da saukar Chief Onyx da Robot dinsa Gely, Uncle Jalal yana zaune daram, ko kwayar idonsa bata motsa ba. Ya kalli Onyx ne kawai a matsayin wani baƙo, ba tare da fargaba ba...
Maayah ta kalli Uncle Jalal ta ga ko zai nuna tsoro, amma ganin yadda ya hadiye natsuwa ya sanya ta kara jin kwarjininsa a ranta...
Sarki ya ɗaure fuska, amma a cikinsa fargaba yake yi kada Chief Onyx ya tona asirin cewa Yumna ba jininsa bace, kanwarsa ce shi da Reems.. Sarki ya riƙe ta ne tun tana jaririya don boye asali, kuma ya nemi alfarmar Onyx kan kada kowa ya sani.
Yumna ta ji zuciyarta na wani irin bugu. Tana son ta mike ta ruga ta rungume dan uwanta Onyx, amma alkawarin da ta yi wa Sarki na boye dangantakar su ya sanya ta tsumaye a mazauninta, idanunta cike da hawayen farin ciki da raɗaɗi...
Ayat ta kalli Chief Onyx, wani irin ɗaci ya ziyarci makogwaronta. Ta tuna yadda ya tafi da Autar sarki, wato kanwarta uwa daya uba daya, ya mayar da ita baiwa a Pavilion. Ta so ta mike ta shaƙe shi, amma hasken Alkur'anin da ta gama karantawa ya sanya mata wata natsuwa, ta kasa motsawa sai dai kallon tsana...
Chief Onyx yana takowa cikin isa, ya zo wucewa ta inda Inuwa yake tsaye... Lokaci guda, Chief Onyx ya ji tsikar jikinsa ta tashi, wani irin ƙiran jini ya ziyarce shi. Ya tsaya cak, ya juyo a hankali ya ƙura wa Inuwa ido...
King Diamond wanda yake matsayin Inuwa shima bai ɗauke idonsa ba. Ya kalli Onyx har cikin kwayar idonsa, anan ya tabbar da akwai alaƙa a tsakaninsu...
A ransa yana wani irin farin ciki na ganin twins ɗinsa da aka raba su tun suna kanana..
Chief Onyx ya zare idonsa cikin zargi. Ya tuna lokacin da ya zo daukar Autar sarki, ya ga wannan Guard din Inuwa, kuma a lokacin ya san mace ce. Amma yanzu da yake kallonsa, kwarjinin da yake gani ya wuce na mace, kuma wannan jan ragamar tsikar jikin da yake ji ya tabbatar masa akwai wani boyayyen abu a tare da wannan bawan...
Ba tare da ya ce uffan ba, Onyx ya wuce ya je ya zauna a kujerar dake kusa da Sarki, ya shimfida ikonsa...
Duk da wannan tashin hankalin, aka cigaba da rabon abinci da abin sha na walima...
Maayah tana faman satar kallon Chief onyx Daman bata san shi ba, sai kawai labarinsa...ta haɗiye yawu a ranta take faɗin
"Wayyoo, wannan ne Chief onyx? Tsararren sarki, wannan ya wuce yadda nake tunani...haɗaɗɗe da shi..."
Amma da zaran idonta ya sarƙe da na Uncle Jalal sai ta fara yatsine fuska, tana nuna masa har yanzu dukan da ya mata yana nan a ranta. .
Uncle Jalal ya ɗauki kofin ruwa ya sha, ya kalli Maayah ya girgiza kai kadan, yana mata kallon babu wanda zai saurari jahila fa...
A daidai lokacin da Chief Onyx yake zaune yana kallon kanwarsa Yumna cikin alfahari, can Zayana tana ta faman dukan kofar cell ɗinta. Tin sautin jiragen da ta ji ya isa kunnenta, ta ɗauka mahaifiyarta ce ta zo... Domin tasan ba za ta ƙyale kowa ba...
✨
Chief Onyx ya ba da umarnin a shigo da wasu manyan akwatuna na zinare. Abubuwan dake ciki sun fi karfin kwatancin dan adam, akwai sarƙoƙi na duwatsun Ruby masu haske, akwai turaren da akayi masa haɗi na gaske wanda kamshinsa kawai zai iya warkar da marar lafiya, da kuma agogo na musamman da ke nuna yanayin tsaron jikin mutum...
