Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rasa ka kenan...me ya sa ka tafi a wannan lokacin?" ta furta cikin murya dake rawa... Ta jima a haka, tana kuka na tsawon kusan minti talatin, tana jin tamkar rayuwarta ta rage amfani tunda ta rasa abokin hirarta kuma garkuwar zuciyarta... Can sai ga kuliya ya bayyana a gabanta.. Muryar kuliyar dake fitar da wani siririn sauti ya sa Ayat ɗago kanta da sauri. Tana ganin Reems a gabanta, zuciyarta ta cika da farin ciki... "Reems!" ta faɗa tare da miƙewa da sauri don ta rungume shi. Amma kafin hannunta ya kai gare shi, sai wani zazzafan haske ya bayyana, tare da wata guguwa mai ƙarfi da ta tada furannin lambun sama. Ayat ta sa hannu ta rufe fuskarta saboda ƙura da ƙarfin hasken da ya kusan makantar da ita. Bayan hasken ya lufa, ta sauƙe hannunta a hankali, tana addu'ar kada abin da take zargi ya zama gaskiya... Idonta ne ya sauƙa akan abin da ya fi kowane tsoro.. Mutumin nan mai farin gashi!.. King Diamond ne tsaye a gabanta, yana mata wani kallo mai cike da mallaka da isa. Ayat ta zazzaro manyan idanunta, kyakkyawar fuskarta ta bayyana tsantsar firgici....Sai da ta ƙare shi da kallon sama da ƙasa, sannan ba tare da ta tsaya wata-wata ba, ta buɗe ƙaramin bakinta ta saki wani uban ihu ta juya da gudu, tana son barin lambun kafin zuciyarta ta buga... Gudun Ayat bai kai ko ina ba, domin kafin ta ankara, King Diamond ya ɓace ya sake bayyana a gabanta... Saboda ƙarfin gudun da take yi, ta kasa tsayawa, sai kawai ta faɗa kan faffaɗan ƙirjinsa dake da ɗumi. Firgicin taɓa shi ya sa ta yi baya da sauri tana shirin faɗuwa ƙasa, amma ya miƙa hannunsa mai ƙarfi ya cafko hannunta, ya tsayar da ita kyam a gabansa... A wannan lokacin, King Diamond ya sauya siffarsa zuwa asalin siffar Sarkin Power Pool. Yana sanye da fararen kaya na alfarma masu ratsin zinare da gwal. Sumar kansa fara sol an tuƙe ta a tsakiyar kansa da wani ƙarfen gwal, fuskarsa tana fitar da wani haske mai ban mamaki sakamakon tsantsar farin jikinsa.. Duk yadda Ayat take da kyau, a wannan lokacin ta ji kwarjininsa ya kusan danne nata. Ya kura mata ido, yana kallon yadda fuskarta take sheƙi ba tare da mayafi ba, yayin da ita kuma take tsaye jiki na ɓari. Duk da bugun zuciyarta da ya kusan kayar da ita, Ayat ta dake. Ta tsaya kyam tana kallon cikin idanunsa, hannunta dake cikin nasa yana rawa. Ta kasa magana, amma idanunta suna tambayarsa.. "Shin duk wannan lokacin, kai ne kuliya ta? Kuma kai ne ka ga duk abin da na ɓoye?" King Diamond ya matsa kusa da ita, numfashinsa yana dukan fuskarta, ya raɗa mata cikin muryar sa mai cike da kwarjini.. "Ayat... Shin yanzu kin yarda cewa babu inda za ki iya ɓuya min?"... Ta fizge hannunta daga nasa, tana kallonsa daga sama har ƙasa, idonta cike da ruɗani da tsoro... Ya ɗan saki murmushi, ya ce cikin natsuwa, “Meyasa kika firgita haka? Ni ne Reems.” Cikin mamaki, muryarta na rawa, ta ce, “Reeeems…?” Ya gyara tsayuwarsa, ya ce, “Ke kika sa min wannan sunan. Amma sunana na gaskiya King Diamond.” Ta zazzaro ido, zuciyarta na bugawa da ƙarfi... “Kana nufin… kai ne kuliyar da na ceta?” Ya girgiza kai a hankali... “Ni ba kuliya ba ne. Ni Aljani ne. Amma meyasa kika tsorata bayan na nuna miki kaina? Shin