Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Maayah dake kwance tana murƙususu. Dai-dai lokacin ta gama waƙar... Ta turo baki, ta zura wa Maayah idanu na wasu daƙiƙoƙi kafin ta ce cikin muryarta ta shagwaɓa... "Haba Aunty Maayah! Tun jiya nake jin kina ta ihu kamar wadda aka sace maki takalmi... Me ya faru ne? Wai dama gudu kike yi? To ai na gaya miki ke ba doki ba ce, me ya sa kike son gudu irin na dawakai?"... Maayah ta buɗe jajayen idanunta, tana kallon Chingching cikin tsananin takaici. Ta so ta daka mata tsawa, amma zafin ƙunƙuminta ya hana ta ko motsawa... "Ching...ching... tafi nan! Ba na son ganinki!" Maayah ta faɗa cikin raunannen murya.. Amma ina, Chingching sai ma ta ƙara kusanto gadon, ta kalli Doctor ta ce.. "Doctor, shin gaskiya ne Aunty Maayah ba za ta iya sake tashi ba? Naji ana faɗa a waje wai bayanta ya rabe gida biyu. Idan haka ne, to wa zai riƙa tura ta a keken guragu?.." Ta juya ga mahaifinta, ta rungume shi tana magana... "Daddy, ka ga Aunty Maayah ko? Ai ni na san me ya sa hakan ta faru. Kullum tana cikin fushi-fushi da masifa-masifa a zuciyarta, shi ne injin ya yi kaca-kaca da ita ya yar da ita ƙasa." Kowa a ɗakin ya yi shiru.. Chingching ta nuna wa bayinta alamar su ajiye abubuwan da suka kawo.. "Ga fure na kawo miki Aunty Maayah, don idan kika kalle su kya ji sanyi. Amma gaskiya ki daina gudun nan, ni gashi ina zaune ina kallon katun ɗina, amma babu abin da ya faru da ni." Ta ƙara matsawa daidai kunnenta ta raɗa mata.. "Kiyi haƙuri kin ji? Amma idan ba za ki iya tashi ba, inaso duk takalmanki masu bala'in tsayin nan ki kwaso mun su...." Daga nan ta juya, ta yi nuni ga bayinta, suka fita tana ta rangwaɗa sannan ta cigaba da waƙar ta, ta bar Maayah tana huci, ranta ya ɓaci fiye da yadda jikinta yake ciwo... Sarki ya dafe kansa, ya san cewa halin Chingching sai dai addu'a... "Maayah, kiyi haƙuri... yarinya ce," ya ce a hankali. Amma Maayah a ranta tana faɗin... "Wallahi idan na tashi, Chingching za ki san kin shigo ɗakina kin mun rashin kunya!"..... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣1️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Bayan ficewar Chingching ɗakin ya ɗan yi tsit, amma sanyin iskar ya sauya yayin da aka fara jin takun takalmin Gimbiya Zayana.. Ba surutu, ba hayaniya sai kawai ƙamshin turarenta mai tsada wanda ya riga ta shigowa ɗakin.. Zayana ta shigo ɗakin da takun alfarma, kanta a ɗage tamkar ba ta son taka ƙasa. A bayanta wasu bayinta ne guda uku sanye da kaya masu kyau, kowaccensu tana riƙe da tiren azurfa dake maƙil da zaɓaɓɓun fruits waɗanda aka yanka su cikin fasaha.. Zayana ta tsaya nesa kaɗan da gadon Maayah, ta nannaɗe hannuwanta a ƙirji tana kallon Maayah da wani irin kallo na isa da kuma tausayi mai haɗe da izgilancu. Ba ta zauna ba domin ita a ganinta zama a gefen gadon mara lafiya ƙasƙanci ne.. "Ashe abin har ya kai ga kwanciya, Maayah?" Zayana ta furta cikin muryarta mai sanyi dake soka mutum tamkar kibiya... Maayah ta ɗaga kanta da ƙyar, idanunta suka sarƙe da na Zayana. Duk da ciwon dake jikinta, ba ta bar izzarta ta fito ba. Ta haɗe rai ta