga hannu alamar dakatar da shi, muryarta mai sanyi amma kalmomin suna yankar zuciya... Ta ce
“Gyara? Kai fa kana ƙoƙarin mallaka ne, ba tarbiyya ba. Kana son mu zama yadda kake so, ba yadda muke ba.”
Sarki ya daki ƙasa da ƙafa cikin ɓacin rai tare da faɗin
“Zayana! Ki kula da bakinki! Ina magana da ke a matsayin uba da sarki!”
Ta kalleshi kai tsaye, ba tare da tsoro na,
“Ni kuma ina sauraronka ne a matsayin mutum, ba gunki ba. Idan tarbiyya ta tilas ce, to ka sani zuciya ba a tilasta mata gaskiya.”
Shiru ya sauƙa na ɗan lokaci...
Sarki ya yi kamar zai sake magana.
Sai Zayana ta ƙara da murya mai kaifi..
“Za ka iya min hukunci, sannan ka iya yi mun tsawa, amma ba za ka taɓa sa ni in zama abin da ban yarda da shi ba.”
Nan take ta juya, ta ɗaga habarta cikin izzah.
“Na gaji da zaman fadar nan...”
Ta fice daga fadar ba tare da waiwaya ba.
Tana takun gadara, ta bar kowa cikin mamakin rashin tarbiyyarta.
Sarki ya tsaya cak, kalamanta suna maimaituwa a kansa kamar sara..
Ayat ta kalli bayan Zayana, ranta yana suya. Ta ji zafi yadda Zayana ta wulaƙanta mahaifinsu a gaban malamai. A ranta take cewa,
"Zayana, akwai ranar da za ki san kuskurenki." Amma sarki ya danne tasa damuwar ya kalli Maayah, wadda hankalinta yake wani wajen...
Tun farko ya lura hankalinta ba ya nan gaba ɗaya. Kamar akwai wani abu mai nauyi da ke damunta.
Cikin murya mai ɗan tsauri..
"Ke kuma fa? Ko ke ma rashin kunyar za ki tsaya min?" Sarki ya tambayi Maayah.
Maayah ta girgiza kai a hankali. Ta ɗago idonta ta kalle shi, murya a sanyaye ta furta.
"Duk lalacewar tarbiyyata, ba zan yi musayar yawu da kai ba, Abul.... Ko da naman jikinmu kake yankewa kullum, hakan ba zai sa mu ƙi ka a matsayin uba ba.”
Sarki ya ji sanyi a ransa, "Allah ya miki albarka ƴata. Yanzu ke kin haddace?"
Maayah ta gyara zama, ta ce cikin ƙwarin gwiwa,
"Abul, ban haddace duka ba, amma na kusa... domin yanzu haka ina Suratul Musa."
😨😨😨!!! Fadar ta ɗauki shiru. Malamai suka zaro ido, Sarki ya daskare...
Ayat, duk da baƙin cikin Zayana da ke ranta, ta kasa riƙe dariya, sai da ta tintsire da dariya har sautin na fita sosai, rabo da a ji Ayat tayi irin wannan dariyar tin da ake da ita, ba'a taɓa ji ba, ba ita ba hatta sauran ma gabaɗayan su....
Yumna ta kalli Maayah cikin mamaki,
"Aunty Maayah, Suratul Musa kuma? A ina take a Alkur'ani?"
Maayah ta ɗanyi tsuru-tsuru, ganin yadda kowa ya zuba mata ido. Ta shafa goshinta cikin wayancewa da murmushin jin kunya...
"Wayyo! Na manta ne... kuyi haƙuri. Wai zan ce Suratul Isa ne sai nace Musa. Yauwa, ina Suratul Isabul Maryama."
A wannan karon ma, malamai suka kalli juna suna murmushin tausayi da dariya. Sun gane cewa Maayah ba ta ma san sunayen surorin ba, balle ta san karatun. Daga Suratul Musa zuwa Suratul Isabul Maryama duk ƙage ne irin na Maayah don ta nuna tana karatu...
Sarki ya sauƙe ajiyar zuciya, yana girgiza kai. Ya gano cewa yayin da Yumna da Ayat suke can cikin hadda, Maayah tana can tana Suratul Musa a duniyar tunaninta....