Bayan ya miƙa wa Sarki wani sirrin Memory Card wanda ganin haka yasa Sarki ƙara ruɗe wa, Chief Onyx ya nufi inda Yumna take...
Ya durkusa a gaban Yumna, ya ɗora hannunsa a saman kanta cikin wani salo na girmamawa da kauna. Ya fara tofa mata addu'o'i cikin sanyi, yadda mutane za su ɗauka girmama karatunta yake yi...
Yumna cikin muryar raɗa ta furta
"Nagode Yayanaa..."
Chief ya ce, "Kada ki damu, kyakkyawar kanwata. Ba zan taba barin ranar murnarki ta wuce ba tare da na shaidi nasararki ba."
Ya sakar mata wani murmushi wanda shi kaɗai ne yake da shi, sannan ya tashi..
Domin kada mutane su zargi wani abu, Chief Onyx ya nufi inda Ayat take zaune domin ya bata nata kyautar... Ya natsu zai dora hannunsa a kanta don yi mata addu'a kamar yadda ya yi wa Yumna, amma kafin hannunsa ya taɓa mayafin kanta, Ayat ta buge hannun da wani irin zafin nama...
"Kada ka kuskura ka matso kusa da ni! Ka janye wannan hannun naka mai cike da jinin mutane!...Ba na son ko iskar jikinka ta gogi tawa!"
Chief cikin muryar sanyi mai tsoratarwa ya ce,
"Gimbiya, ina ƙoƙarin nuna miki girmamawa ne saboda wannan rana ta Alkur'ani, amma naga kina son wuce gona da iri."
Ayat muryarta na rawa saboda kuka da bacin rai ta ce,
"Girmamawa? Daga gare ka? Tun yaushe azzalumi ya san girmamawa? Ka gaya min, da wane ido kake kallon mutane a nan? Kana tunanin na manta ne? Na manta yadda ka shigo fadar nan ka fizge ƙanwata, jini na, ka tafi da ita cann a matsayin baiwa?"
Taron ya yi tsit, kowa ya zura ido. Ayat ta ci gaba da magana cikin daka tsawa..
"Me ta yi maka? Me yarinya ƙarama kamar ta ta sani na gaba da mulki da za ka mayar da ita baiwa? Ka raba uba da ɗiyarsa, ka raba ni da kanwata ba tare da wani dalili ba! Ka sani sarai, duk ranar da na samu iko, sai na ga bayanka! Mugun banza, azzalumi!"
Ran Chief Onyx ya ɓaci fiye da yadda kowa yake tunani. Kalmar Azzalumi da aka nanata a gaban baƙi da malamai ta soke shi...
Ba tare da ya furta komai ba domin shi ba mai son hayaniya bane, cikin zafin nama ya zabga mata wasu lafiyayyun mari guda biyu a kunci biyu har sai da ta kife akan kujerarta...
Marin ya sauka a kuncin Ayat da duk ƙarfin hannunsa. Marin ya kasance mai ƙarfi yadda har sai da hular Rolling ɗin kanta ta fice, ta dafe kuncinta tana kallonsa cikin rashin yarda tana ƙasi zaune...
Sarki ya miƙe tsaye a gigice, amma kwarjinin Onyx da sojojinsa ya sanya shi daskarewa...domin a wannan ranar ba ya buƙatar tashin hankali domin ranar farin cikinsa ne, yana son duk baƙin da suka zo, su koma gida cikin ƙoshin lafiya...
Master Ibrahim ya zare takobinsa, yana jiran umarni, amma ya san taɓa Onyx yanzu tamkar taɓa wutar lantarki ne...
Sarki ne ya ɗaga musu hannu akan su ajiye makamansu...
King Diamond ya dunƙule hannunsa har jijiyoyinsa suka fito raɗau... Idanunsa suka fara rikiɗe wa zuwa launin blue...Yana jin kamar ya bayyana asalin sa ya fatattaka Chief Onyx a nan, duk da jikinsa na gaya masa akwai alaƙar jini a tsakaninsu....kuma alkawarin da ya yi wa kansa da kuma sirrin Ayat ya sa ya tsaya yana rawar jiki saboda bacin rai...