ce, "Kamar yadda kika gani Aunty Zayana. Amma kada ki damu, wannan kwanciyar ta ɗan lokaci ce. Ba zan ba ki farin cikin ganina a haka har abada ba." Zayana ta yi murmushin mugunta, ta nuna wa bayinta alamar su ajiye tiren fruits ɗin. "Na kawo miki waɗannan ne don su ƙara miki ƙarfi. Na ji ance faɗuwar taki ta yi muni, har ana zargin ƙashin bayanki ya samu matsala. Gaskiya ya kamata ki riƙa sani cewa jikinki ba na ƙarfe ba ne, akwai abubuwan da suka fi ƙarfinki." Zayana ta ƙara takawa kusa da gadon, ta sunkuya kaɗan ta yadda Maayah kaɗai za ta ji abin da za ta faɗa.. "Kina ta gudun neman Inuwa, gashi Inuwa ya jefar da ke. Yanzu wa zai zama gwarzon fada tunda jarumar gidan tana kwance tana kuka?". Maayah ta cije laɓe, ran ta ya ɓaci matuƙa... "Fita ki ba ni wuri Aunty Zayana! Bana buƙatar fruits ɗinki, kuma bana buƙatar tausayinki na ƙarya.".. Zayana ta miƙe tsaye tana gyara riga, ta kalli mahaifinsu dake gefe ta gaishe shi cikin girmamawa sannan ta juyo ga Maayah.. "Kiyi sauri ki warke... Masarautar tana buƙatar hayaniyarki. Amma kafin nan, ki ji daɗin kallon rufin ɗakin nan." Ba tare da ta sake cewa uffan ba, ta juya ta fice daga ɗakin, bayinta suna biye da ita. Ta bar Maayah tana jin wani irin ɗaci a ranta, domin kalaman Zayana sun fi allurar Doctor zafi... Sarki Nourdeen ya ja numfashi, ya kalli Maayah ya ce, "Ku daina haka, gimbiyoyi ne ku fa..." Amma Maayah ba ta ko saurare shi ba, ta juya kanta gefe tana kuka, kukan takaicin yadda kishiyoyinta na gidan sarauta suka zo suna ganin rauninta... Bayan ficewar Zayana, ɗakin ya rage saura ɗacin kalaman da ta bari... Maayah tana kuka ranta ya ɓaci, tana jin tamkar kowa ya tsane ta. Sai dai kwatsam sai ga Gimbiya Yumna ta shigo... Yumna ba ta zo da takun alfarma ko takun nuna mulki ba. Ta shigo ne tare da bayinta guda hudu waɗanda kowa ya sani ba bayinta ba ne kawai a wurinta, ƙawayenta ne.. Suna hira cikin kulawa har suka shigo ɗakin.. Ganin Maayah a kwance cikin wannan halin, idanun Yumna suka cika da kwalla nan take. Ta bar sauran bayin nata a baya, ta ƙarasa da sauri har gaban gadon Maayah... Ba tare da bata lokaci ba Yumna ta durkusa a kasa a gefen gadon, ta kama tafin hannun Maayah tana murza su a hankali, tana kallon fuskarta cikin matukar damuwa da tausayi.. "Aunty Maayah, dan Allah kiyi hakuri," ta fada cikin muryar kuka, "Wallahi tun da na ji labarin hatsarin nan, hankalina ya tashi. Allah Ya baki lafiya, Allah Ya kawo miki sauki..." Maayah ta kalli Yumna. A karon farko ta ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta. Ta lura cewa Yumna ba ta zo domin yi mata gatsali ko nuna mata gazawarta ba.. ta zo ne da gaskiyar zuciya... Kodayake Maayah mutum ce mai girman kai, amma ta kasa kwace hannunta daga cikin na Yumna.. "Yumna... na gode," ta faɗa a hankali, muryarta a sanyaye.. Yumna ta cigaba da murza hannun ta, tana kokarin sanya mata kwarin gwiwa... "Kada kiyi kuka, Doctor ya ce za ki warke. Kuma zan riƙa zama dake ina taya ki hira har sai kin tashi. Duk abin da kike bukata, ki fada min zan sa a shirya miki." Sarki wanda yake kallon dambarwar da ta faru tun daga kan