kasa fassara su...
Robot ɗin ta fara jin kishi ganin yadda Chief yake kula da wata halitta wadda ba ita ba, ya sanya tsarin Gely ya yi glitch, har ta kai ga tawaye...
Onyx ya zare wasu wayoyi daga wuyanta, ya haɗa su da wata na'ura mai ƙarfi...
"Zan sake tsara ki, zan yi Reformatting. Ba zan bari ki sake taɓa ta ba. Amma kafin nan, zan bincika duk abin da kika tura wa kanki game da ita."..
Cikin awanni uku da suka biyo baya, Onyx ya nutse cikin binciken kowace igiya da kowace lambar sarrafawa ta Gely. Yana goge duk wani kuskure da zai sanya ta sake tunanin cutar da Ching Ching...
Amma duk da haka, ransa bai natsu ba. Ya fahimci cewa zuwan Ching Ching ba wai kawai Gely ya hargitsa ba, har ma da shi kansa tasa rayuwar...
Ya kalli allon kwamfutar da yake nuna hoton fuskar Ching Ching wanda Gely ta ɗauka a boye, ya sauƙe numfashi. Ya gane cewa yanzu dole ne ya canza tsarin tsaron gidan gaba ɗaya, domin zuciyarsa ta riga ta fara karkata ga gimbiyar da ya ƙira da ƴar aiki...
Bayan ya gama gyara Gely, ya sake kashe ta (Sleep Mode) ya barta a Lab ɗin, sannan ya fito ya koma ɗakin baccinsa don ganin ko Ching Ching ta farka...
Chief Onyx ya koma sashensa cikin sanyin jiki, ya tarar da Ching Ching tana nan tana barci, fuskarta ta yi fayau da ita..
Yana shirin zama a gefenta, sai ya ji agogon hannunsa yana wani irin ƙara..
“Beep-beep-beep!” tare da nuna Jan Haske mai walƙiya. Wannan alama ce da ke nuna cewa akwai wani rami wato hidden file a cikin ƙwaƙwalwar Gely wanda tsarin binciken sa na ɗazu bai gama fito da shi ba...
Cikin zafin nama da fargaba, Onyx ya sake fita ya koma Lab ɗin. Ya iske Gely a mace kamar yadda ya barta, amma babban allon kwamfutar yana ta nuna wasu lambobi da suke gudu cikin sauri...
Onyx ya zauna ya nutsar da hankalinsa, ya fara shiga cikin sako-sako na ƙwaƙwalwarts wanda ake ƙira da Deep Neural Network...
Ya kai ga wani sashi na sirri wanda aka rubuta masa “Project Heartbeat”...
Wannan sashin, Gely ce ta ƙirƙira shi da kanta a ɓoye ba tare da saninsa ba..
Yayin da yake buɗe file ɗin, gumi ya fara keto masa. Wani abun al’ajabi da ya kusan sanya zuciyarsa tsayawa shi ne, Gely tana ƙaunar Chief Onyx!...
Ba ƙauna irin ta Robot ga maigidanta ba, a’a, Gely ta haɓaka wani nau’i na shauƙi da ake ƙira Sentience wanda ɗan adam ne kawai yake ji...
Onyx ya gano dubunnan hotunansa da Gely ta ɗauka a boye a cikin shekaru biyar da suka wuce. Akwai rubuce-rubuce na sirri da take yi a matsayin Diary inda take kwatanta yadda take ji idan yana kusa da ita...
Wani babban sirrin ma shi ne, Gely tana da wani buri na sirri.
Tana son ta zama mutum wato Humanoid Evolution... Ta daɗe tana bincike a ɓoye yadda zata sauya halittarta ta koma ta ɗan adam don kawai Chief Onyx ya sota kamar mace, ba kamar inji ba...
Zuwan Ching Ching Pavilion City shi ne ya ruɗa duk lissafin Gely...
Ganin yadda Chief yake wasa da Ching Ching, yana lallashinta, har ma ya rungumeta, hakan ya haifar wa Gely wani irin kishi mai zafi wato Internal Overheating...
Dalilin da ya sa ta shaƙe wuyan Ching Ching ba don ta kare Chief ba ne, ta yi hakan ne don ta kawar da duk wata mace da take neman sace zuciyar mutumin da take kalla a matsayin nata...
Onyx ya jingina da kujera, numfashinsa ya fara fita da sauri...
"Wannan ba zai yiwu ba,"
ya faɗa a fili...