*GASKIYA IDAN HAR KUNA SONA KUMA KUNA SON NEXT PAGE A YAU, TO KU NUNA MUN BAJINTA SOSAI...MORE LIKE AKAN PAGE ƊIN DA COMMENTS..*
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 3️⃣2️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Sarki ya ɗaga hannu, "Za ku iya tafiya, Allah ya muku albarka. Zayana kuma... Allah ya shirye ta."
Maayah ta fita tana rarraba ido, tana jin daɗin yadda ta wayance, a tunaninta ta ba da amsa daidai... yayin da Ayat take tafiya tana danne dariyarta, Yumna kuma tana satar kallon Sheikh Shureim kafin ta fice daga fadar...
Bayan ficewarsu, fadar ta dawo shiru. Sarki ya kalli Malam Mubarak da Sheikh Shureim..
"Ina son ku haɗa kai," in ji Sarki. "Tunda Ayat da Yumna duka sun kammala hadda, ina son walimar nan ta zama abin koyi a duk faɗin ƙasar nan. Ina son a raba kyaututtuka ga marasa ƙarfi, kuma a gayyato manyan malamai su shaida wannan nasara."
Malam Mubarak ya jinjina kai, "Ranka ya daɗe, wannan babban ra'ayi ne. Za mu tsara yadda za a yi gasar karatun a ranar, domin kowa ya ga irin ƙoƙarin da suka yi."
Sheikh Shureim, wanda fuskarsa ke nuna natsuwa, ya ƙara da cewa, "Zan fara tsara tsarin jadawalin taron, tare da zaɓar ayoyin da za su karanta waɗanda za su ratsa zuciyar jama'a. Wannan taro zai zama haske ga masarautar nan."
Bayan malamai sun gama bayanan su, Sarki ya yi shiru na ɗan lokaci, yana tunanin Maayah.
Maganar Suratul Musa ta nuna masa cewa Maayah ba ta san komai ba game da karatun da take ikirarin yi a makaranta..
"Akwai matsala," Sarki ya faɗa ƙasa-ƙasa. "Maayah tana ɓata lokacinta ne. Kuma wannan rashin tarbiyyar ta Zayana, ba zan bar ta ta shafi Maayah ba."
Nan take Sarki ya ƙira babban hafsan hadimansa..
"Maza ku shirya motoci ku tafi makarantar su Maayah. Ina son ganin Principal da kuma malamin ajinsu, a nan fada yanzun nan. Ina son jin hakikanin gaskiyar abin da Maayah take yi a makaranta, domin ba na yarda da sakamakon da ake kawo min na first class.."
Hafsan hadiman ya duƙa, "An gama Ranka ya daɗe."
Cikin ƙanƙanin lokaci, jerin gwano na motocin fada suka tashi da gudu zuwa makarantar, wanda hakan zai zama babban tashin hankali ga Principal...
✨✨
Babban Hadimin ya wuce kai tsaye zuwa ofishin Principal ba tare da neman izini ba. Principal yana zaune yana lissafin kudin da yake samu na gyara sakamakon jarrabawa, ya ga mutane sun daka masa tsawa..
"Sarki yana ƙiran ka yanzun nan a fada!" In ji Hafsan...
"Kai da malamin dake koyar da ajin Gimbiya Maayah..."
Principal ya shiga in-ina, zufa ta fara keto masa duk da sanyin AC dake ofishin.
"Lafiya... lafiya dai ko? Ko wani abin ne ya samu Gimbiya?" Ya san cewa idan asirinsa na ba ta First Class na ƙarya ya tonu, to kashinsa ya bushe.
A ɗayan ɓangaren kuma, Uncle Jalal yana cikin aji, yana gyara wasu takardu. Hadimin ya iske shi ya gaya masa saƙon Sarki. Sabanin Principal, ba tare da ya firgita ba, ya gyara kwalar rigarsa, ya rufe jakarsa cikin natsuwa...
"Madalla," Jalal ya faɗa cikin murya mai kwarjini. "Dama akwai maganganun da ya kamata a ce Sarki ya ji su tun can baya."
Principal dake tsaye a bayansa yana rawar jiki ya yi masa kallon lallai Jalal zai kaimu ya baro mu, amma Jalal ko kallo bai nuna yana jin tsoro ba.
Yayin da ake jiran isowar su Uncle Jalal, Malam Mubarak da Sheikh Shureim sun fito zuwa wajen fadar, inda suka zauna a karkashin wata inuwar bishiyar flowers don tattauna maganar walimar..