Chingching, Zayana, har zuwa kan Yumna, ya sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya. Ya ji daɗi ganin yadda Yumna ta sanyaya ran ƴar uwarta... Bayan Yumna ta gama rarrashi, ta sa bayinta suka ajiye duk wasu kayan bukatu da suka kawo sannan ta sake sumbatar hannun Maayah kafin ta miƙe... ✨✨✨ Washegari da safe, masarautar tana cikin wani yanayi na daban. Ayat tana cikin babban ɗakinta, yau ma ta riga ta kammala shigarta ta mazaje, tana duba takobinta da sauran kayan aikinta... Saratu wadda ita ce amintacciyar ma'aikaciyar ta tana tsaye a wajen kofar dakin tana magana, domin Ayat ta kulle kofar yadda babu mai shigo wa... "Gimbiya! Labari ya iso cewa halin Gimbiya Maayah ya tsananta. Faduwar jiya ta taɓa ƙashin bayanta sosai. Yanzu haka ana shirin fita da ita kasar Indonesiya domin neman lafiya a manyan asibitocinsu," Saratu ta fada cikin damuwa. Ayat tana zaune, ta gyara rawuninta sannan ta amsa ta cikin kofa.. "Allah Ya ba ta lafiya.... Saratu ki haɗa kai da sauran ma'aikatana ku kai mata gaisuwa, na wakilce ku gaba ɗaya. Ku faɗa mata cewa idan sun dawo daga kasar wajen zan duba ta da kaina. Yanzu ina da ayyukan da zan kammala ne." Saratu ta amsa da "To shikenan Gimbiya," sannan ta juya ta tafi domin cika umarnin... Bayan jin tafiyar Saratu, Ayat ba ta bata lokaci ba. Ta nufi ɗakin sirrinta, ta danna madannin da ya buɗe mata elevator. Ta lula can karkashin kasa, ta bi dogon ramin nan dake cike da sirri har ta fito ta tsakiyar lambun masarauta inda iskar safe ta bugi fuskarta. Ta fara nata takun domin fita wajen masarautar... A ɗaya ɓangaren kuma, ɓangaren Gimbiya Maayah ya cika da ma'aikata da fadawa. Saratu da sauran ma'aikatan sun iso inda suka tarar da yanayin cike da sauri-sauri... Sarki yana tsaye fuskarsa cike da damuwa. Ko da yake shi ba zai tafi ba saboda nauyin sarauta da kuma matsalar Pavilion dake tunkaro shi, amma ya haɗa dukkan abubuwan da ake bukata. Wani babban jirgi na alfarma yana can yana jiran su a filin jirgin masarauta... Yumna wacce ta ƙara ziyartar Maayah tana gefen gadonta, tana rike da hannun Maayah. Ganin yadda ake shirin tafiya, Yumna ta kasa jurewa. Ta kalli mahaifinta sannan ta ce cikin damuwa "Abul, dan Allah ka ba ni izini in bi Aunty Maayah. Ba zan iya zama a nan ina tunaninta ba. Ina son in kasance kusa da ita har sai ta samu lafiya.".. Sarki ya kalli Yumna, ya san dacewar zuciyarta. Ya jinjina kai sannan ya ce, "Na yarda Yumna. Ki tafi ki kasance kusa da ita." Haka aka shirya komai cikin kwarewa. An ɗauki Maayah a kan stretcher domin kada kashin bayanta ya motsa... Wasu rantsattsun ma'aikatan fada da dakarun tsaro wato Special Guards suka bi bayansu domin basu kariya a kasar wajen... Motocin asibiti na alfarma suka dauke su zuwa inda jirgin yake, yayin da masarautar ta yi tsit, kowa yana addu'ar samun lafiya ga gimbiyar da kowa ya sani da takama, amma yau gashi rashin lafiya ya kwantar da ita... Yayin da aka kwashe Maayah aka nufi filin jirgi, ɗakin taron fada da sashen ma'aikata ya cika da raɗa da surutu. Ma'aikata da dama sun fara tofa albarkacin bakinsu... "Wai kun lura? Duk