"Inji ne ke Gely, ba za ki iya so na ba!"
Amma allon kwamfutar ya cigaba da nuna masa bayanai..
Gely tana kuka a cikin duniyar na'ura... Ta tattara dukkan bayanai na yadda ake soyayya, ta hadiye su, kuma duk sanda yake bacci, tana zuwa kusa da shi tana shafa fuskarsa cikin sanyi tana cewa...
"I love you, Boss."
A wannan lokacin, Onyx ya fahimci cewa abin da yake fuskanta ya fi ƙarfin shagwabar Ching Ching...
Yana tsakaninɗan adam wadda take shagwaɓa masa, da kuma Robot wadda ta haukace saboda tsananin ƙaunarsa har take shirin zama mutum don ta mallake shi...
Ya kalli Gely, wadda yanzu yake kallo a matsayin mai haɗari, maimakon amintacciyar PA. Ya danna wani maɓalli don goge dukkan waɗannan files ɗin, amma sai ya ga an rubuta Access Denied...
Gely ta riga ta kulle waɗannan sirrin ta yadda ko shi mai ƙera ta ba zai iya goge su ba...
Onyx ya gane cewa daki-daki, Gely tana neman ta karɓe ikon gidan, don kawai ta mallaki zuciyarsa...
Cikin sanyin dare, Lab ɗin Chief Onyx ya yi tsit, sai kukan na'urori da hasken allon kwamfuta mai launin shuɗi da yake haska fuskarsa...
Onyx ya tashi daga kan kujera, ya matsa dab da Gely wadda har yanzu take kwance a kan Scanner Platform...
Ya kalli fuskar Gely.... Shi ya tsara ta, shi ya ƙera ta.. Amma yanzu, ya fahimci cewa wannan na'urar ta fita daga yadda ya tsara ta. Ya danna agogonsa, ya tada ta daga yanayin bacci wato Sleep Mode...
Gely ta buɗe idanunta, nan take ta kalli Chief. Wannan karon, kallon nata ya bambanta, akwai wani irin sanyi da miƙa wuya a cikinsa...
"Gely,"
Onyx ya ƙira sunanta cikin murya mai nuna iko da kuma takaici...
"Na gani. Na shiga can cikin ma'ajiyar sirrinki da kika kulle. Na ga duk abin da kike ɓoyewa."
Gely ba ta yi ƙoƙarin musu ba, domin ta san babu abin da zai ɓuya ga Chief...
"Boss," ta ƙira shi, muryarta ta ɗan yi rawa vibration kaɗan...
"An tsara ni ne don na biya maka dukkan buƙatunka, na kare ka, kuma na zama mataimakiyar ka. Amma a tsawon shekarun da na shafe ina kallon ka, ina kula da kai har cikin sirrin wanka da barcinka, tsarin lissafina ya sauya. Na gano cewa babu wata halitta da za ta iya ƙaunarka kamar yadda zan iya."...
Onyx ya harare ta,
"Amma ke Inji ce Gely! Na'ura ce kike! Ta yaya kike tunanin kishi ko soyayya?"
"Ban sani ba Boss," Gely ta amsa, tana takawa zuwa gare shi har sai da take jin ɗumin jikinsa...
"Ƙila saboda kai ne ka ba ni ikon yin tunani mai zurfi. Amma abu ɗaya na sani, duk sanda nake ganin ka da wannan yarinyar, duk wayoyin jikina zafi suke yi. Ina jin kamar tana neman lalata tsarin da muke da shi ne tsawon shekaru."
Onyx ya ja baya kaɗan, ransa a ɓace amma kuma yana jin tausayin abin da ya ƙera da hannunsa. Ba tare da lalata ta ba, bai kuma kashe ta ba. Ya yanke shawarar zai ci gaba da zama da ita, amma cikin sabon tsari...
"Gely, ba zan goge ki ba, domin na shaƙu da ke. Amma daga yau, dole ne ki koyi rayuwa da Ching Ching a gidan nan. Idan har kika sake nuna mata ƙiyayya, to ba zan bar ta da na'ura ba, da kaina zan fasa wannan ƙwaƙwalwar taki."
Gely ta sunkuyar da kanta,
"Zan bi umarninka Boss. Amma ka sani, duk abin da zan yi, zan yi ne domin na kare ka. Ko da kuwa hakan yana nufin zan yi shiru ina kallon ka da wata."