Malam Mubarak ya dube Sheikh Shureim da murmushi,
"Sheikh, lallai Gimbiya Yumna ta samu malami nagari. Natsuwar da ta nuna a fada yau abin sha'awa ne."
Sheikh Shureim ya sunkuyar da kansa, muryarsa cike da girmamawa. "Duk godiya ta tabbata ga Allah. Amma maganar gaskiya, kalaman Gimbiya Ayat sun ba ni mamaki. Burinta na zama sojan sama ba ƙaramin abu ba ne. Shin kana tunanin Sarki zai amince?"
Malam Mubarak ya yi ajiyar zuciya. "Ayat mace ce mai zurfin ciki. Ta daɗe tana karance-karancen littattafan bincike da dabarun tsaro... Ni kaina na san cewa ranta ba ya kan likitancin nan, sai dai kawai tana biyan burin mahaifinta ne. Amma yanzu da ta fito fili, ina jin za a yi gumurzu a masarautar nan."
Sheikh Shureim ya jinjina kai, "Allah ya tabbatar da alheri. Amma batun walima, ina son mu tsara yadda su biyun za su fito su yi tilawa a gaban kowa, domin a ga banbancin dake tsakanin hasken Alkur'ani da duhun jahilci, musamman ga sauran 'yan uwansu."
Malam Mubarak ya amince, "Hakan ya yi. Bari mu fara rubuta sunayen manyan malamai da za mu gayyata kafin taron."
Maayah tana can sashenta, duk ta fita a hayyacinta. Jin cewa an je kiran Principal da Uncle Jalal ya sa ta san asirinta ya kusa tonuwa. Ta lallaɓa ta koma sashen fadar sarki kafin su iso ta laɓe a bayan labulen,
Zuciyarta tana dukan uku-uku, tana jin inama Uncle Jalal bai taɓa zama malamin su ba...
Can sai ga motocin sun faka, aka shigo da su.. Principal yana taku yana tanga-tanga, jikinsa har rawa yake yi, yayin da Uncle Jalal yake tafiya cikin natsuwa da kwarjini, kai kace shi ne mai masarautar...
Lokacin shima Sarki ya fito ya zauna akan karagarsa, fuskarsa ba annuri..
"Principal, na ƙira ka ne domin in ji dalilin da ya sa kake yaudarata da sakamakon ƙarya na Gimbiya Maayah."
Principal ya zube a ƙasa, "Ranka ya daɗe... kuskure ne... muna dai ƙoƙarin ƙarfafa mata gwiwa ne..."
Sarki ya dakatar da shi da hannu, ya kalli Uncle Jalal..
"Kai ne malamin ajinsu, ko? Faɗa min gaskiya, yaya Gimbiya take a karatu?"
Uncle Jalal ya gyara tsayuwa, ba tare da ya duƙa ba...
"Ranka ya daɗe, magana ta gaskiya ita ce.. Gimbiya Maayah ba ta san komai ba game da karatun da nake koyarwa. Ba ta yin rubutu, ba ta karatu, kuma tana tunanin sarautarta za ta sayi ilimi. Sakamakon da kake gani na ta ɗaya, duka na bogi ne. Maayah tana matakin 'yan Nursery ne a fannin ilimi."
Principal ya so yin magana, amma Jalal ya cigaba..
"Hasali ma, na zo ne da wasu littattafanta don ka gani da idonka. Wannan shi ne abin da ake kira cin mutuncin ilimi a makarantarka."
Sarki ya karɓi littattafan da Jalal ya miƙa masa. Ganin rubutun Maayah ya sa Sarki ya fusata. Ya buga hannunsa a hannun kujerarsa,
"Ina Maayah take?! Maza a fito min ita yanzun nan!"
Maayah dake laɓe ta ji ƙafafunta sun ɗauki karkata. Ta san idan ta fito yanzu, kashinta ya bushe. Ta fara kuka a hankali a bayan labule, tana tsinewa ranar da Uncle Jalal ya fara shiga ajinsu...
✨✨✨
A ɓangare guda kuma, Ayat ta kasa samun nutsuwa akan ganin yadda Zayana ta ci mutuncin mahaifinsu...daga part ɗinta ta fito zata fita.
Ta sa aka kawo mata tsararren dokinta wanda ya sha kwalliya da kayan ado masu tsada...
Masu tsaro suka dakatar da ita ganin bata juma da shigowa ba kuma za ta ƙara fita...