gimbiyoyin gidan nan sun zo ganin jikin Maayah, har da su Chingching da Zayana da ba su shiri, amma ban ga Ayat ba," in ji wata baiwa.. Wani bafade ya amsa, "Gaskiya ne, abin da ban mamaki. Ko da yake ta aiko Saratu amma ai kamata ya yi ta zo da kanta tunda tafiyar waje ce." Hatta Maayah tana kwance a cikin motar asibitin, zuciyarta cike take da takaici. Duk da ciwon dake jikinta maganar Ayat ta tsaya mata a rai. Ta lura cewa duk wanda take gani a matsayin ƙashin wuyanta ya leƙo ta, amma Ayat wadda take ganinta a matsayin mai nutsuwa, ita ce ta nuna mata halin ko-in-kula... Ba su sani ba, Gimbiya Ayat tana nan kusa amma ba a matsayin gimbiya ba... Tana sanye da shigar Inuwa tsaye a lokacin da aka fito da Maayah.. Ta kuma ga damuwar dake shimfiɗe a fuskar mahaifinsu.. Ayat ta sauƙe wani nauyayyen ajiyar zuciya. Ba wai ba ta jin tausayin Maayah ba ne, a'a, zuciyarta tana cike da wani nauyi ne wanda ba za ta iya bayyanawa kowa ba... "Allah ya ba ki lafiya Maayah," ta faɗa a hankali cikin muryarta ta Inuwa.. A cikin jirgin kuwa, Maayah tana kwance a sashin gaggawa na jirgin ICU section, Yumna tana zaune a gefenta tana mata addu'a... "Aunty Maayah, ki daina tunani kinga har mun fara tafiya,".. Maayah ta kalli Yumna, sannan ta cije laɓe.. "Yumna, kin ga Ayat kuwa kafin mu fito?" Yumna ta yi shiru, ta kasa cewa komai sai daga bisani ta ce, "A'a Aunty, amma ta aiko Saratu..." "Saratu ba Ayat ba ce," Maayah ta katse ta cikin fushi. "Idan na dawo, zan nuna mata cewa ni ma na san darajar kaina.".. ✨✨✨ Bayan ficewar su Maayah, Gimbiya Ayat ba ta tsaya wata-wata ba. Ta nufi ɓangaren dawakai, ta hau dokinta ta fice daga masarautar Alhamra da gudu. Zuciyarta tana muradin isa babban kogin da ta saba zuwa, domin ta kwana biyu ba ta leƙa wurin ba... Tayi tafiya mai nisa, iskar daji tana dukan fuskarta har ta isa bakin kogin. Ta sauka daga kan dokin, ta shafa bayansa alamar rarrashi sannan ta nufi gaban ruwan. Bayan ta duba tsuntsuwarta ta ga tana lafiya, har ma ta tafi yawonta ta bar kananan ƴaƴanta, Ayat ta tsaya tana nazari... Hoton Maayah a kwance cikin jinya ya dawo mata, tana jin wani irin yanayi a ranta.. Kwatsam, waigawar da za ta yi, sai idanunta suka sauka a kan abin da ba ta yi tsammani ba... A can nesa kaɗan ta hango wannan mutumin mai farin gashi. Yana tsaye a bakin wani katon rami, wurin magudanar ruwa inda ruwa yake zuba da karfi. Kowa ya san wannan ramin, rami ne mai zaman kansa wanda duk wanda ya faɗa ciki, mutuwa ce kawai take jiran sa, domin ba ya fito wa... Mutumin ya juya baya, yana kallon yadda ruwan yake gangarawa cikin wannan zurfin. Dogon gashinsa dake ta sheƙi yana kaɗawa a iska... Wani murmushi na mugunta ne ya bayyana a fuskar Ayat. Ta ce a ranta, "Yau ce ranar da zan raba ka da wannan kwarjinin naka.".. Ta fara zaro takobinta a hankali, gudun kada ya ji motsinta. Idonta yana kansa tamkar mikiya, amma a cikin hanzarin zarowar takobin, sai takobin ta yanke tsakiyar tafin hannunta.. "Ahh!" Ta saki wani ɗan ƙaramin ƙara saboda raɗaɗi, cikin sauri ta kai ɗaya hannun ta toshe bakinta tana zaro ido, tana fargabar kada ya ji. Jini