Ayat tana dafe da kuncinta, idanunta suka cika da hawayen radadi da wulakanci, tana kallon Chief Onyx wanda yake huci kamar zaki....
Uncle Jalal ya miƙe tsaye ganin haka, kwarjininsa ya cika wajen... Ya kalli Chief Onyx ba tare da tsoro ba..
"Haba bawan Allah, wannan ba halin girma ba ne. Ka daki mace a gidan mahaifinta a ranar farin cikinta?"
Chief Onyx ya juyo ya kalli Uncle Jalal cikin sauri, idanunsa suka rine...
"Kai kuma wanene da za ka sa baki a harkar Pavilion da Alhamra?"
Maayah tana hararar Uncle Jalal a cikin ranta take faɗin
"Ku ji! Ku ji!! Munafiki, jiya ka gama duka na makaranta amma yanzu kana magana akan dukan mace..."
King Diamond zuciyarsa ta gama harzuƙa, wani irin hasken shuɗi ne ya bayyana a cikin kwayar idonsa... Ya ɗora hannunsa akan makamin dake ƙugunsa, yana jiran kawai ya ga Ayat ta zubar da hawaye na biyu don ya fito da dukkan asalin sa ya koya wa Onyx darasi, ko da hakan zai tona asirinsa...
Ayat dake ƙasi har yanzu tana riƙe da kunci, ta kalli yadda King Diamond yake domin tasan dole zai ce zai aiwatar da wani abu, ganin yanayinsa ya sauya hatta idonsa yasa tayi sauri girgiza masa kai akan ya dakata...
Haka ta fara masa magana ta zuci..
"Ka da kayi komai, ka bari, ka koma yadda kake, Master Ibrahim zai kalleka yanzu, ka koma..."
Dai-dai lokacin da master ya kalli Inuwa wanda yayi ready zaro ido, King bai bari ya ga yanayin da yake ciki ba...
Gely kuwa ta nufi Uncle Jalal da wani irin gudu na inji. Ganin Boss dinta ya fusata, ta yanke shawarar koya wa wannan mutumin darasi, ya daina shiga shirgin da bai shafe shi ba...
Uncle Jalal, wanda asali jarumi ne kafin ya zama malami, bai girgiza ba. Ya fizge takobi daga hannun wani jami'in tsaro dake kokarin buya a karkashin teburi. Gely ta matsa wasu maballai a hannunta, nan take wani takobi mai dauke da wutar lantarki ya fito daga jikinta...
Sai ƙarar Kwang! Kwang! Kwang ake ji...
Sautin takubansu ya riƙa tashi. Uncle Jalal yana kare kansa cikin kwarewa, yayin da Gely take amfani da karfin karfe...
Maayah tana can takure, zuciyarta na bugawa. Tana hawaye tana cewa, "Don Allah kar a kashe shi!" Duk da dukan da ya mata, ta gane cewa rayuwarta ba za ta taba zama ɗaya ba idan babu Uncle Jalal..
Ayat ta kasa jurewa. Marin da ya mata da kuma tunanin kanwarta da yake hannunsa ya sanya ta rasa nutsuwa...Ta miƙe tare da zaro wata matacciyar takobi, ta kewaya ta bayan Chief Onyx tana nufin soka masa a tsakiyar bayansa...
Shi kuwa Chief tin tinin ya ga yanayin jami'in tsaro wato Inuwa wanda King Diamond ne, tin daga lokacin da ƙwayar idonsa ta koma shuɗi, Chief onyx ya ri ga da ya gane cewa shi ɗin ba kowa bane face REEMS...
Ya gano komai yanzu, domin Chief na da saurin fahimta da hangen nesa, tinin ya gane cewa akwai alaƙa a tsakanin Reems da Ayat, kuma a baya yasan Ayat ce take matsayin guard, saboda a yau dole ta fito a matsayin gimbiya da kuma guard yasa Reems taimaka mata..gaba ɗaya ya tafi dogon tunani, idonsa na kan King Diamond...