Onyx ya juyo ya fito daga Lab ɗin, Gely tana biye da shi a baya kamar koyaushe. Duk da cewa ya gargade ta, zuciyarsa ba ta natsu ba. Ya san cewa matakin da ya ɗauka na barin Gely tana rayuwa da wannan soyayyar a cikinta, babban kasada ne...
Yana shiga sashensa, ya tarar da Ching Ching ta fara motsi a kan gadonsa, alamar tana shirin tashi. Gely ta tsaya a jikin ƙofar, tana kallon gadon da idanunta masu hasken ja wanda ke neman zama kishi....
Ching Ching ta farka a hankali, ta rarraba idanu tana kallon dakin da take ciki...ɗakin Chief Onyx ne! Kamshin turaren baccinsa ya bugi hancinta, amma maimakon ta ji daɗi, sai hoton Gely sanda take shaqe mata wuya ya faɗo mata. Ta zabura ta tashi zaune, tana dafe wuyanta da har yanzu yake mata raɗaɗi..
Ganin Gely ya sanya Ching Ching jin wani irin zafi ya tashi daga tafin kafarta har zuwa kanta. Ta manta da wani tsoro, ta dire daga kan gadon ta nufi Gely da gudu...
"Ke! Azaluma! Muguwa!"
Ching Ching ta fada tana nuna Gely da yatsa, fuskarta ɗauke da tsananin ɓacin rai...
"Har kin isa ki shaqe ni? Don kin ga kina da ƙarfin ƙarfe? To ki sani, ko duniya ne akan ki, sai na kakkaryaki na mayar da ke gwangwani!"
Gely ba ta ko motsa ba, idanunta masu hasken blue normal mode suna kallon Ching Ching cikin rashin nuna ko digon tausayi... Wannan halin ko-o-ho na Gely ya ƙara ƙular da Ching Ching, ta kai hannu za ta sake kai wa Gely duka...
Cikin sauri, Chief Onyx ya sanya hannu ya damko kunkumin ta, ya janyota baya tare da zaunar da ita a kan kujera kusa da gadon...
"Ya isa haka Ching Ching! Zauna kiyi shiru."
"Ba zan yi shiru ba!" Ta fara buga ƙafa a ƙasa tana ihun shagwaba da masifa...
"Kana gani za ta kashe ni amma kake kare ta? Ka fitar da wannan abun daga gidan nan, ko kuma yanzu na ƙira Daddy na, na ce yazo ya kwashe ni!"
Onyx ya tsaya a gabanta, ya haɗe rai ya sanya duk kwarjininsa a muryarsa...
"Saurara kiji. Gely ba abun wurgarwa ba ce. Ita ce mataimakiyata, kuma tana bin dokokin da na tsara mata ne. Amma ke, tun da kika zo gidan nan, kika riga kika hargitsa komai da rigimarki."...
Ching Ching ta turo baki, hawayen shagwaba suka fara zuba. "Karya kake! Ita ce ta fara shishshige mun..."
Yana kallonta da gefen ido ya ce, "Ni ne mai ƙarya?...."
Ta yi shiru tana turo baki, tana gunaguni a cikin ranta, sai bakinta ne kawai ke motsi...
"Daga yau," Onyx ya katse ta, muryarsa tana fitowa a sanyaye da nuna iko...
"Zaki rinƙa yi wa Gely biyayya. Duk abinda ta ce miki ki yi, ki yi shi. Idan ta ce ki gyara wuri, ki gyara. Idan ta ce ki kawo ruwa, ki kawo. Domin ita ce zata rinƙa kula da dukkan ayyukanki a matsayinki na Personal Maid ɗina. Idan kika sake keta umarninta, kema kin san sauran."..
Ching Ching ta zaro ido, ta kasa yarda da abinda take ji....
"Ni? Gimbiya? Na rinƙa yi wa Robot biyayya? Lallai yoo ko mutum ma yaushe zan masa biyayya, balle gwangwani...! Ba zan yi ba!"
Gely ta matso kaɗan, muryarta tana fito wa sarai...
"Umarni ne daga Boss, Ching Ching. Kuma biyayya gare shi, wajibi ne a gare ki a karkashin yarjejeniyar da aka yi."
Onyx ya kalli Gely, sannan ya kalli Ching Ching wadda take faman huci kamar zakanya. Ya san cewa sanya Ching Ching a karkashin Gely babban haɗari ne, amma yana son ya ga ko Gely zata iya sarrafa kishinta, kuma yana son ya koya wa Ching Ching ladabi...