ya fara zuba daga tafin hannunta, amma ba ta ma kula da hakan ba. Wani irin kishi da fushi ne ya rufe mata ido... Ta ruga da gudu tana nufar kansa, takobinta a ɗage sama. Niyyarta guda ɗaya ce, ta sare masa wuya a yanzu tunda bai san da zuwanta ba. Tana isowa, ta kai masa wani mahaukacin sara a saitin wuyansa... Cikin wani irin salo da kwarewa dake nuna ba ɗan Adam ba ne, mutumin ya ɗan sunkuyar da kansa ba tare da ya juyo ya kalle ta ba. Takobin ta wuce, amma maimakon wuyansa sai takobin ta yanki tafin hannunsa shima, daidai inda ita ma take da ciwo.. Ganin bata sare shi ba, ga kuma yadda hannunsa ya yanku, firgici ya sa Ayat ta rasa inda za ta taka. Ƙarfin sarar da ta yi ya sa ta kasa saita tsayuwar ta, takobin ta subuce mata, ƙafa ɗaya ta zamile... "Aaaaaaaahhhhhhhh!!!!" Wani irin uban ihu ta saki yayin da ta tafi sama, ta faɗa kai tsaye cikin katon ramin nan dake zuba da ruwa. Zurfin ramin ya sanya ihunta yake ƙara nisa yana ɓacewa... Yayin da take sulalewa cikin ramin, tana ihu mai nuna cewa rayuwarta ta zo karshe, fararen idanun mutumin nan suka canza launi, suka koma shuɗi mai tsananin sheƙi. Wani irin haske mai launin shuɗi ya bayyayna, ya mamaye sararin ramin... Kafin ma jikinta ya taɓa ruwan dake karkashin ramin, King Diamond ya yi wani uban tsalle ya riga ta isa ƙasa, ya sa hannu ya rugume ta... Abin al'ajabi ba su faɗa cikin ruwan ba, kuma ba su yo sama ba kawai sai suka tsinci kansu suna shawagi a cikin iska, hasken shuɗin nan ya zame musu garkuwar dake riƙe da su... A cikin wannan yanayin, lips ɗinsu ya haɗe wuri ɗaya, suka shiga wata zazzafar sumbata mai cike da sirri. King Diamond ya haɗe tafin hannunsa mai ciwo da nata mai ciwon, ya harɗe yatsunsu ta yadda jinin da yake zuba daga hannayensu ya gauraye, ya zama guda ɗaya. Ɗayan hannunsa kuma yana riƙe da ƙunƙuminta ta baya, suna yawo a sararin iska idanunsu a lumshe... Bayan wani lokaci, ya buɗe idanunsa waɗanda suka zama shuɗi tsantsa. Ita ma ta buɗe nata, idanunsu suka sarƙe. Nan take Ayat ta dawo cikin hayyacinta, ta kawar da kai tana sakin wani irin ihu na firgici!.. ✨ Nan take hasken ya ɓace, suka bayyana a kan doron ƙasa a bakin kogin. Amma wani babban al'ajabi ya faru... Sun yi musayar siffa wato Body Swap!.. King Diamond ya koma asalin siffar Ayat. Yana tsaye sanye da kayan gimbiyanci na alfarma, sumar gashinsa na Ayat ta bazu har gadon baya, kyawun fuskarsa a bayyane yake radau babu rufin fuska ko gilashi... Ita kuma asalin Ayat, tana sanye da siffar King Diamond. Tana kwance a ƙasa ta kifa kanta, farin dogon gashin dake kanta ya zube har gadon baya, sanye da fararen kaya irin na aljanu.. King Diamond dake cikin siffar Gimbiya Ayat ya kalle ta, ya yi magana da muryarta ta mace mai zaƙi.. "Sannunka..." Ayat dake kife da fuska ta ji muryar mace, kuma muryar tata ce! Ta ɗago da sauri ta kalli wacce take tsaye a kanta. Tana ganin siffarta da fuskarta da take ɓoyewa, ta miƙe da sauri tana zaro ido, ta ce. "Wacece ke mai kamar siffata?!" Ba zato ba tsammani, Ayat ta yi shiru. Ta lura cewa maganar da ta yi, ba da muryarta ta yi ta ba! Da muryar King Diamond