ba ni kika zo nema ba?” Cikin fusata da kunya, ta ɗaga hannu, ta zabga masa mari sosai... Kan sa ya juya gefe sakamakon marin. Ya dawo ya kalleta kai tsaye, ba tare da ya nuna fushi ba.. Hawaye suka cika idonta. Ta fara lissafa masa duk abin da ke ranta, muryarta na rawar baƙin ciki... “Na cire kaya a gabanka. Na ci abinci da kai. Na ɗauke ka a cinyata. Abu mafi muni ma, na kwana gado ɗaya da kai! Ka cuce ni! Na yi nadamar sanya maka sunan Reems ɗina... Wallahi kai shaiɗani ne!” Murmushi kawai ya yi, yana kallonta kamar komai bai dame shi ba... “Kin ceci rayuwata. Kin ciyar da ni. Ina so in biya ki. Da me kike so na biya ki?” Cikin tsananin fusata ta ce, “Ba na son komai naka! Kuma ka fita daga rayuwata!” Ya girgiza kai. “A’a. Dole ne in biya ki taimakon da kika yi min.” Ta yi tsaki. “Ni ba abin da nake so.” Ta wuce ta gefensa zata tafi, amma sai ta tsaya cak. Ta juya ta kalli bayansa, shi kuma yana kallon yadda ta tsaya kafin... “Akwai wani abu…” ta ce.. “Za ka iya zuwa ka ɗauke min kundirmon nono da na siya maka. Ya ishe ni da wari.” Ya juyo ya kalleta, ya ce cikin sanyin murya, “Ai ba ki ba ni shi ba. Shin ba zaɓinki ba ne?” Ta harare shi... “Kana so ne, shi ya sa na siya maka!” Ya ɗan murmusa... “Tooo… wato kin siya min.” “Eh! Da kuɗina! Kuma yana da tsada!” Ya katse ta. “To meyasa baki tambaye ni ko ina so ba?” Cikin tsawa ta ce, “To wa ya yi tunanin kuliya na magana?!” Sannan ta ƙara da tsauri, “Kada ka manta ka je ka fitar min da shi.” Ta juya zata wuce. Sai ya ce, “Kin manta kin fito ba tare da abin rufe fuskarki ba.” Da sauri ta ɗaga hannu tana shafa fuskarta, nan ta tuna ashe da gaske ba ta fito da mayafin fuska ba. Hankalinta ya tashi... Sai ya miƙa mata gyalen rigarta da take rufe fuska da shi.. Cike da mamaki ta ce, “Yaushe ka ɗauko shi? Kuma ta yaya bayan kana tsaye ba tare da mayafin ba?” Ya ce cikin natsuwa, “Kar ki manta, ni Aljani ne.” Ta fizge gyalen daga hannunsa, tana hararansa cikin shakku. Ta yamutsa fuska tana kokkoyan abinda yace.... ta ce, “Kai ki manta ni aljaji ne” Ta zazzaro masa ido, ta rufe fuskarta da gyalen, sannan ta juya ta tafi da sauri... fuuu! kamar ana tura ta da ƙarfi.. Saboda wurin self-secret ne, lambun yana rufe da tsaro sosai, ba a jin komai daga can cikin part. Saboda haka, ihun da ta yi babu wanda ya ji shi… ✨✨✨ Pavilion City Washegari da asuba, hasken rana ya fara ratsa labulen ɗakin Ching Ching. Tana cikin baccin shagwaɓa, babbar yatsanta a baki tana mafarkin tana masarautarsu ana rarrashinta, Uma Altine tana mata wanka kwatsam sai ta ji wani sanyayyan abu ya taɓa ƙafarta... "Lokacin tashi ya yi, Shugaba Ching Ching." Muryar Gely ce ta fito a sanyaye, babu alamar wasa... Ching Ching ta ƙara jan bargo ta rufe kanta tana gunaguni... "Ke rabu da ni! Ƙarfe nawa ne ma? Kin san ba a tashi na da wuri haka?" Gely ba ta bata amsa ba, sai kawai ta danna wani maballi a bango, nan take labulen ɗakin ya buɗe gaba ɗaya, hasken rana ya cika ɗakin... Kafin Ching Ching ta farga, Gely ta yaye bargon ta miƙa mata mopper da bokiti... "Boss yana jiran karin kumallo... Kuma kamar yadda ya ce, ni zan jagoranci aikinki. Yanzu, ki tashi ki gyara ɗakin nan, sannan ki tafi kitchen ki karɓo abincinsa ki kai masa dining..." Ching Ching ta tashi zaune gashinta duk ya hargitse, ta kalli Gely da ɓacin rai... "Daga tashi har kin fara? Ke baki san ana sallah bane? In ke arniya ce to baki san ana wanke fuska ba ne?"