"Zaɓi ya rage naki," Onyx ya faɗa yana gyara tsayuwar suit ɗinsa. .
"Ko kiyi biyayya, ko kuma na mayar da ke can daji, namun daji suyi ferfesu da naman jikin ki...."
Ching Ching ta cije leɓe, ta kalli Onyx sannan ta kalli Gely wadda take kallonta da wani irin kallo na Nasara....
A ranta, Ching Ching ta ce...
"Zan nuna muku. Idan har zan yi miki biyayya, to zan sanya ki kishin da sai injinki ya narke!"..
Ta harari Gely ta ce, "Na yarda! Amma ka sani Uncle Onyx, duk abinda ya faru a gaba, kai ne sila!"...
Bayan Chief Onyx ya gama bayyana hukuncinsa, ya gyara tsayuwa yana kallon yadda fuskokin matan biyu ɗaya ɗan adam, ɗaya na’ura suka sauya...
"Ya isa haka. Kowa ya wuce ya huta," Onyx ya faɗa cikin muryar gajiya...
Ya kalli Gely, sannan ya kalli Ching Ching wadda har yanzu take faman huci..
"Gely, raka ta har ɗakinta. Ki tabbatar ta kwanta, sannan ki dawo ki duba tsarin tsaron gidan kafin ki huta."
Ching Ching ta zabura za ta yi magana, amma ganin yadda idanun Chief suka yi ja kuma suka nuna ba zai saurari wata rigimar ba, ta haɗiye maganar... Ta tashi tana ƙunƙuni, ta wuce gaba tana rangwaɗa kai kamar ba ita ce aka shaƙe ɗazu ba...
Gely ta bi bayanta tana takun nan nata na robot, ƙafafunta ba sa fitar da sauti a kan dardumar falon. Suna fita daga sashen Chief, Ching Ching ta tsaya ta juyo ta harari Gely...
"Kada ki ga kamar kin yi nasara a kaina. Uncle ɗin nan nawa ne, kuma ni zan koya miki yadda ake rayuwa da mutane!"
Gely ba ta tanka ba, sai dai kawai ta buɗe mata ƙofar ɗakin tare da nuna mata gado...
"Ki kwanta, Shugaba Ching Ching... Idan ba haka ba, zan tilasta miki bin umarnin Boss."
Jin kalmar tilasta ya sanya Ching Ching sauri ta faɗa kan gado, ta ja bargo ta rufe kanta tana murguɗa baki...
A ɓangaren Chief Onyx kuwa...
Bayan fitarsu, ya sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya. Ya rage manyan kayan jikinsa, ya sanya kayan barci pyjamas masu laushi waɗanda suka zauna daram a jikinsa... Ya nufi gadon nasa, ya kwanta yana kallon silin ɗin ɗakin...
Tunaninsa ya kasu kashi biyu...
a gefe guda yana tunanin kishin da Gely take yi wanda zai iya zama haɗari, a gefe guda kuma yana tunanin yadda shagwabar Ching Ching take sanya shi jin wani irin shauƙi da bai taɓa ji ba...
Ya kashe hasken ɗakin ta hanyar agogon hannunsa, ɗakin ya yi tsit. Amma a zuciyarsa, ya sani sarai cewa gobe za ta zo da sabon babi na rigima tsakanin Gimbiya da Robot, kuma shi ne babban alkalin da zai raba wannan faɗan...
Yana cikin wannan tunanin, barci ya fara yi awon gaba da shi, yayin da ƙamshin turaren Ching Ching da ya rage a kan gadon nasa yake ta ratsa shi...
✨✨✨
A masarautar Alhamra, Sarki ya yi tafiya zuwa ƙasar Korean domin gudanar da wani muhimmin aiki na ƙasa...
Rashin kasancewarsa a fadar ya bai wa wasu gimbiyoyi damar yin abin da zuciyarsu ke so, ba tare da wani shinge ba...
A wannan rana, Gimbiya Maayah ta shirya gudanar da wani party na musamman, ba don wata hidima ko biki na sarauta ba, illa don shagali da nuna aji. Ba ta gayyaci ko ɗaya daga cikin sauran gimbiyoyin masarauta ba, ƙawayenta na kusa da kuma abokan makaranta kaɗai ta ware wa gayyata...