Ganin Ayat tayi baya da takobi zata soka masa, gaba ɗaya mutane suka zaro ido a gigice, har sarki kam ya daskare a yadda yake..
"Ayat! Don Allah kada ki yi haka!" Yumna ta dakawa Ayat tsawa cikin tashin hankali...
Kafin Bodyguards ɗinsa su ankara domin suna ɗan nesa da su..
Amma Ayat ba ji ba gani.. Ta tura wukar da nufin kashe shi, amma Chief Onyx kamar mai idanu a baya, ya sa hannunsa ya cafke bakin takobin daidai lokacin da zai taba jikinsa...
Ayat ta yi firgigit, ta yi kokarin fizge takobin ta yadda za ta feɗe masa tafin hannu, amma sai ta ji takobin kamar an manne shi a cikin dutse. Chief Onyx ya rike wurin kaifin wukar sosai ba tare da hannunsa ya tsage ba ko da digon jini ɗaya...
Sojojin Pavilion sun nufota da gudu, amma Onyx ya ɗaga musu hannu su tsaya. Sarki ma ya dakatar da dakarunsa don kada a fantsama cikin yaƙin da ba za su iya ba...
Chief Onyx ya saki wani murmushin gefen bakin nan nasu domin a jininsu yake, sannan ya yi wani uban janyo, ya jawo Ayat tare da takobinta. Saboda karfin jan, Ayat ta tafi luuu ta faɗi a gabansa tana huci...
Chief ya kalle ta kyau sannan ya furta..
"Matsalo ne kawai yake kawo farmaki ta baya... Ki kiyaye gaba yarinya. Ƙarfin zuciya ba shi ke ba da nasara ba, sai idan an haɗa da ƙwarewa..."
Ya ɗaga wa Gely hannu, nan take ta janye takobinta ta kyale Uncle Jalal, wanda shi ma ya sauƙe numfashi yana kallon wannan robot ɗin cikin mamaki, dake yana da kwarewa shima bai ba ta damar cutar da shi ba..
Chief bai sake cewa uffan ba, ya gyara bakar rigarsa, ya yi wa Sarki wani kallo na raini, sannan ya juya tare da bodyguards ɗinsa da Gely zuwa wurin jiragen su..
King Diamond ya bi su da kallo, idanunsa suna faɗin abubuwa da dama. Ya so ya bi ɗan uwansa amma ya san ba a wannan lokacin ba...
Sarki yayi wani fusata ya miƙe tare da yo wa kan Ayat wadda take durkushe a ƙasa, tana karkarwa saboda raɗaɗin marin Onyx da kuma ɗacin zuciya...Bai tsaya wata-wata ba, ya fizgota da karfi ya sake zabga mata wani lafiyayyen mari wanda ya sa kanta sarawa..
Yana huci, idanunsa sun yi jawur ya ce,
"Wace irin mahaukaciyar yarinya ce ke? Wace irin dabba ce ke da ba ki da tunani? A gaban waɗannan dubunnen mutanen za ki nuna wa duniya cewa ba ki da tarbiyya? Har kina da ikon fito da takobi ki nufi Chief Onyx?"
Ayat ta ɗago fuskarta dake cike da hawaye ta cikin niƙab, muryarta na rawa cike da tauri...
"Abul... me ya sa ka kyale shi? Me ya sa ya zo ya ɗauke min kanwata ya tafi da ita Pavilion? Jini na ne ita fa!"
Sarki ya sake daka mata tsawa..
"And so what? Kin fi ni son Ching-Ching ne? Ko kuma cewa aka yi miki cutar da ita yake yi a can? Ko kina tunanin Pavilion ɗin wasan yara ne?"
Ayat ta ce,
"Amma Abul... baiwa ya mayar da ita! Kanwata tana bauta a karkashin azzalumi!"
Girgiza kai yayi yana zaro mata idanuwa..
"Baiwa? Wa ya gaya miki hakan? To ki shiga taitayinki! Onyx ba abokin wasanki ba ne. Shi wuta ne, kuma duk wanda ya taɓa shi sai ya ƙone ya zama toka. Shin idan aka barki dake da shi, kina tunanin za ki iya cin galaba a kansa ne? Kina tunanin takobi ɗaya zai kifar da Pavilion?"