... "Na baki minti biyar kacal," Gely ta faɗa tana kallon agogon jikinta.. Kai tsaye sashen Chief, Gely ta nufa..ta iske shi yana shirin shiga wanka.. "Boss, yanzu Ching Ching zata yi sallah kafin ta fara gudanar da aiki..." "What? Sallah yanzu?..." Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe takwas har ta wuce, ya girgiza kai ya ce, "Daga yau, kina tashinta ƙarfe biyar tayi sallah..." Ta amsa masa cikin girmamawa, daga nan ya shige bathroom yana ɗaure da towel a ƙugunsa.... Bayan minti biyar, Ching Ching ta fito tana ta tura baki, tana sanye da kayan aikinta... Gely ta tsaya a kanta, tana sanya ta goge kowane saƙo na falon. Duk sanda Ching Ching ta yi ƙoƙarin ƙin yin aikin, Gely sai ta matso kusa da ita da idanunta masu hasken ja, nan take Ching Ching take tunawa da shaqar jiya, ta cigaba da aikin tana kuka kasa-kasa... Zuwa ƙarfe tara da rabi... A bangaren Dining Area... Chief Onyx ya fito sanye da rigar bathrobe, gashinsa a jiƙe alamar ya fito daga wanka. Ya zauna a kan dining yana jiran abinci... Can sai ga Ching Ching ta fito daga kitchen tana turo tiren abincin, Gely tana biye da ita a baya kamar tana korar shanu... Ching Ching ta zo gaban Chief, ta ajiye masa abincin cikin ɓacin rai, har kofin shayin yana neman zubewa... "A hankali mana, Shugaba Ching Ching," Gely ta faɗa cikin muryar robot... "Kuma ki durƙusa ki gaida Boss yadda ya kamata." Ching Ching ta zaro ido, ta kalli Onyx tana neman taimako... "Uncle Onyx! Dubi yadda take sanya ni aiki kamar baiwa! Har gaidaka sai na durkusa?" Onyx ya ɗauki jaridarsa ya fara dubawa ba tare da ya kalleta ba... "Gely ce take da iko da ke yanzu. Duk abinda ta ce, shi za a yi." Ching Ching ta ji ranta ya ɓaci, ta kalli Gely wadda take kallonta da wani irin mugun murmushi... Ta cije leɓe, ta duƙa kaɗan a gaban Onyx... "Ina kwana..." Onyx ya kalle ta daga bayan jaridarsa, ya ga yadda idanunta suka cika da shagwabar nan tata mai sanya zuciya narkewa... "Lafiya lau. Yanzu ki zuba min shayin.".. Ching Ching ta fara zuba shayin, amma da gangan ta karkatar da hannunta ta zubar da rabin tea a kan rigar Chief Onyx!... "Ayyah! Yi hakuri Uncle! Hannuna ne ya yi sanyi," ta faɗa tana ƙoƙarin goge masa da kwalin kanta, tana sanya kirjinta yana gogayya da kafaɗarsa... Gely ta matso da sauri, ta ture hannun Ching Ching... "Ni zan gyara wa Boss. Ke kuma, je ki wanke duk kwanonin da aka yi amfani da su a kitchen, duka da hannunki, ba tare da amfani da na'ura ba!"... Ching Ching ta fashe da kuka... "Uncle! Kaga abinda take yi min ko? Wallahi na tsani wannan gwangwanin!" Ta ruga kitchen tana kuka tana shura ƙafa... Onyx ya kalli Gely, ya ga yadda idanun Gely suka sauya launi zuwa ja na wucin gadi sa'ilin da Ching Ching ta taɓa shi... Ya fahimci cewa wannan biyayya ta Ching Ching ta zama filin daga ne na kishin Gely... Ching Ching tana shiga kitchen, ta tarar da ƙaton falon kitchen ɗin cike da Robots masu girki waɗanda suke ta aiki ba ji ba gani... Ta kalli tarin kwanukan da Gely ta ce ta wanke, ta