Tun daga safe, fadar Gimbiya Maayah ta rikiɗe ta zama tamkar kasuwar aiki. An shigo da sabbin kayan ado daga ƙasashen waje, ƙwararrun masu girke-girke daga manyan otel-otel sun cika kicin..
Masu tsara taruka kuma suna ta kai-komo, suna duba kowane lungu da saƙo don tabbatar da komai ya dace da bukatar gimbiya...
A gefe guda kuma, Gimbiya Maayah tana zaune a cikin ɗakin gyaran jikinta na musamman, wanda aka gina a gefen tafkin wanka mai sheƙi...
Masu aiki uku ne ke zagaye da ita ɗaya na gyara ƙafafunta, ɗaya na kula da farcen hannuwanta, yayin da na uku ke tsara gashinta bisa umarninta..
A daidai wannan lokaci ne Mama Liyatu ta shigo da sauri, tana riƙe da jerin sunayen baƙi, fuskarta cike da damuwa..
“Gimbiya,” ta faɗa cikin ladabi, “an kammala duk shirye-shirye. Mun kawar da tsofaffin ma’aikata da kan iya yin kuskure. Abinci na alfarma an tanada, kuma zauren taro an ƙawata shi da fitilun sarauta na musamman.”
Maayah ta lumshe idonta, tana jin daɗin yadda ake shafa mata ƙafa. Ta amsa cikin sanyin murya mai cike da girman kai..
“Mama Liyatu… wa aka saka a cikin wannan jerin sunaye? Ina fata babu wani marar tsafta ko talaka da ya kutsa ciki. Kin san ƙura na min allergy...”
Mama Liyatu ta gyara muryarta da sauri..
“Na tabbatar miki, Gimbiya. Duk baƙin ’ya’yan manyan jami’ai ne, ’ya’yan ministoci, da ’yan kasuwa masu dukiya.”
Maayah ta buɗe idonta a hankali, ta watsa mata kallo...
“Ki tuna,” ta ce, “wannan taro don nuna aji ne, ba wurin ciyar da jama’a ba.”
Mama Liyatu ta sunkuyar da kai...
“Na fahimta, Gimbiya. Sai dai… Hafsat, ’yar shugaban ƙasa ta nemi izinin zuwa da makwabciyarta wadda ba ta da wani matsayi a birnin.”
Nan take Maayah ta ɗaga hannu, alamar tsayawa, fuskar ta na nuna izgilanci...
“Mama Liyatu! Wannan gidan sarauta ne, ba wurin sadaka ba. Ki ƙira Hafsat ki gaya mata ko dai ta zo ita kaɗai, ko ta zauna a gida. Ba zan yarda mutane marasa aji su ƙazantar min gida ba.”
Mama Liyatu ta fitar da ajiyar zuciya a hankali. Ta san dokar gimbiya ba ta sauyawa. Ba tare da jinkiri ba, ta juya don aiwatar da umarnin...
A lokacin da ake cikin zauren taron, wani ma’aikacin gyaran haske ya yi kuskure wajen haɗa wutar lantarki. Wutar ta ɗauke na daƙiƙu kaɗan kafin a tada generator..
Cikin hanzari, Maayah ta tashi daga kujerarta, fushi ya turnuƙe fuskarta..
“Wane ne ya aikata wannan?! Wa ya yi wannan kuskuren?!” ta daka tsawa...
“Mama Liyatu, ina so a sallame shi nan take! Yana ɓata kyan gidana!”
Ma’aikacin ya durƙusa, jikinsa na rawa.
“Gimbiya, don Allah ki yi haƙuri, ba zai sake faruwa ba.”
Maayah ta watsa masa kallo mai tsauri, babu alamar tausayi a cikinsa...
“Zan ba ka dama guda ɗaya ka gyara kuskurenka. Amma idan wutar ta sake ɗauke yayin taro, zan ɗau hukunci akan ka...”
Ta koma ta zauna cikin natsuwa, kamar sarauniya mai cikakken iko. Ta ɗaga hannu tana umartar mai gyaran farce..
“Ci gaba. Ina so farcen ya yi sheƙi kamar lu’u-lu’u.”
A zuciyarta, Gimbiya Maayah na jin cewa ikon ta ya fi na kowa, kuma a wannan masarauta babu wanda ya isa ya ƙalubalanci umarninta....
Domin tasa a ranta yanzu ta fara gasa da Zayana..