take magana, muryar namiji mai kwarjini. Ta dafe maƙogwaronta cikin firgici "Ya muryata haka? Me ya faru da ni?!" Asalin King Diamond dake cikin siffar Ayat ya yi wani ɗan tsafi da hannunsa, nan take wani madubi ya bayyana a gabanta. Ya haskaka mata fuskarta.. Ganin kanta a cikin madubi ta koma siffar abokin gabanta, ta fara zunduma uban ihu amma ihun namiji ne yake fita daga bakinta!. Ta kamo gashin kanta tana kallo, ta ga farin gashi ne radau, jikinta kuma fararen kaya... Cikin hargitsi ta nuna shi da yatsa tana faɗin "Kai mugun aljani ne! Ta yaya ina mace za ka ba ni siffarka? Wannan siffar marar kyau! Sannan ka karɓi tawa siffar?" Ba zato ba tsammani ta tuna wani abu, ta ƙara fusata.. "Kalli fuskata a buɗe! Ni fa bana buɗe fuskata idan ina a matsayin gimbiya, amma ka bar min ita a buɗe! Ka koma siffata kuma ka bar fuskata a waje kowa ya gani!" Ta rasa inda za ta sa kanta, yayin da shi kuma yake kallonta da muryarta yana mata murmushi... 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ⚠️ SANARWA⚠️ Wannan littafi dukiyata ce a matsayina na marubuciya. ⚖️ Ba a yarda wani ko wata ya: kwafa gyara sauya ko amfani da wani sashe na wannan labari ba tare da izini na kai tsaye ba. Duk wanda ya saɓa, alhaki yana kansa.. ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 1️⃣2️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* Ayat dake cikin siffar King Diamond ta kasa daina duba hannayenta da fararen kayanta. Wani irin kishi da haushi ne yake turnuƙe ta. Ta matso kusa da shi tana huci, muryarta dake fita irin ta namiji yana dukan duwatsun dake wurin... "Ka maida ni yanzu! Na ce ka maida ni!"... Ta damƙi wuyan rigar dake jikinsa, rigarta ta gimbiyanci wadda take matuƙar so. "Wallahi ba zan motsa daga nan ba, kuma ba zan tafi ko'ina ba har sai na dawo siffata ta mace. Ba zan iya rayuwa a cikin wannan siffar taka mai ban tsoro ba!" King Diamond dake cikin siffar Ayat, ya yi murmushin nan na Gimbiya Ayat mai kyan gani, ya haskaka fuskarsa wadda take sheƙi. Ya sanya hannunsa ya ɗan shafa dogon gashin dake kansa, sannan ya ce da muryarta.. "Aayat, kiyi haƙuri. Wannan ba nufina ba ne, haɗuwar jininmu ne ya janyo hakan. Kuma ki sani, ko ni ma ina son siffata, amma yadda kike a yanzu kinfi kowa kyan gani a idona." Ayat ta ƙara fusata, ta ji tamkar tana faɗa da kanta ne a madubi ta ce, "Kayi mun shiru! Kar ka sake magana da muryata! Kuma kar ka sake ƙirana da sunana da wannan muryar!" Ta juya tana kallon magudanar ruwan, tana tunanin ta yadda za ta koma masarauta... "Ta yaya zan koma gida a haka? Master Ibrahim ya san ni a matsayin Inuwa, mahaifina ya san ni a matsayin Ayat. Idan na shiga masarautar nan a siffarka, kashe ni za a yi!" King Diamond ya matso kusa da ita, ya ɗora hannunsa a kafaɗarta. "Ni kuwa ina son kasancewa da ke a haka. Ina son in ga yadda za ki yi amfani da ikona, kuma ina son in ga yadda zan rayu a cikin takurarki. Ba zan maida ke ba yanzu ba domin ina jin daɗin yadda jininmu ya sarƙe."... Ayat ta buge hannunsa dake kan kafaɗarta da ƙarfi. "Ba zan tafi ba! Kuma ba zan bari ka tafi ba! Za mu zauna a nan har sai wannan sihirin naka ya karye. Ba zan zama namiji ba, ba zan zama aljani ba!"