murguɗa baki... "Wai ni Gely za ta sanya aiki? To za ta gani. In har ni Gimbiya ce, to yau sai na ruɗa duk tsarin gidan nan!" Ta san cewa Gely tana kallon komai ta hanyar kyamarorin jikinta, amma Ching Ching ta san yadda za ta yi. Ta matsa kusa da babban Robot ɗin da yake sarrafa girkin safe... Ching Ching ta sani cewa Chief Onyx yana son coffee ba tare da sukari da yawa ba...duk da akwai wani a can amma zata ƙara kai masa... Ta kalli Robot ɗin yana haɗa coffee na biyu na Chief... Cikin zafin nama da sauri, yayin da Robot ɗin ya juya, Ching Ching ta ɗauki babban cokali na gishiri ta zuba a cikin kofin shayin Chief, sannan ta juya shi da sauri... "Haka ne," ta raɗa a hankali... "Idan ya sha wannan, lallai zai yi fushi da Gely tunda ita ce take kula da kitchen ɗin!" Ching Ching ta lura da wani akwatin lantarki (Control Panel) a jikin bango wanda yake ba wa Robots ɗin kitchen umarni... Ta tuna wata rana ta ga Gely tana danna wasu lambobi. Ta matsa wurin, ta fara danna maɓallan ba tare da sanin me suke nufi ba... Nan take, Robots ɗin kitchen suka fara hauka! Wani ya fara jefa soyayyen ƙwai a sama, wani kuma ya fara zuba ruwan sanyi a kan biredi... Kitchen ɗin ya hargitse, hayaƙi ya fara tashi!.. Ching Ching ta ɗauki coffee mai gishiri ta ruga da gudu tana kukan ƙarya, ta fito falon dining inda Chief da Gely suke... Ta ajiye kofin akan table tare da faɗa wa jikin Chief Onyx tana kuka mai ƙarfi.. "Uncle! Uncle! Ka tsoratar da ni! Dubi abin da Gely ta sanya Robots ɗinka suke yi! Suna so su kashe ni a kitchen! Gely ta haukata su domin ta huce fushinta a kaina!"... Onyx ya miƙe tsaye cikin firgici, ya ji ƙaurin hayaƙi yana fitowa daga kitchen... "Gely! Me yake faruwa a can?" Gely ta tsaya cak, idanunta suna walƙiya... "Boss, tsarin kitchen ɗin ya fuskanti System Interference... Ba daga gare ni ba ne..." "Ƙarya take! Ita ce!" Ching Ching ta ƙara nanname Chief, tana goge hawayenta a jikin rigarsa, tana yi wa Gely gwalo ta ƙarkashin hannunsa... A daidai nan, Gely ta matso za ta janye Ching Ching daga jikin Chief, sai Chief ya daka mata tsawa.. "Gely! Jeki ki dakatar da haukan da yake kitchen yanzu! Kuma idan na gano ke ce kika haddasa wannan, to akwai matsala!" Gely ta yi shiru, ta juya ta nufi kitchen ɗin. A data center ɗinta, ta san Ching Ching ce ta yi wannan, amma tana jin zafi yadda Chief ya amince da kukan yarinyar nan fiye da rahoton da ita take bayarwa... Ching Ching kuwa, tana ganin Gely ta shiga kitchen, ta ɗauki kofin coffee nan da ta zuba mawa gishiri, ta miƙa wa Chief tana murmushin mugunta.. "Sha kofinka Uncle, ka huce fushin nan. Ni na haɗa maka shi na musamman..." Ching Ching ta tsaya tana kallon Chief Onyx da idanunta masu cike da annurin mugunta, tana jiran ya kurɓi kofin nan mai cike da gishiri domin ya zazzage wa Gely masifa... Tana kishingiɗe a jikinsa, tana nuna alamun tausayi na ƙarya... Chief Onyx ya kai kofin bakinsa, amma daidai lokacin da zai sha, sai ya ga yadda kwayar idon Ching Ching take rawa da murna... Kasancewarsa mutum ne mai matuƙar fiƙira da basira, nan take ya gano cewa akwai wata manufa a tattare da wannan murmushin nata.. Ya sauƙe kofin daga bakinsa, ya kalli kofin, sannan ya kalli fuskar Ching Ching... "Kin