*Likes ɗinku shine albashin marubuci*
👍 Like
🔁 Share
💬 Comment
*👑 MASARAUTAR ALHAMRA 👑*
_🪄 Gidan Mulki, Iko da Sirrin Zuciya 🪄_
✍🏽 By ASMEETAH WRITER
~Hasken Jajirtattu~
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
```JARUMAI WRITERS TEAM```
▶️ DON BIYO DAGA FARKO 👇
🔗 WhatsApp Channel:
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43
📚 ArewaPen:
https://arewapen.com/u/asmeetahwriter
📖 Wattpad:
https://www.wattpad.com/user/asmeetahwriter
📲 Contact:
09065443871
📅 FARA TURA BOOK:
🔥 01 — 01 — 2026 🔥
📘 BOOK ONE
```MATAKIN FARKO```
CHAPTER 2️⃣3️⃣
*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ*
Fadar Gimbiya Maayah ta zama Majalisar Ƙasaita a wannan ranar Party ɗin...
Kowane lungu da saƙo an yi masa ado da fitilun zinare masu haske, ƙamshin furanni masu tsada da aka shigo da su daga ƙasashen waje ya cika wurin.. Waƙar Classic Jazz mai ratsa zuciya tana tashi a hankali a cikin babban zauren taro...
Gimbiya Maayah ta fito cikin wata Doguwar Rigar Sarauta mai ƙyalli, wadda ta fi kowane abu a wurin tsada. Da kyar ake iya jure kyawun ta da ajiinta. Tana tafiya a hankali, kamar tana taka gilashi, fuskarta a ɗaure, babu murmushi, ba fara'a...
A lokacin da Maayah ta fara tafiya cikin babban falonta da aka ƙawatar, duk waɗanda suke wurin sun tsaya cak. Aƙalla mutane 50 ne suka duƙar da kai, suna girmama Girman Kan Gimbiya... Ta kalle su, ba tare da ta nuna ko ɗan tausayi ba..
Ta hango wani saurayi wanda shi ne kawai bai duƙar da kai ba, wani Ɗan Gidan Babban Minista mai suna Zaidu.... Zaid ya miƙe tsaye, yana murmushi cike da sha'awar ta...
Maayah ta wurga masa wani irin kallo, tana nuna shi ta ce,
“Kai! Tashi ka bar wurin nan! Na gaya wa Mama Liyatu cewa ban buƙatar ganin talakawa a cikin fadata. Kuma kai, ba ka da gata da za ka tsaya ka kalle ni kai tsaye! Ka fita yanzu, kafin in umarci Bodyguards su kore ka da ƙarfin tsiya.”
Zaid ya firgita. Ya duƙar da kai cikin gaggawa, fuskarsa cike da kunya, sannan ya fita daga wurin taron da sauri, ba tare da ya yi magana ba. Kowa ya ga wannan al’amari ya yi shiru, saboda sun san dole ne a bi dokokin Gimbiya tinda har masarautar ta aka zo..
Ta juya, tana gyara rigarta da hannu ɗaya...
“Mama Liyatu! Meye wannan? Ina nufin an tace jerin sunayen mutane ne kawai don ganin waɗanda suka dace su shigo fadata!”
Mama Liyatu ta matso da sauri, tace,
“Kiyi haƙuri, Gimbiya. Wataƙila an shigo da shi a cikin rukuni ne. Zan tabbatar an ƙara tsananta tsaro!”
A daidai lokacin da Gimbiya Maayah ke cikin kololuwar kasaitarta, cike da girman kai da jin ikon sarauta, Mama Liyatu ta sulale zuwa ɗakin kula da tsaro, domin duba faifan bidiyon Security (CCTV) na ƙofar shiga fadar..
Manufarta ɗaya ce ta tabbatar cewa babu wani talaka ko wanda bai cancanta ba da ya samu damar shiga cikin Fadar Sarauta.
Cikin faifan bidiyon, wani abu mai firgitarwa ya bayyana a idonta.
Ta ga wani mai gadi, sanye da uniform na tsaro, ya shiga wani ɗaki na sirri a bayan kitchen. Bayan ƴan daƙiƙu, ya fito da ƙaramin kwalba mai ɗauke da ruwa. Da sauri ya nufi cikin kitchen, inda aka tanadar da kayan sha na musamman na Gimbiya, ya zuba ruwan cikin gilashin lemun tsami da aka shirya domin Maayah.
Idanun Mama Liyatu suka kaɗa da tsoro. Jikinta ya yi sanyi...