Ba ta tsaya sauraronsu ba ta nufe su da dokin tana shirin bi ta kansu.. da gudu suka matsa mata tare da faɗin "zan je wurin sarki..."
Da ga nan ta nufi sashen Zayana akan dokinta...
Masu tsaron sashen Zayana ne suka buɗe mata ganin Gimbiya ce.
Ayat ta shiga falon Zayana cikin takun fushi, mayafin fuskarta yana kadawa...
Cikin ɗaga murya ta furta.
"Ina Zayana take?"
Wata daga cikin bayin dake goge falon cikin kunfar baki ta ce,
"Haba Gimbiya, ai kya girmama sunan nata ko? Babbar gimbiya ce fa..."
Ayat ta watsa mata kallon raini, "Ban ga dama ba! Duk wanda ba ya mutunta mahaifina, to shima babu sauran mutunci a idona. Kuma ki kiyaye ni, kafin in yanke miki harshe! Ba wurinki nazo ba, wawaye kawai waɗanda ku ma ba'a ɗauke ku mutane ba."
Mimi ta sauƙo daga bene tana kallon Ayat cikin idanun nan nata na kyanwa...
"Ke mai rufe fuska! Me kika zo yi mana? Ba ma sonki, ki bar mana fadar mu!"
Ayat ta tsaya dambar tana kallon yarinyar, sannan ta furta.
"Ai kuwa kun mutu da ni! Domin wannan fadar mahaifina ne, ba wai gidan agolar masarauta ba."
Ayat ta dakata tana jin takaicin amsar da ta bawa Mimi domin tana ganin girmanta ya zube da ta tsaya biye wa ƙaramar yarinya...tana cikin tunani sai ta ji..
Mimi ta ce cikin muryar yara "Ƙarya kike yi! Masarautar mu ce!"
Ayat ta duƙa har matakin idon yarinyar... Ba tare da wata-wata ba, ta ɗauki almakashin dake gefen table ta yanke tulin gashin Mimi mai launin ruwan ƙasa, ta mika mata a hannu...
"Gashi nan, ki kai wa mahaifiyarki kice ni na bayar."
An raba tsakiyar gashin biyu, rabin gashi a hannun Mimi, sai na kanta da ya zamo short hair..
Mimi ta fashe da kuka mai sauti, "Wayyo gashina! Mommy! Gashina ya tafi!"
Zayana ta sauƙo bene a guje, idanunta sun yi jawur saboda bacin rai....tin farkon shigowarta ta sani already..
Cikin ɗaga murya tana daka wa Ayat tsawa...
"Stop it! What is wrong with you?!"
ta kai wa Ayat wani zafafan mari...
Ayat ta dafe kuncinta, sannan cikin zafi ta mayar mata da nata marin, har sau biyu....
Cikin fashin murya Zayana ta furta,
"Ni kika mara? You slapped me?!"
Ayat ta ce, "Ni ɗin gunki ce da zan tsaya ki mare ni? Idan kin saba dukan bayi, to kinyi kuskuren taɓa jinin sarki!"
Zayana ta fara magana da hausa dake gauraye da turanci cikin raunin lafazi, dake ba ta wani kware sosai a Hausa ba...
"You are nothing! Ke ba komai bace! Mahaifina ma tsorona yake yi, balle ke!"
Ayat ta ce,
"Mahaifinki ba tsoronki yake ba, yana kyaleki ne don girman kansa! Amma ki sani, duk wata izzah da kike takama da ita, a karkashin inuwar sarautarsa take. Amma yau kin nuna cewa baki da tarbiyya, baki da asali, kuma baki da godiyar Allah!"
Cikin fusata Zayana ta daka tsawa
"Shut up! You have no right to come into my house and........"
Ayat ta katse ta da kakkausan murya,
"I have every right! Wannan gidan mahaifina ne. Kuma bari kiji, rashin kunyar da kika yi masa a fada yau, ita ce ta karshe. Idan kika sake wulaƙanta shi, to ba zan tsaya a gashin 'yarki ba, zan ruguza muku dukkan izzarku! Ke baturiya ce a jini, amma kin rasa ko da ɗan mutuncin turawan ma, kin koma tamkar dabba mai cin naman wanda ya rene ta!"
Zayana tana huci ta ce,
"Zan ga abin da zaki iya yi..."
Ayat ta ce,
"Kin riga kin gani! Ga gashin 'yarki a ƙasa, ga kuma marin fuskarki. Wannan gargadi ne na farko. Next time, it will be worse. Ki kiyaye mahaifina!"