Ayat ta kalli takobin dake gefenta, wanda akwai jinin Onyx a jiki, ta yi wani murmushi na ɗacin zuciya.. ta ce,
"Abul, ai ko yanzu na ci galaba a kansa. Dubi wannan takobin, jininsa ne a jiki. Ya riƙe takobi ta wurin kaifi, haƙiƙa salon jarumta ne, amma ko ba komai... na sa ya zub da jini a gaban mutanensa. Na taɓa fatarsa!"
Sarki a ruɗe kuma cikin fushi ta ce,
"To ke marin da ya zazzabga miki fa? Shegiyar yarinya! Ai shi wannan ɗan ciwon tafin hannun ba komai ba ne a wurinsa. Mutumin da yake yaƙar dubunnan sojoji shi kaɗai kuma ya rayu lafiya, don ya ji wannan raunin sai me? Ko a matsayin cizon sauro bai ɗauki wannan ba! Amma ke... kin janyo wa kan ki, kuma ki kiyaye ni!"
Sarki ya juya cikin zafin rai ya kalli Uncle Jalal, wanda har yanzu yake rike da takobin da ya yi faɗa da Gely da shi...
"Kai kuma Malam! Daga yau, kada ka ƙara kuskuren shiga maganar da ba ta shafe ka ba. Ka kame bakinka ka yi shiru kamar yadda kowa ya yi. Idan har kana son rayuwarka, to ka sani cewa takobinka ba zai taɓa kare ka daga fushin Pavilion ko na Alhamra ba. Kai malami ne, to ka tsaya a matsayin malami!"
Uncle Jalal ya kalli Sarki, ya kalli Maayah dake can tana hawaye, sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin girmamawa amma ba tare da nuna tsoro ba. Ya san cewa yau ya kulla abota da mutuwa, amma bai yi dana-sanin kare mutuncin fadar ba...
Taron ya watse cikin firgici da tsegumi. Masu sauƙar Alkur'ani duka sun koma sashensu cikin damuwa, yayin da fada ta ɓarke da wata irin hayaniya ta daban...
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 37
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
A cikin katafaren jirgin Chief Onyx mai ɗauke da fasahar zamani ta Pavilion, shiru ya ratsa cikin jirgin, sai dai kawai sautin injin jirgin dake tashi a hankali. Chief Onyx yana zaune a kan wata kujera ta alfarma, idanunsa a lumshe, yayin da fuskarsa dake sanye da karfen azurfa take haskaka karkashin fitilun jirgin...
Gely tana tsugune a gabansa, hannayenta na robot suna motsawa cikin kwarewa da sanyi. Ta riƙe babban hannun Chief wanda takobin Ayat ya ratsa. Tafin hannun ya tsage, jini mai kauri na digowa, amma Onyx ko kifta ido bai yi ba, kamar ba a jikinsa ake aikin ba.
Gely ta kunna wani haske mai launin shuɗi (Laser treatment) daga yatsunsa, wanda yake bin asalin inda takobin ya yanke jikin. Tana goge jinin da wani lallausan kyalle mai ɗauke da sinadarin kashe kwayoyin cuta.
Gely cikin muryarta mai sanyi irin ta na'ura ta ce,
"Boss, raunin ya ɗan yi zurfi. Takobin yarinyar nan yana da kaifi na musamman. Me ya sa ka bari ta taɓa ka? Da ka ba ni izini da na raba ta da numfashinta tun kafin takobin ya karaso."
Chief Onyx ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalli tafin hannunsa dake ta konewa karkashin hasken Gely. Murmushin nan nasa na gefen baki ya sake bayyana...
"Gely, wani lokacin jini yana bukatar ya zuba domin mu tuna cewa mu mutane ne. Yarinyar tana da jini mai zafi... jinin Alhamra ne yake yawo a jikinta. Tana bukatar tarbiyya, amma jarumtarta ta burge ni."
Gely ta kammala ɗinke raunin da wani irin ɗinki na zamani wanda baya barin tabo. Ta shafa masa wani magani mai sanyi, sannan ta naɗe hannun da wani farin kyalle mai ɗauke da tambarin Pavilion...