... Haka suka ci gaba da tsayawa a bakin kogin, iska tana kaɗawa. Ayat tana ta kai-komo tana zage-zage da muryar namiji, shi kuwa yana tsaye yana kallonta da fuskarta, yana jin daɗin yadda ya samu damar kasancewa da ita ta wannan hanyar... ✨✨ Dare ya tsala har ƙarfe 10, duhu ya lulluɓe kowane sashi na dajin dake kewayen kogin. A lokacin King Diamond ya haskaka wurin da wani irin koren haske na sihirinsa, wanda ya sanya wurin ya zama tamkar a cikin almara yake. Duk da kyawun hasken, zuciyar Ayat dake cikin siffar namiji tana tafasa da wani irin zazzafan fushi da firgici... King Diamond yana tsaye a mutum-mutumi, bai ce uffan ba hakan ne kuma ya ƙara rura wutar fushi dake zuciyarta. Ta ɗaga kai ta kalle shi, idanunta cike da tsananin ƙiyayya da tsoro a haɗe... “KAI!!” ta daka masa tsawa, muryarsa mai nauyi dake fita daga makogwaronta ya sa ta tsorata da kanta... Ta miƙe tsaye tana fuskantarsa.. “Me kake son aiwatar mun? Me ka ke so kayi da rayuwata, kai mugu?!” Ta fara zagaye kanta da hannu cikin hauka, tana janyo dogon farin gashin dake kanta wanda yanzu nata ne, tana kuka kamar yarinya karama.. “Na rantse zan kashe ka! Wallahi zan sare ka idan har ka maido min da jikina!” Cike da raɗaɗi, ta durkushe a ƙasa da ƙarfi, tana bugun ƙasar da hannuwanta masu faɗin gaske.... “NA TSANE KA! NA TSANE KA!! NA TSANE KA!!!” Ihun nata yana dukan duwatsun dake bakin kogin, yana dawo mata da sautin namijin da ba ta son ji, abin da ya sa ta ƙara razana... A wannan lokacin ne King Diamond ya ɗaga girarsa ɗaya cikin natsuwa. Ya fara takowa a hankali, takunsa ba shi da sauti tamkar iska, har ya tsaya a gabanta yana kallonta daga tsaye... Da muryarta ta mace mai sanyi, ya ce.. “Ki daina ihu.”.. Ta daka tsalle ta miƙe tsaye tamkar wadda wuta ta taɓa.. “KAR KA ƘARA MAGANA DA MURYATA!!” ta faɗa tana toshe kunnenta... “Na tsane jin muryata tana fita daga wannan bakin naka!” Ta juya da gudu kamar tana son tserewa daga wurin, amma sai ta tsaya cak bayan taku kaɗan. Ta kalli hannuwanta, faɗaɗin kafaɗunta, da nauyin jikin da take ɗauke da shi. Ta sake fashewa da kuka mai cin rai... Ta sake faɗuwa ƙasi tana kuka. “Me zan yi da wannan kaskantaccen jikin naka? Ta yaya zan koma fada a haka? Ta yaya zan kalli idon mutane?”... King Diamond ya zo tako yanda take sannan ya sunkuyo kaɗan domin ya daidaita fuskar sa da tata. Yana kallonta da wani irin yanayi na nazari, babu fushi a tare da shi.. “Kin zo ne ki kashe ni,” ya faɗa cikin sanyin muryar mace, “amma kin ga abin da kaddara ta yi.” Ayat ta girgiza kanta cikin galaita... “Wannan ba kaddara ba ce! Wannan mugunta ne! Kayi amfani da tsinanniyar sihirinka!” Ta ci gaba da jan sumar kanta tana kuka. “Mayar min da jikina... dan Allah... dan Allah ka mayar min da siffata...” King Diamond ya tsaya yana kallonta na wasu dakikoki. A karon farko wani baƙon abu ya motsa a kwayar idonsa. Wani irin yanayi ne na sha’awa da mamakin yadda kaddara ta hada su... “Yanzu,” ya raɗa mata a hankali, “zaki ji yadda nake ji tun lokacin da na ɗora idona

Chapter 9 of 39