ce ke kika haɗa min wannan musamman don na huce?" ya tambaya cikin muryar da ba ta nuna alamar wasa ba... "Eh Uncle... saboda na ga ranka ya ɓaci," ta amsa tana ƙara narkewa a jikinsa... Onyx ya yi wani murmushin gefen baki, ya miƙa mata kofin... "To tunda ke kika haɗa shi da kanki, kuma naga fuskarki ta nuna kina jin ƙishirwa saboda kukan da kika yi, fara kurbawa kiji daɗin abin da kika haɗa min...." Ching Ching ta zaro ido, zuciyarta ta buga tum-tum!.. "A’a Uncle... naka ne ai... ni ba na shan kofi da safe..." "Na ce ki sha!" Onyx ya daka mata tsawa guda wadda ta sanya ta kusan saki fitsari... Ba yadda ta iya, Ching Ching ta karɓi kofin hannunta yana rawa. Ta kai baki ta kurba babban domin ta nuna masa babu komai. Nan take ta ji wani irin ɗaci da gishiri ya ziyarci makogwaronta!.. Gishirin ya kasance mai yawan gaske har sai da ta ji kamar za ta amayar da hanjinta... "Puhhh!" Ta fesar da ruwan a firgice, ta sake kofin akan cinyarta, duk ya ɓata mata kaya ga zafi...furzarwar da tayi a fuskar Chief ta watsa wa, duk ya ɓata masa fuska....itama fuskar ta ya ɓaci... "Meye wannan?" Onyx ya miƙe tsaye, ransa a ɓace... "Gishiri kika zuba min a kofi? Kina so ki kashe ni ne?" Daidai nan, Gely ta fito daga kitchen bayan ta kashe duk hayaniyar da Ching Ching ta haddasa... Ta tsaya tana kallon Ching Ching wadda kofi ya ɓata mata fuska da ta Chief, tana ta tari... Gely ta buɗe wani allo a jikin hannunta, ta nuna wa Chief Onyx bidiyon sirri na kyamarar kitchen.. "Boss, ga dalilin da ya sa kofin yake da gishiri, da kuma dalilin da ya sa Robots ɗin kitchen suka haukace. Shugaba Ching Ching ce ta hargitsa tsarin."... Onyx ya kalli bidiyon, ya ga yadda Ching Ching take ta danna maɓallan lantarki tana dariya. Ya juyo ya kalle ta wadda yanzu gishiri ya fara sanya mata ƙaiƙayi a maƙogwaro... "Kin raina min hankali Ching Ching!" Onyx ya faɗa cikin zafin rai.. "Kin kusan kashe kanki da kanki.... Gely, ɗauke ta ki kai ta kitchen. Tunda tana son danna maɓallan kitchen, to yau duk kwanukan fadar nan ita za ta wanke su da hannunta, kuma ba za ta ci komai ba har sai ta gama!"... Gely ta matso kusa da Ching Ching, ta damƙi hannunta cikin ƙarfi na ƙarfe... "Muje, Shugaba Ching Ching. Lokacin wanke-wanke ya yi." Ching Ching ta fara ihu tana kiran Daddy, amma Onyx ya juya mata baya ya shige sashensa. Gely ta ja ta zuwa kitchen, tana raɗa mata a kunne... "Na faɗa miki, ni na'ura ce, amma na fi ki saurin tunani. Makarkashiyar ɗan adam ba za ta taɓa yin nasara a kan lissafin na'ura ba.".. *Likes ɗinku shine albashin marubuci* 👍 Like 🔁 Share 💬 Comment *👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑* _🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_ ✍🏽 By ASMEETAH WRITER ~Hasken Jajirtattu~ 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ ```JARUMAI WRITERS TEAM``` ▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇 🔗 WhatsApp Channel: https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 📚 ArewaPen: https://arewapen.com/u/asmeetahwriter 📖 Wattpad: https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter 📲 Contact: 09065443871 📅 FARA TURA BOOK: 🔥 01 — 01 — 2026 🔥 📘 BOOK ONE ```MATAKIN FARKO``` CHAPTER 2️⃣5️⃣ *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ* *Wannan part ɗin kam duk ya ƙare akan Chingching* 😅😅😅 Bayan watsewar Party na Gimbiya Maayah, labarin abin da ya faru da yadda ta wulakanta mutane, da yunkurin kisan da aka so yi mata, duk ya karaɗe kowane lungu na fadar Alhamra.. Duk da cewa Maayah ba ta gayyaci 'yan uwanta Gimbiyoyi ba, kowacce ta samu labarin abin da ya faru ta hannun hadimanta... Sashen Gimbiya Zayana.. Tana zaune a kan gadon ta na alfarma, hadimanta biyu suna yi mata fanning da furen peacock. Lokacin da babban hadiminta ya kawo mata labarin dambarwar da aka yi a wurin taron Maayah, Zayana ba ta ko motsa ba, sai dai wani murmushi na raini da ya subuce mata... “Taron banza, taron hargitsi,” Zayana ta faɗa cikin muryar nan tata ta nuna isa... “Maayah har yanzu ba ta san ma'anar kasaita ba. Gayyatar taron abokai masu kuɗin ƙarya da 'yan banzan birni... ai dama wannan taron ba kala ta ba ce. Ni ba sa'ar ta ba ce da zan zauna a cikin wannan kazantar... Girmana da darajata sun wuce in zauna a inda ake dukan mutane da bulala don nishaɗi... Ni taro na, na sarakuna ne, ba na 'yan koli ba.”... Ta juya kai gefe, tana ƙara gyara zaman rawanin dake kanta, tana nuna cewa ko ambaton taron Maayah ma ɓata lokacinta ne.... Sashen Gimbiya Ayat.. A ɗayan bangaren fadar, Gimbiya Ayat tana cikin ɗakin karanta-karantanta wato Library room dinta... Lokacin da aka shigo mata da labarin cewa Maayah ta gama taron ta cikin ɓacin rai, Ayat ba ta ma ɗaga kai ta kalli mai maganar ba... “Kada ki sake kawo min labarin Maayah a yanki nan,” Ayat ta faɗa a takaice, idonta yana kan littafin dake hannun ta... “Ta gayyaci wanda ta ga dama, sannan ta ƙi gayyatar wanda ta ga dama. Ko an gayyace ni, shin zan je ne? Ko oho! Rayuwarta ce, damuwarta ce. Idan ta ga dama ta ƙona fadar ma, matukar ba ɗakina ne ya kama wuta ba, ba ruwana.”... Sashen Gimbiya Yumna... Ita kuwa tana zaune ne a lambun fadar tana shan iska tare da ƙawayenta.. Lokacin da aka fara tsegumin rashin gayyatar su, Yumna ta gyara zama tana wasa da zoben hannun ta... “Haba, ku daina damuwa,” Yumna ta faɗa tana murmushi... “Ai dama Maayah taron kawaye da abokan makaranta ta yi. Mu 'yan gida ne, mu na gida ne ai... Babu komai idan ba a gayyace mu ba, kowa da kalar nishaɗinsa. Idan mu ma za mu yi namu, ai za mu yi ne yadda muke so. Ba sai an sanya kishi a ciki ba.”.. Duk da kalaman Yumna sun nuna rashin damuwa, amma a cikin ranta ta san cewa Maayah ta yi hakan ne don nuna cewa ita ce mace mai iko a fadar... ✨✨✨ Pavilion City An kwashe kwana biyu Ching Ching tana ɗanɗana takurar muryar Gely. Ko’ina ta juya, Gely tana biye da ita, tana takura mata da aiki da dokoki masu tsanani... Chief Onyx kuwa ya daƙe, ya ƙi sauraron duk kukan shagwabar da take yi, hakan ya sanya ta fara jin cewa kowa ya tsane ta a gidan... *A Yau...