Chief Onyx ya dunƙule hannunsa don jin karfin dinkin,
"Ina so ki sa ido akan wannan Guard ɗin. Akwai wani abu a tare da shi wanda ya fi karfin kwayar idon mutum. Tsikar jikina ba ta taba tashi a banza ba, kuma bisa alamun ba mutum bane...."
Gely ta ce, "An gama Boss. Na riga na ɗauki hoton kwayar idonsa na tura wa babban kwamfutar Pavilion don bincike."
Chief Onyx ya ƙura wa sararin samaniya ido ta taga, yayin da jiragen suke kutsawa cikin gajimare. Zuciyarsa tana can fadar Alhamra, yana tunanin ɗacin zuciyar Ayat da kuma kwarjinin Inuwa dake taɓa ruhinsa....
✨✨✨
Sarki Nourdeen ya saka ƙaramin Memory ɗin a cikin na’urar kallo ta hologram dake falo ɗinsa. Nan take haske ya bayyana a tsakiyar ɗakin, hoton wani fili mai ɗauke da fasahar zamani ya bayyana.
A tsakiyar hoton, Ching-Ching ce tana sanye da kayan makaranta mai kalar navy blue and white, fuskarta tana sheki da alamun wayewa da natsuwa. Tana zaune a gaban wasu manyan malaman bincike da malaman addini...
Bidiyon ya fara nuna yadda ake jifan ta da tambayoyi masu wahala..
Fannin Kimiyya Malami ya tambaye ta game da tsarin kwayoyin halitta da fasahar makaman nukiliya. Ching-Ching ta amsa da yaren Turanci British Accent cikin kwarewa, tana bayani daki-daki kamar ita ce ta ƙera na'urorin...
Fannin Addini kuwa Wani malami ya nemi ta yi bayanin wasu hadisai da ka’idojin ilimin Mantiq. Nan take ta sauya harshenta zuwa Larabci mai kyan gaske, tana kwararo hujjoji daga litattafan da sarki bai taɓa tunanin yarinya karama kamar ta za ta sani ba.
Sarki Nourdeen ya daskare yana kallon allon, idanunsa sun cika da hawayen alfahari. Ya ga yadda diyarsa, wadda ya ɗauka tana can tana bauta a matsayin baiwa, ta zama wata kwararriyar malama kuma masaniya a karkashin kulawar Chief Onyx...
Sarki cikin muryar raɗa ya furta
"Masha Allah... ashe bawan nan Onyx bai yaudare ni ba. Ya mayar da Auta tauraruwa. Wannan ilimin ya wuce tunanin kowa."
Ya gane cewa Chief Onyx ya ɗauke ta ne ba don wulakanci ba, sai don ya tafi da ita inda za ta samu ilimin da babu shi a Alhamra...
Sarki ya sake tunawa da yadda Ayat ta kusan kashe Chief Onyx da takobi. Ya ƙara jin haushin Ayat a ranta...
"Wannan yarinyar Ayat tana so ta lalata komai! Gata tana can tana zargin Onyx azzalumi ne, alhali gashi ya mayar mata da kanwa sarki-ta-fannin-ilimi. Idan ta kashe shi, wa zai cigaba da rainon Ching-Ching?"
✨✨✨
Sydney...
Sarauniya Ruma tana zaune a cikin babban fadarta. Tana riƙe da wani kofin giya na alfarma, sai ga wani baturen ɗan leken asirinta ya shigo cikin gaggawa, ya zube a gabanta...
Dan Leken Asirin ya ce,
"Your Majesty... labari ya zo mana daga Alhamra. Gimbiya Zayana tana tsare a Cell yau kusan mako guda. Sarki Nourdeen ne ya sa aka rufe ta, tana cikin kaskanci, ba abinci mai kyau, ga kuma azabar sauraye da kadaici."
Kofin dake hannun Ruma ya faɗi ya fashe, jan giyar cikinsa ta bazu a kasa kamar jini. Ruma ta mike tsaye, idanunta masu kalar kuliya suka rikiɗe suka koma wani irin kore mai firgitarwa. Wani irin ihu ta saki na ɓacin rai wanda ya sa ɗaukacin dakarun dake wajen ɗakin firgita...