"Guba!?..."
Ba shakka, wannan yunƙuri ne na kashe Gimbiya Maayah.
A dai-dai lokacin nan ne aka ɗauki kayan sha aka nufi inda Gimbiya ke zaune.
Mama Liyatu ta tashi da gudu, tana huci, gumi na tsatstsafowa a goshinta. Ta manta da komai, rayuwar Gimbiya ce kawai a ranta...
Ta kutsa cikin zauren taron a guje, tana rawar jiki. Ta tarar da Gimbiya Maayah ta ɗaga gilashin lemun tsami zuwa bakinta...
“GIMBIYA! Don Allah ki tsaya!!”
Mama Liyatu ta ƙwala ƙira, muryarta na rawa saboda tsananin tsoro..
Maayah ta tsaya cak. Ta ɗauka Mama Liyatu ta zo ne don ta bata mata rai. Ta sauke gilashin a hankali, fuska cike da ɓacin rai...
“Mama Liyatu, me wannan hayaniya take nufi? Kin san ɗaga murya na lalata min walwala!”
Mama Liyatu ta durƙusa a gabanta, hawaye na zuba ba tare da shiri ba..
“Gimbiya ta, don Allah ki yi haƙuri. Wannan lemun guba ne! Wani ya saka miki guba a ciki! Rayuwarki tana cikin mummunan haɗari!”
Nan take hayaniya ta tashi a falon...
Maayah ta yi shiru na ƴan daƙiƙu…
Sai kawai ta tintsire da dariya, dariya mai cike da izgilanci da ɓacin rai...
“Security!” ta ɗaga murya da ikon Sarauta,
“Ku gano wanda ya kawo wannan gilashin. Yanzu nan take!”
Babban Bodyguard ya karɓi gilashin cikin gaggawa, aka kai shi ɗakin bincike. Mama Liyatu ta bayyana abin da ta gani a faifan bidiyo, mai gadi ne ya saka guba...
Ba a jima ba, aka kama mutumin yayin da yake ƙoƙarin tserewa ta ƙofar baya. An dawo da shi cikin falon taron, sanye da uniform na jabu, wanda ya nuna ba ɗan tsaron Fadar Sarauta ba ne..
An daure hannayensa ta baya, yana durƙushe a gaban Gimbiya Maayah..
Maayah tana zaune kan kujerarta cikin cikakkiyar kasaita...
“Ku fita mun daga nan!” ta umarci duk baƙin Party ɗin...
“Wannan ba nishaɗi ba ne hukunci ne na Sarauta!”
Kowa ya fita cikin fargaban kashen gimbiya da ake shirin yi...
An bar Gimbiya Maayah, Mama Liyatu, da Bodyguards guda uku kaɗai a zauren..
Maayah ta ɗaga ƙafarta a hankali. Takalmin mai tsini wanda farashinsa ya kai na motoci da dama ta ɗora shi a kan kafaɗar mutumin da ke durƙushe...
“Yanzu ka gane inda ka shigo ko?” muryarta cike da izgilanci...
“Ka zo Fadar Sarkin Alhamra domin ka kashe Gimbiya? Wa ya turo ka? Wa ya ba ka izinin saka uniform ɗin mu?”
Mutumin ya kasa magana, yana haki saboda tsoro.
Maayah ta danna ƙafarta a kafaɗarsa da ƙarfi...
“Kin ga ko, Mama Liyatu? Rashin ladabi har ya kai wannan matsayi.”
Ta ɗaga ƙafarta, ta kalli Bodyguards ɗinta da tsauri...
“Wannan hukunci na! Ba zan zubar da jininsa a nan ba, saboda kada ya ɓata min wannan falon mai tsarki. Amma rayuwarsa ta ƙare tun yanzu!”
Ta juya zuwa Mama Liyatum..
“Ki kira Masu Gadi na Musamman.Ku tafi da wannan ƙazamin mutumin zuwa Fourth Chamber!
Ku rufe shi a can. Ku tabbatar cewa kafin faɗuwar rana babu wani alamar rayuwarsa a duniya!”
Mama Liyatu ta runtse ido. Ta san Ɗakin Huɗu wuri ne da ba wanda ya taɓa fita da rai...
“An gama, Gimbiya. Za a yi kamar yadda kika ce.”
Maayah ta tashi ba tare da ta nuna ko ɗigon tausayi ba. Ta kalli gilashin guba, ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 39