* Ganin yadda Ching Ching ta yi sanyi, Chief Onyx ya yanke shawarar ba ta hutu... Ya ba ta wata kwamfuta ta musamman, ya sanya mata fina-finan Indiya masu ban tausayi da nishaɗi don ta nutsu ta yi kallo... Ching Ching ta koma gefe ɗaya a falo, ta maƙale a kan kujera tana kallon film, idanunta sun cika da ƙwallar tausayin jaruman film ɗin.. A ɓangare guda kuwa, Chief Onyx da Gely suna cikin babban ofishinsa na gida (Private Office).... Wurin ya yi tsit, sai ƙarar na’urori da danna maɓallan kwamfuta. Gely tana tsaye kusa da shi, tana karanta masa wasu muhimman bayanai na sirri, yayin da shi kuma yake shigar da su cikin tsarin bincikensa... Bayan sun gama aikin, Chief ya sauƙe ajiyar zuciya yana ƙoƙarin miƙewa don ya huta... Kwatsam! Sai Gely ta yi wani irin tangal-tangal kamar za ta faɗi ƙasa, jikinta ya fara wata irin rawa... "Boss..." ta ƙira sunansa cikin wata murya wadda ba a saba ji daga robot ba... Onyx ya zabura a ruɗe, ya tashi da sauri ya riƙo ta kafin ta kai ƙasa. Saboda ƙarfin jikinta da nauyinta na ƙarfe, sai ya jawo ta jikinsa, ta tsinci kanta a zaune daram a kan cinyarsa, yayin da hannuwansa suke kewayye da ita. "Gely! Me yake faruwa? Akwai matsala a tsarin jikinki ne?" Onyx ya tambaya cikin damuwa, fuskarsa tana kusa da tata sosai. Gely ta ɗaga idanunta waɗanda suka sauya launi zuwa wani haske mai sanyi, ta kalle shi cikin ƙwayar ido... "Boss... na ji wani irin System Overheat ne a ɓangaren sarrafa saƙonnina. Ina jin kamar duk wayoyin jikina suna neman narkewa ne idan ina kusa da kai. Na kasa gano dalilin wannan matsalar a lissafina.".. Wannan ƙarya ce tsagwaronta, Gely ta ƙirƙiri wannan yanayin ne don kawai ta mallaki damar zama a jikin Chief Onyx. Ta sani cewa idan ta yi hakan, zai rarrashi jikinta kamar yadda yake rarrashin Ching Ching... Ta matso da fuskarta daf da tasa, hancinsu yana gogayya da juna... "Ina jin kamar akwai wani abu da kake buƙata daga gare ni, wanda ni kuma nake son ba ka shi... amma wannan yarinyar tana toshe duk hanyoyin." Onyx ya tsaya cak, numfashinsa ya fara sarƙewa. Ya kalli leɓen Gely wanda aka ƙera shi da wani irin roba (synthetic skin) mai taushi kamar na mutum... Ya kasa gaskata cewa Gely ce take faɗar waɗannan kalaman. Ga ɗumin jikinsa yana neman ratsa na'urorin jikinta. A daidai lokacin da bakinsu yake neman haɗewa, sai aka ji ƙarar buɗe ƙofar ofishin... Ching Ching ce ta shigo da gudu, riƙe da kwamfutar a hannunta tana kuka.. "Uncle! Uncle! Dubi abin da ya faru a film ɗin nan! Jarumin ya rasu..." Maganar ta maƙale a maƙogwaronta sa'ilin da ta ga abin da yake faruwa. Gely a zaune a kan cinyar Chief, suna fuskantar juna kamar za su yi sumba... Kwamfutar hannun Ching Ching ta kuɓce ta faɗi ƙasa... Gararrass!... Kwamfutar da take hannun Ching Ching ta rabe gida biyu a ƙasa, amma hayaniyar faduwarta ba ta firgita Gely ba. Maimakon Gely ta tashi daga kan cinyar Chief Onyx cikin kunya kamar yadda ɗan adam zai yi, sai ma ta ƙara nannaɗe hannuwanta a wuyan Chief, tana ƙara tura kanta a saitin fuskarsa. Ching Ching ta tsaya cak, numfashinta ya fara fita da sauri-sauri, idanunta suka firfito waje... "Uncle... me... me kuke yi?" muryarta tana rawa... Onyx ya so ya ture Gely amma ta ƙara matse shi, sannan ta juyo da kanta a hankali ta kalli Ching Ching da wani irin kallo na isa da nuna iko... "Baki ga abin da yake faruwa ba ne, Shugaba Ching Ching?" Gely ta faɗa cikin murya mai sanyi wadda take amo na ban mamaki... "Boss yana kula da ni ne. Tsarin jikina yana buƙatar ɗumin jikinsa domin na daidaita. Shin ba ke ce kika ce 'ba a miki tsawa, sai dai lallashi' ba? To, ni

Chapter 22 of 39