Ruma cikin muryar dake fitar da hayaki ta ce,
"Nourdeen! Ka taɓa jini na? Ka taɓa guda ɗaya tilo da nake so a duniyar nan? Na gaya maka zan rusa Alhamra idan gashi ɗaya na kanta ya faɗi, ashe ba ka ɗauke ni da gaske ba!"
Ta fara zagaye ɗakin tana numfashi sama-sama, kissar dake fuskarta ta ɓace, sai mugunta ta bayyana..
"Ba zan tafi Alhamra yanzu ba. Ina so Nourdeen ya ji daɗin mulkinsa kaɗan kafin in ruguza masa shi. Amma daga yau, Alhamra ta daina sanin lafiya."
Ta juya ga babban janar ɗin dakarunta na Sydney..
"Ƙira min dakarunmu na sirri. Ina so a fara gurgunta duk wata mashigar abinci da makami dake shiga Alhamra. Ina so mu fara shakarsu ta tattalin arziki kafin mu shakarsu ta wuya."
Ta nufi taga, tana kallon birnin Sydney amma tunaninta yana can fadar Alhamra inda Zayana take kuka..
"Nourdeen, ka sanya ɗiyata a cell saboda kana tunanin kai sarki ne? To zan nuna maka cewa ni mace ce da nake mulkar sarakuna. Zan sa ka roƙi mutuwa amma ba za ka ganta ba. Zan mayar da fadar Alhamra kango, inda jemage kawai zai rika shawagi. Kuma sai na fito da Zayana da kaina, sannan na sanya ka durkusa a gabanta kana neman gafarar jinin jiki na."
Ta ciro wani takobi karami na azurfa, ta yanke tafin hannunta kadan, ta bari jinin ya digo a kan hoton Sarki Nourdeen dake kan tebur...
"Wannan shi ne alkawari na na jini. Masarautar Alhamra za ta zama makabarta muddin diyata ba ta fito ba cikin kwana ɗaya ba... amma kafin nan, zan fara aikewa Nourdeen da sakonni da zasu sanya shi zazzabi."
Bayan kwana ɗaya..
Sarki Nourdeen yana zaune a babban falonsa, yana duba wasu takardu sai ya ji wani irin sauti Buzzzzz... a bakin tagarsa. Wata karamar na'ura ce mai kalar azurfa, wadda aka kera ta a siffar tsuntsu, tana shawagi a iska.
Sarki ya mike da sauri. Ya gane wannan fasahar, ta fadar dake Sydney ce. Na'urar ta shigo dakin, ta sauka a kan teburinsa, sannan ta bude wani dan karamin Screen na hologram.
Fuskar Sarauniya Ruma ta bayyana a jikin hasken. Idanunta dake zubar da wutar fushi..cike da izza da sanyi mai ratsa kashi..
"Nourdeen... Na gaya maka kada ka taba jini na. Na gargade ka cewa muddin gashi ɗaya na kan Zayana ya faɗi, to masarautarka ta zama kango. Yau kwana shida diyata tana cikin cell cikin azaba, tana shan azabar da ko bawan da ka fi tsana bai cancanta ba."
Sarki ya tsorata, ya fara zazzaro idanu. "Ruma... ta yaya kika sani?" ya fada a ransa...
Ta ci gaba da magana kamar tana ganinsa...
"Kada ka damu da yadda na sani. Ka sani kawai cewa, daga daren yau, barci ya tafi daga idanunka. Zan fara shakƙun tattalin arzikin Alhamra tun daga Sydney har zuwa sauran kasashen duniya. Idan har Zayana ba ta fito daga wannan cell din ba cikin sa'o'i ashirin da hudu ba, to zan aiko maka da kawunan jakadunka guda 50 dake nan Sydney a matsayin kyautar karin kumallo'."
Daga nan hoton ya ɗauke,
Sarki Nourdeen ya zauna a kan kujerarsa, gumi ya fara keto masa duk da sanyin dake ɗakin. Ya san Ruma mace ce mai cika alkawari, musamman idan aka taɓa Zayana. Idan har ta fara gurgunta kasuwancinsa a Sydney, Alhamra za ta shiga matsin lambar da zai iya jawo bore daga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 39