Ayat ta juya cikin takun alfarma, ta bar Zayana tana tsaye tana karkarwa saboda tsananin fushi, yayin da bayin falon suka yi tsuru-tsuru suna kallon ikon Allah...
✨✨
A can fada kuwa, Hadimin da aka aika ya ƙira Maayah ne ya dawo, ya sanar da ba ta nan,
Maayah jin haka yasa ta fito daga bayan labule, fuskarta duk ta jike da hawaye, idanunta sun yi jawur. Ta tsaya tana karkarwa, sannan ta wurga wa Uncle Jalal wata uwar harara mai cike da kiyayya...
Uncle Jalal, maimakon ya fusata, sai ya saki wani ƙasaitaccen murmushi, yana kallonta kamar yadda malami yake kallon ɗalibi waton kallon shashasha da asirinsa ya tonu...
Sarki ya kalleta ya ce, "wato laɓe kike mana ko? Me ya sa ba ki koma sashenki ba?..."
Maayah tayi shiru kanta a sunkuye...
Cikin muryar takaici Sarki ya kuma cewa,
"Maayah, wannan ƙwaƙwalwar takin ba irin ta mahaifiyarki bace. Ke kin fita daban! Duba irin rubutunki, duba irin yaudarar da kuke yi min da wannan Principal ɗin."
Daidai lokacin, Master Ibrahim shugaban tsaro na musamman ya shigo fadar cikin takunsa na jarumta...
Ya gaishe da Sarki cikin girmamawa...
Sannan ya furta "Ranka ya daɗe ka aika na zo..."
Sarki ya dubi Ibrahim sannan ya ce,
"Master Ibrahim, yanzu nake son ka je ka koya wa Zayana hankali. Ka hukunta ta yadda ya dace, sannan ka tafi da ita ka kulle ta a Dark Room No. 2 na tsaro. Ba na son jin wani bayani har sai ta san darajar mahaifinta."
Master Ibrahim ya ji zuciyarsa ta buga. Ya san ɗakin duhu na biyu, ɗaki ne da ko ɓera aka kulle a ciki sai ya firgita, balle Zayana mai izzah... Ya san kowa yana tsoron mahaifiyarta, amma umarnin Sarki ya fi karfin kowa..
Master Ibrahim ya ce,
"An gama, Ranka ya daɗe."
Ya juya jiki a sanyaye, yana tunanin yadda zai fuskanci Zayana wadda kowa ya san ba ta da mutunci..
Bayan ficewar Master Ibrahim, Sarki ya mayar da hankalinsa kan Maayah da Uncle Jalal..
"Ke kuma Maayah, tunda kin ce kina Suratul Musa, kuma kina Suratul Isabul Maryama, yanzu za ki nuna mana abin da kika sani...
Malam Jalal, ina son ka ba ta jarrabawa a nan gaba na yanzun nan. Idan har ta kasa amsawa, to ke ma hukuncinki yana jiran ki."
Maayah ta ƙara fashewa da kuka, tana kallon Uncle Jalal kamar tana roƙonsa da ido, amma Jalal ya riga ya buɗe littafinsa yana neman tambayar da zai wanke mata lissafi...
Sarki ya gyara zama, fuskarsa cike da ɓacin rai amma kuma yana son ya tabbatar da abin da Uncle Jalal ya faɗa...
Ya kalli Uncle Jalal ya jinjina masa kai alamar ya fara...
Cikin muryarsa mai natsuwa dake cike da izgilanci ya fara...
"To Gimbiya Maayah, bari mu fara da abin da kika sani a fannin ilimin addini tukunna."
Maayah ta tsaya tana karkarwa, hawaye suna ɗigowa daga idanunta, tana kallon Uncle Jalal cikin kiyayya...
"Faɗa mana, guda nawa ne rukunnan Musulunci? Kuma rukunin farko menene shi?"
Maayah ta goge hancinta, ta kalli Sarki sannan ta kalli Uncle Jalal. Ta yi shiru na kusan minti biyu, kafin can ta buɗe baki...
"Rukunnan Musulunci ai... ai guda talatin ne!"
Duk hadiman dake wurin suka kalli juna. Sarki ya dafe goshi, yayin da Uncle Jalal ya ɗanyi murmushin nan nasa na gefen baki..
Uncle Jalal
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 39